Showing 54001 words to 57000 words out of 94661 words
. Baya ma sani Mene yake fadi a halin yanzu , tun daga zuwan sa , baya tsammanin zai dawo natsuwar sa sai idan Ance masa Ma'eesha ta dawo hayyacin sa. Tabbas a yau a kuma yanzu ya fahimci har a yanzu Ma'eesha rayuwar sa ce! Ba wai kallon da yake kokarin mata bane a yanzu , har a yau soyayyar nan nashi da kulawar da ya saba tun daga yarintar ta babu abin da ya ragu . Fiye da mintina talatin yana a haka gumi ya jiƙa shi sosai , don tuni nurse Zulfa'u ta gudu ta bar sa anan , don ta tsorata da lamarin Aliyu Haidar, ita ko a labarai bata taɓa jin na soja irin wannan ba. Zafin ransa yayi yawa ƙwarai .
Wannan yasa ta nufar emergency don ayi komai a gaban ta , idan Ma'eesha ta tashi to ta tsaya idan kuwa aka samu akasin haka , tabbas ita zata fara guduwa daga Asibitin tun kan a sanar mawa Aliyu Haidar ”.
Shikam Ogan namu Aliyu Haidar jin shiru tsawan mintuna kusan Arba'in yasa Shi fara tunanin nufar emergencyn , dai dai nan Wayar sa ta fara ringing tare da waƙar mum my heart ❤️. Wannan yasa shi fahimtar mai kiran tun kamin ya kai hannun sa ya ɗaga sunan Mami ya bayyana masa . “ Cikin sauri tare da dai daita natsuwar sa yana ƙaƙaro murmushin dole tamkar wacce Mami ke a gaban sa ya furta “ Mami Howfar? How is your day? . Fine HAIDAR where is my baby love ? Ina Ma'eesha na take ? Ta katse shi cike da annashuwa . Ƙirjinsa ne ya buga masa da ƙarfi wannan yasa shi ɗan kai hannun sa yana dafewa kana yace “ Mum she's well , Yanzu ta samu barci amma zuwa Anjima zan kira ki kiji Muryar Babyn naki.
Murmushi Mami tayi mai sauti kana tace “ Alhamdulillah har naji sanyi da ya kasance tana lafiya a yanayin ka ko baka faɗa mun ba nasan Baby Ma'eesha tana jin dadin zaman ta anan , Ka kula mun da ita sosai Ali kana jina ?"…yeah...Yessss Mami ya furta cikin ɗan kame kame . Cikin sanyi cike da rashin Fahimtar komai Mami ta cigaba da cewa “ Ina SO Aliyu ka kula mun da Ma'eesha don Allah ko bayan Raina, bata da kowa da ya kai ka a rayuwa , ina so ka riƙe Ma'eesha ba matsayin ƴar uwa ba , ba ƙanwa nake so ka riƙe ta ba , ka riƙe mun ita tamkar rayuwar ka! A taiƙaice da da hali ka gatanta fiye da kowa ciki har Dani kai na. Ka ɗauke ta tamkar ƴar da ka haifa ko ma fiye da haka . Idan kayi mun wannan To ka gama mun komai Aliyuuu don Allah ka sauke zafin ranka a kan ta , still now she's a child yarinya ce ƙarama ka fini sani ka kula mun da ita sosai ko bayan rai na ”. Mami ki daina wannan maganar inshallah nayi Miki Alƙawari zan kula da ita ”. Daƙyau Haidar thank you my SOJA . 😬 dariyar yaƙe yayi yana jan Ajiyar zuciya tare da cewa “ Love You ma'am , bye bye ”....ƙitttt ya datse kiran yana Fara nufar emergency don ganin halin da Ma'eesha ke ciki .
