Showing 39001 words to 42000 words out of 73969 words
lokacin Yana wata shida.
Sannu ahankali dad ya warwarewa JJ dukkanin sirrin dukiyarsa da rayuwarsa tareda dorasa akai duk da dai komai NASA yariga ya yanke shawarar sunan Nadiya da abinda ta Haifa zaa saka dukiyarsa kaf yace tasuce tunda sune Abu mafi soyuwa a rayuwar Zaki.
Sosai rayuwar JJ tafara canjawa musamman da dad din yasa aka ware masa wani program na classes dayake zuwa dauka na degree dakuma na aikin kakin soldier na shekaru biyu dazaiyi yagama.
Yawan geaming dinda yakeyi saiya fara bude jikinsa ahankali yafara zama wani qaqqarfan najimi gashi yanzu wani irin hutu da dukiya sun fara ratsashi musamman dayake dad din baiwani jin hausa sosai tunda asalinsa ga yanda yake Kuma yadawo nan din.
Duk wata tare suke zuwa dubo Nadiya Amsterdam suyi kamar kwana hudu kafin sudawo sbd dr sayyid tuni ya mayarda hankali kan fannin asibitoci da kamfunan magungunan NOAH.
Lokacinda Nadiya tashiga 9month dinta alokacin ne Suka dawo Amsterdam dukkaninsu harda Dr sayyid Wanda bai wani Jima da dawowa daga Nigeria ba sbd dubo alqawarinda yayiwa Zaki tuntuni na kulada familynsa Saidai Bai fadawa kowa yajeba.
Two weeks after labour yazo Mata inda hankalin asibitin yayi mummunan tashi sbd tun Daren jiyan take fama da labor gashi sbd mental problem dinta yasa ihun azaba takeyi sosai Bata wani iya daurewa tunda batasan metake yiba.,
Ganin abin yafara fita out of their control yasa sukai transferring dinta to wani babban asibitin su dad Suka kwasa sukai can Babu Mai nutsuwa.
Da isarsu aka shiga labor theatre da ita sbd bazata iya haihuwa da kantaba gashi tayi weak sosai.
Lokacinda dad yasa hannu a takardar tiyatar Saida JJ yariqe hannunsa sbd yanda yake rawa cikin sanyi da dauriya yace"
Dad insha Allah lafiya zata fito.
Daga masa Kai dad din yayi Yana murmushin qarfin Hali da jarumta.
Har dare suna zaman jiran sai qarfe bakwai nurse biyu Suka fito cikin farin ciki dayar tace"
Congratulations Congressman.
Dayar ce ta karbe zancen da cewa"
It a baby girl sir.
Hamdala suka sake dukkaninsu tare cikin farin ciki dad yace"
Thank you for this wonderful news ladies.
Fitowar doctors ne yasa dad kallonsu Yana cewa"
Dr hw about the mother????
Kallonsa Dr Allen yayi ya jinjina masa Kai suka nufi office Yana sake karanto masa reports dinta dasuke saka ran tadawo normal daga mental issues dinta.
Lokacinda JJ yadauki babyn wani irin murmushin farin ciki tareda hawaye yakeyi yanajin tsananin qaunar yarinyar ya Dan shafi fuskarta dake yanayi data babanta ahankali Yana murmushi hawayensa na qaruwa.
Dan motsawa yarinyar tayi Hana 'dan turo harshe cikin tsananin farin ciki ya furta"
Zainab baby.
Dad dake bayansa sukaji yace"
Harkawa 'yarku huduba kenan.???
Qarasowa yayi ya karbi babyn shima yayi Mata addua Dr sayyid ma yayi nurse tazo ta karbeta ta mayarda ita gadonta dake kusadana mamanta da Bata farfadoba.
#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_
*08030811300*
*07067124863*
*_Mamuhgee27_*
Kwana biyu da haihuwarta taji sauqi sosai Saidai har lokacin Bata yiwa kowa magana sai shiru datakeyi hawaye na fita idanuwanta musamman da dad ya gabatar Mata da kansa dakuma matsayinsa na uba ga mijinta Kuma kakan 'yarta baby z.
Ranarda aka sallamosu Suka koma asibitinta na psychiatric Suma Suka gama nasu binciken Suka sallameta Suka dawo starling city anan Suka tararda Nanny's da qarin sabbin masu kulada gidan da ita kanta nadiyar.
Wani tangamemen hoton Zaki ne na zane dake facing duk Wanda yashigo makeken polon Wanda masu zanen Suka samoshi sosai kamar shi din ne aka dauka.
