Showing 21001 words to 24000 words out of 42966 words

Chapter 8 - AUREN FANSA COMPLETE NOVEL

23 Aug 2025

497

kefa? To yi murmushi
mana."
Ya fad'a cike da shagwa6a, hakan ya bata
dariya sosai. Kamo ta yayi yana fad'in.
"Zo muje na siyo maki abin dad'i."
Tayi murmushi suka fice.
***
Da misalin k'arfe 8:35pm yayi sallama, Dada na
aiki a laptop nasa ya dakata gami da amsa
sallamar sannan yayi murmushi.
"Ahh Faruk kaine tafe? Shigo mana."
Faruk ya shigo bayan ya zauna yace
"Dada an wuni lafiya?"
Yace
"Lafiya lau ya iyalin naka da fatan tana lafiya?"
Yace
"Lafiya lau Dada daman wurinka nazo."
Ya dube shi kafin ya cire gilashin dake idonsa na
karatu yace
"To gani lafiya dai?"
Faruk ya sunkuyar da kai tukunna yace.
"Dada daman so nake na nemi izini wurinka zan
k'ara aure."
A razane Dada ya dube shi gami da gyara zama
yace
"Aure fa kace Faruk? Aurenku da ko sati ba'ayi
ba sai kace zaka k'ara aure? Kaima kasan
hakan bazai yiwu ba. Tukunna ma wacece zaka
aura?"
Ya sukuyar da kai
"Dada daman Jidda ce..."
"Ban lamunta ba! Idan ma mafarki kakeyi to ka
farka!"
Mama ta fad'a tana tsaye a bakin k'ofa daga
ganinta kasan tana cikin 6acin rai.
MSB💖

AUREN FANSA 27
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Hip!!!hip!!!hipp!!!
Hurray!!!!!!!
Wishing u long life in Islam and prosperity
Faridat Allah k'aro shekaru masu albarka ya
kuma k'ara basira da hazak'a Amin💃🏻💃🏻💃🏻😍😍
🌹27🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Gaba d'aya suka dube ta sadda take k'arasowa
cikin parlon tare da zama gefen Dada sannan ta
d'ora.
"A gaskiya Alhaji banga amfanin aurensa ba
duka duka yaushe akayi aurennan da zai bijiro
mana da zancen wani auren kuma? Haba me
kake so duniya tace mana? Ko sati d'aya fa
bakuyi ba da aure haba Faruk ka bani mamaki,
me tayi maka? Me ta tsare maka? Yarinya
salihar baiwar Allah zaka ce zakayi ma kishiya
daga yin aure yanzu? To a gaskiya ban lamunta
ba Alhaji, ya sake lala."
Dada bai ce uffan ba yana dai ta kallon Mama
tana zuba har sai data gama sannan ya
numfasa yace
"Wai da kike ta wad'annan maganganun kece
zaki zauna masa dasu ne? Bashi yace yaji ya
gani ba? Ba wanda ya masa dole ay, kuma ni
bazan iya hanasa yin aure ba, amma abinda
nakeso ka sani Faruk shine kasan shi aure ba
abin wasa bane, sannan kuma kaji tsoron Allah
idan har kayi aurennan tofa dole sai kayi adalci
a tsakaninsu, idan kuwa bazakayi adalci ba
gaskiya ban yarda ka sake aure ba kuma bada
yawu na ba, sannan magana ta k'arshe sai na
tuntu6i ita Jiddar naji ta bakinta tukunna..."
"Ay Alhaji kar ma ka 6ata lokacin ka saboda
Jidda ta dad'e da ciwon son Faruk a cikin ranta,
don ma ina kwa6ar ta ay da tuni ta sanar maka
tana sonsa, sai dai Alhaji dole fa sai mun tashi
tsaye kasan halin Jidda bata jin magana ina
gudun kar taje tasa d'iyar mutane a gaba kaga
babu dad'i hakan."
