Showing 51001 words to 54000 words out of 73969 words

Chapter 18 - BURI DAYA Hausa Novel

Mahmugee   

08 Oct 2024

20455

ace bazata sake somewa ko gama wannan tunanin batayiba idanuwanta suka sake lumshewa zata sume yayi saurin girgizata Yana cewa"

No no Not again please....

Ware idanuwanta tayi murya na rawa jikinta na daukar sabon mazarin tsoro da tashin hankali daqyar ta bude baki tace"

Ya...ya...yya yaaa...

Daga Mata Kai yayi tareda sake girgizata sbd ganin alamar Bata hayyacinta sbd tsoro Kuma kamar Bata Gama tabbarwa da shi din bane cikin wani irin yanayi yace"

It's me,nine I'm real ba fatalwa bane ban mutuba da Raina,
Ki dawo hayyacinki karki illata kanki nine da gaske ba wani gixo ba Ni din daine a gabanki......

Wani mugun yunquri tayi ta turasa baya tareda yin baya tana masa wani irin kallo idanuwanta jajir da fargaba tace"

Kana cewa baka mutuba Kaine Kaine,
Kana tunanin gwaninta kayi ko dadi zaka sani da fadar hakan??
Qwalqwalwata bazata iya daukaba,
Ciwon haukana dawowa zaiyi I'm only imagining this,,,,ya Allah karka Bari na sake dandanar ciwo da radadinda ke cikin hauka....

Ya Allah ka tayardani daga wannan mafarkin danakeyi....wlh I'm going insane....

Da qarfi ya damqota tareda girgiza ta da qarfi ya Kira sunanta sbd ganin yanda jikinta ke rawa sosai tana surutai da qarfi....

Qwacewa take sakeyi tana neman ihu da fixgewa ya sake riqeta Yana Kiran sunanta hankalinsa na tashi Saidai Sam batamasan yanayiba gabaki daya ta fice hayyacinta..

Jin zuciyarsa na neman karyewa da halinda tashiga yasashi rungumeta da qarfi cikin jikinsa tareda kwantarda kansa cikin wuyanta Yana Kiran sunanta da wata irin muryar sanyin jiki kamar zaiyi kuka sbd gab yakeda zaucewar shima matuqar wani Abu yasake samunta.

Tabbas yasan Dole zata gigita da ganinsa sbd ana maganar mutuwane,
Tasan ya rasu shekaru sama da biyar saikuma tagansa yanzu Kai tsaye Dole hankalinta zai tashi.

Yanda ya matseta a jikinsa Yana Kiran sunanta ahankali tun tana fixge fixge hartayi sanyi jikinta ya saki gabaki daya alamar ta sake somewa.

Lumshe ido yayi tareda girgiza kansa Yana tallafota gaba daya yasake maidata ya kwantar Yana mamakin yanda take somewa ita tunda can.

Wasu ruwan yasake shafa Mata
Tareda tsayawa bakin gadon yayi folding hannuwansa zuciyarsa duk a hargitse.

Ahankali tasake bude idanuwanta ta kafesa dasu wannan karon ko motsi kasawa tayi ta lumshe ido tasake budewa ta sauke masa
Take taji zuciyarta ta karye sbd yanzu Kam tabbas tasan shi din ne Babu maganar fatalwa kokuma hauka..

Wasu hawayen dataso ruqewane Suka gangaro ta gefen idonta sbd tasake tabbatarda da dai shi dinne Yana raye.


Kasa cewa komai tayi sbd wani mugun nauyi da dukkanin gabban jikinta suka dauka sbd mutuwar jikin data sameta,
Wani irin sanyi qasusuwan jikinta suke sake dauka akaro na farko a rayuwarta dataji zuciyarta ta toshe da wani irin nauyin gaske Wanda ya Hana bakinta budewa bare magana.

