Showing 3001 words to 6000 words out of 42966 words
sauri Goggo tace
"Hamza kana ina yanzu?"
Yace
"Inagida Goggo, lafiya dai ko?"
Tace
"Babu lafiya Hamza, maza maza ka taho asibiti
k'anwarka na nan na nak'uda, kuma ta kafe
tak'i shiga d'akin haihuwar wai sai ka zo, kuma
ga haihuwar tazo kar ta haihu a gaban d'aki
Hamza, kayi sauri don Allah."
A rud'e yace
"Gani nan yanzu wace asibiti ce?"
Tace
"Alheri clinic kayi sauri."
"To." Kawai yace ya fito da gudu daga d'akin,
takalmansa ma daban daban yasa tsabar rud'u
ga gabansa sai fad'uwa yakeyi. Haka dai ya
daure ya figi mota ya fice da sauri, duk da
asibitin batada nisa daga gidansa amma gani
yake bazai isa da sauri ba. Cikin k'ank'anin
lokaci Hamza ya iso Alheri clinic da gudu ya
shiga ciki yana tambayar suna ina. Koda yaje
hanashi shiga akayi sai da ya kira Goggo yace
gashi nan sun hana shi shigowa. Da k'yar ta
rok'esu suka barshi ya shigo.
Yana shiga ya iske Amina sai faman nak'uda
takeyi mai zafi tana kiran sunan Hamza tana
kuka. Da sauri ya isa gareta tana ganinsa ta
k'ara sautin kuka tana fad'in
"Ya Hamza na gode da kazo, wata magana zan
fad'a maka."
Jikinsa yayi sanyi yace
"Koma meye ay sai ki bari ki haihu tukunna..."
"Ya Hamza bazaka gane ba bazan iya bari sai
na haihu ba, amma don Allah ka tsaya ka
saurareni!"
Ta fad'a cikin muryar tsawa, tashi yayi ya fara
safa da marwa idanunsa sun kad'a sunyi ja,
yasan tatsunniyar gizo bata wuce ta k'ok'i,
tabbas yasan maganar da ta saba fad'a masa
yau ma ita d'in ce zata fad'a masa. Don haka
sai yace
"Ko meye zaki fad'a na riga na sani, don haka ki
tashi a shiga dake d'akin kar ki haihu a nan."
Duk'awa tayi tare da fasa wata irin giggitaciyar
k'ara wadda bama Hamza ba har Goggo da
malaman asibitin sai da suka rud'e, fad'i take
"Bazan shiga ciki ba ya Hamza sai kayi min
alk'awari na k'arshe."
Da sauri ya kalleta
"Haba Amina! Meyasa kin faye kafiya ne? Ba
mun gama maganar nan tun tuni ba? Meyasa
kike tado zancen kuma, ki bari ki haihu zamuyi
magana."
Girgiza kanta tayi tana hawaye
"Kayya ya Hamza, don Allah kayi min alk'awarin
kawai."
Goggo ce ta sa baki tace
"Hamza kasan zafin haihuwa, kawai kayi mata
alk'awarin a shiga da ita."
Da k'yar ya iya bud'e bakinsa yace
"Na maki alk'awari Amina, Allah ya sauke ki
lafiya."
Duk da zafin nak'udar da Amina keyi ba hanata
yin mumushi ba, sannan tace
"Nagode ya Hamza nagode!"
Juya mata baya yayi don bazai iya jure ganin
Amina cikin wannan halin ba, a haka aka shiga
da Amina rik'e da hannun Goggo wadda aka
samu aka raba su da k'yar."
Goggo kuka takeyi sosai ji take kamar Amina
bazata fito ba idan ta shiga. Hamza ya zo ya
dinga rarrashinta har ya samu tayi shiru.