Kai tsaye ya faɗa inda yaga Wayan babu Ma'eesha babu labarin ta tamkar ba anan aka shigo da ita ba😱 . Keeee!!! Ya daka ma wata nurse Tsawa inda sai da kayan aikin hannun ta suka faɗi ƙasa . Malama ina yarinya ta take ? Ya furta a zafafe idanun sa suna jajir tamkar garwashi jijiyo na ratso masa ta ko ina . Itace Ma'eesha ko? Ta far...far... farfaɗo an kai ta Ɗakin hutawa”. Ta ƙare maganan tana inda inda don ta tsorata da Aliyu . Huuuuuuuwwwww.....Ya Jah numfashi mai ƙarfi kana tamkar ba shi ba , ya furta “ Na gode na gode da kuka taimaka wurin ceto mun rayuwar ta . Zaki iya kaini ɗakin da take . Special room muka kai ta sir , amma muje na kai ka yanzu . Thanks....ya furta yana bin bayan ta ”. Sun fito daga emergency room dinnne kiran taxt massage na mami ya shigo masa inda idanun sa ya fara rawa yana ganin Saƙon kaman ba dai dai idanun sa ke gani ba .
Ga abun da ta rubuta kamar haka ya fara karantawa .
_Hello Am sorry my son , na manta ban faɗa maka duk da Abin na raina , ka tayamu farin ciki mun ga ƙanwata Hajiya Hajara wacce ta ɓata Tsawon shekaru goma sha biyar . Yanzu haka tana gidan Hajiya , kuma tana cikin ƙoashin lafiya 🤗 naji a yanayin ka ɗazu kamar kana busy shiyasa Nima na manta . But a ko wani lokaci kuka dawo zaku haɗu inshallah, please take care of my baby girl , idan ta farka kace mamin ta na gaishe ta ”._
Dafe kan sa yayi kana ya tsaya cak yana dakatawa da tafiyar a sarari yana furta “ Mom Hajara fa tace ? Matar da mu kan mu ba muyi mata cikakken sani ba , itace ta dawo ? Mom Hajara matar da tun da ta taso rayuwar ta ba'a ƙasar nan take yin shi ba , rintse ido yayi yana tunanin to a ina aka ganta? A hankali ya fara tunawa da labarin ta . Kana yace “ Ƙaddara kenan ko wani bawa da kalan nasa life destination. Wannan abu da ya faru da Mom Hajara dama haka yake rubutacce ne a life circle nata . Kallon Nurse din yayi kana yace “ 1 minute please Ina so zan yi kira yanzu. Yana maganan tare da fara kiran numbern Mami don yaji tabbacin Abun shin da gaske ne ko kuwa idanun sa ne basa gane masa dai dai .
Dakatawa da tafiyar nurse din tayi tana furta “ Ok sir ”.
**
Special room .
Ɗago da sexy eyes ɗin nan nata tayi tana kallon nurse narret da ke zuƙar Allura daga sirinji Da'alama ita zata tsira mawa . Nurse gaskiya kin iya aikin sosai don kin yi kokarin ceto rayuwata thankyouuuu very much ”. Murmushi nurse narret tayi tana jin lokaci ɗaya Ma'eesha tana shiga mata rai . Wannan Aiki na ne . Zaki iya faɗa mun sunan ki ?. Yessss ....Sunana Aisha seleh yelwa ,Amma ana kirana da Ma'eesha ”. Wow nice name . Nurse Narret ta furta tana ƙarikowa zuwa inda Ma'eesha ke kwance .
Kinji sauƙi sosai ko kina jin wani ciwo a tare dake ?. No. Ma'eesha ta furta tana Girgiza mata kai tare da sakin mata murmushi. Gyaɗa kai nurse narret tayi kana tace “ Aƙwai wani Abu da zan taimaka Miki dashi ?. Saurin gyaɗa kai Ma'eesha tayi kana tace “ Taimako ɗaya Nurse zaki mun , don Allah idan Uncle ɗina ya tambayeki me yasani suma a lokaci guda . Just told him that I can't be a land army , nauyin ba zan iya ba , I want to be a nurse like you . Amma shi Ya nace yana so na zama SOJA kamar shi . But for me I hate it at all , bana son zama soja ƙwata ƙwata . So can You help me for .....is ok dear , kada ki damu na fahimce ki , a farko nayi tunanin yayan ki ne don kunyi kama sosai , kyaun ku iri ɗaya . Sunana Narret ki dauke Ni tamkar Yar uwar ki, sannan zan Miki wannan taimakon amma Kema da akwai taimako ɗaya da zaki mun wanda bana tsammanin zaki iya.
