Showing 27001 words to 30000 words out of 127530 words
bakin cikin da bazan manta da shi ba.ba a taba bata min rai ba tunda ni ke sai kai,ya yi shiru,don shi ya gaji da wannan wasan kwaikwayon,ya ce,to in na baki hakuri fa?ta ce,ka rike kar ka bani don bazan karba ba,ka barni in rama. ya ce,ba laifi,daga nan yayi banza da ita,sai kuma ya mike tare da kwasar littafansa,ta ce,na sallame ka ne?lokacin ka bai cika ba,ya ce,ba amfanin zaman,tunda ba karatun zaayi ba ya ta fi abinsa. yana zuwa dakin shi ya kira hajiya sauda da nufin ya fada mata komai,suna gaisuwa sai ta soma yi masa godiya har ya kasa fada mata,suka yi sallama, ya kwanta yana tunanin abin yi.haka suka yi ta yi har ranar lahadi,wacce ta kasance ranar da alhaji bishir zai amshi bakuncin sabon abokinsa,ministan man fetur.karfe takwas zai zo,amma tun shida an hana kowa sakat a gidan.girki an yi shi yafi kala goma,ban da nau'in kayan sha na kanti,ga busassu tun daga kan goro dabino,kayan marmari ma gasu na kala-kala.takwas zai iso gidan, don haja zuwa lokacin kowa na ta shiri.ya kira alhaji bishir ya ce,alhajin ALLAH zan zo fa da nawa iyalan ne.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (70)Alhaji bishir ya ce,na yi murna sosai,ina yi maku maraba. Ya fito daga dakinsa yana kiran nafisa,ta fito cikin sauri tana cewa,sun iso ne?ya ce,aa da iyalansa zai zo,ta ce,ALLAH ya kawo su lafiya.cikin azama ta shiga dakin na'ima ta same ta tana yin kwalliya, sai ta ce,yawwa na'ima ki yi gayu sosai,da iyalansa zai zo,inda namiji kiyi kokari ki ja raayin shi,ta haka ne za ki samu shiga gurin dadinku.zai so ki fiye da MIMI,na'ima ta ce,ya fada ne?mommy nafisa ta ce,aa ba ya fada bane,kin san yana son zama kut-da-kut shi da minista,in surukanta ta shiga tsakanin su yaya kike gani?na'ima cikin murna ta ce,zan yi kokari, amma in shi kanshi ne mommy ai yayi tsufa. ALLAH ya sa yana da yara maza mommy,nafisa ta ce,ina ruwanki da tsufansa?daura shi zaki yi a wuya?kudin muke bukata, ballantana a ce kin haihu,randa duk ba shi mu sha gado,ga gata gurin dadinku,na'ima ta ce,lnsha ALLAH za ta yi hakan. MIMI tana daki tana shirin ta,ita ba gwanar shafa abubuwa rakwacan ba ce,amma man ta da hodar ta zuwa turare tsadarsu ta isa.jambaki kurum ta shafa pink ta saka riga da wando damammu bakake a sama ta dora pink din shimin kayan ta zo mata gwiwa,ta tattare gashin kanta zuwa gefe ta kama shi da pink din ribom kasa-kasa,ta fesa turaranta na yau da kullum,don ta fi son turarukan arabia,takalmin ta flat baki mai ratsin pink. ta dauki wayarta daidai lokacin da wayar ta soma ringin,ta daga dad ya ce, uwata sauko sun iso,ta ce to daddy.lokacin da ta sauko falon kasan babu kowa,sun tafi tarbo bakin, bata bisu ba,sai ta samu kujera ta kame.suka shigo da sallama,ta tashi ta nufe su,matar minista ce suka shigo tare da mommy nafisa,sannan su alhaji bishir din,sai wani saurayi sannan na'ima da wata budurwa saar MIMI,sannan kananan suka shigo tare da su ahmad.kan kujerun fakon alhaji suka zauna,sun gaisa inda suka gabatar da junansu,ko in ce alhaji akilu ya gabatar da iyalansa.ya nuna uwar,ga madam dina hajiya bilkisu,sai yaro na na farko abbas.