Showing 18001 words to 21000 words out of 30805 words
zai inya k'wank'wasa sau d'aya, bata cire hijabin jilkinta tai hanyar k'ofar ko mak'otane. Salis(Baby) tagani yabita da Shu'umin kallansa, yace "Minyi waya da Usee in yanzu zai dawo yace najirashi"
Jin haka yasa tabashi hanya yawuce, kamar wani gidansa yazauna a inda suke zama tareda d'ora k'afa d'aya kan d'aya yana chanja tasoshi, sa6anin da datakai saudi Qur'an tana sauraran K'ira'a, tinda taji yace Habibintane yace yajira shi, kitchen tashiga takamai dambun naman datai jiya tahad'o da lemu, ruwa da cup a tray. Ganin ta ajemai yasakar mata murmushi tareda cewa "godiya nake Sarauniya. Itadai jitai wani banbarakwai wai sarauniya. Saurin d'auke tunanin maganar tai aranta.
"Tin wajen 11:30 yazo gidan, tanata 'yan aikace-aikacenta, dukda a d'ar-d'ar take dan basan zamansa takeba. Kitchen ta shiga ta d'ora girki Tuwan Semovita tai da Miyan Kuka tabirge kaza aciki, tuwan kuwa ta mulmuleshi a leda tasa a warmers. Kafin biyu ta kammala tashiga wanka. Ta had'o da alwala seda tashirya cikin riga da skirt na atamfa tai sallah, tana cikin d'aura dankwali taji sallamarshi, kafin tafito har Usman ya shiga toilet, tai sauri ta kammala kintsawa cikin sassauk'ar kwalliyarta tad'ora babban mayafi akan kayan.
Kafin yafito tafito mai da k'ananun kayan dazai chanja. Tak'ara tattare d'akin tai kitchen.
"Babbar leda da ake cin abinci akai ta shimfid'a tajere wermers guda biyu na Tuwo dana Miya ga roban manshanu da yajin daudawa agefe, tasamusu plates masu zirfi biyu da cokula ga roban wanke hannu agefe komi dazasu buk'ata ta ajiye. Usman Yana fitowa kuwa suka hau cin abinci. Salis(Baby) yanata zuba surutu Usman sede yai murmushi ko "Ah, A'A" danba d'abi'arshi ceba magana inyana cin abinci. Naja'atu tana gefe taji yak'ara bata haushi kaman ta bubbugeshi kawai sotake yatafi amma ba alama.
A kwanakin da suka biyo baya Salis(Baby) yamaida gidan gurin zuwansa inbezo daranaba zezo da dare tinda dasafe suna asibiti ko makaranta. Ko Usman d'in nanan kobayanan haka zaizo. Yabi yashiga jikin Usman sose komai tare suke. Abun yafara damunta tarasa yazatai da lamari irinnasa. Rufe k'ofa tafarayi, koyazo tanaji bazata bud'eba, hakan kuwa ba k'aramin rigima yasa sukayiba. Ranar tasha mamakin Usman din akan wani aboki zenemi yatada musu da hankali. Yak'ara jaddada mata indai yazo ta bud'e masa ai arzik'i nema anuna anayi dakai.
'Yar rama tafara dalilin sa damuwa datai aranta. Ganin zata jawa kanta ciwo yasata cire komai daka ranta ta fauwalawa Allah lamuranta da duk wata damuwarta. Allah yabayyana gaskiya kowa yaganta.
"Fuskarta d'auke da farin ciki tagama waya da Mamansu Usman takira Innarsu, bayan sun gaisa take sanarmata da kud'in auren su Samiha za a kawo, dan babansu yace duk aure zai musu kowacce tacigaba da karatunta a d'akin mijinta, murna kaman tarufe ido taganta agaban Innar tasa albarka suka gaggaisa da 'yan k'annanta tai hanging wayan.
Gama wayanta keda wuya Maman Benua tashigo. Ganinta yasata fad'in "kinji shiru ko mama(wani lokacin haka take kiranta tunda tagirmemata) kika biyo bayana, ainace nadena zuwa tunda bakyasan shigowa. Maman benua kuwa cikin rikitacciyar hausarta tace "baniso nazo mijinka yadawo yaganni nahanaku sakewa bare masoya irinku "to mezaimiki kai Mama made yanzude mekika kamun? Sukai tahira abunsu secan tatafi nata 6angaren.
*Six Month letter*
Seda sukai rabin shekara sukaje ganin gida, Naja semunna take dantayi kewarsu bakad'anba.
