Showing 54001 words to 57000 words out of 73969 words
numfashinsa ya sarke yafara Jan numfashi daqyar Yana dafe qirjinsa.
ganin Yana kokuwa da numfashinsa yasa fammah saurin riqosa am kuwa motar police dinda aka bude aka fitoda mum dinsu data sauya kamanni gabaki daya gefenta kuwa mayor ambryam ce cikin shigar kayan sanyi.
Da gudu yayi kan mum din ya qanqameta Yana Kiran sunanta
Itama kukan takeyi sosai....
Jin fammah na Kiran sunan dad din yasa Suka juyo da sauri Suka yo kansa cin tashin hankali am ke shafa bayansa Yana kirana sunansa tareda nuna masa yaja numfashinsa da qarfi.
Cikin wata irin murya me Kama da rugugin damuna haydar yakoma zakinsa yace"
Ku daina wahalar ceton Wanda tasa tariga tazo qarshe rufe sauran babinsa zamuyi kamar yanda yasan yasaba rufe babikan wasu....
Dikko ka miqe tsaye da kyau ka fuskanceni sbd yaune zanbaka bugun zuciyarka na qarshe.
Ka godewa Allah haryanzu sa'a na tareda Kai sbd JJ and....kasa fadar sunanta yayi ya lumshe ido yacigaba da cewa"
Sun lalata rayuwarka batareda Ni na qaddamar da abinda na shiryowa rayuwarka ba Wanda zaisa ka dauki makami da kanka ka dauke rayuwarka da kankaba,
Kaji dadi sun baka hukunci Mai sauqi sbd Dilla da nine kasamu hukunci daga gareni toda ko kare bazaici namankaba sbd nayi niyar mayarda rayuwarka mafi qanqancin rayuwa wadda dabba saiyafi daraja a idanuwan duniya Amma saigashi kasamu hukunci Mai sauqi daga familyna Wanda ko hakan ya isa ya tabbatar maka da cewa Zaki ko baya raye zuriata sunfi qarfinka..and one last thing shine dukkanin cases na kashe kashenda kayi tun kafin haihuwata na budesu you're not going anywhere dilla..
Files din hannun lawyernsa ya karba tareda budewa ya saki wani mugun murmushi tareda daga masa files din yace"
17 murders cases,
One murderer,
Kafara da kashe uncle dinka da matarsa da yayansu biyu a Dilla Ethiopia ka gudo da dukiyarsu Nigeria inda ka kashe wani dattijo a wani qauyen jalingo ka gade gidansa,
Ka kashe yayan matarka zeel kuka gade tasa dukiyar kuka Kori yayansa,
Ka kashe ma'aikatan dasuke maka aiki da dama kafin kazo ka kashe Amininka ALIYU HAIDAR NOAH... Owner NOAH'S PUBLICATIONS, Noah's empire....
Dukkaninsu atare Suka dago Suka kallesa cikin mummunan firgicinda tunda aka fara wainnan balain Basu shugesaba....
Dagowa Dilla yayi da kyar ya kalli Zaki da idanuwansa dasukai jajir sbd tsananin azabar ciwon dayake ciki zaiyi mgn Amma yakasa bude baki police suka marmatso cikin bindigoginsu da cuffs zasu kamasa ya kalli zeel,am da fammah ya bude baki daqyar zaiyi magana zuciyarsa ta buga ya zaro ido Yana dafe qirjinsa take yafara tari Mai qarfi Wanda sukaga jini na biyo tarin
Koda su am Suka riqosa cikin tashin hankali tuni jinin yafara biyowa ta hancinsa da bakinsa Koda Suka tarosa jikinsa yasaki suna ihu suna kuka suna kallonsa ya rasu agurin..
Rintse idanuwa JJ yayi sbd irin kukan dasukeyi da ihunsa irinsane yayi alokacinda aka kashe masa nasa iyayen Yana tuno abin har lokacin yanajin radadin abin...
Zaki kuwa juya baya yayi sbd kukan fammah dayake taba zuciyarsa da dukkanin tausayinta akaro na farko..
