Showing 60001 words to 63000 words out of 73969 words
dasukai wani aminin Wanda shima Dan juma ne da Dan jummai suka bazama yawon Shan shayi da maiqo har dare Basu dawoba
Sai washe gari tagansu shi dinma tana Jin motsinsu tayi saurin fitowa tun kafin tayi mgn iya talatu da itama take qule dasu ta fito ta watsa musu wani kallo cikin takaici tace"
Allah dai yasa kusan kun tsufa kudaina wannan yawon ta zubar din,
Harda qasardaba qasarku ba bazaku iya riqe qafafuwanku ba ku zauna guri daya wannan abin kunya har ina.
Cikin daure fuska dattiya yace"
Ke talatu ki fita idona banason Rashin mutunci da Rashin iya mgn,
Meye amfanin zuwan idan mutum Bai zaga yaga koina ba......
Cikin takaici ta katsesa da cewa"
Dan Allah dattiya kudaina wannan yawon kungafa gobe zamu koma Amma kun kasa tsay.....
Cikin kufula idi da dama yake cikeda ita tun wancan lokacin yace"
Talatu waike meyasa Allah bai zuba Miki dangana da iya Kama bakinkiba,
Bansan yaushe qiyayya tashiga tsakaninmu ba ranar har farin ciki kikeyi kika kirani sbd nazo Naga matattu da dagaske ne matattun ne wato nagansu zuciyata ta buga na mace agurin tunda dattiya baida kowa saini yanxu,
To dattiya kashiga tsakanina da talatu hakama ita tashige gaba tasa shafa daga hankalina a qasa Mai tsarki akan auren nan danayi niyya ta gashi nan nafasa auren Amma ba yanxu zankoma gidanba tukarin zamuyi muma.
Zaro ido nadey tayi cikeda faduwar gaba tace"
Baba wane irin tukari ana zaune qalau Dan Allah kuyi hkr yau tsakar dare jirginmu zai tashi.
Washe baki dattiya yayi yace"
Badamu zaku koma ba anan zamuyi takari alhaji garba zamu zauna agurinsa hanyoyin dogaro dakai gasunan birjik su zai koya Mana a qasar shekara daya mundawo gida.
Tagumi talatu ta rafka daga tsayen tanajin inama baazo dasuba wannan abin kunyar dasu dattiya zasu jawo musu.
Duk yanda Nadiya tayi dagewa Sukayi akan raayinsu batasan lokacinda tafashe da kuka ba tana sake roqonsu Amma Suka wucewarsu Suka barta iya talatu nabinsu da hararar baqin ciki da takaici.
Zama Sukayi dukkaninsu Suka rafka tagumi cikin baqin ciki da damuwa
Nadey datasha kuka harta gaji ta dauki waya takira haydar.
Yana kallo wayarsa nata ringin yaqi dauka Kuma yasan itace Amma yayi banxa da ita sbd zai banbanta Mata Aya da tsakuwa.
Qaruwa damuwarta tayi sbd tasan mulkinsane da izzarsa yasa yaqi daukar wayarta sai takira dad.
Cikin tsananin damuwa tafara fada masa abinda ke faruwa abin yabasa mamaki sosai sadai Kuma yasan dadine yasasu cewa bazasu dawonba takari zasuyi.
Cikin lallashi yace"
kwantar da hankalinki nadey nasan ya zan musu zasu dawo kafin kutashi tafiya.
To tace murya a sanyaye.
Ita su iya talatu nema ke Bata tausayi musamman shafa'atu da duk tafiyar ta fice aranta tun lokacinda mijinta ya ha'du da takari.
Dad nagama waya da Nadiya yakira layin wayar dattiya da aka siya musu kafin tafiyarsu wadda bayan Zaki da JJ Babu Wanda ya taba kiransu sai yanxu dayaji tana ringin cikin aljihun babbar rigarsa.
Da sauri yacirota Yana cewa"
Zaki ne ke Kira qila yaji bayanxu zamu dawoba bankwana zamuyi.
