Showing 54001 words to 57000 words out of 94417 words

Chapter 19 - Garkuwa Book 2

11 Oct 2024

3622

duk basu tsira ba.
Ina fargabar a sake baiyana wani a ahlinta.
kada tarihi ya maimaita kanshi.
Murmushi Lamiɗo yayi kana yace.
"In Sha Allah babu komai fashe al'kyairin Allah, Magauta sunyi tasu nasarar sun gama, yanzu lokacin masu gaskiya ne".
Shiru Abba yayi yana jin kalaman iyayen nashi, suna masu uzzuro mishi ciwon dake zuciyarshi.
Galadima kuwa kwalin babban ashanan da Ummi ta buɗe wanda yake cike tab da ƴaƴan ashana ya kalla tare da yin murmushi.
Wannan itace babbar shaidar mace in ta kawo budurcinta gidan mijinta a masarautar Joɗa.
Shine asa kwalin ashanan a cikashi tab da yayansa, in kuma bata kawo budurcinta ba, sai a zazzage ya'yan ashanar asa fonko haka ba ɗa ko ɗaya a ciki.
Kuma za'abi sashi-sashi na Masarautar a nuna kowa shaida to indai anga fonko babu ɗa a ciki to shaidar ta zubda budurcinta a woje.
Ci gaba da ɗaga kayayyakin Ummi tayi.
tana nuna musu.
Ɗaya daro ta jawo shi kuwa, silke ne da sirdi a ciki sai linzamin doki, kana sai takalman hawa doki kala biyu na mace dana miji,
sai kuma ɗaya kwaryan cike yake da gero sai citta da kanamfari sai kwalin sugar irin mai ƴaƴan nan.
Kai ta ɗan ɗago ta kallesu tare da cewa.
"Ga haɗin kayan da dawakai biyu mace da namiji ɗaya macen na Aysha ɗaya namijin na Sheykh.
Sai kuma kyautar zabbi ashirin na jinyar Aysha daga Masarautar Joɗa."
Cikin jin daɗi Gimbiya Aminatu tace.
"Masha Allah. Allah ya sanya al'khairi, kira yan rakiyarki su rakaki ku nunawa kowa dake Masarautar Joɗa.

To Ummi tace kana ta miƙe ta fito falon forko dasu.
Saratu da Larai ta kira sukazo suka ɗauki kayan.

Nan suka fara da sashin Hajia Mama.
Koda aka nuna mata kayan shiru tayi cikin wani irin yanayi ta gyaɗa musu kai tare da nuna musu hanyar fita ba tare da tace ko ƙalla ba.

Daga nan gidan Galadima da sauran dottawan masarautar suka nufa.
Sai da suka gama da gidajen manyan kana suka nufi, Side ɗin Gimbiya Saudatu kasancewar itace matar babban ɗan Lamiɗo.

Wani irin masifeffen kallo tabi sarƙar tamɓarin Masarautar Joɗa da akasa cikin kayan kana ta kalli Ummi tare da cewa.
"Uhummm za'a kuma kenan, wata sarƙar aka kirkiro ko dai waccar ɗin ce aka gano?
Ita dai Ummi kai ta sunkuyar.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu Baba Basiru dake gefenta ta kalla tare da cewa.
"Ashe ɗan naku waliyi ne?".
Da sauri yace.
"Waliyi kuma".
Cikin takaici tace.
"Eh to gani nai wata shida kenan da yin aure.
Ace bai kusanceta ba sai yauwa ai da gani kasan munafurcine da ƙarya, harda basu dawakai ma'aurata ko meye manufar hakan?".
Cikin nuna tsantsar tsana Baba Basiru yace.
"Wani salone hakan".
Ita dai Ummi dasu Saratu sun gaza tashi.
Cikin bala'i Baba Nasiru da yanzu ya shigo yace.
"Kai da Allah ku ɓace min da gani".
Da sauri suka ɗauki kayayyakin suka fice, sukaci gaba da nunawa.

Su kuwa Gimbiya Saudatu da muƙarraba ta suakaci da tattaunawa.