Ambulance na zuwa aka daukesa har lokacin kuka sukeyi sosai cikin tsananin tashin hankali da baqin cikin dasuke ganin zai samesu idan sun rasa dad.
Ambulance na barin gurin da Dilla wasu karnuka dake gefen Mansion dindake kusadana dillas din suka qaraso suna shinshina jinin suna haushi.
Karnukan am ya kalla ya dago ya kalli Zaki Suka hada ido hawaye suka gangaro masa ya riqo mum dinsa da fammah dasuke kuka suna shidewa ya sakasu a taxi sukabi bayan ambulance din.
Watsewa gurin yayi kowa ya wuce har Yan media tuni Suka watse ana yada labarin rasuwar Dilla.
Juyowa yayi zaiyi magana yaga yanda JJ ya tsaresa da manyan idanuwansa
Ya saki wani sirrin numfashi tareda zare shades dinsa yayi tareda kallon JJ zaiyi magana saikuma yakasa ya rungumesa da qarfi Suka rungume juna kowannensu najin tsaftatacciyar qaunar Dan uwansa wadda sunsan Allah ne yasaka musu qaunar junansu fiyeda komai.
Sunkoma ahaka kafin Suka saki juna JJ yasake kallonsa cikin mutuwar jiki yace"
Nasan reason dinka baifi karka dawo garemu a cutatar damu sbd Kai Amma meyasa bakayi tunanin idan Muna tare zamu iya Kare junanmu tareba musamman bab.....
Kasa karasawa yayi sbd jin nauyin sunan akaro na farko.
Kallonsa haydar yayi yaji wani iri shikansa sai ya basar da cewa"
Let's go.
Zama sukai a palon haydar na qurya
Haydar ya miqa masa glass of raspberries juice ya zauna suna facing juna ahankali yafara cewa"
Dr sayyid yazo headquarter da Kash masu dibbin yawa akan bailing Dina gurin CM Kuma cikin saa ya amince yace zai sakeni anjima da dare Amma ana Sakina nabar qasar,
Akan haka Suka gama magana Dr sayyid na tafiya cm yakirani har office yayi min bayani tareda nunamin kudi da passports da Visa tareda ticket dinda Dr sayyid ya bayar akan abani Ina fitowa cikin Daren naje airport akwai jirginda zanbi zuwa US.
Cikin Daren nan am yazo da kansa tareda yaransa hudu tareda dukiya Mai yawa akan sunason abarsu su kunnawa cell Dina wuta.
Cm baya headquarter acikin Daren Ina kwance inaji Suka kunnawa side dinda muke wuta sosai atake gobara ta tashi.
Shiru ya danyi cikin tuno irin azabar dayasha alokacin kafin yacigaba da cewa"
Daqyar da yardar Allah nasamu na buge window na fada baya bayan kusan gefen jikina yafara kamawa da wuta Amma I couldn't give up sbd my family needs me.
Naso dawowa gida alokacin Saidai hakan zaikawo fitintinu da dama Wainda nasan Dilla zai iya kashe kowa a familyna without anyi hesitation,
Daga nan ne naje office din cm na balle nashiga na dauki visa da ticket dinda akayimin da check din kudin nafice.
Aranar na wuce sbd qonuwata is getting worst.
I suffer,
I suffer JJ,nayi rayuwar kadaici,baqin ciki,azaba,wahala da gwagwarmaya..tun a cikin jirgi bansake sanin inda nakeba sbd qonuwata is very deep and serious.
Daga airport hospital aka wuce Dani and I spend morethan 2month a kwance asibiti.
Bayan na warke sun sake sakoni jirgi Suka dawo Dani Nigeria acikin Daren direct gida nadawo and unfortunately Ina xuwane cikin tsakiyar Daren na tararda abinda yafaru Wanda adaren suka kashe zainab...
Naganku lokacinda kuka fito,
Nabiku tun adaren nake bibiyar rayuwarku har lokacinda tayi zama a asibitin Zurich,
Sbd ita nakoma Zurich I started my business from there,
Every morning kafin fita aiki sainaje gurinta hakama da yamma before going home.
