Showing 84001 words to 87000 words out of 94661 words
a binciko mun naga yar gidan uban waye? . Khalil ya furta yana janye idanun sa daga hanyar da Nasreen ta wuce . Mom Hajara ce ta furta “ a yau nake so ba sai gobe ba! Murmushi Khalil yayi yana furta “ Kiyi Haƙuri Momy yau inshallah ”. Juyawa yayi yana bin bayan Nasreen don shima ran sa sosai ya ɓaci da ita .....Bin bayan sa Suka yi da kallo Mami na sauke wani irin gwauron Numfashi kana tace “ Ya tabbata Ali yana kula watsatstsun mata irin wannan yarinyar kenan? . Ta furta zancen tana kallon su tare da faɗawa cikin wani irin yanayi na daban.
Kallon ta jidder tayi tana kallon mom Hajara wacce itama har a lokacin take cika kana tace “ Ƙwarai mami to kina tsammanin Ya Khalil ba gaskiya zai faɗa ba kenan ?”. A'a ba haka nake nufi ba , Kar ki manta Khalil na son ma'eesha a jikina ina jin Haidar na yin wani abun amma ban taɓa kawo masa wannan cikin rashin jin sa ba .
Gimtse fuska Mom Hajara tayi tana gyara Zaman mayafin ta kana tace “ Ohhhh wai ke Mamin Haidar bakya taɓa magana ne ba tare da kin saka sunan ma'eesha ba? Komai Ma'eesha Ma'eesha haba don Allah....! Ita yarinya wata can ƙasa gajera ga ƙiba mara sha'awa mtswww.....” ta ja dogon tsaki tana komawa tare da zama bisa kujeran dake kusa da ita .
Uhm”. Jidder ta furta tana ɗaga ƙafarta tare da cewa “ Mom sai kinyi haƙuri , Ai wannan ma kaɗan ne tun da bata gurin , suyi ta mata ɓarin jiki kamar wacce aka ce Aljannar su na ƙarƙashin ƙafafunta . Ni yanzu zan tafi 1:30pm muke da shiga exam .
Ɗagowa Mom Hajara tayi tana kallon ta kamin ta kalli ƙaton agogon falon , ba distance learning kike yi ba ? . Yessss Mom shi nake yi , Amma exam kin san aƙwai wasu da dole sai Mutum yaje hall ya rubuta . Ok Allah ya bada Sa'a . Amin Jidder ta furta tana gyara mayafin ta . Kana ta kalli mami tare da hugging ɗin ta “ Bye bye mom sai na dawo ”. Ta furta tana ficewa daga Falon .
Murmushi Mom Hajara tayi cike da son nata ta furta “ Yarinya mai hankali kenan! . Kallon ta Mami tayi tana caɓe baki kamin ta zauna , Muryar Mom Hajara na cigaba da cewa “ Kin ga har Khalil yasa an binciken yarinyar , Ga taxt din shi ya shigo . Ohk duba ɗiyar Wacece? Mami ta furta tana kallon Mom Hajara wacce take scrolling chart ɗin. Ɗan gyara zaman medical Glass din ta tayi kana tace “ Waye Alhaji Adamu Billionier ? Wai inkiya ɗin sa kenan .
Kallon ta mami tayi tana furta kai anya Alhaji Adamu Billionier ina dai jin sunan sa kamar ɗan kasuwa ne babba , amma ban tabbatar ba gaskiya . Ƴar sa ce kenan? . Girgiza kai Mom Hajara tayi kana tace “ eh a abin cikar da aka yi ba. Amma yanzu zamu sani ai ...daga gobe zasu bata wadataccen tarbiyyar da idan taga mutane zata san yanda ake masu magana da dadin lafazi ”.
**
Gaba ɗaya Ma'eesha ta gama birkicewa kuka take yi kamar ran ta zai fita . Ƙoƙarin controlling kan ta take yi amma ta gagara , Wayyo Uncle ban ƙyauta ba , na zalunce ka , ban maka halarci ba ban kuma maka Adalci ba . Ka yafe mun Uncle.............🥹 Tana maganan tana jin yanda yake jawabi ta Mick cikin Arrogant voice ɗin nan nashi na jarumta . Muryar sa ta ji yana kiran sunan ta wanda gaban ta sai da ya faɗi....cikin sauri ta fara dai daita natsuwar ta tana rufe diary ɗin kana ta goge hawayen fuskar ta wanda bata tsammanin zasu iya daina zuba har ta isa gare sa ”. Ƴammata da manyan mata kowa a wurin crushing ɗin Wannan soja ake yi , wanda in his young age ya zama major . Da dama na tambayar baya da mata ko? Suna jin an ce eh sai ko wacce ta kara gyara zama tana jiran a gama taro ta amshi card numbern sa .