Minti kusan talatin ana abu d'aya Amina ta kasa
haihuwa, har an fara shawarar ayi mata CS don
da k'yar idan zata iya haihuwa da kanta. Har
sun fara shawarar a sanar da 'yan uwanta Allah
cikin ikonshi ta haihu. Su Hamza suna jin kukan
jariri suka fara murna suna hamdala.
Jim kad'an wata sister ta fito da jariri tana zuwa
su Goggo suka yo kanta, Goggo ce ta fara cewa
"Alhamdulillah! Ta haihu lafiya."
Hamza kuwa hannu yasa ya kar6i babyn yana
kallo kafin kuma ya kalli nurse d'in yana
murmushi sosai. Nurse d'in ce tace
"Ta haifi mace."
"Alhamdulillah!!" Shine kawai abinda suke cewa.
Kafin kuma Goggo tace
"Ina ita Aminar? Ba'a gama kimtsa ta ba mu
shiga?"
Nurse d'in ce tace
"Sai dai kuyi hak'uri..."
"Me kike nufi da kalamanki?" Cewar Hamza a
d'an rud'e, Goggo ma ta rud'e tace
"Bamu gane abinda kike cewa ba."
Nurse d'in tace
"Abinda nake nufi shine kuyi hak'uri Allah ya
amshi kayanshi, ma'ana Amina ta koma ga
mahaliccinmu."
Saura kad'an Hamza ya saki d'iyar sai da nurse
d'in tayi saurin amsar ta, Goggo kuwa in banda
salati ba abinda takeyi kafufuwanta kasa
d'aukarta sukayi ta zauna da sauri.
Hamza zaman k'asa yayi dirshen yana salati
kafin kuma ya fashe da kuka kamar k'aramin
yaro.
"Daman Amina tafiya zakiyi da gaske? Tasha
fad'a min mutuwa zatayi na kasa yarda." Haka
yayi ta sambatu kamar zautacce a yayinda
Goggo ke kuka rungume da babyn.
Sai da aka fiddo da gawar Amina lullu6e cikin
farin zanin gado bisa gado mai taya a lokacin
kuma suka gasgata ta mutu d'in. Wurin ya kuma
rud'ewa inda Hamza ya rugo ya rugume gadon
yana magana da gawar Amina. Goggo na tsaye
tana kuka tana tausayin Hamza, da k'yar aka
6am6are shi daga jikin gadon aka sanya ta cikin
doguwar ambulance.
Hamza na tuk'i yana kuka har baya ganin
gabanshi, ga kukan baby dake k'ara rud'a shi.
Can gidan Goggo dake cikin G.R.A suka nufa.
Suna isa aka shiga da gawar a cikin gida.
Bayan anyi ma Amina wanka an mata sutura sai
kuma aka d'auketa za'a kaita makwancinta na
k'arshe, gidanta na gaskiya! Hamza na ji na gani
ya saka Amina cikin kabarinta, Masha Allah
Amina tayi mutane don kuwa har tutse akeyi
wurin sakata a makwancinta.
Bayan an gama kuma suka juyo gida inda su
Hamza suka cigaba da kar6ar gaisuwa.
Itama Bilki kullum sai tazo amma bata ta6a dafo
komai ba a matsayin abincin sadaka ba hasali
ma sai tayi kwalliyarta take zuwa bata nuna
wata damuwa ba.
A haka aka yi sadakar uku ana zaman makoki,
inda Hamza ya dangana yana amsar gaisuwar
kowa saidai fa baya magana sai dai yayi shiru
ya k'ura ma wuri d'aya ido kamar yana tunani.
Ko kuma idan akayi masa gaisuwa sai ya dad'e
yana kallon mutum kafin kuma ya amsa
gaisuwar.
Shikenan Amina ta tafi, mutuwa mai yankar
k'auna mai raba tsakani, saidai Allah baya barin
wani don wani yaji dad'i. Allah kasa mu dace,
Allah kayi mana kyakkyawan k'arshe Amin
thumma Amin.
