Showing 6001 words to 9000 words out of 30805 words

Chapter 3 - DUTSEN CIKIN RUWA Complete Hausa Novel

12 Oct 2024

4634

k'udur cewa yai aransa yau seya bita yagano a inda take. Wurin Iyayenta direct zashi, ji yake yayi mata akaro na biyu🙀 (tofah! Wace ta farkon🤔). Kiran gaggawa ne yasameshi, daka ministry yazo jikin mahaifinsa yatashi, hankali tashe yatafi batareda yayi abinda ya k'udurtaba.


Se 5 na yamma tada gida, kantai komi seda tacika cikinta. Tai wanka.
Tana zaune a barandar k'ofar part insu. Itada Deedat da Kamal ansamai shinfid'a awaje kafin magriba. su Samiha da Salim suna Islamiyya, gani sukai anata shigo da Akwatuna, harsaida aka shigo da guda 7.

Inna Ya,haris ya kirata, bayan ya zura kansa a k'ofar d'akin, "ki fito ga kayan lefan Labiba, anfara kawo nata.
"Masha Allah" inna ta ambata. Yace maza nema suka kawo. Tafurta ai hakan yayi daidai. Allah yasa alkairy yasa ayi damu. Saura naka inji Inna. Yace ai duk tare za a had'a mu shudan, Labiba Musa Ni Dauda Nasir da Mabruka duk za ai. Kowa yasamu sauk'i. Yanzunma jiran 'yan gidansu Saurayin Mabruka. Dankomi ayi atare. Gaskia yayi kyau hakan. Suka ga kayan Labiban tareda sanya Albarka.

Alhamis da yamma basuda islamiyya, Naja'atu tana 'daki tana guga. Deedat Inna sun fita dashi.
Samiha ce zaune itada Kamal dayafara takawa yanzu kad'an kad'an, suna kallo.

Sallama sukaji ta amsa seganin wanda ya bige Kamal da mota tayi, shida Salim sunshigo tareda kannansa Iman da Ummi. Amsa Sallamar tayi tareda yi masu iso. Tinda tagansu da Salim tasan seda suka gaisa da babansu yabasu damar shigowa.
Gaisawa sukai bayan taka masu ruwa. Mukhtar se satan kallanta yake. Shidai yarinyar tana birgeshi, da alamun bazata amshi rainiba. Yanata sak'ar zuci gameda ita. Samiha kuwa sunata hirar karatu itada ummi, harsuka gane mates nesu. Kiran Naja'atu tai suka gaisa itama, tasanar masu ai Innar batanan. Sungode kuma Kamal yaji sauki sosai. Sede addu'ar Allah yakiyaye gaba.

Har sukai sallama zasu tafi, dukda Mukhtar yaso sun'dan zauna, dan yau tasake sunata hira, ya fahimci ashe *kallan kitse* yakema rogo saukin kai gareta. Amma zaik'ara gwadawa.




Aneesa_didi🍼🍉😜
[2/18, 10:47 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA*.....♡
*Na*
*Haleema g Khaleel*

2⃣1⃣-2⃣2⃣

Shirye-Shiryen Biki ake tayi dako kowane 6angare, musamman gidan Alh Abdul-mu'iz Auwal, dasuka da'de basi biki ba. Gashi kuma bikin mutum shida.
Sauran 'yan matan gidan ma dabandasu a Auren suma ba abarsu abayaba. Kaman su Samiha da Juwairyya sa 'arta se Madina da Bahijja. Itakuwa Naja'atu batada sako mace se namiji. Hakan yasa seta shiga cikin su Juwairiyya, dukda inka gansu zakai tunanin sun girmeta. Dan sunfita jiki.

Abubuwa suka had'e mata dan sunkusa fara exam in 1st semester. Test-Test kawai suke zubawa. Tana dawowa daka Makaranta ko wanka bataiba su Juwairyya k'annanta suka sata a gaba sesun tafi k'unshi da saloon dak'yar suka bari taci abinci suka tafi.

Saloon suka fara zuwa akai musu wash and set. Itakuma steaming akai mata. Dakanan suka tafi Salanta. Gidan k'unshi. Akai masu Lalle maikyau itadai Naja tafisan ja shi ka'dai akai mata. Se bayan Maghriba suka dawo gida. Gidan cike da mutane jikokin gidan da bak'i nanesa da suka fara zuwa. Dan gobe Alhamis zasu fara event in bikin da kamu . Gaggaisawa sukai tayi da 'yan uwa sannan tai 'daki dan tai wanka.
Tinaninta 'daya gobe k'arfe 2:30 Bio214 practical zai masu test, sunyi sunyi ayi dasafe yace shima bayanan dasafe. Haka suka hak'ura. Yanzu ita yazatai? Gashi indai bataje gurin kamunba abin zaizama magana.
Hakadai tana dan duba manual inta tana ha'da musu kayan sawarsu tinkan gidan yak'ara kacamewa da jama'a

Karfe 2 tashirya tatafi makarantar. Seda tagama rok'on inna in su Samiha sundawo tasasu sujirata sutafi tare. Dawuri zatai tafito.