Dada yace
"Haka ne, Faruk a gaskiya sai ka tsawatar ma
Jidda sosai saboda duk wani abin tashin hankali
ta guje shi, idan kuwa bazata iya kiyaya ba to a
fasa auren. Hajiya kira min Jidda tazo ina
nemanta."
"To Alhaji."
Bayan fitar Mama Dada yace
"Ina fatan ka sanar da ita Aminar batun k'ara
aurenka? Kuma ta yarda ta amince da hakan?"
Yayi shiru, Dada ya ce
"Alamu sun nuna min cewa baka sanar da ita ba
Faruk, to a gaskiya idan kaga ka auri Jidda sai
da amincewar Amina, don haka kaje ka nemi
shawarar matarka."
To kawai ya iya cewa ya mik'e, a daidai bakin
k'ofa sukayi kaci6us dasu Jidda zasu shigo, bai
tanka mata ba yasa kai ya fice, bayan sun shigo
Dada ya soma magana.
"Jidda Faruk ne ya zo mana da wani zance wai
yana son auren ki..."
Bai k'arasa ba ta mik'e cike da murna tace
"Dada? Da gaske kakeyi ko wasa? Da gaske
Faruk zai aure ni? Mama da gaske kukeyi don
Allah?"
"Ke meye haka wai!"?
Dada ya daka mata tsawa, zama tayi tana ta
murna a yayinda Dada ya cigaba
"Kinga Jidda ki nutsu ki saurare ni da kunnen
basira, kamar yadda na fad'a miki Faruk yazo
man da zancen aurenki, amma inaso kisani kiji
tsoron Allah Jidda, kar ki cutar da d'iyar mutane
kinsan dai Allah na kallonki, sannan duk wani
abin da zakiyi da bai kamata ba na samu labari
to ki sani k'arshen zamanki gidan Faruk yazo
kenan, don haka ki kama kanki. Hajiya kisa ido
akanta sosai, tashi ki tafi."
Da gudu ta fice tana zuwa d'akinta ta fad'a kan
gado cike da murna, har ma ta fara imagining
wai gata can har sunyi aure da Faruk...
***
Da sallama ya shigo parlon tana zaune kan
kujera tana kallo, tana ganinshi ta mik'e tana
murmushi sosai ta k'arasa wurinsa tace
"Sannu da dawowa my soul." Ta fad'a tana
amsar ledojin da ke hannunsa.
Ya kalle ta tana sanye da army green Indian
sari d'inkin riga da wando, kayan sun matuk'ar
amsarta, fuskarta babu wata kwalliya don
Meenah ba ma'abociyar yin kwalliya bace bata
ma iya ba, hakan yasa kullum fuskanta take
fresh gwanin kyau, d'ankwalin kayan kuwa yana
d'aure akanta d'aurin ya zauna daram a kanta.
Haka kawai kuma sai ta basa tausayi, ganin
mummunna labarin da zai fad'a mata, yana
tunanin yadda ma zata d'auki maganar.
"My soul inata magana kayi shiru."
Ya susa kai yana k'ak'alo murmushi yace
"Ohh sorry baby, banji ba me kika ce?"
Tace
"Nace muje na saka maka ruwan wanka kayi sai
kaci abinci."
Yace
"Ok ok bismillah muje."
Tana gaba yana biye da ita, duk wani motsi
nasa akan idonsa haka kazalika k'amshin
turarenta duk ya cika masa hanci hakan ya
haifar masa da kasala, jikinsa ya mutu.
Suna shiga d'akinsa yau a karo na farko data
ta6a shiga, simple d'aki ne mai d'auke da black
gado duka furnitures d'in dake d'akin black ne,
hartta wasu 'yan kujerun hutawa guda biyu da
table tsakiyarsu suma black ne, carpet black, sai
paintin d'akin ne kawai yake fari k'al hakan ya
haskaka d'akin. K'amshi gami da sanyin ac
kuwa sun had'u sun mata sallama.
