Showing 69001 words to 72000 words out of 73969 words
juna Suka qurawa juna Ido akaro na farko suke yiwa juna kallon tsaf.
Itace kunya tasata dauke idanuwanta tareda sauke Kai Tana kallon wani guri.
Shima juyarda Kai yayi cikin basarwa yayi gaba yana cewa"
Muje.
Ba laifi da kansa ya jidar Mata Kaya sbd ganin takasa sakewa shikuma ya gaji da wannan dolen komawa yakeson Yi shiyasa kawai yafara daukar Mata komai yasamu na buqata.
Dayazo gurin akwatina baiyi tunanin komaiba ya zabi wani simple set masu kyau da tsada masu guda hudu Kuma duk bawani girmane dasuba.
Aiko nan yacigaba da zabar komai dayazo kan undies ne ya fuske tareda tsuke kyakkyawar fuskarsa ya fidda wayarsa yana dubawa bai kalletaba yace"
Kiyi sauri kizaba inada gurin zuwa time yakusa.
Matsawa yayi daga gurin tabi bayansa da kallo Tana jinjinawa kanta da irin tunaninda zuciyarta ta jeho Mata najin inama tanada aure wainnan abubuwan Suka faru da rayuwarta Bata gantale hakaba,
Da koyayane Tana cikin rufin asiri bazata Zama Yar rabe rabe ba ko talakane dashine rufin asirinta take taji so da shaawar aure sun shigeta Amma waye zai sota ya amince ya aureta Tana Yar Wanda sunansa yagama baci a duniya sbd zalunci da kashe Rai ba bakin komaiba.
Kukane da batasan da zuwansaba ya kubce Mata jikinta na wata irin rawar tashin hankalin shikenan iyayensu sun Bata musu rayuwa suntafi sunbarsu da mummunan tabon rayuwa.
Da sauri ya juyo ya kalleta Jin kukanta yaga yanda jikinta ke rawa sbd sheshekar kukanta take yaji jikinsa yayi sanyi tausayinta ya kamasa sbd tabbas yasan iyayensu sun cutatardasu ta wani fannin.
Matsowa yayi bayan ya rintse idansa ya fitarda numfashi mai sanyi ya Dan kalleta tareda zaro handkerchief dinsa ya miqa Mata yana kallonta qasa qasa yace"
Meyasa zakiyi kuka cikin nutane sbd jawo kallo akankine kikeyi so please stop this right now and wipe this now"" yafada yana kallon hawayenta da cikin idanuwanta data dago ta kallesa tayi saurin janye idanuwanta sbd kasa hada Ido datayi dashi hawayenta na qaruwa.
Ganin takasa daina kukan sbd yariga yazo Mata yasa yabata key yace Takoma mota zai biya yazo.
Tattara kayan akayi guri daya aka Fara aikin hada kudinsu kusan minti arbain kafi aka Gama ya biya aka fiddo da kayan aka zuba bt da sit din baya sbd bt din bai dauke duka kayan.
Kasa tayarda motar yayi Saida taji shiru ta dago jajayen idanuwanta ta kallesa ya Dan ya mutsa fuska yace"
Kinsan bazan kaiki gida a wannan yanayinba nadey will feel bad seeing you like this.
Kallonsa tasakeyi da sauri jikinta na sakeyin sanyi,
Nadey taji Dadi tayi Sa'ar rayuwa kowa na sonta yanason farin cikinta.
Share hawayenta tayi ahankali ta furta"
sorry.
Ajiyar zuciya yasauke Jin yanda tace sorry din ya tayarda mota sukabar gidan.
Koda suka dawo shiru sukayi dukkansu cikin motar tsawon mintuna kafin ta Dan dago ta kalli gefensa vata kalli fuskarsa tace"
Thank you.
Daga Mata Kai yayi Shima batareda ya kalletaba.
Budewa tayi ta fito Shima fitowar yayi tareda bude boot ta dauki wasu kayan tayi gaba yabi bayanta da kallo yanda take tafiya kamar zata karye sbd sanyin jiki da damuwa
Bata ankaraba tayi tuntube zata Fadi taku biyu yayi ya tareta ta 'dan fado jikinsa.