Tsabar zumu'di ma, bakin lab in tatafi tazauna, har sauran 'yan class suka fara zuwa seda yaga suntaru sannan ya bu'de musu lab in suka shiga.
Bata ta6a tunanin test in zatai sauk'i haka ba, kafin 3:30 tagama tabayar. Seda ta bari tai Sallar la'asar. Sannan sukai sallama dasu Jidda tamusu sallama kowa yai hanyarsa.

A inda tasaba tsayawa, anan tatsaya. Ganitai anyi parking da mota agabanta. Bata dai fahimci kowayeba. Juyar da kai tayi tana tarar Napep.
"Amincin Allah agareki our future Sonologist"
Taji ya fa'di haka.
Yau kuma tanan ka 6ullo? "Ta fa'di cikin ranta" dantagane muryan. Juyowa tai cike da tsiwa. "Wai kai dan Allah maina tarema? Mikakeso dani? Duk komi nake idanka akai😙".
Tsayawa yai kawai yana binta da ido. Jiyake kamar yaha'data da kirjinshi. Koya rage abinda yakeji game da ita. " 4 the second time, Am deeply Madly in luv with you Naja'atu" gyara tsaiwa yai kamar badaka bakinshi kalaman suka fito ba.
Napep ta tsayar tashige dan ita abin nashima yafara bata tsoro.

Kaman mara zuciya kuwa shima yabi bayansu. Yaga inatake danshi tasama zai biyo mata. Ba irin samarin nanneba dazasu tsaya suna 6atama yarinya lokaci, daka baya kuma yazo bai auretaba.
Yayi aniyar komi bisa tafarkin sunnah zaibishi hatta zuwa zance sai yafara gabatar da kansa gurin iyayanta. Sannan zaikai kanta gareshi.

Lafiyar Allah suka kai gida. Tasauka tabashi kudin, shiga gida tai tindaka waje tafara ganin yara sunsha ankon bikin harma da manya anata tafiya gurin danba a gida zasiba.

Yana daka cikin motar yahangota har tashige gida. Kashe motar yai tareda gyara zama harse sunfito yaga kwalliyarta sannan yawuce.
Tab inshi ya'dauka yafara buga ```Candy crush```. Yanajin da'din game in. Cikeda nisha'di.

'Yar boko se yanzun? Ai seki sauri ki shirya anfara tafiya dan in aka tafi saidai kihau Napep. Yaya,Habiba ke fa'din haka, daka shigowarta. Gaisuwanma bata ida amsawaba tahau sababi😏. Sum-sum tawuce taname Allah ya kyauta.

Ankon material sukai iya matan gidan, kowacce tasha make-up.ni *Didi_Anees Kara zira kai kawai nake nagano Naja'atu.

Canna hangota cikin material innasu milk,colour daratsin golden, dinkin Bubu tadau light make up (kunsandai natural make-up yafi chau👄) tayana mayafinta golden akan kafa'da, se kamshi suke. Tana gyarawa Deedat takalminsa suka tafi. Yaya hafiz ne zai kaisu itada juwairyya dasu bahijja.
Futowa tai taga duk motocin compound in acike suke, waje tafito can taganosu gefan get insu, taja hannun Deedat suwuce, tirjewa yai yana nuna mata abu "shi tasiyamai" juyawa tai taga ashe mai san yoghurt ne, kiransa tai yazo yabashi.

Kamar an tsikareshi ya 'dago, ganinta yai tayi kyau ashe haka take! " *Fatabarakallahu Ahsanul qalik'een.*"da yaro yagansu da alama abu tasaimai. Suka wuce. Addu'a ya hau yi "Allah ya mallakamai wannan halita".
Nidai nace ameen👏🏼.

Awurin biki Amare sunsha kyau shiga iri daya sukai, bayan bu'da taro da addu'a aka hau shagalin biki. K'anne da yayunsu su sukai rabon abinci da seveniour.
Har aka kammala taro lafiya kowa yakoma gida. Kosu Naja ba abarsu sunda gidaba seda aka maida kowa sannan suma suka tafi.

