Showing 15001 words to 18000 words out of 127530 words

Chapter 6 - CANJIN RAYUWA

16 Oct 2024

8162

ce,suna na lsmail,kai fa?ya ce hamisu, kuma nine direban yaran gidan nan.ga daki na nan kusa da na ka,mu biyu ne a cikin dakin,ni da me share-share,game da kula da fulawoyi.lsmail ya ce, ALLAH ya sa mu amfani juna,hamisu ya ce,amin. lsmail ya shiga yana kallon dakin tamkar ba dakin masu aiki ba,hamisu ya ce,ai kurar dakin ba ta yi yawa ba,don kanin momi bai yi sati da tafiya ba,da cikin dakin yake.lsmail ya ce,kurar ba tada yawa ma kenan,amma duk da haka bari in dan kakkabe,ya shiga ciki sosai,hamisu ya ce,in zaka yi sallah ga bandaki nan.lsmail ya ce,tunda muka taso,duk inda sallah ta same mu,sai mu tsaya muyi ta.ya ce, shikenan baka da wani nauyi a kan ka.lsmail ya gyara daki mai dauke da katifa katuwa,sai duruwar ajiye kaya,sai kuma dan teburi a gefan katifar. hamisu ya ce,bari in sa a sanar da momi cewa ka iso,kuma naba ka masauki, yanzu saura abinci. kusan minti ta latin da fitar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (37)Kusan minti ta latin da fatar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa,sannan ya ce,ga abincin ka.shi ma nan haka lsmail din ya sake gabatar masa da kansa, suna na lsmail kai fa?ya ce, suna na jabiru,kuma nine mai dafa abincin rana da dare,lsmail ya bashi hannu suka gaisa.bayan fitan sa ne ya bude plate din abincin, dafa dukan shinkafa ne,ta ji kifi da alayyahu,ya ci ya koshi,ya sha ruwa ya koshi.daga nan barci ya sace shi, saboda gajiya bai taba yin doguwar tafiya kamar haka ba daga katsina zuwa abuja. can da ya farka ya kalli agogo,sai ya ga lokacin sallah ya karato,nan da nan ya tashi yayi alwala,ya fito waje bakin gate don ya ga karamin masallaci a gurin. hamisu yana zaune kusa da maigadi suna hira,yayi masu sallama,suka amsa. ya ce,hamisu ina ladani ya kira mana sallah lokaci yayi, hamisu ya ce,ba a fa kiran sallah a masallacin nan,sai dai kawai kowa yayi alwalarsa ya shiga yayi sallah.lsmail ya ce,saboda me?hamisu ya ce,ni dai haka na tarar suna yi,to ai duka-duka mu uku ne ke yin sallar,ni da maigadi da mai shara.ko maigidan ba kullun yake sallah a cikin masallacin ba,ya fi yi a cikin gida.yaron sa namiji daya. ya kai shekara shabiyu, amma ko shi ba a turo shi. lsmail ya ce,ko ku uku za ku iya jam'i,don haka ni kam zan kira sallah. lsmail ya shiga ya ga da abin magana da komai,yana kwada kiran sallah daidai lokacin motar alhaji bashir tana kunno kai ko da direban ya tsaya bai fito ba,sai da ya ji karshen kiran sallah,muryar tamkar balaraben saudiyya. maimakon ya shiga gida sai ya samu kansa da nufar masallaci,gurin da aka tanada don alwalla,nan ya je ya tattara hannu rigarsa ya soma alwalla.su hamisu suka tsaya suna kallonsa, nan dai lsmail yaja su sallah,hamisu yayi masu ladanci,sai dai alhaji shi kadai ya tsaya a sahunsa. suna idarwa suka fito, lsmail ya gaida alhaji,ya nuna masa jin dadinsa da sallar da ya kira har suka yi jam'i.lsmail ya ce.