Showing 36001 words to 39000 words out of 73969 words

Chapter 13 - BURI DAYA Hausa Novel

Mahmugee   

08 Oct 2024

20456

Mana akan abinda akaiwa Yaya Zaki
Amma yanzu Yana buqatar adduarmu ga gawarsa can an kawo.

Kallon zainab tayi kamar wata wawuya batareda ta iya magana ba sbd bakinta daya bushe har zuwa maqoshinta haka zainab ta kamota ta fito da ita inda gidan yake cikeda mutane har gaban gawar ta ajiyeta babansu dake gefen gawar Yana kukansa Babu boyo yakai hannunsa dake rawa ya bude qonanniyar gawar tareda sake fashewa da kuka su zainab ma kukan sukeyi sosai.

Miqewa tayi da sauri tareda ja Baya tana girgiza Kai sai alokacin hawaye Suka sauko Mata akaro na farko datai magana tace"

Wannan ba gawarsa bace,
Komai qonewar dazaiyi Ni zangane gawarsa,wannan ba ita bace
Ko Yaya Zaki ya qone yafi wannan,
Ba gawarsa baceba........

Da sauri iya talatu da zainab Suka riqota ganin Sam ba a hayyacinta take maganarba ta qwace da qarfi tana kuka tace"

Ina cikin hayyacina ban haukaceba wlh wannan ba gawarsa bace ba......

Rirriqeta akayi ganin hauka tuburan na bayyana cikin maganganunta wasu kuwa tuni tafara Basu sabon tausayi sbd ganin zaucewa ce tayi.


Ahaka akayi jana'izar gawar aka dawo nan aka cigaba da zaman makoki.

Sati daya da mutuwar ta koma kalar tausayi kowa tausayinta yafi damunsa yanxu Dan kuwa wata irin muguwar rama datayi gashi Sam Bata magana koyaushe tana dakin Zainab kwance kuka ma Sam ya qafe Mata sai hakan ya taba lafiyarta sosai duk da ma Dr sayyid yazo kusan so uku Yana dubata.

Yau akai sati biyu da mutuwar Nanu yazo yakawo Mata wasu takardun zakin da duk abubuwansa dake hannunsu sukai musu sallama kowa zaije yakama gabansa.

Wani irin kallo tai masa idanuwanta na cikowa da hawayen tafiyar tasu sbd sune Wainda Zaki keyiwa kallon danginsa na biyu haka Suma yawancinsu duk marayune zakin shine gatansu.

Tana kallo Suka taru kusan su talatin da hudu sukai Mata sallama Suka tafi kowannensu na baqin cikin rabuwa da inda Zaki yayi musu gatanda yanxu basuda Mai musu shi gashi tun bayan rasuwarsa aketa kama wasunsu ana rufewa ba wani dogon dalili.




****
Cikin wani irin Jin dadin daya Jima shekara da shekaru Yana jira ya daga takardunsa dasuka gama kammaluwa yace"

Finally Dilla will be the richest business tycoon da Babu kamarsa daga yanzu.

Kallon familynsa yayi da dukkaninsu kowa yasamu cikar burinsa musamman am da ya kawarda Zaki Wanda shine matsalarsa da mum dinsa.

Zeel na karanta wasu takardu tace"

Before mubar qasar gobe akwai wani aikin daya kamata mu qarasa Dan rufe matsalarda muka magance gabaki daya saboda karta bullo Mana a gaba.

Atare dad da am din suka kalleta ta aje takardun tareda kallonsu Kai tsaye tace"

Familyn Zaki,,,,matarsa in particular sbd hankalina Bai kwantaba tunda naji kunce yanda Mata I just can't take any risks sbd matarda aka kashewa miji abar gudu ce,
So Dole arufe chaptern Zaki gabaki daya.

Kallon am dad din yayi tareda dauke gira daya yace"

You heard your mum.

Daga Kai am din yayi Yana cewa"

Done.



