Showing 21001 words to 24000 words out of 30805 words
*66-70*
""Nannauyan numfashi Abban su Usman ya sauke, wajen 12na dare suka bar Asibitin. Baban su Naja'atu da Abbansu Usman sun tattauna sosai da Likitocin inda suka sanar musu da tashin Usman se wani ikon Allah.
Washegarin ranar tun bayan asuba Abban suka koma Asibitin ko Maman bai yarda taje alokacinba sha'anin mata saisu. Tin kafin Likitan yagamai masa bayani ganin Usma d'in a lullu6e yatabbatar da zarginsa yazama gaskiya, wasu zafafan hawaye yaji suna bin fuskarsa, "Allah sarki Usman Ubangiji yaimaka Rahmarsa yaro mai biyayya da girmama nasama dashi. Allah yasa Mutuwa tazama Rigar hutu agareka." Addu'a sosai yai masa yashare hawayen dasuka zubomai. Duk wani ciki-cike yayi dan abashi gawar Usman d'in gida. Tun a Asibitin yaja gefe yana buga waya duk wanda yakamata yasani.
Kiran V.C in Jami'ar da suka aiko su Usman d'in Worlkshop wanda akan hanyarsu suka sami Accident. Tun awayar yafara masa Ta'aziya dan tun cikin daren sak'on mutuwar wasu daga cikin D'alibansu kuma Likitoci ya riskesu. Anan Abban yanemesu su sako Matar Usman ajirgi akata Kanon sabida cikin dake jikinta, zatai kumburi intai zaman mota tunda tafiyace ba kad'an ba. Yace "bakomai za ai hakan dayardar Allah" suka aje wayan. Kafin 8 nasafe sunda gida Mutane har sun fara zuwa dole aka maida Jana'izar 11 nasafe. Musamman sabida Naja'atu itama tai masa addu'a dafatan samun dacewa da tafiyar. Mama kuwa saida Abban yad'aureta da jijiyoyin jikinta kada tai kururuwa. Duk da haka suma tai da aka shigo da gawar Usman d'in.
"Naja'atu kuwa V.C in suna gama waya da Abban Usman tingari baigama haskeba suka nufi Staff Quaters in, tareda matarsa Yarabawane amma Musulmai ne, matar tabashi shawaran su nemi taimakon Naibours insu. Baban Benua shiya bud'e k'ofan ganin V.C dakansa yasashi rusunawa suka gaisa cikin yaren Yoroba bayani sukad'an masa yataso Maman Benua si musu taimako seda tafito yadda bazasi musu kwarwa ba V.C yasanar musu Dr Usman Mak'ocinsu dawasu likitoci da aka turasu Workshop sun sami Accident, har wasu sun rasa rayukansu. V.C yace "Gidan Usman d'in zasu rakasu" Maman Benua kuwa k'ara tasa tareda d'ora hannu akai tafara "Oh my Goodnees woo!" Dak'yar matar V.C tabata baki tai shiru. "Matar za a tura injishi, ance ciki gareta suje ahad'a mata kayanta duka za aturata kanon a Jirgi.
Naja'atu tana daka kwance tunda tai sallah takasa rintsawa tunane-tunane kawai take da sak'ar zuci, wayarta kuwa har tamutu sabida neman wayan Usman batareda tasameshi ba.
Jin bugu yasata tashi dak'yar seda tatsaya taja numfashi had'e da zumbula Hijabi kan faffad'ar rigar baccinta har k'asa, tanufi k'ofar.
"Bak'armin tausayamata sukaiba ganin idanunta duk sun zuge, tunaninsu tasan abinda yafaru "Am so sory" shine abinda sukee cemata, itadai basu guri tai suka shige ganin harda Mak'otanfa. V.C yai mata bayanin abinda yakasu batai musu musuba, suka shiga tattara mata kayayyakinta. Maman Benua da Lokaci-lokaci take share hawaye a wayance karta k'ara birkita Naja'atun, suka tattaramata duk kayansu itada matar V.C. dukda haka seda Maman Benua tahad'a mata kakkauran shayi wanda dak'yar Naja'atun ta iya sha. Sukai musu sallama.
"Dawani captain Oba V.C yahad"ata dan basu samu jirgin dazaije Kano awannan safiyarba se Abuja inda acan sukesa ran samun mezuwa Kano kafindai Ranar ta bud'e. Akasai mata ticket Kayanta duk aka shi cikin jirgin. K'arfe takwas nasafe sukai Abuja.