Tsayawa tayi cak tareda qurawa hoton ido tanason riqe kukan daya danne qirjinta tsawon watanni ta sakesa da qarfi tareda durqushewa gurin komai nasake dawo Mata sabo
Kunnuwanta na dauko Mata qarar sautin kuka da magiyar iyayenta tareda qarar bindigar Daren da abin yarafu dakuma qonanniyar gawar mutum mafi soyuwa a rayuwarta dake dawo Mata a ido.
Nanny Nancy ce tayi saurin riqota tana durqusawa gabanta cikeda tausayinta duk da batasan meye damuwarta ba Amma yanayinta ya nuna tsananin quncin da zuciyarta ke ciki.
Dad da JJ ma duk jikinsu sanyi yayi sbd ita yanzune data dawo daidai takejin komai yadawo Mata sabo musamman idan takalli maraicinda yarta zata taso dashi na Rashin uba.
Cikin sanyi dad yace nanny Nancy tayi ciki da ita.
Wani tangamemen dakin dayafi kowanne kayan qyale qyale da haduwa aka kaita inda aka zuba komai sabo na baby z Dana nadiyar tundaga situru da abubuwan buqata na gyara.
Bakin gado ta zaunar da ita tareda kwantar da baby z cikin gadonta ta fice.
Kuka takeyi sosai tanajin wani irin zafi da radadi na qona zuciyarta inda takejin wata irin tsana da qiyayyar familyn dikko Dilla musamman am datake gani a idonta lokacinda ya buge babanta yaja zainab cikin daki ya harbeta.
Cukuikuye jikinta tayi sbd tsananin abinda takeji na wutar tsanarsa dake ruruwa a jininta taci gaba da kuka.
Yini guda a dakin tayisa Bata fitoba tun shigarta gashi daga dad din har JJ Babu Wanda yayi yunqurin shiga dakinta Dan karsu takurata.
Su nanny da masu aikine keta hidimar kulada gidan da baby z sukuma su dad suna can sun maida hankali kan business dinsu.
Washe gari ma Bata fitoba a daki ta wuni kwance idanuwanta sunyi zuru zuru sbd Rashin bacci da tunani.
Sannu ahankali lokacin yafara tafiya har baby z tafara girma takai wata hudu cikin na biyar sosai nanny Nancy ke kulada ita musamman ta bangaren Bata madararta sbd nonon Sam baida wani ruwa sai kawai Suka maida himma gurin Bata Madara.
Duk yanda taso yakice abinda ke rura wutar qiyayyarta saitaji takasa sosai takejin batada sukunin zuciya Dana jiki akan irin kisarda akaiwa mijinta da 'yar uwarta tareda iyayenta,
Abu daya tasani shine bazata taba hutawaba saita biwa 'yar uwarta da mijinta haqqin ransu,
Dole za'a bawa matarda aka kashewa miji justice hakama uwar da aka kashewa ya agabanta.,
Babban abinda yafi azalzala wutar zuciyarta shine yanda ta haukace taso a maidata gurin iyayenta Amma dad ya Hana tareda fahimtar da ita matuqar tanason babanta tanason lafiyarsa ta nesanta kanta dasu yanxu sbd bayyanarta hadarine ga iyayenta dakuma 'yarta.
Akaro na farko dataji tana tsananin sha'awa da buqatar karatu Mai tsananin zurfi a rayuwarta sbd da shine kawai zata iya fuskantar Wanda yayi ajalin mijinta wato AM DILLA.
Sakin jikinta tafarayi ahankali tana koyan turanci sosai gurin nanny Nancy tareda wasu abubuwan.
Dad ma ganin tasaki jiki sosai lokaci guda sai abin yabasa mamaki Amma yaji dadi sosai musamman yanda tafara sakewa dashi Saidai yanayin zafinta yakan bawa JJ tsoro da mamaki sanin ita din Mai tsananin sanyi ce.
Dad da kansa yasa aka dauko Mata wani Dr Marshall Yana koyar da ita karatu da wasu hanyoyin business sbd shi arayuwarsa komai business ne,
Shi kansa babu abinda yakeso kamar nadiyar tazama independnt business woman dazata jagoranci _NOAH EMPIRE_ nan bada dadewaba.
Ahankali baby z tayi wayo zuwa lokacin Nadiya harta sauya sosai sbd yanda nanny Nancy take matuqar kulada cimarta sbd Sam tace Mata batason tayi jiki.
Rashin fitarta yasa fatarta tayi mugun canzawa musamman dayake cikin masu musu aiki akwai Becca wadda Tai aiki wani babban beauty parlor ita ke sake kulada skin din nadiyar ta bangaren abubuwan datake amfani Wainda suka mugun karbar brown skin dinta.