Cike da Wannan takon nata with confidence na RAINON SOJA take takawa ixuwa inda Yake . Gaba ɗaya hankulan mutanen ya dawo akan Wannan kyaƙyƙyawar yarinya wacce ta shige zuƙatan mutane da dama . Sunan murmushi take yi amma wasu irin hawaye ne ke bin kuncinta wanda ta rasa fahimtar na menene ita kan ta . Nishaɗi take ji ko akasin haka , ga narkakkiyar tausayin sa dake tsuma ta . Ƙanwar sa ce hala? Kaji wurin an fara maganganu ƙasa ƙasa . Wow she's beautiful.....Muryar Aliyu ne ya kuma katse su inda suka ji ya yi magana ta Mick da cewa “ That's my wife ❤️ uuuwhmmmmw💋 ya hura mata Wani irin sumbata a Mick ....ihu aka saka da Tafi sojojin wasu na Ƙara ƙamewa na girmamawa . Abun ka ga mace mai fara'a tuni Ma'eesha baki yaƙi rufuwa a hankali ta isa gare sa cikin sauri yana ware mata hannu ta rungume shi ƙaaaam tana sakin kuka , shafa bayan ta yake yi yana ɗan rarrashinta duk da bai san dalilin kukan nata ba . I Always proud of my husband Ina Sonka Uncle Haidar.....Maganan ta ne ya fita ta Mick don basu lura da Mick ɗin na kusa da bakin ta ba . Ihu kika ji na mata da maza har sojojin Tsuma suke yi bisa ga nin irin wannan soyayya mai daɗi da sanyaya zuciya .basu taba ganin so a ƙwaratan irin haka ba , bare kuma sojoji da ake gani basu iya soyayya ba . To yau dai ya ƙaryata . Murmushi yayi yana kai hannun sa tare da goge hawayen fuskar ta , a hankali ya kamata suna sauka daga wurin ....Muryar Mata kake ji suna furta “ Sweat couple 4 life 🥰 ”.
Ficewa suka yi daga taron don hankalin sa ya fi karkata da yasan kukan mene take yi ? Kuma ya akayi ta sauya a lokaci ɗaya....sannan yau da bakin ta take furta “ Ina sonka Uncle Haidar? Abun duka ya basa mamaki ƙwarai . Moto suka shiga inda kai tsaye drivan sa ya ja moton da sauran sojojin da aka kara masa masu kula dasu suna biyo bayan su. Tun da suka shiga moton yake rarrashin ta tare da kissing ɗin ta , bai kuma tambaye ta kukan mene take yi ba ,duk da yana son yin hakan , amma abinka ga miskili sai ya bakin sa ya gangara masa. A haka har suka isa .
Wani irin mahaukacin gida ne ta gan su a ciki ......komai na tsarin gidan na soja ne , har ta fentin gidan milk ne Army green . Flowers din gidan lufffff luffff suma sunyi Kore shataf alamu suna samun kulawa . Ko ina ginin burgewa don tsayawa Ma'eesha tayi tana mamakin gidan , kana ta kalle shi tana cewa “ Uncle nan gidan ka ne ? ”.
Eiye kin ga yafi na Daddy kika nace zama a can ƙyau ? .
A'a Mu ma ai gidan mu da kyau . Dariya yayi yana kama kumatunta tare da cewa “ A'a haba ba haka bane . Ina zaki haɗa Gidan Ali Haidar dana Daddy . Uhmmmm Tom ai dai na Daddy yafi girma . Ta furta tana kallon sa tana murmushi . Eh amma dai nan yafi kyau ya kalle inda ta tsaya itama tana masa ƙurrrrr kaman mai tunanin wani Abu . Ma'eesha tunani me kike yi? Ya furta yana kafeta da lulun idanun sa. Ina sonka Uncle Aliyu.............💯!
