Showing 24001 words to 27000 words out of 42966 words

Chapter 9 - AUREN FANSA COMPLETE NOVEL

23 Aug 2025

499

rud'e dan
Allah Zarah, to ba komai bane ba illa wai Faruk
zai k'ara aure..."
Lemon da ta kai bakinta shi yayi sanadiyyar
k'warewar da tayi hakan yasa ta dinga tari, da
k'yar Meenah ta dinga bata ruwa har tarin ya
tsaya tana ta faman yi mata sannu.
Sai da ta nutsu Zarah tace
"Wai wane Faruk d'in tukunna Meenah?"
Meenah ta d'anyi dariya tace
"Akwai wani Faruk da kika sani bayan mijina ne?
Shi dai nake nufi Faruk da na aura a matsayin
mijina to shine zai k'ara aure."
Salati Zarah ta shiga yi cikin tashin hankali
sannan tace
"Faruk dai your soul Meenah? Wai aura fa kika
ce? To kuma shine kika zauna kamar baki damu
ba?"
Meenah tayi murmushi
"To ya kikeso inyi? Kashe kaina zanyi ne?
Abinda Allah ya kaddara waya isa ya hana?
Nidai na rungumi kaddara kuma ina fatan wadda
zai aura mutuniyar kirki ce, sannan ina fatan
bada tashin hankali zata shigo min ba, amma
nidai idan mijina na sona banida matsala."
Zarah nata kallonta tana magana cike da
mamaki, sai data gama Zarah tace
"Lallai an gaishe ki Meenah, kinyi k'ok'ari sosai,
ba kowace mace bace zatayi abinda kikayi ba, ni
gaskiya inda nice bazan yarda ba, sai anyi
tashin hankali ba kad'an ba, tab kishiya fa lallai!"
Meenah tayi dariya.
"To Allah ya kyauta dai, kedai kiyi ta addu'a
Allah ya baki miji na gari shine kawai.
Wai shin ina Nabeel kuna ta shan soyayya ko?
Kuma yana zuwa zance ko kuwa?"
Zarah tayi dariya
"Han! Kin cika ni da tambaya wane zan fara
amsawa?"
Suka d'ara su duka, Meenah tace
"Duka zaki amsa mana."
Zarah tayi murmushi mai bayyan hak'ora tace
"To Nabeel yana nan lafiya lau, yana ta zuwa
wurina and kuma Baba yace ya turo iyayensa."
Cike da murna Meenah tace
"Masha Allah! Allah ya tabbatar da alkhairi
Zarah."
Tace
"Amin... yauwa Meenah ina za'a samu mai aiki?"
Meenah tace
"Mai aiki kuma? Me za'ayi da ita?"
Zarah tace
"Mami mana, ta matsa ita 'yar aiki takeso, wai
gwara ta samo don idan nayi aure nima babu
kowa gidan."
Meenah tace
"To kin ta6a ganin na samo masu aiki ne?
Amma zan tambayi Faruk ko yasan inda ake
samu."
Zarah tace
"Yauwa nagode, batun result naga sunayenmu
sun baki Business admin ni kuma Biology."
Cike da murna Meenah tace
"Alhamdulillah, kin anso admission letter?"
Zarah tace
"No sunce sai next week, so zamuje sai muyi
registration."
Nan sukayi ta murna marar misaltuwa.
Kafin Zarah ta tafi sai da ta taya Meenah tayi
abincin rana, shinkafa da miya sukayi da salad.
Bayan sun kammala Zarah ta fara shirin tafiya.
Nan sukayi bankwana akan Meenah zatazo gida
ta gaida su Baba, Zarah kuma ta tuna mata
batun mai aiki.
***
Tarin takardu ne da laptop a gabansa ya tasa
gaba yana kallo, amma a zahiri hankalinsa baya
wurin idonsa ne kawai ke kan takardun, tunanin
Meenah yasa shi a gaba ya hana shi sak'at har
ma ya rasa inda zai sa kansa. B'angare d'aya
na zuciyarsa yana tunani akan yadda zai cimma
burinsa, d'ayan 6angaren kuwa, Meenah ce tayi
masa tsaye a rai duk yadda yaso yakice ta daga
ransa abin yaci tura. Sai ma dad'a gaba abin
yakeyi.
K'wank'wasa k'ofar akayi, ya bada izini aka
shigo, matashiyar budurwa 'yar kimanin shekaru
ashirin da biyar (25) a duniya, suna kiranta da
young detective, saboda sabuwar shiga ce
sannan gata yarinya.