Akaro na farko dayaji wani Abu a taba jikin mace sbd duk turawan dayake huldar aiki dasu yana shaking hands dasu wasuma har hugging Amma baitaba Jin komaiba Sai yau yaji wani irin shock da kasala lokaci guda.
Itama jitayi tasake loosing balance gabaki Daya jikinta yasake sakewa.
Kawu dake Shirin fita yana sanyo kai harabar gidan yayi sauri zaro idanu tareda sake fitowa Yana quresu da kallo daidai lokacin Suma su nadey sun fito Yana riqeda gefen qugunta suna dariya Yana sake riqota Yana Mata rada Tana kamo wuyansa dayayi Mata tsawo Yana sake dagata.
Juyowa kawu yayi gefensu Suma Yana kallonsu kamar zai rusa ihu
Yasake maida idanuwansa kansu JJ da kamarma sunfi su nadeyn shagala cikin masifa da daga murya yace"
Kowane shege ya tattara yazo yabarmin gidana.
Da sauri su nadey suka saki juna sbd sai alokacin suka Ankara dashi suka ga halinda jj da fammah din suke.
Nadey tayi saurin Isa ta riqo fammah din sai alokacin suka saki juna nadey ta riqeta zasu shiga ciki kawu yace"
Kudawo Nan kafin na karya qafafuwanku masu kama da takandar rage hardai ke me kama da jikar ifiritu Ashe kin koyawa fatimar rashin arzikinki gashinan su arana tsakiyama Kuma Dan tsabar anrainani ko aure Babu....
Cikin sauri jj yace"
Kawu bafa yanda kake tunani bane kayi hakur.....
Jabiru kadaisan a qule nake dakaiko?
To kayimin shiru agurin ko wlh na fusata na daura muku aure ayau saiku qarata can kaida ita
Kema Ina ganinki ta arziki Ashe kinkoyi rashin munyarsu..
Girgiza Kai fammah din tayi da sauri zatai mgn yace"
Zakimin shiru agurin kosaina fasa bakinki Mai kama da qofar kasuwa.
Zaro idanuwa famman tayi da qarfi tareda cewa"
Kasuwa????
Dariya suka danne sbd sukam sunsan halin kayansu tsaf itace sabuwa a abin.
Kayan menene nake gani harda akwatina???
Kallon kayan jj yayi yace"
Kayane aka siyo Mata.
Lefenka ne kenan ka hado Babu sanina sbd anrainani ban isaba kokuwa shi aliyun shine yabaka dama to ai ita fatiman a gidana take Dan haka a ikona take bazan bayarba.
Da sauri Zaki ya matso Yana cewa"
Yi hkr kawu dama Ina zaayi wani Abu bada izininkaba kawai kayan ne yasiyo tukuna.
Wani banxan kallo jj ya jefawa zakin Yana cewa"
Sarki karka sake hadabi da kawu mana,
Wlh kawu dama Babu wani wannan mgnar kayane na sawa batada aka siyo Mata thats it.
Kallonsa fammah tayi akaro na farko taji wani na rejecting dinta Kai tsaye duk da tasan he's right saidai yanda yayi mgnar cikin bayyana rashin sonta a fili.
Cikin wani irin yanayi ta bude Baki tace"
Baba Babu komai a tsakanina dashi ya taimakenine da suturar dazan saka ne kawai koba komai mezaiyi da 'yar da akewa kallo da laifin iyayenta,
Bashibama Babu Wanda zaiso aurena sbd karya auri 'yar mutanenda akewa kallon azzulimai,
Nasani Babu Wanda zai taba shaawar Sona bare aurena Dan haka kuyi hkr dukkaninku Nima ba laifina bane....
Kuka tasaki tareda juyawa ta shige ciki Tana toshe bakinta.
Sanyi dukkaninku jikinsu yayi musamman shi jj ya juya jiki ba qwari zai bar gurin kawu yakira sunansa.
