Showing 15001 words to 18000 words out of 42966 words

Chapter 6 - AUREN FANSA COMPLETE NOVEL

23 Aug 2025

491

dafawa?"
Zarah tayi dariya tace
"Ay Goggo surukinki ne zaizo, shine fa su
Meenah ake ta shiri haka."
Meenah ta sunkuyar da kanta tana murmushi,
Goggo tayi dariya tace
"Ahh lallai kice munada babban bak'o, ay gara
dai yayi yazo ko zamu huta hakan nan."
Bata gama komai ba sai da k'arfe bakwai harda
rabi. Kasacewar yace mata da anyi sallar isha'i
zaizo.
Tana gama wannan aikin ta shiga wanka ta fito
ta shirya cikin wani lace ruwan zuma (coffee
brown) da light pink a jikinshi, d'inkin riga da
skirt. Da taimakon Zarah ta d'aure d'ankwalin
kayan irin na zamin da ake kira mai steps. Ga
d'ankunne an sa kalar kayan. Tana gama fesa
turare wayarta ta hau ruri da alama Faruk ya
iso. A karo na farko taji ta gigice, kasancewar a
yau zata ta6a fuskantar wani d'a namiji a
rayuwarta da idanun soyayya. Bayan ta d'auka
ya sanar da ita isowar tasa cewar yana bakin
k'ofa. Ba yadda batayi da Zarah ba akan ta
shigo dashi tak'i, harda zolayarta wai ay ba
saurayinta bane ita. Hakan yasa ta d'auki waya
ta tura masa da message akan yasa a shigo da
shi bakin k'ofa (main entrance).
Tana bud'e mishi k'ofa suka bi juna da kallo mai
kwantar da zuciya, kafin kuma dukkansu su saki
murmushi mai d'auke da wani 6oyayyen sirri.
Mamaki takeyi akan yadda yafi kyau a fili akan a
hoto...
Ta kauce ta bashi hanya ya shigo, yanan sanye
da shadda marar nauyi kalar sky blue sun kama
jikinshi, idonshi mak'ale cikin farin glass wanda
ya k'ara fito da cikar kamalarshi na cikakken
namiji, wanda boko ya zauna masa sannan kud'i
ma suka zauna masa had'e da hutu, ga kuma
uwa uba kyau, ba abinda ke tashi a wurin kamar
k'amshin turarensa mai sanyaya zuciya.
Meenah fa tayi nisa a kallonsa yayi murmushi ya
soma karkad'a mata key d'in motarsa, taji kunya
sosai ta wuce ciki kanta k'asa, yabi bayanta.
Suka zauna kan kujeru parlon Goggo, da k'yar ta
ce
"Ya hanya? Ya kuma gajiya?"
Yayi k'awataccen murmushin dake fizge zuciya
yace
"Alhamdulillah, ya gida ya hutu?"
Tayi murmushi still bata d'ago kanta ba tace
"Komai alhmdulillah, yasu Anisah?"
Yace
"Suna can lafiya lau, ina Goggo da Zarah?"
Kafin tayi magana Zarah ta fito da k'aton tray
mai d'auke da lemo kala kala da cups d'in glass
guda biyu. Sai data dire bisa center table d'in
dake parlor sannan ta zauna suka gaisa a
mutunce, yace
"Ga Zarah nan kenan? Itace sweet sister d'inki.
Sannu Zarah ya kike? I've heard so much about
you, gaskiya sister nan taki tana ji take."
Zarah tayi dariya
"Haka ne, nima ina ji da ita ay."
Tana gama fad'an haka ta mik'e tsaye ta fice.
Ba'a juma ba kuma ta dawo d'auke da wani tray
d'in mai d'auke da kuloli guda biyu, plate biyu
sai kuma bowl na snacks da salad. Bayan ta dire
sum sum ta fice saboda yadda taga sun kasa
6oye soyayyar da ke zuciyoyinsu a gabanta.
Ta lek'o don zuwa kitchen had'o tea, daman ita
Zarah al'adarta ce duk dare sai tasha ruwan
lipton (green tea) kafin ta kwanta, nan ta hango
su suna cin abinci a plate d'aya, sai kuma
sukayi mata kyau, kuma sun mugun dacewa da
juna, abinda Faruk zai nuna ma Meenah shine
haske fata don shi fari ne nesa ba kusa ba,
Meenah kuwa bak'a ce (chocolate color). Suna
cin abincin suna kallon juna, fatar bakinsu kuwa
kad'an take motsi daga lokaci zuwa lokaci. Ta
koma d'aki tana mamaki sai kace ba Meenah ba,
gaba d'aya ta fad'a tarkon so.
