Showing 45001 words to 48000 words out of 73969 words

Chapter 16 - BURI DAYA Hausa Novel

Mahmugee   

08 Oct 2024

20448

din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*


*_Mamuhgee33_*
Fammah dake hawayen baqin ciki ta riqo cikin tausayinta da sigar lallashinta tace"

Karki damu fammah Allah na tare dake.

Kallonta fammah tayi hawayenta na sake gudu cikin muryan kuka tace"

Meyake Shirin faruwa damune????tsakanin jiya zuwa yau komai na neman lalacewa,mun aikata wani Abu ne da muke ganin hakan?????

Girgiza Mata Kai nadey tayi tareda katseta da cewa"

Fammah kidaina fadan haka karki sabawa ubangijinki,
Wannan abin shi ake Kira da fitar haqqi.

Batareda ta wani fahimci maganar fammah dinba Suka dungumo cikin gida dama dad dinsu da am tuni suka dauki mota sukabi Police.

Cikin gidan ganin yanayin fammah yasa tadan nuna damuwarta akanta tana ta sake rarrashinta sbd tabbas fammah bazata iya handling abinda zai cigaba da zuwa ba musamman idan suka wayi gari sun koma zero account.


Acan police headquarter kuwa duk inda su am ke tunanin abin ya wuce nan sbd yanda yau waisu dillas ake qin saurara sai wani kwana kwana suke musu anmaqi Bari sugan zeel din tuni aka qargameta su saima anan suke ganin hotunan gidan mayor din da aka dauko jini ko Ina anyi kaca kaca da Kaya.

Abu kamar Wasa saigasu har kusan yamma anqi Bari suyi komai a kan case din gashi suna jiyo ihunta cikin tsananin azabar da ake Bata tafadi inda gawar mayor da 'yarta suke.

Jin bazasu iya daurewaba yasa Suka tattaro Suka dawo gida jiki amatuqar mace zuciya na matuqar daci.

Koda Suka dawo gidan fammah na ganinsu tasake fashewa da kuka sbd ganin Basu dawo da mum dinba dakuma yanayinsu dake nuna Babu wani sauqi.

Ranarma a Daren Babu Wanda yayi dinner sai nadey dataje kicin ta zauna akan kitchen island taci pancakes dinta da Apple ta koshi Tasha fresh milk da ruwa kadan Takoma sama daki ta tube tayi wanka da ruwan zafi sosai ta gasa jikinta tafito ta shirya cikin sleeping dress fara Mai Dan kauri ta daure kanta da band tazo ta kwanta gefen fammah da baccin wahala ya dauketa tun dazu.


Washe gari tunda safe dukkaninsu suka sake komawa headquarter wannan karon anbarsu su ganta aka kaisu dakinda zasu ganta Suka zazzauna jiran akawota.

Lokacinda aka shigo musu da ita dukkaninsu Saida Suka miqe tsaye cikin tsananin tashin hankali sbd irin mugun dukan dake jikinta gabaki daya ta sauya kamanni idonta daya ko gani bayayi ya rufe gabaki daya sbd kumburin jini hakama gefen bakinta ya kumbura harya juye gefe.

Daqyar take daga qafa tana ganinsu da idonta daya dake gani tafara wani irin kukan tashin hankali tana cewa su ceceta karsu barta cikin wannan halin.

Dukkaninsu jiinsu rawa yakeyi sbd tashin hankali,
Ita kanta nadey din Saida taji wani iri sbd yanayinda zeel din Takoma a kwana daya da yini.

Ko mintuna goma batayiba suka jata tana ihu tana Shure Shure Suka mayar da ita.

Hakan ya sake daga hankalin dillas musamman da anqi bayarda bail dinta kafin shiga court gashi kamar wani hadin baki ko Wainda aka saka azaba suke gana Mata akan ta fada inda gawar su mayor take.