Dawowa yayi ya tsaya yana sauke Kai.
Cikin nutsuwa kawun yace"
Jabiru idan nine zanmaka zabi da aure kamar yanda nayiwasu Zaki to haqiqa na zabar Maka Fatima sbd jahadi zakayi ka tallafi rayuwarta marainiyace zaka samu tarin lada da kwanciyar hankali insha Allah.
Baisoba har cikin ransa Amma ayanda kawun yake uba agaresu bazai iya musawaba,
Sarkima yayi Masa zabi ya daura Masa aure bai musaba bareshi.
Ajiyar zuciya ya saki a boye kafin ya dago ahankali yace"
Nagode kawu Allah yaqara girma da nisan kwana.
Dafasa Zaki yayi cikin basa qwarin gwiwa yace"
You won't regret this my magaji I promise,
Bakasan yanda auren dolen kawu yakeda Dadi bane zakazo yiwa kawu godia Ina Nan.
Wani kallon takaici kawun ya jefawa zakin zaiyi mgn jj yayi saurin cewa"
Yi hakuri kawu.
Jinjina Kai yayi zaiyi mgn saikuma ya fasa ya wuce Yana cewa"
Bazaa dauki lokaciba tunda baa buqatar wani abin inaga kufara Shirin Nanda wata Daya dai zanfadawa babanku.
#MAMUH. *_Mamuhgee46_*
Kamar wani mugun labari haka ya dauki zancen auren Amma Kuma Daya tuna kawun ne yayi Masa zabin saiyaji zuciyarsa ta kwanta da alamarin saidai baisan ta Ina zaifara rayuwar iyali da fammah din ba.
Tareda Zaki suka fita zuwa ma'akatar dasuka bude gini guda sbd 'yan daba irinsu a da wadda aka budeta sbd su kawai Dan tallafi da yancinsu na bawa kowa jarin irin sanaarda zaka iya idan ka shiryo aka bude tsohon case dinka sune ke tsaya Maka da haka Allah yataimakesu abubuwan dabanci suka Fara ragewa yan ta'adda nata shiryiwa wasu Kuma ana tallafa musu suna komawa makaranta masu shaye shaye kuwa idan yayi tsamari gurin yan drugs suke muqasu da sharadin ba azaba Mai tsanani shekara gudane idan Allah ya taimakeka ka daina kenan har abada wasu ko shekarar basayi sun fito sun daina.
Cikin dakinsu kuwa nadey ce tafadawa fammah abinda baban yace ta Dora da cewa"
Kiyi hakuri nasan baba zai fahimta idan har bakyaso,
Zaiyi fada sosai amma daga baya zai hkr sbd bayada riqo ko fushi irin na wasu iyayen,
Baba haka halinsa yake saidai shi haka tasa qaunar take idan baya Miki fada to bayasonki sbd shi abinda yakesone kawai yake sawa gaba da fada komai kayi laifine.
Girgiza Mata Kai fammah tayi cikin yanayi na sanyi tace"
Akaro na farko a rayuwata da want yayi min abinda mahaifine kawai keyi,
Banda Mai tsayamin,
Banda Wanda zankira nawa saiku,
Baba yayimin abinda zaiyiwa 'yarsa konace abinda yayiwa 'yarsa Wanda Nima Ina yiwa kaina shaawar samun Ingantacciya,wadatacciya da kwanciyar hankalin rayuwan aure kamar naki to mezaisa naqi zabinda Wanda yadauki matsayin uba aguna?
Na amince da duk zabi da hukuncin baba akaina kowane irine.
Murmushi nadey tayi tareda tausayinta sbd Tana hango maraicin dake cin fammah din atareda ita sbd fammah din mutum ce Mai tsananin so da qaunar familynta.
Tasani kewar am haryanxu Tana cinta saidai tamayarda hankali gurin yimasa addua tareda nemawa iyayenta gafara.
Ahankali nadey itada iya talatu da fadime suka bude akwatinan suka zuzzuba kayan aciki komai Kuma ya shige abinda Babu daga baya nadeyn tace zataiwa jj din magana saiya qaro ko yabayarda kudi su siyo.