Kafin ya tafi ya d'auko kyauta gift d'in turare da
agogo ya bata, amma sam tak'i kar6a, sai da
yayi da gaske har yana neman yin fushi sannan
ta kar6a tana godiya sosai.
Soyayya tsakanin Meenah da Faruk kullum abin
dad'a gaba yake cike da salo na ban mamaki,
basu iya yini d'aya basuyi waya ba, haka ma
kullum yana kan hanyar zuwa wurinta.
Tabbas zuwa yanzu soyayyar da Meenah ke ma
Faruk bata misaltuwa, abin mamaki Faruk ya iya
tafiyar da soyayya yadda ya kamata ya kuma
son hanyoyi daban daban na yadda zai jawo
hankalinta gare shi, ga yaci sa'a wannan shine
karo na farko data fara sanin yadda ake soyayya,
sheyasa a halin yanzu duk wanda zata so zata
soshi ne da dukkan zuciya da kuma ruhinta.
Faruk ya riga da ya saye zuciyarta farat d'aya,
ko irin kalaman da yake furta mata kad'ai ya isa
ya saye zuciyar Meenah, don haka sheysa bai
sha wahalar yiwa zuciyar Meenah kamun kazar
kuku ba!
Batada wani tunani sai na Faruk, batada wani
ra'ayi sai nasa, sannan batada wani buri sai na
mallakarsa a matsayin mijinta na abokin rayuwa
na har k'arshen rayuwarta ba.
AUREN FANSA 21
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹21 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bayan kwana biyu da safe sai ga Baba ya diro
garin wai da niyyar d'aukar su Meenah,
hanakalin Meenah ya tashi don tasan da k'yar
idan Mami zata barta tayi soyayya ba, tasan dai
Baba baida matsala, amma Mami take ji. Aikuwa
tana sanar da Faruk cewar gobe zasu koma
Abuja yace shima zai tattara ya koma daman ya
gama abinda ya kawo shi, sai ya koma zai
cigaba da kawo mata ziyara.
Washe gari kuwa suka tattaro suka dawo gida.
Duk da hankalinta a tashe yake hakan baisa taji
ko d'ar a zuciyarta game da son da takeyi wa
Faruk Adam ba. A ganinta shi d'in yasan menene
so, yasan darajar abinda yakeson, ya kuma iya
tafiyar da shi ta hanyoyi daban daban, ya iya
tarairaiyar mace da bata kulawa yadda ya
kamata. Sheyasa son da take masa shi yake
k'ara bata k'warin gwiwar fuskantar Mami.
Suna dawowa kuwa kusan kullum sai yazo, har
dai ya zama d'an gida, yadda taga Baba ya
amshi Faruk hannu bibbiyu ya sanya dole taja
bakinta tayi tsit, kuma kullum yazo Zarah ke
raka Meenah fira, hakan yasa ita kanta Mamin
ta rasa gane wurin wa yake zuwa, amma tana
fatan wurin Zarah yake zuwa, don a yadda take
gani mutum ne mai kud'i sosai.
*
K'arfe takwas na dare kamar kullum Faruk ya isa
gidansu Meenah, kasancewar ya zama d'an gida
tsakanin Baba da Mami.
Bayan sun gaisa da Baba, a lokacin Baba yana
da niyyar fita, haka ma Mami tana sama tana
fama da lissafin kud'in kasuwancinta.
Yana nan zaune yana jiran Meenah. Aikuwa sai
gata ta fito tayi kyau kamar kullum cikin material
mai taushi silver da ratsin bak'i a jikinshi, d'inkin
doguwar riga, d'inkin bai kama jikinta ba. Tun
daga nesa suke sakarma da junansu murmushi
mai sanyi. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa,
centre table ne mai bak'in glass a tsakiya wanda
aka d'aura kayan marmari cikin tray kala kala a
cikinsa, irinsu Apple, grapes, banana, orange,
pear da sauransu. Zamewa yayi ya zauna k'asa
gami da rausayar da kai yace.
"Barka da hutu!".
Dariya ya bata sosai saboda yadda yayi
maganar, tace
"Alhamdulillah, muna ta sha kam."
Yayi shiru zuwa wani lokaci sannan yace.
