Showing 3001 words to 6000 words out of 94417 words

Chapter 2 - Garkuwa Book 2

11 Oct 2024

3608

JOTTAN MA'EN ne, Wuitin'en."

Kanta ya manna kan ƙahon zuciyarshi dake harbawa.
Shiru tayi tanajin yadda sautin bugawar keyi.

A hankali yace.
"Ngd da wannan bayani Shatu Bororiyar daji mai tallan nono da kiwo".

Cikin jin daɗi tace.
"Asalina kenan tushena bana ɓoyeshi.
Ina al'faharin kasancewata bafulatanar daji makiyayiya yar Fulani makiyaya kuma manoma".

Idonshi ɗaya ya lumshe tare da buɗe mata ɗayan.

Ita kuwa a hankali.
Bacci ya fara surarta sabida jin yana hura mata sassanyar iskar bakinshi.


Da sauri yace.
"Kada kiyi bacci Tashi muyi salla, sai mu wuce."

Buɗe idonta tayi a hankali, kana suka fito.
Su suka shiga wani gida dake kan hanya sukayi salla.
Su kuma maza suka shiga Masallacin.

Bayan sun idar sun fitone.
Sukaci gaba da tafiya.


Baifi awa ukuba su isaba aka kira sallan magriba.
A wani ɗan kekyawan ƙauye suka tsaya sukayi sallan magriba da isha'i.
Kana suka shiga Mota sukaci gaba da tafiya.


Kasan cewar dare yayi kuma ga garin hadari ya ɗauro
Haka yasa cikin motocin yin duhu.

A hankali ya jawota jikinshi da kyau.

Ruggume ta yayi gam a jikinshi.

Lafewar tayi a jikinshi dan ba abinda takeson yi sama da bacci.
Dan taci gaseshen naman da Affan ya saya mata.
Tayi haniƙan tasha Dudunta mai sanyi.

Tayi salla ga gajiya ga kuma.
Bacci.

Numfashin gajiya taja a hankali tare da shaƙar daddaɗan ƙamshin jikinshi.

A haka tayi baccinta kana sukaci gaba da tafiya.

Ƙarfe goma da rabi tayi musu cikin masarautar Joɗa.

A hankali aka nufi bakin part ɗin kowa.

Har bakin mashigar hawa barandar falonshi motar ta ajiyesu.
Ya sani Ummi bata nan tana sashin Gimbiya Aminatu shi yasa.

Yace.
"Alhamdulillah Ado fita jeka kawai, saida safe kazo ka ɗauke motar a nan".
Cikin girmamawa Ado yace.
"To".
Daga nan ya fita ya juya ya tafi.

Shi kuwa a hankali ya ɗan ɗagota tare da cewa.
"Aish tashi mun isa gida".
Ido ta ɗan lumshe tare da cewa.
"Yah Sheykh Na gaji".
Buɗe marfin motar yayi kana ya fito.
Tallabe da ita.
a bakin ƙofar falon ya direta, kana ya kalli inda Ummi ke ajiye mishi key ya ɗauka.
Buɗe wa yayi ya shiga, riƙe da hannunta.

Binshi kawai takeyi idonta, a lumshe alamun tana baccinta.

Shiru Side ɗin. Sai dai komai yana share yana goge ko ina fes-fes sai ƙamshi yakeyi.

Side ɗinsa ya wuce da ita.
Tana dai biye dashi kamar yar yaye.

Har cikin Bedroom ya wuce da ita.
Tana ƙoƙarin konciya kan gado, ya jawota suka nufi Bathroom.

Har cikin wurin wonkan ya shiga da ita.

Kamar daga sama kamar mafarki taji sauƙan ruwan sanyi a jikinta.
Wani irin zaro ido tayi tare da firgici tace.
"Innalillahi".
Sai kuma ta kalleshi ya karkata kai ya tsura mata kyawawan idonshi.

Cikin tsiwa tace.
"Nifa bazanyi wonkaba".

Juyawa yayi ya fita tare da cewa.
"Ashe kuwa yau a ciki zaki kwana".
Yana fita ya maids marfin ya rufe.

Da sauri tasa hannu ta rufe ruwan sanyin.
Kana ta buɗe na ɗamin.