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (71)Ga shi nan ina ta fama ya yi aure yaki.ya gama karatunsa,yanzun yana aiki da central bank ne,alhaji bishir ya ce,ya kamata kam a yi aure.abba zai shekara talatin ko?alhaji akilu ya ce,talatin din ce kuwa,alhaji bishir ya ce,saan abba kenan dana na fari.shi kam yayi aure har sun yi min takwara, alhaji akilu ya ce,ka gani ko abinda ni ke buri kenan in ga 'ya'yan.alhaji bishir ya ce,ka kokarta ka ji dana? abba cikin murumushi ya ce,lnsha ALLAHU. ya nuna ta mace,waccen kuma aisha ce tana shekarar ta ta farko a jami'a ta kasar ghana,sai samira da azima da jamil duk 'yan primary ne da j.s.s. alhaji bishir ya ce,masha ALLAH,ALLAH yayi masu albarka.kai ba su da yawa ni yara na ishirin da biyu, mata na uku,alhaji akilu yayi 'yar dariya,ku manya ne, amma hakan yayi kyau, dama ka yi kokari ka cike, suka dariya,alhaji bishir ya ce,mu yi tare,kai ta biyu sai a yi rana daya.suka kalli matan wadanda suma dariyar suke har suna hada baki gurin fadin ku yi ta yi mana,ga dai yaranku nan,sun girma.bayan sun gama gabatar da iyalansu sun dan yi wasa da dariya, sai kuma mommy nafisa ta ce,ya kamata mu je dining, nan fa aka hau kan teburin cin abincin. MIMI ta kalli na'ima cikin maganar nan ta ta a hankali ta ce,ki lura tun daga kan aisha zuwa kasa ni zan ji da su daddies, mommies da brother abbas.yanda tayi maganar, iyayen suka sa dariya,haka ta yi ta zuba masu sai da kowa ya ce,yayi,ita ma na'ima ta kula da na ta gefen.bayan an kammala aka koma kan kujeru, MIMI da ba son hayaniya take yi ba,sai ta kama hannun aisha zo mu je sama na.haka yayi wa mommy nafisa dadi,har ma ta dauki wayarta ta tura ma na'ima messege,inda ta ce,ga dama nan ta samu,ki lura da abbas kuma ki ja hankalinsa.a sama,aisha sai santin falon MIMI take yi, MIMI ta kai ta ko'ina a saman ta,ta ce,gaskiya MIMI kin ji dadi,ke kam 'yar gata ce,duk nan ke daya?a ina ki ke karatu?MIMI ta ce,dubai,ai in fada maki aisha dad yana ji da ni fiye da zaton ki,duk abinda ni ke son.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (72)A sama,aisha sai santin falon MIMI ta kai ta ko'ina a saman ta,ta ce, gaskiya MIMI kin ji dadi,ke kam 'yar gata ce,duk nan ke daya?a ina kike karatu? MIMI ta ce,dubai,ai in fada maki aisha dad yana ji dani fiye da zaton ki,duk abinda ni ke so yana yi min.can kasa kuwa mommy nafisa ta ja hajiya bilkisu zuwa dakinta,alhazan su ma tasu hirar suke yi,kananan kuma sun bar falon alhajin sun nufi na su,suna gaban damfareriyar talabijin din falon suna buga game, Na'ima ta koma kusa da abbas wanda ke ta latsa wayar shi ta ce bros ya kokari,ya kalle ta, alhamdulillah,ya makaranta? ta ce,ai yanzu ina gida ne ban fara zuwa makaranta ba,ina son in je wajen ni ma,amma dadinmu ya ce, ko abuja ba zan bari ba.ya ce,kila kina rawar kai ne,ta ce,aa raayinsa ne haka,sai kuma ta canza maganar da cewa in ga phone din ka bros,ya mika mata ga shi. ta yi ta shiga nan fita nan ta dinga kallon hotunan shi lokacin yana