****
Ahankali yake bude idanuwansa wannan karon tsaf yake ganin komai har idanuwansa Suka gama budewa yaringa qarewa dakin kallo tareda daga hannunsa daqyar ahankali ya dafa gefen cikinsa dake masa ciwo tareda rintse ido yasaki wani irin Nishi yafara qoqarin tashi zaune.

Yana qoqarin miqewa dafeda gefen cikinsa yaji budewar qofa da sauri ya dauki wata blade din asibiti dake cikin kayan dressing din ciwonsa dake gurin yayi Shirin soke Wanda zai shigo.

Da sauri Dr sayyid yayi saurin ja da baya Yana cewa"

Hey easy man saurara ka ajiye blade din
Ni ba Wanda zai cutatar dakai bane idan zaka tuna nine na daukoka daga asibitin Dilla lokacinda kake neman fita hayyacinka bayan yaran am Dilla sun kunnawa dakinda kuke wuta.


Dafe gefen cikinsa yayi Yana rintse ido sbd zafin ciwo da zuciyarsa dake ci da wutar fushi da wani irin rage dabaisan yanadashiba yace"

Wlh nine ajalin dillas da.....

Kasa qarawa yayi sbd wata irin azaba da gefen cikinsa keyi ya rintse ido yasake bude jajayen idanuwansa da fushinsa ke qanqantasu yace"

BURINA DAYANE yanzu Nine downfall na dillas.

Saurin riqosa Dr sayyid yayi ganin ciwonsa yafara jini yace"

Sanin hakan yasa na cetoka sbd son samun Wanda zai tayamu cika namu burin na ganin dillas a qasa.

Cikin dauriya JJ yazame jikinsa Yana nufar qofa yace"

Ina buqatar magana da Zaki yanxu nan bana iya tsayawa banyi magana dashiba Dole zaisan waya turo kb ya kasheni sbd naji maganar am kafin su kashemu yace idan sunason samun full control na Zaki saisun kawarda Dani Zaki yakamata yasan wannan yanzu.

Da sauri Dr sayyid yasha gabansa tareda cewa"

Idan dai zakinda nasani kake magana to saidai kayi hakuri ya.....

Kasa fada masa yayi sbd jin nauyin zancen Dan baisan alaqarsu da junaba yanajin nauyin yaji rasuwarsa abakinsa.


Da wani irin zafi JJ din ya zame ya fice duk da dare ne sosai baiyi la'akari da hakanba yanufi qofa Yana neman hanyar fita.

Duk yanda Dr sayyid yaso hanasa fita sbd yanayinda yake ciki yakasa Dole yajawo mota yasakashi Suka fita ya nufi inda JJ din yace masa duk da yagane gidansu Nadiya ne Saidai baice masa komaiba.

Qarfe biyun darene gidan yayi tsit Saidai gidan Babu Wanda yayi wani dogon bacci sbd Sam yanzu ji suke basuda wani dogon tsaro bayan na Allah tunda yaran Zaki suka watse.

Yau hakanan taje dakinsu tayi kwanciyarta bayan ta shimfida rigarsa a jikinsa ta rufe idanuwanta hawaye nabin gefen fuskarta.

Kamar daga sama sama tafara jiyo motsi cikin gida da kamar kuka ta tashi zaune tareda saukowa gabanta na Dan faduwa ta lalubi makunnin wuta zata kunna saitayi tuntube da wani sabon takarminsa data gama ajewa gabanta tayi kallo dazu sai Bata tsaya kunna wutar ba ta lalubi takarmin ta dauka tana dagowa taji kamar ihun iya talatu sai kawai ta bude qofar dakin ahankali ta fito tana tafiya a hankali ta nufi cikin gidan tasa qafarta ciki taji anjawota baya da qarfi tareda toshe Mata baki Dr sayyid yayi saurin haska Mata fuskarsa Yana Dora hannu a bakinsa alamar tayi shiru karta motsa
Saiya haska Mata fuskar Wanda ke riqeda ita tana ganinsa Bata zaro ido saikuma tafara rufewa alamar zata Suma yayi saurin jijjigata Yana cewa"

No no no ba yanzu ki bude idanuwanki.