"Zuwa yaushe kike ganin za'a aurar da ke?"
Ita dariya ma ya bata tace
"Aure ay lokaci ne... sai lokaci yayi sannan."
Ya langa6ar da kai yace
"Haka ne, amma ni ko yanzu aka bani ke zan
kar6a hannu bibbiyu, zan nuna maki k'auna ta
ban mamaki, sai dai bansani ba ko ke zaki so ni
kamar yadda nake son ki... sannan ina so idan
Allah ya kaimu zan sanar da iyayenki cewar
aurenki zanyi..."
Ta lumshe idanu cikin wata sabuwar k'auna
dake k'ara mamayarta, ta kuma k'ara lallu6e
mata zuciyarta, tace
"Kar kayi tantama a kaina ya Faruk, soyayyarmu
had'in Allah ce, i respect you and your values..
Faruk d'in da nake so bana ganin kowa sai shi,
bana jin k'aunar kowa sai shi... haka ma banida
buri a yanzu sama da mallakarka a matsayin
mijin aurena na har abada..."
Sai bayan ta furta hakan kuma kunya ta kamata
had'e da mamaki, yadda ta zauna tayi ta zuba
kamar pampo, amma daga baya sai take ganin
kamar su6utar baki tayi. Sai tayi saurin cewa
"Nidai fatana ka rik'e soyayya ta, kada kaci
amanata, ka yarda dani, idan kayi min wannan
to ni kuma nayi maka alk'awarin baka dukkan
kulawa."
Sai ya rasa abin cewa kuma, murmushi tayi ta
sauko k'asa ta shiga yanka masa kayan
marmarin yana sha.
***
Bilki ta soma tsarguwa da yawan zuwan Faruk
cikin gidansu, da yawan ke6ewa da sukeyi shida
Meenah akan Zarah suna fira. Ga wata sabuwar
al'ada da Meenah ta 6ullo da ita na yawan
kwalliya wadda ta gama lura don Faruk take
yinta. Ta gigice ta shiga damuwa sosai, neman
k'arin bayani takeyi tasan Zarah bazata ta6a
fad'a mata ba saboda an ta6o 'yar uwarta haka
bata ganin aibunta, su koda wani abin ne ba'ajin
ta cikinsu kashewa sukeyi su rufe babu mai ji.
Ko fad'a sukayi baya wuce yini d'aya idan kuwa
sun dad'e to kwana d'aya ne sun shirya sun
kuma manta komai. Don haka taga babu mafita
illa ta tunkari Meenah tayi mata bayanin abinda
take zargi.
K'arfe tara na dare ta raka Faruk ya tafi, tana
dawowa ta taradda Mami tsaye gefen gadonta
ta hard'e hanyayyenta wuri d'aya tana huci.
"Mami....?"
Ta dube ta sosai daga sama har k'asa tace
"Amina....!"
Bata amsa ba illa ta dube ta a yadda take
kiranta cikin wata irin murya. Sai kawai ta jeho
mata tambaya
"Meke tsakaninki da Faruk?"
Ta sunkuyar da kanta k'asa, batayi magana ba,
sai da Bilkin ta daka mata uwar tsawa mai gigita
k'wala.
"Bada ke nake magana ba?!"
Cikin sark'ewar murya tace
"Da...ma yace yana...so...na tun muna Katsina,
kuma daman gobe ne Faruk d'in yake niyyar
sanar daku muna son junanmu... mun yanke
shawarar yin au..."
Ji kake tassa!!! Mami ta d'auke ta da wani irin
wawan marin da har sai data ga giftawar wuta,
ta nemi ji da ganinta ta rasa!
AUREN FANSA 22
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Dedicated to Mrs Fawwaz, Sadnaf, Momyn
Sultan, my sakwara, Maman Khady, Jannatuwa,
Faridat Musa, Rufaida Yusuf. One luv guys❤️😍
🌹22 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bilki ta soma magana cikin fushi.
"Kin bani mamaki Meenah, yanzu har yaushe
idonki ya bud'e da kike neman k'wace ma 'yar
uwarki saurayi? Ke ko kunya bakiji ace 'yar
uwarki tana son wani kema kina sonsa? Fatima
fa k'anwarki ce Amina, ay na d'auka ke mai
d'auka ce ki sadaukar mata da wani idan ta
kama, amma wai ke! Kece mai k'wacewa
Meenah."!
Ta share hawayenta cikin tsantsan mamakin
Mamin tasu, muryarta na rawa ta soma magana.
