Showing 24001 words to 27000 words out of 30805 words
sun bata tausayi sosai taji itama kamar tasa kukan, dandai kadata k'ara bata k'arfin gwiwar yin kukan yasata danne zuciyarta. Anan suka sanarmata uku tahaifa sedai d'ayar batazo da raiba. Zaro idanu tayi tace "duk acikina, lallai Iyayenmu sunsha d'awainiya damu. Kuma dole miyi Biyayya agaresu tahanyar dabata sa6awa mahalicci ba muddin munaso mu wanye lafiya a duniya. Alllah yasaka musu da d'umbin Alkairu yabiyasu da babban rabo. Allah yak'ara bamu ikon cigaba da faranta musu dayi musu biyayya bisa turbar Islama. Itakuma Allah yamata rahma yakyautata namu k'arshen. Duk mutan d'akin suka amsa da Ameen.
Kwanansu biyar a Asibitin mai jego tawarware sosai, har tana shayarda yaran. Namijin mai hak'uri, macen kuwa rikici gareta. Danna Inna da Samiha basu gajiya da d'awainiya dasu ko kuka suke tana bacci ba kasafai suka fiya tashintaba. Inna takance "batta tai bacci tad'an samu hutu, ita kada'i tasan gumurzun datasha daga rainnan ciki har haihuwarsu." Dukda dai kowace mace da kalan nata abubuwan.
© *Didi_Sady*🍼🍉😜
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*81-85*
_Afuwa Makaranta wannan labari. Bajan rai bane kunsan d'an adam ajizi ne. Abubua sunyi yawa. Kwana biyu kuma banida lpy. Ga bukukuwa da aketayi a fam. In sha Allah before Jan 2017, zan kammala. Nagode da k'aunarku gareni aduk inda kuke._
~~~Aran kwana bakwai da haihuwar aka sallamesu da rana. Duk wani kud'i da aka kashe tun farkon zuwansu Asibitin Baban Usman ne yabiya, dan cewa yai "Haryanzu da nauyinta akansu, dan haka duk abinda ake buk'ata yace "Agayamasa" Mama kuwa suka 6alle bakin aljihu akai komai cikin mutunci da girmamawa.
Bare dasukaga anhaifar musu Tagwaye. Kayan barka sosai suka siya ranar dasuka koma aka bisu da tukwici dak'yar suka kar6a. Acewarsu "Ai yiwa kaine anriga anzama d'aya.
Ranar suna kuwa bawani taro akai ba. Rad'in suna akai aka sawa Namijin sunan Usman itakuma macen aka samata Asma'ul Husna. Samiha tasa musu Hassan da Husna. 'Yan barka sukai tazuwa 'yan uwa da abokan arzik'i. Kayan barka iri-iri suka samu, wasuma sa shekara suna amfani dashi.
Mejego tayi k'alau da ita. Dan jego mai kyau ake mata har sukai wata biyu. Yaran sunyi 6ul-6ul dasu, kamarsu da mahaifinsu se dad'a baiyana take. Ita kanta Naja'atun kamar ba ita ta haifesu ba, dan gyara sosai Inna da taimakon k'anwarta Aunty Husna sukai mata. Irin zugudan nan dayawan masu ciki keyi bayan haihuwa, basu bari tayiba.
Tayi k'alau da ita. Sedai idan takalli yaran nata takanji tausayinsu natashi dazasi basuda mahaifi. Tak'udurce aranta bazata ta6a bari siyi Maraiciba.
Duk yadda zatai takare Mutuncinsu zatai wanda bai kaucewa shari'a ba. Kuma ga kakannunsu da dangin mahaifinsu dasuke sansu da ji da k'aunarsu.
*BAYAN SHEKARA HUD'U*
Hangota nai cikin _Nagarta Shoping Complex_ d'auke da basket a hannunta. Deedat nagani yak'ara girma rik'e da hannun wasu yara masu kyau dabazasufi shekara uku da rabi ba. Mace da Namiji, kalan kayansu iri d'aya, sedai Bambanci na Mace da Namiji. Macen anmata kalba datasha Bead se reto suke ajikinta.
Tsayawa tai wurin kayan k'amshin gida tanata duba irin wanda takeso. Domin ita ma'abociyar k'amshi tundaka najiki zuwa na d'aki hakama kyawawan 'yan biyun 'ya'yanta Hassan sa Husna.
