Showing 30001 words to 33000 words out of 94661 words
tana kafe shi da ido zuciyar ta na harbawa da ƙarfi lokaci guda , don bata san mene zata ce masa idan ya tambaye ta ina Ma'eeshan nasa ba?”. Ɗan rufe idanun ta tayi tana ware su kana tayi saurin kallon stairs ɗin da Khalil ke saukowa hannun sa Ɗauke da Laptop da alama wani Abin zaiyi mai muhimmanci ko yana kan yi. “Hummmm....Dogon Numfashi ta sauke tana maida kallon ta ga Ali Haidar, da yake sakin mata murmushin nan nasa, fuskar sa ya tara ƙasumba tamkar ba Daga Aikin soja yake ba. Duk wata cikar zati na Cikakken Namiji saurayi ya gama bayyana masa, Don a wannan lokaci yakai 27 . Yana sanye cikin ƙananun kaya na Hutawa da shan iska , White t.shirt da boxer wani Black mai yarfin kakin Soja...He looks neat and breathtaking💔 Bin ta yake da innocent face ɗin sa kana taga ya ware hannun sa yana furta “ taho mana Jidder na”.
Murmushi Tayi cike da jin dadin ganin nasu don bata yi tsammanin Dawowan su ba ta nufi Aliyu tana zama tare da shigewa jikin sa tana furta “ Oyoyo Ya Haidar 💃🏻”....Kee ina Ma'eesha ? ” .
Muryar Khalil ya katse su , Wanda a hankali ta ɗago tana kallon sa kana ta kalli Aliyu sai ta fara kame-kame tana cuno bakin ta gaba . Ya Khalil bakayi kyawata ba ne kake tambayar Ma'eesha ita kaɗai? . Zama yayi a kujeran dake fuskantar nasu kana yace“ Nayi kyawar ku duka, yau aka yi Hutu ina result din ki ? Ina kuma nata nasan ta she is talented, Shiyasa na ƙagu naga na nawa tayi ?”. Hummmm Ai ba tare muke ba ....kaman ya ba tare kuke ba ? Yess tana hanya zata shigo yanzu. Kamin Khalil ya ƙara magana tuni ta miƙe tana faɗin “ Lemme go and take shower , idan na dawo sai ka duba result din nawa ”. Bin ta da kallo Khalil yayi , kana ya kalli Aliyu wanda yake shan Lemun tsamin da yasa aka yi masa juise nashi. Shan Lemon sa yake tamkar baya jin mene suke faɗi.
Takaici ne ya kama khalil tabbas shi jikin sa bai bashi ba , Miƙewa yayi yana furta “ Ali baka ji menake cema jidderh ba? Wai kai wannan lemon amfanin me yake maka?. Kallon sa Aliyu yayi a Miskilance kana ya kalli Ruwan lemon hannun sa , motsa laɓɓan sa yayi tare da cewa“ Baka taɓa sanin mene lemon tsami ke sawa ba ko ragewa? , Tsayawa Khalil yayi kana yace “ Ban sani ba ”. Aje cup ɗin yayi yana kallon sa tare da gyara zaman sa kamin yace “Alright rage sha'awa , don Ni fa bana tsammanin Zan koma Bakin Aiki ba tare da Aure ba , da matata zan koma. “Wani irin kallo Khalil yayi masa idan da sabo ya saba da iskancin Aliyu baya ɗaukar sa da mutunci ko yaji kunyar sa na yayan sa ,ya dauke sa tamkar aboki ....mtswwwww Bad behavior, ya furta yana hararan Aliyu tare da Cigaba da cewa “ Na tsani wannan Ɗabi'ar naka Haidar, idan kaso ka Auri Huɗu a lokaci daya.
Wani irin dariya Aliyu yayi wanda sai da na ƙara kallon sa , gaba ɗaya ya sauya ya wani koma Arrogant har a Muryar sa. Dariya yayi irin ta Basawan soja “Hahahaha...”! Ai shikenan Ya Khalil dama na faɗa maka Ni mace ɗaya ba zan iya rayuwa da ita ba ,don ba zan samu biyar buƙatan.......Ɗaga masa hannu khalil yayi yana dakatar dashi kana yace “ Ka bari idan Daddy yazo sai kayi masa bayanin Aure kake buƙata , Ni Bara na leƙa naga Ma'eesha, na ƙosa naga yanda yanzu ta girma shekaru uku bamu ganta ba”.