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (38)Ismail ya ce,alhaji zan yi wata magana,amma in na bata maka rai ka yi hakuri,amma hakki ne a kaina in sanar da kai.bai kamata ka tsaya ba a sahu ba,duk da cewa mu din masu nema a karkashin ka ne,amma gurin allah ba bu bambamci,musamman gurin sallah.sahu dole ne,na san alhaji ya sani.tuni kawai na yi masa,alhaji ya ce.na gode ba komai,sannan ya nufi cikin gida. sai karfe tara na dare, kuku ya sake kawo masu abinci,da ya karba sai ya fito,ya samu hamisu shi ma yana cin nasa,ya aje ya ce, me zai hana mu rinka ci tare?hamisu ya ce,ba damuwa bisimillah.suna ci hamisu ya ce,na ji mamaki da na ga kana magana da maigidan nan,wai me ka ce masa ne?lsmail ya ce,wata magana wanda bai dace in fito na fada ba,a takaice kuskure ne nayi masa tuni, hamisu ya ce tabdi,gaskiya ka yi saa,ai maigidan na mu mafadaci ne na gaske. wanda bai son a shiga huruminsa,kuma yana da wata yarinya mara mutunci,wanda kowa ke tsoron ta,hatta matan gida. sai dai gaskiya yana biyan kudi da tsoka,shi ya saka ga na jure,ni ne direban yaran gidan,don haka na fi kowa wulakanta. lsmail ya ce,na san ta,kuma ni malaminta ne,na zo in koya mata karatun addini. hamisu ya dago ya kalle shi,yayi dan murmushi, lallai ina mai baka shawara,ka nemo duk wani hakuri da kau da kai,ka kara a kan wanda kake da shi.lsmail ya yi 'yar dariya,ya ce,ta taba yi maka?ya ce,to da wanda ta raina ma iri na? ban san iya sau nawa ta zuba min miyau a fuska ba.banda kalaman cin mutunci.lsmail ya ce,kai kuma sai ka tsaya kana kallonta?hamisu ya ce,ya ya zan yi,tunda ina so,dubu talatin yake biya na a wata,ba ko'ina zan samu haka ba.lsmail ya ce,sannu da kokari,amma ni kam ba zan dauki wulakancin nan ba.sun jima yana ba shi labara,kafin suka yi sallama. haka da asubahi ya kwada kiran sallar farko, MIMI wacce lokacin ta yi sallama da kalil dinta wanda suke chatin tun misalin taran dare,ta bude idanunta tana jin sabon lamari a gidansu.ta tashi ta sauko daga kan gado,ta kunna wutar dakin na ta,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (39)Sannan ta nufi windo,ta yaye labule tana kallon masallacin,wanda dama saitin windon nata yake.tabbas masallacin nan ne,to wane ne wannan da karfi hali?lta tunda ta ta so bata taba jin an kira sallah a masallacin nan ba.ta koma ta kwanta ta saki tsaki.za ta ga mai wannan kokarin na hana mutane barci.ta fara barci ta ji an sake kiran sallar,aka shiga masallaci aka yi sallah,ba ita ta samu barci ba sai da aka idar da sallah. don haka bata farka ba sai shabiyu,ta yi mika tare da hamma,ta silalo kafarta kasa kan lallausar kafet. tamkar sarauniya ta ke jan taku har zuwa bandakinta, wanda aka tsara shi da kalar pink,kalar da take bala'in so,bandakin da yafi na kowa tsaruwa a gidan, hatta mahaifinta.ta shiga bahonta,bayan ta cika shi da ruwan dumi,sama da awa daya ta dauka a wanka,ta fito.gurin shafarta daya ne da kayan sawanta, bata cika yin kyale-kyale a fuska ba, hoda kadai sai jambaki bayan mai,amma tsadarsu ta ishi talaka jari. ta saka wando baki irin mai kama jikin nan,da riga ja,ta ja dogon gashinta ta kama shi da bakin ribbon. ta soma wanka da turaruka.ta nufi gadonta ta dauki wayarta tana dubawa,miss call kusan goma dadin