Showing 63001 words to 66000 words out of 73969 words

Chapter 22 - BURI DAYA Hausa Novel

Mahmugee   

08 Oct 2024

20452

iri kenan abin haka yake suna taqura jama'a suna wulaqanta kansu ba girma ba wani mutunci cikin mutane.

Idan kana roqo Wanda kafi qarfin arzikima wlh yafika girma cikin jama'a.

Da wannan tunanin kawu yacewa maroqan gurin su samesa gida bayan kwana biyu insha Allah zai Basu jari Kona sana'ar lemo ne yafi wannan yawon zubarda mutuncin.

Aikuwa nan Suka hau godia suna sake sakawa aure albarka da jero masa manya manyan adduoi.


Ba zato tajisa gabanta sosai harsaida tayi Dan Baya ya riqota a kasalance ya sake kallonta da idanuwansa dasuka sake rikita nutsuwarta yakai bakinsa kunnenta cikin kasala yace"

Yunwa nakeji sbd farin ciki yau ko ruwa banshaba tun safe please ki dubeni kar yunwa ta kashewa baby z uncle takashewa kawu Dan gaban sirikinsa.

Turesa tayi tareda harararsa tana yamutsa baki yasaki murmushi Mai kyau tareda juyawa bayan ya jefeta da wani kallonda yasan sirrin tasirinsa akanta tun a wancan lokacin dabatasan takamu da sonsaba bare yanzu datagama dulmiya cikin son nasa.

Aikuwa take duka gabobinta suka sake taji wani sanyi na shigarta
Boyayyan murmushi ya subuce Mata ta juya zuwa kitchen tana sake waiwayon qofar daya fice.


Yana zuwa part dinsa tubewa yayi yafada wanka sbd yau din amatuqar gajiye yake sosai.
Yana fitowa ya shirya cikin doguwar jallabiya baqa Mai laushi da tsantsi kasancewarsa fari saitayi Masa kyau matuqa ya tayarda sallar ishai da akayi Yana wanka yayi abarsa.

Yana gamawa ya dawo Palo ya zauna jiran takawo masa abincin bayan yakashe dukkanin wayoyinsa.

Agogo yasake dubawa yaga lokaci yatafi sosai shiru sai kawai ya miqe ya fito Yana 'dan dafe kansa dake ciwo kadan.

Tsayawa yayi daga balcony din part din nasa sbd hangota tafe daukeda tray fuskarta a daure sosai Wai ita karyaga damarta
Abin saiya basa dariya da mamaki yasaki murmushi kadan Yana juyawa kallon gate da aka bude mota tashigo yakumasan kawune ya dawo.

Kawu datun shigowarsu ya hangeta gabansa ya Dan tsinke Yana fitowa mota yace"

Kai waye agurin nan????

Gintse dariyarsa Zaki yayi tareda saukowa ya qaraso gaban nadiyar data tsaya cak jikinta na rawar kunya

Ya tsaya gefenta cikin cinnawa kawun tashin hankali yace"

Barka da dawowa kawu?
Nadey ce kawu ninace takowomin abinci naci.
Allah ya tashemu lafiya kawu.

Wucewa yayi gaba kawun yabisa da kallo idanunwansa kamar zaiyi kukan takaicin yanda Zaki Sam baisan kunyaba ya iya cinna masa hauka wato ga dattiyan mahaukata ko?
To wlh inanan a dattiya Dina kudi Basu canzaniba cikin masifa yace"

Wato Zaki nidai duk yanda naso shikenan mutanen Lagos sunci galaba akaina jininsu yafi na ruqayya qarfi akanka idona kake kallo kanacemin Allah yatashemu lafiya da 'yar tawa,

Ke Kuma ido tsakiyar Kai kinfito Lilo Lilo dake kamar gwaiwa Zaki kaiwa miji abinci wato dai ko yanzu bazaku Bari ace ku tareba to wlh Babu shegenda zai kaini yabaro kamar wancan karon so kukayi na Gama asarewa gurin zagayen kariyar mutuncina acikin gidana Ina daga kwance Kuna tsallakeni Kuna zuwa shaaninku...


