Showing 87001 words to 90000 words out of 94417 words
tayi taɗaure fuskar nan tamau tamiƙe tsaye tare da ɗan jan guntun tsaki,
tanufi bedroom ɗinta.
Bin bayanta sukayi da kallon mamaki,
Hajiya Mama kuwa
"Uhhuhhhhhhhmm".
Kawai tace tare da jinjina kai da ita kaɗai tasan ma'anar hakan.
Umaymah kuwa hira tasoma jan Hajiya Mama da shi wai dan kada ta sa wani abu aranta gameda abin da Shatu'n tayi mata.
A ɓangaren Hajiya Mama kuwa kawai dai tana jin tane Amma hankalinta baya gun tatafi wata duniyar nadaban tana kimtsa shirin takun da zatayiwa Shatu.
Suna dai zaune a parlour'n har wajen ƙarfe 10 kana Hajiya Mama tayi musu saida safe takoma part ɗin ta.
Washegari
Kwance Shatu take bisa gadon ta da waya kare akunne suna magana da Rafi'a,
Mikewa zaune tayi tana cewa
"Dan Allah da gaske Rafi'a".
Rafi'a dake riƙe da waya tace.
"Allah da gaske ance acikin wanna satin za'a koma makaran ta".
Cikin tsananin jin daɗi Shatu tace.
"Kai Alhamdulillah da ma na matsu a yi a koma makarantar nan dan wlh ina gajiya da zama shiru kuma nayi kewarki".
Cikin tsokana Rafi'a tace.
"Toke meyi gaminki da komawa makaranta ai ke kingama karatu, sai yi mana ronon Babynmu da kula da Abbashi.
sauran karatu kuma duk Sheykh zai koya miki kya karasashi a ɗakinsa".
Rafi'a tafad'a had'e da tsigar zulaya,
Dip Shatu takashe wayar batare da tabata amsaba ta aje wayar tamike da sauri tanufi parlour, sabida so take ta gayawa Umaymah da wuri gwarama da Allah yayi Umaymah na nan, dan tana tuna randa ta fara yi mishi mgnar kowarta makaranta ko kulata baiba.
Direct ɗakin Ummi tashiga da sallama,
A zaune tasami Umaymah bakin gado kai ta ɗago tareda amsa mata sallamar fuskarta ɗauke da murmushi, takaraso tazauna gefen,
Tana faɗin
"Barka da safiya Umaymah".
Yauwa tace tare da ɗan zuba mata ido ganin yadda tadanyi ƙasa da kai tana murza ƴan yatsunta,
Gyara Zama Umaymah tayi kana tace.
"Ya dai Aysha wani abunne kike so?".
Tayi mata tanbayar cikeda kulawa.
Ita kuwa Shatu kai ta ɗaho da sauri kamar dama jira take a tam bayeta.
Kai ta ɗan lankwasar gefe cikin sanyi tace.
"Dama batun karatu name Umaymah.
Ance yajin ai kin da a ke a makarantun jami'a an janye nan da kwana sati ɗaya za'a koma.
To kuma ina son komawa inci gaba da karatuna, to kuma naga kamar Yah Sheykh baya so.
Shine nace Ayyah dan Allah Umaymah kiyi mishi magana yabarni nakoma makatarantar Dan Allah nasan in sha Allah in kece kika masa mgn zai yarda".
Ta ƙarashe mgnar cikin rauni.
Ganin yadda tawani marairaice kamar zatayi kuka ne yasa.
Umaymah tasauke numfarfashi tasan abune mai ɗan wuya ya iya barin ta takoma makarantar.
Amman sai ta dake.
Ɗan ɗago ɗaya hannunta tayi ta
Ɗaura kan hannun Shatu wanda tarike Hannun ta dashi cikin karfafa guiwa tace.
"To babu komai zan sameshi nayi masa magana insha Allah zai barki, kada ki damu".
Cikin tsananin farin ciki da jin daɗi Shatu tarika yimata godiya kana tamiƙe takoma ɗakinta.