Jin motsi sukai saurin lafewa bayan qofar soron cikin duhu.

Am dilla na yashigo tareda yaransa daya dama yaransa hudu tuni Suka shigo gidan suka fitodasu zainab.

Kallon tsana ya watsawa su dattiya dako dago Kai sun kasayi kafin ya kalli zainab dake tsiyayar hawaye yace"

Matarsa dama mukazo kashewa kamar yanda mukai masa kashewar wulaqanci yanaci da wuta har ransa ya fita itama zamu Dan Dana Mata azaba kamar yanda muka dandanawa mijinta.

Cikin tsananin kuka irin na uwa iya talatu ta dago ta kalli zainab ta bude baki zatai magana zainab ta gangaro da hawaye tareda girgiza Mata Kai akan karta fada musu ba ita bace matarsa.

Da ido am din yayiwa yaransa ido Suka ja masa zainab din iyayenta na kuka suna riqeta sukaqi sakinta
Ba Imani yasa kan bindiga ya bugi kan dattiya take ya yanke jiki agurin bayan kansa na jini.

Iya talatu kuwa kuwa duka sosai sukai Mata itama ta suma agurin suka ja zainab din daki sudai su Nadiya zai qarar bindiga sukaji

Batasan sanda ta qwace da guduba ta tareda qwalla qara a mugun firgice dukkaninsu su am din suka fito yace"

Akwai wani a gidan ku kamosa wlh akashesa a duk inda aka cimmasa kuyi sauri.

Da gudu su JJ Suka jawo Nadiya ganin zata kawo musu matsala yasa JJ daukarta tsaf Suka gudu ko mota Basu tsaya shigaba sbd zaa iya ganinsu.

Gudu sukeyi sasai Basusan Ina suka saka qafafunsu ba har Suka bulla titin bayan layin sai kawai suka hango wata mota tafe a guje da sauri Dr sayyid ya Kara saura kadan motar tabi ta kansa akai saurin taka burki.

Direban moyarne kawai ya fito tun baiyi maganaba Suka fada motar shima ganin haka yashiga Suka figa da gudu.

Wani airport suka nufa Saidai suna isa jirginda Wanda ke cikin motar zaibi yariga ya tashi ahankali Wanda ke cikin motar daga baya basuma wani luradashiba sbd Dr sayyid agaba yafada JJ ne dake daukeda Nadiya Suka fado baya.
Cikin wata irin kwantacciyar murya ya bude baki yace"

Muje side nabi private jet.

Dukkaninsu atare suka kallo gefen quryar motar daga baya Jin muryarda Basu taba tsammaniba Saidai ganin Mai muryar yasa dukkaninsu sake dauke wuta sbd tsantsan kamanin Zaki da muryarsa dake gabansu Saidai wannan shi dattijo ne Sosai Amma duk da darene Kuma cikin tsananin tashin hankali suke suna iya hango hutundake tattaredashi.

Nadiya da tuni dama ta suma JJ dashima dinkin ciwonsa ke jini sosai yakejin wata irin muguwar azaba ya girgiza da qarfi Yana kiran sunanta daqyar cikin dauriya
Jin Abu Mai dumi na bin jikinsa da alama Kuma daga jikinta abin ke fitowa.

Shafo na jikinsa yayi ya dago hannunsa yaga jini gabansa yayi mummunan faduwa ya kalli Dr sayyid dashima yashiga sabon rudu yakasa magana kafin shima yasake bude baki idanuwan JJ din Suka fara rufewa duk jarumtarsa da daurewar dayake abin yaci qarfinsa haka idanuwansa Suka rufe ya some a gurin.