Iya talatu da hayaniyarsa tasata fitowa ta tararda abinda ke faruwa ta qaraso cikin takaicin Halinda baya canzuwa kamar na dattiyan tace"

Haba Dan Allah Kai Wai yaushe zakasan ka girmane??
Karka manta yanzu fa jikokine dakai Kuma 'daya na cikin gidan nan idan taji irin diban albarka dakakewa iyayenta wlh ka zubar musu da mutunci a gurinta...

Ke Ni banason qabli da baadi,
Ni bakiga irin renin dasukai min bane Ina ubansu,
Shi wancan qaton mara kunyar dangin Lagos bakiji cemin yake Allah yatashemu lfy sbd tsabar raini to wlh daidai nake da gyarawa ko wane Mara kunya zama a cikin gidan nan sbd gida nawane baza'a rainani cikin gidanaba.

Dawowa Zaki yayi cikin yanayi na sake haukata kawun yace"

Kawu kayi hakuri zamu kiyaye insha Allah baza'a qaraba,
Baby kibawa kawu hkr.

Cikin tsananin mutuwar jiki ta bude baki murya na rawa zatai mgn kawun dake hararar Zaki baqin ciki yagama cinyesa agabansa Zaki ke Kiran 'yarsa da baby a hasale yace"

Kina bude baki agurin zan karya qafarki Mai kama da hayaqin tsintsinyar qamshi.

Tsit Sukayi dukkaninsu harda iya talatu dake boye tata dariyar tace"

To kaji sunbaka hkr dai yanzu muje daga ciki ke Kuma wuce kikai abincin.

Wucewa yayi Yana gyara babbar rigarsa haryayi gaba ya dawo yace"

Idan kinkai karki dawo rufe qofata zanyi Kuma naji kin kwankwasa Ina budewa kusani yau saikun barmin gidana.

Da sauri ta kallesa ta girgiza Kai cikin rawar murya tace"

Nafasa baba wlh Bari na......

Ba shiru taji zakin ya janyeta tana qwacewa tana masifa ya wuce da ita har part dinsa ya bude qofar palon suka shige ya rufe.

Kawu daya saki baki cikin tsananin mamaki da takaicin yanda surukinsa Kuma 'dansa yagama rainasa.

Qyaci yayi yace"

Zakusha mamakina acikin gidan nan Dan wlh bazaku batamin jika da wannan Rashin kunyar da Rashin mutuncin nakuba.

Yana shiga yasakawa qofar babban palonsu key Yana cewa talatu duk kika bude qofar nan kinfi kowa sanin abinda zanyi Dan wlh hanaki kowace irin Sanaa zanyi.
#MAMUH._ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee42_*
Suna Shiga palonsa ta qwace jikinta tareda ajiye abincin ta juyo a fusace zata fara masa masifa taji bakinsa cikin nata ta zaro ido da qarfi zata qwace yasake matseta jikinsa Yana kashe Mata ido daya Yana shafo gefen cikinta.

Saurin qwacewa tayi da qarfi tana sauke numfashinta dake fita da sauri a boye ta zauna bakin sofa tana kasa dagowa ta kallesa.

Zama yayi hankali kwance kusada ita tareda yin balance yace"

Bani black tea din tukuna saiki bani veg din kadan shima.

Kasa motsi tayi sbd gabaki daya yagama hargitsa nutsuwarta hannuwanta har 'yar rawa sukeyi ta matsa kadan ta zuba masa black tea din ta miqa masa ya karba Yana kallon hannuwanta dake rawa ya hada dasu ya riqe tareda sakin ajiyar zuciya ya kalleta da idanuwansa masu sakata nutsuwa ahankali cikin kulawa yace"

Hey it's me,
Your husband,
Nine dai Yaya zakin dakika sani Babu wani qari ko ragi ok??

And I love you more than anything danake dashi arayuwa bazan taba cutatar dakeba,
Kawu duk wannan abin dakikaga yanayi yanayine sbd dabiarsace bawai haqiqanin abinda yake fadane acikin zuciyarsaba besides idan kawu ya daina wannan halayen nasa to ba lafiyaba sbd ciwone kawai zaisa ya daina Wanda bama fatan hakan,,,
So just chill my beautiful baby bride""yaqarasa fada Yana Mata wani siririn murmushi.