Umaymah kuwa tamike tanufi parlour'n shi da sallama tashiga cikin parlour'n zaune tasameshi kan kujera 1str yana riƙe da al'ƙur'ani yana kallonsa shafi-shagi alamu wani aikin duba gyara marubucin yakeyi, kuma aikine mai muhimmanci yake dan shi akanawa ya nazarceshi kasancewar wani matashinshe mahaddaci ya rubutashi to shiyasa aka miƙashi garesu malamai mahaddata su tantanceshi.
Batare da yaɗago ba ya amsa mata sallamar,
Tana kallonshi ta ƙaraso ta zauna kan ɗaya kujerar dake gefensa,
Kallonsa tayi da kyau cikin kaunarsa da santsar kulawa tace "Yanzu ya kamata kakwanta kasamu kaɗan huta tun da ba samun baccin dare kakeyiba in ka farka kayi karatun ko"
Sai yanzu yaɗan ɗago tare da shafa gefen fuskarsa kana yace
"So nake naɗan ƙarisa a bin da nake yanzu zanje naɗan kwanta dan naji idanuna sun fara ɗan yimin nauyi".
Cikin tausaya masa tace.
"Ai dole tun da kam a na kwana ba bacci".
Shiru yaɗanyi a kasan zuciyarsa kuma cewa yake
"Uhum to yazanyi tun da Ina rainon baby nane"
Shuru gurin yaɗauka bata kuma cewa komai ba shima haka.
Har saida taga ya rufe al'ƙur'ani kana ya nisa, ya ajiyeshi bisa stoll kana ya jawo system ɗinshi.
Muskutawa tayi kana tace.
"Jazlaan".
Ɗagowa yayi jin yadda takira sunan nasa da irin muryar da idan zata yimasa magana mai muhimmanci take kirashi.
"Na'am". yace yana mai maida hankali kanta ita kuma cikin nitsuwa
tace.
"Jazlaan Kanada labarin nan da kwana bakwai za a koma makarantun University ko sakamakon janye yajin ai kin da a kayi".
System in yarufe tare da gyara zaman sa yace
"Eh nasani wani abinne Umaymah?".
Numfashi taɗan sauƙe kana tace
"Kasan dai BSU nanne makaran tarsu Aysha yanzu ta sameni da batun son komawar ta makarantar yanada kyau ace itama takoman kam".
Da sauri yace.
"Umaymah takoma makaranta kuma? To cikinfa? da cikin zatake yawone".
Ya ƙarashe mgnar yana gyara zamansa.
Ita kuwa Umaymah da sauri tace.
"A'a Jazlaan baza'ayi haka ba kagabafa yarinyar nan tana cikin karatunta aka katse mata shi da aure ka, da Allah ya bata sa'anan tazo baifi da satiba aka shiga yajin aikin.
tun da yanzu tanuna son ciga bai kamata a hanataba batun rainon ciki kuma ai ba komai mata nawa ke ziryar karatu da ciki".
Baki yabuɗe zai kuma yin magana tayi saurin cewa
"Kada kace komai dan ALLAH!".
Maida bakinsa yayi yarufe dan yasan tagama da shi tun da ta haɗashi da Allah.
Kai yagyaɗa alamar gamsuwa da magar nata,cikeda jin daɗi tayita sanya masa albarka, kana tamike tafi.
Shutu na kwance a gado manne da waya a kunne tana magana da Ummey'n ta Isma na gefen ta tamike zaune tana faɗin yauwa Ummey ga Ishma mai irin muryar Junaina 'yar Aunty Rahama kanwar Maman Yah Sheykh wacce nace kuna kama da itanan Allah Ummey hatta muryarku iri ɗaya da Aunty Rahama kuna kama sosai".
Dariya Ummey dake biye da wayar tayi tace
"Ah to bani ita naji mai irin muryar Junaina ta".
Manna wa Ishma wayar tayi a kunne Ishma tace
"Inayini Ummey yagida".
Da mamaki Ummey ke sauraren muryar yarinyar sak muryarta iri ɗaya da Junaina'n Babu abinda yaraba cikin al'hinin tace. "lfy lau Alhamdulillah Ishma."
