Showing 9001 words to 12000 words out of 30805 words
mana wannan rana dazanga Auranki 'yar jikalle.
"Assalamu Alaikum"
Sallamar Yunus ta katsesu,
Wa alaikumus salam.
Ummi tace "shigo mana Malam Yunus".
Ummi barka da safiya ya gida? Alhamdulillah. Ya mutan gidan?
Lafiya lau suna gaidaki.
"To madallah"
Sa'udun yaje 'dauko mota anan baya. Kajirashi. Gidan Husna ma zaikai Naja'atu.
Se asannan Najan tagaisheshi. Ya amsa cikeda fara'a.
Ummi nadawo Sa'ud yace. "Au 'dan halak yak'i ambato kajishima ya dawo"
A ah! Abokina yaushe kashigo? Yamik'a mai hannu suka chafke. Futama zanyi bara in'dan zuba ruwa. Daughter kina ina sry kinji bari nai wanka.
Kai kawu danAllah kabari inka dawo kayi. Aibawanda zai ganka, "toke haka zaki tafi baki wankaba" salon budurwata taganni ba wanka" kaga shikinanma sainaga antyn tawa, tafa'da tana murmushi. Aikam ba ayi hakaba Yunus yasako baki shima, "kidaiyi hakuri k'anwarmu yayi wankan seya kaiki ko? Nima nayi rakiya".
Shikinan karka da'de kawu. Suka fice yana fa'din "yanzu zaifito suje".
Tak'ara tattarewa Ummi gidan dukda bawani datti yaiba.
Basu sukaje gidan Husnanba saiwajen 12 na rana, Anty Husna tai matuk'ar farin cikin zuwanta, Naja ta tausaya mata ganin Tsohon cikin dake jikinta Haihuwa yau ko gobe, dasuka gaisa Kawu Sa'ud yaimata Sallama yatafi yana mamakin girman ciki irin na Husna.
Wasa takeda Khaleefa 'dan Anty Husnan, yaro 'dan shekara biyu da 'doriya, cikin kwana biyun datai sukai sabo sosai, abinka dame san yara da juriya da dabdalarsu.
Bayan tagama duk ayyukan gidan, ta 'dora musu girki. Shiru-shiru taji bata fito ba, seta bari cewa Bacci Antyn tata tasamu. Ganin har tagama girkin ranar, lokacin Sallah yayi bata fitoba, shiga 'dakin tayi da Sallama, ganin Antyn tata tayi durk'ushe, abakin gado. "Subhanallah" Anty lafia. Hmm kawai tace da ita. Ganin tarasa yaza tayi yasa tabugawa kawu Sa'ud waya yagayama Ummi Anty husna ba lafiya.
Cikin mintunan dabasu fi Arba'in na, saigasu shida Ummi, tanata mata addu'a, taha'da mata duk kayayyakin Sa'ud yakaisu asibitin datake zuwa. Dan mijinta baya gari. Ita kanta Ummin batai tunanin watan haihuwar Autar tata yatsayaba.
Naja'atu kuwa sai kuka take rungume da Khaleefa, dama haka haihuwar take, lallai iyayenmu sunyi k'ok'ari. Taji tasake san Innarsu ha'de da jinjina mata.
(Luv u my Innarmu. Mom like no otherππ).
Tasha wuya sosai, sannan tahaifi 'diyarta mace, akai tawaya anagayawa 'yan uwa da abokan arziki. Kansu dawo gidan har mahaifiyar mijinta da k'annansa sunzo gidan, seganinsu kawai sukayi.
saboda haihuwar Naja'atu tazauna se bayan suna.
*Kano*
Kamar yadda suka zartar, sati na zagayowa, Baba Sani da Baba Saminu, sukaje gidan Alh Abdul-mu'iz, Usman 'din dakansa yai musu rakiyar. Baban nasu kuwa yakar6esu da karamci irin na Kanawa, suka rattabo meke tafe dasu, "'Dansu yaga 'yarsa kuma yanaso". Domin subi k'a'idar musulunci yasa suka zo k'afa da k'afa, nemar masa izinin zaifara zuwa gurin ita yarinyar. Alh kuwa yai farinciki, tareda yarda da nagartar yaron, sawa yai akira Usman in yaganshi. Baba Sani yakirashi awaya, yazo yarisuna yagaida Alh Abdul-mu'iz cikeda girmamawa dajin nauyi. Yamasa 'yan tambayoyi, duk ya amsa, yasanar musu da Najan ma batanan taje ziyarar dangin Mahaifiyarta a Gusau.