Naja'atu kenan matashiyar Bazawara, datun bayan rasuwar Mijinta bata sakeyin wani auren ba. Asalima catai ita tagama, seda mahaifanta suka tsaya tsayin daka da Addu'a da rok'on Allah tasaki ranta tadawo da walwalarta daduk wata mu'amala harta koma Makaranta da D.E daga level2 tafara har take shekarar k'arshe a course in ```Nursing and Nursing science```.
Jitake zata iya Aure ayanzu, kowaye yazo muddin yanada d'abi'a da mu'amala ta k'warai, kuma yakwanta mata tayi Na'am dashi da wanna tasamu tarufe bakin Iyayen nata. Ganin ana shirye-shiryen Auren Samiha da sauran k'annanta Mata, amma ita shiru.
K'wace hannunsa Hassan yayi, daga hannun Deedat ganin Husna tayi gurin toys dandama tafishi wayo. Da gudunta nayara tayi gurin toys tagano 'yar tsana, Bangazar mutumin dataine yasata tsayawa. (Sanadi😻)
Agogon daya d'aukane samfurin ```Dior``` yafad'i daka hannunsa har saida Glass in ya tsage. "Ya salam! Ya furta da _Husky voice_ insa mai amo. Irin yawan dayasha yana neman ```Wrist watch``` in besamuba se anan gashi yanzu kuma abinda yafaru ko biyan kud'inshi baiyiba, cikin jin haushi da takaici afuskarsa yad'ago zai mata masifar wata irin matace dabata tafiya a hankali? Tajamai wannan d'anyen aikin. Batasan irin wuyar dayasha yana abu guda naneman brand na Agogonba.
'Yar k'aramar yarinya kyakyawa idanuwansa sukai tozali dasu.
Husna kam ganin yasha mur bashiri takama kunnuwanta tai kalar tausayi tace "Am sory Uncle" ai saurayin besan sanda ya murmusaba yaji yarinyar ta burgeshi sosai. Inama 'yar sace, tunano yadda Mahaifiyarsa babu abinda takeso irin yayi Aure, har matakaiga samun zuri'a.
Shafa kanta yai yace mata "Be careful kinji Babyta next time kirik'a tafiya a nutse karkije kima wani irin tawa yadakeki, bama haka ba kada kiji ciwo kinji." D'aga kanta tayi alamun taji tace "Thank you Uncle" Matashin saurayin yace "Oya give me five" yabata hannunsa suka tafa sunata dariya.
Hassan ganin ba a daki Husna ba, sunata dariya, shima yataho yana dariya dabaisan akan me ake ba.
Da mamaki afuskarsa yake kallansu duka. Mik'amai hannu Hassan yayi da nufin su gaisa. Saurayin kuwa yakama d'an hannun Hassan suka gaisa. Tsugunawa yai dai-dai tsayinsu yace "U are identical 2wins?" Saboda tsananin kamanninsu yayi yawa. Yakuma fad'in "Am i right?" Yana cigaba da kallansu.
Husna da surutu takuwa hau zuboshi "Mamynmu tace mu Triplet ne amma d'ayar tamutu ita bamugantaba.
Dariya yahauyi sosai daya jima baiyi irin taba. Yace "Shikenan nikam nayi new friends yau, amma bansan sunankuba."
Husna takuma cafe maganar tace "Mu 2wins in Mamynmune yanzu amma sunannu ni tanuna kanta sunana Husna Usman Bello Galadima, shukuma Hassan sunanshi Usman Usmab Bello Galadima, sunan Babanmu aka samai shine ake cemasa Hassan. Amma har yanzu Abban bai dawoba Mamy tace "Yayi tafiya inda ba a dawowa. Shiyasa bayanan.
Kuma mu kullum baya d'aukomu a school, sukuwa su Farouk Abbansune yake zuwa d'aukansu." Tafad'a tareda kama hannun Hassan. Shima yace "Se Mamynmu ko Uncle."
Sunbashi tausayi sosai, yafahimci komai wato Mahaifinsu yarasu basuda wayo ko ba a haifesuba.
Kama hannayensu yai duka yace "Tare dawa kukazo gurin nan?
Hassan yace "Da Mamy da Ya Deedat. Batasan munzo nanba dan tace mudena surutu inba Alkairi mutum zai fad'a ba yai shiru. Har Rok'o dayawoma tace. Ana sace mutum inyaje yawo inda baisaniba yadena ganin kowa har Mamanshi." Ko Husn Yafad'a yana kallan Husna. Surutun kuwa sukai tamasa yanata record dan sun birgeshi. hadda tambayarsu to in aka saceku yazakuyi. Zaro ido sukai suduka. Husna datafi wayo tace "semu kira Mamynmu awaya ko Uncle Isma'il da Ibrahim."