A hankali Dr Kubra ta shigo falon ta sallama a bakinta.
Su Jalal ta samu suna breakfast kamar kullun.

A falon ta zauna bayan sun gaidatane, Jamil yace.
"Ummi tayi cikin masarautar Joɗa jirata zata zo".
"Okay ba matsala". Dr Kubra ta faɗi tana gyara zamanta.

Jim kaɗan sai ga Ummi ta shigo su Saratu na biye da ita a baya da kaya niƙi-niƙi.
A ƙa'ida a hannun miji za'a danƙa kayan sai ya haɗa da nasa tukuicin ya miƙawa amaryarsa.

Cikin sakin fuska Ummi ta kalli Dr Kubra tare da cewa.
"A a lale marhabin da Dr".
Murmushi tayi kana tace.
"Yauwa Ummin Sheykh ya mai jikin".
"Alhamdulillah jiki da sauƙi.
tace.
Tana amsar kayan hannun Saratu.
Tare da cewa.
"Yauwa kawosu nan, kije ki kawowa Dr ruwa".
To Suratu tace.
Ita kuwa Ummi amsar kayan tayi kai tsaye falonshi ta nufa da sallama a bakinta, yadda ta barsu haka ta samesu.
kai tsaye bedroom ta wuce da kayan taje ta ajiye kana ta dawo ta wuce ta ɗauko sauran sannan taje ta ajiye, tana fitowa tazo kusa dasu cikin kula tace.
"Yauwa Sheykh gacan tukuicin masarautar Joɗa, sai ka da kashi gareta sanda kaso".
Kai ya jinjina ba tare daya ɗago kanba.
Ita kuwa Ummi Aysha ta kalla tare da cewa.
"Aysha tashi muje ga likita tazo".
Cikin sanyi ta buɗe idonta kana tace to.

Ita kuwa Ummi tuni tayi gaba.

Yunƙura tayi a hankali ta miƙe tana mai cewa.
"Wash Allah na".
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
"Allah'nmu dai".
murmushi yayi ganin yadda ta fara tafiya.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
"Dawo ki zauna ba inda zakije kina tafi like ƴar kaciya.
ki tsaya zan duba abina da kaina, zanyi gyaran ɓarnar da nayin".
Cikin rauni tace.
"Ni bana so ita zata dubani".

Kanshi ya gyaɗa kana yace.
"Okay".

Ummi kuwa jin shirune yasa ta dawo,
nan yace su shigo nan ɗin.


A mutunce Dr Kubra ta gaisa da Sheykh kana ta kalli Aysha cikin kula tace.
"Meke damunki?".
Ido ya ɗan zuba mata don jira yake yaji me zata ce.
Ajiyan numfashin yayi a hankali jin tace.
"Kaina ne ke min ciwo sosai, sai kuma zazzaɓi, da jiri nakeji idona na ganin duhu".
Juyowa tayi ta kalli Sheykh cikin sanyi tace.
"Dr ni ai bansan ka dawoba, da bazanzo ba. Gaka a wuri kuma me amfanin nemana.
Yanzu zamu fita da Jamil sai in turo mata mgnin da kaga ya dace".
Kai ya jinjina kana yace.
"Kin san maganin wanda baka saniba yafi daɗin karɓa a wurin wasu, rubuta mata kawai ba matsala ki bawa Jamil ɗin ya kawo."

To tace tana murmushin yadda Aysha ta turo baki.

Bayan ta fitane Ummi kuwa ta zauna.
Ferfesun zabi ta zuba a plate yana zuba tiriri mai ƙamshi kana tasa mata tea, sannan tace.
"Zoki zauna kici kinji ko!".
Tana faɗin haka ta fita.