Kan gado ya zauna a yayinda da ta shige toilet
nasa ta had'a masa ruwan wanka ta fito. Tana
fitowa tace
"My soul ga ruwan can na had'a maka, idan ka
fito ina parlor."
To kawai ya iya cewa shi duk jikinshi a mace
yake ya rasa dalili.
Bayan ya fito ya kimtsa cikin kayan baccinsa
kalar dark blue, ya fesa turare mai sanyin dad'i
ya fito.
Tana zaune a parlor tana jiranshi, yana zuwa ta
mik'e tana murmushi tace
"Har ka fito my soul? Ga abinci nan na girka
maka."
Yayi yak'e yace
"Thanks my baby."
Tare suka zauna ta shiga zuba masa tuwon
shinkafa miyar ku6ewa d'anya da k'ashin rago a
ciki sai man shanu, bayan ta zuba masa da
tsiyaya masa lemon kwakwar da tayi masa a
glass cup, sai taja kujera tana fuskantarsa, a
natse ya fara cin abincin sai dai gaba d'aya
hankalinsa ba'a kwance yake ba. Ya kalle ta
yaga hankalinta a kwance tana kallonsa, ya
k'ak'alo murmushi yace
"Baby bangane ba ke bazakici abincin bane?"
Tayi murmushi tace
"Zanci amma ina so sai kaci ka k'oshi tukunna."
Ya kalleta cike da mamaki yace
"Sam ban yarda ba, idan bakici ba nima bazan ci
ba."
Da sauri tace
"Haba dai? To zanci."
A tare suka ci abincin bayan sun kammala ta
gyara wurin. Tana kitchen tana d'auraye plates
ya kirata. Ta fito tana zuwa yace.
"Baby zauna ina son magana da ke."
Tace "to." Ta zauna. Ya had'iye wani miyau mai
d'aci tukunna ya fara magana.
"Meenah kinsan dai ina sonki ko?"
Da mamaki tace
"Sosai ma my soul, nasan kana sona amma
lafiya?"
Yace
"Kuma kinsan dai ina k'aunar ki ko?"
Tayi murmushi
"Nasani."
Yace
"Yawwa, kinsan kaddara mai kyau da marar
kyau ko?"
Tayi dariya mai cike da mamaki tace
"Nasani mana."
Yace
"Kinsan kuma dai kowa da tasa kaddarar
Meenah, maganar da zan fad'a maki tana da
nauyi, amma ina so badan ni ba don Allah da
kuma soyayyar da kike min ki fahimce ni."
Jiki a sanyaye tace
"Don Allah my soul ka fad'a min ko meye, sai
kwana kwana kakeyi."
Yayi shiru cikin nazari, can yace
"Hakane zan fad'a maki amma ina so kiyi min
alk'awari guda d'aya."
Tace
"Na me?"
Yace
"Bazaki d'aga hankalinki ba sannan bazakiga laifi
na ba."
Gabanta yayi mummunan fad'uwa, tace
"Don Allah ka fad'a min my soul ka barni a duhu
don Allah."
Tashi yayi tsaye yana mai juya baya don ya
kasa ma had'a idanu da ita. Da k'yar ya iya
tattaro kalamunsa wuri d'aya, yace
"Auren zan k'ara Meenah..."
A gigice take kallonsa, kanta yayi wani dum!
Nuna sa takeyi da hannu tana fad'in
"Anya naji da kyau, sake maimaita mini."
Yace
"Kiyi hak'uri haka d'in dai nace, aure zan k'ara."
"Innalillahi wa inna ilahir raj'iun." Take kuma
gumi ya dinga sassarfo mata ta ko ina, kafin
kuma taji wani irin kuka ya taho mata cikin
tashin hankalin ta fasa ihu sai dai yaji abu ya
fad'i k'asa tim!
