Showing 9001 words to 12000 words out of 94417 words

Chapter 4 - Garkuwa Book 2

11 Oct 2024

3619

taku zuwa jikin show glass ɗin shi.
Buɗewa tayi cup and tea spoon ta ɗauka.

Zama tayi jin cikinta na kartawa.

Tea ta haɗa mishi kana ta miƙo mishi amsa yayi tare da cewa.
"Jazakallahu khairan". Tea ɗin ya kurba ba tare da yaci komaiba.

Ita kuwa a hankali ta kifa ƙirjinta kan, table ɗin tare da rumtse idanunta.
Murya can ƙasa tace.
"Amin".
Ido ya zuba mata, har saida ya shanye rabin kofin.
Sannan ya fara cin naman.
Ido ya lumshe jin ɗanɗanon naman ya ratsa mishi jijiyoyin baki, yawunshi sun tsinke.

Yana kallonta yana ci, har saida ya cinye na plate ɗin data zuba mishi tas, kana ya shanye tea ɗin gyatsa yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah".
Miƙa wa yayi ya nufi wurin washing hand Baby, wonke hannunshi yayi kana ya kuskure bakinshi.
Zuwa lokacin har an kira sallan azahar ana gab da shiga Masallacin.

Da sauri ya fito. Ba tare da yace mata komaiba.
Ba kowa a falon, sai dai yaji motsin Ummi a kitchen.
Da alamun ta fara suya ma.

Da sauri ya fita, a can masalacin ya samu su Jalal.

Ita kuwa Aysha a hankali ta miƙa ta tattara plete da spoons ɗin da yayi amfani dasu da kofunan, ta fito falon.
Tanata haɗa zufa.

Kitchen ta shiga.
Nan ta samu Ummi da Saratu suna ta aikin suya
Larai kuma tana can tanayi musu nasun.

A hankali tace.
"Ummi kawo in karbeki jekiyi salla kinga har lokacin ya tafi".

Cikin kula Ummi tace.
"Zaki iya kuwa Aysha nafa lura baki da lfy".

A hankali tace.
"Zan iya jekiyi salla".

To tace kana ta fita ta tafi.

Ita kuwa ta amsheta.

Tana idar da salla ta dawo tace.
"Jeki kwanta ki huta".
Batayi musuba sabida tana jin masifeffen ciwon ciki jikinta har rawa yakeyi.

Wonka ta farayi wai ko zata denajin zufar.

Tana fitowa tasa wata tattausan atampa, riga da siket, kalarta orange mai kyau sai rashin yellow-yellow kaɗan a ciki.
Batayi wata kolliya ba, amman tayi kyau sosai kalar kayan yazo kusan iri ɗaya da kalan fatarta,
ɗinkin ɗan ɗagos.
Ɗaurin ɗankwali mai sauƙin tayi.
Kana ta fesa turare.
Da sauri ta konta jin cikin ya murɗa ko mayafin bata yafaba.


Tana kwanciya kiran Hibba na shiga wayarta.
Da sauri ta ɗauka tare da cewa.
"I miss you Hibba".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Nanda wata ɗaya dai zakuzo auren Ya Haroon sai kin mana wata uku muma yadda nayi muku".
Dariyar ƙarfin hali tayi tare da cewa.
"Har biyarma zanyi".

A hankali ta juyo ta kalli Ummi dake bakin ƙofa tana sallama.
"Wa alaikissalam. Ummi shigo mana".

"A a sauri nakeyi ki fito Sheykh ne yace kije".

Fuska ta kwaɓe tare da cewa.
"To".
Hibba ce tace.
"Aunty Aysha bawa Ummi wayar".
Da sauri tace.
"To Ummi ga Hibba zaku gaisa".
Murmushi Ummi tayi kana ta juyo tazo ta amshi wayar.
Sannan suka fito tare, da mayafin a hannunta.
Tana worworeshi ne ta nufi falonshi.

A falon ta sameshi, zaune a Dinning area.
Kujera ya nuna mata, a hankali ta zauna.
Shi kuwa tasowa yayi ya dawo kujerar dake kusa da ita.
Foodflaks ɗin ya buɗe, plate ɗin da ya ɗauka a show glass ɗinshi.
Yasa mata Special Arish da haɗin naman da kwai.
Da kuma na Kabejin.
Tura mata gabanta yayi tare da cewa.
"Kici".
Fuska ta ɗan yamutsa tare da cewa.
"Banajin yunwa".