Yamasu sallama yai waje. Basu tafiba saida suka bada ku'din zance. Tinda bawani lokaci sukeso a 'diba ba. Gaisuwa suka k'ara irinta manya, sannan suka rabu sunata zuba godia. Shi kuma Alh yashiga cikin gidan yasanar musu, kowa saida yai mamaki, bama Inna da bata ta'ba ji koda wasa Najan tai maganar Usman dinba. Amma wai gashi harda ka ku'din zance. Addua tashiga yi Allah yatabbatar da alkairi koma menene.
(Topha ita amaryar bama tasaniba maji magani dai).
*************
Ana i gobe suna duk taha'da komatsanta waje guda, ranar Suna kuwa, suna akai irin namasu rufin asiri ba alamun k'arya aciki, yarinya taci sunan Raheena.
Aranar sunan da daddare tatafi gidan Ummi dan gobe zatai sammakon tafia kano, anriga ankoma Sch shiyasa zata tafi. Kawu Sa'ud shi yamaidasu gida ita da Goggo, dan Ummi k'in zuwa sunan tayi. Jitai kamar kada surabu dasu Anty Husnan, barema Khaleefa boy inta hadda guntun hawayenta.
K'arfe 9 na safe, bayan sunyi karin kumallan safe, Ummi taita mata Nasiha akan rayuwa da kukanta sukai sallama da Ummin, tareda fatan Alkairy gaba 'dayansu. Suka ha'da mata tsaraba fal.
kawu Sa'ud yakaita tasha yabiya mata ku'din motar sai kano ta dabo timbin giwa.
*Aneesa_didi*πΌππ
[2/18, 10:47 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: β‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*β‘
*Na*
*Haleema G Khaleel*
2β£7β£-2β£8β£
Sassanyar iskar data chanja ce ta tabbatar da sun shigo Kano, a tashar mota ta Kano,line aka sauk'esu.
Drop in Taxi tayi har gida, yasauk'eta abakin Get insu, kayanta tafara shigarwa ciki, sannan ta mik'a masa ku'din yatafi.
Bakowa a harabar gidan, yaran duk suna makaranta, manyan kuma yawanci suna gurin sana'arsu. Da sallama tashiga cikin gidan, Deedat da wasu yara dabata gane suwaye ba sunata wasa, muryarta da Deedat yajice yasashi tahowa da gudunsa ya 'dafeta "oyoyo yaya Najata". Oyoyo autan Inna Deedat 'dina, suka sa dariya, ajeshi tai yai 'dakin Innar da gudu.
'Dakunan sauran matan gidan ta shishshiga, suka gaisa sannan tai 'dakin Inna. Tanata mamaki jin Gwaggwo Safiya, takirata da Amarya hadda Allah yasa akairy, yasa ayi dasu. To yaushe tazama Amaryar? Kowani abun yafaru batanan? Duk wa'dannan tambayoyin bata da me bata amsa sai Inna, jiki salu6e tashiga falon Inna, a kujera ta zube, tanata maida numfashi kamar wadda tai gudun shekara.
Inna ta futo daka 'daki tana "lafiyarki kuwa yayar Salim naganki haka?".
Seda ta rusuna tagaida Innar, tace lafiya lau kawai gajiyar hanyace. Sannu to yakika barosu? Ina masu jego? Ah tagayamin munje kasuwane lokacin da k'annan Abban Khaleefa, sunanan lafiya duka. Duk suna gaidaku har matansu Kawu Haruna da Kawu Bashir, Ummi ma tace gawani magani nan wai kitafasa mana dukanmu muna sha. Allah sarki Ummi, yajikin nata kuwa? "Alhamdulillah Inna dan taji sauk'i sosai" kawu Sa'ud wankane kawai baya mata. "Ina ruwan Sa'ud, nagadai yazasu rabu da Ummi, wannan shak'uwa tasu."
Ai Inna nagayamasa kawai inyatashi auren yai zamansa a gidan, yasa dariya yaga kamar wasa nake masa. Yacede zai duba. Allah dai yai mana jagora Innar tafa'da tafita zuwa 'dakin Babannasu.
Sallah kawai tayi tahau bacci, k'arar da Samiha tasane yasata farkawa agigice, ganin Samiha tai tanata tsalle ha'de da "ki'da da jikin wardrobb insu tana Wellcome back Amaryarmu, mata agidan Ya,Usman". Tanatayi. Binta kawai Naja take da ido, se yanxun tafara ```Tuna baya```{Anty sumy takori} tatuno duk irin yadda sukayi da Usman 'din, tanan ya 6ullo kenan. Jitai hawaye yana bin kumatunta dabata tantance namenene ba. Bak'in-ciki ne ko Farin-ciki??.