ta,da na dear khalil,dana hajiya guda biyu. bakin gadonta zaune tana kiran layin dadinta,ya daga tare da cewa uwata ya ya aka yi?cikin shagwaba da muryarta din nan wanda ke fid da sauti a hankali cikin salo ta ce, dad na ga miss call din ka ne fa?ya ce,uwata har na fita baki tashi ba,lafiyarki kalau ko?ta ce,eh dad,emm yawwa dad wane ne jiya cikin dare ya hana ni barci da kiran sallah?ya ce, malaminki ne,gabanta ya yi bala'in faduwa ta ce,dad shine da zuwansa zai canza mana tsarin gidanmu?mene ne nufinsa da haka?ya ce,babu komai MIMI,kin san malamai da son masallaci,yau ni mana samu yin sallar asuba a kan lokaci,sannan makwabtanmu sun shigo mun yi sallar tare da su.ta ce kash dad,yanzu gidanmu gurin tara mutane kenan? ya ce,kar ki damu musuluncin kenan,ina fata za ki sauko domin daukar karatu.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (40)Gurin malamin na ki.kuyi amfani da falon baki, ko falo na ki ke so?ta ce,aa dad ya tsaya can falon baki,ba falon ka ba,da wannan bakauyiyar kafar tashi.ya ce,shikenan tunda naima tana gida ita mata soma karatun,in su ahmad sun dawo da yamma sai yayi masu,ta ce,shikenan dad,bari in kira hajiya naga ta kirani.ya ce,ok nima yanzu muka gama waya,ki ce ina gaida ta.cikin fargaba ta kira mahaifiyarta,hajiya ta daga cikin lallausar murya ta yi sallama,MIMI ta amsa tare da cewa,ina ki ka bar waya?ta ce,ina barci yanzu nayi wanka sai naga miss cal dinki.hajiya ta ce,na zaci kin fita gurin karatu ne?ta ce,hajiya ban san ma ya zo ba sai yanzu dad ke fada. ln na yi break zan yi yanzu,hajiya ta ce,ki maida hankali saboda ki san abinda zaki bauta ma ALLAH mahaliccin ki.suna yin sallama kiran kalil ya shigo sai da yayi daf da tsinkewa ta daga,wannan wani raayinta ne.ta ce, hello dear ya aka yi?ya ce,ba komai ina son in ji muryar ki ne?yanzu ki ka tashi?ta ce, fh,yaya hutu?ya ce,ga shi muna yi,don ALLAH ina son in zo gidanku wannan karon,ina jin tsoro kamar zan rasa ki,kar ka damu dear na fada maka don juna aka yi mu,ina jin haka a jiki na. ya ce, lovely har yanzu ban yi mafarkin haka ba ina ganin sai zancen ya je gurin manyanmu.ta yi 'yar dariya, ka san fa dad naka ba zai yarda ka yi aure yanzu ba, ni kuma in dad dina ya ganka guri na kila ya ce,zai min aure,ka ga sai matsala ta samu. ya ce,na fahimce ki,ba na son na sha wahala a aurenki kamar yadda na sha kafin na samu amincewar soyayarki na garu.ta yi 'yar dariya cikin salon maganarta ta ce,dear ka manta da haka,bari na karya,ya ce,to shikenan sai in mun hadu online ta ce,tam.cikin tafiyarta tamkar mai tausayin kasa take saukowa daga benenta,wanda ita kadai ce a sama ta ke mallakin kato falo da dakuna uku.daya dakin barcinta daya kayan karatun ta,tun daga computer zuwa kasa, dayan kuwa rufe yake duk da cewa shima da komai a cikinsa.