Nagaya miki ba inda zaki ga gidanki shima yana buk'atarki, kawai de ko ina kyaje ki wunan musu. Turo baki tai had'e da muryar shagwa6a tana "haba nawan dan Allah ko kwana biyu kabarni nayi yaushe rabona dasu.
Nafa gama magana nagaya miki yaja bargo yakwanta. Itama kwantawa tai tajuya baya sa6anin da dasetajita manne ajikinshi suke bacci, sabo dolenta tajingina dashi tahau baccin.
"Duk inda yadace seda sukaje, cikin sati biyu damin sati uku zasiyi, duk tabi takasa gane kanta, barin hakan tai dalilin zaman dabasayi.
Randa taje gidansu kuwa Inna duk tagano komai dake tattare da 'yartata, tak'ara cika da murjewa abin gwanin birgewa taita k'ara addu'a aranta. Naja kuwa sawatai akai mata d'anbagalaje taitaci kamar an aikota. tofi azam-zam innar taimata tasha, haka taitayi tana aikamata kansutafi.
Dazasu koma kuwa taimata tofin dayawa tahad'a mata da kayan kad'i yaji K'uli-k'uli har garin rogo seda tahad'a mata. Amota kuwa warin fetur yahau kanta taita kwara amai. Agalabaice dai suka dawo seda ya d'aura mata drip tada hayyacinta.
"Wani abu data futo dashi kuma cin k'uli-k'uli, taitace wataranma hadda lemu take had'awa. Idantasa daru dolensa yanemo ko a inane, ganin haka yasashi d'aukar jininta yaje lab in cikin sch dashi bayan yayi Spinig in Blood in yai Pragnency test, anan yaga positive result. Godiya ga Allah yafarayi, no wonder abubuwan da Queen keyi kaman shigan ciki ashe shid'inne. Lallai ubangiji yanasanshi tinda yaza6eshi cikin wan'yanda zasiga k'wansu a duniya. Yak'ara godewa Allah. Jiyai soyayyar Naja'atu da abinda ke cikinta tunkanma yaga meza a haifa tak'aru. Bejira komaiba yakoma gida.
"Tana tsaye tana gugan inner wears insa, jitai an d'agata juuu anjuyata, abinka dame jiri jitai tana neman fad'uwa, saurin tarota yai a jikinsh taruntse ido tareda k'ara k'ankameshi tanasake saka kanta ajikinsa.
"Kujera ya ajiyeta, yasamo ruwa yabata tasha.seda ta da nutsuwarta yatambayeta meke damunta?
"Itadai ba abinda kedamunta se nauyin da jikinta yayi, kuma taita kwad'ayi wasu lokatan, tace tana yamutse fuska.
"Lakuce mata hanci yai yace to k'aruwa muka samu. Babynane acikinki shike saki komi kikeji.
Aibata bari yak'arasaba ta sadda kanta jikinshi cike da kunya. Add'ua yaita mata yana gaggayamata abubuwan dazata kiyaye da irin wanda zatana ci. Sekuma zuwa asibiti yakuma dubata acan.
"Naja'atu tak'ara kyau takuma murjewa abinka dame matashin ciki.
Zaune take tanacin Teba da miyar Ogun da Maman Benua taka mata. Tanaci d'an tsamin teban namata dad'i, har wani lumshe idanu take. Daka ita sai wando three quater iya gwiya yamatseta da 'yar ficilar rigarta me fad'i cikinta d'an wata hud'u yataso sosai kaman wata takwas. Jitai kawai anbud'e k'ofan, tajuya ma k'ofan baya. Tasande bame shigowa se Usman, maidakai tai tacigaba dacin abincinta.
Hannu kawai taga ansaka a kwanon. Yadda kuwa takeji dad'in abincin kowaye bazata bashi yaciba. Janye kwanan tayi tace gaskiya Habeeb bazakaciba a shagwa6ance tai maganar. Haba Sarauniya nid'in?
Jin haka yasata dubansa dan bahaka yasaba gayamata ba.
"Caraf idanunta cikin nashi, Innalillahi kawai tahau ambata cikin razani tanemi tashi amma takasa dan suman zaune tayi...
Nima zaro idanu nai👀 nai duba garesu duka!!!
Kubiyo didi. Danjin yazata kaya!
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: {12/12, 5:00PM} Didin Anee😍
♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*56-60*
Zafafan hawaye taji suna bin kuncinta, ita tarasa wannan wace irin rayuwa ce sam mutum baida sakewa acikin gidan, kawai wani k'ato yashigo batare da ambashi iziniba, kome gidan aiyana nuna alamun dawowarshi bare wani daban.
