Showing 33001 words to 36000 words out of 94661 words

Chapter 12 - RAINON SOJA COMPLETE Hausa Novel

Unknown   

05 Oct 2024

45168

kallon idanun Ma'eesha kana tace “ ina zaki je haka da sassafe ?” . Hummmm inda na saba zuwa da sassafe idan Uncle ya dawo mana! Ta ƙare maganan tana farrr da idanun ta tare da shagwaɓe ma mami fuska ”. Au yanzu da asuba ne ya shigo miki? Wannan wacce irin damu ne? Jiya fa da karfe goma na dare suka dawo shine yaki barci ko Hutawa baiyi ba shine Kema zai hana mun ke sukuni? Maza koma ki kwanta bari naje na sam......Aaahhh🙀 Ma'eesha ta bude baki tare da saurin riƙo Mami tana cewa “ A'a ina mami kinji zauna nima ina so na motsa jikin sai na dawo”. Tana furta haka tayi saurin ficewa daga falon ba tare da ta jira jin mene Mami zata ce ba”.

Bin bayan ta da kallo Mami tayi kana ta Girgiza kai tana furta “ Ma'eesha kenan na Uncle,wato duk wahalar da zai bata ta gummaci tayi koda bata son hakan . Ba zan ɗauki wannan exercise ɗin ba yarinya ta yar lukuta ce ba so nake ta tsiyaye a wahala ba ,macace ba Namiji ko Soja irin sa ba . Mami ta yi zancen tana ɗaga kai tare da kallon Upstairs inda Bedroom din jidderh yake. Itama jidder Bara na tada ita yanzu , tun da ƙanwarta ta tashi itama ta miƙe hakanan, ace mutum ba zai shiga Jami'a ba sai karfe tara ko Goma just because your father general yelwa shi yasa wani gatan baya da amfani. Mami ta ƙare maganan tana nufar Upstairs.

**
Tun da suka fara exercise ɗin a idon Khalil dake daga saman bene yana hango su , hannun sa riƙe da mug na Cofee yana sha da Wannan safiyar don gari yayi shaaa bai haske ba sosai . Kallon ma'eesha Ali haidar yayi inda take tsallen da igiyar nan don yafi bata Wannan training din tamkar wanda zata je atisayen zama Soja ko police . Ma'eesha yau zamu sauya exercise ɗin namu gudu zakiyi kije ƙarshen can ki dawo a minti ɗaya🤔. Saurin kallon nisan wurin tayi kana ta Girgiza kai don babu yanda ta iya ta juya tana fara gudun tun kamin ta kai ta siƙe amma a haka taji yana faɗin “Ƙi ƙara gudu ....don dole tana haki ta isa tana dawowa zuwa inda yake tare da Sauke numfashin gajiya. Kin san minti nawa kikayi kuwa ? . Girgiza kai tayi ta haɗa gumi sharɓan.....Kallon timer⏲️ yayi kana yace “Ni da nace minti ɗaya ke mintuna biyar kika ɗauka har da ƙarin sakan talatin . Kamin Ma'eesha tayi magana ne ya furta “ Maza Juya ki ƙara ki dawo daga farko....Wayyo Uncle I'm tired . You are what? Ya Furta yana kallon ta babu wasa . Sauke idanun ta tayi ƙasa cire da yarinta a galabaice ta furta “ na gaji ba zan iya ba”. No impossible in life , Oya koma ki sake a minti ɗaya zakiyi kije ki dawo . Muje tare.....a tare suka fara gudun yana na wuce ta ya dawo yana furta “ Kina so kiyi kuka a safiyar nan kenan? . A'a Uncle. To ki ƙara sauri . Da gudu tayi gaba tana ƙarawa dai dai Gyefen benen da Khalil yake tayi baya Numfashin ta na ƙoƙarin ɗaukewa luuuuuu tayi zata zube ƙasa da sauri Aliyu ya kai hannun sa yana riƙota tare da rungume ta jikin sa....Numfashin ta ke sauka da ƙarfi da ƙarfi tana jan shi da ƙyarrr. Shafa bayan ta yake yi cike da kulawa a hankali cike da miskilalliyar Muryar sa ya furta “ I'm sorry , Zaki iya kinji Ma'eesha ”.