AUREN FANSA 05
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Dedicated to mairo😜 aka Maryam Gafai I heart
you sis❤️ and my sisi Ammin SS 😘😘😘
🌹05 🌹
BAYAN KWANA BIYU
Ranar suna yarinya taci sunan mamanta
marigayiya Amina, daman bawani taron sunan
da akayi wane taro ma ana zaman makoki?
Amina duk da tana jaririya Allah ya zuba mata
hak'uri ga bata kuka sosai sai dai idan taji
yunwa ko wani abin na damunta. Kammaninta
sak na mahaifiyarta ta d'ebo hartta gashinta irin
nata ne lub lub, hasken ne kawai bata d'ebo ba
sa6anin marigayiya da take fara tas kamar
yayanta Hamza amma Amina babyn ita ba fara
bace tas, sai dai tana da kyau duk da batada
hasken ana ganin kyawunta. Idan ta bud'e ido ta
kalli mutum zaka gansu manya ne farare tas!
Baya 'yan kwanaki a lokacin Amina ta kwana 20
cif a duniya Goggo ta kira Hamza da Bilki
gidanta akan cewa tana son magana dasu.
Bayan sun iso suka gaisa Goggo ta d'auko
Amina dake kwance kan gado tana bacci, ta
mik'a ma Hamza ita tana murmushi tace
"Hamza kamar yadda kasani marigayiya ta baka
amanar rik'on Amina kuma ka d'auki alk'awarin
haka, don haka yau na damk'a maka Amina a
matsayin d'iyarka halak malak, da fatan zaka
rik'e ta bisa amana."
Sai kuma ta juyo ta kalli Bilki tace
"Bilkisu ga amanar Amina nan ki rik'e ta amana
saboda kar ki manta marainiya ce gaba da baya
idan har kika ci zalinta Allah zai mata sakayya."
Hamza yace
"Insha Allah Goggo kar ki damu ina k'auanar
Amina kamar 'yar dana haifa haka nake jinta a
raina. Insha Allah zamu rik'e ta amana, Allah ya
taya mu rik'o."
Goggo tace
"Amin, daga cikin dukiyar da mahaifinta ya bar
mata a ciki ake siya mata su pampers da su
madara, sai kayan sawa da sauran abinda ba'a
rasa ba, amma ba kasafai nake amfanin da
kud'in ba sai idan ba kud'i hannuna, amma
tunda yanzu zata dawo hannunku da zama
sheyasa zan damk'a maka kud'inta a hannunka
ka adana mata ko ka juya mata su duk yadda
kaga ya dace."
Jiki a sanyaye Hamza yace
"Insha Allah Goggo."
Daga haka Goggo ta tashi ta had'o kayan Amina
tas sannan ta kira mai gadinta ya saka cikin
mota.
Sai da suka ci abincin rana sannan suka koma
gida, inda ko a mota Bilki ce ta rik'e Amina
sannan ga mamakin Hamza bata nuna komai ba
har rungume ta tayi tana fad'a ma Hamza d'iyar
ta shiga ranta sosai. Ba k'aramin sanyaya mishi
zuciya hakan yayi ba, duk wata fargaba dake
ransa ta kau yadda yaga Bilki na tarairayar
Amina kamar 'yar cikinta.
Bayan sun koma gida da daddare Bilki ta had'a
ruwan zafi tayi ma Amina wanka tas sannan ta
shirya ta cikin kayan baccinta wato overall pink
wadda tayi mata kyau, gashin babyn ya wani yi
irin pam d'innan sannan duk da haka a nannad'e
yake gwanin kyau.
Bayan ta gama ta had'a mata madararta ta bata
tasha ta k'oshi, sannan ta rirrigata ta tayi bacci,
duk akan idon Hamza wanda yake mata kallon
mamaki, abinda baiyi zato ba yau gashi Bilki
nayi.