karatu a waje, ya birge ta sosai.ta ce,ka hade fa bros,ya ce,na gode,ta saka lambar wayarta ta ce.ga lamba ta nan,in maka saving din ta, ya ce,eh,ta ce,kana da me irin suna na?ya ce,aa ta saka sunan,ta yi saving din ta shi.kamar daga sama sai taji ya ce,sa min ta sister din ki,mene ne sunanta na gaskiya?ta ce,khadija,ya ce,ok sa min lambarta,da ta tashi,sai ta canza lamba daya ta mi shi saving ta ce,in kun tafi sai yaushe?ya ce,ku ya kamata ku kawo mana ziyara ai,ta ce,haka ne,za mu zo,muryar alhaji akilu bala ta katse su. Goma tayi ku tashi mu tafi,alhaji bishir ya ce,tun yanzu?to sai mun zo muma, alhaji akilu ya ce,abinda zance kenan muna jiran zuwan ku,amma da rana za ku zo mana ko?alhaji bishir ya ce,in ka samu lokaci ka sanar da ni sai muzo,ya kalli na'ima,je gurin mominku ki ce su fito, alhaji akilu ya ce,ka san mata da kus-kus.sun fito inda mommy nafisa ta cika hajiya bilkisu da kayan mata,alhaji bishir ya cika yaran da kudi,na'ima kuwa abbas tayi wa kyautar turaruka masu kamshi,ita kuma MIMI kawarta aisha ta yi ma kyautar irin kaya jikinta.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (73)Da takalmi da kuma turare,sannan suka yi canjen number,alhaji bishir ne ya kira MIMI ya ce,su sauko,abbas ya kosa ya sake ganin MIMI don komai na ta yayi masa,kuma ita ce yake ganin zai zaba ta zama matarsa,tunda suka fito yake sake kallonta zuciyarsa tana kara kuranta ta.sun raka su har bakin mota katuwa jeep, direba yana ciki yana jiransu,aisha ta rungume MIMI sis sai naji ki,MIMI ta ce,yawwa sis aisha sai kin ji ni. Tunda suka koma gida, abbas ke kiran layin da na'ima ta sa mi shi na MIMI, wani ke dagawa,duk ya damu sai kai kawo yake yi a gefen nasa,ji yake yi tamkar ya nufi gidan su MIMI ya fada mata ya na sonta. a gidan alhaji bishir kuwa bayan sun yi bankwana da juna kowa ya shiga makwancinsa, dad da momi sun shiga nasu makwancin,sai take ce masa,alhaji na ga kamar na'ima da abbas sun aminta da juna,ya ajiye rigarsa da ya dauka da niyyar sawa ta bacci ya ce,haba!!ta ce,(cikin dariya) da gaske kuwa,har canjin number ta ce min sunyi.ya kamo hannunta nafisa ALLAH yasa haka ta tabbata da sai nafi kowa murna.da na'ima ta ga aure gata,ina son mu hada surukanta sosai,ta haka zan zama na gaba a cikin masu yin dillancin man fetur,buri na in zama na daya mommy nafisa ta ce,kar ka damu,zan kula maka da wannan alakar tasu,lnsha ALLAHU har a kai ga yin auran,ya rungume ta,ke kanki kyautar ki daban ce,suka sa dariya. Abbas ya samu aisha a cikin falon su,ya sami waje kusa da ita ya zauna ya ce.sis don ALLAH ba,ta ce ina jin ka,ya ce lamba za ki bani,ta kalle shi,ta wa?ya ce kawarki,ta sa dariya, wacce kenan?ya ce.ta gidan da muka kai ziyara mana,na ga kun kulle.aisha ta ce,ok,MIMI ko lallai ka samu 'yar gaye,ka ga gefenta kuwa?ta shiga ba shi labari.yana sauraronta zuciyarsa tana kara fari.ta bashi number ya koma sasan shi.sai dai abin takaici ya kira ta kusa so biyar amma ba ta daga ba. abinda bai sani ba.MIMI bata daga number din da bata sani ba,don haka tana kallon wayar tana yi tana katsewa.