Ahaka Ina taredaku a asibiti ta haihun Saidai bazan iya zuwa na karbi 'yataba nayi Mata addua duk sbd dillas.,
Bayan haihuwarta tadawo lafiya klau nakoma nashiga school a nan Zurich,
I spend 1 year Ina karatu Ina business din shipping cikin 5yrs nayi achieving duk wani Abu danakeso ciki har soyayyan fammah akaina Wanda da itane dama zanshigo dillas...
Bantaba mantawa daku ba sbd koma meyene nayi nayi ne sbd ku...
Nayine sbd safey dinku,
Nayine sbd girman soyayyar....
Kasa qarasawa yayi sbd ja da idanuwansa Sukayi sbd tuno yanayinda suka rabu da ita jiyan Wanda haryanzu abin ke cin ransa.
Rungumesa JJ yayi tareda buga kafadarsa ahankali ya iya furta karka damu zata saukane just give her time.
Acikin Daren jirginsu ya sauka a starling city inda dad da kansa yaje daukarsu airport
Kallon juna Sukayi shida haydar kafin ya jawosa jikinsa ya rungumesa da qarfi cikin farin ciki Mara iyaka yaugashi ga dansa.
Sunjima ahaka kafin Suka dunguma zuwa gida inda zuciyarsa ke harbawa da qarfi sbd yaune Karo na uku dazai rungumi 'yarsa cikin jikinsa.
Ya rungumeta a Karo na farko a school dinta dayaje ganinta a boye itama Bata sanshiba kawaidai ya daga Mata hannu Kuma taje da gudu.
Sai na biyu Kuma a garden din wasan yara dasukaje da nanny Nancy..
Mamanta ya tuno take yaji gabansa ya buga Amma a fuskarsa Babu Mai iya gane halinda zuciyarsa ke ciki.
Suna Isa gidan dukkaninsu Suka fito zuwa ciki shikuwa duk takunsa daya qara bugawar zuciyarsa yakeyi.
Dad ne agaba baby z tazo da gudu ta fada jikinsa tana ganin JJ tasake tayi gurin JJ tana cewa"
Yehhhhh nanny Nancy my daddy is back.
Dagata sama yayi cikeda farin cikin ganinta ya ajiyeta qasa Yana cewa"
I miss you my angel.
I miss you too Daddy.
Dan matsawa yayi tareda nuna Mata haydar dake tsaye Yana kallonta cikin wani irin tsananin so da qaunar 'yarsa tsotsonsa da kawunsa yake gudun a haifar masa namiji
Take yasaki murmushi tareda ware Mata hannu aikuwa da gudu tayi gurinsa tana cewa"
Uncle you hia??
Daukarta yayi sama shima ya rungumeta tsam tsam yanajin soyayyar mamanta fiyeda kowane lokaci.
Tsakiyar palon Suka dawo dukkaninsu har lokacin tana jikinsa sai farin ciki sukeyi shikuwa idanuwansa nakan stairs akai akai.
A gajiye tadawo office sanye cikin traditional Milano gown lilac.
Kai tsaye tashigo palon riqeda keys da jakarta musamman datake jiyo hayaniyar baby z.
Tana shigowa a cikin idanuwansa nata idanuwan suka fara sauka qafafuwanta suka harde atake saura kadan ta kife taku daya ya riqota Yana zuba Mata idanuwansa dasuka qarasa rikitata tayi saurin kwacewa tareda Dan kallon gefensa ta wuce tana qoqarin sakin fuska tanawa JJ oyoyo.
Bata wani tsayaba ta haye sama ta zauna tana jero ajiyar zuciya jikinta na Dan rawa.
Saidata nutsu kafin ta tashi tafada toilet tayo wanka tazo tayi Sallah tashirya saitakasa fitowa takira nanny aka kawo Mata abincinta a daki.
Haka taqi saukowa har washe gari,
Cikin sauri tayi Shirin office zata fice gidan ta sauko ko gurin dad batajeba ta sulale ta fice.