Fuskarsa take sake qarewa kallo,
Haskensa da kyawunsa na nan saima qaruwa dasukayi sbd hutu da Jin dadin daya samu,

Ahankali ta sauke kallonta a gefen wuyansa zuwa kunnensa na dama dasukayi duku tareda alamar qonuwa Wanda tabonta yakusa bacewa gabaki daya wasu sabbin hawaye suka silalo Mata.

Ahankali ta dafa ta tashi zaune tareda dauke idanuwanta daga kansa ta sauko gadon yanabin jikinta dake wani irin rawa a boye Wanda ya tabbatarda na ganinsane.

Fuskarta ya kalla yaga yanda yanayinta ya sauya sosai Babu wata rahama a fuskar tata saima hawayenta data share tana miqewa tsaye daidai agabansa.

Am in trouble""yafada tareda sake ajiyar zuciya ya matso zai kamo hannunta tayi baya ahankali batareda ta dago ta kallesaba ta juya zata fice ya riqe hannunta tareda dawo da ita baya zaiyi magana ta rigasa da qwace jikinta cikin qoqarin danne halinda take ciki tace"

Please Ina buqatan komawa inda ka daukoni.

Kallonta yayi da fararen idanuwansa tareda dawowa gabanta ya kalli fuskarta dake sunkuye yace"

Ina kike maganar komawa kenan???

Inda ka dauko ni Dilla's.

Sakinta yayi tareda mayarda fuskarsa yanda yasaba wato a tamke shima ba sauqi Kai tsaye yace"

Bazaki koma can ba infact ko Ina bazaki komaba Ni nasan inda zan kaiki.

Dagowa tayi wannan karon takasa riqe tarin baqin cikin dake cin zuciyarta kamar zata mutu tace"

Nace gida zankoma so inaga Banga wani dalili ko iko dakake dashiba na hanani besides karka manta satoni kayi Wanda Ni bansan manufarka akan hakan ba and inada damar dazansa a Kamaka akan hakan.

Idanuwansa ya zuba Mata cikeda yanayi na tsananin mamakinta akaro na farko dayaga zallar fushi Mai qarfi atareda ita.

Kina tunanin banda wani ikon hanaki kokuma kina tunanin Zaki iya sakawa a kamani din sbd kina taqama da me????

Cikin fushi tace"

Koma Dame nake taqama it's none of your business,
Kai me kake taqama dashi dazakazo bayan shekaru ka tsaya gabana bakaji kunyar Allah da tsoronsa ba na barin matarka dakayi da 'yan uwanka tsawon shekaru kana raye baka nemesu ba,baka dawo garesu ba,
Bakasan irin halinda suka shigaba sbd rashinka,
Bakasan ya rayuwa tayi musu tsanani ba sbd Babu kai....rawa muryarta tafara Yi hawaye na ciko idanuwanta tace"

Dama basuda mahimmanci da wani matsayi a rayuwarkane daka zabi barinsu Babu waiwaye kokuwa dama lokacine ka dibar musu a rayuwarka,

Meye laifina Dana mahaifina daya bakani ko kuwa munzama takurane a rayuwarka????

Meye laifin babana Dani kaina???
Idan duk munada laifi damuka zabeka fiyeda kowa meye laifin baby z ita????

Sai alokacin ya matsota sosai Yana kallonta da idanuwansa dasuka rikide ja sosai ya daga hannu zai kamota tasake ja Baya cikin daga murya tace"

Enough..enough Mr haydar,,,ka daina kusantoni da yawa sbd haryanzu ban manta da darajataba ta 'ya mace Kuma musulma....

Ba zato ya jawoto jikinsa ya matse tareda zuba Mata jajayen idanuwansa jikinsa na rawa sbd bacin ran zancenta yace"

Shi wancan da kike tare dashi a gidansu shi musuluncin Bai hau kansa bane????
Wlh bazaki sake zama a gidanba idan Kuma kinason kwada qarfin ikon danake dashi ne akanki da rayuwarki ki gwada zakisha mamakina sbd inanan bawai canzawa nayiba.....


