Showing 15001 words to 18000 words out of 30805 words
yasa kishiga a sa'a abinda ta iya furtawa kenan. Tai musu alamada hannu aka wuce da Amarya. Deedat ya k'ank'ameta shi bazata tafi tabashahiba dayawa cikin mutan gurin saida sukai k'walla. Aka tafi da Amarya gidanta dake Sharad'a. Gidan ya k'ayatar da mutane danba k'aramin dukiya dangi suka narka mataba. Kowa yataho akabar ta daga ita sai halinta.
Semuce Allah ka d'anbaba mai k'uli-k'uliπ
Am so sry makaranta Abubuwan dayawa shiyasa baku ganin postn akai2. Inkomi ya gyaru zakunajina koda yaushe inasanku nima aduk inda kuke. Allah bar zuminci da k'aunar juna
Luv u allπ
Β© *Aneesa_Didi*πΌππ
[2/18, 10:48 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: [25/11, 2:50PM] Didin Aneeπ
β‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*β‘
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*41-45*
Abokanan Ango sukayo masa rakiya suka wuce bayan sunyi Addu'o i danemanmusu farinciki dazama lafiya mai d'orewa. Suka d'anyi ciye-ciyensu itadai akunyace tasha Ruwa shima danya matsamata ne.
Usman ya Umarci Naja'atu data sake alwala, cikin toilet in d'akin tai Alwala. Sallar isha suka fara sannan suka d'ora da nafila yai musu Addu'a mai tsaho sannan yai mata tambayoyi gameda Addini, yak'ara mata haske har Wankan Janaba yakuma mata bayani dayadda take samuwa. Kanta a sunkuye yake tamata bayani, wani tai magana wani tai shiru.
"Hannunta duka yakama, yajanyota jikinshi janye mayafin duka yayi yarungumeta tsam ajikinsa, dukda hakan bak'on abune agurinta jinta tai she is safe, zippin rigarta yasoma yana kuma cusa kanshi ajikinta cikin wani salo na soyayya dabata ta6a tunanin haka abin yakeba, nikam danaga lamarin yajuye abin yafi k'arfin ganina. Najuya nabasu guri.
Kunsandai bakyau bincike balle su wannan daya zama sirrinsu. Asuba tagari couples.
"Wayewar asabar, komi shiyayi mata, Addu'a kuwa tashata ba adadi takuma narkewa soyayya yake gwada mata wadda ba algus acikinta. Har sukai karin kumallan safe. nok'ewar da takene adan fusace yace "ai aikin gama yagama, abunda take kunyanma yagani tomiyai saura? Itadai murmushi kawai take tana k'ara sunkuyar dakai. Kujerar da take kai yadawo ganin ta mik'e yasashi janyota tafad'a kanshi. K'ok'arin zamewa take yak'ara k'ankamota.
Zauna ma kiji abinda zaki fara ma shine indai ina gida bakida gurin zama daya wuce nan, yanuna mata jikinshi. Kinsan body contact yanada tasiri wurin shak'uwa da mararin juna ga ma'aurata.
"Bugun k'ofar da akeyine yadakatar dasu, saurin mik'ewa tai daka jikinshi tayafa mayafi akan kayanta tanufi k'ofa danta bud'e, Abdullah ne da Shukra k'annan Usman mama ta aiko suka mata abincin Rana.
Guri tabasu suka shiga falon gaisar da Yayan nasu sukai, itama suka gaidata tacikasu da kayan mak'ulashe. Shukra Autar mama dasaurin sabo duk inda Najan tayi tana biye da ita. Har Usman ke tsokanarta tayi 'yar zaman d'aki, murmushi tai tace " aikam danaji dad'i daza abarta ta zauna.
Hararar wasa yabita da ita tareda fad'in "bakowa ma kink'i sakin jiki musha Luv inmu bare anka miki wannan mai surutun. Tace " aida Mama zata ban ita danaji dad'i.
"Hmm! Bakisan yadda Mama da Shukra suke bane bame rabasu se makarantar data shiga amma da ko ina suna tare, har yanzunma. Bata yadda tazauna agidan kowa se Mama. Dakwai sanda mama suka tafi Dabinai aka kaisu gidan Sisto, har yamma basu dawoba data fara kuka, kowa seda yaji haushinta Sadiq da Anas sukai zamansu harsun kwanta amma Shukra seda akada da ita gida k'arfe 10 nadare. Tana ganin Mama shiru kikeji.