A canma bayan 'yar hada-hadar dasukai Allah yataimaka dakwai jirgi mai zuwa Kano daga abuja ticket aka kuma siya mata kafin 11nasafen sun isa Kano. Babansu dakansa yazo d'aukarta shida yayunta biyu da Samiha. Dalabinta take k'ok'arin tsugunawa tagaidasu Baban yai saurin dakatar da ita. Idanun Samiha taga sunyi ja sosai, bade wanda yace mata komai sukasa duk akwatunanta amotar suka tafi Baban nasu yana k'ara tausaya mata. Ganin k'atotan cikin dake jikinta duk abinda keciki yazama *Maraya* yanzu kuma taje tatarar da Mummunan labari. Da dabara yashare hawayen daya zubo mai batareda wani yaganiba.
Naja'atu kuwa ganin sunyi hanyar sharad'an tunaninta ko gida zaikaita, zuciyarta tai wani bugu ganin ciccirindon mutane tun daka farkon layin, har suka zo gidan Mama. Jitai duk wani k'wari datake dashi ya salu6e motsi ma dak'yar takeyi kanta tahau tambayar meke faruwa anan? Dukda haka takuma kumburi akan nada
Kasa fitowa tai daka motar dole Samiha da Baban suka fito da ita takunma dak'yar take, tunanin Mijinta yahauyi da Usman ne seya had'ata da jikinsa, ya tallafota yanayi yana mata sannu cikeda kulawa suje duk inda zasu. Toko ina yake daba'azo d'aukarta dashiba? Cikin gidan suka nufa, nanma ganitai mutane dayawa dangin su Usman Mata da Maza yawanci duk sun zubo mata idanu. Ahankali tafurta Mamace tarasu? Jikintane yahau rawa. Baban su kuwa tak'ofar gaba suka shigar da ita falon Abbansu Usman da mutane da dama a falon wasu daga ciki sunci kuka Yusra yayar Usman tana ganinta takuma sa kuka. Jitai wasu nafad'in "Mutuwa mai yankan k'auna kinga matarsa da tsohon ciki, jitai cikinnata yawani hautsuna har tana naman durk'ushewa.
"Agaban gawar Usman d'in aka ajeta. Kwance yake amik'e anmasa sutura nannad'e da Likafani ankuma yafa zani akai. Idanuwanta takai kan mutanen falon kowa taga yananan har Innarsu cikin jimami da taraddadi y
Suke, to bataga Mijinnataba. Hannu takai tana shafar jikin zanin da aka lullu6e gawar Usman dashi
"Kiyi Hak'uri Naja'atu *Kullu nafsin za'iqatul maut/ kowane rai seya d'and'ana zafin mutuwa*.kowana lokaci takan iya riskarmu to Allah daya fimu sanshi yakar6i abunsa.
"USMAN NE NE KO BABA? Abinda ta iya fad'i kenan dayawa agurin sunji tausayinta. Dan bakasafai zakaji ta ambaci *Usman* d'inba. Gaba d'aya iyayen suka matso kusa da ita suna banbaki da nasiha "tayi hak'uri da tawalkali wataran kowa in lokacinsa yayi seya amsa kiran Ubangijinsa. Karki tumami dan
*Annabi S.A.W yace "Basa tare damu, #Masu marin fuskokinsu, #Da masu yaga Aljihunansu, #Da masu D'aga murya suna kira irin Na Jahiliyya. Ayayinda akai Mutuwa. @bukhari da muslim ne suka rawaito.*
"Kiyi masa addu'a zaitafi gidansa nagaskiya muma wataren mune haka" Inji Maman Usman tana dafo bayan Najar.
"Allah yai masa rahama yakyautata namu zuwan" abinda ta iya furtawa kenan. Dukkansu sunaji suna gani musamman Naja'atu da jinta take kamar kara cikimma tanemeshi tarasa haka aka fita da Usman d'in akai mai Sallah suk tafi kaishi zuwa kushewa.
Semuce Allah yajik'an Muslim Umma. Ameen.!!
@Team naja'atu kuzo mujewa Naja ta'aziyya gsky
#sharar hawaye!!!
Β© *Didi_sady*πΌππ
[2/18, 10:49 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: β‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*β‘
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*71-75*
""Tunda aka fita dashi ta d'ora idanuwanta kan k'ofar, gani take kamar a mafarki. Lallai Rayuwa batada tabbas, yanzu kake Mutum yanzu zaka iya zama Gawa. Shiyasa ake so kazamto mai aikata Alkairi arayuwa kazauna da mutane lafiya yadda kobayan ranka Kyakykyawar Shaida zata rik'a binka. *Hak'ik'a duk Mutumin daya manta Allah to tabbas yana tareda Shaid'an*. Allah Yai mana muwafak'a. Ameen.