Washe gari juma'a bayan sallar juma'a dubban jama'a suka shaida 'daurin Auren 'ya'ya 6 na Alh Abdul-mu'iz, a masallacin Jumu'a na Shaik J. Dayake Alh mutum ne na mutane. Sunga mutane kuwa.

Yau ba abinda zasi se dinner da angon Labiba Farouk suka shirya, a Xahra event, dayake 'dan unguwarsu ne a bayan gidansu yake. Mahaifinsa abokanaine da babansu. Har kuma zumincin yak'ara karfafuwa Silar auren 'Ya'yannasu.

Bayan sallar Isha kuwa motoci suka cika layin, dagani kasan bikin manyane.
'Yan mata mata kawai aka gayyata se yayunsu wasu daka ciki.
Su Samiha 'yan mata se shiiri suke, ya Najah yanxun kekuwa bazakiba? Juwairiyya tace. Hmm barni kawai Juwai. Nagaji kuma kinsan exam ce a gabana.
Amma bari nashirya muje shikinan?
Yauwa yayarmu suka tafa.
Zaman jiranta sukai dukkowa suntafi. Sukai kwalliyarsu mai 'kayatarwa.

Se gurun 8:30 suka isa. Ganisukai maza dayawa, hakan yasa duk sukai rufaffan yafe.
Dukda haka saida wani yakulasu. Juwairiyya yake tabi. Sukai gaba suka barsu.
Samiha kamar ankirata ta 'dago caraf idanta yashiga nashi.

Mukhtar kuwa yasakarmata k'ayataccen murmushi, tasowa yai yanufosu, dukda a 'dan tsorace Samiha take. Yitai kamar bataganshiba.
Salamu alaikum yayanmu barka da dare, yataro? Naja'atu tai mamaki miyakashi nan. "Abokin angone ni" yace shiyasa kuka ganni a anan. Anata shan shagali ko k'anwata?
Hmm kawai tace suka gaisa yatafi.

Haka aka gama shagalin bikin aka kai amare gidajensu. Sukuma angwayen duk kusada gida zasu zauna. Sedai muce Allah yabada zaman lafiya.


*Bayan sati biyu*

Da taimakon Allah da jajircewa ta kammala exams inta. Suka sami hutu. Hakan yabata damar tafiya Gusau dan zaga dangin Innarsu.


Usman yanzu gaba 'daya kak'i aure sabida wani dalili naka na daban! Mahaifinsa Alh M Bello yafa'da yana daka kwance.
Abba ba haka neba. "Sonake natsaya da k'afata" ba irin yadda akai a bayaba. In sha Allah Abba "dana samu aiki" dukda mu aikin ba wuya yakeba. Da akwai abinda nake jira.
Kaidai ba yaro bane daza ana lalla6inka akan kai Aure. Wani abunba saida Auren ake samunsa. Kiyi hakuri Mama. Adduar dai za a cigaba da tayamu. "Wata 'dalibata ce" amma nafiso afara tura manya tukun su tambayo. Kamin nan mun sasanta..
"Au dama batama san kanayiba? Maman tace.
Ba haka bane mama. Tasan ina santa. Kawaidai nafiso manya su shiga lamarin. To Madallah! Allah yashige gaba.
Baban yace inna k'ara warwarewa zamuje Dabinai. Se asan abinyi akan lamarin.




Afuwa pls makaranta. May be
Zaku 'danji shiru. Inkomi yai settln zancigaba.
Just need your Du'a

Didi luvs you all😘

Aneesa_didi🍼🍉😜
[2/18, 10:47 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA*.....♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

2⃣3⃣-2⃣4⃣


*A Gusau*

A Unguwar Birnin-Ruwa ta yada zango, Gidan kakanninta ta sauka wato gidansu Innarsu. Abinka da jika tasamu tarba da karamci irin na Zamfarawa. Gashi dama ta da'de bata zoba.
Hajiya Ummi mahaifiyar Innarsu, mace mai kamala da sanin yakamata. Ga rik'o da addini. Babban 'danta ya gyara mata sashinta kamar na Amarya. Kawu Haruna kenan, ace warsa lokacine gara si mata wataran sai labari.

Aka cikata da kayan motsa baki. Su Hoce, Tuwan'Bula, Amala da miyan ku'bewa,cima irin ta Zamfarawa de, taci wanda zata iya. Tamike a kujera, tinda fashin Sallah take. Se can yamma ta tashi tai wanka. Tahau taya Ummin aikace aikace. Dukda tanada kishiya, da mijinsu ya rasu aka rabamusu gado kowa aka ware mata 6angarenta. Batare da wani ya takurawa waniba acikinsu.