Tea ya haɗa mata tare da miƙo mata yace.
"Kici ko".
Tea ɗin ta amsa sanin ruwan ɗumi ne.

Shi kuwa ido ya zuba mata dole yasa taci.
Bayan ta ɗanci ne yace.
"Meyake miki ciwo".

Kai ta girgiza alamun babu.
Hularshi ya ɗan tura ya maidashi ƙeyarshi kaɗan tare da cewa.
"Kenan ƙarya Ummi tayi cewa baki da lfy kuma tunda gari ya waye bakici komaiba".
Da sauri tace.
"A a ba ƙarya bane".
"Uhumm!". yace tare da tura mata plate ɗin dole taci, kaɗan kana tace ya isheta.

Miƙewa yayi tare da cewa.
"Meke miki ciwo?".
A hankali itama ta miƙa tare da cewa.
"Ya bari".
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"To muje kiyi min tausa bayana ciwo".

Ya ƙarashe mgnar yana kamo hannunta suka nufi bedroom.

Da goran zam-zam a hannunshi.
Bedside drower'n ya buɗe.
wasu magunguna ya fitar, ya ɓalli guda biyu a ciki ya miƙa mata.
amsa tayi,
"Sha wannan sauran na wancan wotan ne". Yace mata.
sashi a baki tayi shi kuma ya miƙo mata goran zam-zam ɗin ta sha ta haɗiye mgnin.

Gariyar jikinshi ya zare ya saƙala cikin durowa, kana ya cire rigarma ya saƙala.
Hakama dogon Wondon da hularshi.

Hannunta yaja suka hau kan gadon.
A nitse yace.
"Ɗan daddanna min bayan".
Ya kwanta a kife.
Shiru tayi sabida rawan da jikinta keyi.

Juyowa yayi ya ɗan kalleta tare da cewa.
"Umarnine fa ba shawaraba".

A hankali tace.
"Yah Sheykh cikina marata ciwofa".
Jawota jikinshi ya kontar da ita, kana ya juyata rigingine.
Hannunshi yasa kan cikinta.
A hankali ya ture rigarta sama kaɗan.
kana yayi ƙasa da siket ɗin.

A hankali yake shafa mararta-ta yanayi yana ɗan lallatse wurin da danneshi.
Shiru tayi sabida tanajin daɗin yadda yake matan.
A hankali ya ɗan manna bakinshi kan goshinta.
Kiss ya manna mata tare da cewa.
"Na sani ai baki da lfy, ɓoye min kikeyi. Sannu".
Kanta ta gyaɗa tare da lumshe ido.
Cikin sanyi tayi bacci tare dasa hannunta kan sajenshi lokacin data juyo ta konta a rigingine.

Gyara musu kwanciyar yayi.
Lokacin ɗaya sukayi baccinsu.

Ummi kuwa da Saratu cikin sauƙin suka gama aikin hajji.
Jannama sai gobe.
Bayan sun gama suyan ne, Ummi ta dama musu kunun shinkafa kyau.
tasa manyan flaks.

Sannan ta koma ɗakinta itama ta ɗan kwanta.

A can jihar Tsinako kuwa, sosai fa shirye-shirye bikin Haroon da Jannart ya kankama.
Tuni an haɗa kayan lefe a saura kaiwa kuma sai bikin yazo a kai.
Haroon ya shiga ribibi.
Yau tunda gari ya waye baiyi waya da Jabeer da Ibrahim ba, sai yakeji kamar shekara yayi baiyi mgna da suba.
Kiran Sheykh ya farayi sai kuma ya tuno, yanzu duk inda yake lokacin baccinsa ne, in kuma baiyi baccinba to yana babban uzurin da bazai barshi ya ɗaga wayar Bama.

Umaymah kuwa tunda safe tayi mgn da AYSHA data kirata tayi mata barka da salla.

Ibrahim ma ya kira Jabeer ba'a ɗagaba.
Wayar Aysha kuwa Rafi'a da sauran ƙawayensu duk sun kikkira.
Bappa ya kirata.
Hakama Junaidun da Binto budurwar ya Gaini.

Sannan ƴan uwanta ahlin Abboi duk sun kirata.
Wani Ummi ta amsa wani ta bari.