Yanda yake shafa mata baya yana mata magana yasa Khalil sakin cup din ba tare da ya sani ba . Nan take ya fashe yana tarwatsewa ruwan Cofee din yana fallatsa har inda suke. Wannan yasa Aliyu Haidar ɗagowa daga jikin Ma'eesha yana kallon saman. Kallon kallo suke yi tsakanin su . Kamin Ma'eesha itama ta ɗago tana saurin kallon daga inda taji ƙaran nan .

Gani tayi Khalil ya kama karfen benen daga sama yana dirkowa ƙasa sam bai tsaya bi ta hanya ba. Bude ɗan ƙaramin bakin ta tayi don ta dauka yanda ya dirko to fa ya karairaye ya gama. Tun kamin ya ƙariko Aliyu ya kalli Ma'eesha yana cewa “ Go and rest”. Da sauri ta furta “ Ya Khalil baiji ciwo ....cewa nayi kije ki huta......!!! Yayi maganan yana ɗaga Murya . Da gudu tayi baya tana cewa to.

Isowa inda Aliyu Yake Khalil yayi kana ya furta “ Ali haidar meye na ga kana mawa ma'eesha yanzu? . Wani irin kallo Aliyu yayi masa ba tare da yace komai ba. Kasan nasan ka fiye da kowa a cikin gidan nan . Ɗan ɗaga gira Aliyu yayi kana yace “ Go direct to the point ”. Cike da fushi don Ali dan rainin hankali ne nan Khalil ya furta “ nasan ka nasan yanda kake lalata ƴammata da ko wacce mace ta shigo gonarka. Kai din ɗan iska ne ba mutumin kirki ba , kai Ƙwarto ne shahararre....Don haka daga yau kar ka sake hugging ɗin Ma'eesha bare har ka shafa wani ɓangare na jikin ta..........!


*To masu masoyana makaranta littafin rainon soja anan na dasa aya....✍🏻 Sai mun hadu a night update....Ina sake faɗa don Allah kar ki karanta mun idan baki biyani zufa na ba , rubutun ba sauki ne dashi ba bare kuma tsara labari....ga masu buƙatar karanta littafin Regular payment ₦500 vip payment ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932....Maman teddy's write✍🏻*
[1/13, 7:33 AM] +234 704 512 5150: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*



Page 14
______________________
*Alhamdulillah mun dawo daga ɗan gajeren hutun da muka tafi na kawo maku Cigaban wannan littafi Mai taken rainon soja...ina fatan Ubangiji Allah ya bani ikon kammalawa cikin aminci kaman yanda muka fara. Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban yafe ba😭...ga masu buƙatar payment regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*
________________________

Don haka Ma'eesha ta isa munzalin da Mutum kamar ka koda na kirki ne bai kamata ya shiga jikin ta bare kuma kai . Khalil ya ƙare maganan tare da shan kunu yana haɗe giran sama da ƙasa tamau. Kallon sa Ali haidar yayi yana sakin wani shu'umin murmushi kana ya kauda kan sa can gyefe yana duban inda Ma'eesha take itama idanun ta akan su , don zuciyar ta ya bata da akwai wani abun ne shi yasa Khalil ya dirko daga saman bene hawa na ɗaya . Ganin kuwa yanda fuskar sa tayi tamau yasa ta Fahimtar tabbas da akwai abun da Ya shiga tsakanin shi da Ƙanin nasa .


Ganin yanda Ali Haidar yayi masa banza yasa Khalil ƙara fusata nan ya cigaba da cewa“Miskilancin banza da wofi wurin iskanci kafi kowa shahara ”.