Ɗan kallon ta Ma'eesha tayi kana tace “ Why can't I do it for you just go direct to the point,Ina sauraren ki .
Hummm....Numfasawa nurse narret tayi kana ta fara cewa “ Zan faɗa mawa Uncle ɗin ki cewa “ Ba ki da ƙarfin zuciya , ma'ana Abu kaɗan yana iya dagula Miki tunani hankalin ki ya tashi , wanda idan aka cigaba da matsa Miki da Abin da bai Miki at any time you can attack with heartbreak, so dole a rinƙa baki kulawa ana nesantar ki da dukkan Abin da zai ɗaga Miki hankali , daga karshe dai kina buƙatar kulawa fiye da komai. Wow you are so wise Sis...😄 . Ma'eesha ta furta tana washe baki tare gyada mawa nurse narret Kai alamun maganar nata yayi mata dai dai .
Yanzu faɗa mun me kike a gare Ni , wani taimako zan kuma Miki indai bai fi ƙarfi na ba ”.
Ina so kisa ma Uncle ɗinki soyayya ta a zuciya🙀”. Ina son shi a kallo ɗaya danayi masa .
What???🙀🤔 . Ma'eesha ta furta tana waro idanun ta waje kana ta cigaba da cewa “ Uncle Aliyu kike so? Please change .....ki sauya shi , Uncle ba mutum bane , ba zaki iya rayuwa dashi ba. Cox ba dai mutum bane kawai ki fahimce ni . Ban san na jefa rayuwarki cikin haɗari . Zafin ransa yayi yawa bai san meye ma SOYAYYA ba .
Ya sani...., narret ta furta tana kallon Ma'eesha ido cikin ido . Kana tace daga lokacin da ya kawo ki nan , irin Soyayyar da nagani mai cike da tsafta da kulawa a kwayar idanun sa dangane dake abun ya tsuma Ni , sannan na dade ina neman namiji kamar sa . Komai irin wanda nake so ne na gani a tare da yayan ki ,sannan idan ina so abu ko ta halin yaya ina samun shi .
Kin iya faɗa dai ko? Ma'eesha ta furta cike da Yarinta, tana cigaba da cewa “ I see like you're not Muslim are you a Christian? . No I'm not . Ni ruwa biyu ce , mahaifina musulmi ne ,mahaifiya ta ce take Ba musulma ba . Amma addinin mahaifina nake wato Musulunci .
Kar ki damu zan yi farin cikin ki zama daya daga cikin ahalin mu . Murmushi narret tayi tana kokarin magana kenan , suka ji motsin kofa da sauri Ma'eesha ta rufe ido tana jan numfashi tamkar mai barci .
Aliyu ne ya shigo da wannan nurse din , fuskar sa tamkar ba shi ba a yanzu . Wani sanyi yake ji yana ratsa zuciyar sa . Kallon narret yayi da ta kashe shi da ido yana cewa “ na gode da kukayi wannan kokarin , zaku iya bari na daga Ni sai Ma'eesha ina so na ganta sosai . Okay sir amma yanzu ta samu barci . Okay . Ya furta yana takawa ixuwa inda Ma'eesha ke kwance kana Narret ta furta idan ka gama zaka iya samu na a Office sai nayi maka bayanin ciwon nata . Ok ya furta yana yin ƙasa da Gwiwowin sa zuwa gaban fuskar Ma'eesha . Nan su kuma suka juya suna barin room ɗin.