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (74)Sake komawa ya yi hankali tashe gurin aisha yana tuhumarta cewa bata bashi lamba daidai ba.ta ce,bari in kira ta da layi na,a ringin na hudu ta daga ta ce,hello sis aisha ya ya aka yi?lafiya lau in ji ta,bros ne yayi ta kira baki daga ba,shine ya zo ya tare ni wai na bashi number ba daidai ba.ta ce ok dama shine?ayya ban sani ba tsari na shine bana daga bakuwar number, amma zan yi saving dinta yanzun nan,ta ce to zai kira ki,MIMI ta ce babu damuwa ya kira kawai. Sasan shi ya sake komawa,sanna ya kira ta,sun gaisa bai tsaya bata lokaci ba ya ce,MIMI kin tafi da dukkan tunani na,tun da na ganki naji gaba daya na birkice,ke ce matar dasu dad su ka ce in nemo, lokacin da suke min maganar aure,ke kawai nike kallo a amaryar.MIMI ta yi shiru tana jinsa,sai da ya kai aya sannan ta ce kayi hakuri da abinda zan ce yaya abbas.gaskiya ina da wanda ni ke so sosai,ban san adadin son da muke yi wa juna ba.don ALLAH kayi hakuri saboda gudun faruwar haka na bar falon don na lura da yawa satar kallon da ka ke min,amma ina me yi maka adduar samun wadda tafi ni.sannan zan baka shawara ga kanwata na'ima,bata tare da kowa, kuma tana da hankali,ya katse ta,ki bani lokaci in zo muyi maganar daga zaune. ta ce kowane lokaci ina gida,ya ce,in zo yanzun?ta ce a!haba dai mu barshi gobe.sannan sharadi kar ka zo da batun so na kazo da batun kanwata,yayi 'yar dariya,sai dai in na zo din,ta ce shikenan. Misalin shadaya lsmail ya nufi gurin karatunsa kamar kullum,ya jira sannan ta fito,haka nan ya bude kur'ani yana karantawa kamar yadda ya tsara.ya gama ya kalle ta,gaskiya ya kamata yau ki karanto in ji,ko kina rikewa tunda kin ga mun kammala shafi biyu na suratul bakara,sai ji amma a ce kullum ni zanyi karatu,ke kina danna waya don ban sa ran cewa kina ji ba.ta ce,in fahimta,ko kar in fahimta ya shafi albashinka?don haka kayi kawai ina jin ka dama aya biyar yake yi kullum,don haka ya karanto mata ko daya gama ya dago ya kale ta daidai lokacin..