Fixgewa tayi itama cikin Hana kukanta zuwa tace"

Bana magana akan rayuwar kowa da canzawar kowa anan Ina magana akan rayuwatane da abinda Naga damar Yi da Wanda Naga damar bari,
Idan kana maganar baka canza ba to Ni na canza ba Nadiya bace wannan ND NOAH ce...and stay the hell out of my life.....

And bana buqatar ganin qarfin iko ko dukiyan dakake dashi sbd dama Abu ne nasa kaina sbd tunanin anrabani da abinda nakeso fiyeda tawa rayuwar Ashe bansaniba shine ya rabu Dani Dan haka Ni kaina daga yau na fita daga fadanda Babu ruwana zanje na fuskanci Wainda suka cancanci qaunata da lokacina.

Tana Gama fadar hakan ta fice da gudu sbd wani irin kuka Mai tsananin nauyi da qarfi dakeson zuwan Mata tana dannesa numfashinta har sarkewa yakeyi jikinta Babu inda baya rawa.

Kasa motsi yayi sbd duk jijiyoyin jikinsa sun daure da mamakinta da fargabar tashin hankalin maganganunta dake bayyanarda tsantsar radadin baqin cikin barinta datake ganin yayi.

Securities Basu wani hanata fitaba tana fita ta tari wata taxi data kawo ta fada kawai sai alokacin tasake wani irin kuka Mai tsananin cin Rai da damuwa tareda ciwon abin datake ji cikin ranta.

Har Sukayi nisa Bata saniba Saida yasake tambayar inda zai kaita ta bude baki daqyar tareda fada masa tana share hawayenta tareda qoqarin barin kukan duk da tasan bazata iya barinba.

Yana Isa qofar mansion din ta fito ahankali tareda ce masa ya jirata tafito.

Ciki tayi tana qoqarin maida kukan dayake sake taso Mata sbd fammah data hango tsaye jikin qofa tana knocking qofar side din am tana kuka sosai kamar zata shide.

Kasa riqe nata itama tayi tasakesa tareda wucewa ciki da gudu tanajin inama duk shekarun nan a gaban babanta ta zauna tayisu da tabbas bazata cutatu yanda takejin ta cutatu yanzu ba.

Sama ta haye tahau hada duk wasu kayanta tafara jawo luggage dinta tana share hawayenta dasuka qi tsayawa a Palo taci Karo da am da fammah tsaye dukkaninsu Babu Wanda baibata tausayiba take zuciyarta tasake karyewa ta silalo hawaye masu radadi ta rintse idanuwanta ta bude saitaji takasa kallon fammah ga am da zuba Mata idanuwansa dasuka shanye sukai jajir a dare guda ya lalace yakoma tamkar asalin Dan giyar dayayi shekaru ashirin Yana sha,
Hawaye ne cike da idanuwansa Saidai Basu saukoba sbd muguwar karayarda zuciyarsa da gangar jikinsa suke ciki,

bude baki tayi daqyar ta furta"

I'm leaving......

Ba zato qafafuwansa Suka sare ya zube gabanta tareda riqo qafafuwanta cikin wani irin yanayi na kuka da tausayi yace"

Baby Dan allah karki barni wlh bazan iya rayuwa Babu keba,
I can't live or survive without you,
Karki tafi kibarni a wannan halin I will die if you leave me.... please baby idan na Miki wani laifi ne forgive me Dan Allah please baby don't leave.....

Kuka tasake sbd akaro na farko daya fara Bata tausayi musamman yanda fammah ke jansa tanason tayar dashi cikin tsananin kuka Yana kwacewa Yana surutai da kuka sosai..

Cikin tsananin kuka itama ta janye qafafuwanta ta ja Baya yayi saurin rarrafowa Yana wata irin magiya gabaki daya baya cikin hayyacinsa.

Cikin tsananin kuka fammah itama ta zube gefen Dan uwanta ta dago ta kalli nadey din tana kuka tace"

Dan Allah Ina roqonki daki rausayawa rayuwata ki tallafi Dan uwana dashine kadai ya ragemin a yanxu,

Bansan wane sirrine yake boye a tattareda saninki da familynaba Amma Dan Allah kiji tausayin maraicina ki tallafi Wanda zai tallafi tawa rayuwar.....