Kiran salla ne ya tadashi a bacci.
A hankali ya zare jikinshi daga nata.
Ya shiga bathroom yayi al'wala kana ya fita sukaje sukayi salla.

Ƙarfe huɗu dai-dai ya kuma dawowa.
Dasu Jalal a falon suka zauna wurin Ummi suna cin soyayyan naman.


Shi kuwa cikin ɗakin nashi ya wuce.
Har yanzu tana bacci.

Wayarshi ya ɗauka Haroon ya fara kira, sukayi hira kana ya kira Ibrahim.

Yana cikin mgna dasune yaga ta tashi da sauri.

Sauƙowa tayi tana kallon jikinta, dasa hannun ta shafa bayanta dai-dai mazaunanta.

juyowa tayi cikin tsarguwa irin ta macen da takejin alamun jikinta ya ɓaci.

Ta gefen ido ya kalleta ganin ta juya zata nufi hanyar fita.
Da yatsarshi ya nuna mata jikin sawunta, da jini ke ɗan gangarowa.
A hankali alamun yanzu ya samu tsinkowa yadda yakeso.
Dan tun lokacin data shiga yin wonkan idi taga zubowanshi kaɗan sai kuma yanzu.

Ganin ta tsaya ne ya sashi kwaɓe fuskarshi tare da nuna mata hanyar bathroom nashi yana cewa.
"Kiyi sauri ki shiga kada ki samin najasa a tsarkakken ɗakina".
Hannu tasa ta tattare bakin siket ɗin kana ta nufi ban ɗakin.

Tana shiga ta ɗan leƙo tare da cewa.
"Ayyah Yah Sheykh dan Allah a kawo min zani mana".
Shiru yayi itama shiru tayi tana leƙenshi.
da alamu abu yake rubutawa a wayarshi.
Saida ya gama har ta buɗe baki zatayi mgna.
Sai taga ya miƙe ya fita.

Bai kula su Jamil da Affan ba ya wuce.

Yana buɗe durowar, ya shaƙi ƙamshin sabbin kayayyakin dake jere.
Wata doguwar rigar material Sky blue ya ɗauko da ɗan kwalinta, ganin akwai rasin fari a jikine yasashi ɗaukar mata farin gyale.
Har ya rufe zai juya sai kuma ya dawo.
sunkuyowa ya ɗanyi. Inda yaga jerin bra and panties ɗauka mata yayi fara.
Sai kuma yaga audugar mata a gefe.
Kwaya ɗaya ya zaro kana ya juya ya fita.

A kan gado ya ajiyesu.
Kana ya juya ya fita ya koma falo bai ce mata komaiba.

Sake leƙowan da tayine bayan tayi wonka, taga ya ajiye mata kaya kuma ya juya ya tafi.

Da sauri ta fito da towel ɗin shi a jikinta.

Sauri-sauri ta kimtsa jikinta,
ta shirya tsab, sabida taji sauƙin marar tata sosai.

Bathroom ɗin ta koma ta wonke wanda ta ciren ta shanyasu a cikin, kana ta fito.
Gaban dreesing mirror ta tsaya, turaren shi ta fesa, kana ta juya ta fito.

Hanyar fita ta nufa, shi kuwa yana tsaye ta sameshi da alamun wani wurin ya nufa, har taje bakin ƙofa yace.
"Zo".
Ɗan juyowa tayi ta kalleshi ganin kamar bashine yayi mgnarba, yasa ta juya ta nufi hanyar fita.
"Zo". Ya kuma cewa.
A hankali ta juyo, ta nufi inda yake gabanshi ta ɗan tsaya.

Kanta a sunkuye.
"Waya baki izinin samin turarena?".
Da sauri ta ɗan kalleshi tare da girgiza kai alalum a a.
Fuskar shi ya tsuke tare da cewa.
"Ƙarya nayi miki kenan".
Still kanta ta jujjuya, shi kuwa kallonta yayi sama da ƙasa ya kalli iya tsawonta da ɗan jikinta da wuraren da sukafi abki a jikinta welcome and bay-bay ɗinta.
"Baki da turaren ne?".

"Inada shi".

"To meyasa kika samin nawa".

Baki ta ɗan zumbura tare da cewa.
"Nifa bansa maka tutarenka ba".
Tana faɗin haka ta juya ta nufi hanyar fita.

Da ido ya rakata, tana fita shi kuma ya buɗe ƙofar da zata sadashi da Garden ɗin da ke bayan sashin nasa.