Ok Ali ya furta yana kauda kan sa gyefe , yayin da Khaleel cikin sauri ya fice daga Falon ”.
**
Bayan mami sun fita ba daɗewa ruwan ya fara tsagaitawa, Ya zama sai dai yayyafi irin mai ƙarfin nan. Titin babu kowa kaman an share ko abun hawa babu masu wucewa kowa ya fake a mafakarsa. Ma'eesha ta hanga ita kaɗai tana tafiya tana rungume da hannayen ta alamar sanyi na kaɗata. Gaba ɗaya ta jiƙe sharɓammm sai tafiya take , komai nata a salɓi take yin shi alamu har ta gaji da tafiya. Fitowa Mami tayi daga moton jikin ta a mace zuciyar ta na kuka ta fara takawa ixuwa inda Ma'eesha take. Ɗan nesa da ita ta tsaya tana ƙare ma kyaƙyƙyawar fuskar ta kallo wanda kan ta ke ƙasa sam bata lura da Mami ba , har ta tako zuwa gaban ta .
Ƙafafun mami ta gani a gaban ta ,wannan yasa ma'eesha saurin Ɗagowa suna haɗa ido da Mami dake zubda Wasu irin ƙwallah...Cikin Sanyin murya tana Wangale mata baki cike da fara'ar nan nata ta furta “ Mami...”! Lumshe ido Mami tayi wasu hawayen na sauko mata kana cikin sauri ta furta “ Na'am Babyn Mami taho gare ni”. Da gudu Ma'eesha ta faɗa jikin mami data rage Tsawon ta itama tana Rungume Ta tsammmmm....Ina sonki Ma'eesha na , tayi maganan tana ƙara mannata da jikin ta . Ina sonki Nima mami. Caaakkk ta ɗauki Ma'eesha tana murmushi tare da cewa“ Yau Ali da Khalil sun dawo fa😄”.
Yeeeeee Mami muyi sauri Uncle sun dawo? Daddy fa? Moton suka shige kana Mami tace “ Jidderh ce tace ki fita ? Me Yasa baki fake a wani wurin ba? Yau sai na hukunta Jidder, yanzu zan kira Doctor Isma'il ya taho ya duba ki , za kisha magani ko Ma'eesha na?
Murmushi Ma'eesha tayi kana ta gyaɗa mata kai cike da yarinta ta furta “Eh mami amma kar ki ma Anti jidderh komai , laifi nayi mata ” . A'a nafa sanki bakya laifi Ma'eesha . To mami na kiyi Haƙuri ki yafe ma Anti Jidder.
Tsayawa Mami tayi tana kallon ta kana ta kai hannu tana kwantota bisa ƙirjin ta . A hankali take shafa bayan Ma'eesha tana cije laɓɓanta ita kaɗai tasan halin baƙin cikin da zuciyar ta ke ciki a halin yanzu .
**
Fitowa tayi daga Bedroom ɗin ta tare da isowa tsakiyar falon, sai ƙamshi take yi tana hura hanci .....Sanye take cikin rigar Atampha doguwa mai ƙaramar hannu an mata ɗinkin da ya kama jikin ta sosai . Dama ba gwanar saka Kallabi Bace haka ta fito Attachment ɗin kan ta na reto har tsakiyar baya , Wanda yake ɗauke da launin milk don ba bama baƙi ta sanya ba . Kunnen ta ɗaya cikin ear phone yayin da hannun ta ke ɗauke da Wayar ta. Plate shoe ta sanya tana mai isowa zuwa Tsakiyar falon Nasreen tayi tana wannan yauƙi tare da caɓe baki tana bin Ma'aikatan dake falon da Wani irin wulaƙantaccen kallo . “Barka da wannan lokaci Hajiya ”.