Dole ta cire wannan kayan ta saƙalasu gefe.
Kana tayi wonka fes.
Sannan ta fito a zatonta yabar cikin bathroom ɗin bata san yana cikiba.
Ta fito ɗaure da ɗankalinta daga gugunta zuwa guiwarta ta fito da niyar ta ɗauka towel.
Tana fitowa ta ganshi tsaye a gefen wurin da al'kyabbar jikinshi yana brush.

Da sauri ta juya.
Shi kuwa bayanta yabi.
Ya kamota buɗa al'kyabbar shi yayi gaba ɗaya kana ya haɗa da ita ya rufe kirif tare da cewa.
"Ina zaki je?".

"Zan ɗauko zaninane in ɓoye jikina".

Ɗan taɓe baki yayi tare da cewa.
"Meme za'a gani a nan?."

Ya ƙareshe mgnar da ware al'kyabbar, da sauri tasa tafin hannunta ta tare ƙirjinta.
Juyawa bayanta yayi ya cire al'kyabbar tashi.
Kana ya zura mata a jikinta tare da rufeta kirib yace.
"To jeki kwanta".

Da sauri ta ware hannayenta ta sasu cikin hannun al'kyabbar kana ta haɗa bakinshi ta riƙe ta juyo ta fito.
Kan gadonshi ta hau ta shiga borgon ba tare da ta cire al'kyabbar ba.

Shi kuma wonka yayi kana ya shirya cikin kayan baccinsa.
Sannan ya fito.
Yanata zuba ƙamshi.

Ita kuwa cikin ɗan baccin data farajin yana fizgarta ta ɗan buɗe idonta a hankali ta kalleshi sai kuma ta maidasu ta lumshe.

Wutan ɗakin ya kashe kana yazo ya zauna gefen gadon.
Hannunshi yasa ya lalubo wata yar mitsitsiyar waya dake kan Bedside drower'n dake gefenshi.

Wasu yan danne-danne na 5 minute yayi.
Kana ya juyo ya hau gadon ya kwanta yana fuskantarta.

A hankali yasa hannunshin ya kamo hannunta ya jawota jikinshi.
A tare suka sauƙe numfashin,
Murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
"K....!



Uhummm wani kayan sai amale. Wata soyayyar sai malamai ma gada annabawa. Wannan shafin nakune matan malamai da ustazai Dan ku kaɗai ne kuka san irin salon Sheykh.


Littafin GARKUWA na kuɗine akwai Normal group da a wata ɗaya za'a gama Part two, ki sayi katin mtn ki kofi numbobin ki turomin ta wannan number da nakeyin whatsApp da ita 09097853276. Akwai kuma Special Group wanda a sati biyu kacal za'a gama Part two da izin Ubangiji a shiga Part 3 Shi Special Group 1k ne zakiyin min transfer'n ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turomin shaidar biyanki ta wannan number ta WhatsApp 09097853276. Dan Allah kada kiyi min VTU kada kiyi min TRANSFER ɗin katin waya bana so. In kinyi min VTU wlh ba ruwana.



Uhummm Ya Allah ka bani sa'a mu gama littafin nan kafin azumi al'farmar Annabi da al'ƙur'ani.



By
*GARKUWAR FULANI*
3/23/21, 5:06 PM - ": "Ke zo nan, zoki cire min rigata."
Da sauri tasa hannunta tattare rigar ta riƙe gam tare da cusa kanta cikin pillow'nshi tana ƙoƙarin juya baya tace.
"To ai kai ka samin ita".
Da sauri yasa hannunshin ya riƙo hannunta tare da cewa.
"To dana sa miki ita ce miki nayi rigar baccice?.
Tashi ki cire min riga kar ki yamutsa min ita".

"Uuuhmmm ni kam ka barni inyi bacci na".

"Anƙi a barki ɗin, cire min rigata sai in barki kiyi baccinki daga nan har safiyar gobe".

Cikin baccin daya buwayeta.
Ta zare hannunta cikin rigar tare da matsawa gefe, kaɗan zare ɗaya hannunma tayi, sannan ta migirna ta matsa gefen
Blanket ɗin ta jawo ta dugungune a jikinta.

Shi kuwa Sheykh zare al'kyabbar yayi ya maidata gefe.
Kana a hankali ya mirgina ya isa inda take.
A bayanta ya kwanta.

Kanshi ya ɗan ɗago ya tallabeshi da hannunshi na hagu.
Fuskarta ya ɗan leƙa ila kuwa ta lumshe idonta alamun zata maida baccin koma ta medashi.