Tana daka zaune take jada baya, ganin haka yasashi mik'ewa.
Batasan sanda tafara gaya masa maganganu marasa dad'i ba. Ta inda tashiga batanan take fita ba. Tanayi tana kuka. Fita kawai yayi batareda yace komaiba.
Ranar kasa gane kanta Usman yayi, daya matsa mata da magana tasa mai kuka, badan yasoba ya hak'ura da tambayarta yajanyota jikinsa yana shafar bayanta.
To cikin kwanakin sam yakasa fahimtarta, abincima dak'yar takeci duk tabi ta ruruce masa banda ramar datayi se tulin ciki datake fama dashi fuskarta tai fayau. Hawaye kawai taga yanabin kuncinsa ad'an firgice ta d'ago tana kallansa, yahau fad'in "Queen yakikeso nayi? Nayi nayi kifad'amin damuwarki kink'ki, ko gida kikeso namaidaki?
"Ah ah" tace tana girgiza kai "to mikikeso kowani abun namiki plss Queen kifad'amin. Banasan duk wani abu dazai takura rayuwarki akullum banida addu'ar data wuce murayu cikin aminci da k'aunar junanmu da tattali har tudun tsira. Yaita gayamata kalamai masu shigarai da kwantar da hankali.
Hawaye tashare yabata tausayi bakad'anba, tashiga yimasa bayani duk irin abubuwan da Salis(Baby) yake mata tun randa suka zo garin har k'arshen zuwansa gidan. Yadad'e yana jimamin abun idanunsa sukai jajir yana fidda wani gauran numfashi, ya hasala sosai, ganin yai haka tashiga bashi baki. Har zuciyarsa ta sauka. Abinka da mata da miji sai Allah (Maganar gaskiyace) suka shirya kansu kamar ba abinda yadamesu.
Washegari tun safe yatafi da ita asibitinsu. Inda yake kaita Antinatal. Sabida complain in datai na nauyin jikin datakeji dole aka mata Scanning. Murmushi kawai yake dayaga hoton 'ya'ya kwance acikin mahaifarta dakoni Didi bebarni nagano muku guda nawa bane. yaita tasbihi da godiya ga Allah. Ranar kaman yamaidata ciki. Ko suraba cikin yakeji. Seda yakaita gida danufin zeda dayamma sud'an zagaya. Tana shiga kayan jikinta tarage ta watsa ruwa tazauna daka ita sawata riga iya gwiwa me fad'i. Bacci tahauyi harseda yunwa tatasheta. Sallah tai tashiga kitchen.
Tana tsaka da jajjaga attaruhu yashigo gidan, kai tsaye yayo kitchen in jin k'amshi yacika gidan. Da sallamarsa yace "Queen mikike dafama unborn babys ina kuma?
" Babys kuma? Tafad'a tana kallansa.
Bagarar da zancen yayi yahau bud'e tukunya.
Karka k'one Habibi Taliya nake dafawa me daudawa, murmushi yayi baice komaiba yak'arasa mata jajjagen yayankamata albasa harta kammala suka gyara gurun. D'aki yanufa dan yawatsa ruwa. Itakuwa kafin yafito tabaje ak'asan carfet tahaucin abincin kaman tashige kwanon.
Futowa yai kawaiy gani yai tanata zuba loma duk ta had'a zufa, fanka yayo saitinta da ita yazauna tareda nad'e k'afafu, sa6anin itada ta ware k'afafu cokali yagani agefe dawani plate in. Bismillah yayi yahaucin abincin adaddafe yai spoon biyar yakur6i lemon dake gefe. Ita kuwa seda taji dam cikinta ya d'auka taja gefe, kallanta yake kawai cike da tausayi dan duk tafara kunbura tunkamin cikin yatsufa ma kenan inaga yatsufa. Dakansa yad'auke kwanunkan yamaida kitchen. Yazauna sukaita hira abunsu.
Wajajen bayan la'asar suka fita, sun d'anyi nisa damakarantar ganin tafara gajiya yasamammusu taxi. Kasuwa yakaita taga abubuwa iri-iri na al'adun yaroba da Igbo awani 6angaren kuma hausawa ne. Siyayya yamata sosai mother care haka kayan baby komai setaga ba guda yad'aukaba itadai binsa kawai take ta idanu inya d'au wani abun seya saka ajikin cikinta itadai sede tai murmushi takalleshi kawai. Kaya fall suka siya. Wani gurin hutawa yabiya da ita tasha kayan sanyi. Tayi enjoying futar sosai, ranar ko girkin dare bataiba da gajiya dakansa yamata wanka yasa mata rigar baccinta me fad'i dan yanzu sutafi sawa dan tafi sakewa cikinsu. Komi yahad'ashi inda yadace kaman zasi tafiya.