Washe gari kuma ranar suyan jan nama, sosai Aysha ta tsaya kan aikin, dan cikinta yabar ciwon nanda nan sukayi aikinsu suka gama.

Haka dai akayi shagulgula bikin ƙaramar salla lafiya.

Yau kwana huɗu da yin salla a wuni na biyar ne.

Affan da Aunty Juwairiyya kusan a tare suka shigo.

Wani roba mai kyau Affan ya miƙa Aysha tare da cewa.
"Aunty ƙarama gashi inji, Mami a kawo miki".
Murmushi tayi tare da amsar robar.
Soyayyan namane yayi kyau ya samu kekyawan aiki sai nason mai yakeyu.
"Kai a lallai nako gode sosai".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Wai tasan naku duk muke haɗuwa muna cinyewa, wai kowa ya bar na gidansa yazo ya cinye naku".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Tayi gsky ai haka kuke gaku bakwa gajiya da cin nama kamar ba Fulani ba.
Gwara ma Jalal shi bai fiye damuwa da namaba amman Kai Affan Jamil Imran da Sulaiman ko kuraye sai haka".
Murmushi sukayi.
Kana Aunty Juwairiyya ma ta miƙo mata robar da tazo dashi tare da cewa.
"Gashi wannan a bawa Sheykh".
Fuska ta ɗan yamutsa tare da cewa.
"A a barshi kawai".

Shiru Ummi tayi dan tasan za'ayi hakan.
Ta rasa dalilin da yasa Aysha batason kyautar komin na wurin Juwairiyya da Hajia Mama.
Su kuma basa gajiya da ba amsa takeyin ba sai sun bata.
Cikin tsareta da ido Juwairiyya tace.
"To aini ba ke na bawaba Sheykh nace a bawa".
Fuska a daƙile tace.
"Bazan bashi ba, bazai ciba.
Kije kici abunki. Baya buƙatar nakin".
Da mamaki Affan yace.
"To Aunty ƙarama meyasa".
Juyowa tayi ta ɗan kalli Affan tare da cewa.
"Ita ai tasan dalili".
Daga nan ta juya ta nufi ɗakinta.
Sosai Affan yayi mamaki.
Ita Juwairiyya kuwa, ciki takaici tace.
"Uhumm lallai ma yarinyar nan, bansan me take nufi da niba, ban san me nayi mata ba, shiyasa yanzu ni bana ko son shigowa nan".

Ta ƙareshe mgnar tana miƙewa zata fita.
A hankali Ummi tace.
"Kiyi haƙuri JUWAIRIYYA KINSAN abubuwan sai a hankali kada ki damu, kin san mutun in yanada ƴar matsala wasu lokutan ma, ba yin kanta bane".
Uhum kawai Juwairiyya tace ta fita.

Sukuwa sukaci gaba da hirarsu.
Washe gari Hajia Mama ta aiko hadimanta su kawowa Sheykh dambun nama.
Suna shiga tace, suje su rabashi an basu.

Dama Ummi kam tasan za'ayi hakan.
Sheykh dake shigowa kuwa cewa yayi.
"Ke aka bawa ne da zaki kyautar dashi".
Fuska ta ɗan yamutsa tare da cewa.
"Bazaka ci bane".

Amsar kwanon yayi a hannun Ummi tare da cewa.
"Kuje kuce ngd".

Daga nan ya nufi ɗauki shi.
Da sauri ta miƙe tabi bayanshi.

Yana shiga ya ajiye kwanon kan Bedside drower'n.
Ɗauke kwanon tayi tare da cewa.
"Dan Allah dan Annabi kada kaci, ka barshi, in dambun kakeso ai nayi maka".
Taɓe baki yayi tare da cewa.
"Nata yafi daɗi akan naki ai".
Da sauri ta kalleshi idonta na cicciko da hawaye.
Juyawa tayi ta fita da kwanon.
"In kinje kin boye kizo".
Yace mata, to tace.
Ai kuwa taje ta zubar dashi ta bawa Saratu kwanon tace ta maida mata.

A zaune ta sameshi da wata leda a gabanshi.
Nuna mata ledar yayi tare da cewa.
"Gashi ni na mance tun zuwanmu Umrah Aunty Hafsat da Umaymah suka bada sukace in baki".

Sunkuyowa tayi ta ɗauki ledar tare da cewa.
"Ngd matuƙa Allah ya biya musu buƙatunsu".