Girgiza Mata Kai nadey tayi hawayenta na sake gudu ahankali ta furta"

I'm really sorry fammah...

Tana fadar haka ta fice da sauri tana sakin siririn kuka tana jiyo ihun fammah na Kiran sunansa Amma Bata tsayaba sbd zuciyarta data fara karyewa alhalin itama tallafin take buqata a tata kuncin Wanda zuwanta gaban mahaifintane kawai zai yaye matashi.


Taxi din tashiga sukabar gurin.
Direct gidansu Annah yakaita canma Basu gane kantaba tana Shiga ta tattara sauran kayanta suna tayata hada kayanta data kasa hakuri anan ne tasaki kukanta Mai qarfi datake riqewa mum din Annah da Annah na gefenta Suka Bata damar tayi kukan duk dake cikin ranta kozataji sauqin zuciyarta.

Sosai tayi kukanta saidataji sauqin nauyin datakeji a qirjinta kafin ta shiga toilet tayo wanka tana fitowa takira JJ da wayan annah ta shirya cikin skinny jeans fari da farar loose chiffon top ta Dora black full-length jacket da black scarf ta fito da kayanta daidai isowar JJ kallo daya yamata yaji nauyin zuciyarsa ya qaru sbd idanuwanta dasuke a kumbure musamman data gansa sai idanuwanta suka sake cikowa da hawaye tun kafin yayi magana ahankali da rawar murya ta furta"

Dady j I can't handle this anymore,,,inason ganin babana Dan haka it's time for me to go home....

Da sauri ya qaraso gabanta cikeda kulawa Yana cewa"

Baby please karki dagamin hankali tell me yafaru?
Meya sameki?
Waye ya daukeki?
Ina ya kaiki?
Meya Miki?

And....and..fuskar Wanda ya daukeki Dana gani was it re.....

Yes dady j shine,Yana nan da ransa Bai mutu ba Muna wahalarda rayuwarmune akan Wanda baisan munayi ba....

Da manyan idanuwansa yake kallonta ko qyaftawa yakasa Yi shima duk jarumtarsa zuciyarsa bugawa takeyi sosai sbd kukuwar yarda da zancen,

Girgiza kansa yakeyi tareda juyawa da qarfi ya daki iska Yana sake girgiza Kai sbd wannan zancen ya girmi tunaninsa Kai tsaye Rana tsaka ace Wai sarki Bai mutu ba,
To meyesa ya boye musu kansa???
Idanma Bai nemi kowaba shi Bai kamata yakasa nemansaba qarin abin tashin hankalin shine suna taredashi Bai sanarmusuba Kai this is so confusing.

Wani murmushin takaici tasaki tace"

Shall we???

Dago jajayen idanuwansa yayi ya kalleta yaga yanda fuskarta tayi jajir ta kumbura take yaji ransa yaqara baci Saidai shikam yau zasuyi face to face da sarki yau zasuyi magana as man to man.

Direct airport yakaita Babu me magana acikinsu harsuka karbi tickets ta juyo ta kallesa zatayi magana shima daqyar yarigata da cewa"

Karki damu yau zuwa gobe zamu Gama claiming komai a gobe zaa buga sunayen Noah's a kamfaninsu da mansion dinsu da angama zandawo jibi insha Allah.

Jinjina masa Kai tayi tareda juyawa ta shige shikuma ya koma.

Bata fi mintuna ashirin ba aka Kira flight dinsu ta tashi ta shige.

Yamma sosai ta Isa starling city dad da kansa yazo daukarta sbd yayi wata da JJ yafada masa komai dake faruwa gameda haydar.

Ji yayi duk duniya farin cikinsa yadawo Sam kasa boye farin cikinsa yakeyi tuni labarin yafara yaduwa a cikin abokanan mu'amalarsu ta business har zancen yafara fita.