Yace "To tayaya zaku kira?" Digit tahau fad'omasa yanata mamaki.
Jiyai sunkuma shiga ransa, kamar yatafi dasu tunda duk yaji details insu har Adress in gidansu dana kakanninsu. Suka gayamai yaran masu d'ankaren surutu kamar sunci Kabarai. Ga wayo. Kuma ai shima 'ya'yansane. Tunda hausawa sunce *D'a nakowane*
Tinanin dayai idan yatafi dasu Mahaifiyarsu yazatai dan ko ina take bazataji dad'i ba. Toma haka ake daka ganin Sarkin Fawa sai Miya tai zak'i Koshi bazaiso amai haka ba. Dankuwa sai inda k'arfinsa yak'are.
Yace musu "Shi sunansa Uncle mai zane, daga yanzu yazama Uncle insu shima. Sukuma sun zama Friend d'insa. Suka tafa dukansu. Sunata mumma, yama manta da batun Agogonsa.
Zagaye sukai tayi, yasai musu toys da chocolate, wafer,biscuit dayawa. Aikam yasha godiya gurinsu.
Sukaje aka biya kud'in. Har waje yarakosu, kaya taganosu dasu nik'i-nik'i. Ita Husna ma jan kayan take.
Nemansu take tayi har suka futo zasu shiga mota. Cogewa tai tana kallansu se muzurai suke.
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*86-90*
~~~Yaran sunsan in Mamyn tasu tai shiru, tana kallansu sunyi laifi kenan.
Tun basu fahimtaba, har suka gane me shirunta kenufi, dukansu suka saki kayan hannunsu suka kama kunnuwa atare sukace "Afuwa Mamy" ganin tayi shiru batace komaiba suka k'ara langa6ar dakai, kalar tausayi sukai sosai.
Shigewa mota tai kamar zatatafi basu, da gudunsu suka taho har Hassan yakusa kifewa, "kayanfa wakuka barwa" Mamyn tasu tace, tana kuma kallansu, tasha mur. Suma d'if sukayi suka sunkuyar dakai.
Bud'e motar tai atsawace tace "Kushige mutafi, zakusan kunje yawo daga zuwa daku harda rok'o, punishment zaku kwana kunayi, Abincima bazakucuba tunda bakujin magana.
Ai bata k'arasa maganganunta ba suka shige motar dasauri suna kuka dukansu jin hukuncin daza amusu.
Duk abinda yafaru yanadaka gurin k'ofar shiga _Complex_ in yana hangosu,"dukda baiga fuskartaba, hakan datai musu yanuna tanasan sukasance cikin tarbiya, ba kwad'ayi dasan abin duniya ba.
Kayan dayasimusu suka bari, yazo yad'ibesu amotarshi yasa, yabar gurin shima ko siyayyar dayazoyi baiyiba. Direct gida yawuce.
Mahaifiyarsu dasuke kira da Umma, tana zaune littafin *Garkuwar Musulmi* ne a hannunta tana dubawa, da Sallama yashiga falon. Ganinshi tai d'auke da kaya. "Sannu da gida Umma" yace tareda zama. Ummantasa tadubeshi da kulawa tace "Harka dawo ashema ba jimawa zakaiba, afitarba?"
Ajiyar zuciya yasauke yace "Ah Umma d'an akasi akasamu a inda naje.
Anan yakwashe komai yagayamata, dan itace abokiyar shawararsa tun yana k'arami, shi ko yawan abokanai bashida su. Ummansa itace kominsa, har _recording_in surutun di Hassan da Husna yakunna mata taji, na dariya tayi na tausayi ta jimanta, yad'ora dacewa "Shifa gaskiya seya bisu yakai musu kayan" yashige d'akinsa. Umman tasu tabishi da kallo aranta tana Addu'ar Allah yabashi mata tagari dazata kuladashi. Shima yai Auren koya dad'a samun nutsuwa arayuwarsa.
Arc Sulaiman Tajuddin Kazaure shine sunansa. Mahaifinsa Alh Tajuddin Hafiz Kaxaure da mahaifiyarsu Hajiya Maryama. Asalinsu 'yan jihar Jigawane, Aurensu tunna Saurayi da Budurwa, Allah ya albarkacesu da 'ya'ya Hudu duk Maza, Muhammad Kabir shine Babba Barister ne mai zaman kansa, suna zaune a Abuja tareda Matarsa Farha da 'yayansu uku.
