Showing 66001 words to 69000 words out of 73969 words

Chapter 23 - BURI DAYA Hausa Novel

Mahmugee   

08 Oct 2024

20458

rahama da yafiyar ubangiji.

Wanka nadey tasata tayi tabata Kayanta tasaka tasata tayi sallah takawo Mata abinci da kanta ta zauna ta ringa Bata taci abincin sosai tabata maganin ciwon Kai tace ta kwanta tayi bacci.


Kitchen takoma ta hada masa simple thai salads da white rice ta hada a wani openwood basket Takoma daki tayi wani wankan ta saka dark grey fitted Arabian gown ta saka half hijab da iyakacinsa wuyanta Wanda ma na baby z ne da kawu ya siyo Mata su doxin guda kala kala Wai jikarsa bazata takura karatu cikin gida ita kadaiba da kansa yasata islamiyar anguwar shike kaita shike daukota suna tafe a hanya riqeda hannunta suna fada
kullum haka suke zuwa da fada su dawo da fada gashi ya Hana asata ta nesa da gida babba yace aa bazai dauki dukaba gwara nan kusa suna dukanta zaikama hanya yaje yaji cikakken bayani Kuma duk malaman yasansu a gabansa Suka tashi yasan uwayensu tsaf zai tariyo musu asalinsu idan Suka Dakar Masa jika sabanin can idan ankaita dogon turanci ma bazai iyaba bare larabci da yanxu alee idi yace sufara zaman karatun tsakanin magriba zuwa ishai shinefa mal zailani ke musu yanxu Kuma ba laifi suna ganewa Dan kuwa dama suna danda ilimin addininsu dama nemane ya Hana karatun.


Batai knocking ba ta bude qofar tashige tareda rufowa ta nufi dining ta ajiye abincin ta shiga kitchen ta dauko ruwa da lemon mix dinsa da baya rabo dasu ta ajiye a dining din tareda plates da cup duk saidata gama jeresu kafin ta nufi bedroom dinsa tana Dan dafe gabanta dake bugawa sbd abinda ya faru yau da safen.

Kai tsaye tashiga bedroom din saitaga da Dan duhu kadan sbd komai a kashe yake.

Gadon ta kalla tagansa kwance Yana bacci dagashi sai dogon wando Babu riga a jikinsa tabi jikin nasa da kallo tanajin 'yar fargabar yanda zata ringa fama da wannan maji qarfin sbd jikinsa a bude yake alamar qarfi gashi haryanzu yakasa daina geaming shiyasa muscle dinsa ke sake budewa.

Cikin sanyi ta zauna bakin gadon tareda dafa kansa ahankali ta tana shafawa tareda Dan sakar masa iskan bakinta me dumi a kunnensa.

Wata irin kasala ta sakar masa da hakan datayi Saidai Kuma zuciyarsa har lokacin radadin alaqarta da am yakeji ya tsuke fuska batareda ya bude idanuwansa ba yace"

Kije banason hayaniya please.

Wat???""""tafada cikin tsananin mamaki da haushi.

Zatai magana ya bude idanuwansa ya Dora akanta take takasa maganar tafara rawar murya tana inda inda

Ganin yasake zuba matasu gasu da alamar baccin dake cikinsu yaqara sauyasu taji duk duniya Babu abinda tafi son kasancewa dashi yanxu kamarsa
Tanason narke masa yadan lumshesu yasake sauke Mata take ta miqe jiki amace ranta na zafi ta fice tana ayyanawa aranta bazata sake dawowaba saiya nemeta da kansa.
#MAMUH._ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee44_*
Tana komawa Kai tsaye daki tashige ta kwabe hijabin ta zauna bakin gadon tareda dafe kanta tana Jin kamar ta fashe da kuka.

Yau da itama 'yar uwarta nanan data Bata shawarar yazatayi sbd batasan yazata iya handling Zaki ita kadaiba ba shawara.