Muryar Ma'aikatan ya katse ta inda ta ƙara ƙare masu kallo a ciki ta amsa su da “ yauwa, tana wuce su tare da fitowa falon zuwa wajen farfajiyar gidan.....Babban magana gida ne na gani wani irin mahaukacin gida mai girman gaske wanda ya ƙayatu har ya gaji da ƙayatuwa. Gida ne zaka rantse da Allah unguwace guda ,don yafi girman wasu unguwan....Part part ne sun kai 7 amma ko wanne da bene bisa kan part ɗin , Benen ma biyu aka ɗaura ba Ɗaya ba. Gida ce da ka gani kasan na wani attajirin me kudin ne wanda irin su ma baka ganin su a gida Nigeria.....Abu ɗaya ya bani mamaki shine Yanda naga duk Girman gidan da kuɗin dake cikin ta ba'a Aje wasu masu tsoron gidan birjik kaman na gidan General Saleh Yelwa ba . Wannan ya sani tunani da kuma ƙaguwa na son ganin mamallakin wannan gida. Gani nayi Nasreen ta kai hannun ta tana bi ta lifta kamin tayi sama tana hayewa ixuwa wani irin falo mai ɗauke da Adon Golden komai na wurin .
“Hello , Hello babe ...” Maganan take jikin ta ko ina rawa yake yi kar-kar-kar tamkar zata kifa saboda tsoron wanda take wayar dashi . Al...Aliyu ina hanya don Allah mu haɗu kaji? Kasan ba zan iya rintsawa ba idan ban sanyaka cikin idanuwata ba......Yanzu Ruwan ya ɗauke zan taho guest house ɗin ka yanzu.
Duk maganan da take zuba shi take ba tare da ta jira jin mene Ali zai ce mata ba , Murmushi tayi tana datse kiran tare da furta “ Ohhh mah Handsome....Nayi kyawarka sosai. Ta furta zancen tana kutsa kan ta ixuwa Ƙaramin falon dake cikin babban falon da ta baro.
Wani attajirin Alhaji na gani sanye cikin shigar sa ta manyan mutane cikin faran shadda fari ƙal wanda tsadarta ma ƙwaƙwalwa ba zata ɗauka ba . A shekaru yakai 65 a duniya haka zaliƙa kan sa babu ɗigon farin gashi . Kallon sa tayi a kaikaice tana ɗan ƙasa da murya tare da cewa “ Abba nazo ne amsan Kuɗin Yes da No😱” .........................!
Masoyana free page zai ƙare a next page me kuka gani a wannan salon tafiyar 💃🏻tun a yanzu nasan abubuwan sun fara sauya maku😄badaƙalar na gaba ....shin waye wannan Abban da bai san Meye Yes da No ba😹? Ku Cigaba da biyo alƙalamin Aysha mmnteddy.
*Littafin na kudi ne book 1 zai ƙare a next page book 2 Kuma sai a fara payment nashi..... regular group ₦500 vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN.*
[1/13, 7:33 AM] +234 704 512 5150: *🕊️RAINON SOJA🕊️*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story.*
Page 13
______________________
*Alhamdulillah mun dawo daga ɗan gajeren hutun da muka tafi na kawo maku Cigaban wannan littafi Mai taken rainon soja...ina fatan Ubangiji Allah ya bani ikon kammalawa cikin aminci kaman yanda muka fara. Don Allah kar ki karanta ki fitar mun , haka duk wacce ta karanta bata biyani haƙƙina ba ban yafe ba😭...ga masu buƙatar payment regular group ₦500...Vip group ₦1000... Special payment ₦1500 via 7782217014 Mohammed Hassana FCMB shaidar biya ta wannan number 08081202932 ko katin MTN ta Wannan number na sama ƴan Niger katin Artel 500f.*
________________________
Ware dara-daran idanun ta Ma'eesha tayi tana zuba su bisa Kyaƙyƙyawar fuskar shi Wanda har a lokacin Lulun idanun sa basu ɗauke daga Kallon ta ba. A hankali Zuciyar ta tafara mata magana da cewa “Shine fa ya dawo”. Ma'eesha..! Ya kuma kiranta a wannan karon har ta fuskar sa ya sauya yana shirin rufe ta da wannan faɗar nasa da take bala'in tsoro. Saurin muskutawa tayi tana juyi tare da Faɗi ƙasss timmmm daga Gadon. Saurin miƙewa Ma'eesha tayi tana Furta “ Uncle a'aaa Kai kaine?”. Ɗan janye idanun sa yayi daga kallon ta kana yace “ maza ɗauro alwala ki taho morning exercise ”. Shiru tayi tana kallon sa idanun ta na ciko da ƙwallah kaman zata sa kuka , Kawai sai kuma ta juya tana nufar wurin Waldrop ɗin ta , hannun ta tasa tana buɗewa a hankali tare da fiddo da Towel, kawai sai hawaye rau-rau suka fara zubo mata. Jan shashsheƙa tayi wannan yasa shi fahimtar kuka take yi. Ɗaure fuska yayi tamau kamin cike da Muryar sa wanda ita kaɗai yake yi mawa magana a hankali cike da taushi da shi ... kukan me kike yi? .