Dauka kawai yayi sbd koya tsaya duba sunan ba ganewa zaiyi sosaiba.
Jin muryar neyo yasashi sake washe baki Yana kurbar shayinsa na larabawa Mai shegen zafi yace"
Aliyu ya Nigeria??
Murmushi dad yayi tareda cewa"
Lfy klau alhmdllh yaya,
Yaya ibada da Kuma baqunci?
Lafiya kalau ibada baqunci Kuma ai munxama Yan qasa tuni.
'yan qasa Kuma yaya?
To dama Ni akan maganar gidankane kaida Yaya idi dazu aka kawo takardu Wai gidan mallakin wasu ne ba nakuba.......
Wata qatuwar ashar ya mulmulo Yana qonewa da ruwan shayin ya miqe yace"
Wane Mai rabon wahalar ne yace haka?
Gidan damuka gida da guminmu,
Ganinan tafe Nigeriar Inga wane Dan iskan kudun ne.
Alhaji idi da tuni ya dire kofinsa Yana jiran qarin bayani yace"
Meyasamu halalina???
Ciki ciki dattiya yayi da qananun idanuwansa ransa amatuqar bace yace"
Wani Dan baqin cikin dayakasa ganin munyi gaba ne Wai filin gidansa ne.
Miqewa idi yayi Yana cewa"
Dama yanxu magauta tako ina kunno Kai zasuyi Amma daidai nake dasu Dan Ni Dan iskan takari ma nafi qarfinsa bare na Nigeria muje.
Alhaji garba na musu maganar zamansu tuni sukace sun fasa yanxu Amma zasu dawo.
Yace"
to shagon damuka hada kudi muka Kama fa zamuyi sana'a??
Kai alhaji garba bakaji Wai hawun dake neman hawanmubane kake mgnar shagon Saida shayi da kaji.
Masaukinsu suka dawo lokacin har anyi sallar magriba suna zuwa ba kunya Suka hada kayansu tsaf Babu fuskarda kowa zai samu tambayarsu ya akayi dayake Suma sansan halin sai Basu ce musu qalaba har akai ishai Suka sake kakkamta kayansu mota tazo ta daukesu zuwa jidda suna Isa basuyi ko mintuna arbainba aka Kira jirginsu Suka miqe har lokacin su kawun fuskar nan a tsuke tam.
Suma haka Suka fecesu hardai iya talatu ita dama shafa'atu jira take akoma ta gyara masa zama.
Baby z ce kawai ke walwala a tsakaninsu sbd zuwa lokacin tasaba da kakanta sosai suke dasawa Saidai idan tayi Abu kadan turawa nashan zagi ba sauki.
Qarfe goma na safe jirginsu ya sauka a Lagos sun fito Dan neman taxi zuwa masauki sai Jin tayi baby z ta kwace daga hannun babanta tana cewa"
Yeehhh my uncle.
Faduwa gabanta yayi ta dago da sauri ta kalli inda z din tayi tagansa sanye cikin wasu Armani wears normal size blueback sun masifar fitarda kyawun hasken fatarsa yasaki wani guntun murmushi tareda warewa 'yarsa hannu yadagata sama yana cewa"
My baby is back.
Kiss tai masa a kumatu tana dariya sosai tace"
I miss you so much uncle.
I love you so much my little miss Noah.
Su iya talatu ya qaraso Yana gaidawa fuskarsa a Dan sake kafin ya maida kallonsa kansu kawu da mal idi ya bude baki gabaki daya Yana kallon wata taquwar Mata data wuce da wani wando daya gama kamata kusan komai Bata ana gani sai wata riga Mara hannu da wani kalar gashi kalar Blue data saka akai.
Dattiya kuwa takalminta yake kallo Yana tafiya har yayi tuntube da jakar kayansu saura kadan ya kife talatu ta girgiza Kai tana cewa"
Karkaji ciwo alhaji kalli gabanka.
Fuskewa yayi Yana amsa gaisuwar zakin Yana sake kakkallon mutanen dake harkokinsu a airport din.