Da sauri Shatu tazare wayar a kunnenta takai nata kunnen tana faɗin "Ummey kinji muryarta ko".
Cikin tarin mamki tace
"Ai kamfa muryarsu iri ɗaya Allah mai iko kenan".
Ɗakita Umaymah tanufa dan ta sanar mata ya amince tana shiga Shatu tamiƙe tana cewa "Yauwa Umaymah ga Ummey na kugaisa". Ta ƙarashe mgnar tana
miƙa mata wayar murmushi Umaymah tayi kana ta amshi wayar takara a kunne tare dayin sallama.
"Assalamu alaikum Ummey Shatu".
Ummey dake kwance bisa wani tattausan kati, wani irin zabura tayi ta tashi zaune.
Jin wannan muryar da take gab da sa zuciyarta tasowa ta fito woje.
Da sauri tasa hannunta ta dafe ƙirjinta cikin sanyi tace.
"Wa alaikassalam, Umaymah'n Shatu".
Wani irin masifaffen faɗuwar gamane yadiyar musu dukansu a lokaci ɗaya zuƙatansu ke harbawa da masifar ƙarfi.
Cikin al'ajabi da kaɗuwa Umaymah ta kuma ƙara manna wayar a kunnen ta nan
Yayinda itama can Ummey hakan tayi.
Cikin rawan da zuciyarta keyi tace.
"Ngd matuƙa Umaymah Allah ya bar zumunci ngd da kulamin da Shatu tana yawan gaya min alkharanki gareta dake da Ummi na gode da riƙe amana".
Zuwa yanzu jikin Umaymah ya fara tsuma ta can ciki.
Cikin sanyi tace.
"Ayyah ba komai ƴar uwata ai ƴaƴanki yaranane, mun gode da samun zuriya ta gari."
Ta ƙare mgnar zuciyarts na harbawa da karfi-karfi cikin sananin kaɗuwa danjin muryar Ummey'n tamikawa Shatu wayar lokacin da suka gama gai sawar.
Cike da al'hini da kaɗuwa
ta killi shatu da kyau cikin sanyi tace.
"Aysha wacece wanan Shatu muryarta irin ta Rahma?".
Cikin murmushin Shatu tace.
"Ummeyna ne Umaymah, muryarsu kam iri ɗaya da Aunty Rahma".
Cikin mutuwar jiki ta jinjina kai tare da cewa. "Mamarki ce?".
Ta kuma jefo mata tanbayar,
Dariya Shatu tayi cikin tsananin son Ummey nata tace.
"Eh".
A ɓangaren Ummey ma haka abun yake wani irin bugawa zuciyarta yakeyi da masifar karfi jin muryar matar da suka gaisa da ita tanajin kamar tasa mai wannan muryar kamar dai ta taɓa sanin irin wannan muryar.
Jiki a saɓule Umaymah tajuya tafita ta koma ɗakin Ummi zama tayi kusa da ita da sauri Ummi tajuyo tana kallon yanayin ta da gabaɗaya yasauya da sauri tace.
"Yah dai Umaymah'n Sheykh lfy kuwa?".
Wani irin dogon numfashi mai masifar zafi ta sauƙe hawaye na zuba tace.
"Yau naji abin da ya firgitani tabbas mafarkina.
Yana gab da iya zama gaskiya na tabbata yau naji muryar 'yar'uwata wlh Ummin Jabeer naji muryar Mameyn Jazlaan...!
Assalamu alaikum, fatan muna lfy, sai kuyi haƙuri da page ɗinga banyu editing ba, zakusha fama da typing errors wata ƙil wata mgnarma ku ganta a guntule, aiyuka ne sukayi min yawa biki mukeyi.
Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 babbancinsu a yawan posting ne.
In Zaki biya ga ac no 0005388578 Jaiz Bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsApp 09097853276.
By
*GARKUWAR FULANI*
3/23/21, 5:06 PM - ": Cikin wani irin yanayi mai cike da al'ajabi da farin ciki da yanayin fatan tabbatar batun da Umaymah keyi Ummi ta miƙe zaune.