Dataji takasa sake miqewa tayi ta nufi gaban wardrobe tahau cire rigar tanajin damuwa sosai cikin ranta.

Wata Morocco gown tasaka Mara nauyi ta zo gefen fammah data samu baccin wahala ya dauketa ta kwanta tana mayarda hawayen dake ciko idanuwanta.

Sam batasan meyasa yanxu jituwa na neman qaranci tsakaninta dashiba.
Ahankali ta furta"

Allah yaji qanqi zainab yasa aljannace makomarki.

Tun tana tunane tunane har baccin qarfi da yaji yayi gaba da ita.

Sai yamma ta farka kusan lokaci daya da fammah nan Suka miqe atare nadeyn na 'yar miqa da hamma tace"

Fammah ya jikinki?
Hope you're feeling ok now??

Kallonta fammah tayi tareda qoqarin maida hawayen dasuka ciko idonta ta bude baki ahankali tace"

Alhmdllh I'm fine now.

Sake kallonta nadey tayi cikeda tausayi tana tuno gata da Jin dadin da fammah ke rayuwa aciki.

Matsowa tayi ahankali tareda kamo hannun fammah din cikin kulawa tace"

Fammah insha Allah life will become colourful again idan kika rungumi hukunci na qaddaran da Allah ya doro Miki.

Akaro na farko ta qaqalo murmushin yaqe tana qoqarin sake sakawa kanta da zuciyarta nutsuwa yace"

Allah yabani ikon jurewa nayiwa familyna adduar yafiyan ubangiji.

Amin suka furta kusan atare suna kallon juna cikin qoqarin sakewa da junan kamar da can.

Fammah dince tafara miqewa tana cewa,

Bari nayi alwala lokacin sallah ya wuce Muna bacci.

Da kallon tausayi da Jin nauyi nadey ta bita tanajin zafin yanda fammah din Takoma Kuma itace da babban kaso akan mayarda rayuwarta hakan.

Tana tunani har famman ta fito itama ta miqe jiki ba qwari ta fada toilet din tayo alwala tana fitowa gefen fammah ta tayarda sallar itama.


Tare suka fito palon itada fammah tajata har kitchen tana qoqarin ganin tasakata tasake jikinta da gidan sosai sai niyar datayi ta Dora fammah din akan rayuwarda zata koyi komai na bangaren addini Dana zaman rayuwa tareda koyan ayyuka.

Tuwon semolina Suka tararda fadime na kwashewa cikin Leda takalli tuwon tana cewa"

Abincin da uncle din baby z yakeso.
Shine yace adafa masa?

Ta fada tana kallon fadime cikin Rashin Jin dadi.

Aa alhajine keson tuwon masara shine akeyi Masa wannan din.

Jiki a sanyaye tace"
Ok.

Kallonta fammah tayi tana Yaba sa'a irinta nadey.,

Bebiyar datayo rayuwar qunci da Rashi da maraici abaya Amma yanzu itace cikin gata da niimar ubangiji Wanda sukuma dasukayo rayuwar gata,yanci,Jin dadi da mulki yanzu Kuma sune suke neman taimako da dauki daga waccan bebiyar,

Ayau namijinda kowace macen datasansa ke fatar ganin yasota Ko kulatama shine bayaji baya ganin kowa agabansa sai nadey.

Ya Allah ka gyaramin rayuwata koban samu gata da niimar nadey na nasamu wadatar ilimin dazai sadani da rahamarka,iliminda zai Kai rahama kabarin mahaifina da rayuwar mahaifiyata data Dan uwana.

Cikin qoqarin kawarda damuwarsa aranta nadey ta nufi fridge ta dauko fruit mix dinda tayi masa dazu da niyar kaimasa da yamma ta dire gabansu tafara Sha tana cewa"

Fadime Gama kwashe tuwon nizanyi miyar nida fammah.

Fammah datai zuru tana kallonsu kamar Mara lafiya takalli nadeyn ahankali Jin abinda tace sbd ita Sam ko ruwan zafi bata taba dorawaba arayuwarta bare girki.