Allah yagani shikam bai taba ganin anbawa mahaukata damar kaida kawo hakaba sai anan.
Mota Suka dunguma dukkansu dama wata black BMW bus ce aka kawosa da ita ta daukesu duka suka nufi babban gidansa dake Victoria island.
Sosai ikon Allah yagama kamesu kawun tako Ina tun lokacin Suka dau hanyar zuwa gida Zaki yace"
Kawu kana cikin Lagos ne fa.
Kallo juna Sukayi da idi cikin ransa yace"
Ashe mutanen Lagos din sunfini iya tsula tsiya.
A boys quarter aka sauke su baban inda Suka hau baccin gajiya bayan sunyi sallah sunyi nis.
Bedroom biyune a palon qasa su iya talatu Suka shiga daya ta shige dayan.
Wanka tayi tai sallah ta kwanta sbd tana buqatan hutawa Dan tunda sukai tafiyar nan batada hutu haukacewama tasoyi sbd tsabar tension.
Bata fitoba sai yamma shima sbd yunwane.
Babu kowa a makeken palon sai hayaniyar z datake jiyowa a palon sama ta nufi qofar datake sakaran qila kicin ne tana budewa taga Babu komai ba kowa ta bude fridge shima drinks ne kawai sai apples ta dauki daya tanaci ta fito tana duba best restaurant a Lagos din ta wayarta sbd tayi order.
Wani kitchen crafts dake kusa tayi ordern chips source da white veg pasta sai coconut water mix tadawo palon ta zauna tana qoqarin Kiran dad taji qamshin possession royaltee man yashigo hancinta tareda sanyin aircon split dake daukeda qamshin airfresh na rosallee.
Lumshe idanuwanta tayi tareda budesu ta dago ta kalli direction din saman Suka hada ido take jikinta yasake mutuwa takasa Koda motsi harya sauko yazo ta gabanta ya wuce ya fice yabarta dabin bayansa da kallo jiki amace.
Koda aka kawo order dinta takarba tabiya kudin tadawo ta nufi dining taci.
Tana gamawa tasake komawa daki.
Da daddare semo da miyar kaji tareda gasashen kifin dayaji lemon yasa aka kawo gidan kowa yaci yaqoshi.
Saida yabari su kawu sun qoshi yace"
Kawu muje kuga gari.
Ba musu Suka kwasa Suka bishi tun Abu nabasu mamaki harsuka fara gigicewa da balain dasuke gani tuni dattiya yafara shafawa kansa lafiya da Yan iskan Lagos musamman wani gurin dayake gaisu sukasan da gayyane saiga su da salati suna ya maidasu gida.
Dattiya daya dawo harda hawayensa Yana cewa"
Lallai Ashe iskanci na Lagos shine yake cewa yafi Yan Lagos iya iskanci.
Allah yarabasa da iskanci irin na Lagos.
Dasuka dawo tuni kowa yayi bacci ya hayewarsa sama ya tube yayi wanka ya kwanta Yana danne abinda zuciyarsa keso.
Washe garima haka yasa aka dinga yawo dasu kawun a Lagos saigashi sun haukace da kallon ikon Allah da wani balain dayafi qarfin tsufansu.
Cikin saa kuwa suna wata anguwa lekki fada yatashi akahau sare sare da qona tayoyi take sukahau rawar jiki ba arziki Suka daga hankalin driver jikinsu Babu Wanda bai hada zufan balai ba harsuka dawo gida jikinsu rawa yakeyi mal idi ma Saida yahada dashiga bayi tun daga ranar harsukai kwana biyar basu sake marmarin fita koinaba.
Ranar dasuka cika sati aranar zasu koma gida har wani murna sukeyi sbd sunyi kewar gida matuqa musamman da duk tsorace suke sudai da Lagos din.
Airport Suka nufa kowa da ticket dinsa a hannunsa Banda Zaki sbd badashi zasu komaba Yana wani aiki ne.