Haka tazama kamar Mutum Mutumi, tana kafe aguri d'aya kamar gunki. Motsi ma kasawa tayi bare Kukan dataga dayawan mutan gurin nayi, wani irin d'imuwa tasamu kanta aciki, bugun da zuciyarta tayi hasseda taji Motsin abunda ke cikinta, kuka takeso tayi kota samu raguwar Nauyin da K'irjinta.
Cikin kwanakin Naja'atu tazama komai sede aimata ko magana bayinta tacikaba. Abinci se anyi kamar anayi zataci shima kad'an. Tabi tarafke tayi wani bak'i se k'atotan ciki dake jikinta. Damuwace sosai tattare da ita. Agidan su Usman d'in take kwana.
D'akin Maman suke kwana itada k'anwar Maman Yaya Yusra da 'ya'yanta se autar Maman. Bacci ma sede 6arawo ya d'auketa duk tabi tad'ashe tazama wata iri da ita.
Daren ranar da Usman yai kwana uku darasuwa, Naja tana kwance dare yatsala tunanin rayuwar ta take harta gangaro kan zamantakewarsu da Usman cikin Aminci, Yarda, K'auna, Kulawa da Soyayyar junansu. Lokaci d'aya Allah yad'aukeshi daga cikinsu badan baya sanshiba, tatuno yadda yake san cikin jikinta tunkafin tahaifo shi irin burin daya d'ora akan abin dayake cikinnata. Kuka tasaka mai tsuma zuciyar mai sauraro, tin tanayi a 6oye har shashshek'arta tafito fili, Yaya Yusra dabata jima da komawa bacci ba, taji alamun kukanta tashitai tareda kunna fitilar wayarta tahaska kan gadon , jijjigar dataga jikin Naja'atun nayine yatabbatar mata da ita keyin kukan, gadon tanufa itama kamar jira take tasa nata kukan har Mama tashigo d'akin ganin suna kuka zuciyarta tak'ara tsinkewa, bata hanasu kukanba musamman Naja'atu dasukeso tayi kota samu ragin damuwar datake ciki.
Batasan sanda itama hawaye yakecemata ba har wani nabin wani. Maman tai dauriya tai shiru Yaya Yusran ma, ita kuwa Naja'atu seda tai mai isarta Mama tatasheta tareda jingina ta ajikin pillow Ruwa tabata tasha sannan suka hau lallashi da nasiha tareda bata Misalai iri-iri na Rayuwa itadai jinsu kawai take.
Cikin kwana bakwai darasuwar, sunsha bak'i daga 6angare daban-daban dayawa kuma sun mata ta'aziyya. Har 'yan gidansu dukda irin zaman doya da manjan dasuke. Zuwa lokacin ta kuma rama ba kad'an ba. Zagayayyar fuskarta tayi fayau da ita. Danna Inna kullum saitayi mata tofi cikin zam-zam tanasha, Addu'oi dadama take mata banda wanda tabata takeyi. Taga kuwa fa'idar hakan dan damuwar datake ciki taragu sosai. Tafauwalawa Ubangiji duk lamuran rayuwarta shiyasan miyake nufi dayai mata haka.
Bata kuma rikicewa ba seda aka kawo kayan Usman ranar dayacika kwana takwas darasuwa, taga abubuwansa dayawa komai yananan shid'in ne babu yatafi inda ba'a dawowa. Aranarma tasha kuka wanda har zazza6i yasaukar mata.
Kwananta goma gidansu Usman d'in. Alh Abdul-Mu'iz mahaifin su Naja'atu dakansa yanemi takoma gida dukda anriga anzama d'aya nanma gidane. Ganin irin damuwar dake tattare da ita, bayan hakama komai sai anmata. Hakan yasa sukace "zasu tafi da ita gida. Mama kuwa sotai abarta agurinsu har ta haihu. Kayanta duka aka kaimata gida tasha kuka harsu 'yan gidanma haka tatafi tana ganin kamar rabuwa sukai. Itada zuwa kuma se ikon Rabba. Danma zuriyar data shiga tsakaninsu in Allah yaraya abinda zata haifa.
Har sukaje gida bata k'ara cewa k'alaba, dasukaje gidan nema bayan anfito da ita daga motar wasu daga cikin 'yan Mazan gidan dasuka tarar a harabar gidan suka k'ara yimata ta'aziyya. Da hawaye tashiga gida. D'akin Innar aka gyara mata bayan gadon dake d'akin, k'atuwar katifa baban yasaimata aka samata daka gefe daduk sauran kayanta aka shirya mata, kwanciya tai tanata maida numfashi. Tafad'a duniyar tunani har bacci yai awon gaba da ita.