Duk murnarsa raguwa tayi dayaga halinda nadey ke ciki yafara qoqarin danne murnarsa da farin cikinsa Yana duba yanayinta itama sbd tabbas wannan abin abun dubawa ne ga miji yabar matarsa tsawon shekaru Babu waiwaye.

Da gudu baby z tazo ta rungumeta itama cikin tsananin kewa da soyayyar 'yarta ta rungumeta tareda rintse ido hawaye na silalo Mata.

Nanny Nancy ma rungumeta tayi cikin kewarta dasukayi suka shige har dakinta har lokacin baby z na maqale a jikinta itama Sam takasa sakin 'yarta.

Wanka tayi tayi sallah tana qoqarin danne komai tasake dasu Suka hau labarai dad ma sakewa tayi taqara masa bayanin halinda ake ciki gameda mansion dinsu Dilla data siye harda na Nigeria and dad Insha Allah I will be going back to Nigeria next week zanji da maganar claiming takardunsu na can da muka karba.

Kallonta yayi cikin farin cikin ganin Bata wani dauki abin da zafi ba yace"

Ok allah yakaimu Saidai idan kinje ku zauna gidan Dr sayyid tunda nasan za'ayi renovating gidan Yaya dattiya ne sbd nasan no matter what Yaya bazai iya barin anguwar nan ba.

Murmushi tasaki ahankali sbd tuno irin burikan babanta musamman na zama sarkin maroqa.


Da daddare da 'yarta ta kwana bayan tayi waya da JJ.


JJ kuwa daga airport gida ya wuce ya shiryo cikin wasu irin suits yasa aka Kira media akan yaune zaa karbi sunan dazaiyi replacing dillas Wanda yakeson acan ne zai fuskanci sarki
Sarki ya fuskancesa.
#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee37_*
Cikin gaggawa fammah tafara ihun Kiran sunayen masu aikin gidan Suka fito amatuqar rikice a gigice take cewa su kirawo Mata Dr kar am ya mutu ya barta.
Aikuwa amatuqar gigicen Suka fara neman wayar Kiran Dr din daqyar Suka samu tashiga Yana dauka Suka sanar dashi yace gashinan zuwa.

Da kanta ta kamashi tareda taimakon su Jenna Suka kaisa bedroom din mum dinsu dake kusadana dad.

Kasa zama tayi takasa tsayuwa tana kaida kawo cikin tsananin tsoro da tashin hankali.

Kafin zuwan Dr hankalinta yakai qololuwa gurin tashi sbd dad dinsu daya farfado adaidai wannan lokacin shima Saidai basusan ya zasuyi masa su rabasa da oxygen dinda ke maqale a fuskarsaba.

Gaban dad din ta zauna tareda riqo hannunsa cikin tsananin farin cikin farfadowarsa tana Kuma hawayen kwantawar Dan uwanta.

Isowar Dr ce tasa tayi saurin miqewa ta basa guri yafara zare oxygen din dad Yana yabawa da yanda ya farfado lokaci daya kafin ya juya gurin am dake buqatar taimako yahau dubasa.

Sosai ya dubasa tareda dubarunsu na likitoci saigashi ya bude idanuwansa dasukai jajir Yana qoqarin tashi fammah da Dr na dafesa cikin kulawa Dr yace masa Yana buqatar hutu a yanxu.

Wani irin wahalallen kuka ya sake tareda qanqame hannun fammah dake kuka tuni yace"

Fammah meye laifina????
Meye laifina danake Mata mugun so irin wannan??
Fammah kinsan radadi da ciwon danake ji a zuciyata sbd ta tafi ta barni??
Ciwo nakeji anan sosai"""yafada Yana dafe qirjinsa dake masa tsananin ciwo musamman sbd alcohol dinda dayasha sbd Sam baya Sha baima taba  shaba.

Ahankali fammah ta rungumesa tareda lumshe ido hawayenta na sake gudu sbd batamasan mezata iya cewa ba.