Murmushi nadey tasakar Mata tana daga Mata tace"

Karki damu I'm here,we can do it right????

Kai ta daga Mata ahankali tana qaqalo sakin fuskar dole.

Mix din ta takurata sukasha abinsu sosai suna cikin Sha Kiran JJ yashigo wayarta ta kalli wayar tareda kallon fammah data mayarda hankali gurin jujjuya mix din tanasha ahankali.

Daukar wayar tayi tareda saka handsfree tace"

Yes dady j?

Nadey Kinga Dan Allah ki taimakeni da kawu wlh ya daga hankalina da Kira Wai adawo da baby Wai islamiyya kar a wuceta,Kuma malamai na duka idan anyi fashin zuwa and abubuwa da yawafa ya bayar Ni yau akainama ya qarasa sauke fadan dazu da safe.

Dariya tayi cikin jinjina fada irin na babanta tace"

Dady kawai kakirasa ku daidaita wlh Ni kasan dama a qule yake damu Ina magana zaice mubar Masa gidansa mukoma gurin dad.

Bari nakirasa gskia Ni Zan canza Mata makaranta sbd wancan da kawun keso tayi sunyi lungu da yawa.

Ba ruwana nidai ka nemesa da kanka and pls kar ko sunana yafito aciki wlh akaina zai sauke haushi da fadan.

Kamar daga sama sukaji fammah cikin tsananin sanyin murya tace"

Please kudawo da ita nan I want to see haydars look alike.

Kallonta nadey tayi sbd hakanan zancen yadan kayar Mata da gaba sbd sanin son haydar din ne yasa takeson ganin yarsa.

JJ kuwa tsit yayi tareda son sake Jin muryan sbd Jin yanayin yanda akayi maganar kamar da shagwaba ciki.

Jin yayi tsit yasa fammah din sake cewa"

Please bring her back.

Jin baice komaiba yasa nadey gyaran murya tana kallon wayar tace"

Fammah ce ke mgn dady j.

Wat???yafada ahankali tareda Dan tsuke fuska duk da basa ganinsa Yana daqile wayar sbd takaicinda haka kawai ya kamasa,
Shifa ko gaisuwa baya fatan tasake hadasa da 'daya daga cikin dillas din nan har abada baida wani sauran abinda ya rage yayi dasu.

Su kuwa duka su biyun da ido sukabi wayar kowanne da mamaki.

Mayarda sauran mix din tayi fridge ta bude freezer ta fito musu da Naman rago dayayi qanqara tana cewa"

Ok fammah let's start our soup sbd mugama da wuri.

Ahankali tafara aikin fammah na zaune ta rafka tagumi tana kallonta ita yanzu komai na nadey a burgewa take kallonsa.

Saida aka fara Kiran magrib Suka gama komai fadime tagyara kitchen din Suka fito Suka dawo daki.

Wanka Sukayi tareda alwala sukai sallah suna idarwa tayi qaramin adonta cikin straight Vandana gown fammah kuwa doguwar riga ta zumbula ta bacci wadda take ta nadey din.

Daqyar fammah ta iya daurewa taci abincin sosai tareda nadey a dining sbd gidan Basu wani Saba cin abinci atareba tun da can shiyasa ko yanxu kowa daban daban yakecin abincinsa.

Suna cikin cin abinci suka jiyo muryansa Mai fadar da gabansu duk su biyun yayi sallama qasan maqoshi yashigo palon Yana sanyeda baqar jallabiya data qara fiddo haskensa sosai Saidai fuskar nan tasa a tamke take kamar ko yaushe ba wani Wasa.

Ko inda suke Bai kallaba ya nufi tsakiyar palon Yana gaisawa da iya talatu dake zaune tana kallo itada fadime yace"

Ina kawu yakirani Yana nemana.