Wai lallai kuwa naga ranar rabuwarsu da Mama. Allah sarki aikam dolene rabuwar ta fad'a tana rau-rau da ido.
Laah! Nibance kiman kuka ba kingama natafi. Yafice daka kitchen in yana dariya.
"Bak'i sukai tayi danginsa da nata danma ankakkamata abinci taita zuba musu faranfaran takar6i jama'ar. Tacikasu da kayan arziki.
Washe garima haka sauran danginsu dabasu tafiba sukazo ganin idan amarya.
"Anty Husna dasu Samiha se yamma suka tafi bayan sun gyaramata ko ina dasauran kayayyakin ta nagida, takuma ware wasu kayayyakin daza a rarraba harda wasu daka cikin kayan lefanta. suka turare mata gidan bayan anty Husna tasata tai wanka kwalliya sosai tasa tayi, dan yanzu bada bace dole sekina gyara ladabi da biyayya sannan zaki mallake mijinki atafin hannunki. Kud'an bamu guri tace dasu Samiha. Suka fita suna k'us-k'us batasan yaran zamani wasu sunmafi masu Auren sanin abubuwa ba.
Tacigaba dabata tip da dabarun zama da miji. Da sirrikan dazasu k'aramata Ni'ima batareda tayi amfani da abunda zasu cutarda itaba wanda batasan dame akaiba.
" *Sirrri na daya*:- kisamu kankana kiyayyanka kisa madara kinasha.
" *Sirri na biyu*:- kisamu zogale ganyansa da cocomber kiyi blending insu sekisa zuma da madara zakisha mamaki.
" *Sirri na uku*:- kwakwa dabino dankalin,hausa(kadan) farar shinkafa cukwi. Ki markada shiima kinashan ruwan. Inkinso kuma zaki iyayin na gari kina damawa da madara kinasha.
" *Sirri na Hudu*:-kihadasu gero mazankwaila dabino farar shinkafa kwakwa busasshiya busasshen muruci kida kasu siyi gari. Seki zuba man habbatussauda kihadesu guri daya. Yazama gumba.
" *Sirri na biyar*:-Man zaitun Man tafarnuwa Man Habbatussauda Miski kihadesu kina shafawa/insert.har maganin sanyi yikeyi.
"Taita gayamata abubuwa tana rubutawa wanima intayi harshi zasuna sha kaman inzata dafa shayi tazuba Minannas da kirfa aciki kunasha tare tsafta dayadda zata tsaftace gida da jikinta turaren bayan kunne daban nagashi, na matse-matsi cibiya. Shikansa mijin tadinga tsaftaceshi da kayansa yadda bazai taba zamada daud'a ba balle ajiwani unwanted odour yana tashi daga jikinsu.
Seda Anty Husna tacikata da abubuwan Alheri sannan suka tafi tanata kewarsu.
"Alwala tai tazauna kan akira sallah tanata lazimi abinta. Alamun bud'a k'ofa taji da sallama yashigo cikin husky voice insa, sansanyan k'amshin turare yaji yabigi hancinsa wanda bazai tantance ainayi wasu iri bane. Tun alokacin tafara aiki da hud'bobin Anty Husna.
Tasowa tai zuwa inda yake ganin kaya da ledoji fal a hannunsa tarusuna tamai sannu da zuwa takar6i kayan hannunsa janyota jikinsa yai yakuma jin wani k'amshi na musamman natashi. Eye ball to Eye ball suke kallan junansu yana mata wani sassanyan kallo da murmushi dashi kad'ai yasan ma'anarsu.
"Kinyi kyau yace da ita. Tallafota tai tagefansa suka k'arasa cikin falon, takai kayan inda yadace shikuma yai Alwala yatafi Masallaci.
"Cikin kwanakin Amarcinsu kawai sukeyi, seda tai sati sannan yakaita gidansu tagaida Mama da Abbansu. Dabinai kuma seta k'ara kwana biyu zaikaita taga danginsu nacan. Yanata rawar kai agaban Maman itakuma duk yasa tatakure, Maman bata k'ara ganin rashin kunyaba saida suka gama abinci tazubamai waishi da Matarsa zaici. Taitamai tsiya kuwa, itadai Naja sai murmushi kawai take ta duk'ar sa kanta. Da Maman tagaji da shak'iyancin nasa tace itama tatafi gano nata Mijin. Bak'aramin burgeta sukaiba yadda suke abunsu faran-faran kamar ba Mahaifiyarshiba. Komansu a kammale ba raini in social life. Taji sunk'ara shiga ranta. Musamman mijinnata. Habeeb injita da fad'a dukdan karta ambaci sunanshi. Yayi-yayi da ita amma taki, irin abubuwan dasuke k'aramata Martaba da Daraja agurinsa Allah yai yawa dasu, banda zazzafar Soyayyar dayake mata wadda bazata misaltuba. Agidan suka wuni se dare sannan suka tafi tinda bawani nisa garesuba duk Unguwa d'aya ce.