Hannun sa yakai yana shafa kyaƙyƙyawar fuskar ta . A hankali ya fara tuno da Shafa fuskar ta da ya fara yi a rayuwa kamar haka , a lokacin da take hali mawuyaci, na rayuwa ko mutuwa na hannun ALLAH . Wasu irin ƙwallah ne yaji sun zobo masa suna sauka saman fuskar ta ,inda taji ruwan hawaye na ɗigar masa . Lamo ta ƙara yi tana yi tamkar mai barci . Jin al'amarin take tamkar a mafarki dama Uncle Aliyu Yana kuka?. A hankali taji laɓɓansa yana sauka saman goshinta yana manna mata kisss 😘 tare da furta kalmar “ I love you!🥹 Cikin raunanniyar murya ya fara furta “ Na gode ma ALLAH da ya zamana kin farka babu Abinda Ya sameki Ma'eesha na , Tun kina ƙarama nake Sonki na kuma raineki saboda mutuwar son da nake miki, me zai sa a yanzu na wahalar dake ....Saboda Wancen shashashan mana!!! Ya furta da ƙarfi yana sauke wuci tare da kiran sunan Khalil da ƙarfi , yana fara masifar nan nasa tamkar wanda Khalil dinnne a gaban sa . Dole kowa ya bar mun Ma'eesha domin ita din tawa ce ". Kun manta lokacin da kuka guje ta , ciki har da kai Khalil sai a yanzu Zaka ce kana Sonta wannan ba me yiwuwa bane , ba jin son ta kake a jinin jikin ka ba , a taiƙaice sha'awar ta kake yi , daga lokacin da kayi archiving what You want from her , shi kenan zaka mai damun da ita abun tausayi, a Kullum mafarki na Ma'eesha ta yi rayuwar farin ciki , daga hakan ne yasa Ni na yanke shawarar zama Abokin Rayuwar ta na har Abada! Ma'eesha ita kaɗai zan Rayu da ita..........ya yi maganan yana kama hannun ta tare da maƙale shi da nata yana ɗaura laɓɓansa bisa hannun nata tare da furta kalmar “ i love you.......!
*Don girman Allah kar ki karanta in dai Baki biya ba . Regular payment ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 #mamanteddy#mrs usm.😘*
[1/19, 5:15 AM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*
https://youtube.com/@mamanteddy4123?si=1cwxAAGsGEzYkelS
Subscribe to my channel@maman teddy.
29~30.
*Don Allah kar ki karanta wannan labarin indai baki biya kuɗin sa ba . Ga masu buƙatar payment na littafin Rainon soja ga yanda tsarin yake.... Regular group₦500 Vip group₦1000 SPC payment₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932*
_________________________
Sosai yake kissing ɗin taffaan hannun ta ta baya , wanda ita kanta Bata san iyaka Adadin lokacin da ya ɗauka akan ta a hakan ba . Huwwwwmmmm....Saukar Ajiyar zuciya sa da taji ne yasa ta ƙara yin lamo tana bin lafiyar Gadon , duk da Zuciyar ta Wani irin bugawa yake da ƙarfi da ƙarfi amma kuma a haka ta daure ta kasa motsa koda ɗan yatsa bare ya fahimci idanun ta biyu . Wata zuciyar ne take ce mata “ Ma'eesha kika yi kuskuren buɗe idanun ki ko kika motsa ki ka tashi daga wannan barcin ƙaryar da kike yi Wallahi Uncle ya fahimci kinji mene yake cewa sunan “ Sorry , don sai ya karairaya ki . A yanzu abun da ya kamata ki yi shine shiru ki kama bakin ki , Tom Amma Sauran ƴammatan sa duka baya san su ne? Me yasa ya ce dani kaɗai zai yi