Showing 27001 words to 30000 words out of 30805 words
yadda yagayamata, Innartamusu fatan alkairy da za6in Ubangiji.
To 6angaren Sulaiman yagayawa Ummansa yasamu Mata, amma Bazawarace hadda 'Ya'ya biyu, Umman tai shiru kamar bazatai maganaba.
"To amma ita yarinyar tana sanka?"
Murmushi yai yace
"Batada matsala Ummana ki amince tazama Surukarki, Matar d'anki, dazata bawa Autanki cikakkiyar kulawa."
Umman tadubeshi tareda cewa "to Allah yatabbatar da Alkairi."
Rungumeta yai yace "ina sanki Ummana, Nagode Nagode yabata peack agoshi."
Dariya Umman tahauyi, tana hango yadda Matar dazata Auri Sulaimanunta zatai d'awainiya dashi, da shagwa6a dukda ya girma befasaba.
Sukaita hirarrakinsu kafin akirashi awaya yafice daga Gidan.
Fad'uwar da gabanta yake ya tsananta aranar, tunda Sulaiman(Uncle mai Zane) yace mata zaizo.
Simple makeup tayi, ita kanta kwalliyarma takwan biyu bataiba. Less _Mint Blue_ tasa riga da skirt tai d'aurinta daidai da zamani, spray tasa kad'an da turarenta _Urban Woman_ ta d'ora babban gyale akan kayan. Jelolinta Hassan da Husna suna gefanta suma sunsha ado. Sun nutsu kamar basuba kar ace kartace bazata fita dasuba. Ta dubesu tai murmushi.
Wayarta tashiga Sauti, Hassan dasaurinsa ya mik'a mata, ganin sunan "Uncle Sman" a Screen d'in wayarta, dan haka tai _saving_. Samun kanta tai da rikicewa kaman bata ta6a tsayawa da namijiba. Seda takai zuciyarta nesa tad'aga wayar. Cikin sassanyar muryatta, ya amsa tareda langa6ar dakai "Ran Gimbiya yadad'e, fatan nasameku lafiya?"yafad'a kamar yana gabanta.
Murmushi takumayi, suka gaisa yasanarmata dagashi ya iso, tasa aimasa iso. Seda tai jim sannan takashe wayan.
Innarsu tasanarwa take tasa Fawad yashigo dashi falon bak'i na Babansu, Ruwa tabayar aka kaimasa da leman d'anyar citta, daya d'au sanyi dai-dai sha had'eda Meat-pie.
Akunyace tacewa Inna bari taje, tabita da Murmushi tanaimata Addu'ar samun Alkairy.
Zaune yake d'aya daka cikin Kujerun falon, wadda take fuskantar k'ofar shigowa, yanata danna wayarsa. Sassanya kuma Zazzak'ar Muryatta datai masa Sallama tasashi d'agowa, ya amsa idanunsa akanta, sanda ta d'ago itama idanunsu suka had'u, dukkansu saida wani bak'on al'amari ya tsirga musu, itatai saurin d'auke idanunta ta sunkuyar dakanta.
Tana guri guda daka can gefe tazauna, su Hassan da Husna suka gaidashi kowa ya mak'ale agefan kafafun "Uncle mai Zane" injisu da fad'a.
Naja'atuma ta d'ago kai tareda rusunawa tagaidashi "Barka da Yamma" muryatta kaman ana busa sarewa.
Ya maidamata da "Barka kadai Mai kyau, nasameku lpy?"
Murmushi tai daya k'ara fito da tsantsar kyanta. Tace "Lafiya lau ya mutan gida?"
Hira yaitamata, dukda rabin hira ta Yarantace, Hassan da Husna, sedai tad'an saki jiki dashi kad'an.
Jaka yad'auko agefansa guda biyu, yabasu kowa d'aya ahannunsa yace "Sukaiwa Inna" danduk yaji labarinsu gurin 'yan biyu, yahad'asu da Sweat suka fita sunata Farinciki. Dukkansu suka bisuda kallo suna murmushi.