"Sir wai kana nema na ko?"
Yace
"Yes ina nemanki, bismillah."
Tace
"Ok sir."
Bayan ta zauna ne yace
"Wani taimako zakiyi min Hajir, amma kafin nan
bari na baki labarin komai tukunna."
Nan ya shiga bata labari tun daga farko har
k'arshe sannan yace
"To yanzu kinji inda nakeson focusing, ina so kije
kiyi tunani nima zanyi tunanin hanyar da zamu
dinga samun information daga gidan, da naso
muyi magana sosai but gaskiya na gaji kuma
bana d'an jin dad'in jikina, so zan tafi."
Ya duba tima k'arfe 3:47pm. Yace
"La'asar ta kusa, zan je masallaci idan na tashi
daga nan, sai na wuce gida, zuwa gobe idan
nazo zamuyi magana."
Tace
"Insha Allah."
Yace
"Ya batun case d'innan da akayi assigning d'inki
kin gama shi kuwa?"
Tace
"Na gama amma case d'in ya bamu wahala
sosai, sai dai cikin ikon Allah munyi succeeding."
Yace
"Haka ake so ay, nima akwai cases masu bani
wahala amma da mutum ya sa confidence a
ransa da kuma jajircewa akan aikin sai kiga
komai ya tafi yadda ake so."
Tace
"Haka ne."
Ya mik'e ya soma tattara komatsansa cikin
briefcase yace
"Hajir zaki iya tafiya, sai goben insha Allah."
Tace
"To sir Allah ya kaimu."
Yace
"Amin."
Daga haka ta fice a yayinda ya kammala kimtsa
kayansa sannan ya fice daga office d'in....
AUREN FANSA 30
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹30🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Mairo Gafai Allah ya baki lafiya yasa anyi a sa'a
😍
Daga d'an nesa yakejin kamar ana k'wala masa
kira, hakan ya dakatar dashi daga bud'e motarsa
da yakeyi. Hango Najeeb yayi yana k'arasowa
cikin d'an gudu gudu, tun daga nesa yake hango
sa kamar yana cikin damuwa. Sai da ya k'araso
dab da shi sannan Najeeb yace
"Wai tafiya zakayi da wuri haka? Wurinka nazo
fa."
Faruk yace
"To, kuma gashi har na rufe office zan wuce
gida, amma idan maganar batada tsawo mu
shiga daga ciki."
Najeeb yace
"No batada wani tsawo sosai, no need ma mu
shiga daga ciki muna iya tsayawa a nan."
Faruk yace
"Ok kafin nan ya gida ya k'anwata da fatan ana
kula min da ita sosai?"
Najeeb yace
"Haba mana kai kason yadda nakeson Anisah
ay, dole ma na kula da ita. Yawwa wata magana
nake ji daga gida cewar zaka k'ara aure, shin
gaskiya ne ko ba gaskiya bane ba?"
Faruk yace
"Wannan magana gaskiya ne, haka take."
Najeeb yace
"Amma ka bani mamaki Faruk, ta yaya zaka
k'ara aure yanzu? Daga yin aurenku, baka bari
nan gaba kad'an idan ma zaka k'ara sai ka
k'ara. Haba Faruk..."
Faruk yayi murmushi yace
"Najeeb kenan, gani nayi fa ba haramun bane
k'ara aurennan, sannan ba wata bare bace zan
aura 'yar gida ce."
Najeeb yace
"Nasani mana, amma baka ganin Jidda bata
dace da kai ba?"
Faruk sai ya kama dariya yace
"Ta yaya?"
Najeeb yace
"Haba Faruk, yarinyar nan kasani sarai batajin
magana, kullum cikin yawo take, gata ta tara
k'awaye a gida, baka ganin yadda su Dada ke
fama da ita? Kai baka tunanin ta zame maka
matsala a gidanka da kai da iyalinka nan gaba?
Kuna zaman lafiya kaje ka jajibo ma kanka
masifa har gida...?"
"Wa'iyazubillahi! Haba Najeeb ka daina kira min
masifa a gida, insha Allah babu abinda zai faru
sai alkhairi. Kuma da kake batun Jidda bataji
zan gyara ta, kai kanka zakayi mamaki."
Najeeb ya kad'a kafad'a alamun oho yace
"Well it's your choice not mine, don't say I
didn't warn you to."
Faruk yace
"Yawwa kuma nagode da shawara, zamu iya
tafiya?"