Suna wucewa gaba ya kamo hannunta ya dawo da ita baya tareda matseta jikin mota Yana kallon cikin idonta da wani irin kallo dake kashe Mata jiki.
Hannu yasa ahankali ya shafo fuskarta tareda hura Mata iska ya daga Mata gira qasa qasa yace"
Babu ko bankwana Zaki tafi...???
Dan zamewa tayi yasake matseta tareda Kama hannunta yayi kissing yace"
Ki shirya Dana dawo zamu tafi.
Ahankali ta girgiza masa Kai batareda ta dagoba.
Yasaki wani siririn murmushinda yasake kashe Mata jiki yakai bakinsa kunnenta yace"
Okk nagane agaban kawu kikeson ki jere masa jikokinsa kenan ko????
Turesa tayi da sauri murmushi na kufce Mata tayi gaba tareda waiwayosa kadan Suka hada ido tasake juyawa da sauri ta wuce.
Dattiya da tuni yaketa masifa da baby z akan saita koma gurin uncle dinta ya danneta cikin takaici Yana cewa"
Ke banason taurin Kai irin na jajayen kunnuwan america,
Waincan uwayen naki basuda kunya ko kadan musamman ubanki daya Gama tarwatsamin tarbiyar 'ya tun bakizo duniyaba nake fama da Rashin arzikinsu dasunaji dasun daina Amma Ina..
Qwacewa tayi tana cewa"
Banaso sakeni.
Riqota iya talatu tayi cikin dubara tana cewa"
Kyalesu zainab ai yanzu mamanki zatazo.
Barta karma ta qyale kakkarya shegun qafafuwanta masu Kama Dana bebin roba zanyi kowama ya huta,
Iyayenta sun rainani itama ta rainani bazai yiyuba jaira Mai kama da baquwar aljana babbakewa da asarewa nawane banyiba kafin zuwanta duniya saikuma tazo Ina magana tanaimin turanci tunda ga dattiyan mahaukata,
To wlh ko mahaukatan lagos qarya suke bare na turai.
Isowar nadey ce tasa fadan yakoma kanta harsuka shiga jirgi fadan yakeyi idan yaga wani abin kallon saiya saurara ya kalla kafin yaci gaba.
Candai bayan yagama fira ta barke tsakaninsa da aminin Amana yace"
Kai alhaji idi wato su Lagos duk rabinsu mahaukatane.
Hmmm alhaji dattiya Ni wlh yanzu ko labarin Lagos naji anayi Aina daina shiga na zaqalqale,
Mutane ana kallo suna tafe a tsirara sbd lalurar hauka Amma duk ankasa masu taimako Kuma Amma dayake Naga basa duka ko ihu lafiya kalau suke tafiyarsu shinema saukin abin.
Dariya dattiya yayi yace"
Wato sbd girman lagos kana gani mahaukansu ma a natse suke fes fes abinsu,Amma fa Lagos nada dadi kawai dai balainsu ne yafi qarfin dattiya Dole Zaki ya tsula tsiya Ashe ba abanza ya deboba,
Ruqayya tayi qoqarin zama anan.
Itadai nadey tanajinsu har suka iso jirginsu na sauka jj ne yazo daukarsu mota biyu shida nanu tun a mota yake tambayar maqwaftansa sbd so yake Koda zai Isa duk suna nan suyi masa barka da dawowa.
Suna isowa qofar tangamemen gate din gidansu guda biyu da akayi komai iri daya Suka fito da sauri harsuna rige rigen cewa"
Wato dai da gaske wani shegen saman ya mallake gidansu.
Dariya Nanu yayi tareda yin horn me gadi ya wangale gate Suka shige sai alokacin suka lurada su mal zailani dasukazo tarbonsu suna musu barka da isowa tareda murnar sabon gidan take Suka gano saisuka hau washe baki suna karba gaisuwarsu ana sake tambayar yaushe rabo.
Koda Suka shigo gidan sosai farin cikinsu yakasa boyuwa sukahau duba gidan suna aikin sakawasu zakin albarka da adduoi.