"Mami Faruk bai ta6a cewa yana son Zarah ba,
ni yake so tun asali, ko ita Fatiman ba sonsa
take ba, ni bansan ina kika ji cewar saurayin
Fatima ne ba, idan ma kina tunanin cewar
saurayin Fatima ne to ki daina tun wuri." Sai
kuma ta juya mata baya gami da had'e
hannayenta wuri d'aya tace
"A baya kinsha k'wace min kyauta a makaranta,
amma gaskiya yanzu bazan yarda a k'wace min
Faruk ba, hak'uri zakiyi ki sa mana albarka!"
Sai kawai Bilki tasa salati, yau tana fad'a
Meenah na fad'a.
"Lallai wuyanki yayi k'wari ya isa yanka, akan
nace kin k'wace wa 'yar uwarki saurayi kike
neman ki fad'a min magana Meenah."
Ta fad'a tana nuna kanta.
"Bafa saurayi na bane Mami."
Duk suka d'aga ido tana tsaye bakin k'ofa
idanunta sun kad'a daga fari zuwa ja! A hankali
ta k'araso cikin d'akin tana share hawaye tace
"Akan me zaki mare ta akan maganar da bakida
tabbas a kanta? Mami! Ki sani Meenah 'yar
uwata ce ta jini, ta yaya kike tunanin zata
k'wace min saurayi? To bari kiji abinda baki sani
ba, Faruk saurayin Meenah ne bani ba, ko don
kinga ina zuwa muna fira dashi kikayi tunanin
saurayina ne?" Tayi murmushi tace
"To ba haka bane, ni kawai mun saba ne
sheyasa kikaga ina fita amma lokuta da dama
ay tare da Meenah muke zuwa, duk randa kika
ga naje ni kad'ai to Meenah ta tura ni akan in je
kafin tazo." Ta kalli Meenah dake hawaye wani
na bin wani, tasa hannu ta share mata tace
"Daina kuka 'yar uwata, kiyi hak'uri da abinda
Mami tayi miki, sannan kisa a ranki Faruk naki
ne ke kad'ai kinji?"
Suka rungume juna suna kuka.
Haushi ya kashe Bilku kafin kuma sum sum ta
fice daga d'akin cike da kunya!
A wannan daren Bilki batayi bacci ba, yadda
taga rana haka taga dare.
Washe gari Meenah taga fushin Bilki fiye da
yadda ta saba gani, da Zarah take sabgoginta,
itama sai ta kama kanta a d'aki tak'i fitowa
tana karance-karancenta. Sai dai zuciyarta cike
take da tsoron Mamin, data tuna marin da tasha
jiya sai gabanta ya fad'i.
*
K'arfe goma na safe Faruk yazo, Bilki na zaune
parlor tana chanza channel, tun daga jin
sallamarsa tabi ta d'aure fuska yadda bata ta6a
yi masa ba. Yana zuwa ya zube k'asa yana
gaishe ta, sai kawai ta kafa masa ido bata amsa
ba, k'arshe ma sai ta mik'e ta haye bene zuwa
d'akinta ba tare da tace komai ba. Meenah na
daga bak'in k'ofar kitchen tana ganin komai, ita
kunya ma ta kamata ta kuma kasa k'arasowa
ciki. Sai da ta d'auki akalla minti biyu sannan
tayi ta maza ta shigo parlon kanta a k'asa.
Dukkansu sunyi shiru aka rasa mai fara yin
magana a cikinsu.
Da k'yar Faruk ya daure yayi murmushi cikin
basarwa yace
"Munyi ma Mami laifi ko?"
Ta d'an d'ago suka had'a ido, ta lumshe idanu
tace.
"Tun jiya take haka, mun rasa gane mata."
Yayi shiru cikin tunani, can kuma yace
"K'ila bata amince dani ba..."
Tayi saurin cewa
"Bakomai zata huce ne."
Baba ne ya ke saukowa daga mattakalar bene
Bilkin na biye da shi tana rik'e da briefcase
d'insa, ya hango shi a parlor zaune, da sauri ya
mik'e cikin girmamawa yabi bayansa don yaga
kamar parlonsa ya nufa daga can 6angarensa.
Baba nakan kujera Faruk na gefensa daga k'asa.
Bayan sun gaisa kamar kullum cikin mutunci da
girmama juna, can Baba yace
"Umar Faruk."