Janye borgon yayi da ƙarfi.
Da sauri ta yunƙura ta juyo.
Hannunshi ya ɗan buɗe hakan yasa ta faɗa jikinshi.
Meda hannunshi yayi ya ruggumeta tsam a jikinshi sabida wani irin kallo da yayiwa ƙirjintan.

Lib tayi a jikinshi tana jin ɗumin jikinshi da ƙamshinsa.


Shi kuwa Sheykh gyara kwanciyarsa yayi da kyau kana ya jawo musu borgon ya rufesu dukansu kab, daga samansu har ƙasansu.

Hannunshi ya ɗaura kan cikinta tare da ɗan taɓa wa a hankali yace.
"Yunwa kikeji ko?". Ya faɗa a hankali.
Cikin baccin tace.
"A a ni a ƙoshe nake".

Uhumm yace tare da juyota da kyau ya haɗe ƙirjinta da nashi wuri ɗaya.

Lumshe idonshi yayi sabida wani abu da yakeji yana bin dukka jinin jikinshi yana zaga sasan jikinsa gaba ɗaya.

Hannunshi yasa kan ƙirjinta.
Da sauri ta maƙalƙale shi gam ta hanashi samun hanyar saka hannunshin.


Hancinsa yasa yana shaƙar ƙanshin jikinta.

A haka sukayi bacci.

Washe gari da asuba shiya fara tashi.


Bathroom ya shige yaje yayi wonka yayi al'wala.

Kasan cewar ko kiran forko ba'ayi bane, yasa ya shimfiɗa sallayarshi ya yayi nafila.
Kana ya fara karatu.
Har sanda akayi assalatu.

Nan ya miƙe yazo bakin gadon.
Ɗan sunkuyowa yayi tare da cewa
"Aish tashi kiyi salla".
tanada nauyin bacci shiyasa ko motsi batayi ba.
Hannunshi yasa ya ɗan bugi pillow'n da kanta ke kai, tare da cewa.
"Tashi kije kiyi al'wala kizo kiyi sallah Aish".

A hankali ta buɗe idonta tare da kuma maidasu ta lumshe.
Jin ya ɗan bugi ƙafarta ne yasa ta ɗan buɗe ido tare da yunƙurawa ta tashi zaune.
Sam ta mance daga ita sai ɗan kwali iya ƙugunta.
shi kuma juyawa yayi ya fita.

A hankali ta miƙe taje ta shiga Bathroom tai wonkanta kana tayi al'wala sannan ta fito.

Ganin kayanta a shanye a kan wani ɗan ƙarfen da yake shanya ƙananan kayanshi ne, yasa tasa hannu ta ɗauki zaninta.
Ta ɗauka kana ta fita.
Ɗakinta ta wuce, shiru dai babu motsin kowa a Side ɗin.

Haka nan sai taji gidan ya mata girma ita ɗaya.
Tsoro ya ɗan ɗarsu a ranta.
Gsky in babu Ummi a nan bazata iya zama ba.

A hankali cikin ɗan tsoron ta saka kaya.
kana ta fesa turare, sannan ta zura hijabi ta shimfiɗa sallayarta.
Ta kabbarta sallah.

Bayan ta idar kuwa, Azkar tayi kana ta ɗan taɓa karatun al'ƙur'ani.

Sai bakwai dai-dai ta miƙe cikin kasala da gajiya.
Ta nufi kan gadonta.

Ba tare da ta cire hijabin jikinta ba, ta kwanta.

Mintu goma sha biyu tsakani tayi bacci.


A hankali ya shigo falon.

Shiru babu kowa, sashin ya nufa.
Nanma shiru bedroom ya shiga da sauri ya kuma fitowa, juyowa yayi ya nufi falonta.

Daga nan ya wuce bedroom ɗinta.

Yana tura ƙofar kuwa ya jita a buɗe.

Wani irin ja'irim murmushi yayi tare da nufar kan gadon a hankali ya hau.

Sannan ya motso kusa da ita.
Konciya yayi.

Tare dasa hannun shi ya jawo hijabin cikin baccin tace.
"Uhum". Shiru ya kumayi sai da yaga ta kuma maida baccin.
A hankali ya cire hijabin, kana ya ɗan kalleta idonshi ya lumshe tare da lasan lip ɗinshi na ƙasa.