Cikin kwana biyar gidan Babu Mai iya ko Shan ruwan kirku sunkoma kamar gidan mutuwa ko yaushe kowa na palonsa gashi mahaukatan kudi suke saki Amma Sam Babu wani alamar sauqi saisuka fara sakaran case din da saka hannun wasu manyan dasuka fisu sbd duk wata hanyar sauqi an toshe musu gashi Court za'a fara shiga washe gari.


Da daddare yunwa tasa fammah sulalewa ta fice daga gidan cikin motar fammah ta nufi gida tana waya da JJ akan fa haydar ya tsananta wannan alamarin sbd dillas anwayi gari ko abinci rabonda waninsu yaci anmanta Saidai ruwa.

Tana Isa gidan ta tararda Babu kowa daga mum har Annah basa nan tanada key harzatayi amfani dashi ta bude sai kawai ta fasa ta juya kota shiga bazataji dadin ci ita kadaiba batama da tabbacin ko akwai sunyi.

Wani restaurant ta nufa batareda tashigaba tana cikin mota ta bayarda order dinta ta cikin waya tana jiran su kawo mata.

Wayarta take amfani da ita tana turawa dad dinta saqon wasu files data sa akayo Mata forwarding daga Noah's tanason yasake duba matasu dakyau.

Dan dagowa tayi sai kawai ta hangosa tafe tayi saurin lafewa cikin motar batareda ya lurada itaba ya bude motarsa dake kusada tashi ya fada yabar gurin Bata tsaya komaiba ta buga tata tabisa sbd id card dinta datakeson karba.

Ahankali ya lurada motar na binsa sai yaqara dubawa yaga tabbas motar fammah ce yaja wani siririn tsaki tareda parkawa Yana fitowa itama tana kawowa saura kadan su hadu da juna tayi saurin yin baya daidai wata mota takawo aguje kan titin yayi saurin fizgota ta fado jikinsa ya Mata kyakkyawar runguma akaro na farko jikinsu ya hadu sosai.

Rawa jikinta yafara numfashinta na fita da mugun sauri jin jikinsa anata yasa hankalinta yasake tashi tafara girgiza kanta da qarfi tana cewa"

No no no ba jikinsa bane,
Wannan jikin ba nawa bane yanayin sukeyi,,,,no no I'm only imagining ne....
Qwacewa tayi da qarfi hawaye na ballewa daga idanuwanta sbd zuciyarta dake neman rudata dajin jikinsa kamar na zakinta,
Meyasa takejin kamar jikin zakintane komai da komai.


Juyawa tayi da gudu hawayenta na tsananta tafada mota da mugun gudu Wanda ya daga hankalinsa sbd yanayin yanda taja motar komai zai iya faruwa.

Bin bayanta yakeyi da gudun shima Saidai kasancewar ta roughrider ce sbd a college suna zuwa wasan race da motoci Wanda Annah ce keda son hakan sai itama abin yashigeta.

Tana zuwa gidan ta shige da motar da wani speed tayi parking ta wuce ciki da gudu har lokacin kuka takeyi.

Wani irin numfashi Mai zafi yasaki zuciyarsa na wani irin radadin zafi,
Ako wace safiya yatashi da ciwon zuciyar rashinta yake tashi dashi yake rayuwa,

Tsawon shekarun nan baitaba farin ciki Kona seconds neba sbd rashinta ataredashi Saidai dolene ya boyewa kowa kansa sbd samun zamansu safe har yagama Dora kowa a matsayin daya kamata.

Jan motar yayi da gudu shima ya wuce Yana Jin nauyin zuciyarsa yau Yana qaruwa.

Ya gaji Dole yagama komai cikin qanqanin lokaci yana buqatarta akusa dashi.



Ita kuwa kukan Rashin zakinta tayi sosai acikin Daren kafin tayo alwala tazo tayi sallar nafila tafara jero masa addua shida mahaifiyarta da ummansa.

Yau har wata sabuwar kewar babanta ta taso Mata
Tsananin qaunar ganinsa ta taso Mata takasa hkr ahankali ta lalubo wayarta ta Danna Kiran Dr sayyid.