Shi kuwa Sheykh kanshi a sunkuye idonshi kuma na kan Aysha, a fakaice yake kallon Ummi bayan Ummi ta fitane, ya ɗan ɗago kanshi kana ya ajiye warshi, kusa da ita ya matso, a hankali ya gyara zamanshi suna fuskantar juna, Fork ɗin ya ɗauka ya riƙe yana dan sa Fork ɗin yana saɓule kasusuwan daga jikin naman kanshi a sunkuye yace.
"Ki dena hararata mana, me nayi miki haka kike min mugun kallo?".
Tura ɗan bakinta tayi cikin zubda hawaye tace.
"Ni ban harareka ba".
Kanshi ya gyaɗa ba tare da ya kalleta ba, kana ya sa hannunshi ya ɗauki cup ɗin, miƙa mata yayi har kusa da bakinta.
Kana ya gyaɗa mata kai alamun ta sha.

Wani irin lumshe ido tayi hakan ya bawa hawayenta daman zubowa.
a hankali ta buɗe idonta ta zubasu kan fuskarsa,
wani irin masifeffen abu takeji cikin zuciyarta, zirin kwayar idanunshi ta zubawa ido.
Tabbas Yah Ba'ana kekyawa ne ajin forko, amman yau data nazarci fuskar Sheykh sai take ganin ko rabin kyanshi Ba'ana bai samuba.

A hankali ta buɗe lips ɗinta jin ya manna mata kofin.
Lumshe ido tayi lokacin da taji ɗumi da ɗanɗanon team ɗin, wanda yake tamkar Ummey'nta ne ta haɗashi.
Kaɗan tashe ya janye kofin, kana yasa Fork din ya soki tattausan soƙan gasashen naman.
Bakinta ya nufa sashi tare dasa hannunsa ɗaya ya riƙe hannun damanta ya fara murzawa a hankali kana cikin yin ƙasa da murya yace.
"Haa".
Ya ƙare abun da alamun ta buɗe bakin.
Haka nan taji ta kasa yi mishi musu, cikin sanyi ta buɗe bakin yasa mata tsokar,
Ido ta lumshe sabida wani irin masifeffen daɗi da taji naman yayi mata, Allah ya sani bata taɓajin gashin naman da ya mata daɗi irin na yau ba.
wani ya kuma bata, still ta amsa taci.
Kana ya kuma bata cup ɗin tea ta kurɓa, haka yayi ta bata tanaci yana bata tea kana yana murza tafin hannunta cikin nashi saida tayi gyatsa kana a hankali tace.
"Alhamdulillah".

Ganin ya kuma miƙo matane yasa ta kauda kanta tare da lumshe idanunta tace.
"Yah Sheykh na ƙoshi".

Kanshi a sunkuye yace.
"Ban yardaba".

A hankali tace.
"Allah kuwa".
Numfashi ya ɗan fesar kana yace.
"To muga cikin".
A hankali tace.
"Gashi".

Hannunshi yasa bisa cikin nata, kana a hankali yace.
"Ɗaga rigar".
Tura baki tayi cikin jin bacci tace.
"In ɗaga kuma?."
Kai ya gyaɗa mata tare da cewa.
"Na'am ki ɗaga inga in cikin ya cika, sai muje bedroom inga wurin ciwon kuma".
Cikin zuba mishi ido tace.
"Uhumm". Sai kuma ya ajiye plate da cup ɗin a gefe kana ya miƙe tsaye,
hannunsa yasa ya miƙar da ita tare da cewa.
"Mu tafi bedroom".
Kai ta gyaɗa kana ta juya kamar zatayi bedroom nashi, sai kuma tayi maza ta nufi ƙofar babban falon da sassarfanta tanayi tana buɗa sawunta alamun tana jin ciwon tafiyar.
Ganin kamar yana biyo tane yasa ta ɗanyi ƙara tare da cewa.
"Wayyo Ummey zai kamani".
Sai kuma ta fara sassarfa tanayi tana yarfa hannunta.

Ido ya zuba mata yana kallon tafiyarta, cike da wani shauƙi. Murmushi yayi kana ya ɗauki sauran tea ɗin ya shanye.
Ajiye cup ɗin yayi ya tsallaka kwanukan ya nufi bedroom ɗinsa dan gaba ɗaya jikinsa ba ƙarfi yakeji ga alamun zazzaɓi ga bacci ga wani masha'hurin farin ciki.

Yana shiga ya kwanta lokacin ɗaya kuma bacci yayi gaba da shi.