Wuyan rigarta irin mai faɗin nanne,
haka yasa yadda take konce a rigingine rabin ƙirjinta duk yana woje.

Cikin wani irin masifeffen yanayin buƙatar kasantuwa da itane ya sashi.
Cusa hannunshi cikin wuyar rigar a hankali.

Miƙa tayi tare da gyara konciyarta.

Wani irin numfashin yaja a hankali ya sauƙeshi jin.
taushin fatarta, da kuma laushin lutsama-lutsaman csɓɓullenta, masu girma dai-dai misali.

Hannunshi duka biyu ya cusa,
cikin rigar.
A iya zatonta na cikin bacci Sheykh ne, dan ta lura ya zama wani irin mutun yanzu.
Especially zuwansu rangadin nan, bini-bini ya cusa mata hannunshi cikin riga yayi ta kwance mata lissafin kai.

Shi kuwa Jahan yatsunshi yasa ya fara murza modonon caɓɓullenta.
Yana wani irin lumshe ido tamakar wanda zai suma.

Allah ya sani yana son waɗannan abubuwan masu masifar kyau da tsada da daɗin taɓawa.

A hankali ta buɗe idonta jin yana ɗan goga fuskarshi jikin tata fuskar tasan Yah Sheykh nada saje da gyemu wannan fuskar kuma ta jita sulum.
Wani irin zabura tayi tare da buga tsalle sai gata a ƙasa a tsakiyar ɗakin jiki na rawa cikin kaɗuwa firgici tsoro tashin hankali ta kurma ihun kiran sunan Jabeer.
"Yah Sheykh!. Wayyoooooooo Yan Sheykh".
Tanayi tana tsalle a gigice.

Kanshi ya ɗan shafs tare da cewa.
"Matar liman kiyi ihun a hankali yana can har masallaci ba jinki zaiba, kiyi a hankali kada ki yage wannan ɗan kekyawan ƙaramin bakin naki da nake jin daɗin tsotsa."
Da gudu ta juya.
Ta nufi hanyar fita.

Kai tsaye Side ɗin Yah Sheykh ta nufa tana danna mishi kira.

Baya cikin ɗakin ganin hakane yasa ta juyo da sauri.

A corridor'n shigowa falonshi sukayi kiciɓis da ƙarfi ta faɗa jikinshi tare da ruggumeshi gam-gam cikin kiɗima jiki na rawa tace.
"Yah Sheykh, Jahan ya sake zuwa har cikin ɗakinan.
Yah Sheykh har kan gadona ya hau".
Tallaɓe kanta yayi cikin mamakin tashin hankali da take cike, danne murmushin sa yayi tare da cewa.
"Me ya miki?".
Sai kuma ya janyeta a jikinshi tare da juya wa da sauri ya nufi sashinta.
Da gudu ta biyo bayanshi tana cewa.
"Yana ciki muje wlh yana ciki".
Shiru tayi ganin babushi babu dalilinshi.
Cikin tashin hankali tace.
"Wlh yazo har nan har kan gadona.
Da ina ta kiranka yace min wai Matar Liman kiyi a hankali ba jinki zaiba dan yana can masallaci".
Gaba ɗaya dariyar mugunta ke cinsa.
Sanin in yayi dariyar zata iya fahimtar wani abune yasashi zuba mata ido.
Sosai ta gigice, hannunta ya kamo suka nufo babban falon.
Suna fitowa Ummi da Saratu na shigowa.
Da sauri Saratu ta nufi kitchen.

Ummi kuwa ta nufi kansu.
Cikin kaɗuwa tace.
"Sheykh meya faru?".

Yana riƙe da hannunta yace.
"Ummi wai cewa tayi yauma Jahan yazo har cikin ɗakinta.

Ni kuma tun kwanaki da take cewa, yazoma na bincika akace min baya ƙasar nanma gaba ɗaya.

Ya fita UK kuma ance zai kai wata shida kafin ya dawo.
To waye Jahan ɗin da take gani, taketa ihu duk jama'ar masarautar Joɗa naji in ba aljanunta ba."

Cikin damuwa Ummi tace.
"To wake firgitata har hakane".

Cikin riƙo hannunta gam ganin yadda taketa fizge-fizgen tana rantsewa wlh ƙarya akeyi yana garin.
A hankali yace.
"Kawai fa Ummi al'janunta ne ke zuwa da wani sabon salo.
Kuma zanci musu mutumci, bazasu medamin gida sansanin ihu da kururuwa ba".