Bayan ta rirriga Amina tayi bacci zuwa tayi kusa
da Hamza tana rok'on gafarar abubuwan da ta
masa, bai gasgata ba sai da ya ga Bilki na kuka
sosai tana rok'onsa, take ya yarda ta yi nadama
don haka sai ya yafe mata suka shirya.
Haka cikin dare da Amina tayi kuka Bilki zata
tashi ta bata madara har ta koma bacci, gashi
sam bata kukan dare yunwa kad'ai ke tashinta
da kuma an bata madara zata koma shikenan
kuma sai asuba.
Da safe ma haka tayi mata wanka tas ta bata
madararta, koda wasa Hamza bai yi tunanin
za'a samu wata matsala ba daga wurin Bilkin
ba.
Don haka sai ya saki jikinsa ya manta da
maganar k'arin aure.
Duk sadda Hamza ke gida to Amina na
hannunsa yana mata wasa, yana ce mata
"Meenah!" Ya bata madara, ya chanza mata
pampers, ya mata tsarki, sannan ya rirriga ta
har sai tayi bacci.
A haka har sunan ya bita don Hamza Meenah
yake ce mata idan yana mata wasa.
Watan Meenah biyar amma ta zama wata irin
k'atuwa tayi nauyi sosai, da k'yar ake d'aga ta,
ga bata wasa da abinci komai ci takeyi, sai
dad'a kyau takeyi kullum.
Hamza na matuk'ar nuna mata kulawa kullum
yana manne da ita especially weekends ranar da
ba aiki, baya zuwa ko ina zai zauna gida yana
kula da Meenah. Sannan komai yana siya mata
daidai gwargwado bai ta6a nuna gazawarsa ba,
tsaye yake kai da fata wajen ganin Meenah ta
taso cikin ingatacciyar rayuwa.
Watan Meenah bakwai daidai Bilki ta samu ciki,
Allah cikin ikonshi cikin baya bata wahala, murna
had'e da godiya ga Allah suka yi ba adadi.
Zo kuga zakwad'i da rawar kai wurin Bilki. Tun
cikin bai tasa ba ta fara siyayyar kaya kamar
hauka a 6oye, tasan Hamza zai bata kud'i idan
lokacin yayi amma tsabar son abin duniya yasa
bata iya hak'uri. Ko kuma ta d'auka idan ya aje
da yake bai ta6a tunanin tana masa sata ba
sheyasa bai farga ba, sai dai idan yaga kamar
kud'in ba daidai suke ba yayi ta tunanin yadda
akayi ya kashe su.
***
Faruk ne kwance bisa gadonsa na alfarma yayi
ruf da ciki yana game cikin system d'insa. Sai
yanzu na k'are ma d'akin nasa kallo, color d'in
d'akin dark da light blue ne, hartta gadonsa blue
ne da bed-sheet d'in da ke shimfid'e a sama.
Carpet d'in da ke shimfid'e a d'akin blue ne.
Gefe guda kuma study table ne shima blue, sai
cikin wata k'atuwar box kayan wasansa ne
wanda mafi yawa nafi hango jirgin wasa kala
kala, hartta kan gadonsa jirgin wasa ne yakai
biyar gefensa, d'aya kuma a hannunsa, a raina
nace to shi kuma son jirgi yake?
Mummy ce tsaye bakin k'ofa tana kallonsa kafin
kuma ta k'araso tare da zama a kusa dashi ta
dafa shi.
Juyowa yayi yana kallonta kafin yace.
"Mummy na."
Murmushi tayi tana shafa gashin kansa sannan
tace
"Faruk ya naga kana game? Ba nace kazo ka
koyi hardarka ba, ba gobe zaka bayar ba a
islamiyya?"
Murmushi yayi yace
"Nayi Mummy."
Tace
"Anya Faruk?"
Yace
"Allah yanzu na gama."