Aysha kuwa a can falonsu ta samu Ummi, riƙe waya da alamu da Umaymah take mgna.
Tana ganinta ta mike tsaye tare da kamo hannun ta, bedroom ɗin Ayshan suka nufa tana mai cewa Umaymah.
"Alhamdulillah komai ya kusa baiyana da izinin ubangiji.
Gata ma".
Ta ƙare mgnar tana miƙawa Aysha data zaunar a bakin gadonta waya, cikin sanyi Aysha ta amsa kiran da Umaymah tayi mata.

Ido ta lumshe tare da konciya ta juya ta bawa Ummi baya sabida masifar kunya da takeji, da sauri ta kuma rumtse idanunta jin Umaymah na cewa.
"Sannu ko Aysha, Allah ya miki al'barka yasa al'barka a taraiyar ku, Allah yasa nanda wata goma masu zuwa inji lbrin haihuwar jika kamar yadda naji lbrin tukuicin masarautar Joɗa."
Cike da kunya tayi shiru sai dai a zuciyarta tace.
"Amin".
Ummi kuwa falo ta fito jin muryar Jamil.
Ledan magungunan ta amsa tare da nufar Dinning area fridge ta bude DuDu mai sanyi ta dauko,
ta dawo ɗakin Aysha.
Magungunan ta bata tasha da sassayan DuDun kana, ta gyara mata rufuwan ta, sannan ta amshi wayar ta juya ta fita tana mai ci gaba da mgna da Umaymah tana gaya mata abubuwan da aka haɗawa Aysha na tukuici.

Ita kuwa Aysha tuni bacci yayi awon gaba da ita.

A can birnin Yahunde kuwa na ƙasar Cameroon,
Ba'ana ne zaune gaban bokanshi sun sa kasko a gabansu.
Cikin tuhuma Ba'ana yace.
"Tun ɗazu nake cewa ka buga min ƙasa inga Mata inga meke faruwa da ita, sai kayi tamin zanen banza ka gaya min meya faru?."
Cikin tsananin tsoro da kaɗuwa Boka yace.
"Ba komai ita bacci ma takeyi yanzu haka. Kaje sai jibi mu buga muga meke wakana' dan sam yau abun yaƙi nuna komai sai haske mai kashe ido".

Cikin kwaffa Ba'ana yace.
"Lallai kwannan zan tafi Nigeria dole zan koma domin amso matata dole zan tafi".
Yana faɗin haka ya juya ya fita.


Alhamdulillah Aysha kuwa tana farkawa bacci taji komai ya lafa sosai sai abinda ba'a rasa ba.

Bathroom ɗinta ta shiga gasa kanta ta kumayi da ruwan ɗumi kana tayi wonka ta fito ta canza kaya,
Sosai taji daɗin jikinta, sallaya ta shimfiɗa dan yin salla.

Sheykh kuwa tuni ya nufi masallacin Masarautar Joɗa.

Bayan ta idar da sallan Ummi ta kirata suka fito falo.
Tana gaba Ummin na Binta a baya don so take ta kalli yanayin tafiyarta.

Bayan ta zaunane Ummin ta ɗauko tray mai ɗauke da Foodflaks tazo ta ajiye a gabanta.

Acan masallaci kuwa ana idar da sallan Sheykh ya nufo gida.

Yana shiga falon, ko tsakiyar falon bai isoba yaji Muryar Gimbiya Saudatu a bayanshi tana cewa.
"D...!"







Littafin GARKUWA na kuɗine in kinason ga number ta 09097853287 kiyi min mgn


By

*GARKUWAR FULANI*
3/23/21, 5:06 PM - ": GARKUWA




PAGE 25

"Da Mamaki kwallo a maƙabarta.
Wato dai haka za a cigaba da gwara kawunan mutanen. Masarautar Joɗa ana mayar da su marasa tunani?".
Gimbiya Saudatu Ta faɗa tana ya mutsa fuska don ta kasa kallon ƙwayar idon Sheykh.
Banza ya yi da ita duk da ya waiwayo ya kalleta, ya so tanka mata, amman sai ya share yaci gaba da takunshi cikin nitsuwa yana tafe yana tasbihi.
A hankali ya isa falon.