Ya d'ago da fararen idanunsa ya dube shi yace
"Na'am Baba."
"Meke tsakaninka da Amina?"
Faruk ya rud'e ya shiga inda inda saboda yadda
yaga Baban ya masa kwarjini, take kuma ya
sadda kansa k'asa.
AUREN FANSA 23
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹23 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Baba yayi murmushi yana dubansa yace.
"Faruk ka saki jikinka dani mana, ka d'auke ni a
matsayin mahaifinka, ka bani amsar tambayar
da nayi maka."
Ya daure yace
"Da...dama Baba, dama... dama... ina so mu
lokaci ne, sannan na gabatar maka da kaina a
cikin manaiman auren Meenah, duk da dai tace
min batada wanda ta tsada, to amma... amma
mun daidaita kanmu."
Baba yayi murmushi gami da lumshe idanu na
'yan mintina, sannan ya bud'e su a hankali kan
Faruk.
"Haka ne, Meenah batada wanda ta tsaida,
hasali ma kai ne mutum na farko da ta ta6a yin
soyayya da shi, sai dai wani hanzari ba gudu ba,
kafin na amince maka da auren Meenah, ina so
kayi min alk'awarin rik'e ta bisa amana da
gaskiya, kar ka ci amanarta kar ka yaudare ta,
shine kawai abinda nake buk'ata daga gare ka.
Duk da nasan dai mahaifinka mutumin kirki ne
kuma ina da tabbacin tarbiyarsa gareku, kuma
ina masa addu'a Allah ya jik'ansu da gafara."
Yace
"Amin Baba, indai wannan ne kar kayi haufi a
kaina insha Allah babu matsala."
Baba yayi murmushin jin dad'i yace
"Alhamdulillah, amma kuma ina so ka bari in
tuntu6i yarinyar tukunna inji ta bakinta, nafiso
na tabbatar sai a sanar da kai don ka turo
magabatan naka." Faruk yayi murmushi.
Yace
"To Baba babu damuwa insha Allah."
Baba yayi murmushi gami da mik'ewa tsaye.
Yace
"Kana iya tafiya Allah yayi muku albarka. Ya
amsa da "Amin."
Baba ya yi gaba, Faruk yabi bayansa yana
jinjina al'amarin.
***
Abu k'arami na neman zama babba, tun tana
ganin abin kamar wasa ta fara ganinshi babba.
Cikin k'ank'anin lokaci Jidda ta fahimci Faruk
soyayya yake, kuma wacce yake so d'in ta kame
masa zuciya farat d'aya, duk wani observation
nata akan Faruk ta gama gane komai, tausayin
kanta ya kama ta. Anisah ce ta shigo d'akin
tana tsaye a bakin k'ofa ta k'ura ma Jidda
idanu, hannunta d'aya d'auke da cup d'in tea
d'ayan kuma yana rik'e da wayarta k'irar
Samsung galaxy S6, a hankali ta k'araso ciki
tana murmushi. Zama tayi kan gadon da Jiddar
ke zaune a kai ta dafa ta.
"Yaya Jidda..."
Firgit! Ta dawo daga duniyar tunani tana kallon
Anisah, sai kawai ta k'ak'alo murmushin dole.
Anisah tayi murmushi.
Meyake damunki?"
Tayi tsai kamar mai tunani kafin tace
"Babu komai."
Anisah ta girgiza kanta.
"Sam ban yarda ba yaya Jidda, na dad'e da
ganin chanzawarki, gaba d'aya kin bi kin sussuce
kin zama wata iri? Har Mama ta soma
tambayarmu abinda akayi miki,a gaskiya yaya
Jidda koma meyake damunki ki fito fili ki fad'a
mana, k'ila da akwai taimakon da zamuyi
miki..."
Har yanzu bata d'ago ba kanta na k'asa dai tana
kallon wayarta. Yusra ce ta lek'o tace
"Anisah ya Najeeb na kira, kuma yace kiyi sauri
kiran nada mahimmanci."
Sai a sannan Jidda ta d'ago tana dariya tace.
"Kice dai za'a je a soye, wai yanzu Anisah har ta
girma ta iya soyayya ko?"
Anisah ta sunkuyar da kanta k'asa tana
murmushi kafin kuma ta fice da gudu ganin zasu
sakata gaba da zolaya.