"Amin Amin". Yace.
Juyawa tayi ta fita.

Shi kuwa wayarshi ya zaro yabi bayan kiranda Haroon yaketa mishi.


Ita kuwa Aysha tana shiga ɗakinta ta buɗe ledar.
Turarukane masu kyau da ƙamshi.
Harda setin na miski da manshi da samubulunshi da turaren.
Taji daɗin su sosai.
Dan dama yanzu take shirin tayi wonkan tsarki.
zata ci gaba da salla daga la'asar.

Wonkanma ta shiga, ta fitowa tasa ɗaya daga cikin dogayen rigunan da suka turo mata.

Yau kwana goma da yin salla ya kama saura kwana sha biyar auren Haroon da Jannart ƙanwar Juwairiyya.
Tako ina shirye-shiryen biki ya kankama.
Washe gari kuwa su Aunty Hafsat da ahlinta duk suka zo.

Kai tsaye masarauta Leddi julɓe suka nufa.
Daɗi a wurin Sitti babu bayani.
Ga ƴaƴanta ga jikokinta, dan Umaymah ma ta kasa jira su iso wurinta randa sukazo da safe suka iso ita kuma da yamma ta iso.
Farin cikin Sitti da Jadda basa faɗuwa.
sai dai duk sanda sukayi irin wannan haɗuwar, yana tono musu tabo da damuwarsu da tashin hankali su.

Hibba ce ta kira, Aysha, take sanar mata.
Su Aunty Hafsat sun iso. Yanzu an fidda ankon aure da tsara duk abubuwan da zasuyi.
Kwanan Umaymah uku a can ta koma ita da Hibba da Isha yar Aunty Hafsat budurwa, kamar Hibban komai na biki Umaymah ta shiryawa Aysha shi.

Yau auren kwana bakwai bikin.
Suna zaune shida Ummi suna tsara tafiyar tasu.
Dan dole Juwairiyya zataje, amman zata tafi da Ya Jafar da yaransu da Jalal.
Su kuwa zasu tafi da Jamil da Ummin.

Sai Hajia Mama da su Ramla da Batool da har yau bata komaba.

Kiran Haroon ne ya shigo wayarsa.
Bayan sun gaisa ne yake cewa.
"Wai kai Sheykh yaushe zaku zone? Dudufa yau saura kwana bakwai ne, kuma daga gobe za'a fara hidimomin".
Da sauri yace.
"Kai haba Haroon ka nitsu mana kaja numfashi kayi mgna a hankali.
Ni dai bazan je duk sauran shagulgula kiɗe-kiɗe da raye-raye kuba bazan ce kada kayi bane, sanin Abun harda Aunty Rahma iyayen bidi'a."
Cikin hatsala Haroon yace.
"Za dai kazo kayi mana walima kam".
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"Eh walimar maza ba, shima dan Abba da kanshi ne yamin mgn da dan ta kaine ba yi zamba sabida, ba amfani da abinda ake faɗa a walimar akeyi ba".
Dariya Haroon yayi tare da cewa.
"To Ustazu Allah ya kawo ka lfy".
"Amin". yace
"To yaushe zaku zone?".
Jibi ya bashi amsa a taƙaice."

Daga nan sukaci gaba da hira.

Yau saura kwana biyu bikin kuma yaune zasu tafi.
Aunty Juwairiyya da Ya Jafar da Jalal kuwa tun jiya suka tafi.

Su kuma yau zasu tafi da dare.

Ƙarfe takwas dai-dai jirginsu ya tashi zuwa jihar Tsinako.

Tara dai-dai jirginsu ya sauƙa cikin birnin Tsinaku.

Bayan sauƙansu da wasu ƴan daƙiƙu, aka buɗe jirgin, kana aka fara fita, daki-daki.
Kasan cewar Ummi da Jamil na ta bakin ƙofar sune suka fara fita.
Sheykh Jabeer da Aysha kuwa suna can VIP Side. Hakan yasa kusan sune ƙarshen-ƙarshen fitowa.

A hankali yake taku cikin nitsuwa da kamala ta nitsastsun malamai magada annabawa.
A hankali ya saƙo ƙafarsa kan step ɗin forko na farfin jirgin.
ido ya lumshe tare da buɗesu yana son jihar Tsinako so mai tarin yawa sabida, yanada jigo shaƙiƙai masu sonshi fiye da yadda suke son kansu.
Su Umaymah, Haroon, ga ƙarinsu Aunty Hafsat, da Aunty Rahma, da ahlinsu.