Qatoton palone da three bedroom sai wani palon me bedroom daya Wanda nan ne na kawun,
Sai boys quarter me Palo da daki sai toilet Wanda shikuma ba nanu ne sai dakin me gadi.
Sai wani babban part dake gefen nasu Kawun Wanda yake babban palone da bedrooms biyu sai kitchen da dining room shikuma shine na zakin JJ yace zai zauna da dad.
Komai iri dayane Dana alhaji idi Kuma anzuba musu furnitures da komai na buqata.
Iya talatu da shafa'atu duk bacin Rai dasuka dawo dashi tini suka aje Suka hau murnar sabuwar duniya baqi da Yan anguwa sai murna suke shigowa yi.
Daki daya ta zaba a Palo kusadana iya talatu anan ta baje itada baby z dayan dakin Kuma me aikin da aka daukoce.
Basu samu hutuba sai dare sosai mutane suka tsagaita.
Itakam da wuri tayi bacci iya talatu kuwa anacan anata baza sabon lissafin rayuwar daza'a fara.
Daqyar su alhaji dattiya Suka samu sauqin mutane suka shigo gidajensu amatuqar gajiye sai yanzu suke gane wani lokacin ba wulaqanci masu kudin keyiba kawai gajiyace da takura irinta mutane.
Abinci aka Kai masa Mai raida lafiya yaci yakoshi yashige daki yayi kwanciyarsa yana cewa"
Daban dawoba da yanzu talatu ce zataji wannan dadin ita kadai.
Hararar gefensa tayi tace"
Kaikuma baqin cikinka karnaci wannan arzikin nikadai.
Murmushi yayi tareda gyara kwanciya akan lafiyayyan gadonsa Yana cewa"
Ke yanxudai ki koyi daa ga miji dama can zafin talauci da rashine yasa nake dauka,yanzu hayaniyar mutane ma ta isheni.
Dariya abin yaso Bata saita gintse ta miqe ta kwanta itama.
Washe gari bayan ankai masa Kari yayi ya shirya cikin wata babbar shadda gezner fara qal sai daukan ido takeyi ya fito inda akace yanada baqi harabar gidan aka shimfida masu babban dadduma yafito ya zauna suna gaisawa cikin farin ciki baqinsu ne na kasuwa dasukai sana'ar lemo tare.
Alhaji idi ma cikin bulun shadda Mai qyalli ya qaraso Yana gyara babbar rigarsa ya qaraso ya zauna suna sake gaggaisawa.
Har yamma suna tarbon baqi idan lokacin sallah yayi masallaci suke shiga suyi sbd shima angyarasa sosai.
Abinci kuwa haka ake fitowa da kuloli daga gidajen biyu su mal zailani tuni Suka fara lasa arzikin Suma duk da Zaki kusan duk dattijan anguwan yabisu da jari ba laifi.
Yau kwanansu biyar da dawowa yaune Kuma jumaa dad da kansa yazo gidan suka Jima sunata magana.
Dukkaninsu hidima sukeyi sosai tsakanin gidajen biyu dadynta kuwa sai tambayarta metakeso yakeyi sai abin yabata mamaki tace"
Dad meke faruwane???
Aurenki zaa sake daurawa yau after juma'a.
Kallonsa tayi da sauri muryarta na rawa gabanta na faduwa tace"
Aure Kuma dad?
Dawa???
Nine na zabar Miki mijin kinji nadey karki damu.
Murmushi ta qaqalo tareda sunkuyar dakai sbd dad bazai taba magana tace aa ba.
#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*
*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_
*08030811300*
*07067124863*
_*Mamuhgee41*_
Duk yanda taso daurewa kasawa tayi bayan fitar dad gurin iya talatu taje inda take kicin tareda matar dahiru da fadima me aikinta suna yanka fruits ta qaraso tanason tambayar iya din saita kasa tasake ficewa.
Tana fitowa tsakiyar palon wasu baqi su biyu Suka shigo farare tas dasu Saidai kammaninsu da dad yasa tasake kallonsu cikin Dan qaqalo murmushi tace musu welcome.