Dr sayyid ya juyo gabaki daya bayan tareda riqo hannun JJ yaji pulse dinsa cikin sauri yasaki ta lalubo hannun Nadiya ya riqe yanajin pulse dinta ya dago da sauri ya kalli mutumin cikin tashin hankali yace"

Sir she's pregnant Muna buqatar zuwa asibiti cikin gaggawa idan munason tsayarda bleeding din.

Cikin tsananin zafi da bacin rai tareda wani irin radadi dake fita muryarsa da fuskarsa yace"

Kozaka rasa ranka you better save this baby sbd laifinka da sakacinka sunyiwa rayuwata mummunan illa sayyid hw cud you ever hide this from me bayan kasan Mena turoka kayi Amma kabari na rasa the most precious thing a duniyar,,,I will never forgive you for that sayyid...

Kai tsaye yacewa driver muje side din a Daren nan zamubar qasarnan idan munshiga jet you better stop the bleeding.
#MAMUH.*_ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*


*_Mamuhgee26_*
Murya na rawa da Rashin gskia tareda fargabar halinda nadiyar ke ciki Dr sayyid ya bude baki yace"

Sir bazamu iya barin qasa a wannan halinda take cikiba Dole Ina buqatar Bata wasu injections yanzun nan.

Wani kallo ya watsa masa cikin tsananin zafi da tafasarda zuciyarsa keyi masa na Rashin dansa qwaya daya tal a duniya batareda sun haduba ya danne bacin ransa sbd kar ayi biyu ya rasa dansa yazo ya rasa jikansa Kai tsaye yacewa driver suje gidan Dr sayyid din.


Cikin qanqanin lokaci suka Isa gidan Saidai sanin yabaro motarsa acan su am zasu iya ganowa su biyosa gidansa sai yafito motar da sauri ya shiga gidan yafara tattaro duk wani abin buqatar Mai mahimmanci tareda passport dinsa da takardunsa tareda magunguna da allurai ya fito da sauri Suka wuce.

Cikin motar jikinsa na rawa da sauri ya hada ruwan injections yayi Mata guda hudu sannan ya hada na JJ shima da sauri yayi masa Saidai shi Yana yimasa ya farfado Yana sakin wani gurnanin nishin azaba Yana qoqarin bude baki yana tambayar ya Nadiya.

Direct airport suka nufa cikin qanqanin lokaci akai cuku cuku sbd girma da kudinsa sukabi flight din tsakiyar Daren zuwa Lagos.

Bayan sallar asuba har gari yayi haske suka sauka Lagos wata qatuwar baqar jeeb tazo ta daukesu ta private exit inda Babu Wanda yagansu suka bar airport.

Wani qatoton mansion daya ninka na Dilla dasuka sani kusan so biyar Suka shiga Saida suka wuce gate uku kafin Suka Isa main harabar gidan Dana tun acan Sukayi ordering nurses guda uku Mata daga Primus private hospital atake cikin gaggawa aka shigada Nadiya sbd har lokacin Bata farko ba Saidai bleeding din ya tsaya gabaki daya.

JJ ma ciki akayi dashi duk da ya farfado Bai iya tsayawa miqe sbd gefen cikin nasa.

Securities ne suka budewa Mai gidan qofar mota sai alokacin yafito fuskarsa Babu annuri ko daya ya wuce Yana amsa gaisuwarsu da Kai yayi ciki.

Direct qaton bedroom din dake palon ya nufa inda aka Kai Nadiya saidai Bai shigaba ya tsaya tsaye tsakiyar palon Yana kaida kawo cikin wani irin tsananin bacin Rai na shekaru dayake zaburo masa,

Tabbas sbd kada dawowarsa ga dansa yazamo ha'dari ga rayuwar gidansu gabaki daya yasa ya boye kansa ya nesanta kansa da dansa dayasan haka zata faru tabbas daya fito sunyi gaba da gaba da dikko.....