Baby z nada shekara daya admission dinda dad ya nemarwa Nadiya a university of Toronto Canada yafito dayake duk a shirye suke Babu Bata lokaci ta wuce aka bar baby z agurin nanny Nancy da sabuwar nannyn da aka qaro Mata musulma daga qasar Libya sbd kulada bangaren tarbiyan addininta musamman dayake tafi sabawa da nnany nancy da dad said JJ datakewa kallon shine mahaifinta.
Babban Abu na farko da Nadiya ta mayarda hankali akansa bayan karatunta shine shiga harkar tsadaddiyar rayuwa sosai sbd tanason ta iya komai,komai ya zauna arayuwarta da jikinta tareda dabiarta sbd ta hakanne zata samu cikar burinsu daya zamo daya itada dad 'dinta da JJ.
Sosai take karatu musamman da rayuwarta ta sauya cikin shekara daya da fara karatun tuni ta sauya komai ta koma tamkar haihuwar turawa rayuwarsu ta shigeta ta bangare daya dad ma ya dage sosai yake sakata a harkar business tun Bata ganewa harya shigeta tana gane business sosai.
JJ ma yagama karatunsa yanzu yafi maida hankalinsa akan harkar training dinsa dakuma business din sosai sbd shine abinda dad yafison yashigesu.
So biyu kawai tazo starling city hutu tunda tadawo Canada din Saidai kusan kullum tana video call dasu nanny da baby z shi dad kusan Yana yawan zuwa kokuma idan yace tasamesa wata qasar Akan harkar business.,
Shikuwa JJ dama kusan duk yasamu time Yana hanyar zuwa Canada din gurinta.
N.D NOAH take amfani dashi a dukkanin takardunta da passports dinta tareda duk wani id card dinta ma'ana Nadiya dattiya Noah.
Yawanci friends dinta turawa sukan kirata da nadey Noah.
Ahankali karatunta yayi nisa harta kai shekarar qarshe Saidai zuwa gabaki daya rayuwarta da ita sunyi nisa da hannun riga da rayuwarta ta dah.
Bazaka taba kallon shape da zubin slimmy figure dinta kace ta taba daukan ciki bama bare haihuwa,
Skin dinta yatashi daga brown yakoma tamkar na half-caste ko black Americans sbd tsabar hutu da kyawun tareda tsadar products dinda take amfani dasu,
Sam ta manta when last ta zauna da wani tayi yarenta na hausa sbd dama dad ne shima Bai wani cika hausaba tunda dama ba tarensa bace,
Sai JJ shima turai tashigesa sosai Sam sai can suke hausa a tsakaninsu kokuma baby z dasukewa sbd ta 'dan iya.
Duk wani motsi da tarihin Dilla's suna sane dashi a tafin hannunsu yake yanzu zasu fara nasu wasan THE NOAH'S sbd shima JJ JABEER HAYDAR NOAH yake amfani dashi.
Shekara hudu cikin ta biyar cif ta Gama kammala first and second degree dinta a fannin business da harkar modeling fashion.
Ranarda ta sauka us a ranar cikin dare dad dinta ya hada wani gagarumin taron dinner inda ya bayyanarda ita a matsayin owner NOAH'S EMPIRE.
sosai Yan press Suka dinga daukarta hotuna suna Mata tambayoyi inda ta ringa Basu amsa cikin wani irin yanayin daya ringa rikita zuciyar manyan abokanan business din dad dinta da 'yayansu tun anan wasu Suka fara miqa business offer dinsu sbd duk wata suffar daukar hankalin 'da namiji tagama hadasu atare da ita musamman dinner gown dinta black Mai tsegen kyau dake daukar idon mutane sbd stones da Kuma kyawunta dake kashe musu ido.
Washe gari da qyar ta bude manyan idanuwanta dasukai laushi sbd bacci ta lalubo alarm dinda ke gefen gadonta Yana kuka ta kashe tana sake komawa cikin bargon.
Qarar wayarta yasata Jan qaramin tsaki tareda lalubo wayar ta dauka batareda ta duba ba tace"
Yes please.
Cikin yanayi na farin ciki JJ yace"
Nadey come downstairs now,you need to see this.
Bude idanuwanta tayi da sauri tana cewa"
Am coming.
Saukowa gadon tayi tareda zura bedroom slippers dinta na gashi masu tsananin laushi ta fito tana Kama gashinta bayan ta saka jacket saman kayan baccinta.