Kubiyo *Didin anee*π danjin ya rayuwar Naja'atu zata kasance bayan Aurenta???
Β© *Aneesa_Didi*πΌππ
[2/18, 10:49 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: Didin_Aneeπ
β‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*β‘
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*46-50*
Da k'afa suka k'arasa gidan, shi yabud'e musu get in gidan tunda ba maigadi garesuba. Seda yakunna hasken gidan, Masallaci ya wuce dangabatar da Sallar Isha, ita kuma tashiga ciki, wanka tafarayi tagabatar da tata sallar, shafa tazaunayi rigar bacci tasa silk light blue, turare tafeshe jikinta dashi, kowana sak'o seda ta mulkeshi da nashi kalan turaren. Tahad'e gashin kanta da ribbon tareda d'ora hula aka. Jin shiru beshigoba yasata dawowa falon kallo takunna, Eternal Love take kalla a Ztv.
Bata dad'e da zamaba taji Karan rufe k'ofa Alamun yadawo kenan, da d'an saurinta tataroshi, kayan hannunsa ta kar6a tai kitchen, tana wawwarewa yashigo kitchen in. Yatayata aje kowane abu agurinsa ita kuma tayayyanka fruits in dayashigo dashi, tin a kitchen in yahau shan kankanar datake yankawa, dataga haka ta d'auke plate in kankanar ta ajemai na lemo dasauran kayan fruits in.
"Abun ma hakane? Yafad'a ashagwa6e kaman shine matar, ganin tayi blending in ragowar Kankanar, ido kawai yabita dashi tamarkad' kankanar tasa madara da zuma amemakon Sugar. A fridge tasa tagyara gurin suka fito atare daka kitchen in se murmusawa take ai kuwa ya hau fad'in.
"Shifa beyadda da wannan murmushin da take ba, tafad'a masa metake shiryawa.
Murmushin takumayi sannan tace "bakom muje nahad'ama ruwan wanka tinda ba abinci zamuciba. Tashige cikin d'akin tana dariya ganin yadda yabita da idanu kaman baisantaba.
"Ruwan wanka ta had'a masa wankanma seda ta lalla6ashi yashiga. Wai yayi fushi tinda tak'i gayamasa metake shiryawa. Kayan bacci tafito mai dashi tafeshesu da turare, tak'ara kintsa d'akin dukda bawani datti yaiba se bada k'amshin freshner yake.
Kallonta tacigaba dayi tanata farin ciki itama da Allah yabata miji irin Usman. Ganin yadda Sahiba da Ranveer suke zuba salon tasu soyayyan.
"Kitchen tashiga, ta d'auko kankanar datai blending tayi sanyi, bame yawaba tazauna tanasha, d'an sanyi dayai yanabin jikinta harwani lumshe ido take, k'anshin turarensa kawai taji tabud'e manyan idanunta duka akansa, k'arasowa kujerar datake yayi yazauna jikinsa na gogar nata. D'ebowa tai zata kai bakinta yai saurin kai nasa bakin, "irin dad'in dakike sha kenan ashe, yafad'a yana lumshe narkakkun idanunsa.
Sunkuyar dakai kawai tai murmushin de takuma, hannu yasa ya d'ago fuskar yahad'ata da tashi kowa nashak'ar numfashin d'an uwansa, yana mata wani sassanyan kallo dashi kad'ai yasan ma'anarsa. Cup in hannunta ya kar6a yana bata yanasha har suka shanye, seda yakalli News sukai brush yasunkuceta sukai d'akinsu. Tareda rufo k'ofa.
Safiyar alkairi.
"Kwance yake kaman bazai tashiba tinda yai bacci dagari yafara haske, bayan yagama yamutsa Naja atun Queen injishi da fad'a.
Wayan tak'ara ringin akaro na uku, jin vivration in yayi yawa yasashi bud'a ido da kyar. Ganin a sch inda sukai ne yai saurin ansa wayar, "ok godiya nake prop, Allah yak'ara girma. Yamike yashiga band'aki already yasan tahad'a masa ruwan wanka ilai kuwa tarufe mai ruwan yasamu yayi daidai wanka.