Miqewa tayi da sauri zatabar gurin ya riqo hannunta yadawo da ita kan cinyarsa Yana kallon fuskarta dake fidda annuri Yana Shan tea dinsa.

Harya Gama tanakan cinyarsa tana kallon yanda yakeyin komai nasa cikin izza da burgewa tun dacan haryanzu,
Haryanzu Bai wani iya sake fuska sosaiba Saidai murmushinsa da yanzu ya yawaita musamman agareta.

Murmushi tasaki Bata saniba tana kallon hannunsa inda tabon cizonsa yake a hannun haryanzu Wanda tasan da gangan yabar tabon Yana kallonsa bayan yana iya shafa magani tabon ya Bata.

Inda take kallo ya kalla ahankali take nutsuwar dayake Shiga duk lokacinda ya kalli tabon tashigesa sbd wannan moment din shine best moment a rayuwarsa sbd aranar yasan meye mace Kuma macenma wadda zuciyarsa da gangar jikinsa tafiso fiyeda komai.

Murmushi yasake ahankali tareda kallon nadeyn da kyau yana tuna yanda batai qwarin yanzuba a wancan lokacin taci wahala harda taumashi Amma Kuma yanzu tafi sanin ciwon jikinta musamman da hutu ya batata yanzu Amma zai banbance da kansa.

Matso da ita jikinsa yayi sosai tareda shafo cikinta murya qasa qasa yace"

Kinsan dai kawu yace bazaki Bata masa jikoki da Rashin kunyaba ko????

Murmushi tasaki tareda da kallonsa da idanuwanta dasuka mugun ta6asa Amma ya basar da shafo idanuwan Yana cewa"

Hmmmm kinason rabani da nustsuwatane?? That's not gonna happen.

Dauke gira daya tayi tana kallonsa da mamaki tace"

Really??

Hannunta ya matse cikin nasa Yana sake kallonta yace"

Hmmm.

Wani juyi tayi da ido tareda narkewa ajikin nasa tana lafewa tace"

Ok bacci ni nakeji gashi kasa babana ya koroni a Karo na biyu.

Murmushi yayi tareda safa wuyanta dake buso masa wani sirrin qamshi yace"

Kuma nasan yau bazai iya bacci ba Yana tunanin 'yarsa bazata iya daukar lalurar jarumin sarki kamataba....

Dukan qirjinsa tayi tana qoqarin miqewa yasake riqeta cikin jikinsa Yana Kiran sunanta cikin slow.

Shiru Sukayi dukkaninsu kowanne idanuwansa arufe suna sauke numfashi ahankali cikin nutsuwa.


Sun Jima ahaka kafin ya miqe da ita ajikinsa ya nufi hanyar bedroom dinsa Yana kallon fuskarta data rufe idanuwanta.

Kan king-size bed dinsa ya kwantar da ita tareda juyawa ya nufi closet ya fiddo wasu ellecrux sleeping set na couples ya cire na mazan ya ajiye Mata na matan.

Jallabiyarsa ya zare ya nufi toilet yayo alwala Yana fitowa ya tararda tasaka Bata tayi saurin kwanta tareda lallubewa ya dauki nasa yasaka ya fesa Hugo boss spray dinsa ya kashe lights yazo gefen datake ya kwanta tareda shigewa jikinta sosai musamman sbd body contact dasuka samu na yanayin rigarta datafi Kama da Babu duk da taqi Bari yagani Amma yaji sbd Saida yasaka hannuwansa ahankali ya Gama lalabo yanda yanayin rigar yake ajikinta.

Akan cikinta ya ajiye hannuwansa Yana sauke Mata numfashi Mai dumi a wuyanta daya sata qanqamesa tana sake shigewa jikinsa da narkewa cikin jikin nasa.

Jin tagama hautsina duk wani tunaninsa yasa ta janye ahankali tareda sakin murmushin jindadi tana rufe ido cikin sanyin murya kaman zatayi kuka tace"

Bacci nakeji kaina da cikina harma da qafafuwana duk ciwo sukeyi.