Ana Kiran magrib ta fito kitchen daukeda basket data jero semo dinda tayi Masa da fresh vegetables soup sai lemon mix da Babu sugar ko kadan aciki sai Zuma kadan itama.
Wanka tayo tareda alwala Tana fitowa sallah tafarayi kafin tafara shiri cikin wata doguwar royal blue straight D&G rubber fab gown.
Wani hot red lipstick tasaka na oriflame akan lips dinta sai powder kadan da eyeliners shima kadan baama ganewa ta sake gyara gashinta ta feshesa da hairspray ta dauresa tsakiyan Kai.
Bold hot red lipstick dinta shine yafi daukan hankali sbd yanda ya zauna.
Shape dinta da rigar tabi ta lafe fammah ta kalla Tana ayyanawa aranta itama saitayi haka zata samu zuciyar mijinta da kyau idan sukai aure sbd har cikin ranta ta karbi auren sbd ta tabbata jj zai inganta rayuwarta tabata kyakkyawar rayuwa so ita kam ta karbesa hannu bibbiyu tunda haydar yagama yimata nisa gwara ta rungumi abinda ya sawwaqa gareta sbd inganta rayuwarta karta tsaya hange rayuwar batada tabbas afterall Zama cikinsu shine rufin asirinta da farin cikinta,
Asalinsu basuda alaqar jini kusan dukkaninku zuriar gidan,
Aminci ne da amintaka tun dagakansu baban da amininsa hakama jj dasu Dr sayyid dasu nanu Amma sun riqi junansu tamkar jini daya,
Sun maida kansu zuria daya suna qaunar junansu fiyeda komai,
Iyayenta sune silar duk wani kuka da qincinsu Amma still sun karbeta acikinsu tazama tasu haka Dan uwanta sun basa damar gyara rayuwarsa.
Batada wasu dangi nata bayansu Wanda sai yanxu take sanin dadin qauna da tattalin juna tareda sakewa da juna Wanda basusamuba koyaushe iyayensu na hidimar neman kudi kota kyau kota sabanin hakan.
Murmushi yasauka a fuskanta ahankali ta tashi tazo ta rungume nadey data saka kimono da Vail saman kayan cikin farin ciki ta furta"
Thank you nadey dattiya Noah.
Murmushi nadey tasaki tareda rungumeta tace"
And wat are you thanking me for Mrs j.d Noah???
Murmushi fammah din tasake saki sbd Jin itama she'll soon be fammah D Noah.
Sake cewa tayi"
Thank you for giving me a wonderful life and family to call my own again.
Dariya tayi tareda daukan turare ta fesawa Vail dinta kafin ta juyo ta kalleta Tana dariyar farin ciki tace"
Welcome to the family to but ba amatsayin sirikaba but as new daughter of the dattiya Noah family.
Dariya sukayi dukkansu kafin ta juya ta dauki wayarta dake ringing taga dad dintane ta dauka da sauri Tana cewa"
Dad I'm really missing you Amma baba da Uncle sun hanani fita and this is not fair..
Cikin farin ciki yace"
Kyale haydar zanyi Miki maganinsa Amma Yaya kam saidai hkr duk mu duka.
Dariya sukayi itada fammah tace"
Dad kaima kana shakkar baba bare...
Murmushi Mai sauti yayi ahankali Yana tuno masifa da daru irin na yaya dattiyan su basumaga komaiba ai yayi sanyi ahakan Koda sukazo duniya yasake wani murmushin kafin yace"
Kudai kucigaba da lallabasa sauqinsa ma kuka samu shiyasa kuke Masa wani rashin Jin hardai haydar.
Wlh dad ko yanxu da dama dai Amma baba rigimane ahaka muke sonsa.
Maganar wasu takardu na wani sabon contract suka fada tafara yimasa bayani kafin tace Masa sauran bayanin suna hannun jj Dan contract din na hannunsa sbd new Noah's publications na Zurich a hannunsa yake.