Cikin sanyi Ummi tace.
"Babu maijin ihunta fa Sheykh, kai dai ka ƙara bincike da kyau akan al'amarin."

Sai ta kuma kalli Aysha da har yanzu a gigice take.
"Ki nitsu ko Aysha gani gashi ga Saratu.
Babu wanda zai shigo nan zamu ganshi".
Cikin sanyi ta gyaɗa kai.

Jan hannunta yayi suka nufi falonshi.


Ummi kuwa wurin Saratu taje suka fara aikinsu.

Shi kuwa yana riƙe da hannunta ya zauna bisa kujera kana ya zaunar da ita.
System ɗinshi dake hannunshi ya ɗaura kan stoll ɗin dake gabanshi.

Tare da buɗe wa, ɗan juyowa yayi ya kalleta.
jin har yanzu jikinta rawa yakeyi, a hankali yace.
"Ke wai me ya miki".

Cikin rawan murya na tsoro tace.
"Abunda kakeyi min".
Da sauri ya juyo ya fuskanceta tare da zaro idanunshi woje cikin ɗan ɗaga sauti da haɗe fuska yace.
"Me nakeyi miki da yayi miki?".
Ya ƙarashe mgnar a fakaice.
Cikin takaici tace.
"Hannunshi yasa a rigata".

Jawota yayi jikinshi tare da miƙewa tsaye.
Cikin faɗa da zafi rai a ɓace na fatar baki yace.
"Zancen banza kenan.
Ko iskarki ce, ta isa in haɗa muhalli da itane, bare wani can Jahan da ba'a san asalin menene shiba menene addininshi ba.
Ke wacce iriyar yarinyace, da zaki tsaya har ya kalli abinda Muhammad Jabeer ya kalla har ya taɓa min kayana.
Lallai ya nemawarwa kansa masifa da yayi gigin kai hannunshi inda hannuna ya kuskura ya taɓa."
Juyawa yayi a fusace ya nufi.
Bedroom wayarshi ya ɗauka tare, da kiran Jamil wanda ma'akacine a ma'akatar su Jahan.
Cikin kausasa murya yace.
"Ka binciko min waye Jahan ina yake suwa yakewa aiki nanda rabin sa'a ina son amsoshi na".

Da sauri Jamil yace to.

Ita kuwa Aysha a inda ya tashi ta kwanta.

Bayan wani ɗan lokacin.
Jamil ya kira Hamma Jabeer ɗin ya shaida mishi cewa da tabbas Jahan baya nan.
Baya ƙasarma gaba ɗaya tsawon watanni biyu.
Kuma babu wani Jahan da ya sani."

Jin hakane yasa Sheykh, yin wani sihirtaccen murmushi da kyau.
Ko Jamil bai san komai kan Jahan ba.
Murmushi yayi tuno yadda yake cewa al'janin Aysha ke zuwa da salon iskanci.


Ranar dai a gida ya wuni, yana fakewa yaita murmushi lokaci zuwa lokaci.

Ita kuwa Aysha wurin Ummi ta koma.


Sai da Yamma Sheykh da Galadima sukaje suka samu Lamiɗo sukayi mishi dukkan bayanin tafiyar da sukayi da nasarorin da suka samu a ciki, da alamar matsalar da suka tarar, nan sukayi tattaunawa tamu sannan kan al'amarin.


Aysha kuwa sai washe gari Ummi ta mata jagora taje, Sashi Gimbiya Aminatu.

A can ta samu, Aunty Juwairiyya da Mamin Affan.

Nan suka zauna sunata hira.

Sai yamma ko wacce ta nufi Side ɗinta.


Yau sallan layya saura kwana uku.


Mutane nata shiryawa shirin ƙaramar salla.


Yau tunda safe da Sheykh ya fita bai dawoba sai dare.

Washe gari da Safe, Junaidun ya kira Aysha bayan sun sha hira yake cemata.
"Adda Shatu, jiya Dr Sheykh yazo Rugar Bani, wurinsu Arɗo Bani da Babanmu.

Sunata godiya dai sunce ince miki ki ƙara yi mishi godiya kan hidimar da yayi mana."
Cikin mamaki tace.
"Au dama shine likitan da ya maidaku asibitinshi ya kula daku?".