Tace
"Ok zo muje muyi dinner Daddy da Anisah (auta
'yar shekara uku) suna jiranmu."
"Ok." Yace a yayinda ya d'auki jirginsa ya bi
bayan Mummy....
MSB💖
AUREN FANSA 06
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
🌹06 🌹
Kan dinning suka nufa inda Daddy da Anisah ke
zaune suna labari harda dariya, zama sukayi
itada Faruk
da Daddy ke musu fira a yayinda Mummy ta
zuba ma kowa abincinsa. Wurin kuma yayi tsit
sai k'arar spoon ake ji. Anisah ce ta katse shirun
ta hanyar jefo ma Daddy tambaya.
"Daddy idan na girma me zan zama?"
Daddy dake shirin kai loma a bakinsa ya dakata
yana kallon Anisah kafin kuma yace
"Anisah kenan, duk abinda kike so shi zaki zama
ay."
Anisah tayi dariya
"Ni banason na zama komai nafiso na shiga
aljanna."
Kowa a wurin sai da ya maida hankalinsa gareta
kafin kuma Mummy tace
"Insha Allah zamu shiga aljanna kinji ko?"
Mummy tace
"Abban Faruk ya batun baka manager d'in ko
sun fasa?"
Daddy yayi murmushi
"Ba fasawa sukayi ba Reemah, sai sun duba
cancanta kafin su bada, idan na dace a bani
manager zasu bani, idan kuma wani ya dace a
ba za'a bashi."
Tayi murmushi
"Haka ne kuma, nidai fatana Allah ya baka sa'a
a dukkan lamuranka"
Yaji dad'in addu'ar matarsa ba kad'an ba,
abinda ke k'ara masa sonta kenan kullum cikin
yi masa addu'a takeyi yana murmushi yace
"Amin ya Allah Reemah."
"Ka fidda ranar da zamu tafi Disney world d'in
kuwa?"
Reemah tace bayan ta had'iye abincin dake
bakinta. Daddy ya sha cup d'in Apple juice kafin
yace
"Eh zuwa upper week dai insha Allah lokacin su
Faruk sun gama exams a islamiyya."
"Yeeyy! Mummy Disney world zamuje da gaske?"
Mummy tayi murmushi tace
"Eh Mamana ko bazaki ba?"
Anisah ta zum6ura baki
"O'o ni zanje."
Faruk yace
"Kalle ta to baza'a dake ba."
Anisha ta sa kuka
"Daddy wai baza'a je dani ba?"
Daddy yayi murmushi
"Ya isa yace bazaki ba, ay kece head d'in tafiyar
gaba d'aya zamu iya barinsa amma ke bazamu
iya barinki ba."
Gwalo ta ma Faruk tana share hawayenta. Faruk
yasa dariya. Anisah tasa kuka.
"Mummy kinga Ya Faruk na min dariya ko?"
Mummy ta harari Faruk
"Zaka fara ko Baba na? Meyasa kakeson ganin
kukan k'anwarka ne?"
Yayi dariya
"Aww dariya ma kakeyi Faruk? Bazaka bata
hak'uri ba?''
Ya buga k'afa.
"Wannan 'yar yarinyar zan ba hak'uri? Tab
bazan bada ba."
Daddy yace
"Just say sorry Faruk, you know she won't stop
crying unless you apologize."
Mummy tace
"Oya Faruk now!"
"Ok sorry!"
Take ta bar kukan inda kuma ta cigaba da cin
abincinta kafin kuma ta kalli Daddy
"Daddy zansha ice cream."
Mummy tace
"Me nace miki akan zak'i?"
Anisah ta turo baki
"O'o ni zansha."
Mummy zata k'ara magana Daddy ya d'aga
mata hannu
"Ba ruwanki Reemah, zan siya mata ice cream."
Anisah tashi tayi da gudu ta wuce parlor tana
tsallen dad'i.
Daddy yayi dariya Mummy na taya shi tace
"Anisah kenan, badai rigima ba."