Bayan tafiyar Dr gurin dad dinsu Suka tafi acan Suka zauna tasa aka kawo Mata abinci Mara nauyi ita tayi feeding dinsu su biyun tabawa kowannensu magani anan Suka koma bacci tare ta miqe ta kashe musu aircon ta fita.

Dakinta taje ta tube tayi wanka daqyar tayo alwala tazo tayi Sallah Wanda zamanta da nadey ne tasan tayi sallah akan lokaci Kuma duk lokaci idan yayi sbd itadai bazata iya tuna lokacinda iyayenta Suka taba cewa tayi sallah ba kokuma idan tayi shiyasa so da dama idan tayi to wani lokacin Kuma idan lokaci ya wuce shikenan saikuma gobe Amma zama da nadey tun tana basarwa harta fara Jin kunyar nadey na sallah itama musulma kamarta Bata cikayiba sai hakan yasa tafara dagewa tanayi cikin lokacin Kuma ko yaushe,
Tun abin na gasane hartazo tasaba ko nadey na gida ko batanan idan lokacin sallah yayi yin sallarta takeyi.

Tana Gama sallar ta duba agogo taga dare yayi sosai saitayi kwanciyarta agurin tana tunanin yanda rayuwa ta juya musu baya lokaci qanqani.


Washe gari tunda safe abinda yafara yaduwa a gidajen tv da jaridu shine makeken sunan NOAH'S PUBLICATIONS daya bayyana baro baro a saman makeken kamfanin dillas dakuma qaton mansion dinsu suna ciki basusan ancire sunansuba ansa Noah's.

A tv Suka fara gani da safen Dilla yayi zuru ya qurawa tv ido sbd balain dayake ciki yafi qarfin magana sbd mamakinsa akan kenan nadey Noah duk sune su JJ tazo ta yaudaresu sun karbe musu komai.

Am kuwa wasu irin hawaye ne ke gangarowa daga idanuwansa jikinsa na wani irin rawa ahankali fammah tasake qanqame hannuwansu su duka biyun sbd tana zaune ne a tsakiyansu.

Babban tashin hankalinsu shine inda zasu zauna sbd yau Dole zasu bar gidan gashi kayan jikinka kawai kake fita dashi.

Cikin wani irin yanayi na sanyi da tsananin damuwa Dilla ya kalli fammah zaiyi mgn ta miqe da gudu tabar gurin tana kuka.

Dakinta taje ta hada kayanta cikin akwati guda da duk abinda yakeda amfani da mahimmanci agareta.

Daga nan dakin dad taje shima ta hada masa komai a akwati daya hakama mum tayi Mata akwati daya ta jawosu ta fiddo dasu ta nufi dakin am shima ta ha'do masa nasa takawo palon tana kallon yanda am ke kuka sosai cikin baqin ciki da radadin da zuciyarsa ke ciki.

Dad ma daka kallesa kasan kowane irin lokaci zuciyarsa na gap da bugawa.

Passports dinsu ta fitar ta dauki wayarta ta fita harabar gidan takira tayi musu booking tickets din Daren yau dazai tashi zuwa Nigeria.

Dawowa tayi ta zauna tsakiyarsu tareda sakin murmushi Mai ciwo ahankali tace"

Wannan wata jarabawace daga ubangiji mu karbeta da hannu bibbiyu insha Allah it will pass.


Suna nan zaune jigum jigum akazo Basu tunin lokacin fitarsu gidan yayi fammah ta riqo dad da har lokacin baida wani kuzari suka fito am kuwa idanuwansa sunyi jajir ko dagowa ya kalli tarin media dake gurin baiyiba Suka fito mansion din sai daukarsu hoto akeyi.

Black anaconda fc din haydar ce ta Sha gabansu tareda motar police biyu a bayansa.

Cikin wasu black Armani wears yafito motar fuskarsa sanyeda Benz dark shades ya qaraso gabansu ya tsaya daga gefen JJ dashima yake tsaye gabansu cikin Gucci's.

Kallo daya Dilla yamusu

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login