Da Sauri Ma'eesha ta juyo tana kallon sa tare da saurin goge hawayen nata tana Girgiza kai tare da cewa “ A'a Uncle ba kuka nake yi ba. Mura ce take damuna shine idona ke hawaye.
Kallon ta yayi yana ɗan sauke idanun sa , don tarrr yake kallon ta kuma ya fahimci dalilin kukan nata. Kallon sa tayi shima yana kallon ta ba tare da yace mata komai ba a fuskar sa ta fahimci mai yake nufi . Wannan yasa ta a hankali kai hannun ta tana cire ƙaramar Wandon kayan barcin nata tare da ƙoƙarin cire rigar jikin ta . Keeee!!!
Muryar sa ya katse ta cike da tsaawa wanda sai da Hantar cikin ta ya kaɗa . Sam bata san lokacin da ta saki rigar barcin nata ba jikin ta na ɗaukar kyarma kawai sai ta fashe masa da kuka tana ɓarin jiki don ko ina nata rawa yake kar-kar-kar .
Miƙewa taga yayi Daga inda yake yana takowa ixuwa inda take. Baya Ma'eesha ta fara yi cike da tsoro tana fara kiran sunan Mami....a gabanta ta gan shi nan take tsoron ya ƙara kamata hawaye na sauko mata babu ƙakƙautawa . Wayyo Ya Khalil Uncle zai duke Ni.....Ya khalil kazo! Idanun Haidar ne suka kaɗa suka yi jahhh a lokaci guda kiran sunan Khalil da tayi shi ne yafi ɓata masa rai . Bama cire kayan da take ƙoƙarin yi a gaban sa bata jin tayi wani Abu . A hankali Zuciyar sa na raya masa cewa “ A gaban Khalil ma haka take cire kayan ,duk ya gama ganin jikin ta , shiyasa yake damuwa da ita ashe yana kallon na bulus ne. Wannan sakacin waye ? Nawa ne ? Ko na Mami da har bata san darajar jikin ta ba?”. Zuciyar sa ce ta basa amsa da cewa “ is your fault, sakacin naka ne. Muryar ta ya kuma ji tana furta “Don Allah Uncle ka tafi yanzu zan fito naje wurin Ya Khalil muyi exercise ɗin tare.....Yi mun shiru ko yanzu na ƙarairaya Miki ƙafa ɗaya kuma a haka kiyi mun exercise ba tare da an ɗauraki ba...Waro 🙀 ido Ma'eesha tayi tana kama kan ta na nashiga uku, tana taɓe baki cike da shagwaɓan nan nata tana ƙoƙarin fashe masa da kuka ya ƙara matsawa jikin ta ....wannan yasa ta yin shiru don yanda ya gwamitseta har shi kan sa yana jiyo bugun numfashin ta.
Wani irin gumi taga yana tsartsafo ma saman Goshin sa...Uncle sorry kayi hakuri zan rinƙa tashi da wuri daga yau ba zaka sake zuwa ka ga ina barci.....Rufe mun baki🤐Gumm ta kame bakin ta . Tana raba idanu tare da cigaba da tsiyayar hawaye.
A haka kike cire kaya a gaban kowa saboda rashin hankali? A gaban Khalil ma cire kayan jikin ki kikeyi kenan? Haka ne? Yayi maganan yana watsa mata dulu-dulun idanun sa. Saurin gyaɗa masa kai tayi alamun eh . Don ita sam rainon nasa ne bata san ya ake ƙarya ba bare tayi masa .