Ganin tafara hawaye yasa Samiha daidaita kanta, zamatai akusada ita tafara bata hak'uri, Naja kuwa murya na rawa tahau tambayar Samiha meya faru dabatanan? Zayyano mata komai tayi, bata 6oyeba. Murmushi tai wanda dakajinsa na yak'e ne. Allah yashige gaba shikinan, tai ban'daki tabar Samihan hangame da baki.
Da maghriba, suna zaune a falon, Inna ta wawwarewa kowa tsarabarsa, aka kaimusu. Sungama cin abinci Inna takira Naja'atu, alokacin suka warwarewa juna duk abinda ake ciki. Naja bata musaba ta amsa. ```Tunda dama iyaye keda right dazasu za6awa 'yarsu budurwa mijin Aure.``` iyayen iyayansuma da akaimusu auren basusan mazajenba sun zauna maiya samesu, gashi kuma har akasami wa'danda suka kasu duniya. Balle ita tasan wayema dazata Aura.
Albarka Innar taita sakamata ha'de da fatan Alkairy a rayuwarsu duka. Sukaita hira abinsu, hakan ba k'aramin kwantarmata da hankali yaiba.
Bayan isha, dasuka ci Abinci suka gyara gurin, da taimakon Samiha suka gyara kayanta, taha'da duk abinda zata buk'ata, dan gobe dawuri zata shiga sch tanemi time table, sun shiga final semester se sun dage. Kowa yanemi makwancinsa ya kwanta.
Wannan kenan.
Usman bek'ara kiranta a wayaba tunda akace batanan, koda aka koma sch dayaga bata dawoba, ya kar6an mata time table, Lectures in datai missing yasamammata Hand-out da manual, wasu har jotting yayiyyimata ajiki. Duk yaha'da yasa a leda yabawa su meenoh da Jidda Ja'o subata watak'ila kozata shigo shi bayanan. Suma sunyi mamaki daganin haka. Seda yace musu ma shi Visitin lec ne suka k'ara mamakantuwa.
Da safe duk suka shirya suna Karin,kumallon safe suka fice, har Deedat ansashi awata Islamiyya tasafe. Inna ka'dai suka bari a 'dakin.
Su biyar duka suka tafi a Napep aka sauk'esu a Kuntau, itama aka sauketa aka wuce da Fawad Al-Azhar shi acan yake.
Kamar sun ha'da baki suka ha'du da Meenoh. Seda sukaje class suka ha'du da Jidda Ja'o sannan su Meeno suka gaggaya mata abubuwan da akai batanan. Suka mik'a mata sak'on da Usman yabadar subata. Amsa tai taimusu godiya dukda tasha mamakin zak'ewa irin tasa.
Lectures sukai tayi babu wani interval sosai, saboda semester ta chanja.
K'arfe biyar suka tashi, sunzo fita abakin get taganshi se asannanma tasan yana cikin Makarantar dan sam bata ganshiba se yanzu.
Matafiya kuma tafiya ba sallama? Shiru tai kamar bada ita yake ba. Har suka fita wajen makarantar. Ba abinda yadameshi. Yanata janta da hira.
Seda taga idanu zasi musu yawa tasakammai wani mischevious smile, jiyai kamar yarungumota ajikinsa, amma babu halin haka.
"Kayi hak'uri ka tafi"
Babu halin sauraranka anan.
Badan yasoba yajuya yatafi. Yana mai farin cikin yau Queen of Heart inshi tamasa magana.
*Didi_Aneesa*πΌππ
Anisadidi.pun.bz
[2/18, 10:47 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: 11/11, 3:47PM Didisco
β‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....* β‘
*Na*
*Haleema G Khaleel*
2β£9β£-3β£0β£
Dawowarta kenan tazo wucewa ta k'ofar part in Babansu, Alh yayo kiranta dayaga wucewarta, Sallama taimasa tarusuna tagaidashi cikin ladabi da girmamawa daya kamata duk wani 'da nagari yayiwa Iyayensa.
Suka gaisa ha'de da raha kamar ba 'diyarsaba. Dan yana tsananin san Naja'atu sabida biyayyarta agaresh da hak'urinta.
Naja'atu yakira sunanta. Kiyi hak'uri namiki laifi, "Subhanallah" Baba dan Allah kadena fa'din haka, kana da damar dazaka bani kowana umarnine nabi, in dai ba sa6awa mahalicci neba, matuk'ar inaso inga Haske a rayuwata.
Alhamdulillah! Alh yace "Abinda yasa kenan banji 'dar ba na amshi ku'dinsu nasan bazakiban kunya ba".