Yana dauka ta tasaki ajiyar zuciya ahankali tace"

Babana Dr Ina yawan tunaninsa cikin kwanakin nan I hope canjin damuke buqata ansamesa I can't continue hiding Ina son ganinsa wlh.

Ki kwantarda hankalinki nadey babanki ansamu cigaban da akeso sbd yanxu yafara Sanaa Kuma ba laifi Naga ta karbesa sosai kayan fruits yake siyarwa ammafa wani lokacin shike zama yasha kayansa saiya qoshi.


Murmushin Dole ne ya subuce Mata Jin halin baban dai yana nan kawai dai qila kwantawa yayi sbd yanayin rayuwa.

Cikin Jin dadin babanta nanan da halinsa na ban dariya da takaici tace"

To Dr inaga tunda yasan amfani Sanaa yanxu zaka iya bashi kudinda kace Yaya Zaki yabaka.

Kinaga lokaci yayi kuwa?

Eh kabasu kawai aisun wahala ba laifi zasu tanada yanxu nasani.

Ok to insha Allah zanje nakai masa.

Harzai kashe murya cikin tsananin sanyi tace"

Dr idan zaka bashi ka dauko min fuskarsa inason ganin farin cikinsa Dan Allah.

Murmushi yayi yace""

Insha Allah.

Tana kashe wayar ta share hawayen tausayin babanta da iya kafin ta miqe ta kwanta a darare sbd gobe sunada zuwa court.


Washe gari dukkaninsu da sanyin jiki Suka tashi har itama din Saidai ita nata daban ne.

A mota daya suka isa court din am ne ke tuqi sai dad da fammah a baya ita agaba cikin wata baqar jeeb Mai daukan ido.

Motarsu na tsayawa Yan media Suka zagayesu ko gurin fitowa Babu Saida securities sukazo suna tutture musu su suka samu fitowa ana karesu Suka samu shiga Court din.

Zamansu bada jimawa ba haydar ya iso kotun tareda securities dinsa biyu ya qaraso gurinsu ya miqawa dad din hannu Yana jajanta masa hakama am fammah kuwa narke masa tayi yadan saki fuska kadan Yana cemata karta damu komai zai daidaita kowa zaisamu abinda yayi deserving.

Satar kallonsa tayi Suka hada ido da ya zuba Mata idanuwansa take tafara kame kame tana hadiye yawu daqyar.

Ahankali ya mayarda idanuwansa kan 'dan space dindake tsakaninta da am wanda dashi gwara Babu.

Ya dauke kai Yana murmushin dashi kadai yasan mezaiyi.

Shigowa akayi da zeel data sauya kamanni gabaki daya cikin sati guda nan aka fara shariar Saidai Sam Babu haske ga dillas saima qara zurfafa zancen keyi ana bankado wasu asiransu Wanda yafara Basu tsoro da mamakin ya akai suke fitowa.

Ranar haka aka tashi court din Babu wani sauqi Suka nufo gida.

Kamar Wasa saiga shariar na tsawo ankasa samun wani taqamaimai dogon sanin inda zeel takai gawarsu meyo gashi dukkanin evidence suna nuna itace tayi kisar nan kotu kawai ta yanke hukuncin arufeta gidan yari tsawon shekarunda zata fadi Ina gawarsu take.

Ihu zeel keyi tana kuka tana Kiran dikko da am su taimaketa karsu Bari akaita prison wlh Bata kashesu mayor ba ita batama San gidantaba haka aka tafi da ita tana kuka tana riqe fammah dake kukan itama kamar ranta zai fita.

Am ma da dad din hawayene kawai basuyiba Amma dukkanin hankalinsu ya tashi idanuwansu duk sun Kade zuwa jajir ga uwar dukiyar dasuka zubar a wannan case din.

Nadey ce riqeta fammah harsuka nufo hanyar gida saigashi aka Kira daga office Kiran gaggawa.