Dariya Aliyu yayi yana shafa sajen fuskar sa tare da cewa“ Khalil kenan! Wai duka wannan sababin saboda Kawai hugging ɗin Ma'eesha da nayi daga faɗi Kasan da zata yi shine kake ta wannan maganganun....kaman ta waye Ni Ali Wacece kuma ma'eesha a tare dani? . Maganan lalata mata da kake yi ai wannan ya isa ya tabbatar maka da cewa Ni Lafiyayyen namiji ne. Sannan mene zanji a jikin wannan Yarinyar? Ka dube ta fa ka gani ƙwailah da ita mene zanji a jikin ta ya Khalil.

Ni kake faɗa mawa magana? Khalil yayi magana yana takowa daf dashi don Zuciyar sa ya fara tafarfasa .

Juyawa Ali haidar yayi yana ƙara kallon ɓangaren da Ma'eesha take kana ya Juyo yana zuba ma Khalil Lulun idanun sa . Cike da Miskilalliyar Muryar sa ya furta “ Kaci albarkacin ta bana so muna saɓani a gaban ta...don Allah ya Khalil mu daina irin wannan Abun yanzu , Kar ka manta tun muna yara muke samun matsala akan ma'eesha a yanzu ne har ka nuna kasan darajar ta? . Ɗaga kafaɗa yayi alamun bai dame shi ba . Yana juyawa tare da wuce Khalil da ya tsaya yana kallon sa .


Takawa yayi yana isa inda Ma'eesha take sai raba ido take don tsoron sa Ma'eesha keji ƙwarai da gaske .

Wuce ki bani wuri!

Ya furta fuskar sa babu alamar wasa ko sakewa. Sum-sum ta juya tana wucewa tare da bashi wuri . Ya Khalil ina kwana . Ta furta da Sauri tana raba shi ba tare da ta jira Jin amsar da zai bata ba . Cike da fara'a ya furta lafiya lau Ma'eesha maza ki yi break fast .

Takaici ne ya kama Aliyu , Humm Wai me Khalil yake nufi ne? Son Ma'eesha yake yi ko mene? Zuciyar sa ta fara masa wannan tambayoyin. Saurin Girgiza kai yayi yana cewa “ a'a Sam ba haka bane ba , don Khalil a wannan watan za'a sanya baikon sa da Rahama. To mene wannan tijaran nasa yake nufi kawai saboda nayi hugging ɗin ta. Ya manta Meye ban sani ba na jikin Ma'eesha. Hattara tsarki Ni nake yi mata amma a yanzu yake faɗa mun munanan maganganu....ko yana tunanin ina jin wani abu dan gane da ita...Aikin banza sai na shayar dashi mamaki tare da shi za'a yi mana baiko dole na fidda ɗaya a cikin biyu , Maryam ko Mimi. Hummmm....sauke numfashi yayi mai huci kana ya cigaba da maganar zuci da cewa “ Duka ba zaɓi na bane....Mami ke liƙa min su , a wannan karon i must accept it. Dole na zabi ɗaya don na ƙaryata tunanin Khalil akaina da Ma'eesha.............✍🏻



Tom kunsan night update Babu yawa🥱 mu tara ana safe lafiya....muje yanda al'amarin zai kasance . Shin waye Mimi??? Sannan kuma Wacece Maryam? Wacce a cikin su Ali gadanga zai zaɓa😄 ya kuke kallon wanga tafiyar......ku Cigaba da biyo alƙalamin mamanteddy✍🏻 . Yau inshallah zamu bude Comment GRP don jin sharhin ku bisa ga wannan labari na rainon soja.......!
[1/13, 7:33 AM] +234 704 512 5150: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*



Page 15
______________________
*Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban yafe ba😭...ga masu buƙatar payment regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*

#Always Alhamdulillah🙏🏻 ________________________

Da wannan tunanin ya nufi falon Mami inda Ya tadda su duka a Dinning table suna breakfast. Takawa yayi yana isa gare su tare da jan kujera yana zama , Bin sa da kallo Mami tayi a ranta tana cewa “ Da'alama Khalil ne ya hana shi wahalar da Ma'eesha da wannan masifaffen morning exercise ɗin nasa”. Dariya ta Gimtse ganin yanda yake cika yana batsewa ita dai Ma'eesha tun da ya zauna tayi ƙasa da kan ta tana sabgogin ta don bata son su haɗa ido bare ya ce tayi wani laifin. Gaishe da General Saleh yayi kana y juya yana ma Mami Barka da Safiya...daga nan kuma ya ɗaure fuska yana mami na fara serving din shi ....Kallon Mami yayi yana cewa “ Mami kina gida gobe? ”.