Kafin iya talatu tayi mgn saiga kawun yafito daga palonsa Yana daure fuska shima ya zauna tareda sake tsuke fuska yace"

Nakira jabeeru tun dazu akan yadawo da zainabu akan islamiyarta yaqi kawota sbd ya nunamin shine ubanta ko?
To ku sani matuqar Bata dawoba duk barmin gidana zakuyi Dan Banga amfanin aje gardayeba tunda kun karbe yarku.


Cikin sauke murya yace"

Kawu kayi hakuri wlh Ni banmasan ya kukayiba Amma aini to Babu ruwana acikin zancen tunda ka kirasa ainasan zai kawota ko zuwa gobene...

Goben idan yakawota uban waye acikinku zai bita yayiwa malamai mgna kar adaketa.

To kawu ko yanzu yakawota ai Dole sai goben zataje tunda yaudai Kam dare yayi ayi hkr.

Qin sake tankawa kawu yayi ya kalli iya talatu Yana cewa,

Talatu bani abinci kinji.

Hkr zakin yakuma basa kafin ya juya ya fito.

Kiran JJ yayi JJ yaqi dauka sbd yasan ko maganar meye bazai wuce ta maido baby z ba.


Bayan fitarsa wani irin haushi ya maqale Mata a wuya yanda yashigo ya fita ko inda take yaqi kallo.

Miqewa tayi ta wuce daki babanta yabita da muguwar harara yanajin kamar yace subar gidan adaren kowama ya huta.

Zama tayi tana duba wani email da Jasmin tayo Mata forwarding ta laptop dinta har akayi Kiran ishai ta aje tayi sallah tana gamawa Bata sake bi takan komaiba tayi kwanciyarta tana Jin kamar tayita rusa kuka.



Tunda yagama komai yake zaune Yana jiran shigowarta Amma shiru yakalli agogo akashi na ba adadi Yana sake daure fuska sbd takaici,

Tun Rana baici komaiba Yana jiran tazo takawo Masa Amma shiru Kuma Dan raini tayi laifi shine take sakeyin wani laifin akan wani.

Kasa hkr yayi ya dauki wayarsa ya Danna kiranta Amma wayar Bata zuwa.

Sake Kira yayi still not reachable.

Aje wayar yayi tareda rintse idanuwansa cikin damuwa da takaici ya miqe yashiga daki kawai ya kwanta Yana sakin siririn tsakin takaicin shiririta da Rashin tunani irin na Mata.


Dagashi har ita daqyar sukaga wayewar gari tana Gama breakfast ta shirya tacewa fammah ta shirya suje su siyo kayanta na sawa.

Cikin riga da skirt na red super Sheraton Mai golden kadan ajiki tasakata babbar kimono jallabiya akai tareda yin rolling gyalen jallabiyan kawai ta dauki handbag da key din motar Kai baby z school wata 'yar eclass3033 2019.

Fammah kuwa doguwar ash jallabiya tasaka sai qaramin gyalen jallabiyan Suka fito bayan sunyi bankwana da iya talatu akan saisun dawo.


Geaming yagamayi dagashi sai wasu riga da wando na Nike marasa hannu sai hularsu ya hada gumi sosai musamman sbd tsananin bacin Rai da tsananin kewarta daya kwana da ita yasa yakeyi yaqi tsayawa saiga Kiran JJ.

Dauka yayi tareda dakatawa ya miqe Yana cewa"

Saida kagama hadani da kawu kake kirana yanzu.

Dariya JJ yayi tareda cewa"

Gani Nan Nazo ai bawa kawun hkr da kaina.

Fitowa yayi harabar gidan daidai shigowar motar JJ ciki Suma daidai lokacin suka fito kowacce na ganinsu ta daure fuska.

Ita fammah hakanan taji Rashin Jin dadin abinda JJ yayi jiya a waya da akace itace tasan cewa yanajin haushinta da takaicintane sbd ita Dilla ce shiyasa ta dauke Kai tareda Dan kame fuskarta data gansa haydar ma Sam ko ganinsa batason yi yanzu sbd kallon datake masa a mijin nadey Wanda itama tata zuciyar haryanzu tana sonsa.