Haske tagani Walll! Tajuya tana kallansa, yasakar mata k'ayataccen Murmushinsa daba kowa yakewa shiba. Waya tagani a hannunsa alamun Hoto yamata. Sulaiman Ganindayai takafeshi da _Bold Eyes_ d'inta yasashi cewa "Am sory Ummana zan kaiwa taga Surukarta mai kyau that why nai Snapinng naki dukda Original Pic inki yananan Album guda a Bottom of my heart" sunkuyar dakai takumayi ganin irin kallon dayake binta dashi yace "Lallai yau kinaso nakwana gidannan indai zaki cigaba damun wannam Smile innaki dake tafiya da Ruhin mai kallo, Uwa Uba Kunyar ki datake k'aramin shauk'in san kasancewa tare dake."
Anan yarik'a bayyana mata *Babban Sirri (My Yaya Hajja Novel)* dake ransa. Ita kuwa Naja'atu mamakinsa take daga *Had'uwar Farko* mutum ya zak'e, lallai saitayi dagaske zata gano irin San dayake mata bata k'ara mamakantuwaba seda taji Sulaiman yace "Naja'atu ga k'ask'antaccen bawa yazo gareki da k'ok'on barar soyayya har tazama ta Aure *Ni dake (Phertylicious ta)* muzama k'ark'ashin inuwa d'aya, ga miji yazo gareki akaro nabiyu. Amma zanbaki lokaci ki shawara saidai da had'uwarmu da Auren bazai wuce wata biyuba banma son hakan."
Baijira maizata ceba yaimata sallama yatafi.
Ita kuwa Naja'atu bin bayansa tai da idanu harya fice. Dak'yar tatattaro dukkanin nutsuwarta tashige cikin gida.
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: *♡DUTSEN CIKIN RUWA.....♡*
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*94-95*
~~~Lokutan dasuka biyo baya, duk batada sukuni. Gani tai Tunanin bazeje mataba sai tashiga adduoi da neman za6in Allah.
Har d'an fad'awa tayi yasa Inna takuma mata nasiha.
Kullum cikin dare zatai Nafila Raka'a biyu ta *Salatul Istikara* tai addu'a danneman za6in Ubangiji.
_Garemu 'yan uwa Musulmi yayinda wani abu yashige mana duhu komike shiga dabaibayi gameda neman abu ko samun abu na Rayuwa, Neman Aiki, Neman Aure, Karatu. Wani Abu dai makamancin haka. Inmukai hak'uri komi mai sauk'i ne_.
Cikin Hisnul Muslim(Garkuwar Musulmi) dasauran Litattafai na Addini da Addu'ar tazo.
*Jabir bin Abdullah Allah yak'ara musu yarda: Manzan Allah S.A.W yakoyar damu ISTIKHARA acikin kowane al'amari kamar yadda yakoyar damu sura daga Al-Qur'ani yana cewa:- "Idan d'ayanku yana dawani Al-amari seya Sallaci Sallah raka'a biyu, badaga cikin Farilla ba, seyace:-* ```ALLAHUMMA INNI ASTAKIRUKA BI ILMIKA, WA'ASTAQ DIRUKA BIQUDRATIKA, WA'ASALUKA MIN FADHLIKAL AZEEM. FA'INNAKA TAQDIRU WALA AQDIRU, WATA'ALAM WALA A'ALAM, WA ANTA ALLAMUL GUYUB.
ALLAHUMMA INKUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA(ka/ki fad'o Matsalan taki ko wani abu daki/ka ke nema) KAIRULLI FI DINIY WA MA'ASHI WA'AQIBATA AMRI, FAQADIRHULI WAYASSARHULI SUMMA BARIKLIY FIHI, WA INKUNTA TA'ALAMU ANNA HAZAL AMRA (ki/ka fad'o matsalan kowani abu daki/ka nema) SHARRILY FI DINIY WAMA ASHI, WA AQIBATU AMRI FASRIFHU ANNIY WASRIFNIY ANHU, WAQADURHULI KAIRA HAISU KANA SUMMA ARDINIY BIHI.```
Yaitayi in sha Allahu zaisamu daidaito da za6in ubangiji.