Ɗago fuska mami tayi tana kallon sa kana ta ɗan Girgiza kai tare da furta “ A'a gobe ina so na leƙa gidan Hajiya na gaida ta ....da wani Abu ne Haidar?. Girgiza kai yayi alamu a'a , yana Cigaba da Karin kumallon sa....Sam Ma'eesha ta' rasa' samun natsuwar ta , haka ta kasa sakin jikin ta .

Kallon Haidar tayi tare da kallon Daddy cike da zazzaƙar Muryar ta wanda tana fara magana Haidar ke furta yi mun shiru ki rage mun murya. “Daddy Uncle Haidar gobe zai koma ko yaushe? ...Dariya ne ya kama General Saleh Wanda sai da yayi mai isar shi kana yace“ Ma'eesha bagaki ga Uncle ɗin naki ba? Ki tambaye shi mana....ya kare maganan yana kallon inda Ali Haidar yake ,yana jin duk abun da suke cewa amma tamkar baiji ba ko baya a gurin. Muryar Daddy ne ya katse su yana Cewa “ Ali kayi shiru Ma'eesha fa tambaya take yaushe zaka koma? . Dariya mami ta sheƙe dashi tana buɗe baki zatayi magana Muryar Jidder ya katse su wanda cike da masifa ta furta “ Tun da gidan na uban ki ne dole ki ƙosa ya koma ”.

Shiru Ma'eesha tayi ta tsaya turusss gwiwar ta yayi sanyi qlau.

Wannan wacce irin ɗabi'a ce kike dashi Jidder? Wani irin mugun hali ne ke gareki? Ina yawan faɗa Miki ki kiyaye mawa Ma'eesha billahil Azeem ranar da na shige Miki ba zakiji da daɗi ba ......! Mami ta furta tana ƙanƙance idanun ta cike da faɗa don ranta ya ɓaci. Muryar General Saleh ne ya katse su yana furta“ Maza Ma'eesha kiyi karin kumallon ki ,idan kin gama kizo Falo na yau zancika Miki alƙawarin ki ....Buɗe baki Ma'eesha tayi tana wangalewa tare da washe shi tana furta “ da Gaske Daddy?”.

Ƙwarai kuwa....” Gimtse fuska Jidder tayi Khalil na kallon ta yana zabga mata harara.
**
Da hantsi wuraren ƙarfe 12 na rana bayan Mami ta tafi gidan Hajiya tsohuwa mahaifiyar General Saleh Yelwa...tun daga falon farko har zuwa na tsakiya zuwa Ɗakunan barcin su kowanne shiru kake ji tamkar babu ɗan adam a cikin gidan . A dai-dai wannan lokacin ne Ma'eesha ta zauna tsakiyar gadon ta tana Fiddo da littafan ta tana karatu . Ɓarayi guda al'ƙur'ani ne da ta gama karantawa kamin ta fara na karatun boko . Gyfen ta ruwa ne wanda ta dauko daga ƴar ƙaramar fridge ɗin ta . Littaffin ta na Chemistry take karantawa duk da kasantuwar Hutu suke yi a wannan lokaci amma hakan bai hanata kullum kasancewa cikin karatu ba . Atom and molecule take karantawa tanajin daɗin karatun don sai da ya fito masu a exam nasu na wannan zango . Hummmm.....numfashi ta ja tana saukewa tare da Lumshe Idanun ta , fuskar Ali haidar ta gani wannan yasa gaban ta yankewa yana faɗi da ƙarfi dafe kan ta tayi tana saurin ware idanun ta. Zuciyarta kawai taji ya tsinke tsoron jarabar sa take yi a ko yaushe.