Rayuwa? Shi kuma Ya Khaleel cewa yayi damu biyu zai yi Rayuwa, amma a zahiri Ya Khaleel shine gatana! Kamar wanda take magana a zahiri wata Zuciyar ta bata amsa da cewa “ Shi Ya Khaleel yana sonki fa sosai , Kuma bai taɓa cutar dake ba , Sannan yana San farin cikin ki ne sosai . Shi kuma Uncle so yake ya Aure ki don ku zauna daga ke sai shi yanda komene zai Miki babu mai gani ko yaji. Ohhhh kika Faɗa Hannun sa kin shiga uku . Gwara ma kiyi sauri ki karbi soyayyar Ya Khaleel da me son ki tsakani da ALLAH ”. Motsin miƙewar sa ne ya katse mata tunanin ta , wannan yasa ta Yin shiru tana tsagaitawa har taji fitar sa kana ta Fara Ware idanun ta A hankali tana bin bayan wucewar sa Da kallo . Ƙarya kake yi Wallahi Uncle ban taɓa ganin mugu irin ka ba . Tun da na taso kake mugunta mun , ba zan taɓa bari na Aure ka ba , ina tausaya mawa macen da ta Aure ka , bare kuma Ni da kaina , ai tuni zuciya ta zata buga , ina dai maka fatan Alheri , Allah ya baka mata wacce zata iya haƙuri da halinka ”. Komawa tayi tana rintse idanun ta sakamakon kan ta da taji yana mata ciwo , alamun barci nason ɗaukar ta . A hankali ta fara sauke numfashi kamin daga bisani ta fara tunanin irin horon Azaban da Uncle Aliyu ke bata wai duk na zama SOJA da Wannan tunanin ne wani nannauyar barcin yayi Awaon gaba da ita ”.
**
Hajiya Atika ne ta kalli Rabi kana tace “ Inaso kamin yammaci a yau Boka Aruguntsu ya Aiko da Aljanun fitina a cikin gidan nan , wanda zai tarwatsa zaman Lafiyar Auren Hajiya Falmata , a taƙaice ina so Ta ko wani hali A yau dai Falmata ta bar cikin gidan nan , ita da shegiyar ƴar cen nata , dama duk wani abu da ya shafi nata ”. Tom an gama Hajiya , faɗa naki aikatawa na Aruguntsu......Rabi ta furta tana wani ƙasa da murya irin na makirai, kana ta cigaba da cewa “ Amma Hajiya Kuɗin nan sunyi ƙasa 100k fa , wannan Aiki ai babba ne kece fa ta Alhaji Adamu, don haka ki daɗo wasu yanda kamin faɗuwar rana zaki ga Aikin Aruguntsu . Kai tsaye cike da jin an fangama ta an fasa mata kai Hajiya Atika ta furta “ Na ƙara Miki kamar sa akai masa 200k Ni dai fatana Aiki ya biya . Wangale baki Rabi tayi kana tace “ Baki da matsala Hajiya Bara yanzu na falfala don mu ga Aikin mu nan kusa . Yauwa rabi Shiyasa a kullum kike ta hannun damata ”. Kwasar kuɗin Rabi tayi tana ficewa daga falon Hajiya Atika kana tace “ Wannan kudin babu Wanda zan ba shi sai Basiru, ALLAH ka gani ina mutuwar son wannan bawa , Allah ka taimake Ni kasa ya Aure Ni ya fiddani daga Wannan zawarcin da nake ciki, ya kuma cire Ni daga Wannan Rayuwar bautar da nake yi na Aikatau ɗin gidan masu hali ”.
Da Hakan Ne Rabi ta gangara tana barin gidan Alhaji Adamu Yes and No 😹 kana ta tare mai Adaidaita tana nufar layin da Take samun masoyin nata wanda Allah ya sa mata Son shi a zuciya , shi kuma a kullum wahalar da ita yake yi , don irin mazan nan ne yan iska masu lalata yara da manya , kuma yana da Aure har da yara Amma shi Abin nashi munin yakai