AUREN FANSA 28
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Wannan page d'in nakune members na MARZAH
HAUSA NOVELS, nagode da k'aunar da kuke
nuna min, Allah ya bar zumunci amin❤️
🌹28 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Da sauri ya juya abin mamaki wai Meenah ce
kwance kamar ba rai, a gigice yayi kanta ya
shiga jijjiga ta, abin mamaki ko alamar motsi
babu a tattare da ita. Tunda yake a rayuwarsa
bayan mutuwar iyayensa bai ta6a tsintar kansa
cikin matsanancin tashin hankalin irin wannan
ba, ya rud'e ya shiga tashin hankali mai wuyar
fassara.
Da gudu kuma yayi dinning ya d'auko robar
ruwan sanyi ya shiga bud'ewa har wani kyarma
yakeyi.
Yayyafa mata ya dinga yi amma ba alamar zata
farka, hakan yasa ya juye mata shi gaba d'aya a
fuska, aikuwa take ta saki ajiyar zuciya sannan
ta bud'e idanunta wanda suka kad'a sukayi ja
kamar garwashi, tarr take kallonsa kamar
sabuwar halitta, shi d'in ma ita yake kallo babu
ko k'yaftawa, a hankali ya sure ta in banda
sannu babu abinda ke fita a bakinsa.
D'akinsa ya wuce ya shimfid'ar da ita kan gado
sannan ya nemi wuri ya zauna gefen ta har
yanzu ita yake kallo.
"Sannu Meenah... ya kike ji yanzu?"
Kauda fuskarta tayi daga kallon da take masa
zuwa d'ayan 6angaren sannan kuma hawaye
suka shiga kwarara daga idanunta masu zafin
gaske.
"Meenah..."
Ko motsi batayi ba bare yasa ran zata amsa.
Hannunta ya kamo duka biyun yana murzawa,
runtse idanunta tayi a take kuma wasu hawayen
sukayi nasarar saukowa, tana cikin mawuyacin
hali mai wuyar fassara, ita kad'ai tasan me takeji
a halin yanzu.
"Tabbas nasan dole kiji ba dad'i, nasan kin fara
tunanin bana sonki ko? Sheyasa nace zan k'ara
aure ko Meenah? Ina so ki fahimce ni Meenah
har yanzu ina sonki kuma ina k'aunarki babu
abinda ya chanza, auren da kika ga zanyi yana
d'aya daga cikin kaddara ta, ina so a matsayinki
na musulma ki d'auki kaddara Meenah, kawo
wata mace cikin gidannan bazai chanza son da
nake maki ba, nidai fatana ki yarda kuma ki
amince don bazan iya k'ara aureba ba tare da
kin amince ba."
Fuskarta ya shafa ya cigaba
"Wallahi ko yanzu kika ce kar nayi aurennan na
fasa kenan ko da kuwa yanzu za'a d'aura shi,
kuma ko wacece zata shigo cikin gidannan zan
zamo mijin da zai kare miki martaba da kuma
mutunci, har abada bazan wulak'anta ki ba, nidai
fatana inji ta bakinki a halin yanzu Meenah..."
Wani gumi ya ziyarce ta, wato dai da gaske
kishiya zai mata kenan? Ita kam batada sa'a a
rayuwa, ta taso tun tana k'arama tana
d'and'ana bak'in ciki a koda yaushe ba
kwanciyar hankali, tana tunanin auren da zatayi
hutu ne a gareta ashe tayi kuskure. Sai dai kuma
dole zatayi hak'uri tunda haka Allah ya kaddara
mata ita kam.
Ta yunk'ura ta tashi zaune tana mai share
hawaye duk da kuwa wani na bin wani amma
dole ta share, kanta kuwa kamar ana sara mata
guduma haka takeji. Cikin wata irin muryar data
dishe tace
"Haba my soul, meyasa sai ka nemi izini a
wurina sannan ka k'ara aure? Ka manta Allah ya
halasta maka daga mace d'aya zuwa hud'u?
Bana cikin irin matan da idanunsu ke rufewa da
kishi har su fad'a halaka, Allah ya halasta maka
aure ni wacece da zan hana? Ay ban isa ba ma."
Tayi murmushi mai ciwo ta cigaba.