Motsin Handle door ɗin ta yasa ta saurin kallon direction ɗin tana kara zare ido tamkar wanda tayi ƙarya , a halin yanzu tasan Ya Khalil baya cikin gidan nan don wuraren 11 yazo ya same ta yana faɗa mata zai tafi wurin zaitoon budurwar sa da'akayi masu baiko , har yana tambayar ta abun da zai zo mata dashi na tsaraba anan tace masa cup cake take so....Don mai masu kayan snack jidder Wancen satin tayi mata bakar tijara , Tom kasantuwar itama tana da Dan ilimin ta kawai dai tana son sana'ar snacks ne yasata yin mawa mami wannan hidimar ana biyar ta duk wata . To a wannan karon Jidder da tayi mata zagin tijara takasa Haƙuri don dole ta bar aiki a cikin gidan . Tabbas a yanzu tasan daga ita sai jidder sai kuma dodon nata Aliyu Haidar wannan yasa tana jin motsin Handle duka ta maida hankalin ta idanun ta duka ga ƙofan....“Daaaam”. ƙirjin ma'eesha ya buga ganin Haidar ya shigo yana zuba wani irin Sanyayyar ƙamshi gaba ɗaya wurin ya mamaye da ƙamshin sa . Sam bata san wani duniya take ba har ya iso inda take kana taji Arrogant voice ɗin sa ya katse ta yana cewa “ Keeee dallah rufe baki , kin wani saki baki kaman sakarya.

Kallon sa tayi cike da danne fushin ta don maganan sa ya ɓata mata rai ta kalle sa tana sakin Murmushi Gyefe da gyefen kuncinta na loɓawa . Uncle Barka da rana. Hummmm Me kike yi anan ? Yayi maganan tamkar bai ga littafai a gaban ta ba , Cigaba yayi da cewa“ Dama naji labarin Daddy ya saya Miki waya har da sabon laptop saboda gata . Baki iya komai ba sai sangarci....Humm yayi ƙwafa yana kallon ta tare da zuba mata Lulun idanun sa . Cike da nuna irin ke ya dama yace “ Kar ki manta ke yarinya ce karama SS1 yanzu ne ya kamata kiyi amfani da damarki, sannan charting kar ki so ranar da zan duba wayar ki naga kina ko wani irin media bana son ganin Film ko wani iri a laptop ɗin ki ko a wayar ki duka . Fatan kin fahimce ni?. Y furta yana mai Gimtse fuskar sa babu wasa . Cikin sauri jikin ta na kyarma kar-kar-kar ta gyada masa kai tana cewa “ Ehhh Ehhh..eh Ya khal....Ya Haƙuri Uncle ba zan yi ba Wallahi . Gani tayi ya kafe ta da ido kaman a wannan ranar ya fara ganin ta a rayuwa . Sosai ya tafi tunani na yan sakonni kana ya furta “Kin iya girki? Kamin ta basa amsa ne ya furta“ Ko da yake shekarar ki nawa a yanxu ace baki iya girki ba . Maza miƙe yau wanda tunanin zan iya aure zasu zo . Mimi da Maryam. A cikin su i must choose one ko mimin ko Maryam amma dole sai nayi masu jarabawa wacce taci ita nake tunanin..........Shiru yayi yana kallon Ma'eesha da ta zuba masa ido yana sauraren sa . Tashi ki bani wuri ki ɗaura masu Abinci kala ɗaya ya isa . Sai lemu da ruwa . Ki haɗa masu da farfesun naman rago.

Idan kin ɗaura girkin ki tafi bedroom dina ki gyara mun ba falo ba.

Gyaɗa masa kai tayi tana sauka daga gadon tare da ƙoƙarin ficewa daga Bedroom ɗin .

Ma'eesha kin iya jaloaf rice ne?.

Ɗan ƙasa tayi da kanta a zuciyar ta tana Cewa “ Oho dama kasan ban iyaba ka sani ..ai na bari ne nayi maka sai kaci kai da ƴammatan naka ,dagani

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login