Tana mai gyara ɗaurin kallabin kanta, fuska cike da al'hini ta fuskanci Umaymah tare da cewa.
"Kai haba dai Umaymah, da gaske muryar Mameyn kikaji".
Umaymah kuwa, cikin yanayin tabbatar da mgnar da tayi fuska cike da hawaye tace.
"Tabbas lallai ilaihin wannan muryar da naji babu abinda yarabata da muryar ƴar uwata. Inada yaƙini kaso 65%100 Muryar ƴar uwata naji."
Cikin jan wani irin dogon numfashi Ummi tace.
"To me zai hana mu sanarwa su Lamiɗo".
Cikin sauri kuwa tace.
"Eh in sha Allah anjima zanje in sanar masa, muji me zasu ce".
Daga haka sukaci gaba da tattaunawa kan batun Mamey.
Bayan sallan isha'i Umaymah da Ummi ne zaune a gaban Lamiɗo da Galadima sai Abban Sheykh da Gimbiya Aminatu.
Kusan a tare suka sauƙe tagwayen ajiyan zuciya a tare, bayan Umaymah ta koro musu jawabi akan muryar Ummey da taji.
Ganin yadda sukayi ne gaba ɗayansu yasa ta gyara zamanta cikin zubda hawaye tace.
"Wlh Allah Lamiɗo Muryar ƴar uwata naji, wlh itace, Adda A'isha ce wlh koda shekaru ɗari nayi banji muryarta ba in baji zan gane ta, wlh ko cikin gigin tsufa nake in naji muryarta wlh zan gane.
Na gaya muku muryar ƴar uwata naji.
Na gaya muku dama tsawon shekaru ina mafarkin Jazlaan zai auro ba fulatanar daji hatta dukan shaɗi da akayi mishi ina mafarkansa.
Hatta fuskar Shatu na santa a mafarkina tsawon shekaru tun tana ƙarama, ina mafarkin matar Jazlaan itace zata dawo mana da yar uwata.
Ina mafarkin suna tare, in na gaya muku sai kuƙi yarda."
Shiru tayi jin muryar Sarki Jalaluddin Jadda kenan wanda Abban Sheykh ya kirasa video call, ido ta rumtse hawaye na zubawa jin yana cewa.
"Khadija mafarkin annabawa ne kaɗai ke zama gsky.
Ya za'ayi muyi ta yarda da batun mafarkanki kodai ke mafarkanki gsky ne?".
Cikin kuka tamkar ƙaramar yarinya Umaymah ta jujjuya kai murya na rawa tace.
"Jadda mafarkai ba gsky bane.
Nasan mafarkan annabawan Allah ne kaɗai gsky. Amman Jadda naga kaɗan daga cikin mafarkan da nakeyi ya tabbata, wanda haka yasa nakega Allah ya nuna min hakane cikin ikonsa da isarsa da yardarsa da ƙudurarsa, kuma nima bawai nayi imani da mafarkaina bane, illa dai muryarta da naji a yau ɗin".
Sai kuma tayi shiru ta juyo tana kallon Lamiɗo da Galadima, cikin sanyi Lamiɗo ke cewa.
"Ba komai Khadijah na fahimceki, kuma na gamsu.
To amman dole muyi taka tsantsan dan tabbatar da zatonmu.
Kinga duk wannan mafarkan da kikeyi mu kuwa malam Musa ne ya gaya mana shekaru 12 da suka wuce tun lokacin ɓacewar A'isha forki-forko ya gaya mana cewa,
tana raye kuma zata samu GARKUWAR ta, yace mana zata dawo ta dalilin matar ɗanta Muhammad Jabeer wanda kuma ba fulatanar daji bororiya zai aura, malam Musa ya gaya mana tana hannun fulanin daji. Tayi gabas tana wani yanki mai nisa a lokacin amman yace ba jimawa zata dawo kusa da yankinmu, amman bazata dawo garemu ba har sai ɗanta Muhammad yayi aure, hatta shaɗin da za'ayi shima ya sanar mana, to amman bamuyi imani da zantukanshi ba.