Palon ta qarasa saukowa tana kallon tvn dasuke kallo
Take zuciyarta tayi wani irin nauyi ta tsaya tana kallon yanda aketa baza labarai da sunanta ana nunota Saidai sunason ganin ainihin dad dinta Wanda bai taba Bari Yan press sunyi fira dashiba ko daukar hotunansa.
Karbar coffee dinda nanny Nancy takawo musu tayi tafara kurba tana kallon tvn yanda zancen ya baza duniya Yana sanyata nishadi sbd irin zallar dukiyarsu da ake fada tasan duk inda dillas suke yanxu ido rufe nemanta zasu fara Dan hada business da ita Wanda shine first target dama.
Murmushi tayi batareda ta dauke idonta daga tv ba tace"
Am Dilla I'm coming for you.
Aje cup din tayi tareda kallon JJ tana miqewa tace"
Bari naje Naga dad inason magana dashi.
Sun Jima sosai suna magana akan proposals dasuka samu da dama tsakanin jiya zuwa safiyar yau din Wanda Dole JJ ne zaiyi handling rabi ita zataji da sauran sbd dad din kwana biyu Yana fama da Dan nauyin jikin manyanci.
Cikin wata black BMW ta iso Noah's cikin wasu maroon pensil suit na Mata dasuka matuqar fiddo shape dinta sai wasu shegun heels black da black mk bag dinta tashigo companin tana waya da best friend dinta Annah Lauren.
Dukkanin ma'aikatan tasowa sukeyi suna Mata barka da zuwa su pa dinta da wasu ma'aikatan na biyeda ita har bakin office dinta inda aka rubuta CEO PA dinta ta bude Mata tashige.
Aiki tayi sosai tareda meeting harso biyu sbd yawan aikinma yasa sai dare tasamu damar dawowa gida lookacin baby zee tayi bacci Saidai kawai tayi wanka tasha fruits ta kwanta sbd batacin Abu Mai nauyi da daddare.
Washe gari ma a office ta wuni kusan yamma Annah tazo ta dauketa sukaje wani spa dagacan sai dare Suka dawo gida.
Ayyuka sunmata yawa sosai shiyasa gabaki daya she's busy ko lokacin zuwa yawon shaqatawa dasuke da Annah ta rage samu sosai.
Yauma JJ ne yaje ya daukota suka dawo gida.
Babban abinda yafara tunkarosu batareda sun samu proposal daga Dilla empire ba shine bullowar wani kamfani daya dame nasu akan dukiya da suna Wanda a iya bincikenta kamfanin duka duka baifi shekara uku da fitowa ba Amma Yana neman take nasu dayayi shekaru masu yawa.
Tension yayi Mata yawa sosai musamman safiyar yau dataga jaridar wani sati kamfanin zasuyi bikin bude kamfaninsu dake South Africa.
Sake kallon jaridar tayi ta miqawa JJ tareda miqewa tana zuwa bakin glass wall din dake office din Bata tana kallon qasan harabar kamfanin cikin tsananin damuwa tace"
Idan muka rasa wainnan proposals din rugujewa zamuyi sbd dukkanin ribar shekaru muka zuba a wannan karon sbd kawai mukira attention din dillas da yawan proposals namu Amma out of no where wannan kamfanin yazo yasha gabanmu
who the hell is this *_HAYDAR'S BUILDINGS LMT_* ????
dafe goshinta tayi tana jinjina irin hasarar dazasuyi idan Basu samu open contract proposal ba Mai tsananin tsoka.
Qarasawo bayanta JJ yayi ya tsaya tareda zuba hannuwansa cikin wandon ash suit dinda ke jikinsa cikin taushin muryar lallashi yace"
Heyy don't stress your self akan Dan wannan issue din, we'll find a way bazamu taba Bari wannan company ya rusheba okk??? So please just calm down kinji?
Kallonsa tayi tareda Dan daga masa Kai batareda damuwar tasaketaba.
Kallonsa tayi tareda nufar kujerarta ta zauna tana rufe apple laptop dindake kunne gefen flatscreem APPL desktop din office din tana cewa"
Dole zanbi flight din chicago gobe Ina buqatar ganawa da wannan haydars buildings din Bari ma naje nafadawa dad akwai wani conference meeting dazanyi da wani sabon company dasuma haydars din zasuyi meeting dasu inason mu hade acan ina buqatar magana da CEO na wannan haydars buildings din kota yayane.
#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_
*08030811300*
*07067124863*
_Mamuhgee31_
Da sauri tasake bin hannunsa daya janye daga nata dukkanin fuskarsa na bayyanarda wani boyayyan murmushinda yasake jefa kowa cikin mamakin abinda yafaru.