Daddy yayi dariya
"Lokacinta ne, kema kinyi naki ay."
Mummy tace
"Daddy Faruk fa na wurin."
Yayi dariya
"To sai me? Sai na fad'i abubuwan da kikayi ay"
Da sauri ta tashi tana fad'in
"Haba Daddy!"
Yayi dariya
"Kina tantama ne? Bari kiga..."
Kafin ya k'arasa tayi sama da sauri tana dariya.
Daddy ya tashi ya bi bayanta
"Guduwa kikayi Reemah!"
Faruk tsayawa kallonsu yayi yana dariya cikin
ransa yace
"Allah ka k'ara had'a kanmu what a lovely
family!"
***
Meenah na zaune kan carpet tana wasa da abin
wasanta haka kawai kuma sai tasa kuka, Bilki
dake zaune saman kujera tana shan rake tana
kallon wani movie da take so kukan Meenah ya
cika mata kunne. Tsawa ta daka mata
"Ke da Allah kiyi mana shiru yarinya sai shegen
kuka haba!"
Abinka ga yaro wannan tsawa da aka daka mata
ita ta firgita ta yasa ta k'ara fashewa da wani
irin kuka. Haushi ya cika Bilki yasa ta tashi tayi
shigewarta d'aki ta bar Meenah nan na ta faman
kuka kamar zata shid'e. Meenah tayi kuka
baiwar Allah har ta gaji. Nan ta kwanta k'asa
tayi ta ajiyar zuciya har baccin wahala ya
kwashe ta a nan.
Bilki na kwance a d'aki ta jiyo k'arar shigowar
motar Alhaji. Da sauri ta fito tazo ta d'auki
Meenah dake a k'asa ta rungume ta tare da
zama kan kujera tana rirriga ta.
Haka Hamza ya shigo ya same ta, da murmushi
a saman fuskarsa ya k'araso. Yana zama Bilki
ta kalle shi
"Sannu da zuwa Alhaji."
Yana murmushi yace
"Yauwa sannu da aiki Bilki, Meenah bacci akeyi?"
Tayi murmushi
"Eh wallahi yanzu ta gama rigima sai na rirrriga
ta tayi bacci."
Yayi murmushi
"Meenah kenan, ay batada rigima ma k'ila dai
baccin takeji daman."
Tayi yak'e
"Sosai ma ay Meenah baiwar Allah ce batada
rigima."
Yace
"Hakane Allah ya raya mana ita."
Tace
"Amin."
Yace
"Bari naje na watsa ruwa na gaji."
Tace
"Ok sai ka fito."
Tana ganin shigewarsa ta kalli Meenah taja
dogon tsaki, sannan taje ta kwantar da ita a
d'akin Meenah d'in kan gado.
Bayan Alhaji ya gama wanka suna zaune kan
dinning suna cin abinci ya kalli Bilki yace
"Bilki a gaskiya ba abinda zance miki sai dai
nace Allah ya saka da alkhairi akan aikin ladar
da kikeyi. Allah ya baki lada."
Ta kalli Alhaji tace
"Haba Alhaji meye na godiya ay yi wa kaine,
kuma ma Meenah kamar d'iyar dana haifa haka
na d'auke ta. Idan har kana min godiya sai naji
kamar baka d'auke ta a matsayin 'yar cikina
ba."
Yayi murmushin jin dad'i
"Wallahi ko kusa ba haka bane, kawai dai na
yaba da k'ok'arinki."
Tayi dariya
"Allah sarki. Uhm uhm Alhaji dama madararta da
pampers sun k'are shine nace ya kamata a bad
a siyo mata wasu."
Yace
"Wannan ba damuwa zan baki isashen kud'i ki
siyo mata wanda zai dad'e, naga kamar tafison
madarar ma akan abinci."
Tace
"Hakane."