Sir""

Sayyid yakira sunansa cikin sanyin murya kansa a Dan sunkuye cikeda ladabi ya dago ya kallesa murya cikin sanyi yace"

I'm really sorry sir,
Munshawo kan matsalar Nadiya the baby is safe now komai yayi normal insha Allah she just needs to rest Saidai a yanayinda take ciki gskia I can't assure the safety of the baby sbd her BP is very high.

Kallonsa yayi tsawon mintuna kafin ya juya yayi palonsa ya zauna cikin Dan 'dacin rai yace"

Jabeer fa???

Shima insha Allah namasa wani dinkin Nanda 48hrs zaiji sauqin zafin gurin sosai.


Sayyid tell me meyasa ka boyemin abinda ke faruwa???

Gyara tsayuwa yayi cikin jimami da takaicin tsananin damuwar dayake hangowa ga mutuminda yazamo tamkar uba agaresa yace"

Sir dama koda nagama bincike Nagano Zaki shine Wanda muke nema nayi maka email na hotunansa da duk bayanai na yanayiwa dikko aiki to alokacin ne yazomin da buqatar nemawa Nadiya lafiya Kuma abinda yasa muka buqaci kudi daga garesa masu yawa sbd munyi tunanin hakan zaisa yaje ya nemi aikiyi da kansa Wanda nasan samun aikin zaisa yadainawa dikko aiki Saidai abinda bansaniba shine yanda yasamo kudin Kuma aranarda akayi aikin aranar koma menene yafaru yafaru lokacinda labari yafito ankamasa da yiwa qasa sata aranar naje Naga IG nabasa 1million akan case din sbd banasonma kaji hankalinka zai tashi Kuma hakan zaisa ka bayyana kanka Wanda lokacin daka tsara hakan baiyiba tunda akwai gabar da kake jira ka bayyana kanka,

To abinda yabani mamaki shine yanda wuta ya tashi a Daren Kuma babban abin mamaki da zargi shine IG yacemin a Daren dama sukai planning sakin zakin Saidai kafin su Isa wutarne takama and unfortunately......shiru yayi yakasa qarasawa ahankali ya furta"

Kayi hakuri Allah yaji qansa....

Miqewa yayi Bai tsaya sauraron sauran bayananba ya haye stairs Dan kuwa wata irin masiface dikko ya takalowa kansa shida familynsa Bai saniba.

Acikin Daren washe gari ta farka da wani irin tsananin ciwon Mara da zabure zabure Wanda ya tsorata nurses din da sauri Suka dauki waya suka Kira Dr sayyid hankali tashe ya qaraso nan suka hau dubata Yana addua da fatar shock dinda tashiga karyayi affecting babynta da lafiyarta sbd shock ne da high BP suka hadu lokaci daya.


Har asuba suna Abu daya daqyar yashawo kan matsalar yayi Mata allurai tayi bacci.

Dafe goshinsa yayi cikin tsananin tension yake kallonta kafin ya kalli nurse din yace"

Please after 30min give her antropespines.

Ok Dr ""tafada itama cikin tausayin Nadiyar.

Fita yayi yaje dakin JJ shima Saidai shi yaji sauqi sosai Saidai wani irin fushi da zafi dake cinsa Sam jijiyoyin jikinsa Dana kansa sun firfito Wanda har fushinsa ke bawa Dr sayyid tsoron irin burin fansar dayake hangowa a idanuwan JJ din.


Cikin nutsuwa da tsananin kwarjini Mai gidan ya shigo dakin JJ din Dr sayyid na bayansa tareda Mai aiki data shigoda abinci cikeda tray ta aje a bedside drawer ta juya ta fice.

Kallonsa JJ keyi Babu ko qyaftawa sbd ganin zallar kamanni da kwarjini irin na sarkinsu dake tattareda mutumin,

Baya tantama wannan shine mahaifin sarki sbd dama zakin baida tabbacin shin mahaifinsa mutuwa yayi kokuwa da gasken shi Dan fyade ne kamar yanda so dadama yake tsintar zancen gurin kawunsa,

Baitaba tambayar mahaifiyarsa ba waye babansa harta rasu sbd zaizamo tamkar cin fuskane agareta shiyasa yacire maganar aransa Koda shidin Dan halak ne ko sabanin hakan wannan tsakanin mahaifiyarsa ne da mahaliccinta.


