Showing 93001 words to 94417 words out of 94417 words
kami ƙamin gaisuwata gun Aishatu".
Murmushi Abba yake cike da jin daɗin hakama Galadima.
Shiko Sheykh kansa ya ɗan kawar tare da karɓar ƙwaryar da Gimbiya Aminatu take mika masa.
Murya can ƙasa cikin maƙoshinsa yace.
"Koma menene ni zanci tun da nike laulayin ba itaba".
Yayi maganar a saman lips ɗin sa,
Da sauri Abba ya zuba masa ido cike da mamaki, kenan Jabeer gadonsa yayi shikeyiwa matarsa laulayi, murmushi yayi sanin yayi maganar ne batare da yasan tafito ba.
Shiko Sheykh mikewa yayi rike da ƙwaryar yanufi kofa yana cewa
"Sai anjima"
cikin ɗan ɗaga murya Galadima yace.
"A miƙa mana gaisuwa gun ta".
Shidai baice komai yafita dan a zatonsa basuma ji mgnar da yayi ba.
A parlour yasameta zaune ita ɗaya Ummi na kitchen.
A hankali ya ƙaraso gareta.
Hannunshi kawai yasa ya kamo mata.
Ba musu ta miƙe, hannunta yaja suka nufi falonshi.
Bisa kujera ya ajiyeta, kana ya zauma kusa da ita kallonsa tayi tare da kallo ƙwaryar dake hannunsa sai ta daɗa matsowa jikinsa sosai tace
"Menene wannan ɗin?".
gyara rike ƙwaryar yayi tare da cewa.
"Gimbiya Aminatu ce tabani wai in kawo miki irin wai ke mai ciki al'halin nine ma nake miki laulayin.
Dan yanzu dai koma menene ni zan cinye tun da nike laulayin".
Ya karasa faɗa yana ɗage faifayin da a ka rufe ƙwaryar da shi, kindar ne fari sol sai ɗan mai kon yelo a saman sa, yawun da ya cikin mata baki ta haɗiye tana miko hannu tana faɗin
"Bani tunda ni tace ka kawowa".
ƴar karamar ludayin duma dake ɗaure kan fefayin yaɗauka yaɗibi kindar mai sanyi da shi,
kana yace
"Sai dai kijira idan na koshi nabaki sauran".
Ya ƙarashe mgnar yana ɗago ludayin yakai bakinsa, lumshe ido yayi jin garɗin daɗi da sanyi da ɗan tsami-tsami ya gauwaye bakinsa, sosai yaji daɗin yadda yaji ɗan tsamin a bakinsa.
Zumbura baki tayi tare da cewa.
"Ni dai ka bani".
A hankali ya kamo hannunta ya ɗagota ya ɗaurata kan cinyarshi yasa ƙwaryar a tsakiyarsu,
Ido ya lumshe tare da sa hannunshi ya tallabo haɓarta bakinsu ya haɗe, a hankali ta buɗe bakinta.
Shi kuwa cikin sanyi ya lasa mata kidar ɗin.
Kusan a tare suka lalumi tong ɗin juna,
jin yadda ta mishi riƙon lollypop ne ya sashi janye bakinsa da ƙarfi tare da cewa.
"Wash Mamey zata cinye min harshe".
Da sauri ta riƙo hannunsa dake rike da ludayin takarkatashi takawo bakin ta takurɓa, harshenta ta fidda talaso sauran ragowar dake cikin ludayin.
Hannunsa ta sake tana gyara zamanta da kyau ta ce
"Yah Sheykh shanyewa zakayi gaskiya ni dai kabani kayana".
Da sauri ya ɗan zaro idansa tare da cewa.
"Kuma tun yazu kike so in baki."
ido ta rufe kana ta buɗe tana kallonsa.
Sai kuma yasaki wani murmushi da har sai da jerarrun fararen hakoransa suka bayyana,
yatsar sa ya miƙa kan kumatunta yalakaci kindar daya shafu mata a gefen kumatu yaɗa go yatsar, kana yanuna mata, fuska takwaɓe tare da turo baki gaba tace
"Bakai bane".
ludayin yakuma maiwa da cikin ƙwaryar yaɗiba yakai bakinsa yakurɓa tare da mai da ludayin cikin ƙwaryar kana yace
"Danayi mefa?".
baki takuma turawa tace
"Ka hanani a buna".
ido ya kuma zarowa yace.
"Ni Muhammad na isa in hanaki abunki da Allah ywce in baki.
Taso muje ɗaki nabaki abin naki yanzu nan".
Ya ƙarashe mgnar yana mata dariyar wasa kafaɗa ta maƙe gane abin da yake nufin, tace. "Nidai a'a wanna nakeso". ta ƙarashe
tana nuna ƙwaryar. mikewa yy yariko hannunta yace.
"Zomuje duka zan baki ai da wannan ɗin da Jabeer ɗin".
yana rike da hannunta ɗaya hannunsa na rike da ƙwaryar suka nufi bedroom ɗin shi.
Rayuwa kenan. Haka rayuwa tacigaba da tafi kwanaki suna juyawa i zuwa makonni, makonni na shuɗewa i zuwa watanni.
Alhamdullah cikin ikon Allah da buyawansa yanzu cikin Shatu wata shida kenan kuma har yau magauta basu san da shiba dan bata fiye fita kuma cikin baida wani girma.
Tana zuwa makaranta tana karatunta hankali konce.
Tana waya da Ummeynta.
Alhamdullah yanzu zazzaɓin daren da Sheykh yakeyin nan yazamo tarihi yawarke tsaf abinshi,suna rainon cikinsu cikin kula da tarai raya da ɗonkin ganin ranar zuwan Baby.