Wani irin sarawa kan sa yayi da ƙarfi .... Zuciyar sa na masa zafi , ji yake kaman yaje ga Khalil a halin yanzu. Cike da wauta tana shashaƙa ta furta “ Kayi haƙuri ban san babu kyau Na cire kaya a gaban mutane ba Uncle amma ba zan ƙara ba ....Kuma cire kayan kawai nake yi bai taɓa mun wanka irin yanda mami tace a da kaine kake mun wanka har kwalliya... Yanzu me yayi saura ? Ko zaki je ne shima yayi Miki? Mara Wayo wuce ki bani wuri . Saurin sunkuyawa tayi tana Ɗaukar Towel ɗin tare da nufar Toilet.
Ma'eesha!
Muryar sa ya katse ta inda cikin sauri ta tsaya cak tare da juyowa tana kallon shi . Cikin wani irin murya tamkar bana shi ba taji ya furta “ Khalil yaga jikin ki komai da komai?”. A'a ta furta tare da Girgiza kai tana saurin cewa“Uncle sai kuma tayi shiru tana kasa masa maganar ganin yanda fuskar sa ya haɗe kaman hadari ”.
Ina sauraren ki ,tun da baiga jikin ki ba ya kike yi a gaban sa ?.
Kallon shi tayi tana Ɗaura Towel ɗin daga saman ƙirjin ta wanda ya sauko mata har cinya. Kana ta janye rigar barcin nata a hankali wanda ɗaura Towel ɗin bisa kan sa . Kallon shi tayi tana murmushi tare da cewa “ Uncle ka gani ko? Ai kaima baka ga jiki na ba ko Uncle?”. Dan sassauta fuskar sa yayi don tabbas indai haka take yi to jikin ta babu mai ganin shi sai dai ƙafafu. Kallon yan lukutayen cinyoyin ta yayi zuwa ƙasa . Kana yace “ Kin tabbata haka kike yi ,ƙarya fa babu kyau faɗa mun gaskiya ba zan Miki komai ba Ma'eesha ”. Wangale masa baki tayi cire da gasgatawa tace “ Da gaske ne Uncle ƙaima da ka tsaya haka zaka ga nayi”. Murmushi taga yayi yana faɗin “Good girl , Ashe Ma'eesha na ta fara hankali tasaan yanda ake sitirtaa jiki. Wani sabon Annuri ne ya bayyana a Fuskar ta don jin daɗin yabon da yayi mata. Gyaɗa masa kai tayi tana cewa “ Ai yanzu na girma ne Uncle ” .
Wani irin dariya taga ya shaƙe dashi wanda tun da ta fara girma ta taso Bata taɓa ganin irin wannan dariyar nasa ba. Oya yi sauri ki fito ina jiran ki Back yard. Okay uncle. Ta furta tare da saurin shigewa Privacy.
**
Mami ne ke kai kawo tsakanin kitchen da Dinning area. Sanye take cikin shigar wata doguwar riga irin na english wears ɗin nan masu ƙaramar hannu. Gani nayi Shakaru sun ja ta ƙara ƙima dama kun san yanda take. A wannan karon idanun ta cikin medical Glass ne na ƙarin ƙarfin ido . Wannan gayun nata har yau yana nan . Don gashin kan ta yasha gyara an zubo shi baya , daga sama kuma ta sanya wata hula mai kyau na mata na zamani. Ƙafarta cikin room slippers tana kai hannun ta tare da cewa“ Ba zan soya mawa ma'eesha ƙwai yanzu ba ,saboda ba zata tashi ba nasan sai 9:00am.
Motsin fitowa falon yasa ta juyawa tana kallon ƙofar Bedroom ɗin Ma'eesha da take tahowa tare da kallon Mami. Rungume Mami Ma'eesha tayi tare da cewa“Mami ina ƙwana ?”. Kasa amsa ta tayi don mamakin sunyi da ita yau ba zata fito da wuri ba , sai kuma gata da kayan exercise riga da Wando mai yalwa irin masu kaman Jessy ,ƙafarta cikin kambass na mata baƙi irin manyan nan. Fuskar ta ta shafa tana