Bede ido yayi da sauri cikin duhun ya kalleta saikuma yayi sanyi ya qyaleta tareda gyara musu kwanciya Yana lumshe ido.


Qarfe goma na safe ta fito daga part din ta nufi part dinsu baba tana Jin wata irin kunyar hada idanuwa dasu saitafijin kunyarsu ayanxu fiyeda dacan.

Da sallama tashiga palon
Baby z datun safe ta daga hankalin kawun akan Ina mummynta tanajin sallamarta ta taso da gudu tayi gurin nadeyn tana cewa"

Yehhhhh mummy your daddy said you left me hia and....

Shut up z""tafada tana Dan riqo hannunta.

Kawu dayake cikeda z din tunda ta ishesa da surutun neman uwarta yace"

Jaira me Kama da jikar ifiritu zakisan Dani kikeyi uwayenki bazasu maidani mutumin wofiba kema kizo da jajayen kunnuwanki na inyamurai ki rainani.

Dariya zancensa yabawa nadeyn da iya Amma Suka gimtse tana gaidasu ta wuce daki ta shirya cikin riga da skirt na gold atampa maroon ta fito ta nufi kitchen tahau hada masa breakfast sbd baban ya fita iyace kawai zaune a palon tana kallon African magic hausa.

Veg chips source tayi masa da no shuga black tea sai fresh lemon mix.

Saida takai Masa breakfast din tadawo tayiwa baby z wanka ta shiryata sbd dadynta daya Kira a shiryata zaizo ya dauketa harsu aunt su tafi.

Tana Gama fitowa Sukayi Dan zuwa part dinsa din itada z taji ana hayaniya bakin gate ta juya ahankali tana kallon gate din saitaji kamar hayaniyar na qara yawa ta Dan matsa.

Abinda tagani ne yayi mummunan daga hankalinta ta juya da sauri gabanta na bugawa da sauri
Yana ganinta ya ture me gadin da sauri yafado gidan ya riqeta tasaki wani irin ihun tashin hankali da tsoro ta turesa tareda daga hannu zata maresa saita fasa ta janye z baya jikinta na rawa tace"

Am bakada hankali ne?
Get out of here tun kana gane hanya da kanka....

Zubewa yayi gabanta cikin tsananin kuka abuge ya riqo qafafuwanta Yana cewa"

Dan Allah baby kidawo gareni wlh bazan iya rayuwa Babu keba,
Mutuwa zanyi nabi dadyna idan kika barni....

Kukan tsoro baby z tasake tareda qanqame mamanta
Itama nadeyn jikinta mugun rawa yakeyi tafara qoqarin qwace qafafuwanta daya riqe tana ihu da roqonsa da hadasa da Allah daya saketa....

Ba zato nanu da me gadi suka shaqo wuyansa suka tayar dashi basusan da zuwan kawunba sai saukar Marika uku ajere sukaji ya saukewa am din Yana cewa"

Dan ubanka ubanwa yabaka izinin shigomin gida harka tabamin 'ya sbd ja riqa a ta'addanci ko?
To yau Zan nuna maka Ni haihuwar ta'addancin nayi maza Nanu ku canzamin kamanninsa besan dama nemansa nakeyiba dangin kashe kashe.

Cikin daga murya sukajisa daga bayansu Yana cewa nadey dauki z kibar nan I will deal with you later.

Suna barin gurin JJ na shigowa da motarsa Yana ganin am yafito mota da sauri Yana qarasowa gurin sbd ganin yau ran kawu yayi bacinda Basu taba ganiba shi sarki kuwa baa magana Dan tuni yakira 'yan CTU.
#MAMUH.

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*



*_Mamauhgee43_*
Wani wawan Mari zakin ya sauke masa Saida yakai qasa bakinsa na barewa da jini ya dago a gigice Yana bubbude idanuwansa dake neman rufewa sbd azabar marin,

Cikin hasala kawu yace"

Kai Nanu dauko masa Adda ko wani mugun makami yaci Mana ubansa
Wlh yau ka gode Allah bantaba dabanci ba dakaci ubanka da uwarka.