**********
Sulaiman kuwa, Mahaifinsa yasanarwa yasamu mata danhaka Addu'ar dasuke masa akullum lokacinta yayi, sai aje anemomasa Auren.
Ba jimawa Manya suka shiga maganar, aka tsaida za'a d'aura musu Aure tareda 'yan uwanta inyaso tatare daga baya.
Shirye-Shiryen biki ake tayi. Amaren Gidan se kintsasu ake da gyata according to Sunna.
Wayar da Sulaiman kemata, sema abinda yak'aru, har fad'a sukeyi yadda tak'i sakin jiki suzuba Soyayya dashi. 'Yan biyunta su Hassan da Husna sun zama 'yan Gidansu "Uncle mai zane" bawanda besan dazamansuba se yayunsa dabasanan kokuma insunzo lokacin bekasuba. Yazama wani sashe narayuwar yaran dayalashe gurbi dadama a zuk'atan yaran da 'yan uwan Naja'atunma tukafin ya Auri Mahaifiyarsu. Hakan yasa duk yasamu Shaidun k'warai dakykkyawan zato.
Agajiye liss! Tadawo gida daka Sch karatun yad'auko k'arewa basuda wani hutu inba _Exams_ dake gabansu sukai suka gamaba. Ga abubuwa duk sun had'e mata, wayanma ba kasafai take barinta akunneba.
Ruwa tawatsa tazauna tana hutawa, dan fashin Sallah take alokacin. Riga ce Bubu me fad'i ajikinta me launin ruwan Madara tasaka hula ruwan k'asa se k'amshin turarenta na _Urban Woman_ take. Wayarta takuna bata jimaba kiran "Uncle Sman" yashigo kamar bazata d'agaba.
Jin sassanyar muryatta yasashi sakin wata wahalalliyar ajiyar zuciya yace "Haba Mamynmu(inyaso raha haka yake kiranta dashi) kina wahal da daddyn yarafa, ko laifi nayi bansaniba?"
"Ah ah fa Uncle"
"To miyafaru?"
"Allah Uncle ina busy ne dayawa kasan munkusa fara _Final Exams_ dole wasu abun semun hak'ura dashi mi _Concentrate_ akaratunmu kodan muwuce gurin kawai."
Tafad"a dawata irin Murya a shagwa6e.
Numfashi Sulaiman yakuma saki yace
"Allah sarki kice inzo miyi karatun tare, bakomi ma ai nasan Mamynmu _Gifted_ ce ko _Guru_ zance?".
Dariya tasaki tana "kaikam kacika tsokana. Nidai katayani Addu'a kawai."
Irin muryatta yakwaikwaya yabata amsa. Dariya takuma saki sukai ta hira kamar karsu rabu.
Abinda yai shirin fad'a mata ma yabarshi ganin abubuwane agabanta ba kad'an ba.
"Ina sanki Naja'atu"
"Hmmmmmm! Alamun ajiyar zuciya yaji. "Nibazakice kina sonaba?"
"Ina sanka mana Uncle, kaine sanyin idaniyata dazaka maye gurbin abubuwa dayawa... harda zuciya...." bata k'arasa fad'in maizatace ba da _Hanging_ wayar ganin shigowar Inna dasu Ibrahim da Isma'il Yayunta, wanda alokacin sunzama matasa sosai dako Auren kowace mace sukaje nema za abasu yadda Allah yaimusu kwarjini da Baiwar kyau tsantsa. Sunkuyar dakai tayi tana juya Cup in hannunta. Ganin basuce mata komaiba, taware sukaita hira wadda yawancinta ta bikin dazasine da yadda suke shirya Al-amuran sukasance cikin lafiya da kwanciyar hankali har agama bikin.
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*96-97*
~~~Da ikon Allah, aka fara shagulgulan biki. Hausawa sukace Rana bata k'arya.....!