Zamanta agidan tun bayan dawowarta bayabo ba fallasa. Duk abinda takeso dai-dai gwargwado tanasamu. Matan gidan sunanan da halinsu, danma bakasafai take fita ba daga zuwa Asibiti dashima tafi zuwa dadare, se d'an atisayen datake zagaya cikin gidan. Ahaka har cikinta yashiga wata tara. Haihuwa yau ko gobe. Inna duk tatanadi kayan jego da ake buk'ata gamai haihuwa tashirya. Hatta kayan mai jegon duk tashirya sejiran Allah yasauketa lafiya. Zuwa lokacin Usman yayi kwana Arba'in harda d'oriya da rasuwa.
Sosai take kewarsa, danma Inna tayi namijin k'ok'ari wajen hanata zuzzurfar tunani. Data fara zatai tabata hak'uri da nasiha harta samu tasaki jikinta. Maman Usman ma tana yawon zuwa dubata banda aiken datake mata. Haka itama Yaya Yusra tana tafe da abubuwan arzik'i duk dan ragewa Naja'atun damuwa da kewar babban rashin datayi.
Afuwa makaranta ankusa k'arka'arewa da yardar Allah.
Β© *Didi_Sady*πΌππ
[2/18, 10:50 AM] βͺ+234 703 962 5239β¬: β‘ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*β‘
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*76-80*
""Tun suna saran haihuwarta har EDD haihuwar yazo yawuce, ba abinda kedaminta se kumburin dajikinta yake gawani haske da d'ashewa daduk jikinta yayi.
Wata safiya suka nufi Asibiti da ita dan tun cikin dare take abu guda, dak'yar ta iya Sallah asuba. Dan itama Sallar azaune take tunda cikinta yatsufa. Abincin da Inna takawo mata taga bata bud'a komaiba. Tana kishingid'e sefitar da numfashi take da k'yar duk tahad'a gumi. Inna ta tallafota tareda jinginata ajikin garun d'akin "Inna Bayana ciwo" Naja tafad'a dak'yar. "Subhanallah! Badai abinne yazoba? Ina zuwa" Innar tafad'a tafita daka d'akin.
D'akin Mama Luba Uwargida tashiga tasanar mata "ko zatazo takai Naja'atun Asibiti tunda itace babba agidan. Bud'ar bakin Mama Luba secatai "Ita gaskiya bazata iya futaba dan bak'i zatai, yanzuma zaman jiransu take suna hanya." Inna mai sauk'in kai takuma cewa "dama dan kada abin yazama laifi shiyasa tazo tagaya mata dan abata girmanta na babba agidan... bata idasa rufe bakiba Mama Luba tace "kinga dan Allah banasan hayaniya kinzo kin gayamin tunda nace bazaniba a hak'ura mana". Sum-sum Innar tafita tana Addu'ar Allah yanuna mata ranarda mutan gidan zasu shirya.
To yadda sukai da Mama Luba haka sukai da d'aya matar gidan wato Goggo Safiya ita cewa tai ma "Unguwa zataje taje takaita mana su innasune wasuke nema yakai musu. Ranar Inna ranta ya6aci sosai, dandai kawai batada dangi agarin za'ana yimata haka. Samiha tanemo a waya, suka rufewasu Fawad d'akin insun dawo tunda kowa zai iyaima kansa komai dama Deedat takeji inyada yaga batanan.
A Napep suka tafi Asibitin ko Alh bata sanarwaba. To duk zaman awannin dasukai Naja'atu bata haihuba aranar. K'arshema dawowa gida sukai wajen Maghriba da aka tabbatar musu da cewa "ba haihuwar ceba. Haka Naja taita fama saida taikwana biyar ahaka.
Zuwan da Maman Usman tayine suka yanke amaidata Asibiti.kar aje asamu matsala da abincikin ko ita uwar. Da wannan shawarar sukai amfani. Motar da Maman tazo da ita suka kaira Asibitin. Basu nemi kowaba dan ita kanta Maman d'an zuwan datake gidan tafahimci irin zaman dasuke agidan. Dandai su Naja'atun da Mahaifiyarsu sun maida komai ba komaiba sam abin baya damunsu dan dole wataran zasu dena ko duniya tabasu darasi. Lallai hausawa sunyi gaskiya dasukace *"DUTSEN CIKIN RUWA..BAISAN ANA RANA BA"*. Asibitin Nagari Hospital & meternity sukaje dan tun dawowarta Kano nan take zuwa.