Fammah ce tasaki murmushi tana cewa"
Everybody just chill nadey and haydars are business partners I think so please let's all sit and talk about me and my haydar.
Dukkaninsu ajiyar zuciya suka sake a boye musamman zeel da dad din data fara shakkar kar 'daya daga cikin 'yayanta su rasa wainnan biyun.
Zama duk Sukayi ta dago qafafuwanta dasukai sanyi ta zauna kusada am tana qaqalo masa murmushin dole dako gama fitowa baiyiba.
Dagowa tayi ahankali lokacinda am ke gabatar masa da ita amatsayin wadda zai aura ta kallesa idanuwansu suka shiga cikin na juna sbd yanda ya xuba matasu ko qwaqwaran motsi kasawa tayi atake ta sarqe tafara tari ahankali.
Da sauri am ya dauki ruwa ya Bata Yana Mata sannu cikin kulawa Saidai tana saka ruwan bakinta ta qarasa sarqewa sbd azabar dayake Bata da idanuwan nasa Dan har lokacin ko qyaftasu daga kanta baiyiba saima wani irin ja dataga sunayi
Take tsoro da fargaba suke neman shigarta ta miqe da sauri tareda cewa"
Excuse me daqyar tana tari ta nufi stairs da sauri ta haye.
Miqewa am yayi zaibi bayanta haydar yayi qyaran murya tareda cewa"
Ya dawo su Gama gaisawa Mana.
Dawowa yayi Suka cigaba da 'yar fira Saidai dukkaninsu hankalinsu na saman musamman haydar da tuni idanuwansa suka sake rinewa ya miqe batareda yaqara wani lokaciba yace zai tafi.
Duk yanda fammah tayi masa magiyar ya tsaya suyi dinner
Qarshema yanayinsa ya Bata tsoro tayi saurin tsuke baki ta rakasa mota ko qarasowa batayiba ya fice ya barta tsaye.
Hawaye taji sun ciko idanuwanta tana tsaye taji suna neman sauko Mata.,
Meyasa haydar baitaba nuna Mata kulawa ko so ba?
Meyasa tunda ta hadu dashi a airport Zurich take mutuwar sonsa tana bibiyarsa Yana wulaqanta rayuwarta.
Dafata taji anyi tana juyowa taga am tayi saurin fadawa jikinsa tareda sakin kukanta datake dannewa.
Shima jikinsa sanyaye yake sbd yaje yayi knocking qofa kamar me nadey taqi budewa tamayi kamar Bata jisaba.
Ita kuwa nadey hakanan taji hankalinta yayi matuqar tashi tarasa Ina zata saka kanta wani irin shakkar idanuwan wannan haydar din takeji ta rasa meke Mata daidai sai kawai ta zauna bakin gado hawayenda batasan Kona meyeba suna sauko mata.
Tabbas idan har tanason gujewa wannan fargabar koma ta meyene to Dole tayi tagama abinda yakawota tabar nan musamman yanxu da JJ yafara damuwa da maganarta dashi sbd kar wani Abu ya gifta musu ita kuwa idan Koda auren am ne ke nufin kawo qarshensu a shirye take da hakan,
Saita tarwatsa rayuwarsu ta yanda bata taba haduwa zata bar gidan.
Daqyar ta tashi tayi sallah tayi wani wankan tasaka doguwar Pakistani gown ta sauko lokacin dinner Sukayi dinner Yan gidan nata farin ciki da murnar zuwan haydar din.
Itadai Bata tsaya wani dogon firaba tana gamawa ta haye Suka bita da sannu cikin kulawa.
Washe gari tana tashi ta shirya cikin blue skinny jean da white loose lace chiffon half top tayi rolling din gefe da wata qaramar scarf ta dauki handbag da wayarta takalli fammah dake faman Kiran wayar haydar tunda safen Amma baya dauka qarshema ya kashe wayar.
Ficewa tayi tana cewa"
I have a morning private meeting da wasu client Dina so saina dawo.
Tana fita Bata hadu da kowa a Palo ba ta fice.
A harabar gidan ta hadu da am yafito daga sashenda yake geaming jikinsa sanye da kayan geaming din sai sneakers na Adidas.
Qarasowa yayi gurinta lokacinda take fitowa Yana Mata wani kallon so yace"
Gud morning luv.
Murmushi ta mayar masa cikin kulawa da kashe murya tace"
Morning baby.
Are you going somewhere???
Yes baby I have some clients to attend to.
Ok lemme freshen up and.....
Katsesa tayi da cewa"
No I can manage besides I won't be long.
Ok luv you can take my car then.
Keys din motarsa ya dauko Mata ya Bata ta karba tareda kashe