Najeeb yace
"Of course, ni zan tafi sai anjima a gaida gida."
***
A gajiye ya shigo gidan, tana zaune kan kujera ta
zaman mutum uku, hannunta rik'e da remote
tana chanza channel d'in da take muradin kallo.
Tunda ya shigo yake binta da ido, a tsawon
rayuwarsa bai ta6a ganin Meenah cikin irin
wannan ado haka ba.
Wani dark blue leshi ne a jikinta mai yarfin
golding, ga wasu duwatsu dake rauraya daga
gaban rigar, d'inkin an mata wanda ake cema da
peplum sai skirt da ya kamata, d'aurin
d'ankwalin kuwa kamar don ita akayi shi, tana
sanye da 'yan kunne da sark'a kalar kayanta,
yadda kasan wata matar shugaban k'asa ko
wani gwamna saboda yanayin shigarta ya nuna
hakan. K'amshin gidan ya had'u ya gauraye
dana sanyin ac, hakan ba k'aramin dad'i yayi
masa ba.
Bata ankara ba sai ganin mutum tayi tsaye a
gabanta, murmushi ta sakar masa mai saurin
fizge zuciya a yayinda ya mayar mata ba 6ata
lokaci, sannan kuma ta tashi a hankali ta
k'araso inda yake tana mai tafiya cike da
nutsuwa. Shi dai yana tsaye yana binta da idanu,
ta amshi briefcase d'insa tare da kama
hannunsa tace
"My soul lafiya ka dawo da wuri haka?"
Ya dube ta cikin kulawa yace
"Wallahi kuwa na gaji ne, sannan yau bawani aiki
sosai."
Tace
"Ok muje kayi wanka ko abinci zaka fara ci?"
Ya girgiza kansa alamun a'a yace
"Bari inyi wankan dai zai fi, sai inci abincin daga
baya."
Hannunsa take ja yana biye da ita har d'akinsa
sannan ta shiga ta had'a masa ruwan wanka
kamar kullum, bayan ta fito ta taimaka masa ya
rage kayan jikinsa, sannan ta fice ta bashi wuri
ya kimtsa.
Bayan sun gama cin abinci ne suna zaune a
parlor suna hutawa Meenah ta soma magana.
"My soul don Allah na tambaye ka?"
Ya gyara zamansa yana fuskantarta yace
"Eh Allah yasa nasani."
Tayi murmushi tace
"Daman... nace ina kake ganin za'a samu 'yar
aiki?"
Yace
" 'Yar aiki kuma? Me za'ayi da ita?"
Tace
"Mami daman keso, ni bansan inda ake samu ba
shine nace bari na tambaye ka."
Hajir ta fad'o masa a rai, take kuma ya fara
murmushi ganin wata dama ta samu da zaiyi
amfani da ita kuma bazai bari ta wuce shi ba.
Sai yayi saurin cewa.
"Haba indan wannan ne kar ki damu, Mama na
da masu aiki, so samowa bazaiyi wahala ba, zan
mata magana."
Cike da jin dad'i tace
"Kai nagode sosai my soul."
Ya d'an tsunkuli gefen kumatunta yace
"Anything for my baby."
****
Washe gari a office yasa aka kira masa Hajir,
tana zuwa yace ta zauna, bayan ta zauna ya
soma magana.
"Kamar yadda nayi miki bayani jiya zamuyi
magana, to shine yanzu zan miki bayani. Da
farko wani aiki zakiyi min, sannan don Allah ina
buka'atar had'in kanki Hajir."
Hajir tayi dariya
"Insha Allah sir."
Yaji dad'i yace
"Da farko ina so ki chanza identity d'inki gaba
d'aya."
Cikin rashin fahimta tace
"Bangane ba?"
Yayi ajiyar zuciya yace
"Ma'ana ina so ki tashi daga Hajir, 'yar gayu,
mai ilimi, mai kud'i ki koma Atika bak'auya,
marar ilimi, marar kud'i sannan kuma 'yar
k'auye sannan Atika 'yar aiki, amma kar ki damu
aikin naki bazai dad'e ba, sannan zansa a linka
miki albashinki fiye da yadda ake baki."
Da mamaki tace
"Naji bayaninka, amma zan iya sanin dalili?"
Yace
"Yawwa, dalili kuwa shine, information nake
buk'ata daga wurinki dangane da labarin dana
baki jiya, dangane da mutuwar iyaye na. Abinda
nake so dake zakije a matsayin 'yar aiki. So
aikinki yana buk'atar hak'uri, dauriya, jajircewa,
da fatan kin fahimta?"