Kanshi ya ɗan juyo ya kalli tsakiyar falon.
Sam bai hango Shatu da Ummi ba dake zaune a falon.
A nitse ya maida kanshi ga inda ya nufa ya juya zai shiga corridor'n da zai sadashi da falonshi. "Ba ka ji me nace bane? Dutse ne kai ko waliy? Wata da watanni a kawo maka mace a ce sai yau ake bada kyautar budurci dan rainin wayo tuntuni kallon hoto kake mata ko me.
Ba ma wannan ba, wanne irin munafurci ne ya sa aka bada kyautar dawakai amarya da ango? Duk yana cikin sahun munafurcin da boye-boyen.."
Cikin tsawa ya dakatar da ita da cewa.
"Bana son shirme fa! Fitar min a gida tunda ba wancan tsohon ne ya gina min shiba".
Da sauri tace.
"Zan fice ba sai ka koreni ba."
Ta ƙarashe mgnar cikin tsananin takaicin tsawar da ya yi mata don sai da hantar cikinta ta kaɗa.
A dake ta jujjuya idanuwanta tare da cewa.
"To wai ɗaga Muryar na meye ne? Tambaya fa kawai nayi nake son amsa.
Wannan sarƙar kuma ta mece ce? Ta asalince wacce ta ɓace ɓat ko in ce ta yi ɓatan-dabo, ko kuma wata ce ta dabam aka ƙirƙiro, don nasan waccer dai bata kai labari ba, daga wuyan waccer ts..."
Bai bari ta cigaba ba ya tare ta da muryarsa a nutse cikin iya sarrafa harshe, ya lumshe idonshi kana ya buɗesu a hankali yace.
"Dakata, tsaya kiji."
Da sauri tace.
"Uhum ina jinka".
Rausayar da kanshi yayi kana a hankali yace.
"Kyauta ce ta girmamawa, wacce ba kowacce mahaluƙiya ce take katari da irinta ba a cikin Masarautar Joɗa, duk da kyautar ta yi kaɗan a wajen wacce ta cancanci ninkin hakan, bana ji akwai abinda za a iya biyan macen ƙwarai da abun duniya ba ko da kuwa za a bata kujerar masarautar Joda wanda wasu wayayan mazaunan cikinta ke wawasun nema ba. Darajarta da kimar kyautar data bada yafi ƙarfin tukuicin da masararutar Joɗa ke badawa, ita ba irinku bace ta wuce hakan".

Shiru Ummi tayi tana mai jin kalamanshi tare da yin wani sassanyan murmushi.

Ita kuwa Aysha a hankali ta lumshe idonunta tanajin kalamanshi masu sanyi da sanyaya zuciya.

Gimbiya Saudatu kuwa. Wani irin baƙin ciki ne ya turniƙe ta, da kyar ta iya saita numfashinta cikin karkarwar jiki da rasa abin cewa ta ce, "Wannan wanne irin yabo ne haka har sai ka haɗa da sarautar gidan nan?"
Yanayin ta ya kalla ya yi Murmushi, wanda ya ƙara tunzirata kana a nitse yace.
"Dan na tabbatar miki da ƙimarta da darajarta ne, ina son kuma hakan ya zauna a cikin ƙoƙon ranki har illa masha Allah..."
Cikin takaici tace.
"Wannan kuma ka yi kaɗan ka sani adana shi a raina"
Kallon da yake mata ne ya hana ta ƙarasa zancen, don daga inda take tana iya jiyo sautin hucin da yake, muddin ta ƙara sa maganarta tsab zai iya wanka mata marin da zai sa ta rasa jinta na awanni.
Da hannu ya nuna mata ƙofa alamar ta fice mishi a gida.
Kamar munafuka ta wuce simi-simi tana gunguni.