Hannunshi yasa ya tattare bakin faffaɗan al'kyabbar jikinshi mai masifar kyau da taushi tare da sheƙi.

Yanayin garin da ɗan hadari, ko ina yayi lib, garin yayi duhu yayi baƙi mai kyau, gajumare masu duhu sunyisa sararin samaniya ƙawanya.
Ga wasu kyawawan ciyawi kore shar da suka malale can baya kaɗan, iska mai sanyi ke busowa tana ratsa jiki da jinin mutanen dake wurin.
A hankali take biye dashi a baya inda ya taka ƙafarsa ya cire nan take taka tata ƙafar.

Tayi shigar larabawa tayi masifar kyau, kasan cewar tasa Niƙabi baka iya ganin komai sai fararen idanunta da take ɗan jujjuyawa.

A hankali ya gama sauƙa kan, steps ɗin.
Yayinda ita kuma take step ɗin ƙarshe.
Kanta ta ɗan juyo jin dirin wani jirgi a bayansu yana tashi, yana keta gajumare.
Hannunshi yasa a hankali ya kamo nata, da sauri ta ɗan juyo jin hannunshi cikin nata.
Takowa tayi ta sauƙo kana ta fara bin takunshi sabida bai rigaya ya sake mata hannun ba.

Suna sauƙa gefen jirgin kaɗan baifi taku bakwai sukayi ba, suka isa gaban wata tsaleliyar mota fara ƙal mai sheƙin sabunta, ganin dogarai guda biyu a gefe da gefen motar sanye da jajayen kaya da surkin kore, sai tabka-tabkan rawuna, ne ya tabbatar mata su akazo ɗauka.

Shi kuwa tafin hannunshi ta haɗe da nata ya sarƙafe yatsunshi cikin nata.
Wasu dattawane suma sanye da kaya da rawuna amman su ba shigar dogarai sukayi ba, bisa alama suma, sunada ƴar saurata.

Da sauri suka nufi gabasu.
Suna isa dottawan suka ɗan saki murmushi tare da cewa.
"Barka da isa lfy Malam Jabeer".
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"Barka dai Baba Wambai".
Sai kuma ya juya wurin ɗayan tare da cewa.
"Barka da yamma Malam Liman".
Ya ƙarishe mgnar yana miƙa musu hannunshi na dama,
dan dana hagu yake riƙe da hannunta.
Cikin kulawa Malam Liman ya amshi hannunshi tare da cewa.
"Allah yayi maka al'barka ya bada ladan raya zumunci".
Amin Amin yace.
Cikin nitsuwa Aysha ta gaidasu, cike da jin daɗi suka amsa, tare da juyawa suka nufi motar, da tuni dogaran nan biyu sun buɗe musu, bayan motar.

A hankali suka nufi can yayinda Wambai kuma da Malam Liman suka kama hanyar tafiya dan motarsu na can woje.

Shi kuwa Sheykh suna isa ya ɗan ja da baya tare da sakin hannunta, ya nuna mata hanyar shiga da hannunshi.
A nitse ta rusuna kana ta shiga.
Bayan ta shiga ne, ta gyara zamanta tare da lumshe idonta sabida wani irin masifeffen ƙamshi da sanyi da sukayi mata sannu da zuwa a lokaci ɗaya.
Gyara zamanta tayi ganin yana shigowa, can gefe ta matsa,
shi kuwa yana shiga ya zauna, da sauri dogarin dake gefenshi ya kamo bakin al'kyabbar jikinshi ya samishi ita, ta ciki. Sannan ya maida ƙofar ya rufe.

A hankali motar ta fara juyawa alamar direba na ciki.

Su kuwa dogaran suka fara bin motar a hankali, har ta gama juya kanta, ta dai-dai-ta.

Sannan suka fara sauri yadda tafiyarsu zaiyi dai-dai dana motar dake tafiya a hankali.


A haka suka fito asalin farfajiyar kowa da kowa.
Nan Ummi da Jamil suke cikin motar da aka ware musu.
Kana Baba Wambai Wanda yake Aminin Abban su Jabeer ne ƙut da ƙut, shida Malam Liman suka shiga motarsu.
Suma dogaran suka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login