Office din suka wuce gabaki dayansu inda suka tararda wani babban tashin hankalin Yan press ne cikeda gurin suna isowa sukayo gurinsu suna musu tambayoyi Wanda tambayar daya daga cikin Yan media din yake cewa"

Ance kun siyarda gabaki daya shares dinku na Dilla empire da kamfanin gabaki daya harda gidan dakuke ciki yanzu ga Wainda suka siya nan sunzo zasu karbe shin mezaku ce gameda hakan??????

Cak dukkaninsu Suka tsaya cikin mamaki da takaicin Jin abinda ake cewar,
A fusace am ya turesa tareda marinsa Yana cewa"

What rubbish.....

Hakan da yayi yasa Yan media harzuqa Suka ringa daukar abin suna qarfafa yadawa har marinda yayiwa Dan press din.

Basu yardaba Saida Suka Kai cikin building din Suka tararda lauyoyi da ma'aikatansu cirko cirko ga hukumar qasar cike suma ana jiran isowarsu.


Takarda lauya ya daga ya miqawa Dilla Yana cewa"

Ga takardar dake nuni da client Dina ya siya dukkanin shares dinku ga saka hannunku nan ga nasa ga namu lauyoyinsa na shedu ga Kuma stamp na Court so munxo karban ragamar kamfanin ne da komai.

Ko gama karantawa Dilla baiyiba ya baya zai zube am yayi saurin riqosa tareda fixge takardar ya karanta yayi wurgi da ita Yana cewa"

Qaryane Babu Wanda muka siyarwa komai mundaiyi investing kuma......

Katsesa dayan lawyern yayi da cewa"

Ba haka bane Mr am Dilla inaga tun farko idonka ya rufe baka karanta waincan takardunba dakayu Amma hakan shiyake a rubuce.

Kallon lawyern yayi tareda kallon takardar da sauri ya tuno ranarda ya karbo takardun zasuyi signing zai karanta nadey dinsa tashigo tace saiyazo sun fita da sauri yanda ta matsa masa tadau hankalinsa yasa Bai tsaya karantawaba yayi signing Yana fitowa yabawa dad shima yayi ya fita dasu daga gurin shaqatawarsu yaje yakai takardun kotu aka saka shedar kotu.

Dafe kansa yayi tareda durqushewa qasa Yana neman haukacewa...

Miqewa yayi da sauri tareda cakumar lawyern dayafi zubo maganganun Yana cewa"

Qaryane wannan abin zagon qasa ake mana,
Wakeson ganin bayanmu,
Idan mun siyar Ina kudin suke toh?????
Nace Ina kudin suke??
Waye keson ganin bayanmu?????


Daga bayansa yaji ance"

Nine.

Dauke wuta yayi tsawon seconds kafin dukkaninsu Suka juyo baisan lokacinda yayi baya da sauriba Yana neman faduwa bakinsa dake kumafar yawun tashin hankali da masifa a sake.

Dilla ma dibis yayi faduwan Yan bori suna kallonsa daga qasa zuwa sama.

Sanye yake cikin wasu irin designer suit black na kamfanin rugbay sai wasu amneelaurenzo cover dinsa yayi kyau harya gaji sai agogon diamond Rolex dake hannunsa Yana kallonsu ido cikin ido.

Duk da tsananin canzawarsa ga wani irin building muscles dayayi hakan Bai sauya musu kamanninsaba.

Cikin wani irin tashin hankali da fargaba dad din ya miqe ya cakumo am tareda daukarsa da wani irin mummunan Mari a haukace yace"

Dama baka kashe JJ ba kabarsa bayan nida mum dinka munce ka kashesa
Dama nasan bazaka taba yin abinda yakamataba kullum kaike kawo Mana matsala Sam bakada amfani
Gwara haihuwar mace da lusari kamarka.....

Kwacewa yayi cikin tashin hankali yace"

Wlh dad na kashesa wannan ba JJ bane wani ne....