Tace
"Na fahimta sir, kuma insha Allah baza'a samu
matsala ba. Na farko taimako zanyi, duk da ban
ta6a cin karo da aiki irin haka ba, amma na
maka alk'awarin zaka same ni mai cika
alk'awari. Sannan insha Allah zaka same ni mai
hak'uri da kuma dauriya."
Yaji dad'i sosai ya cigaba
"Alhamdulillah, da farko zan d'an baki wasu
kud'i kije kasuwa ki siyo 'yan atamfofi ki kai ayi
miki d'inkin 'yan k'auye, sai ayi ta wanke su har
su k'ok'e, daman ba masu tsada bane hakan
bazaiyi wahala ba. Na biyu idan kin zama ready
sai ki sanar dani sai nasa a kaiki inda zaki fara
aikin. Na uku duk wani abu da kikaji ya zamanto
kin rubuta shi inda hali ma ki mani vnote, ko kiyi
duka biyun. Sannan zan siya miki k'aramar waya
marar tsada ki saka sabon sim card yadda
bawanda ya sanki da layin don kar a samu
matsala. Aikinnan Hajir yana buk'atar lura da sa
ido, ko wane motsi nata akanki, duk abinda kikaji
ki rubuta ki kuma yi recording. Da munsamu
muka had'a duk wani information da zamu
buk'ata shikenan, sai na fad'a miki yadda
za'ayi. Kar kiyi wani abu da zata gane ke ba 'yar
k'auye bace, kar ki kuskura ki nuna kin iya
turanci, kuma ki mata biyayya duk abinda ta saki
kiyi. Shine kawai abinda nake buk'ata a wurinki."
Ta saki ajiyar zuciya tace
"Tabbas bazan baka kunya ba sir, insha Allah na
maka alk'awarin taimaka maka wurin gano
abinda kakeson ganowa, yanzu dana tashi daga
nan zan wuce kasuwa sai na siyo abubuwan da
nake buk'ata, ka bani nan da kwana biyu, zan zo
sai ka kaini wurin aikin."
Yayi murmushi mai bayyana hak'ora yace
"Kai naji dad'i sosai wallahi, Allah ya bada sa'a,
zan rik'a turo maki da kati lokaci zuwa lokaci,
duk sadda kike buk'atar wani abu sai ki kirani. Ki
tafi da babbar wayarki saboda recording d'in sai
ya zamana kin 6oye ta yadda baza'a gane ta ba.
Sai ki rik'a fiddo k'aramar kina amfani da ita. To
make it more successful zaki iya rik'ayin wayar
k'arya kamar kina kiran iyayenki kuna gaisawa a
can k'auye."
Tace
"Babu matsala insha Allah."
Yace
"Yawwa."
Nan ya fiddo cheque ya rubuta mata kud'i masu
tsoka sannan yayi mata godiya ta tafi.
AUREN FANSA 31
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
*PURE MOMENT OF LIFE WRITERS*
*_We don't just entertain we touch the heart of
readers_*
PML
🌹31 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Komai tsab tuni ta kammala, ita da gida sun
d'auki haske da k'amshi. Ta dafa masa Chinese
rice with vegetable soup, sai salad. Bayan ta
gama sai ta fad'a wanka ta kammala ta fito,
yau ranar farko data bud'e 6angaren English
wears, ta fiddo wani shegen tight wando kalar
ash gashi marar tsawo da riga dark pink mai
k'aramin hannu. Ta dad'e tana shawarar ta saka
su, daga k'arshe dai tayi shahada ta sa duk da
tana jin kunya amma dole ta yakice ta wuri
d'aya. Bayan ta saka kayan sai ta taje kanta da
mayuka masu k'amshi tayi parking d'inshi da
pink ribbon daga can tsakiya sai jelar ta sauko
bisa gdon bayanta. Tabi da turaruka masu dad'i.
Ta gama shiryawa da kusan minti goma
idanunta na kan k'ofa har ta gaji da kallo, ta
jawo laptop nata da Baba ya siya mata itada
Zarah ta soma daddannawa, bata ankara ba sai
taji charab an kamo ta. Ta mik'e zumbur cike da
tsoro, sai data juyo suka kalli juna yayi
murmushi.
"Ashe kinada tsoro haka baby?"
Ta zum6uro baki abinda ke birgesa tace
"A'a ba tsoro naji ba."