Yana zaune a garden bisa kujera yana sanye da
jar riga da ash wando (jeans). Kayan sun haska
fatarsa da take kalar fatarsa chocolate mai
haske, ta k'araso tana murmushi, tun daga nesa
yake kallonta har ta iso inda yake. Yayi nisa a
kallonta har bai san lokacin data zauna ba, sai
data kira sunansa yayi firgit ya dawo duniyar
tunani.
"Ya Najeeb."
Yayi sassanyar murmushi yace.
"Anisah kina lafiya?"
Tace
"Lafiya lau, ya naganka nan kai kad'ai?"
Yace
"Ke nake jira ki taya ni fira, ko baza'a ta ya ni
ba?"
Tace
"Uhm, daman Yusra tace kana nema na, sheyasa
na fito."
Yayi murmushi yace
"Hakane, ni nace ta kira ki, daman inji batun
karatunku ina kukayi applying?"
Tace
"Nayi applying first choice d'ina a Base nida
Yusra, sai second choice mukasa Turkish Nile.
Sai last mukasa BUK."
Yace
"Ok yayi Allah ya taimaka."
Tace
"Amin."
Yace
"To ya batun maganarmu ina aka tsaya? Har
yanzu fa baki bani amsa na ba, kullum dana miki
maganar baki bani gamsashiyar amsa, amma
yau ba inda zaki sai kin fad'a min."
Cike da kunya tace
"Wace magana ya Najeeb?"
Yace
"Kin fini sani."
Ta sunkuyar da kanta tana kallon k'asa, yace
"Ke nake saurare fa."
Tace
"Ya Najeeb, wai yanzu kake nufi za'ayi auren?"
Yayi dariya
"Eh mana idan har kin amince me ake jira? Bakiji
me Baba yace ba? Yace mu dukkanmu zai had'a
ya aura damu, yace mazan su fad'i matan da
suke so, matan kuma su gabatar masa da
wanda suke so, yace so yake yayi gaba d'aya ya
huta. Kinga ni da ke sai ayi 'yar gida tuwo na
maina. Ko ba haka ba?"
Tayi shiru bugun zuciyarta ya k'aru, tabbas tana
son Najeeb kuma shima d'in yana sonta sosai.
Tace
"To ya Najeeb Allah ya tabbatar mana da
alkhairi."
Yaji dad'in kalamantanta sosai yace
"To Amin ya Rabbi, daman haka nake so naji
daga bakinki."
Tayi murmushi.
Sai da suka kammala firar tasu ne kafin kuma
su tashi su shige ciki.
MSB💖
AUREN FANSA 24
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹24 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Baba na zaune a parlonshi ya kira Bilki yace ta
turo masa Meenah.
Tana d'akin Zarah a bakin gado tayi tagumi,
Zarah kuma na jera kayanta cikin wardrobe da
aka kawo daga wurin wanki da guga da safe.
Bilki ta shigo d'akin, da sauri Meenah ta d'ago
fararen idanunta ta kalle ta, kallo d'aya zakayi
mata ka tabbatar da tana cikin damuwa mai
tsanani, take Bilki ta 6alla mata harara tace
"Taso muje."
Ta mik'e a sanyaye tabi bayan Bilkin har parlon
Baba, jikinta yayi matuk'ar yin sanyi.
Baba na duba newspaper da idanunsa mak'ale
cikin farin gilashi a lokacin da suka shigo.
Ya ajiye takardun gefe ya kuma cire gilashin yabi
Meenah da kallo a lokacin da take zama kan
carpet, sai ya saki murmushi yace
"Aminatu jiya wannan yaron Faruk yake sanar
dani cewar yana sonki, kuma yana so in bashi
izini don ya turo da magabatansa, k'warai na
yaba da hankalin yaron da kuma nutsuwarsa,
amma kinsan bazanyi saurin yanke hukunci kai
tsaye ba, ina so inji ta bakinki tukunna. Shin
Amina kin amince Faruk ya turo da iyayensa ayi
magana, ko kuma baki amince ba?"
Farin ciki marar misaltuwa taji ya lullu6e ta har
ta gaza 6oye hakan, take kuma ta sadda kanta
k'asa fuskarta d'auke da k'ayataccen murmushi.
Ta kai dubanta ga Bilki taga yadda ta had'e rai
tayi murtuk.
"Amina." Ta d'ago ta kalli Baban tace
"Na'am Baba."
Yace
"Ke nake sauraro, shin kin amince Faruk ya turo
magabatansa ko baki amince ba?"
Da k'yar ta bud'e baki saboda matsananciyar
kunyar

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login