Ko zama batayi a office ba aka bude qofar aka shigo ta dago zatai magana suka hada ido ta daure fuska zatayi magana ya jawota jikinsa ya matseta tareda zuba Mata idanuwansa masu mugun rikitata batareda yace qalaba.
Muryanta na rawa tabude baki daqyar ta iya cewa"
Let go of me please.
Please"takuma cewa muryanta na rawa.
Wani irin murmushi yasakar Mata take ta zaro ido tana neman some masa take abin yasake sashi murmushi ba zato taji saukar kiss dinsa akan idanuwanta zata qarasa somewa ya cirata sama gabaki daya ya fito office din da ita baidamu da kallon da ake musu ba yakaita mota yasa Saida yadawo yashiga motar ahankali ya furta"
Nigeria zamu je a cikin Daren nan jirginmu zai tashi.
Da sauri ta kallesa gabanta na bugawa da sauri.
Gida Suka Isa ya bude Mata qofa ya wuce yabarta sake da baki tanabin bayansa da kallo.
Bata yarda da Nigeria zasu jeba Saida taga kowa na shiri haka tahau Shirin kayanta Dana baby z.
A gurin cin abincin Rana tunda tazauna a dining din idanuwansa ke kanta Saidai abinda yafi hautsinata shine yanda yakoma zakinsa tsaf kallonsa ma faduwar gaba yake sata.
Ganin takasa cin komai sai mutsu mutsu takeyi yasa ta miqe tabar dining din Takoma Palo.
Suna Gama cin abinci suka fice ko mintuna goma basuyi da fitaba akai knocking tana budewa taga order ce akayi ta honey pancakes da sunanta.
Murmushi ne ya subuce Mata sbd tasan waye yayi wanan order din.
Karba tayi tadawo ta zauna tana kallo tanason ci Amma ta Hana kanta ci ta ajiye a inda zaigani yasan bataciba.
Qarfe biyar na yamma dukkaninsu suna airport zuwa lokacin kowa baida wani dogon kuzari sbd sanyi da jikinsu yayi yanda zasu samu su kawun dakuma yanda zaa karbesu su hudu da ake sakaran sun mutu tun shekaru.
Har cikin jirgi Babu me wata magana acikinsu sai tunani har Suka isa gabanin asuba.
Dr sayyid ne yazo yadaukesu da wata baqar jeeb dinsa.
Ahankali Zaki yace"
Gida zaka kaimu.
Kallonsa dad yayi zaiyi mgn nadey ta rigasa da cewa"
Please dad muje can din first Dan Allah.
Daga Kai yayi suka Kama hanyar gidan kawu lokacin duk masallatai sunfito sallar asuba har gari yafara haske.
A qofar gidan Suka tsaya Allah yasa babu wasu mutane suka shige gidan dukkaninsu suna Jin kewar gidan nadawo musu sabuwa.
Da babbar malum malum dinsa yafito daga dakin iya talatu Yana hamma sbd yau baisamu sallar asuba ba sbd kwana yayi da lalataccen ciki na wani romon Kai dasukaje Suka Sha shida mal idi a gurin wani bikin daurin aurenda ko gayyatarsu baayiba.
Buta ya dauka zai shiga bandaki yaji sallama ahankali ya juyo yayi ido biyu da wadda ko mutuwa yayi yadawo fuskarta Bata bace masa,,,
Zaro qananun idanuwansa yayi zai saki ihu saiyaga Zaki yashigo shima cikin sallamar
Take ya saki butar hannunsa jikinsa na daukar mazari saikga JJ yashigo tareda neyo.....
Hannu ya Dora akai tareda zubewa cikin tsananin tsoro da tashin hankali yafara qwala Kiran sunan talatu Yana cewa"
Talatu zoki bani shahada lokacin tafiyar yazo matacci nake gani wlh,
Gashi nidai wlh ban dandadi dadin arkin danake roqoba Koda na awa dayane na roqi Allah yamin arziki Kona wucin gadin ne Amma Banda rabo.....
A rikice iya talatu tafito dakin tana daura dankwali zatayi magana ganin Wainda ke tsaye saita murza ido tasake murzawa...