Tun zuwan Naja'atu kawu Sa'ud yasamu hutu domin duk wani aikace-aikacen gidan shiyakeyi. Tinda yanzu shika'dai ne daya rage bai Aure ba. Komai baya bari Ummin tasu tayi, girki shara wanke-wanke duk ya iya shike mata, iyakaci tai wanka tai zamanta, wataran ma har mai yake shafamata. Kominsa a 'dakin yake, gado ma biyu na ummin da nasa a gefe. Makaranta ce kawai ke rabasu ko wata sabgar.

Tin Ummin tana fa'da har tagaji tabarshi, tasan dayai aure dole yabar mata 'dakin.
Zuwan Naja'atu nema yasashi yakoma kwana a falon ummin, da yai wanka zai shirya ya fice.

Naja'atu ba k'aramin jin da'din zaman gidan kakar tasu taiba, seda tai kwana4 ba inda taje.
A ranar datai kwana na biyarnema tafara zaga sauran dangi.
Gidan Gwaggo Balaraba, Kishiyar Kakartasu tafara zuwa ta yini. Sukai tahira abinsu. Itama tabata tsarabarta takoma wajen Ummi.

Washegari, ne taje gidan Kawu Haruna, da Kawu Bashir k'aninsa shi 'dab gwaggo Balarabane. dayake gida 'daya suke zaune., da nufin takwana biyu ko uku.
Da zuwanta kuwa suka gaggaisa da mutan gidan Anty Khadija matar Kawu bashir ta kar6eta hannu bibbiyu. "Tace tashiga 'dakin faccalatta Anty Sumayya, " matar Kawu Bashir sugaisa.

Da shigarta 'dakin suka gaisa da Anty Sumayyan, suka 'dan ta6a hira, tatashi zata koma 'dakin Anty khadijan, matar Kawu Bashir in tace "ta tsaya su gaisa da sister inta"
Hinduwy tahau kiranta🗣 seda tai wajen sau uku ta amsa da Yep.
Tin asannan Naja'atu tasha jinin jikinta, topah ita kuma wannan wace iri ce?🙄 Take zancen zucinta ita ka'dai.

Fitowa Hinduwy n tayi cikin riga da skirt na atampa matsatstsu, irin 'dinkin nan, sewani yatsina take😣. "Kizo kugaisa da Naja"
Bak'uwa kukai kenan? Ah " 'yar yar Babansu Sadeeq ce dake kano"
Oh! Sannu pha✋🏽 ya kike? Tafa'di kaman anmata dole tanata danna waya ha'de da cin chewngum.

Lafia Naja tace, taiwa Anty khadijan sallama, abakin k'ofar falon sukai kici6us da Sadeeq babban 'dan Kawu Haruna. Ja dabaya tai tabashi hanya yawuce,
Hannu ya mik'a danyfin yakamo hannunta sugaisa, tawaske itafa dama batasan ha'duwarsu. Danshi haka yake, tinda yaje karatu ghana yadawo yafara wannan 'dabi'ar. Sauda dama ma inta ganshi bata yadda suke6e tare, dominshi kama mace ko Hugging inta bakomai ne a gurinsaba.

Ah ah Ya,Sadeeq, kamar yadda kowa yake cemasa. " ashe kana gari,?"
Murmushi yasaki yace: "mutan Kano ne yau agidan namu?
Ai nakwan biyuma tamaidamasa.
Koda yake banje gidan Umminba kwana biyu damun ha'du.

"Ya Sch yasu Inna dakowa da kowa? Inasu 'yan biyun inna?"

Alhamdulillah! Kowa lafiya, sunanan suna gaidaku. "'Yan biyuma Abekuta zasu tafi karatu"
That good haka akeso ai mutara 'yan boko dayawa a Family.

Hmm tace "Allah de yasa Albarka"

Tsuuuuuuu😚 sukaji anja tsaki! Tawuce fuuuuu kaman wata iska😂 Hinduwy ce ganin Ya,Sadeeq in data mato akansa yanzu yashigo ko inda take bai kallaba. Sabida ganin wannan Langen cousing intasa.(Naja'atu Lange😝) zatai maganinsu amma.

Naja'atu datagan haka tai saurin tak'aita hirattasu, takoma wurin Anty Sumayyan da suke kiranta da Momy.