Hannu zakin yakuma dagawa idanuwansa na qara runewa zai sake Dora Masa wani mahaukacin Marin dayafi na farkon JJ yayi saurin dafasa tareda kallonsa shima ransa amatuqar bace yacewa zakin"

Let me handle this.

Kallon JJ yayi tareda tsayawa din sbd yasan zai iya kashe am din kafin zuwan Yan ctu ma'ana Yan 'drugs.

Am shine ciwon zuciyarsa na cikin zuci Dana sarari,
Duk lokacinda yatuno da nadey tayi soyayya da am Jin yake zuciyarsa na zafi kamar zai cinye kansa,
Am yasamu dama akansa wadda Babu Wanda yataba samun wannan damar ta soyayya da matarsa.,
Shine yanzu sbd ganganci da roqarwa Kai mutuwa yazo har cikin gidansa ya taba qafafuwanta matarsa....kaiiiii this is killing me.

Rintse idanuwansa yayi da qarfi yabudesu akan JJ dayasa gorar me gadi Yana yiwa am din dukan tashi kasha gishiri Nanu da Mai gadi na tayasa sbd me gadin shima ya tabo nasa yawon dabancin kafin ya tuba ya nemi aiki.

Kawu kuwa Jin yake dukan Bai masaba sai gyara babbar rigarsa yakeyi Yana saka qafa daga gefe Yana shurinsa ba tausayin am din ko kadan a zuciyoyinsu.

Alee idi dakejin ihun qaton na tasowa daga harabar gidan dattiya din yafito da sauri Yana cewa me gadin gidansa maza dauko gorarka miqomin daya magauta sunkai farmaki gidan 'dan uwana.

Me gadin najin hakan ya rarumo gora biyu ya miqawa idin suka nufo gidan suka fado Yana cewa"

Uban waye agurin?????

Ganin abinda ke faruwa yasashi saurin qarasawa da gudu ya janye am Yana kallon yanda sukai masa cikin mamaki ya kallesu yace"

Lafiya zaku kashesa ana zaune qalau munsamu zamu zauna lafiya ko gama jiquwa bamuyiba ace ankama wani daga cikin dangi ai bamuda wani kwanciyar hankali,
Dan Allah kubari wlh bazadai muso ace wani Abu yasamu dayanku ba,
Bakwa kisa,
Baku taba ba meyasa zakuyi yanxu?????

Cikin hasala kawu yace"

Bar wannan dangin daukan ran sbd abinda Suka iya kenan wato kashe kashe gwara a dandana masa ko kwatan kwacen qanin mutuwarne yaji tunda ubansa ya mutu baici mugun dukan azaba ba shi saiya karba har nasa harna ubansa shegu dangin Ethiopia.

Cikin son fahimta alee idi yace"

Shi din wanene Wai????

Dan gidan dikko Dilla ne.....

Zaro ido alee idi yayi Yana cewa"

Dikko Dilla????

Aiko yau zaici ubansa"""yafada Yana kwabe babbar rigarsa ransa a matuqar bace ya daga gorar hannunsa duk iya qarfinsa zai shemesa aka riqe gorar daga bayansa Suka juyo dukkaninsu.

Kuka takeyi sosai duk iya qarfinta Saidai sbd Rashin qarfin jiki da azabar yunwa data gama cinyeta yasa kukan baya sauti sai sheshekarta da ake gani.

Sakin sandar tayi tareda durqusawa a gabansu cikin tsananin kuka da dasashiyan murya tace"

Dan Allah karku kashesa wlh shikadai gareni shikadai ya ragemin.

Kallonta Sukayi a sheqe Banda Zaki dayaji nauyinta ya qaru akansa sbd tausayinta dakuma kasancewarta mace budurwa.

Rage hargitsin fuskarsa yayi Saidai Bai saki fuskarba Kai tsaye yace"

Get up.

Tashi tayi ahankali batareda takalli fuskarsaba sbd haydar shine abinda zuciyarta take azabtuwa akai.

Ina mum dinku???