A hasale cikin muryar kuka dattiyan yace"
Ke banason diban albarka zakiban shahadane kokuwa saina mutu Banda rabonta...
#MAMUH._*Mamuhgee38*_
Hannu iya talatu ta Dora akai Saidai kafin tasamu ikon yin magana jikinta yasaki tafadi a some.
Dattiya na ganin hakan baisan sanda ya fashe da kuka ba jikinsa na makyar kyarar tashin hankali baki yakeson budewa yakira ceto Amma ya kasa gashi dukkaninsu sun jera masa tsaf a gabansa murmushin Zaki daya Saba masa idan zai masa gayya shiyakeyi ko yanxun sbd shiyace karkowa yayi mgn.
Ahankali ya sanya hannu aljihu yayi kamar zai Ciro Abu dattiyan na ganin hakan yasan addar cire ransa ce zaa fitar sai kawai yasaki jiki yayi baya jikinsa na rawa cikin ransa yace gwara nayi sumar qarya koma menene ayi idona rufe.
Da gudu nadey dake hawayen tsananin farin cikin ganin babanta na nan da hallayarsa ta tarosa jikinta tareda fashewa da kuka tana cewa"
Baba karka Suma wlh Babu wasu matacci dakake gani mune gabanka bamu mutuba,
Kabude idanuwanka kagani mudin daine muka dawo gareka.
Dattiya najin hakan jikinsa yasake daukar mazari yasake sake jikinsa yaqi motsawa danyaqara nuna a some yake,
cikin zuciyarsa kuwa kuka yakeyi sosai Yana tsinewa qarfin aljanunsa dasuka hanashi Suma adaidai yanxun sbd hankalinsa ya mummunan sake tashi ganin matacci gabansa su hudu Ras har Wanda rabonda yagansa shekaru fiyeda talatin.
Murmushi Zaki yasaki tareda matsowa gabansa ya tsaya cikin murmushi yacewa JJ ya shafawa iya talatu ruwa.
Gyaran murya yayi Yana kallon kawun ya dago ya kalli nadey dake kuka cikin sakin fuska yace"
Lemme handle this.
Wayarsa ya fitar daga aljihunsa wandonsa ya kunna fitilar wayar ya kashewa kawun ido da ita saiga idanuwan kawun sun fara marmadi alamar idanuwansa biyu.
Cikin sanyin murya Mai taushi Yana kallon nadey yace"
Ayyya sai hakuri fa yariga ya tafi JJ daukesa muje mu rufesa kawai dama yace idan yatafi kar 'dan dabar dayayi zaman gaisuwarsa.....
Jin kawai Sukayi ya fashe da kuka Yana cewa"
Talatu kinci amanar zaman tare dakika Suma kika barni...
Wata irin dariya Suka sake kusan atare Banda nadey da batasan lokacinda takai masa duka a hannuba tana harararsa da hawayenta
Dad ma matsowa yayi yana cewa"
Ku matsa karku bugarwa da Yaya zuciya.
Kamasa yayi ya miqe daidai iya talatu itama ta farfado Suka zaunar dasu a tabarma dad Yana sake kwantar musu da hankalin Babu wata fatalwa dayake gani ko matattu sudin daine.
dattiya da hankalinsa Bai Gama kwanciyaba murya na Yar makyarkyata yace"
Eh nidai kubari nakira Dan uwana mal idi zanfi Jin hankalina ya kwanta.
Zai tashi iya talatu tarigasa tashi sbd tasan bazai dawoba dagacan zasu iya guduwa shida mal idi din tace"
Bari nakira makashi ta katanga.
Wata irin muguwar harara yabita dashi Yana ayyana irin Rashin qaunar dake tsakaninsa da talatu datake masa irin wainnan abubuwan.
Zaki dayafi kowa sanin waye kawun yasaki murmushin dayasa nadey harararsa ahankali
Ya dauke gira daya cikeda mamakinta wato ta manta waye Zaki Dan bazaice Mata haydar ba sbd shi kansa yafi qaunar Zaki akan haydar.
Mal idi da qarfinsa yashigo Yana asuwakinsa babbar rigarsa tun ta jiyace a jikinsa da ita ya kwana da ita yatashi..