K'aninsa Tasi'u shima da iyalansa su suna zaune a Kazauren inda yake aiki. Mebimsa Yusuf dabai dad'e da Aureba yatafi da Amaryarsa can Bony a Phorthacoat inda yasamu Aiki.
K'araminsu shine Sulaiman matashi dabai haura shekara 30 ba, Archtecturing yakaranta a Jami'ar ```Kano University of Science and Technology dake Wudil ```A Kano . Zane zane da Allah yabashi baiwa da fasaha akan haka, Taswirar Gidaje da Ma'aikatu har mutane ma, yamaida kai sosai akan harkar tasa. Allah kuwa yasamai Nasibi acikinta. Hayarsa ake d'auka gari-gari wani sa'in har wasu K'asashe . K'ark'ashin kamfaninsu mai suna _"The Shariff Construction"_.
Suna zaune a D'an Agundi G.R.A, dake Zoo road, sakamakon Aiki dayada da Mahaifinsu Ma'aikatar Ruwa ta Hadeja-Jam'are, reshen jihar Kano.
Hajiya Maryama mace ce mai tsafta, kawaici dasanin yakamata, uwa uba rik'o da Addini. Ga zumincin 'yan uwa nakusa dana nesa, duk ta d'ora 'ya'yanta akan
turbar hakan.
Allah baibata haihuwa dayawaba, shiyasa takeso Sulaimanu in yai Aure yazauma kusa da ita. Kota rik'a ganin 'yan kufi-kufi akusada ita. Duk sauran 'ya'yannata da iyalansu sunmata nisa.
Wannan kenan.
Naja'atu dasuka koma gida ko kayan data siyo bata idasa ajewaba, takamo 'yan biyun nata Hassan da Husna "Kneel down & close your eyes" tace tana zare idanu. Bashiri sukayi atsorace bawanda yace uffan.
Harta gama jera kayayyakin, ta adana komai inda yadace. Abinci tazubo dantaci, kasa cin abincin tai, dan tasaba yanzu tare dasu takecin Abincin. Abunka da Uwa da d'a tausayinsu yatasomata, janyosu tai duka tarungumesu tsam ajikinta kamar za'a k'wace matasu.
Hak'uri suka bawa Mamyn tasu, taja musu warning sosai, suka fara cin Abincinsu cikeda ladabi dan duk takoyar dasu Ladubban ci dasha:-
*Kaci da hannun dama*
*kaci da Bismillah*
*kaci Abinda ke gabanka*
*kada kai Numfashi acikin kofi/k'waryar ruwan*
*kada kashafi band'aki da hannunka*
Ire irensu da neman yafiya yayinda kaima mutum badedaiba. Duk takoyardasu.
Bayan sungama cin Abincin, aka hau labarai anan taji labarin Uncle mai zane daduk yadda sukai dashi. Taita dariya kuwa, toilet tanufa dan haramar Sallar Magriba.
Sulaiman tunaninsu duk ya addabi kwanya da zuciyarsa, ranar da wuri yashige d'aki bayan yaci Abinci. _Recording_ na surutunsu dayayi yazame masa abokin hira alokacin, tunani yai tayi koyaje yakaimusu kayan gida? To maizaice, gurinwa yazo? Tambayoyin dasuka dami zuciyarsa kenan.
Cikin lokaci k'ank'ani yabi yatakura kansa, zaman hira dasuke da Umman tasu yarage, bashida aiki se saurara _Recording_ insu kusan ya haddaceshi har zanasu yai yadda yagansu. Yakumayi wani haddashi. Yaita kallan zanen hoton.
Ummantasu ganin haka tafara mai zancen yai Aure koya samu nasa Iyalin. Secemata yai "Lokaci nayi zaiyi tacigaba damasa Addu'a.
© *Aneesa_didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*91*
~~~K'arshe shawarar da Umman tabashi, yaje yakai musu kayan, koya samu ganinsu yaji sassauci da rangwame.
Number wayar daya rik'eta akansa kamar karatu, wadda baisan tak'amaimai tawaye cikin wanda suka lissafo maiba, ya rubutata cikin tasa wayar. Yai jimm, yakira koya je harcan gidan? To inyaje, yace gurinwa yazo? Cin biyun dole yai d'aya. Kiran wayar yashiga yi.