Dayar me Dan shekaru ce ta taso tareda rungumeta jikinta sosai cikin kulawa da qaunarta tace"
Hey nadey nice aunt din haydar qanwar dadinsa amby Sam Noah and this is our younger sister Sarah Sam Noah.
Murmushi ta qaqalo cikin farin cikin ganinsu ta sake rungume Sarah Suka sake gaisawa tace Bari takira mum dinta.
Kicin Takoma takirawo iya talatu Suka dawo palon Allah yasa sunajin hausa nan Suka gaggaisa dasu aka fara kawo musu drinks da cake dinda aka siyo na Leda nabawa baqi.
Fira sukeyi ahankali Suna tambayarta yanayin aiki da Shirin bikin tana Basu amsa a sake.
Saida aka tafi masallaci sallar juma'a kafin Suka fito sai alokacin Suka saka aka dinga shigo Mata da kayan akwatinanda haydar yasa sukazo dasu Suka wuce gidan dady.
Aikuwa kayane sosai set din wasu kyawawan maroon alnafyeel bags take iya talatu tasaka aka sanarwa gwaggo shafa'atu Suka shigo ganin kayan.
Itadai daki tashigewarta tana waya da JJ daya kirata cikin sanyin murya da tayata farin ciki yace"
Andaura auren Mrs haydar Zaki Noah.
Wani lumshe ido tayi tareda sakin siririn numfashi tana sake gyara kwanciya kan gadon dakin tace"
Nagode dady j.
Allah yabaka matarda tafini komai na rayuwa da kyawawan halaye nagari.
Amin""yace tareda cewa"
Baby z na gida ko tabi su aunty?
Dama tun dazu tana gurin fadima Amma inaga Bata bisuba tana nan.
Tana Gama wayar ta miqe taje tayo alwala ta tayarda sallah cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Shiru shiru Babu Wanda yadawo har yamma sai kawai ta share itama taci gaba da hidimarta dama gwaggo shafa'atu takira wata madam eliqueen Yar sudance Mai gyara tuni tasamu isowa tafara aikin gyaran jikinta duk da tace gskia tana buqatar sati iya talatu tace satin yayi yawa ayi Mata dai yau da gobe sai jibi sbd jikin nadiyar ma a gyare yake da santsin fata da laushi sbd tsadaddun products dinda take amfani dasu gurin wanka da shafa.
Saida aka fara kirayen magriba Suka kammala eliqueen ta wuce ita Kuma ta fada wanka da ruwan scent dinda tabata na rosallee florish purple sandal scent.
Aikuwa take toilet din ya gauraye da qamshinsa sosai har cikin dakinta
Ita kanta tana wanka tana lumshe ido sbd sanyin qamshin turaren.
Tana gamawa ta fito ta shirya cikin wata purple nolet gown Mara nauyi ko wani dogon hannu batada ta daure kanta daya Dan jiqe baki bakin tasaka hijab ta tayarda sallah.
Tana idarwa ta cire hijabin ta fito tana qwala Kiran z sbd tazo tayi sallar magrib.
Bata lurada mutum a palon ba Saida ta juyo zata sake qwala Kiran z idanuwansu suka hadu gabanta ya fadi sbd wani irin kwarjinin dayayi mata dakuma tsoronsa daya shigeta.
Sanye yake cikin farar shadda qal sai qyalli takeyi yacire babbar rigar tana riqe a hannunsa da alama tunda rana Bai sauyaba.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda kallonta da idanuwansa dake cikeda gajiya sbd taron aurensu na yanzun yafi na farkon cika da jama'a sosai harda manyan abokanan huldarsa Dana dad dinsa gasu kawu Suma yanzu jama'a sun qarar musu,
Dattiya a gurin daurin auren dayaga maroqa sunata faman kirari suna roqo saiyaji abin nabasa kunya
Yaringa Jin kansa suka kalli juna da ido kowanne ransa wani