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (75)Wayarta ta yi ringing,ta daga tare da cewa,brother abbas,ya na'am gani nazo fa,ta ce,ok ka shiga mana,na'ima tana nan a falo ka ce ta kawo ka falon baki na ciki.ya ce, ok to,lsmail ya kalli agogo abin haushi yanzun shadaya da rabi saura minti talatin. Bako yayi sallama lsmail ne ya amsa da ya shigo,sai ya mika wa lsmail hannu.shi ma ya miko masa kenan za su gaisa MIMI ta ce,aa yaya abbas,kar ka hada hannu da shi,abbas ya dakata sannan ya kalle ta lafiya?ta nuna ma shi gurin zaman,zauna kawai,lsmail ya bude kur'anin shi ya ci gaba da karantawa a zuciya,sai dai kunnansa yana gurinsu.ta ce,dan aiki na ne,kana dan minista zaka hada hannu da talaka? ni da zai koya min karatu ma na ki ya ji karatu na don bai kai matsayin ba, sai kai ka hada hannu da shi,kodayake mu bar zancan shi,ka iso lafiya?ya ce,lafiya lau,da farko ai na zaci shine na musamman din naki,ta ce,shishshhh haba mana abbas ka cuce ni,daka hada khalil da wannan,don ALLAH ka bani hakuri don ka cuce ni.abbas ya ce,to shikenan yi hakuri,amma so ba shi da haka,kuma wannan din ban ga laifinsa ba,ta ce zan hau sama in kana irin wannan zancen,ka yi abinda ya kawo ka. Abbas ya ce,ok na san jan ajin ku ne na mata shi ya sa kika ce min kina da wani,kar ki damu da jan aji don kina da ajinkin MIMI.tun ranar da muka zo ban kara sukuni ba don ALLAH ki duba ni.ta ce,yaya abbas don ALLAH ka bar zancen nan,ni da khalil mun fi shekara daya muna tare, shi yasa tun jiya na ce kar ka zo da batun nan,ka zo in ba ka kanwata na'ima.ba laifi in ka ce mu zama abokai,mu dinga ba juna shawara,ya ce,MIMI ni dai ke ni ke so,ta sa yatsan ta a kan lebenta ta ce shhhh, don ALLAH bar zancan,ka amince da batuna, bari ka ga na'ima,tana da kyau kuma ga hankali. Kafin ya ce komai ta danna kiran layin na'ima,ba ri ka ganta da kyau,na'ima daidai lokacin tana dakin momi cikin damuwa tun zuwan abbas da ta nuna mashi falon baki kamar yadda MIMI ta umurce ta. dakin momy nafisa...
[01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (76)Momy ta ce dama na san zai zo,na'ima ta ce,ai gurin sis MIMI yazo. gaban momy ya fadi ta maimaita cewa,gurin MIMI? na'ima ta ce,suna ma falon baki,momy ta yi shiru tana tunani,can ta ce,ni wai yaya zanyi da wannan shegiyar MIMI?wayar MIMI ce ta katse su ta dubi momy,ga MIMI tana kira na,momy ta ce,daga muji,MIMI ta ce,sis na'ima ki kawo ma bros abbas abin sha ta ce,ok gani nan.ta kalli momy,wai in kai masa abin sha,ta ce maza je ki kai masa,har ta fita,ta kwalo mata kira,zo na'ima ta ciro wani turare a jerin turarukanta ta fesa mata sosai,ta ce,je ki ko babanku na fesa turaran nan yana sa shi nishadi.a falo ta ajiye dan kwalin kanta,a ranta tana fadin in gashi ne ni ma akwai. Da sallama ta shiga falon,nan ma lsmail ne ya amsa,wanda ke zaune yana jin komai,ta shiga ta aje,sannan ta sake gaida shi,MIMI ta ce,zuba masa a kofi na'ima ta zuba,sannan ta ba shi a hannu ya amsa yana ta kallonta,sai da ta tafi sannan ya ce,MIMI kuna da bambamci da yawa, kyau kuma ba irin daya bane,ina son ki don ALLAH. MIMI ta ce,in baka amince da na'ima ba to ka tafi ka nemi wata,na yi haka ne don na san iyayanmu za su yi murna.ya ce,ni da ke zasu yi murna,ta ce,to abinda ya yi ni,shi yayi na'ima,ya mike,ke da ita akwai bambamci,zan tafi amma fa ban hakura ba. Ismail dariya yayi ta yi a daki tare da tausaya ma abbas,don ya san menene so,in ya tuna zainabun shi, kila ma in ya ci wata daya sai ya je katsina ya ganta, ya sai mata waya don ya dinga jin muryarta kowane lokaci. MIMI tana cikin damuwa,sam ba za ta so zancan nan ya kai gurin dady ba,domin zai so hakan. tun bayan tafiyar abbas MIMI take sake-sake. momy ta hau sama ta sami MIMI