"Ba k'arin aurenka ya fi d'aga min hankali ba,
kasan me ya tada man hankali?"
Yace
"A'ah."
Tayi murmushi
"Wai ace aurenmu da ko sati ba'ayi ba amma
ace zakayi aure, sannan kuma ina tsoron ka
daina sona ne sheyasa ko kuma ka gaji dani."
Yace
"Haba my baby, kima daina irin wannan tunanin
har yanzu ina sonki, kuma insha Allah zan
cigaba har in mutu."
Tayi murmushi
"Na yarda da kai my soul, kuma ina alfahari da
kai a matsayin mijina, a koda yaushe ina gode
ma Allah da ya bani mai sona mai kuma
k'aunata, idan aurennan alkhairi ne Allah ya
tabbatar, idan ba alkhairi bane ba Allah ya za6a
maka mafi alkhairi."
Gabansa yayi mummunan fad'uwa, ya lumshe
idanunsa kafin ya bud'e, ya kalle ta cike da
sha'awa!
Tunda yake a rayuwarsa bai ta6a cin karo da
mace makamanciyar wannan ba. Matsowa yayi
dab da ita yace
"A gaskiya kafin a samu mace irinki a wannan
zamanin sai an tona Meenah. Nima ina so ki
sani ina sonki ina k'aunarki sannan ina alfahari
da ke a matsayin matata."
Duk da tana cikin wani hali hakan bai hanata yin
murmushi ba, ta yunk'ura zata tashi jiri ya
kwashe ta, da sauri Faruk ya taro ta sai kuma ta
fad'a jikinsa haka ya rungume ta kamar wata
jaririya. Wani shock ya kama ko wanensu,
sannan kuma suka dubi juna cikin ido. Sun kai
minti kusan d'aya a haka kafin Meenah ta fara
kauda tata fuskar tana k'ok'arin tashi daga
jikinshi.
Duk ya dabarbarce, kwanciya tayi sakamakon
wani bacci da taji yana neman kwasar ta.
Duka duka batafi second goma ba bacci yayi
awon gaba da ita.
Jikin Faruk yayi matuk'ar sanyi, sannan kuma
take ya fara tsintar kansa cikin wani irin yanayin
da bai ta6a tsintar kansa a ciki ba. Wani abu
yaji yana bin dukkanin illahirin jikinsa tun daga
kansa har zuwa tafin k'afarsa, take tsikar jikinsa
ta tashi tayi wani yarr!
"Hasbunallahu wani'imal wakil." Shine abinda
yake fad'i, sannan ya mik'e jiki a sanyaye ya
fad'a toilet, a gaban sink ya tsaya tare da bud'e
pampo ya shiga wanke fuskarsa, bayan ya gama
sai ya tsaya yana kallon kansa kuma ta mirror,
ba abinda idanunsa ke gani kamar fuskar
Meenah, wani gurin tana murmushi wani gurin
kuma dariya, tsintar kansa yayi yana mai
murmushin shima. Da sauri kuma ya girgiza
kansa ya fice daga toilet d'in yana ta faman
maimaita "No."
Kwanciya yayi gefenta tare da rufe idanu yana
jin wani bak'on al'amarin da bai ta6a ji ba a
tsawon rayuwarsa ba....
Sassanyar iskar asuba mai k'unshe da ni'ima
tare da tarin albarka shi ya daki fuskar Meenah
kasaancewar tagogin d'akin a bud'e suke. Hakan
yasa taja dogon numfashi tare da motsawa, tayi
tsawon minti biyu a haka kafin a hankali ta fara
k'ok'arin tashi zaune.
A natse ta juya tana maida kallonta kan Faruk
da baisan inda duniyar take ba. Tuni abinda ya
faru jiya ya fara dawo mata, nan ta yunk'ura
cikin k'arfin hali ta mik'e duk da batajin k'arfin
jikinta, kasancewar tana fashin sallah sai ta taka
a hankali zuwa jikin window. Hadari ta gani
sosai, iskar damina had'e da yayyafi ya daki
fuskarta, hakan ba k'aramin dad'i yayi mata ba,
tayi ta shak'ar iskan gami da ware hannayenta
don ya ratsa ta sosai, take taji ta samu k'arfin
jikinta fiye da dah.