Asabar 12 gawatan Goma dubban jama'a suka shaida d'aurin Auren 'ya'ya hud'u na Alh Abdul-Muiz Auwal, Namiji d'aya da Mata Uku. D'aurin Auren yaya Hafiz akafara d'aurowa Tudun maliki, da Amaryassa Maryam.
Juwairiyya da Angonta Aminu. Samiha da Mukhtar, wanda silar had'uwarsu Allah yamasa shiriya kamar dawasa suka fara Soyayya da Samiha kuma Allah yai matarshice takaisu gayin Aure ayau.
Akaro nabiyu aka kuma d'aurawa Naja'atu Aure da Angonta Arc Sulaiman Kazaurw.
Yana daka cikin Al-adun bahaushe nawannan lokacin yayin Aure. Bayan and'aura Aure, Angwaye da abokanansu, sukan shiga gidansu Amarya domin gaisawa da Iyaye Maza da Mata. Hakance takasance gidan Alh Abdul-Muiz A yacika fal da Jama'a masu Hotuna, da Marok'a seyi suke.
Mazajen Samiha da Juwairyya se hotuna ake musu haka Yaya Hafiz ma anatayi dawasu 'yan uwan. Sa6anin Sulaiman dayakasa ganin tasa Amaryar se washe baki yake kaman gonon Auduga. Abokansa kam se tsiya suke masa.
"Yanzuke hakan dakike yayi dai-dai kenan? Inma bazaki shiruba yaci kin kammala shiryawa" Inna data shigo tatsaya akan Naja'atu datake ta shar6an kuka, tunda akakusa bikin tazama sukuku da ita duk tasusuce banda ramar data kumayi. Dayawa sunmata magana tak'i shiru sega Innartasu takuma dawowa.
Anty Husna ganin datai kamar Inna zata rufe Naja'atu da duka tai saurin matsawa kusada ita, Lalla6ata tashigayi ahankali tana mata Nasiha "Haba Daughter na kedama bayau ko gobe zaki tafi gidan mijinba. Ko Samiha kiduba daza akaita gobe batai wannan kukanba ammake anrasa Kukan mekike ko Aurenne bakyaso?" Tana kallanta ta girgirza kai "To maza kishiru kinji Aure ai Ni'ima ne da Daraja. Shine Cikar Zati Kamala da Mutuncin duk wata 'YA MACE muddin tarik'e mutuncinta tobamai kyetamataahi. Kuma kowace Uwa dakikagani Burinta ta Aurar da 'YA'YA MATAn dake gabanta shine samun nutsuwa da kwanciyar hankalinta. Kowa kuma da haka tasaba. Maza k'arasa shiryawa kar Mijinnaki yazo yaganki haka, kinji 'yar albarka". Shiru tai duk tasaurari metace k'awarta Jidda da Mino dake fama da ciki sukai tamata iya-ege, ahaka suka k'arasa gyaramata kwalliyarta data 6ata da kuka suka Shirya fes da french less coffee colour damayafi milk&coffee har kanta se k'amshi take Amarya tafito fess da ita se ajiyar zuciya datake saki.
Gud'ar dasuka jiyoce, taji wata mata dabata gane waceba tanata Kabbara, sekirari takewa Inna da 'Ya'yanta. Sulaiman suka shigo har falon Inna gaisawa sukai tayi da 'yan uwa dake falon. Anty Husna tajata suka fito falon, kanta asunkuye. K'walla tataru a idanunta. Masu hoto da masu d'auka da waya sukai tayi hasken Flash kawai kake gami.
Kukan datake 6oyewa ahankali take shashshek'a, Sulaiman datun shigowarsu seda yaganta farincikinsa yak'aru. Bayan mutane sund'an ragu a falon, duk'addakai Sulaiman yai yad'an tallafo Naja'atun sesuka bada wani Style masu Cemara kam mezasiyi ba hotoba akaita _Snaping_ insu. Ni Aneesa_Didi Duk k'ok'arina na injiyo muku meya cemata akunnenta banjiyoba murmushi nikaina nasa ganin kowa yana darawa.