Suna gamawa ana Kiran sallar ishai sai kawai tayi sallarta Tana gamawa tasake gyarawa ta fice da wayarta a hannunta.
Allah ya taimaketa Babu kowa a palon ta wuce dining ta dauki basket dinta ta fice.
Koda taje baidawo daga masallaciba ta cire kimononta ta ajiye cikin closet din dakinta dake kallon nasa ta fito Palo ta fitarda abincin ta jera a dining taje kitchen din dake palon ta dauko ruwa a fridge Tana fitowa taji anrungumota ta baya tareda sake ajiyar zuciya ahankali Yana shinshina wuyanta dake fidda qamshim wani sanyayyan oud mara qarfi ko kadan.
Aje ruwan tayi a dining tareda juyowa Tana kallonsa cikin wani irin yanga da basarwa Tana wani narkewa.
Kallo Daya yayiwa lips dinta yaji Yana neman loosing control sbd they look damn hot and seductive.
Ganin yanda yake kallon lips dinta idanuwansa na neman qanqancewa tadan motsasu kamar zatai mgn
Kasa hkr yayi ya matsota qirjinsa ya duqo da fuskarsa ya Dora nasa lips din akai tareda lumshe idanu Yana zura harshensa cikin bakin nata.
Qamshin butter lemon mint din bakinsa ya shiga hancinta take kwadayin sweet din ya kamata ta kama harshensa ahankali ta tsotsa Wanda yasashi sake matseta jikinsa Yana sake lumshe ido cikin nutsuwar dake shigarsa.
Tudun qirjinta ta sake manna Masa yasaki numfashi da qarfi Yana sake kusawa cikin bakinta itakuma Tana tsotsan harshensa dayake sarqe da nata.
Saida suka Gama shanye mint din ahaka kafin ta zame tareda Dan kallonsa taga yanda ya kafeta da ido,
Ahaka jarumine Mai bawa wasu mazan tsoro Amma ayanxu tasan yakai gabarda komai tasashi yanxu yi zaiyi ba wani dogon musu.
Wani irin murmushi tasaki tareda kama hannuwansa ta Dora a qugunta Tana cewa"
Honey come let's have our dinner abincin zai fita ranka idan bakaci yanxuba..taqarasa fada Tana yawo da hannuwanta dake kan nasa kan qugunta zuwa gefen cikinta.
Wani murmushinda ba shiri ya sabuto Masa ya ranqwafo daidai kunnenta yace"
Kawu baisan waye yake lalata wani acikinmu ba dabaice nine Mai Bata Masa 'yaba sbd wannan 'yar tasa ni Tama Gama da wuce wayona.
Wata irin kunya taji Amma saita basar tareda sake riqo kansa itama takai bakinta kunnensa saidata Fara sakar Masa wani numfashi mai dumi aciki cikin kirsa tace"
Dinner.
Kallonta ya dago yayi cikeda mamaki sbd tagama kwance duka notikan kansa.
Zama yayi tayi serving dinsa da abincin kadan sbd sanin becin abu me nauyi sosai da dare.
Lemon mix dinsa nema tasan zaisha da Dan yawa shima dama sbd kaman powerhorse yake Yana qarawa maza lfy ne.
Janyota yayi kan cinyarsa ya zaunar da ita ta ringa basa abincin da kanta idonsa na kanta tun anan tafarajin tsoro na kamata jikinta yafara sanyi duk saita saurara Tana sake sanyi.
Kallonta yayi tareda sakin murmushi Yana tunanin tasan bazata iyaba ta takalosa.
Abinci yakai bakinta ta kallesa ahankali yace"
Eat mana my beautiful bride.
Sake kallonsa tayi da sauri Tana kallon murmushin dake fita a fuskarsa taji tasake shiga Dan rudu.
Shafa fuskarta yayi har zuwa lips dinta ya shafasu tareda kallon cikin idanuwanta yace"
I love this,
And i think its driven me crazy tun kallon farko..yaqara shafasu hot red din nasake rikitasa yanajin control dinsa ba saki Amma ya daure Yana sake kallonta.