Wani kyakkyawan Mari JJ yadaukesa dashi yace"

Yanzu ka yarda da nine ba wani ba Ina fata.
#MAMUH.*_ZAFAFA BIYAR na kudine idan idan kanason kowanne daga ciki ka nemi wainnan numbers din_*

*_Daurin boye_*
_safiyya huguma_
*_Buri daya_*
_mamuhgee_
*_Wutsiyar rakumi_*
_billyn Abdul_
*_kaimin halacci_*
_Miss xoxo_
*_Sauyin qaddara_*
_hafsat rano_

*08030811300*
*07067124863*


*_Mamuhgee34_*
_Not edited_
Da jajayen idanuwansu suke kallonsa hawaye na cikowa idon am suka gangaro atake yayi kan JJ zai cakumosa police Sukayi saurin riqesa yanata sakin maganganu masu qarfi jikinsa na rawa idanuwansa na hawaye.

Dilla sai ganin akayi ya yanke jiki ya Fadi fammah tayi kansa tana ihun Kiran sunansa ya kasa ko dagowa ya kalleta jikinsa sai rawa yakeyi sbd tsabar tashin hankali,

Daqyar ya sake zabura ya miqe cikeda balai ya cakumo JJ bakinsa na kumfa yace"

Wlh baka isaba karabani da abinda nayi baqar wahala na Tara tun ba'a haifekaba,
Kasan ta Yaya na Tara wanna dukiyar na tattaleta tazama haka?
Kasan irin gwagwarmayarda nayi Dan ganin na Tara wainnan miliyoyin???
Kasan Rai nawa na dauka akan Naga nakawo yanxu???
Kasan mutum nawa nayi betraying duk akan na bunqasa wannan dukiyar zakazo cikin awanni nawa kace ka rabani da komai bazai taba yiyuwaba kasani,wlh akan dukiyata zan iya kawarda kowa.....


Cikin kallon wulaqanci JJ yace"

Yes nafika sanin dawa dawa ka kashe kafin ka Gina wannan dukiyar sbd namu iyayen na ciki muma kanmu Muna ciki saini Dana dawo Saidai kasani kaman yanda kafada zaka iya kawarda kowa akan dukiya nikuma bana barin duk Wanda ya kashe masoyana saina tabbatarda ko rigar sawa ta gagareka dikko Dilla.

Yana fadar haka ya juyo gaban Yan press yafara koro musu bayani shida lawyoyinsa securities na bayansu tareda daga musu takardar ya nuna musu take aka ringa dauka suna dauka aka hau sama aka Ciro sunan companyn aka jefo qasa daga can hawan qarshe.

Aka ringa fitarda kayan companin ana gwanjonsu Yan jaridu Bata dauka.

Ganin wulaqancin rayuwa yaga rufesu ko Kai sun kasa dagowa am hawaye yakeyi sosai nadey tayi saurin zuwa gefensa cikin hawayenta itama tana basa hkr da qwarin gwiwa kafin Suka fito fammah dake tsananin kuka kamar ranta zai fita tana riqeda Dilla Wanda hawan jini yasa idanuwansa ke gani bishi bishi qafafuwansu daqyar suke dagasu suna jansu.

Dan juyowa nadey tayi suka hada ido da JJ ta sakar masa wani murmushi tareda Yi masa wani irin juyi da ido daya sashi sakarwa 'yan media wani kayataccen murmushinda Bai shiryaba.

Wannan karon itace ta karbi driving din sbd ko gani sosai Babu meyi acikinsu dilla koda Suka Isa gida jikinsa ya rikice gabaki daya BP dinsa yayi high numfashinsa yafara sarqewa tuni akayi ciki dashi aka shimfide aka kirawo Dr da gaggawa.

Sosai Dr ya dubasa tareda daura masa drip da oxygen sbd numfashinsa daya toshe a qirji ko numfashi Bai iyayi bare motsi tuni yakoma kamar wani sauran gawa Dan baisan waye yake kansaba.


Palo Suka dawo suka zauna jigum jigum Babu wani sauran dogon motsi Kuma a gidan.

Da daddare ma kwantawa kawai Sukayi Babu wani sauran bacci bare yunwa balainda suke ciki ya soye baccin idanuwansu tareda toshe hanjin yunwarsu.