Ruwan saman ne ya sauko mai k'arfi, ta mik'a
hannayenta duka ta tari ruwan.
K'arar ruwan saman ne ya farkar da Faruk,
idanunsa k'yam a kanta, sai yau ya ta6a ganinta
ba d'ankwali, gashin kanta ya zubo har bayanta
hakan ya faru ne saboda cirewar ribbon d'inta
jiya da daddare. Kanta a nannad'e yake kamar
na jarirai gashj bak'i wuik!
Yayi zumbur ya mik'e tare da duba time ganin
lokacin sallar asuba yasa ya mik'e da sauri ya
nufi toilet.
Har ya gama sallarsa a d'aki Meenah batasan
yanayi ba. Tana can tsaye tana kallon ruwa na
sauka k'asa, abin burgeta yake tun tana
k'arama, ita dai rayuwarta tana son ruwan sama
yanzu haka ji take kamar ta shiga ciki tayi
wanka.
A hakan ya cigaba da kallonta wanda baison
yana yi ba.
"Ina kwana."
Ta fad'a gami da zama gefen gado. Yayi
murmushi
"An tashi lafiya? Ya k'arfin jiki?"
Tace
"Alhamdulillah."
Har yanzu kallonta yake ganin ba wani yanayi na
damuwa a tattare da ita dangane da maganar
jiya ba.
"Lokacin dana suma jiya kasan me ya kamata
kayi min amma ka kasa sai rud'ewa, ashe dai
kana sona haka?"
Take gabansa ya fad'i, ya rasa dalili da ta
ambaci yana sonta sai ya tsinci kansa da
fad'uwar gaba?
Yana jiyo dariyarta har cikin kansa.
"Yanzu dai ina so ka fad'a min kai da ka ganni
cikin wani irin yanayi ka rasa abinyi saboda
kana tunanin ko mutuwa nayi? Ashe kana tsoron
rasa ni?"
Ta k'arasa maganar tana dariya.
Yayi dum, sannan ya mik'e ya zauna gefenta
tare da rik'o hannunta yace.
"Ay dole na tsorata tunda ina ganin zan rasa
masoyiyata ta hak'ik'a."
A zahirin gaskiya baisan ya furta wad'annan
kalaman ba...
Don haka sai yayi saurin tashi tsaye yana fad'in
"Bari nayi wanka yau zan fita office da wuri."
Da mamaki ta kalleshi
"Yanzu fa k'arfe shidda."
Yace
"Eh wurin bakwai nakeson barin gidannan."
Tace
"Ok bari na had'a maka breakfast kafin ka fito."
Da sauri ya tsaida ta
"A'a kar ki wahalar da kanki tunda bakyajin
dad'i."
Tayi dariya
"Haba ba wani wahala bari yanzu zan gama."
Bata jira amsar sa ba ta fice da sauri. Ya dad'e
tsaye a wurin kafin yayi saurin shigewa toilet.
MSB💖
AUREN FANSA 29
✨⭐✨⭐✨⭐✨⭐✨
⭐🌹🌹🌹⭐🌹🌹🌹⭐
🌹⭐✨⭐🌹⭐✨⭐🌹
🌹✨⭐✨⭐✨⭐✨🌹
✨🌹✨⭐🌞⭐✨🌹✨
⭐✨🌹✨⭐✨🌹✨⭐
✨⭐✨🌹✨🌹✨⭐✨
⭐✨⭐✨🌹✨⭐✨🌟
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
AUREN FANSA!!!