Tun rana da aka kaita Asibitin Naja'atu take abu guda Nak'uda sosai take likitan dake Dutyn Ranar yana kanta har dare lokacin tashinsa yai. Zuwa daren duk k'arfinta yabi yak'are Mama sai mulmula mata bayanta take. Dr nafeesa datake dutyn daren tana zuwa lavour room d'in taga yadda Naja'atun tayi cikin yabi yarairaye yai k'asa iya galabaita tayi bata haihuba. Kayan aiki aka had'a mata da taimakon wash Nurses suka shirya Naja'atun Dr Nafeesan dakanta taturata zuwa ```Theater room``` Emergency C.S zatai mata takadda tabasu sukai singning akai ciki da ita.
Inna Addu'a take ta mata. Suna zaune jugun-jugun. Jiran tsammani har goma da rabi na dare. Dr Nafeesa kuwa suna kan Naja'atu itada Dr Moses da sauran nurses. Baby boy akafara cirowa sannan aka ciro 'yan mata guda biyu d'ayardai andenneta sosai acikin. Yara kamar mahaifinsu duk aka gyaresu sede wadda aka ciro ta k'arshen ita sam batai kuka ba. Dr nafeesa da Dr Moses suka rik'o 'ya'yan tareda wata Nurses suka kawasu Inna yaran. Se farinciki Mama cema tai k'arfin halin cewa Ina Maman tasu bata gama maganarba aka turota akan gado zuwa d'akin hutu aka shigaddasu duka da ragowar kayanta.
Yaran annad'esu a showel harsu uku, Maman Usman kuka tasa sosai da ganin yaran, yau ga jinin Usman alokacin da Usman yabar duniya. Batareda hayaniya ba sukaita d'aukan yaran sud'au wannan su ajiya sud'au wancan. Maman Usman kuwa ga hawaye ga dariya duk afuskarta. Waya tasa tana tai musu Hotuna jitake kamar tamaidasu ciki sekace yanzu akafara haifa mata Jikoki. Inna har tausayinta taji.
Se wajajen shabiyu suka bar asibitin akabar Inna da Samiha. Cikin daren yaran sekuka suke mace d'aya da namijin, d'ayar ko motsawa batai ba. Zam-zam Inna tasa dabino aciki taita basu suna sha, se jijjigasu suke seda sukai bacci suma suka runtsa dukansu.
Da Asbah bayan sun idar da Sallah Dr Nafeesa tashigo dubasu dan dawuri zata wuce. Anan Inna taimata complaining kan d'ayar babyn sam batai Kukaba ko motsi bataiba. D'agata Dr tayi tak'ara jijjigata amma shiru overall d'in Jikinta tayaye duka tad'an d'ala mata, nanma shiru, tak'ara jijjigata ba alamun numfashi tace "I think so dama itace ak'arshe kuma biyun sundanneta dakuma galabaitar da mahaifiyarsu tayi yataka muhimmiyar rawa. Batazo da rai ba." Atafi da ita gida abunne. Allah yaraya sauran yabada masu albarka. "Haihuwar farine ko? Dr Nafi tafad'a tana kallan Inna tareda mik'a mata Jaririyar. Tai musu sallama tatafi idan incharge na safe sunzo zasu duba Naja'atun may b kafunnan ta farfad'o.
Karfe 7 nasafe Maman Usman tazo hae har Yaya Yusra, lokacin sukaita bugawa dangi nakusa dana nesa waya. Suna sanar musu da haihuwar. Mik'o mata Matacciyar Jaririyar Inna tayi tace "wannan bata da rai kutafi da ita gida a bunneta". Allah sarki Mama tace "Allaj yai bame shan wuyar duniya bace." Can Sharad'an suka tafi da ita aka binneta inda aka kai mahaifinsu.
Lokacin dasuka dawo har Alh dasu Sadiq a sannan Naja'atu ta farfad'o. Likitan daya karb'i dutyn safen shiyazo dubata yace "kar abari tai jijjinan motsi sosai, espcly kafarta sannan subata ruwa ko abinci mai ruwa-ruwa, banda abu mai k'ayau. Yafaffad'a musu duk irin abubuwan daza ai mata dawanda bazataiba.
Dataimakon wata Nurse tai brush, aka bata shayi sannan suka gyarata. 'Ya'yan data haifa aka ajiye mata kusada ita sunsha wanka sai k'amshin turaren jarirai suke. Tana daka kwance 'ya'yan duk agabanta, kallansu taitayi cike da k'auna, wata soyayyar yaran taji tanabin kafofi da jinin jikinta. "Kamarsu d'aya dashi ko Yaya Yusra? Naja tace da Muryatta dabata gama warwarewaba, k'wallace tabiyo bayan maganar tata, itama Yaya Yusran