Itakam ganin Sulaiman naneman bata kunya yasata sakin murmushi tareda janyewa daka jikinsa nikuwa nace kaga Masoya. _Gud Moment_ kenan "Tears & Smile".
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:50 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*98-99*
~~~Haka akai biki aka gama cikin farin ciki da Annushuwa, su Husna da Hassan shigar sababbin kaya akai tamusu. Yara masu kyau dashiga rai, kowa sansu yake duk inda suka shiga kamar kasace kagudu abin gwanin ban sha'awa.
Inna nasa k'afa suma suna sauke tasu ko ina suna biye da ita sabida Mamynsu Hauahin kowa takeji jin ance "bazata tafidasuba kosu koma gidan Kakanninsu, duk dashi a 6angarensa bashida matsala Sulaiman ya amince zai Rik'esu koba komai Rik'on Maraya Ladane kuma D'A NAKOWANE. Amma iyaye sunce sesun duba labarin. Hakan yasata 6acin rai.
Sharar hawaye take akai-akai yaranma ko kallansu batayi.
Washegarin ranar lahadi. Daga cikin yayunsu mata Anty Husna ma tabi wanda zasu gidan Samiha suka tafi gidan Amaren dan k'ara gyagygyarawa kafin akai Amaren.
K'arfe uku na yamma agogon Nigeria Niger da Chad. Shirye shiryen kai Amare Juwairiyya da Samiha ake ana la'asar za akai kowacce gidan Mijinta.
Inna dai bata tankaba ganin ita Naja'atu se shirye, shiryen fita take da alama 'yan kai amarya zatabi. K'anwar Babansu Gwagwgwo ta Getso tashigo ganin Naja'atu tana fesa Turare yasata cewa "Hala kai Amarya zaki kema?" Sunkuyar dakai tayi "Ah Gwaggwo dan Allah kuje dani" cike da shagwa6a tai maganar hadda langa6ar dakai.
Dariya sukayi 'yan d'akin. Gwagwgon takuma fad'in "Ai tafiya dake babu matsala mutuk'ar dayaddar Mijinki maizai hana mutafi dake, tunda ke tariyar ba yanzuba." Ai jitai kamar tasa ihu! Matar wansu dasuke mutunci da ita tace "Maida wuk'ar yanzu da Aure akanki, inda zaki fita dole saida izinin ma'ana kin tambaya komai kinma sani ai, sedai k'arin bayani. Ki kirashi kisanarmai inya amince muje mudawo ko Gwaggwo?".
Naja tai shiru tamkar bazatai maganaba. Ganin anata shirin tafiya kai amaren har anshiryasu ankaisu gurin Baban dasauran Matan Gidan sekuka suke. Yatsuna fiska tai kamar tahak'ura ma dazuwa, tai tunani to aikuma batada ranar zuwa k'ara taje yanzu ayama.
Kiran layinsa tayi seda tai Ringin Hud'u yad'aga "Ran Gimbiyata kuma Amaryata yadad'e!" Rasa maizatace tayi dabara tafad'o mata tace "Tare dakai fatan kana lafiya?"
"Alhandulillah, muna lafiya dani har Matata dakowama."
"Uncle mai Zane"
"Na'am Mamyn uncle mai zane"
Shiru bawanda yakuma magana sai numfashinsu dake shiga kunnuwan junansu.
"Dama wai zanbisu kai Amarya shine wai Gwaggwo tace sena tambayeka" tafad'a harda cuno baki kamar anmata dole.
Dariya Sulaiman yai sosai lallai Matar tasa 'yar daruce ko rigima zaice. Jin yana dariya taji inama bata kiraba, kamar takashe wayan taji sedai koma takashe abanza kiranta zaikumayi. Taji yace "Tajirashi yazo yakaita dakansa danba mai kallrmasa kayansa"
"Haba Uncle ga Jama'anan muna zuwa zamu dawo damafa Gwaggwo zamu."
Duk yadda tabi k'iyayi dole shid'in yazo yakaisu. Samiha ita banisa cikin Unguwarsune. Juwairiyya itakuma aka kaita Hausawa.