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (41)Momi nafisa tana zaune tana kallon fim a cikin tafkeken tv dake manne a bangon falon.ta waiwayo,kin fito MIMI?ta kalle ta,na fito momi an tashi lafiya?ta ce,lafiya lau, dadinku yayi ta kiran ki baki fitoba,ta yatsi na fuska,mai kiran sallar cikin dare nan ne ya hana ni barci.momi ta ce,ai malaminki ne,na ga dad dinki ya yaba da hakan.ta ce,na lura da haka a wayar da muka yi dazun. ta isa gurin karin ta hada shayi tana sha,ta dubi mahaifiyar tasu naima fa?ta ce,tana dakinta,ta dauki wayarta dake kusa da ita,ta soma kiran layin na'ima,tana dagawa MIMI ta ce,sis zo mana,naima ta fito cikin riga mai gajeran hannu da wandon jins damamme,kanta ita ma babu dankwali,ta kama gashinta da ribbo blue. ta ce,sis gani,MIMI ta daga fararen idanuwanta ta kalli na'ima cikin harshen turanci suka fi yin magana.ta ce,ki je gurin folina a kicin ki gani ko ta gasa kifin,ta ce,sis mu je snacks store mana mu ci, MIMI ta harare ta,ki yi abinda nasa ki mana,ta daga hannu,alamun ban hakuri ta rinka fadin sorry. folina ta zo,ta shirya wa MIMI gasashen kifi tare da gasashen biredi,tana gamawa ta kalli naima ina son a kira mini malamin da yazo jiya,amma ban san yaya zan yi ba,don ba za kije ba,amma ki duba in kin ga direban ku,ko wani dai ya kira shi,ta ce tam sis. lokacin da hamisu ya sanar da lsmail cewa ya je ciki ana neman sa,sai ya ce,sai mun yi sallah tukuna. don yanzu zan kira.bayan sun idar sannan ya ce,ma hamisu ya yi masa jagora zuwa cikin gidan. barandar kofar falon,nan suka danna 'yar wata danja,jim kadan aka bude. naima ce ta kalle su irin kallon da wasu 'ya'yan masu da shi suke yi wa masu yi masu hidima.ta ce, wane ne malamin?hamisu ya nuna lsmail wanda ke tsaye sanye cikin yadi mara nauyi,hularsa ta dace da yadin wandonsa a dage irin na ahalil sunna. ta kalle shi sama da kasa, ta ce,ina zuwa.kamar minti biyu ta dawo ta ce,sis ta ce,ka shigo,ya shiga dankareren falo wanda tsarin saya wuce duk tananin lsmail ga sanyi AC
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (42)AC ko ta ina.ta waiwayo ta ganshi tsaye, ka bi ni mana,ya ci gaba da binta cikin zuciyar shi yana addu'ar ALLAH ya tsare shi daga sharrin da ke cikin gidan,alherin dake ciki ALLAH ya sada shi da shi. wata kofa suka shigo inda suka iske wani falon madaidaici,shima ya tsaru ta ce,ka jira ta a nan. kusan minti biyar,sannan MIMI ta shigo falon ba tare da sallama ba,rashin sallama yana kona ran lsmail,don haka bai ko kalle ta ba.ta zauna tana kallon fuskar wayarta,ta fi minti biyar chatin ta ke yi da kalil dinta,labarin karfin halin malamin take ba kalil.ta ce, ni da zai ci a gurin ubana, amma ni yake jira in ji da shi,kalil ya ce,kin san talaka da girman kai.ta dago ido ta kalli lsmail wanda ya bude ALKUR'ANI yana karantawa a zuciyarsa.ta ce,hamm mai neman taimako baya girman kai. ya dago ya kalle ta,kafin in ce komai zan soma yi miki nasiha,da saka hijabi don suturta jikin ki. ki koyi sallama yayin da ki ka zo gurin mutane,abu na uku,ba neman taimako na zo ba,ke nazo in taimaka ma wa,don haka yanzu sai ki dauko littafi mu fara daga huruful ija'iyya.ta ce,ba ka isa ka ce za ka taimake ni ba,don baka da komai,kuma ba zanyi sallamar ba,ba zan rufe jikin ba.ln baka sani ba,barin in fada maka,na sa a kawo ka nan gidan ne saboda in tozarta ka,in nuna maka kai kaskantacce ne.ya ce,don na miki wane laifi?ta ce,kai ne mutum na farko dana