Yana ganin baqi masu Kama da turawa yasaki asuwakinsa tareda washe dukkanin haqoransa Yana cewa"
Shikenan mafarkin dattiya yazama gskia da kuzarinsa ya iso shimfidar tareda zagayowa gurin amininsa zaiyi mgn idanuwansa suka sauka akan fuskokinsu yafara binsu daya bayan daya da kallo Yana Dora ido akan Zaki sukaga yayi baya Yana neman kakkafewa.
Dattiya ne ya tarosa Yana basa salati Yana cewa"
Daure danne mal idi wannan duk sharrin talatu ne Kuma zataga matakin dazan dauka.
Cikin yanayi na son fashewa da kuka mal idi ya kalli talatu Yana cewa"
Meya shiga tsakanina dake talatu da kikemin wannan bita da qullin.??
Cikin gyaran murya dad yace"
Wlh anan gurin babu fatalwa dukkaninmu Muna Raye Kuma bamu taba mutuwaba,
Haba Yaya Ina katabajin anmutu andawo ko acikin kafirai bare musulmai,
Tabbas akwai tsoro da bugawar Kai da zuciya kasan mutum ya rasu tsawon Koda wata biyu ne kagansa bare shekaru tabbas wlh akwai furgitarwa..
Daqyar dattiya yabude baki yace"
Wlh Ni ko yanxu mutum ya mutu muka rufosa muka dawo nagansa to akwaifa qura bare shekaru...
Mal idi shidai baisamu na tofawa ba zufan dake masa tsiyaya cikin riga ya sharce sbd wannan shi ake Kira baqar safiya,
Gasu dai an rutsasu cikin gida Babu hanyar gudu to wlh Bari agama dattiya yashiga tsakaninsa da talatu Banda manta alheri dabai tsaya Mata agurin dattiyan ba Aida ba ita zai auraba wata hanne ce.
Sallah Suka farayi dukkaninsu a tabarmar tsakar gidan
Sudai su dattiya na rabe gefe mal idi jira yake yaji abinda bai masa ba yayi ihun kawo ceto.
Dattiya kuwa Banda tagumi daya rafka Yana Kiran Jin idan su dinne yafara zubo nasa zancen.
Aikuwa suna gamawa aka sake gaggaisawa nadey na kusada iya talatu da itakam tuni tafara murna musamman la'akari datayi da cewa nadey dama basuda tabbacin ta rasu tunda Bata tayi.
Ahankali dad yafaro bawa dattiya bayani tun daga ranarda yahadu da ruqayya a Lagos har mutuwarsa da dawowarsa inda yake bibiyan nan gidan haryasan Zaki dansa ne,
Shima yayi gwagwarmaya ta sana'ar Mai kusan shekaru shida kafin yadawo yafada ta masu aikin ginar zinari nanma kusan shekaru goma kafin Allah yayi anan arzikinsa yake gurin aiki yasamu dunqulen zinarenda shine silar arzikinsa.
Ahankali ya koro musu duk labarin nadey Dana haduwarsu da Zaki tareda qarshen dillas...
Cikin tsananin farin ciki iya talatu ta janyo baby z dake jikin JJ ta rungumeta tana hawayen farin cikin tasamu wata zainab din.
Mal idi kuwa gyara zama yayi yana sakin dukkanin fara'ar fuskarsa da bakinsa yafara hamdala Yana kallon dattiya dake kallon nadey baya ko qyaftawa sbd tsananin farin ciki Yana sakin hawayensa dasuka kasa boyuwa.
Zaki yakoma kallo Yana washe baki kafin yasake kallon baby z wadda allah yayi ba agansa zatazo duniyaba duk irin qone qone da azabar dayaci akanta.
Jawota yayi jikinsa akaro na farko da tsananin son qananun yara yakamashi baisan lokacinda ya washe baki ba Yana cewa"
Nadiya wannan 'yarki ce???
Oh ni dattiya Allah nagode maka Ashe dai arzikin ta jikoki zaizo.
Dariya yabasu mal idi yace"
Ai