Shiru tayi hawaye na gangaro Mata sbd kunyarma fada takeji cewa mum dinsu tasamu tabin hankali sunyi cuku cuku sunsamu ankarbeta asibitin mahaukata ta can dilla.

Cikin hawaye tace"

Mum na asibitin mahaukata..

Ina kuke zama??

Shiru tasake na Dan lokaci kafin tace"

Gidan wasu yorbawa muke hayan daki 'daya.

Shiru yayi batareda ya kalletaba yadan sake kallon am din daidai qarasowar motar Yan ctu Suka shigo harabar gidan Babu wata wata Sukayo kansa zakin yayi musu alamar daka tawa ya Dan kalli gefen fammah din fuska daure yace"

Shiga ciki ke,shikuma zamu miqasa hannunsu su zasu horasa yadawo daidai zai fito idan Allah yasa ya shiryu.

Kuka tafashe dashi tareda rungume am din da qarfi tana girgiza Kai tace"

Am Ina sonka wlh nidai koyaya kazama Ina qaunarka Dan uwana kadawo normal muje mu rungumi qaddaran data samemu,
Dan Allah am kace kadaina karsu rabamu idan katafi waye zai zama gatana,Ni kadai rayuwata lalacewa zatayi.

Akaro na farko dayaji hawayen tausayin kansa sun sauko masa awahalce sbd yau shine yakamata yazama gatan qanwarsa Amma shima rabasu zaayi baisan wace gararin zatayi ba bayan Wanda Sukayi dawowarsu Nigeria sbd abincin cima wuya take musu.

Kuka yasaki ahankali tareda daga hannu daqyar ya riqota yana kukan tausayin rayuwarsu da iyayensu Basu Basu tarbiyan dazata cecesu ko bayan mutuwarsuba,
Basu tarbiyantar dasu kan hanyarda zata taimakesu ba ko bayan sun rasa iyayen,
Yanxu gashi sun tafi sunbarsu a duniyarda basusan ta Ina zasu fara Gina kyakkyawar rayuwaba.

Kuka takeyi sosai shima kukan yakeyi ayau Yana baqin cikin gata da Jin dadinda iyayensa suka basa Basu tarbiyantar dashiba gashi shima yanxu baisan yazai fuskanci tasa qaddararba bare yimusu addua,
Tanaji tana gani aka tafi dashi tun a nan suke dukansa cikin Rashin Imani kosu Saida jikinsu yadanyi sanyi musamman sbd tausayin fammah sbd sunsan Yaya soyayyar 'yan uwantaka take komai lalacewarka kuwa sbd Suma sun Dan yanda suke qaunar junansu tun suna a barbadensu kuwa.


Kasa hakuri nadey dake Palo tayi ta fito da gudu tayo gurin fammah din sbd itama kukan takeyi sosai sbd kunci daya lullube zuciyarta na tarwatsa musu rayuwa duk da tasan Suma sun tarwatsa ta wasu Amma data barsu da Allah to tabbas shiyasan irin sakayyar dazaiyi akansu Amma gashi yanxu taje tadauki zunubin daba nataba sbd itama sai Allah yakamata da zambar datayi musu cikin aminci tayi amfani da yarda da so ta lalata musu rayuwa.

Rungume fammah tayi tana sake sakin sabon kuka sbd tabbas ta tabbata itace keda haqqin duk abinda yasamu fammah arayuwa.

Cikin gida tashigo da ita har cikin bedroom dinta tasa fadima takawo Mata ruwa da abinci Amma Sam fammah takasa ko kallon komai sai kukan tausayin Dan uwanta da irin rayuwar dazaiyi hannun Yan drugs ta azaba da ukubar rayuwa.

Itama nadeyn shiru tayi cikin tausayin am dana fammah sbd tabbas ba laifinsu bane tarbiyar da nasu iyayen Suka dorasu akai kenan.

Har Rana tana fama da fammah daqyar tasamu itada iya talatu sukai Mata nasiha ta daukan qaddara akan ta mayarda hankali tayita yiwa Dan uwanta adduar Allah yasa ya samo canjin kyakkyawar rayuwa acan din tareda yiwa iyayenta adduar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login