Juyowa yayi ya nufi cikin, sai kuma ya ɗan juyo ya kalli cikin falon jin alamun akwai mutun a ciki.
Juyowa yayi cikin falo.
Cikin nitsuwa ya kalli Ummi da Shatu.
Da alamun Ummi lallaɓata take taci abinci,
Idonshi ya ɗan lumshe, haka nan yaji wani irin sanyi har cikin ransa yake jin daɗi.

Wani ɗan guntun Murmushi yayi bayan ya kalli fuskar Shatun data ke kwaɓe har da turo baki.
Wayar Ummi ce ta fara suwa juyowa tayi ta ɗan jawo wayar,
tana dubawa taga Umayma cikin farin ciki ta ɗaga, tare da karawa a kunne kana tace.
"Assalamu alaikum, Umaymah Sheykh."
Cikin tarin jin daɗi Umaymah tace
"Wa alaikassalam Ummin Sheykh ina yaran naki? Ya jikin ɗiyar tawa"!".
Murmushi Ummi tayi kana tace.
"Alhamdulillah suna lfy, ɗiyarki jiki da sauƙi gatasu ma kusa dani".
Cikin kula tace.
"Bata wayar".
To Ummi tace kana ta miƙawa Aysha wayar.
Tare da cewa.
"Ga Umaymah".
Amsa Aysha ta yi ciken jin sanyi tace.
"Assalamu alaikum Umayma barka da rana."
Cikin tsananin kulawa Umaymah tace.
"Waalaikumus salam Habibty, sannu Aysha Addana, Allah ya yi miki albarka, Allah ya saka miki da al'khairi, na ji daɗi sosai, in sha Allah al'khairi da haske yanzu zai bayyana, sannu kin ji my dear, ki kula da kanki sosai, ki dinka shiga ruwan dumi akai akai, sannan kada ki yi wasa da kunun nan da Ummi take miki, kin ji ƴata ki yawaita cin gashin naman da zatanayi miki da shan kunun har na tsawon kwana uku kinji ko Aysha."
Wata azababbiyar kunya ne ta rufeta.
A kunyace tasa ɗayan hannunta ta rufe fuska tana jin inama ƙasa ta tsage ta shige cikinta.
Da ƙyar ta iya ce wa,
"To Umayma."
Jin Muryarta ya sa Umayma yin dariya don tasan kunyace irin na ƴaƴan Fulani ne yasa ta yin shiru.
Cikin murya mai baiyana jin daɗin da take ciki tace.
"Yauwa Aysha, Allah ya yi miki al'barka."
Cikin sanyi da jin daɗi tace.
"Amin Umaymah".
Kana daga nan
Suka yi sallama ta kashe.

Sunkuyar da kanta tayi tare da mikawa Ummi waya, don izuwa yanzu kunya ta gama jiƙeta, kallonta Ummi ta yi tana jin dadi aranta tana kuma addu'ar Allah ya nuna musu ranar da ƙwai zai fasha, don ga alamun nan suna ta tabbata.
Shi kuwa Sheykh ajiyan zuciya mai sanyi ya sauke kana ya juya ya nufi falonshi.

Ummi kuwa Kitchen ta wuce da tray'n a hannunta.


Ita kuwa Aysha Anan falon ta zauna tana tunani kala-kala musamman akan masarautar sam ta kasa gane mata.
A kullum da kalar surƙullen da zai bayyanar mata, ko meye ma'anar zantukan da suke yawan yi wanda bata gane masa ba?.
Dazu tajiyo Gimbiya Saudatau da Sheikh maganganunta sun bata mamaki, lallai akwai wani babban al'amari a cikin gidan nan, wanda da sannu zata fahimci menene wannan abu.
Kuma zata tambayi Ummi wani abu ko zata gaya mata, ko ta samu sauƙin Tsarkakkiyar dakw cinnzuciyarta.
Tana nan zaune har aka kira sallar la'asar ta tashi daƙyar don har yanzun bata jin dadin jikinta.
Bedroom ɗin ta ta wuce.
Kai tsaye Bathroom ta nufa.

Al'wala ta ɗauro don har masallacin masarautar sun tada kabbara.

A hankali take taku sabida har yanzu tanajin jikinta na mata

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login