Semuce Allah bada zaman lafiy da k'azantar d'aki amma bata sharaba.
Exams in su Naja tazo shikansa Angonnata Sulaiman sarara mata yai dayin Waya. Dantasamu tai karatun final Exams inta. Dataimakon Allah suka kammala exam inau da makarantarma duka sejiran sakamako.
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:52 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
® *Haleema G Khaleel*
10 jan 2017
*100*
🔚
*_But if they intend to deceive you. Then sufficient for you is ALLAH. It is he who Supported you with his help and with the believers._*
~~~Tunda tafara exams Sulaiman ke kaita yadawo da ita harta kammala.
Watarana yad'aukota daka sch suntsaya a _Go slow_ a junction mutane se hada-hada, suke. Un expected taji anrik'o hannunta abinda Sulaiman beta6a mataba, dagashi har ita wani _Haptonasty Reaction_ sukaji sosai yakuma rik'o hannunta ganin abinnasa nakuma k'aruwa cike da shagwa6a ta turo baki "Allah kaban tsoro kuma sena rama" dariya sosai tabashi yadda bakinta ke motsi da shagwa6anta ya birgeshi yace "to ai nariga nabiya dan wannan kawai, barikiga kad'an daka ciki..." Gaba d'aya ya janyota jikinsa yafara Sumbatar bakinta cikin nutsuwa k'amashin Air freshner motar da Turarensu suka had'u suka bada wani Sanyayyan k'amshi mai Sanyaya zuk'ata. Hakan yakuma ingizashi yakuma rik'ota tako ina aikamata zazzafan sak'o yake yanakuma shafota.
K'arar horn d'in da ake yimusu yayi yawa, dole yahak'ura. Saurin komawa mazaininta Naja tayi d'ankwalinta dayazame tagyara had'eda mayafinta. Allah yasa Motar da Tinted, nawaje bazega nacikiba amma naciki naganin nawaje.
Sunkuyar dakai tai tana wasa da abin mayafinta, tafiya suka cigaba dayi. Jefi-jefi yana dubanta yana sakin wani k'ayataccen murmushi dake k'aramasa kyau da kwarjini.
Sunkusa kaiwa gidansu Naja'atu yai Parking dai-dai gurin wasu masu nama wanda anan suke siyan Nama kowane iri kakeso zakasamu agurin "Haleema Suya Spot" fita yai daga motan yace "yana zuwa."
Binsa tai da idanu aranta tana tunanin dama haka Sulaima yake shima d'an soyayyane, murmushi tai tana kuma tuna abinda yawakana mintina kad'an dasuka wuce.
Bedad'eba yadawo da ledoji a hannunsa. D'aya yasa abayan motar, leda biyun kuma ya d'oramata akan cinya yad'ora dacewa "Ga Tsiran Tsira da Soyayyanan da Kilish, dukda ni nasan tawa a Safe content take."
"Kai Uncle wannan Confidence haka"
Dariya sukai duka yaja motar yak'arasa da ita gida sukai sallama yawuce dan cigaba da shirin taryan Amaryassa.
Kwana biyu da gama Exam inta, Babansu yasa dole tatare asatin fad'a sosai yamata. Hassan da Husna karma susata kuka aka kaisu gidan kakanninsu. Maman aranta taso datana dawani babban d'a Namiji ya auri Naja'atun takasance cikinsu. Yanzuma addua da fatan Alkairy suka mata. Daga canma gidan Yaya Yusra aka kaisu yar Usman Mahaifinsu.
Ranar Jumu'a k'arfe Hudu da rabi, kamar yadda akakai sauran 'yan uwanta. 'Yan uwa da abokan arzuk'a nakusa suka rakata gidan Mijinta akaro nabiyu dake d'an Agundi G.R.A. kuzo kuga wani _Mension_ da Arch Sulaiman yazana Tasweerar Gidan dakansa. Tundaga wajen gidan abin kallone, ido nabud'e harda hanci da baki