taba yin sa-in-sa da shi.wanda ya taba kallon cikin ido na ya fada min magana,kuma ina son ka zama na karshe,wannan shine laifin ka.lsmail ya ce, yanzu dai za ki yi karatun ko a'a?ta ce,na ce ba zanyi ba,ya mike tare da kwashe takardunsa.ta ce,ban sallame ka ba,yayi tafiyarsa ya bar ta zaune. MIMI ta bi shi da kallo cikin mamaki,shi wannan dame yake takama,har da baya jin shakka ta,kamar yadda sauran jamaa suke ji?ya san wace ce ni kuwa?ya san wane ne ubana? Ba wani ba ne uban MIMI fa ce alhaji bashir,dan asalin masari ne,karamar hukumar kafur jihar katsina. mahaifiyarsa 'yar dabai ce,su shabiyu ta haifa,
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (43)Amma yanzu saura su biyar,bakwai sun rasu,mahaifiyarsu ta rasu lokacin ya kammala sakandire,yayyin shi. mata uku ne,sai namiji daya dake bin shi,rakiya da basira a malumfashi suke aure, saratu kuma tana cikin kafur,malam aliyu mahaifinsu ya sake yin aure. inda matar ta kasance mai son kanta game da son zuciyarta.wannan yasa ya bar masari,ya soma shiga cikin garin katsina don neman abin kanshi, maimakon noma da suke taya mahaifinsu,shi da shafi'u kaninsa. ya yi sana'o'i kala-kala, tun daga kan kwandastan mota har zuwa dako,daga bisani ya soma bin wasu abokansa guda biyu da suka kama shago daya su uku,da lsa mani da kabiru naalla suna harkan dabbobi. tun yana karba yana saidawa ya cire ribarsa,har ya zo ya samu jarin kansa. sannu a hankali suka yi zangonsu na dabbobi, lokaci bayan lokaci yana zuwa masari ziyartar danginsa da mahaifinsa kuma yana yi masu alheri. kaninsa shafiu har yayi aure matarsa ta haihu,don haka mahaifinsa da yayyansa kullun burinsu yayi aure.wani zuwa da yayi har mahaifinsa yana cewa,ga 'ya'yan 'yan'uwansa ya zo ya auri daya daga cikinsu,sai bishir din ya ce,yayi hakuri,shi ba ya shaawar auren zumunta,amma duk lokacin da ya ga wanda ta yi masa,to zai yi aure,amma a yanzu neman kudinsa ya sa a gaba. ranar wata jumaa lsa mani ya tare shi yana sauri za shi masallaci ya ce masa,bashir ga wadansu shanu can zaa saida su a rugar fulani nan mashi.bashir ya ce,har mashi?gaskiya da kyar zan je,lsa mani ya ce,za ka samu alheri mutumi na,don jiya na dawo tafiya,ka sani da na saye su,amma ka daure mu je in ka dawo masallaci.hardon gar ne ke son zuwa aikin hajji,shine zai cikon kudi.bashir ya ce,ni dai masallaci na nufa ga shi ina jinjina zuwa mashin nan,lsa ya ce,mu je dai masallacin nan tare ma kawai,da zanje na karfe biyu ne,in ya so daga can sai mu wuce.a masallaci suka hadu da kabiru na'allah,inda suka nufi mashi dukkan su.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (44)Sun je rugar fulani,inda suka shiga garke shanu don duba shanu.ya nuna masu,aka shiga ciniki, an daidaita kuma bashir yayi alwashin kawo kudi gobe,saboda kudi suna banki.suna cikin sallama ne idon bashir suka kai kan wasu 'yan kwailoli guda biyu,sun dawo daga tallar nono,dayar ya kure da ido, 'yar similmila ta yi masa kyau,sai da ta bace ma idanunsa,ya bar kallonta.har lsa mani ya gane,bayan sun bar gurin ya ce,bashir kana ta

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login