Nadey kuwa ganin Zaki yasata Dan daure fuskarta duk da tsorone fal aranta Dan taso su fice batareda yasan sun fitarba.

JJ na fitowa motar shima kallo daya tayiwa gefenda suke sbd fammah sai baisake kallonsu ba yace"

Nadey Ina zaku this early morning????

Mota ta nufa tana tsuke fuska zatai magana sukajisa yace"

She's goin no where.

Kallonsa fammah tayi ya kalleta shima fuska a daure take gabanta ya fadi tafara neman rikicewa Kai tsaye yace"

Ina zaku??

Kallon nadey data sake daure fuska cikin takaicinsa na yanda ya tsare fammah da ido gashi duk muscles dinsa a bayyane tace"

Dama she's taking me to....

To where????yafada cikin 'yar tsawa sbd ransa dashima yagama baci sbd kallo daya yayi Mata yaji zuciyarsa na quna da kishi.

Kayan sawa zata siyamin I don't have any clothes....

Wani mugun kallo ya watsawa nadeyn data fara saduda sbd ganin fushin dake kan fuskarsa ta dauke Kai da sauri tana Dan gyara tsayuwarta.

Kallon JJ yayi Kai tsaye yace"

JJ Kai fammah din asiyo Mata kayan wannan Kuma let me put some sense into her"""yafada tareda fizgo hannun nadiyar ya nufi part dinsa da ita.

JJ kuwa kasa motsi yayi Yana takaicin wannan yawon banzan dazai fitayi bayan shi gurin kawu yazo Dan yasan idan baizoba yau Babu abinda zai Hana kawun Isa can gidan.

Batareda ya kalleta ba ya nufi mota ta biyosa abaya jiki sanyaye sbd taga yanda qiri qiri Rashin Jin dadi ya bayyana a fuskarsa.

Jiki ba qwari tashiga motar yaja da speed yabar gidan.

Suna shiga palonsa ya saketa ya juyo da wani irin fushi zaiyi magana cikin tsananin bacin da sauri ta hanasa ta hanyar fadawa jikinsa ta qanqamesa sbd tsoron karya mammareta.
#MAMUH._ZAFAFA  BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*

*_Mamuhgee45_*
Kasa wani dogon motsi yayi sbd yanda ta cukuikuye acikin jikinsa sbd tsoro da shakkarsa Daya bayyana atareda ita Tana sake cusa kanta cikin  jikinsa hannuwanta na Dan rawa da qafafunta.
Rintse idanu yayi ahankali yanajin dumin hannuwanta na kashe duk wani fushi da bacin ran daya shiga lokaci daya,

Ajiyar zuciya ya sake ahankali tareda kasa cewa qala sbd jikinsa dake neman saki ya saka hannuwansa biyu ya dagota ahankali yana kallon fuskarta cikin yanayi na nuna ikonsa yana basarda yanayinda sonta yagama jefasa ya kalleta da idanuwansa dake sake daga hankalinta cikin basarwa da iko yace"

This should be the last time dazaki sake gwada irin hakan,
Next if you try me again saina karya qafafuwanki da hannuwanki and I mean it kinajina ko???

Dan dagowa tayi da kanta ta kallesa Tana sauya fuska kamar zatayi kuka ta juya cikin haushi zata bar gurin ya fizgota saidata tsorata takallesa da sauri.
Cikin kallon cikin idanuwanta yace"

Ina mgn shine Zaki wuce kina fushi???

Hawayen datake riqewane ta bari Suka gangaro mata ta kallesa tareda sake barewa da hawaye tace"

Naji bazan sake futan ba shikenan Ina?

Yanda tayi yasa jikinsa yin sanyi yaji ransa na dacin yanda take tsiyayo hawaye.

Fuskarta ya quraw Ido yanajin dacin ransa na qaruwa.