Bayan sun gama ya d'auko kud'i har dubu goma
ya bata. Amsa tayi tace
"Shikenan zanje na siyo mata.
Yace
"Toh ko ki bari idan na fita na siyo mata mana."
Da sauri tace
"Kai haba kai ina kake da lokaci? Ni da nake
gida kullum ka bari zan siyo mata."
Yayi murmushi
"Toh shikenan."
***
Watan haihuwar Bilki ya kama. Kullum sai ta
tambaye shi kud'in siyayya bai ta6a hana ta ba
saboda har ga Allah ya d'auka Bilki ta shiryu.
Wata rana nak'uda ta kama Bilki gadan gadan,
Hamza ya kaita asibiti, suna zuwa ba'a jima ba
ta haifi 'ya mace. Kyakkyawa fara tas mai
k'oshin lafiya.
Haka aka cigaba da zaman barka inda komai
Hamza yayi mata daidai gwargwado komai yana
tafiya daidai.
Ranar suna yarinya taci sunan kakarta ta wurin
Hamza wato Fatima. Haka aka gama taron suna
aka watse lafiya kowa ya koma gidansa....
AUREN FANSA 08
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Another page for my Ummi Aisha thanks for all
the support and care one love dear💖Allah ya k'ara
basira Amin🌹
🌹08 🌹
Laila ce ta cigaba da magana.
"Ko dai har yanzu baki fahimta ba ne?"
Ajiyar zuciya Bilki tayi, sannan tace
"A gaskiya Laila ban iyawa, kisa fa kika ce? Don
ina son dukiya sai akace na kashe su, gaskiya
mu chanza shawara dai."
Laila tayi kwafa.
"To sai akace mu zamu bisu mu aikata
k'udirinmu? Ko kusa ba haka nake nufi ba,
abinda nake nufi a nan shine..."
Nan naga ta rad'a mata wata magana daga
k'arshe dukkansu suka kwashe da dariya.
Bilki tana dariya tace
"Shegiyar gari, lallai Laila sai dai a barki amma
ke shu'uma ce wallahi."
Hajiya Laila ta k'yalk'yale da dariya sosai
sannan tace
"Kema haka."
Bilki ta tashi tana gyara zaman d'ankwalinta
tana kallon Laila tace
"Kamar naji kuman Zarah bari na dubo ta."
Laila tace
"Yi sauri kuwa nima naji."
Jim kad'an sai ga Bilki ta shigo da Zarah a
hannunta da alama yanzu Zaran ta tashi daga
bacci, tana zuwa Laila ta mik'a hannu ta fara
mata wasa, can sai ga Meenah ta fito da alama
bacci ta tashi don kuwa kanta buzu buzu yake,
saboda yanayin gashinta mai cika kuma ga
tsawo sheyasa ko ya ta kwanta sai yayi buzu
buzu. Zuwa tayi kusa da Bilki tana murza idanu.
Su kuwa sai faman ta6e baki sukeyi. Meenah
tace
"Maama wunwa."
Laila ta ta6e baki tace
"Uban me tace?"
Bilki tace
"Ohon mata, ke tafi can ki bamu wuri."
Abinka ga yaro da ba ganewa tayi ba, sai ma ta
matso kusa da Bilki ta jingina da ita. Da sauri
Bilkin ta hankad'e ta gefe ta fad'i k'asa tim!
"Wannan yarinya anyi mayya! Mts." Cewar Laila
had'e da jan tsaki.
Bilki ta jawo hannunta da k'arfi, Meenah ta
fashe da kuka.
Kitchen suka nufa ta had'a mata tea a cup tana
tsaki sannan ta dire mata k'asa.
"Oya zauna kisha yarinya bata aje komai ba sai
ci? Haba!" Nan ta zauna ta shanye tas sannan
ta fito daga kitchen d'in.
Tana gama fad'an haka ta fice taje ta had'o ma
Zarah cereal ta