Kwana biyun datai kowa se sanbarka yake da zuwanta. Domin komi yimasu take ba k'yashi ko bak'in ciki. Sa6anin Hinduwy dako kallan arziki bata samu daka gareta. Duk wata hanya dazatabi ta janye ya,Sadeeq tanayi, shigar matsunce, kayan dazasi bayyana tudu da kwarinta duk yi take koya biye mata da zarar yaga Naja zai rabu da ita.
Naja taita mamakin Hali irin na Hinduwy, ke gida bana ubankiba amma kinzo kin zak'e. Allah dai ya shirya


Tanayin kwana biyar tai shirin tafiya, sukai bankwana dukda sunso tak'arasa sati, ita kua taki yadda tunda hutun nata bawani yawane dashi ba. Suka cikata da kayan Arziki. Anty khadija kuwa kayan shafa da makeup tabata. Dakyar Hinduwy ta amsa sallamarta, (se kuma wani jik'on my Hindu😂😘)


*Dabinai kano*

Bayan Alh Bello galadima yasamu sauk'i, da k'warin jiki, dakansa yaje Dabinai yasamu kannansa, Baba Saminu da Baba Sani, wanda yake kulada gidan idan bayanan.
Yasanar musu gameda abinda ketafe dashi. Duk da shi Baba saminu yaso anhada Auren zuminci da Maryama 'yarsa da Usman 'din. Amma haka yaja bakinsa yaishiru. Sukai fatan Alkairy da nufin wani satin zasuje cikin garin, gidansu yarinyar da Usman in yakeso. Domin ai zancen manya.
Se muce Allah yanuna mana.
**********


Kawu Sa'ud ne ya'dakkota daka gidan Kawu Harunan. Dukda taso yakaita unguwar Gada-Biyu, gidan 'yar Autar su Innar tasu mace, Anty Husna ganin yamma tayi yace: "tabari gobe taje setai mata kwana biyu" tinda sati biyu zatai.
Da shigarsu gidan ummi tana tsakar gida tana Alwala, tai masu sannu da zuwa, itama ta aje kayanta tashiga bayi kama ruwa. Shima kawu Sa'ud yai waje

Alwala tayi tashige 'dakin Ummin suka zauna kan atada sallar subi Jam'i.

Bayan sallar isha sungama cin abinci itada ummin, Tuwan shinkafa ne da Kawu Sa'ud in yayi kamin yaje 'daukota, yabarma Ummi Miyar Shuwaka da taji Nama zuk'u-zuk'u tak'arasa.
Kwashe kayan tayi tamaida kitchen. Tadawo tazauna suna kallo, Sallama sukaji ta amsa tareda rage volume in tv.
Kawu Sa'ud ne tareda Yunus abokinsa.
Suka k'arasa shigowa falon Ummin. Har k'asa ya duk'a yagaida Ummin. Malam Yunusa ne yau a gidannamu?
Ya amsa da fara'arshi. Belura da su biyu ke zauneba. Seda yaji Sassanyar muryar Naja'atu har cikin kansa tana gaidashi. Amsawa yai a kasalance tareda kai idanunsa kanta.
Wata kyakkyawar bak'ar yarinya idanunsa suka ganemai. Tamkar Sa'ud, sedai shi yafita Haske da tsayi. duk yadda akai *Jininsu 'daya*(My Anee_luv😘).

Amma ya akai baisantaba. Kuma bai ta6a ganin taba.??


Wanga Samrayi Kodai shima yayi Gamo ne😂😍??? Wayaga Rk&Madhubala😜



*Didi_Aneesa*🍼🍉😜
Anisadidi.pun.bz
[2/18, 10:47 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA....* ♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*

2⃣5⃣-2⃣6⃣

Harararsa tai tareda sunkwi dakai, ganin irin kallon dayake mata,

'Dakin Ummi tai nufin shiga, Kawu Sa'ud yace taka musu Abinci. Bayadda ta iya haka ta'dauko flask guda biyu ha'de da plate da chokula. Taka ta ajiye seda yasata zuba musu. Sannan tashige ciki, dan duk tatakure da kallan da Yunus in yake binta dashi.

A wayewar garin, tashirya tsaf. Tazauna zaman jiran Kawu Sa'ud in zai kaita Gada-Biyu gidan Anty Husna, yaje 'dauko motan gidan dasuke ajewa.

Tsiya Ummin take tamata dantace mata ita batada Saurayi. "An daiyi Budurwar banza" kamarke ace bakida Saurayi kode korarsu kike? "Hmm habade Ummi kawai baruwana dasu".
Gashi nikuma banda miji bare najona masa ke. "Allah ma yakiyaye na auri tsoho".
Aikuwade maga irin mijin naki. "Zakuwa kiganshi zanka'de'de"
Allah de ya nuna

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login