Ahankali ya sake jawota jikinsa sosai yana riqo hanuwanta cikin nasa yace"

To this guntun hawaye da akeyi sbd a gasani ya Isa haka its killing me inside so please ya Isa Nima naji bazan sake fada haka sosaiba ok???

Wasu sabbin hawayen ta sake matsowa cikin son sake rikitasa tace"

Yafi shekara shida da kake cewa saika karyani nidai na.....

Hannu ya Dora kan bakinta yana kallon cikin qwayan idanuwanta ya dauke gira Daya yana sakin murmushinda bai Gama kama fuskansaba yakai bakinsa kunnenta ahankali yace"

Zan karyaki Amma ba irin wancan karyawanba wannan is very special karyawa irin na lokacin samun cikin baby z.....

Zaro Ido tayi da qarfi tareda turesa Tana sakin murmushi da gudu zata tsere ya damqota tareda dawo da ita yace"

Heyyy miss Noah aikin Riga kinshigo sashenki kenan keda shiga can Sai idan kinje gaidasu kawu Kuma sbd inason raba fadan kawu da dad akan baby z soon ta hanyar Basu kawo musu wani Sai araba gardama and this time Zan ringa ban ruwa ga shukatane Dan tayi kwari da kyau tasamu Ingantacciyar yalwa....

Cikin ihun kunya Tana qanqamesa tace"

Please stop mana ko nafadawa babana what your plans are na zaka lalata Masa 'ya.

Dariya yayi tareda dagata sama yana cewa"

Basaikin fadaba nida kaina Zan nuna Masa tunda ke kikeson a rikitasa yana zamansa.

Aa Allah kasan Kaine kakeson neman maganarsa idan baka dainaba mijin baby z zai ramawa babana wata Rana.

Cakularta yayi tayi zillo ta fado daidai kan gado Tana dariya Tana shafa gurin tace"

Mena Maka to ai gskia ne nafada daga bawan Allah yaji qan ka yabaka yarsa Sai neman rabasa da zaman lafiyarsa kake nidai daga yanzu bamai sake tabamin uba ya hanasa sukuni.

Rigar jikinsa ya zame yana cewa"

Hmmmn.

Jikinsa ta kalla ta Dan juyar da Kai Tana Jin gabanta na Dan faduwa kamar tsoro zai kamata.

Saukowa gadon tayi Tana zame kimonon saman kayanta tasaka closet Tana Dan Fara gyara dakin duk da baiyi komaiba Amma amatsayinta na matarsa gari ya waye ya tashi Dole ta gyara Masa shimfida.

Wanka ya shiga yana sake gyara daurin towel dinsa.

Yana shiga ta saki ajiyar zuciya ta Dan kalli qofar bayin tareda sake ajiyar zuciya kafin taci gaba da aikin gyara dakin.



Tafiya sukeyi cikin motar Babu Mai cewa komai
ita dai fammah sbd a takuren datake ko wani qwaqwaran motsi batayi saima Jin datayi gabaki Daya fitar ta fita aranta gida kawai takeson komawa gashi batason ko mgn tayi Masa ganin fuskarsa a daure ya mayarda hankali yana tuqinsa.

Wani qaton mall kawai ya kaita batareda yace mata komaiba yayi paking ya kashe motar ya fito ya tsaya yana duba wayarsa fuskarsa a Dan sauyayyan yanayi ba laifi sbd ganin zasu shiga mutane.

Share siraran hawayenta tayi cikin tuno rayuwarta ta baya da irin gatanta Amma sauyin rayuwa yasa yau itace akewa alfarma wulaqantawa.

Fitowa motar tayi tadan saci kallansa tareda bude Baki cikin sanyin murya tace"

Ko zamu barshi mu koma gidane karna takuraka bansaniba ko kanada abinyi.

Juyowa yayi ahankali ya watsa Mata wani irin kallo dama itama din shitake kallo idanuwansu Suka shiga cikin na

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login