*#Aunty eashat Mmnteddy 08081202932*
[1/29, 10:23 AM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
74-75
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500 Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409....✍🏻🤍#Mamanteddy#mrsusm.*
Book 3
Kallon ta yayi yana ɗan tattare wannan giran nasa kana yace “ Me ya faru Ma'eesha mene ya sauyaki haka?”. Me ya faru ? Ya jero mata Tambayar a lokaci guda.... Murmushi tayi tana motsa laɓɓanta da cewa “ Tom don nace ina sonka Shikenan sai don da Wani abu , ko dama na taɓa cewa bana Sonka ne? ” . Girgiza kan sa yayi kana ya furta “ No! Amma Wannan sauyin ban yarda dashi , faɗa mun menene ya sauyaki? Yayi maganan suna shiga daga cikin falon gidan . Shiru tayi masa ba tare da tace dashi komai ba , sai zuba masa ido kurum da tayi tana tunanin Abubuwa da dama . Huwmmm sauke numfashi yayi yana cigaba da cewa “ Ma'eesha a idanun ki sunnuna aƙwai Abun da ke ƙwance cikin zuciyar ki , ban taɓa ganin haka daga gare ki ba . Please ki faɗa mun na fi kowa sanin bakya so na ,kin fi kowa tsanan hali na ....a yanxu kuma nafi son wannan halin naka ”.....ta furta tana katse shi tare da kafe shi da sexy eyes ɗin ta Wanda a lokaci daya hawayen da suka daina zuba suka cigaba da Saukowa ....Kuka take har da shashsheƙa da sauke Ajiyar zuciya, Cikin sauri yakai hannun sa yana shirin taɓa ta amma sai ta ɗan ja baya dashi . Littafin da take ta ɓoye masa ne ta fiddo dashi kan ta tsaye tana miƙa masa . Wani irin mutuwar tsaye yayi yana yin turussssss“ Sirrina! Ya furta yana mai kallon ta . Ran sa yana fara Hasala don bai yarda ma ko kan sa shi yabi cikin littafin ba , rayuwar sa ce gaba ɗaya ,amma tayaya ita ta ɗauka ? . Baki da hankali ne ?? Ya furta a lokaci daya cikin tsawar nan nasa . Kallon sa ta tsaya tana yi , Hawayen na ƙara gudun bin Kuncin ta . Sirrin ka ne Uncle, kuma yau na duba na karanta duka , Uncle me yasa ba ka taɓa bani labari na ba , dama haka labari na yake ? Ta furta tana takowa gaban sa tare da kai hannun ta tana riƙo nasa .
Uncle me yasa ka saki hannaye na baka cika ga ba da bani rainon da ka saba yi ba , cike da gata da kulawa ? Uncle Ni ashe yar gata ce , kai ne kake Abun tausayi . Shigowa na rayuwar ka masifa ce Baka huta ba har yau......saurin rufe mata baki yayi yana yin ƙasa da Muryar shi tare da cewa “ Ya isa! Bana son jin wannan zancen ko ba yanzu ba ”.
Sannan me yasa kika ɗauki mun diary kika karanta ? . Ɗan Kallon sa tayi tana sharce Hawayen dake sauko mata ba tare da tace dashi komai ba. Shiru yayi jikin sa duk yayi sanyi , a hankali ya kai hannun sa yana Rungumo ta jikin sa tare da Furta “ Ya haƙuri Ma'eesha na ya isa haka kinji bana Son wannan kukan naki....Kin gaji kina buƙatar Hutu ko? Ya furta yana Ɗan kallon ta daga Ƙasa . Ɗago
[1/29, 1:13 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
76-77
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500 Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409....✍🏻🤍#Mamanteddy#mrsusm.*
Book 3
Ɗago da Idanun ta tayi tana gyaɗa masa kai Alamar eh kamin ta sakar masa murmushin nan nata tare da bin sa da wani irin kallo wanda ita kan ta bata san yaushe ta fara yi masa irin sa ba , Kallo mai cike da tausayin juna da kuma soyayya. Ina sonka Uncle Haidar...ta furta tana kallon Manyansu idanun sa. Wani irin nauyi yaji Zuciyar sa yayi , farin ciki da jin daɗi na rufe Zuciyar sa. Ɗan murmushi yayi wanda sai da Hushiryar sa suka bayyana kana ya ce “ Mu shiga daga ciki , ki kimtsa sai muci Abinci ko ?......”
**
Waye wani Alhaji Adamu Billionier? Kamata yayi ko waye shi ka saka a kama mun.......Hajara! Muryar General Saleh ya katse Mom Hajara dake surfa masifa , Yanayin Muryar sa ya sauya . Hajara Wai yaushe zaki daina Wannan Masifar taki ne ? Ki dakata mu bi komai ......A'a janar na fahimce ka , kamar cin mutuncin da wannan yarinya tayi bai dameka ba . To Ni zan saka ayi da ƙarfin iko na! Hajara! Ya kuma kiran sunan ta yana katse ta daga magana da take. Mami ne dake gyefe ta fahimci yanayin sauyi daga janar wannan yasa ta amshe wayan tana karawa a kunnen ta tare da cewa “ Janar ko ma mene ke faruwa ina son sani yanzu , Wacece yarinyar? . Huwmmm Wani irin gwauron Numfashi ya sauke kana yace “ zan taho gida yanzu , ku shirya cikin shirin ku zamu tafi tare daku ne duka ”.
Ƙasa mami tayi da Wayar tana kallon Mom Hajara wacce itama ita take kallo.
Na ji kamar bashi bane , duka ya sauya har a Muryar sa ...meke faruwa ne? Mami ta furta tana kallon Hajiya Hajara. Koma meye ai dai yace yana zuwa yanzu ko? To mu jira isowan sa . Ta furta tana ja baya tare da zama a kujeran falon tana karkaɗa ƙafa .