Mundai zubawa sarautar Allah ido sai bisa wannan ya bani shawarar in naɗa Jabeer a matsayin Garkuwan fulani ta hakane zai samu kusanci da Fulani, to wannan shawarar dai na ɗauka.
To kuma kinga bayan shekaru goma sha biyun Allah ya baiyani Shatu cikin rayuwarsa.
To wannan yasa muka ƙara ƙaiyin yin addu'a, kinga kuma shima Jabeer kullum addu'arsa kenan.
To dan haka ki kwantar da hankalinki in sha Allah zamubi komai a hankali in har dai ana tare ai dole watan-wata rana za'a gana.
Kuma ko jiya nayi waya da shi mahaifin yarinyar.
Ya bani tabbacin sun kusa dawowa ƙasar nan yace nanda wata ɗaya zasu dawo, to in sun dawo.
Kisa ɗan naki mai yawan gaddamar yakai ita Shatu zamu haɗa da Jakadiyarsu da Jamil da Jalal ɗin duk suje tare.
Ai inma itace zasu gano mana zahiri.
Kin gamsu da hakan ko ɗiyata."
Cikin tsananin farin ciki tasa hannunta ta share hawayenta tare da yin murmushi stiil hawaye na zuba tace.
"Alhamdulillah, na gamsu da haka.
Allah ya kaimu Lokacin bisa rai da lfy".
Amin Amin sukace baki ɗayansu.
Sai kuma suka juyo suna kallon Abba da yake sauƙe dogon numfashi mai cike da ƙuna a rai daga nan duk suka watse.
Alhamdulillah a ɗan sakanin ƴan ƙwanakin Sheykh yagawa Shatu komai na komawar ta makaranta.
Duk wani cuku-cukun da yakamata ayi kafin komawar nata duk yagama, ranar Monday da zaizo jibi zata fara zuwa.
Rarar kuwa kusan rabin wuni tayi suna waya da Rafi'a tana faɗa mata ranar Monday da wuri zata shigo makarantar ɗan itama Rafi'a ranar ta dawo, su Umaymah ko sai dariya suke mata wai ɗoki ya hanata zama.
Washe garin ranar Monday tun da Shutu tayi sallar asuba bata koma bacci ba kasan cewar 9 zasu shiga aji.
Bathroom tashiga ta can-ca-ɗa wanka mai rai da lfy, tana fita gaban mirror tazauna.
Mai ta shafa kana tayi simple make-up, bata wani cika fuskarta da wani kayan mulke-mulke ba amma tayi masifar ƙyau.
Mikewa tayi taje gaban wardrobe wata baƙar dogowar riga taciro mai masifar kyau da ɗaukar ido, gaban rigar an ƙawatashi da wani ƙwalliya na musamman wan da a kayishi da wasu duwatsu white and blue masu masifar sheƙi da ɗaukar ido, bra da pant taciro tasaka da dogon wondo, kana tazura doguwar rigar masha Allah ɗamas yazauna a jikinta kamar wanda dama can dominta a kayishi har ƙasa rigar yakai mata har yana ɗan ja kasa, hannun rigar ma har karshen yatsun hannunta yakai, gyalen rigar tayane kanta da shi tayi rolling ɗin shi, takalmi maiɗan tudu ta saka amman tudun ba sosai ba,
hakan yasa ƙasar rigar dake ɗan jamata a kasa yazamo yayi dai-dai baya taɓa kasa sai dai ya ɗan wuce idon sawunta,
baka ganin komai na jikinta sai dai zagayen fuskarta, tayi ras da ita kamar balarabiya.
Gaban mirror tamaso ta ɗau ƙwalbar turare taɗan fesa a jikin ta kaɗan bamai yawa ba dan idai ba wai kazo daf da ita sosai bane bazama kaji ƙamshin turaren ba.
aje ƙwalbar tayi tare da ɗago kai takalli a gogon dake manne jikin garun ɗakin 8:30Am.