Wajen k'arfe goma yafuto, se kamshi gidan yake, yaduba ko ina batanan yai d'akinta.
Sark'a take k'okarin sanyawa, ya kar6a yasa mata har d'ankunnen yak'arasa shiryata, tana tabinsa da kallo ire-iren abubuwannan dayake mata nakulawa da soyayya su suk'e k'ara mata k'aimi wajen yin duk wani abu datasan zai farantamai yasashi nishad'i da farinciki cikin d'an zaman dasukayi tare. So da K'aunarsa kuwa sun mamaye jini da jijiyoyinta, duk wani motsi da zatai da k'aunarsa take, Addu'arta kullum suzama cikin so da k'aunar junansu da farinciki mai yawa a rayuwarsu.
"Rungumeta yai tabaya yad'ora ha6arshi a kafad'arta, suna kallon junansu ta madubin.
"Queen Tunanin mekike kina tare dani? Idan muna tare bakida sauran damuwa a rayuwanki. Am always there for you. *Ina tare dake*(Meemee bea ta) cikin kowana yanayi *Komai Rintsi*(Hama Gee). Kikasace dani kowana hali samu da rashi, cuta da lafiya yafad'a yana k'ara rungumota kaman za a k'wace masa ita.
"Hannayenta duka tasa tana shafo kansa, tahau rattabomai tsadaddun kalamai "kazama ni nazama kai mijina komai inzanyi dole saidakai. A kullum ina godiya ga Allah daya bani kai mai hak'uri da kawaici mijina takuma narkewa ajikinsa. Sund'au lokaci suna kallan junansu kowa na Sakar zuci sukasa dariya gaba d'ayansu yabata kiss a fore head inta, dak'yar yabari ta d'aura d'ankwalin suka fito dansuyi break fast.
Agurguje yaci abincin, shima saida tai kaman zata masa kuka yazauna dakanta tabashi Oat ne yaji madara da Omylet, tanad'e mai Pan cake a foil da ginger drink aroba yatafi dasu. Dan idan yai irin fitar wurinnan baya dawowa da wuri, takanyi k'ok'arin yimai dabarun dabazai sa yaji yunwa dawuriba. Tinda ba abincin ko ina yake ciba.
"A ranar ma kuwa se yamma yada gidan. Tana zaune itakad'ai se Radio data kunna, wak'an Nayi gamo ake tana tabin wak'ar dan tana santa(Miss zo6oπ) kawai ganin mutum tai jitai anyi sama da ita tai saurin rintse ido, yai juyi sosai sannan ya ajeta. Neman kujera tai tai saurin zama gudun fad'uwa, seda ta maida numfashi ta iya cemai sannu da zuwa, kusada k'afarta yazauna yana "Addu'ar dakuke min a kullum ta k'ar6u anza6eni cikin wanda akai sponsoring inmu miyi masters a sch in damuka baro, dan haka kihau shiri dake za atafi. Dirowa kansa tai tarungumeshi tanata murna itama, jin bakinsa tai cikin nata tin tana tirjewa harta soma maidamai da martani ganin yana neman zarcewa yasata janye jikinta tai gefe sunata ajiye nannauyan numfashi.
"Ruwa takamai yasha suk'a k'arasa maganar nanda wata biyu zasu tafi, kannan itama zata zaga dangi har gida zata tinda yau wata4 da zuwanta gidan bataje gidaba. Shiko yajajje gaidasu. Kafin magriba yatafi gida yagayawa Mamansu da Abbansu. Suji zancen suma. Sula kuwa samai Albarka dafatan samun Nasara arayuwarsu gaba d'aya.
*Bayan Wata biyu*
"Kafin lokacin seda tazazzaga dangi, dasukaje gida kuwa Inna kamar tacinyeta dan farin ciki ganin yadda 'yarta takuma cika da murjewa fata se shek'i take alamun hutu da kwanciyar hankali. Tawuni cir agida har mak'ota tazazzagaya.
Gidan Yayarsa Yusra ma takar6esu hannu biyu-biyu sukai ta hira kamar sun saba. Tahado mata abubuwa dangin kayan k'amshi tinda su take siyarwa.
"Daga getso suka ziyarci dangin mahaifinta, yacikasu da shatara ta arzik'i wanda basu sanshibama duk suka ganshi. Gusau suka wuce kwanansu biyu Anty husna kam tafi kowa farin cikin zuwansu. Tak'ara mata dabaru da sirrika irin na Mata masu aji.