Amma dole innemi amincewarki inkin yadda Alhamdulillah. Inkuma bakyasanshi, se amaida musu da ku'dinsu. Yace "kin amince naja'atu koba kyaso?
Sunkuyar dakai tayi ta'dan saki gajeren murmushi, abinka da manya kuma dama *(```Amincewar Budurwa shine Shurunta, Bazawara kuma Maganarta```)*.
Alhamdulillah Alh yace, "Allah yayi miki albarka yasa alkairy arayuwarki yasa kigama lafiya". Ameen Baba. Yayiy yimata nasiha ha'de da yaba Nagartar yaron. Yauwa tashi kije, kituran Innar taki. To Baba nagode.
Sanyi taji zuciyarta tana mata, dukda dai ba sansa takeba, amma zatai ta addu'ar neman za6in Allah tai sallama tashiga 'dakin Innar.
Inna Baba yana kiranki, har kindawo, ah daka gurin baban nake to ina zuwa, tanufi 'dakin Alh.
Zamatai da nufin tahuta, kafin lokacin Sallah yayi, wayarta tashiga k'arar *Antudd kilani Rabbil janna...*, kaman bazata 'dagaba taji da'din kwanciyar datai, mik'a hannu tai tajanyo jakarta, wayan tazaro tai Reciev batare da ta duba wayeba.
Nannauyar ajiyar zuciya taji a kunnanta, "Amincin Allah yatabbata agareki Sanyin idaniya tauraruwa mai haske acikin taurari"
Tare dakai amma dukni ka'dai wanna kirarin, tasamu kanta da fa'da. "Aikinfi hakama words can express how spcl you are" murmushi tayi, tamasa godia, balaife ta 'dan saki jiki sukai hira, dukda rabi hirannasu akan karatune.
Seda zasi hang up yace dole tai fixing date da time dazaizo har gida, kunya ta lullu6eta kaman yana ganinta. Wai yau aganta da namiji tana zance a gida yazatai? "Kinyi shiru kobaki so nazo? A a kawai dai kaban time zan fiddama randa zakazo, "ok tom no prob amma fa kada ki waladdani".
Allah bazan wahalar kaba, but sekamin uzri kaga sch yanzu ta'dau zafi last semester innan. "Hakane kada kidamu, kita Addu'a dai akuma dage, Allah yabaku sa'a".
Ameen nagode Allah yai jagora yace Ameen sukai hang up wayan yanata farinciki. Hadda ```Sujudu shshukur/sujjadar godia```. Dan tsantsan farincikim daya samu kanshi aciki.
Seda yai sallah Isha sannan yashiga gidan, Yanata bu'da hak'ora, Ah A "ko tallan maclean kafarane?" Maman tasu tace tana k'aremai kallo, kokuma Aikinne yasamu?
Adai tayamu da Addua Mama komai yakusa kammaluwa in Allah yayarda, "Allah ya yarda yatabbatar da alkairy, ai haka akeso.
Jiyai yana jin nauyinta, be iya gayamata komaiba akan Naja'atun 'daukar Abincinsa yai kawai yanufi 'dakinsa.
Shirin Duniya tumbin giya takeji agidan Radio, tana zaune akan sallaya gefanta kayan karatuntane, Tirrrrr taji 'yar Nokia tata tayi, message ne ya shigo.
"Nasamu kaina dajin kunyar Mama, nakasa gayamata komi dangane dake, dukda a 'dokance take taji harma gani daka kyakykyawar Surukartata."
Tamaidamasa da
"Hmm topha inni cema ai bazan iya gayaba."
"Kema kenan dannasan bakece 'diya tafarkoba?"
"Marabarmu dasu sutafara haifa amma dani ake kunyan 'yar farin hmm.".
"Hakane amma kinsan ya za ai?
"Ah ah saika fa'da"
"Kawai zangayawa Matata wato uwargidanki ta fa'da mata."
"Mata kuma??
"Ah mana kobakisan inada Mata ba? Kishiryama gidan mai mata zaki"π
Reply in dabata sake maidawaba, dama wannan yanada mata amma baigaya mata ba? Yanzu yazatai, gashi tarigada ta amsa a wurin Baba, da fasawa zatai, dan ita bata marmarin auren mai mata, kodan irin wuyar da Innarsu tasha, dukda bata yadda sanshi takeba.
Anya kuwa Naja'atu?
Kodai kinyi gamo? Kihine dai kawaiπ!!!
Sory 4 late post
So many isues nakeda.
Afuwa plss makaranta ina k'aunarku duka. Allah bar zuminci.