~~~~~~~~~~~~~
Akwana atashi lokaci yaita tafiya wasu daka cikin dangi sun zazzo mata. Harsu Samiha Ya Hafiz yakasu ranar kuwa tasha surutu kaman karsu rabu. Inna taita aiko mata da rubutu da magungunar gargajiya dan ance mata tafara kumburi. Har cikinta yai wata 8 kaman yanzu zata haihu dole wasu abubuwan dakansa yake mata.
Tafiyar gaggawace tataso mai badan yasoba zaitafi yabatta tunda dama yakusa maidata gida danta haihu acan. Yanemi alfarma gurinsu Maman benua da Mijinta kan suna kula masa da ita badad'ewa zaiba danma dole ne tafiyar dabazaiba.
Dararranar kaman bazai bartaba tabashi farin ciki bakad'anba, jiyake kaman sukad'ai ne masoyan da suka rage adoran duniya. Seda yamata wanka shima yayi suka hau hira yanamaijin kama kada yatafi batareda Queen intasaba. Seda ta lallasheshi sosai da kalamai masu kwantar da hankali dasa nutsuwa. Tausa yahau yimata yana lailaya bayanta har tahau bacci yai musu addua shima yakwanta.
Safiyar Alkairy!!!
Waiyo team Naja afuwa plsss. Makaranta abun se hak'uri. Allah de yak'aremu da lafiya. Nagode sosai didi tana sanku duk inda kuke.
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*
*61-65*
Safiyar juma'ar dazasi tafiyar, dawuri yatashi, shara yafarayi yagyara gidan hadda kunna turare a burner.
Ruwan tea yad'ora yahau ferara Irish, yafara suya yana 6arar plantain. Yasoyawa kansa k'wai daban dan ita tunda tasamu ciki bakasafai take cinsaba. Yana cikin wanke kayan dasuka 6aci tashigo kitchen d'in ashagwa6ance tace "kai Habibi kullum saikai ta kwashe ladan" da murmushi a fuskarshi yace "Yo ai kema kullum cikin samun lada kike, farantamin dakikema lada kike samu, ballantanama cikin dake jikinki Allah kad'ai yasan ladan da kike samu. Allah dai yarabaku lafiya. Yau ace ga 'ya'yana Jinina kuma Queen itace ta haifamin wana irin farinciki zanyi. Allah de yanuna mana lokacin darai da lafiya. "Ameen" tace takarasa gyaran kitchen d'in.
"Wanka yafarayi yataimaka mata itama tayi, suka shirya sunata soyayya abinsu. Har sukai Break-fast yakuma gyara gurin, duk saboda tausayinta dayakeji. Jiyake kamar kada yatafi ba ita.
Kaya kala uku tahad'a mai tafiyar kwana biyu zasiyi a k'aramar bus in makaranta zasu tafi awannan karan. Likitoci su biyar aka za6a zasuje workshop a jami'ar kano se driver dazai tuk'asu.
"Kamar bazasu rabuba k'arfe 9 yakaita gidan Maman Benua kada zaman kad'aici ya dameta. Haka sukai sallama tanata musu Addu'uan samun nasara da sauka lafiya, k'arfe 10 nasafe suka d'auki hanyar Kano.
Maman benua da Karamci, dukda ba Musulmai bane amma Kafiran Amanane, tun farkon zuwansu tafahimci hakan. Yanzuma cemata tai "tadena girki zatana aiko mata dashi, dandai cikinta ita kad'ai bazai gagaraba musammanma yadda tai nauyi komai dakyar takeyinsa. Ranar agidan tawuni se kusan La'asar takoma tareda Stepme 'yar Maman Benua da tatayata zama. Kallo takunna mata tashiga d'aki fes-fes dashi se k'amshi yake rigar Usmance a kan gadon ta d'auka ta rungumeta sosai ajikinta tana wasu maganganu dagaji nayabone. Sallah tai tahau had'a kayan duk daya bari kowanne a inda yadace tasakashi.
Falon tadawo suka cigaba da kallan dukda ita rabi kallo rabi tana gwada kiran wayar Usman datak'i shiga.