Zaune suke a parlour Ummi na saman kujera Shatu kuma na zaune a kasan carpet ta mimmike sawunta ta tasa ɗan madaidacin cikinta a gaba,
tana ɗan kurɓar kunun tsamiya da Ummi ta dama mata,
Ummi ta ɗan kalleta tare da cewa.
"Ikon Allah kinga na sha a fa ɗazu Juwairiyya ke cemin Gimbiya Aminatu ba lafiya tana zazzaɓin mura".
A jeyi cup ɗin kunun tayi tana cewa.
"Allah sarki shiyasa tun jiya bata turomin haɗin furan nan ba Ummi muje mudubata tunda ba abinda mukeyi". Ta ƙare mgnar tana miƙe cafal kamar ba mai cikiba.
Cikin fari kenan.
A hankali ta shiga ɗaki taɗauki ɗan ma dai-dai-cin hijabi tasaka a kanta tafito,nan tasami Ummi rike da mayafin ta.
Tare suka nufi sashin Gimbiya Aminatu.
Da sallama suka shiga parlour'n Gimbiya Aminatu.
Ummi na gaba Shatu na biye da ita.
Hajiya Mama da Gimbiya Saudatu duk suna zaune cikin parlour'n.
wani irin mikewa Gimbiya Saudatu da Hajiya Mama sukayi cikin tsananin
kaɗuwa da zallar mamaki suke kallon cikin da basusan farkon saba sai daya baiyana kansa yau rana tsaka suka ganshi,
Cikin wani irin tashin hankali da baƙin cikin Hajiya Mama ta juya cikin wani irin kiɗima tafice a parlour'n gaba ɗaya idanunta sun wani fiffito sun zazzaro waje saboda sabar firgici da baƙin cikin wannan cikin data gani.
Tana fita hanyar part ɗin ta tanufa hankali tashe, ɗago wayarta tayi tana tafiya tana daddanna shi tana sharar ƙwanar part ɗin ta takai wayar kunne,
Tana wani irin huci na tashin hankali,daga cikin wayar kuwa ringing biyu zuwa uku a ka ɗaga me biye da kiran
yace.
"Hajiya bar".
Da sauri cikin ɗaga murya tace.
"Dakata Boka gilmau bana bukatar gaisuwarka! haka mukayi da kai wani irin makudan kuɗine ban zubda makaba k".
Cikin dakiya boka GILMAU ya katse ta.
"Da kata Hajiya ki daina min ihu akunne dan ba fahimtarki zanyiba."
Bokan yadakatar da ita kafin takarass faɗar kalmar k. data furta.
Itako cikin musifar tashin hankalin da take ciki tace
"Gani nan zuwa gurin ka yanzu dan wlh bazai yuwuba dole a sake sabon shiri".
Tana kaiwa nan takashe wayar tashiga ciki taɗau mayafin ta da makullin mota da da wasu kuɗaɗe masu yawa a ɗaure bandir-bandir tafita tanufi in da mota yake tashiga taja da mugun gudu tafi tanufi gidan Boka.
Cikin rawan jiki take tuƙi hannunta ɗaya riƙe da waya ta kara a kunne wanda ta kira Jahan.
Shi kuwa Sheykh (Jahan) kenan yana zaune a Office nashi yaga kira da layinsa na sirri a yar ƙaramar wayar da ko inganta a garƙame yake.
Murmushi yayi ganin 3 bala'i da haka ya seba number.
Wani murmushi iya salon taku yayi kana ya amsa kiran tare da ƙara wayar a kunne ya sauya muryarsa tare da cewa.
"Hajia Mama Uwar Sheykh meke faru".
Cikin faɗa tace.
"Oouxubillahi subahanallahi Jahan kada ka sake cemin uwar Sheykh kai kasan duk duniya babu wanda yasa irin zallar tsanar da nakeyiwa wannan shegen yaron da sihiri baya cinsa data daɗi wlh yau ji nakeyi zan iya zubawa Part ɗinshi Dana ƙannenshi wuta su ƙone su mutu kowama ya huta".
Wata iriyar ja'irar dariya yayi tare da cewa.
"A a to yau kuma me kika gani a kansu ɗaya tada miki hankali ne haka".
Cikin tafasan zuciya tace.
"Dariya ma na haka kenan, to bari kaji wannan shegiyar matar tasace, naga cikine da ita cikima mai girma kuwa".
Da sauri yace.
"To dan ganin cikin ne hankalinki ya tashi".
Cikin tsantsar tsana tace.
"Wlh tallahi sai na zubda cikin nan wlh babu wanda zai ƙara haihuwa cikin ahlin A'isha nida nake son on ɓaddasu a masarautar Joɗa ya zanyi in barsu suyi ta haihuwa wlh zan zubda cikin in Kuma ya fito duniya tabbas zan kashe ɗan".
Wani irin miƙewa tsaye yayi lokacin ɗaya zufa mai zafi ta karyo mishi gaba ɗaya jikinsa rawa yake, cikin saisaita nitsuwarsa yace.
"Eh lallai wannan batun babbane bari anjima zanzo muyi shawarar yadda zamuyi".
Yana faɗin haka ya katse kiran.
Yatsarsa manuniya yasa ya sharce zufan daya feso masa a goshi.
Kana sai kuma yayi murmushi tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun. Hasbunallahiwani'imanwakil."
Yayi ta maimaitawa kana ya koma ya zauna ya dafe kanshi tare da cewa.
"Uhmmmm Hajia Halima kenan rashin sani ya saki kina shuka a idon makorwa.
Wai ni Muhammad Jabeer mena tsare miki nada yan uwan da mahaifiyarmu da kike so ganin baya mu, me cikin matata ya miki, meyasa zaki so cutarmi da Aish da ɗan...!
By
*GARKUWAR FULANI*