Da sauri yace.
"Eh amman nima ban san shine kuma mijinki ba sai.
Yau da yazo.
Ni nayi zaton wurinmu yazo sai naga su Baba da Arɗo Bani sunata murnar zuwanshi, sai na gane bafa wurinmu yazo ba".
Uhum tace tare da cewa.
"To ba matsala in sha Allah zan masa godiya".

Daga nan sukayi sallama.

Konciya tayi tana nazartan takun Yan Sheykh sai dai duk nisan da zurfin tunaninta kafin taje wuri a tunani ko bincike tuni ya wuce ta.
Abu ɗaya ta fahimta, yana bin diddigi akan abubuwa da dama shi mutumum ne bauɗaɗde mai algibata tako ina ka buga zaka sameshi.


A ranar bata ganshi ba.
Hakama washe gari.

Sai da asuba Ummi ta tasheta akan ta kai mishi.
Abun yin sahur sabida gobe za'a tashi da azumin arfa.

A tsaye ta sameshi a falo da waya a hannunshi.

Bisa alamu da Aunty Hafsat yake mgn.
Gabanshi ta ratsa ta ajiye mishi tray'n a kan stoll dake gabashin.

Ba tare da ya kalletaba ya kamo hannunta ya riƙe lokacin da zata juya ta fita.

Sai kuma yaci gaba da wayar.
"Aunty Hafsat wai har bikin ya isone?".
A can ɗaya gefen murmushi tayi tare da cewa.
"Sosai ma kuwa Sheykh saura wata ɗaya da kwanaki ne zulhajji na ƙarewa da kwana biyar na sabuwar wata za'a fara bikin".

A hankali yace.
"To kuma shine zakuzo tun bayan salla da mako ɗaya, yanzu ita Ramatu da wa zata bar mijinta ta taho wata kusan biyu".
Hannunta dake cikin nashin hannun ya ɗan ƙara matsewa.
Tare da janta jikinshi.
sai kuma ya ɗan gyara tsayuwarshi tare da cewa.
"A a Aunty Hafsat ku bari in bikin saura mako ɗaya ko biyu sai kuzo".

Da sauri tace.
"Sai dai biyun".

Uhum yace. Ita kuwa cewa tayi ina.
"Ya Ɗiyata Aysha kuma yar uwata aborso a rayuwarmu".
Murmushi yayi a hankali tare da lumshe idonsa yanaji wasu zafafan hawaye na tashin hankali na tsastsafo mishi yace.
"Gata".
Yana faɗin haka ya liƙa mata wayar a kunnenta.

Da sauri ta ɗago ta kalleshi.
Tsareta da ido yayi. Jin muryar Aunty Hafsat ne yasata ɗan murmushi tare da cewa.
"Aunty Barka da asuba".
Cikin tarin so tace.
"Barka dai Aysha yasu. Jalal da Jamil ya kewan Hibba".

Cikin murmushi tace. "Suna lfy Aunty ina kewar Hibba kam sosai ma".

"Kada ki damu mun kusan haɗuwa ai muma zamu zo ai. Ya Jazlaan yana lfy ko".
Cikin jin daɗi tace.
"Allah ya kawoku lfy Aunty".

Amin Amin tace.
Kana tace.
"Ya Jazlaan yana lfy ba wata damuwar ko".
Ɗago kanta tayi ta kalleshi,
Kwaɓe mata fuska yayi tare da mata alamun bata amsa.
Cikin sanyi tace.
"Uhum Alhamdulillah".

"Masha Allah. To sai anjima ko kada in hanaku yin sahur".

Ɗaga nan sukayi sallama.

Shi kuwa a hankali ya zauna tare da zaunar da ita gefe.
Kana yace.
"Kinyi niyar yin azumin arfanne?".
Kai ta gyaɗa mishi alamar eh.
Kauda kanshi yayi tare da cewa.
"To kin nemi izinine?".

Tura baki tai tare da cewa.
"Izinin wa?".
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"Ok haka kikace ko baki san izinin wanda zaki nema bama kenan ko?."
A hankali ta ɗan kalleshi sai kuma tace.
"Kayi haƙuri. Ina son yin azumin, ka amince inyi?.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Uhuumm ai da kinyi ba neman izinin sai da yamma in karyashi".
A hankali tace.
"Ka karya min shi kuma ɗura zakayi min ne?".
Kanshi ya kauda tare da cewa.
"Aikin wani ladan zanyi dai in Kauda naki da nawan,

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login