Nadey kuwa kicin taje ta zauna acan Tasha brownflakes da warm milk ta qoshi abunta taci apple daya ta boye tayi waya da JJ akan dad shima ya iso Yana gari.

Murmushi tayi cikin Jin dadi tace"

Alhmdllh,,,, finally wannan abin saura Abu biyu mugamasa nasamu damar zuwa gurin babana da iya talatu,
Inason na zauna gabansu nayi kukan mutuwar zainab dinta Wanda nakasayi agaban kowa,

Sujiyo radadin da zuciyata ta cikin kukana na Rashin mijina da 'yar uwata.

Hawayene Suka gangaro Mata takasa sharewa saima sulalewa datayi agurin tana kuka after all this maraicinta na rashinsa zai dawo sabo agareta.

Ta Dade tana kuka agurin kafin ta tashi jiki amace ta fito ta haye sama tana Shiga ta kwanta gefen fammah datai bacci hawaye nafita gefen idonta.
Itama ahankali ta rufe idanuwanta hawaye na fita cikinsu.


Washe gari jikin dad din madai sai ahankali ganin hakan yasa am yafara maida hankali ya duqufa sosai gurin ganin ya kwato musu dukiyarsu gefe daya Kuma ya rasa ta Yaya zaiyi hakan sbd a account abinda suke dashi idan yace yayi wannan harkar dasu kudine zaizubar sosai suzo su rasa komai harka ta qarasa kwabe musu.

Dayaji ya rasa shawarar abinyi saiya shirya ya nufi prison gurin mum dinsa.

Lokacinda yagama Mata bayanin abinda ke faruwa haukace masa tayi tuburan tana kuka sbd jin sun rasa duk abinda suke tinqaho dashi Wanda takesa ran dashi zasu fiddota duk da shedarda wannan Dan press din da am yasa akashe ranarda yayi Mata wannan tambayar a 5star yabada shedar cewa shima tasa akashesa daga tambaya Allah yasa JJ yazo ya taimakesa da yanzu ya mutu.

Ganin lokacinda aka Basu yakusa cika cikin tsananin tashin hankali da damuwa yace"

Mum inason gyara komai gashi bakya nan ga dad Kuma a kwance tell me what to do mum.

Hawaye suka gangaro Mata daga idanuwanta dasukai jajir ta kallesa ganin cikin Dan qanqanin lokaci yanda ya hargitse Yana neman zaucewa shima ta tuno fammah dinta da Bata Saba da irin wainnan tashin hankali ba saitaji hawayenta na qara gudu ta tunoda nadey cikin wani irin yanayi ta kallesa tace"

Ina nadey?

Tana tareda fammah a gida tana rarrashinta.

Ok listen to me very careful kanaji ko???wannan lokacin ne zakayi amfani da soyayyarku musamu abinda mukeso daga gareta.

Da sauri cikin Rashin son bata tarensa da nadey yace"

How mum????

Dole zamu nemi Aron maqudan kudi daga gareta tareda tallafi daga companies dinta su Kama hannuwanmu mu farfado.

Mum kinsan yanda business yake ba'a baka shares irin wannan na manyan kudi daga manyan companies saika bayarda jinginar wani kadaranka which is we have nothing here sai a Nigeria kinsan yanzu dukiyarmu abinda ya rage a Nigeria ne kawai daga mansion dinmu na can sai kamfaninmu 'daya acan....

Yes am ka batasu amatsayin jinginar sbd ba 'yar Nigeria bace Bata taba zuwaba hasalima batasan a Nigeria ta Yaya zataje tayi claiming dinsu ba and our plan ba anan zai tsayaba along with the loan ka fito Mata da maganar aure kuyisa cikin sati guda ta yanda bayan aure Babu wani maganar loan dazai tashi idanma munkasa samun karbar namu companyn saimu mallake nata yadawo namu tunda tazama matarka.


Shiru yayi Yana jujjuya maganar sbd stayi hundred percent Saidai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login