*Aneesa_didi*πΌππ
[2/18, 10:48 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: 13/11, 12:20PM Didi
β‘ *DUTSEN CIKIN RUWA*β‘
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*31-32*
Ta dad'e tana mamaki, har sarkin iya sata yasaceta daka inda take.
Jin shirun yai yawa bata damai da reply ba, shikad'ai yaita dariya abinsa. "Nafara gano lagonki Queen of my Heart". Seda yai salloli da Addu'oinsa sannan yakwanta, da tunanin Naja'atu.
Abaya idan akace zaiso wata macen bayan Bilkisu bazai ta6a yadda ba, amma yanzu gashi daga had'uwarsu da ita komai ya chanja, yanzu yafahimci Soyayyar, duk zaman dasukai abubuwan dayakeji dangane da ita Tausayine, yanzune soyayya tai masa *Dabaibayi* taimasa kamun da saiya had'a da Addu'a, karta sashi a mawuyacin hali.
Jitai kaman ana magana akanta, tafarka da addu'a a bakinta, Innarsu tagani cikin yanayi, tayi k'ok'arin tashi amma takasa koda motsa k'afarta, Naja'atu tace "Inna miyasameki? Lafiyar Allah muka kwanta".
"Kamamin Naja kikaini band'aki" tayi mamakin jin Innar ta ambaci sunanta yau. Da taikamakon Allah tataimaka takaita band'aki, har alwala tai tadawo da ita kan sallaya tazaunar da ita, alwalan itama ta d'auro, taita nafilfili tana kai kukanta gun Rabbi da nemawa Innarsu Afuwa.
Har aka kira assalatu, Innar daka zaune tai sallar, itama tai *Raka'atanul-Fajir*, ta d'ora da Sallar asuba.
Zamatai tanata zikiri, har gari yafara haske, data duba taga Inna tasamu bacci, tashitai tahau kintsa d'akin nasu, tasa Kamal, Salim sukai wanka taiwa Deedat, itama tayi, Samiha kuma duk tahad'a musu kayan karin safe, Inna tafarka tagaduk shinrya, suka gaidata tareda yajiki, addu'a tamusu sosai sannan suka tafi.
6angaren sauran mutan gidan suka biya, suka gaidasu tareda sanarmusu halin da Innar ke ciki, sabida halin rayuwa. Naja tace da Maman danAllah in Iya tazo tasa tataimakawa innan kafin sudawa. Suka tafi makaranta.
Wunin ranar haka tayi sukuku, dandai kawai makarantar suna zangon k'arshene, bataso tasake dawowa inta tafi kawai tatafi, wani sashen na zuciyarta tatuno yanda suka k'are da Usman adaren jiya. Jitai ma komi yafuta akanta, taita Allah Allah atasi.
Sunagama lectures in ranar ko Sallahr, la'asar bata tsaya tayiba tatafi gida, seda ta duba Innar hankalinta yad'an kwanta, sallah tai sannan tataimakawa Innar tai wanka tareda Alwala. Tashafeta damai tasamata kaya, abincima dak'yar taci kad'an.
Homework suke koya musu Fawad da Samiha, itakuma tana harhad'a musu kayan wanki da Unifoam insu,
Inna tana daga d'aki, tari yasark'eta, yitake ba k'ak'k'autawa, dagudu duk sukayo wurinta, me mik'o ruwa nayi masu sannu nayi, Naja dak'yar ta d'agota tanata hawaye, Fawad fita yai da sauri yaje ya fad'awa Babansu yanatareda Idrisa Dauda da Hafiz, atare duk suka shigo d'akin, shigowar Ibrahim kenan, yada daka wurin shirye-shiryen tafiya makarantarsu, Isma'il kuma bayanan.
Sukai ta mata sannu, abin kaman k'arashi ake, ganin haka yasa Alh yace akaita asibiti.
Asibitin Nasarawa aka kaita ```Emergency``` Dr,Badariyya itakeda duty a lokacin, aka kwantar da ita Drip tafara samata, tai mata 'yan tambayoyi, tarubuta magunguna da allura asiyo mata.
Ya,Hafiz da Ibrahim ne sukaje ```Pharmacy``` suka siyo magungunan da alluran aka bawa Inna maganin, allurar kuma akasa cikin drip in.
Abu kamar wasa jikin Inna yak'ara tsanani, dole aka bata gado. Naja ce ke kwana, dasafe kuma Isma'il da Ibrahim su wuni, tunda basu tafi Makarantar ba sukuma sauran k'annannasu sede akasu jefi-jefi saboda Makaranta.
Haka ta had'a da zuwa Makaranta da zaryar asibiti, tsawon sati biyu Ummin tama da Anty Husna saida Kawu Sa'ud yakawosu suka