Yace
"Tsoro kika ji mana, bayan na gani da ido na."
Tayi dariya tace
"Sannu da zuwa."
Yace
"Yauwa."
K'irr! K'arar door bell ta shiga dodon kunnensu,
ya dube ta yace
"Koma ciki Bala direba ne zai shigo da kaya."
Tayi ciki bata k'ara fitowa ba, ta wuce ta had'a
masa ruwan wanka, da kanshi ya lek'o yace fito
muyi fira. Tayi dariya tace
"Kai dai ka shigo ka watsa ruwa kaji dad'i."
Yace
"Angama baby."
Da taimakonta ta zare masa komai, ya shiga
toilet, ta fiddo masa singlet da gajeren wando.
Yana fitowa kuma yace
"Zo ki shafa man mai." Da mamaki kuma ya
dubi kansa wanda baisan ya furta hakan ba. Ta
sunkuyar da kanta k'asa tace
"Uhm bari naje na gyara dinning."
Da sauri ta fice inda shi kuma ya cigaba da
kallon k'ofar data bi, ajiyar zuciya ya saki ya
shirya tsab ya fito.
Suna tsakar cin abinci wayarsa ta fara ringing,
ganin Jidda yasa gabansa ya fad'i, cikin sanyin
jiki ya d'auka sannan ya dubi Meenah data tsare
shi da idanu. Yace
"He...llo."
"Hello ya Faruk a gaskiya fushi nake da kai."
Yayi yak'e yace
"Menayi?"
Tace
"Har yanzu ko kazo wurina ko? Daman nasan
baka sona."
Yace
"Ba haka bane zanzo..."
"To yaushe?"
Ya kalli Meenah har yanzu shi d'in take kallo.
Sai ya mik'e sum sum ya shiga kitchen.
Zuciyarta ta sosu, ko ba'a fad'a mata ba tasan
da mace yake waya. Macen ma wadda zai aura,
bata ankara ba hawaye suka zubo mata, jin
alamun tafiya yasa tayi saurin goge hawayenta
cikin dakewa ta k'ak'alo murmushi tana dubansa
a lokacin da yake zama kan kujera. Ya d'an
murmusa yana kauda fuska cike da kunya.
Sai da suka gama cin abincin ne ya mik'e yana
aduba agogon hannunsa. K'arfe 8:44pm. Kallon
Meenah yayi yace
"Zan fita bazan jima ba zan dawo."
Tace
"Yanzu? Ina zakaje?"
Yayi yak'e yace
"Ahh karki damu bawani dad'ewa zanyi ba."
Da sauri ya koma ciki ya sake shiri cikin light
brown yadi mai matuk'ar taushi, har hular kansa
kalar kayan, yayi kyau sosai. Kiss yayi mata a
kumatu yace
"Sai na dawo baby."
Haka tana ji tana gani ya fita, sai k'amshinsa da
ya bar mata a hanci, wanda ta tabbatar wurin
budurwa zaije. Kuka ya k'wace mata ta yi
d'akinta da gudu ta fad'a kan gado. Zuciyarta na
tafasa kamar ruwan zafi.
***
Tsaye take a gaban madubi ta ci ado na k'in
k'ari kai kace zataje tarbar matar gwamna,
sanye take da wani french lace kalar ja da adon
silver a jikinshi. Wardrobe nata ta bud'e, ta fiddo
wani kwalli da turare da wata laya da k'awarta
Luby ta bata.
"Wallahi idan kikayi amfani da kayannan Jidda
kin gama da Faruk, sai yadda kikayi dashi,
sannan ba abinda zai sa a gaba sai ganin ya
mallake ki a matsayin mata, don haka ki
tabbatar kinyi amfani dasu a daren da zai zo.
Sannan wannan kuma a abinci zaki barbad'a
masa ko lemo da zarar yasha yazo hannu!"
Wannan shine maganar da Luby ta fad'a mata a
lokacin da tazo ta kawo mata kayayyakin.
kwallin ta shafa ta fesa turaren, sai wata laya da
akace ta rik'e a hannunta gam kar ta saki har
sai ya tafi. Bayan ta kimtsa wayarta ta fara
ringing, ganin mai kiran yasa ta saki murmushin
mugunta sannan ta d'auka cikin kashe murya
tace
"Hello my dear."
Yace
"Gani nan parlon Dada, da mun gama gaisawa
zan iso main parlor ki jira ni a can."
Tace
"Angama honey."
Kashe wayar yayi ba tare da ya k'ara magana
ba.