A can ɓangaren General Saleh Yelwa kuwa , Abubuwan ne suka faru tamkar a mafarki tabbas wannan shine ake kira da ikon Allah . Don shi mutum ne mai dattako da girma. Wannan yasa shi ko da yaji labarin Mahaifin Nasreen sai yayi tattaki da kansa ya nufi Gidan Alhaji Adamu. Anan ne abu ya dawo tamkar a yanzu aka yi . Daddy ya kwashi mamaki ya kuma ga ikon Allah . Wanda ba su zata ba a rayuwa ko a mafarki wai yayi Arziki shine Allah ya azurta da ƙazamin ƙuɗi wanda bai san ƙarshen su ba . Wato Alhaji Adamu Yes da No 🤣. Gaba ɗaya a halin gidan an ruɗe don A sa'ilin Daddy yana ganin sa cike da rawar baki da murya ya kira sunan sa.........SALIHU!
Tsayawa Alhaji Adamu yayi yana jin kan sa na juya masa sunan sa kawai da General Saleh ya kira da Salihu. Tun daga nan bai ƙara sanin halin da yake ciki ba , har yanzu da Daddy suka gama magana da Su mami ....
Don Alhaji Adamu yana Asibiti a na basa taimakon gaggawa .
**
Wannan wani irin masifa ne Nasreen kika janyo mana muna zaune lafiya ? Shikenan Yanzu duka zamu tashi a banza a wofi . Don kuwa Alhaji Adamu yana da wowa cikin hayyacin sa yan uwansa ƙila ma har da iyali kin ga mu mun tashi a banza a wofi kenan ......Hajiya falmata ke maganan tana kaiwa da komowa a tsakiyar falon Hankali a tashe......!
[1/31, 5:12 AM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
78-79
*Littafin na kuɗi ne please don Allah kar ki karanta indai baki biya ba . Regular payment₦500 Vip payment₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 idan Vtu transfer ne sai ki tura ta wannan number 09061466409....✍🏻🤍#Mamanteddy#mrsusm.*
Book 3
Shiru Nasreen tayi jikin ta itama ko ina ɓari yake yi , don ba zata so su tashi a haka ba babu tsuntsu bare tarko. Hunmm Mommy ki ƙwantar da hankalin ki ...babu abun da zai faru , iyaka idan kin ga duka abun zai rincaɓe kiyi Aiki wurin boka a kashe shi kawai duk a huta. Ai dai dole a baku Gadon ku , Sannan kuma bai ma riga ya farfaɗon ba bare Har ya gasgata yan uwan sa ne ko suna da jiɓi ko alaƙa tsakanin su . Hummmmm Sauke numfashi mai nauyi Hajiya Falmata tayi kana tace “ Ƙwarai wannan zancen naki yayi kuwa dai dai . A wannan karon da kaina zan tafi , ba zan tsaya yin saƙo ba . Hunmm gyaɗa kai Nasreen tayi tare da cewa “ Gaskiya dai zaifi hakan. A wannan lokaci ne Su duka suka Ari mayafi ko wacce a cikin matann Alhaji Adamu da inda ta nufa. Banda Hajiya Atika da ake ɗaka ana jinya har yau babu Sauƙi sai ƙarin Wahala . Yayi baƙi ta rame wannan jikin matan da cika duka babu ”.
Sunan jinya take amma sosai hankalin ta ya tashi da taji Labarin Alhaji Adamu da kuma halin da ake ciki a yanzu .
**
9:00pm .
Lagos
Ƙwance take a cikin ƙayataccen Bedroom ɗin nata , tana kululluɓe cikin wani lallausar blanket ...tayi filo da Faffaɗɗan ƙirjin sa. Idanun Aliyu Haidar a lumshe suke , akasin nata da suke A buɗe tana aikin zuba masa surutun nan nata Wanda bata gajiya . Ai Uncle ina baka labari yanzu duk na ƙosa ma a koma Hutu don naga Yanda Samira da munaya zasu ƙare ....Uncle! Ta kira sunan sa tana kai hannun ta tare da Shafa Gyefen kuncinsa....idanun sa taji a lumshe, wannan yasa ta cewa “ Barci zaka yi ne ? , Sai a sannan ne ya ware Lulun idanun sa yana gyaɗa mata kai tare da cewa “ Eh ...” Ohk Tom sai da safe ”. Yi addu'a sai muyi barci , ya furta yana ƙara saka hannayen sa tare da Rungume ta tsamm a jikin sa yana daɗa shigar dasu cikin bargo ”.
Motsa bakin ta tayi tana fara Addu'an kana ta kwanta tana furta “ Sai da Safe