"Seda sukai kwana biyar dadawowa daga Gusau sukai shirin tafiya Dabinai. Suka k'ara kwanaki acan yadda dasunda se shirin tafiya. Taga karamci da mutuntaka irinnasu, taita godewa Allah daya had'ata da miji da danginsa masu so da k'aunarta da mutuntata. Tsaraba iri daban2 suka had'o su dashi taita kunya ganin ita bawani abun azo agani takai musuba. Turaruka sai k'ananun turamen atamfofi takai aka rarraba. Sukai ta farinciki dasa Albarka.
"Tun ana sauran kwana5 sutafi kayansu sukai gaba a motar haya, se d'an abunda ba a rasaba, sunata shirin tafiya. Agidansu Usman ne Mama taita musu Nasiha musamman ma shi tinda ita bak'on guri zata shi bayau yafara zuwaba. Tajamai kunne yarik'e mata 'yarta Amana. Yaita dariya yana "ya kar6a to shi wazai rik'eshi? Allah mana inji Maman sukaita abunsu. Itadai Naja kanta a sunkuye. Tana k'ara san sirikar tata da irin d'abi'unta.
"Dayawa daga cikin dangi sunmusu rakiya, haka sauran likitocin da aka za6esu suma yawanci 'yan uwa sun musu rakiya. Akaita sallama da 'yan uwa da abokan arzuk'a. Se alokacin jikinta yai sanyi. Dan tasam zatai kewar gida da dangi gaba d'aya. Taita Addu'ar Allah yahad'ata da abokan zama nagari. Hawaye kawai yagani a fuskarta. Yasa handkchf yasharemata tareda kamo hannunta suka shiga jirgi, tak'ara narkewa ajikinshi tana kewar ahalinsu.
Kowa yabar gida.... Gida yabarshi inji hausa people..!!
Semuce asauka lafiya!
Team Naja'atu suna rakiya..π
Am realy sory makaranta. Zaku naji yanzu in sha Allah akai akai. Tnx 4 ur luv and prays. Luv u allππ
Β© *Aneesa_Didi*πΌππ
[2/18, 10:49 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: {5/12, 9:35AM} Didin_Aneeπ
β‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*β‘
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*51-55*
``` EDO STATE```
Saukarsu keda wuya babbar mota lexirius ta makarantar ita tazo d'aukansu, takwashesu dukansu masu mata da singles in d'alibai.
To tun amota Naja'atu ta lura da wani abokin karatun su Usman d'in ya kafeta da ido duk wani motsin dazatai a idansa yake koya ta d'ago ido sesun had'a ido dashi. Har aka saukesu a Staff Quaters, yawancin masu Aure 2 room apartment aka basu, sukuma marasa matan wasu suna Hostel wasu kuma su 4 gida d'aya aka basu.
"Gida ne matsakaici, babban falone da toilet ahad'e mai d'auke da d'akunan bacci kowanne da band'aki aciki, kitchen matsakaici se varenda.
Tinda suka sauka agidan ruwa kawai ta iya sha suka hau gyara ko ina, sauran kayansu ta aje kowanne a inda yadace. Ruwan wanka tahad'a masa yayi, itama tashiga tai.
"Ranar dai bai barta tayi girkiba. Darana abubuwan dasuka taho dashi sukaci da yammaci kuma yayo musu take away.
"Rayuwarsu a garin tai musu dad'i, rayuwa suke cike da so da kulawa ga junansu. Baya ta6ayin nesa da ita saidai in makaranta yashiga ko Teaching Hospital in da aka turasu. Dayawa mak'otan datayi ba hausawa bane, ita da Fatima matar abokin Usman d'ince sune kad'ai Hausawa itama ganin yadda Fatyn take fiffik'a da d'aga kai yasa tarage shiga sabgarta. Yawanci in yafuta gidan Maman Benue take shiga sita hirarsu takoyamata abubuwa dayawa irin na yaransu da abincikansu. Ba bak'inciki ko hassada zama suke na amana da mutunta juna. Kafin itama yanemarmata gurbi ta d'ora karatunta a Jami'ar tasu. Matsalarta guda ta wani abokin karatunsa maisuna Salis amma amfi kiransa da Baby. Yadda ko kallanta yakeyi seyai wani k'asa da idanu kamar d'an maye.
"Sallar walha ta idar tanata addu'a yau batajin fitar ma, bugun k'ofa take taji, tinaninta Usman ne to amma in shine a yanada key bud'ewa kawai