Irin kallonta JJ ke masa yasa ya matso gabansa tareda miqa masa hannun ahankali ya furta"

*_ALHAJ ALEEYU NEYO NOAH_* Congress man starling city United States of America,Kuma nine mahaifin marigayi aliyu haidar Zaki.

Jajir idanuwan JJ sukai ya rintse ido suna qara yin ja jijjiga Kai Yana son daure kukansa Saidai Sam ya kasa durgushe qasa tareda sakin kukan mutuwar zakin dake hura wuta a jinin dake gudana cikin jikinsa tun Daren jiyan.

Ahankali jikinsu yayi sanyi cikin dauriya Dad din yace"

Fitar duka zakaji sauqi duk da nasan dikko yayi Mana gibi Mai girma a rayuwa da bazamu iya cikewaba tayin ajalin Zaki.


Kuka sosai JJ yayi Amma Sam yakasa Jin abinda ya tokare masa ya fada ya dago da qyar yace"

Har abada abinda nakeji gameda mutuwar sarki bazai fadaba sai ranarda Naga qarshen zalinci da mummunan qarshen dillas gabaki dayansu.

Juyawa dad din yayi shima cikin danne nasa fushin yace"

Qarshensu na zuwa jabir karka damu,
Zan mayarda rayuwar dikko shafaffiya a tarihirin masu arziki,
Zan mayardashi mabaracinda ko suturar sawa baida ita ajikinsa insha Allah.

Miqewa JJ yayi yace"

Dikko,zeel,am nayi alqawarin ganin na mayarda asusun arzikinku daga zero me yawa zuwa zero daya tal.
Yanda kuka cutatardamu cikin zamba da aminci ta fuskar amintaka ahaka zan cutatar daku ta fuskar zamba da aminci.

Kallonsa dad yayi cikin jinjina Kai tareda qaunar JJ din sbd tabbas yaji dukkanin bayanin irin so da qaunarsa Zaki kewa JJ tamkar jininsu daya.

Ya rasa 'dansa Saidai dukkanin abinda dansa zai masa yasan magajinsa sai masa,
Yayi alqawarin saiya zubarda dikko ta hanya mafi ciwo da zafi Dan haka alqawarinsa na nan,
Shida JJ burunsu dayane.



Lokacinda Nadiya ta farka sosai hankalinsu ya tashi sbd dai a iya bincike da abinda Dr sayyid ya binciko shock din ya taba qwaqwalwarta Dole a mayarda ita asibiti.

Hankalin dad da JJ yayi matuqar tashi nan dad din yasa aka fara cuku cukun nemar musu visa Dan kaita asibiti anan is very risky dikko ya wuce duk inda ake tunaninsa zai iya ganonsu.


Cikin sati guda komai ya kammala Suka daga zuwa US a starling city Suka sauka nan akai asibiti da ita gashi abin yafara taba lafiyar cikinta Dole Suka tattara komai suka aje Dan ganin tasamu lafiya gashi dukkaninsu kowa Yana tsananin qaunar cikin basason abinda zai samesa.

Sannu ahankali likitocin qwawqwalwa suke ganinta ana Bata allurai da magani tun abin na hauka sosai saigashi tafara dawowa normal Saidai idan abin yatashi Babu sauqi hauka takeyi sosai tana ihu da Kiran sunan Zaki da zainab wani lokaci hardana babanta.


Ahaka dai Suka Mata transfer zuwa wata babbar asibitin psychiatrist dake Amsterdam inda Sukayi admitting nata ganinta sai wata wata.

Ba yanda suka iya su dad haka Suka hakura Suka barota Saidai kulawarta daban take ta musamman ce sbd cikinta da harya fara tsufa Dan

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login