Befi ci huduba tace Masa ta qoshi ta zame ta maidai kayan kitchen tareda juye miyar a wani Plastic bowl me murfi ta rufe tasaka fridge.
Ta fito Tana tafiya cikin wani karya jiki duk da a tsorace take.
Kamo hannunta yayi yacirata sama Yana cewa"
My beautiful bride what's wrong??
Shigewa tayi jikinsa harsuka Isa bedroom dinsa ya sauketa kan gado tareda zare jallabiyarsa ya dauki waya yakira P.A dinsa daya kirasa kusan so biyar.
Waya yakeyi hankalinsa kwance Tana daga kwance Tana kallonsa cikin burgewa da shauqin sonsa.
Yana ganin yanda take kallonsa ya datse wayar tareda kashewa gabaki Daya yayo gurinta bayan ya rage hasken dakin sosai.
Ya kwanta gefenta tareda Dora kansa akan pillon da kanta yake ya jawota jikinsa tareda zura hannu ya zuge zip din rigarta ahankali Yana cusa kansa cikin wuyanta zuwa qirjinta.
Yana kaiwa qarshen zip din ya zura hannuwansa cikin rigar Wanda yasata Jan numfashinta da yayi sama kamar zai dauke sbd 'dumin hannuwansa dasuka sauka a kan cikinta zuwa qirjinta.
Jin ta dauke wuta gabaki Daya yasashi sake shigewa jikinta tareda zare rigarta gabaki Daya har qarshe ya mirginata qasa yayi Mata rumfa da qirjinsa me Fadi dake bayyane Yana Kai fuskarsa qasa ya kama bakinta yana kissing ahankali cikin sake yawo da hannunsa Daya a jikinta.
9:40am
Morning.
Daqyar ta mirgina tasauka daga kan gadon Tana dafa kafadunta dasuke Mata kamar an gwafce gabaki Daya gabobin jikinta sbd ciwon dasuke mata.
Tausayintane ya kamasa sbd yanda ko asuba datai sallah jikinta ciwo yakeyi sosai.
Bakin gadon ya qaraso ya dagota sama tareda hadata da qirjinsa Yana kallon fuskarta datai fresh ya hura Mata iska a fuska ahankali cikin kashe murya yace"
Sorry wife.
Kwantar dakai tayi a qirjinsa tareda sake shige nasa tanajin jikinta na sake amsawa tace"
Yunwa nakeji and I can't go inside the house like this.
Kissing lips dinta yayi tareda kamota suka fito Palo ya zaunar da ita tareda cewa"
Wait here bari nadubo fammah takawo Miki wani Abu you know I can't cook,I dont even know how to.
Kallonsa tayi Tana murmushi sonsa tace"
I love you for that.
I love you for this also""yafada Yana shafo wuyanta Yana Mata wani irin kallo.
Da sauri ta turesa cikin shagwaba tace"
No this is sweetmouth.
Dariya yayi Yana kallonta cikeda mamakin zancenta yace"
La ila saina fadawa kawu ya......
Da gudu ta tashi ta bisa ya fice Yana wani smiling.
Fammah ce takawo Mata breakfast suka zauna dining sukaci su ukun harda fammah din suna qoqarin sakewa da juna sosai musamman yanda zakin ke takalar nadey din Yana Mata wasu abubuwan yasa fammah Jin shaawar auren nasake shigarta abinka da dama tasaba da rayuwar sakewa saita saki jiki kawai dasu.
JJ ne yazo ya daukesa suka fita guraren qarfe biyu tareda nanu Wanda shima dattiya yabasa auren asmau 'yar alee idi qwaya Daya sai qaninta Daya Ahmad sukadai Allah yabawa idin Wanda tareda nasu jj zaa hade ayi lokaci daya.
Kwananta biyu Tana fama da ciwon jiki ganin idan taci gaba da haka to duk tasamu kasancewa da mijinta za'a riqa ganewa yasa ta Nemo juriya da qarfin Hali