Naja'atu zaune akan k'aramin cushing, Hafsa k'awarta data kamata ziyara tana mata Oiling agashinta,mai tsayi da santsi, Husna nagefanta tana bacci. Hassan kuwa wasansa yaketayi, dan intana gida duk inda tasa k'afa suna gurin. Intatafi School kuma suna gurin Inna, harta dawo.
Wayarta tashiga ruri, ganin bak'uwar Lamba harta katse bata d'agaba, yakuma kira har sau uku, akaro nahud'u ne Hafsa tadubeta tace "Haba my K'awa ki amsa mana, inkuma kink'i ni mik'on wayar nad'aga, wayasan ko sabon Miji muka samu".
Naja'atu dai batace komai ba tad'aga wayar.
"Peac be upon you, danAllah ahad'ani da friends ina, Hassan da Husna. Inason jin lafiyarsu, nakasa sukuni, since the time i was meet them, am feeling like they are my Kids". Yashiru yaji maizata ce.
Itakuwa _Husky Voice_ insa taji amonta har tsakar kanta, kalamansa nak'arshe sun ta6a zuciyarta, basan sanda tace "Kaine Uncle mai Zane da ake tamun surutunta?"
Murmusawa yai kamar yana gabanta yace.
"Nine Arc Sulaiman T Kazaure, Uncle mai Zane,i hope bazaki hanani jin muryar Yaranaba?"
"Gasu"
Tace tamik'awa Hassan wayar. "Hassan ga Uncle mai Zane".
Da murnarsa yakar6i wayar suka hau surutu kuwa hartaji yafad'a masa "Husna tayi Bacci".
Labari Naja'atu suka shiga itada Hafsat, dukda tunaninta yatafi gurin wayar da Hassan suke.
Hassan yamik'o mata wayar tasa akunnanta.
"Please Mamynmu abani Permision nazo naga yarana?"
Dariya tai tace
"Anbaka"
Batasan miyasaba tun kafin suhad'u taji yakwwanta mata, kodan yanasan 'ya'yantane.
Sallama sukai duk sun murmushi, suka aje wayar.
Yammacin ranar kuwa, segashi yazo dukda bata fito ba, yaji dad'in ganin yaran dayazo sabidasu.
Sukai tasurutu yana biye musu harda hotuna. Kayayyakin daya siya musu suka bari yabasu, hadda k'arin zanensu dayai Manya, sukad'ai dawanda yahad'a harshi. Seda yaga shigewarsu gidan shima yatafi.
Kayan suke ta duddubawa, idanuwanta sukai tozali da kyakyawan bahaushe d'an mutan Kazaure, kan Zanen dayai musu, Hoton taji yashi Zuciyarta, taita shafar fuskarsu.
Duk abinda take da yanayin datashiga, a idan Inna, Murmushi tai irin nasu na manya, zataga iya gudun ruwansu duka.
Yawan wayar dasukeyi da sulaiman, yafakaice dayiwa Hassan da Husan waya. Abin yashigesu sosai, har takai ga in ba ai wayar ba basa jin dad'i, banda sak'onni dasuke turawa junansu. dukda basu had'u ba. *Soyayya da Shak'uwa*(littafin my xoxo) tashiga Zuk'atansu.
Naja'atu gani take sabida yanasan 'Ya'yanta, shima yasamu gurbi aZuciyarta.
Sungama waya da Yaran dadaddare, yace
"Subawa Mamynsu"
Mik'a mata wayar sukai, sukatafi kallan Cartoon da Deedat yakunna.
Cikin wata iriyar murya dabata sabajin yayi irintaba a shagwa6ance yace.
"Mamyta!"
Har cikin jikinta da kanta taji amon furucin, kamar shikad'ai yafi kowa iya Ambatar sunan.
Akasalance ta amsa da "Na'am Uncle yaukuma nima nazama taka?"
Kamar yana ganinta yai murmushi tareda fad'in "Zanso hakan Mamyta"
Rintse idanu tai, besam yadda kalamun ambaton sunanta da yake lugwigwita Tanderun zuciyartaba, daya tausaya yak'i ambaton sunan.
Yakuma cewa
"Please kibani dama nanuna miki hakan, bakida matsala dani, in short kiji labarina. Yad'an gaya mata ```Biographynsa```," yakashe wayar yabatta da tunani.
Nannauyar ajiyar zuciya tayi tasan za'ai haka dama.
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*92-93*
~~~Bata 6oyewa Inna komai akan saba,