~~~~~~~~~~~~~
Tunda su Usman suka d'au hanya basu tsayaba se awani k'auye sukai sallar jumu'a, tafiya suka cigaba dayi. Usman yanata kiran Queen d'insa da 'yan gida amma yakasa samu. Tun suna hira jefi-jefi har kowa yai shiru, se karatu da suka kunna masubi nayi masu danna waya nayi. A Kaduna garin gwamna suka k'ara tsayawa basu wani dad'e ba suka cigaba da tafiya har suka shigo kano.
Tsautsayi daba a samasa rana/lokaci sunata sharara gudu daidai kwanar Waratu mai Tifa yafito dagudu shima yai kansu motar su Usman tai gefe se cikin ruwan dake kasan kwaltar, dukda duhun dagari yai mutane sun d'an taru sunata Salati da neman agaji abakin ruwan, motar kuwa tashige cikin ruwa sai gefanta kad'an ake gani.
"Motar wata Ma'aikata ce sukazo wucewa ganin mutane a tsaitsaye sun fara taruwa yasasu parking, dasaurinsu suk'a k'arasa bakin ruwan. Mutanen dake gurin sunyi iya bakin k'ok'arinsu suga sunfito dasu amma badama dole aka nemo fire service, suka ciro motar datacika lumtsum da ruwa. Ganin rubutun dake jikin motar suka tabbatar daga doguwar tafiya suke. A Ambulance aka d'au su Usman daba wanda yake motsi acilkinsu, motar kuma akajata da jan way. Cikin gari akai dasu General hospital ala kaisu A&E ba ai wani dogon bayaniba aka kar6esu danbasu taimakon gaggawa. Tunda sunji bayanin suwaye kuma daka inda suke.
"Mama Mahaifiyarsu Usman tunda yamata waya kafin su taso yasanar mata zaizo gida ayau Abinci iri-iri taimasa yaza6i duk wanda yakeso. Jin shiru-shiru har bayan Isha baizoba wayarsa kuma tanata kira shiru.
Naja'atu takira bayan sun gaisa take tambayarta Usman ko yakirata sun sauka? Takasa samunsa awaya. Naja'atu jitake kamar ta rusa ihu dan ita har batasan iya adadin kiran data maiba muryarta araunane tace, itama tinda yatafi wayarsa tak'i shiga, lallashinta Maman tayi sukai hangin wayar.
"Kiran wayar Samihane yasa takuma motsawa tanata tsokanarta jin Yayar tata tai shiru bakamar yadda takewa samiha ba, tasha jinin jikinta, "Lafiya Maman biyu? Samihan tace tana k'ara rik'e wayar "Alhamdulillah kawai tace suka gaisa tabawa Innar wayan jin Muryarta k'asa-k'asa Innar tad'anji ba dad'i tace "Yayar Salim ko bakida lafiya ne? Kuka tasawa Innar tagaya mata "wayan Ya Usman taketa kira bata shiga dan suntaho kanon, batasaniba kowani abun yasamesu.
Hak'uri Innar tashiga bata ko matsalar network ne tabari zuwa jimawa tasake gwadawa zata sameshi, seda taji alamum tasamu nutsuwa Innar taitamata Addu'a sukai sallama kowannensu da irin sak'ar zucin dayake.
"Ad'aya 6angaren kuma a Asibiti duk wani abu dayakamata ai musu anyi Amma mutum biyune suka farfad'o ansamo numfashinsu daka Driver sewani Dr Hashir suma ba a hayyacinsuba. Suka cigaba da duba sauran. Ganin haka yasa suka kira Vc University aka sanarmusu.
Dolensu suka kira Guadians d'in duk wanda akai tafiyar dasu. Mahaifin Usman suna tsaka dacin abinci dare wajen k'arfe Tara nadare sak'on yariskesu. Bak'aramin tashin hankali suka samu kansu acikiba dajin labarin. Abincin da basu gama ciba kenan suka tafi General Hospital sauk'in abunma agarine.
"Ward d'in da aka kaisu Usman suka nufa. Usman gashinan akwance kamar ai magana yatashi yai wani fayau dashi. Kukan da Mama tasane Alh yarik'ota bashiri sukai waje alokacin yasanarwa da 'yan gidansu Naja'atu. Adaren wasu sukazo har Inna k'annan Usman ba abin suke se kuka manyan nata Lallashinsu. Anan kuma tunanin kowa yakoma kam Naja'atu baiwar Allah idan taji yazatayi ga tsohon ciki. "Hasbunallahu wa ni'imal wakeel" shine abinda sukaji Inna tahau fad'a.
© *Aneesa_Didi*🍼🍉😜
[2/18, 10:49 AM] +234 703 962 5239: ♡ *DUTSEN CIKIN RUWA.....*♡
*Na*
*Haleema G Khaleel*