Dada ne yake shigowa, bayan ya k'araso ya
zauna nan suka gaisa. Dada yace
"Ya gida ya iyali?"
Yace
"Alhamdulillah."
Dada yace
"Tunda nace ka nemi yardar matarka baka k'ara
zuwa ba ko?"
Yace
"A'a Dada wallahi aiki ne yasa ni a gaba, nayi
magana da ita ay ta yarda ta amince."
Dada yayi murmushi
"To kaga ka sauke nauyi, Allah ya tabbatar da
alheri."
Yace
"Amin Dada, yanzu ma wurin Jiddar nazo mu
fahimci juna."
Yace
"Madallah, babu matsala."
Daga haka ya mik'e ya fice.
A sadda Jidda ta fito Faruk na zaune kan kujerar
zaman mutum biyu yana latsa waya, tun kafin ta
k'arasa ya k'ura mata ido har ta iso yana
kallonta.
Ta dube shi sosai ta zauna kusa da kujerarsa
don ya shak'i k'amshin sosai tace
Sannu da zuwa."
A kasalance ya amsa a take yaji wutar sonta na
ruruwa a ransa kamar ana kunna ashana. Ta
dube shi sai taga ya tsare ta da idanu tace
"Yaya Faruk ina wuni ya gida?"
Ya kad'a kai tare da lumshe idanu, ji yake kamar
ya kamota ya rungume, ita kam sai matsar layar
takeyi tare da wani kad'a jiki tana wani fari da
ido. Ya sake dubanta sai yaga tayi wani kyau ji
yake kamar ba wacce tafita kyau...
Ta katse masa tunani da cewa
"Bari na kawo maka abin motsa baki."
Yace
"A'a da kin barshi ma bana jin yunwa."
Tayi wani fari da ido tace
"Ayi haka? Ay ko ruwa kasha kaida ba bak'o
ba?"
Sai wani kashe murya takeyi. Yayi murmushi
yace
"To kawo min ruwan dai ya isa, amma kar ki
dad'e don ban gaji da kallonki ba."
Tace
"To yanzu zan dawo."
Ta mik'e cike fa yauk'i da yanga ta tafi, shi
kuwa sai binta yake da ido har ta shige kitchen.
Ya lumshe idanu kafin ya bud'e jira kawai yake
yaga ta fito ko zaiji sanyi a ransa....
MSB💖
AUREN FANSA 32
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
PURE MOMENT OF LIFE WRITERS
*_We don't just entertain and educate, we touch
the heart of readers_*
P.M.L
Alhamdulillah duk wani masoyina da ya damu
dani nagode sosai Allah ya saka da alkhairi!
Naga sak'konnin gaisuwarku na kuma gode da
kulawa Allah ya bar zumunci ameen. 😘
Haka masu kirana da turo man sak'ko don jin
lafiyata kuma nagode sosai Allah ya bar
zumunci.😘😍
Wannan page d'in naku ne members na AUREN
FANSA FANS, thank you so much for everything!😍🌹
🌹32 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Duka duka batafi minti ashirin ba ta dawo
hannunta d'auke da tray mai d'auke da lemo a
cikin glass cup da aka riga aka zuba, gefe kuma
kwalin lemon 5alive ne. Tafe take tana faman
smiling tana kashe ido, tafiyar ta kuwa kamar
tana tsoron taka k'asa, fuskarta cike da fara'a
da nishad'i kallo d'aya zakayi mata ka tabbatar
da hakan.
Da isowarta sai ta rissuna a hankali ta ajiye tire
d'in, sannan ta dawo ta zauna a kusa dashi tace
"Ya Faruk ga ruwa kasha."
Kallonta yake bako kyaftawa zuciyarsa tana
ayyana masa abubuwa da dama game da ita.
A hankali ta mik'o masa lemo tace
"Bismillah."
Bai iya mata musu yakeji koda kuwa yaso hakan,
don haka sai ya kar6a ya fara kur6a kad'an
kad'an, kuma a hakan suna ta6a fira.
"Kamar yadda na fad'a ma Dada cewar nazo mu
daidaita kanmu to kema haka zan sanar da ke,
don haka me zakice game da hakan? Duk da
kuwa na dad'e da sanin sirrin da ke ranki shiru
kawai nayi, amma duk da haka ina so naji ta
bakinki, kin shirya aure na ko kuwa?"
A cikin ranta mamaki take yadda tashi d'aya ta
sato zuciyarsa a tafin

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login