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
🌹Na🌹
🌹MARYAM S BELLO🌹
(MSB)
🌟🌹Pure Moment Of Life Writers🌟🌹
Dedicated to Anty Zee and AishatFareeda❤️
nagode da k'auna😍
🌹29 🌹
http://MaryamSBello.blogspot.com
Bayan ya gama shirinsa yayi breakfast sai ya
fara k'ok'arin fita, ba yadda Meenah batayi dashi
ba akan ya hak'ura a gama ruwannan yak'iya
yace aikin da zaiyi yana da mahimmanci sosai.
Haka nan ya d'auki umbrella ya fice cikin
ruwannan.
Bayan ya fita kuma ta hau aikin gida kamar
kullum, ta kimtsa ko ina ta turara gidan da
tuararen wuta ta bi da freshener ta fesa ko ina.
Tayi kalacinta bayan ta gama tayi wanka ta
shirya cikin wani simple lace kalar sararin
samaniya (sky blue) da pink. Tana shirin d'aura
d'ankwali wayarta ta fara ringing, ganin Zarah
yasa tayi murmushi ta kara a kunne.
"Assalamu Alaikum..."
Zarah tayi murmushi
"Wa'alaikumusalam, ya kike?"
Meenah tace
"Uhm bansani ba bayan kin manta dani ma."
Zarah ta d'anyi dariya tace
"Haba sis, ni na isa ne? Gani nayi bai kamata na
takura miki ba nasan kina can kina cin amarci
yadda ya kamata, ba kya buk'atar takura..."
"To aku sarkin magana ya isa haka, ya garin ya
su Mami?"
Tace
"Suna nan lafiya, daman kiranki nayi naji idan
kina gida zan biyo, daga school nake ance
admission ya fito shine naje na dubo mana..."
Cike da murna Meenah tace
"Haba don Allah? Munci?"
Zarah tayi dariya tace
"Oho sai nazo dai, amma ina fatan ango baya
gida don wallahi idan yana nan zan wuce gida
kawai."
"Haba mana Zarah wallahi baya nan kizo ina
kewarki da yawa."
Zarah tayi murmushi
"Nima haka sai nazo."
Da haka sukayi sallama.
Minti sha biyar tsakani Zarah ta iso, rungume
juna sukayi suna murna, Meenah ba k'aramin
dad'in ganin Zarah tayi ba. Can ta shiga kawo
mata kayan motsa baki su lemo da cake, su
dambun nama da sauransu. Meenah tayi
murmushi tace
"La Zarah kinga yadda kika jik'e kuwa? Meyasa
kika fito cikin ruwa? Ki shiga d'akina ki cire
wad'annan kayan ki saka nawa."
Tace "Tab kayanki sun mani kad'an ay."
Meenah tace
"Inji waye? Akwai wanda sukayi min yawa ay."
Zarah tace
"To."
Tunda Zarah tazo take bin Meenah da kallo, har
dai Meenar ta tsargu a lokacin da take tsiyaya
mata lemo a cikin glass cup, bayan ta gama ta
koma ta zauna tana kallon Zarah tace
"Wai lafiya kike min wannan irin kallon haka?"
Zarah ta zuba mata idanu, kafin kuma ta saki
ajiyar zuciya tace
"Meenah gani nayi kin rame sosai, akwai abinda
ke damunki ne?"
Meenah tayi murmushin da bai kai zuci ba tace
"Babu komai me kika gani?"
Zarah tace
"Haba Meenah, tsawon shekarun da muka
d'auka tare da ke nasanki, nasan idan kina cikin
matsala ko akasin haka, kuma a matsayina na
k'anwarki bai kamata ki 6oye min abinda ke
ranki ba Meenah."
Meenah taja ajiyar zuciya tace
"Hakane, bawai na 6oye miki abinda ke raina
bane, kawai abinda zan fad'a ne nasan zai rud'a
ki had'e da mamaki marar misaltuwa."
Da mamaki Zarah tace
"Niko zanso inji menene wannan da zai rud'a ni
haka zai kuma bani mamaki."
Meenah tace
"Uhm bari kedai, to ki nutsu kar ki

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login