Da sauri tafito parlour tana gyara rikon wayarta da jakar dake rataye a kafaɗarta, dai-dai lokacin Sheykh shima yafito cikin shigarsa ta al'farma sai baza kamshi yake, ido ya tsura mata cikeda zallar so da kauna bakaramin kyau shigar tayi Mataba, fuska yaɗan gimtse tuno fita zasuyi kuma makaranta zasuje duk ayits kallan masa ita,
ji yayi kamar yace ya janye amin cewar da yayi takoma makarantar.
Ita kuwa Shatu dinning area ta wuce tana gaida Ummi dake saman dinning area'n tana shirya zaman kululin data shirya breakfast a ciki, Ummi ta amsa tana faɗin
"Har kunfito".
sai ta kuma juya takalli Sheykh tace "
Sheykh ga breakfast ɗin kafa Yakamata kukarya kafin kutafi".
A hankali ya fara taku
ya ƙaraso sakiyar parlour'n kana gefen Shatu ya ɗan kalla kana yace
"Ummi bana da wani isashen lokaci sai dai in nadawo kawai".
Shatu kam jan kujerar dinning ɗin tayi ta zauna tana cewa
"Nidai yunwa nake ji bazan iya tafiya banci komai ba".
Murmushi yayi tare da juyawa ya nufi.
Kofar fita yana faɗin
"To shikenan bubbuga rumbun Abboi zauna ki ɗura ni dai na tafi, sai ki zauna sai gobe kizo". Ya ƙarashe mgnar cikin shauƙi.
Wanda ya fitane da nufin zai jirata a mota, dan yanada in gashi gata zaifa ruggumeta.
Ita kuwa Shatu wuf tayi ta miƙe ganin yabuɗe kofa yafita da sauri Ummi taɗau foodflaks in da breakfast ɗin da yake ciki Tamika mata tana cewa.
"Maza bishi ƙwaci a can ɗin".
Da sauri tasa hannu ta amsa dan Allah ya sani yanzu bata ita juran yunwa.
Koda tafito tuni har yashige mota bin motocin dake gaban motar sa da bayan sa tayi da ido, motoci huɗu ne biyu a baya biyu a gaba sai tasa a tsakiya Jamil nazaune agaba mazaunin driver.
Shi kusa Sheykh yana baya a hakimce.
Sauran motocin kuwa duk hadimai ne da dogarai a ciki hakan ya tabbatar mata da rakiya za'ayi musu kenan.
A sannu takaraso jikin motar, cikin hanzarin wani dogari dake tsaye a gun yayi harzarin buɗe mata marfin baya tashiga yamai da marfin ya rufe.
Ita kuwa gyara zamanta tayi tare da ssuƙe numfashin.
Juyowa gareshi tayi da ɗan sauri jin yasauƙe hannunsa kan nata ya ɗan matseshi da ɗan karfe.
Fuska ta ƙwaɓe tare
da turo baki gaba ta
langwaɓar da kanta gefen kafaɗar ta cikin narke murya tace.
"Ashhh zafi".
Cikin yin kasa da murya yace
"Wayace kisa turare in zaki fita?".
baki ta kuma turowa
gaba ta ƙwantar da kanta gefen kafaɗarsa tacusa
hannunta tabayanshi tasakanin sit da jikinshi ta daɗa
kwantowa sosai a jikin shi, da ido nuna mata Jamil
nanan fa, kallon Jamil ɗin tayi gaba
ɗaya hankalinsa nakan tuƙin da yake,
Cikin yin ƙasa da murya murya yadda Jamil bazai ma ji abinda zata faɗaba tace.
"Kaɗan naɗan fa na fesa".
Hannunsa dake kan
nata yaɗan cigaba da murzashi,
cikin muryar shogoɓa tace.
"Wash Yah Sheykh
zaka ɓallamin hannu".
ido yaɗan
lumshe tare da
buɗewa yaɗan karkato da kansa
ai-dai saitin kunnanta yace.
"Baƙyau kada kisa
ke saka turare in zaki fita kinji ko boɗɗo".
Cikin