Showing 60001 words to 63000 words out of 94661 words

Chapter 21 - RAINON SOJA COMPLETE Hausa Novel

Unknown   

05 Oct 2024

45171

layin su ,kana Wata Hajiya ta fito tana takowa tare da buɗe Murfin moton na biyu , inda Ni a kallon farko na ɗauka itace ma aka yi ma rakiyar zuwa gidan General Saleh yelwa . Cike da mulki ta sako ƙafarta ɗaya inda naga Wasu irin awarwaro da rings na gold suna walwali tare da kare hasken ranan wurin . Ƙafar nan nata fari tarrrrr gashi luƙwi dashi wannan zai shaida maka mai ƙafar macece babba kuma mai jikin mata wato mai ƙiba . Jakarta Ta miƙo kana ta fito gaba ɗayan ta . Ohhhh mashaallh shine Abin da na iya furtawa . Yar gayu gayu gayu ce ta ƙarshe . Fuskar nan nata yasha make Up na zamani wanda a shekarun ta baka ce zata yi shi ba . Ta ƙayatu kuma sannan ta haɗu Ainun maƙura . Sanye take cikin wata jallabiya ta mata wanda tsadarta ta haura 100k maroon Color . Doguwar mace ce mai jiki ga tsaho sai ta dirkake tayi dai dai . Ɗan motsa laɓɓanta tayi wanda yake sheƙi kana ta furta “ Bushira riƙa mun Wannan jakar , ta ƙare maganan tare da ɗan datsar laɓɓanta na ƙasa Wanda yayi sanadin motsawar 2 dimples ɗin ta yana loɓawa na gyefe da Gyefen fuska . Tom Ranki ya daɗe Hajajju , Bushira ta furta tana Amsan jakar da tsadarta ya haura 150k haɗe da takalmin ta mai ɗan tudu daga ƙasa . Hannun tasa tana gyara Hular jallabiyar tare da gyara zubuwar gashin kan ta , wanda da fari na ɗauka Attachment ne , sai daga bisani na fahimta gashin ta ne yasha wannan ɗan bara'uban gyaran har gadon baya . Ko mayafi babu gandasdas ta fara takawa tana shiga ixuwa cikin gidan Saleh Yelwa, tana bin ko ina da kallo . Yayin da Bushira ke take mata baya , sauran makarkaban nata suna tsayawa daga Waje . Gilashin idanun ta shi kan shi tsadar shi irin wanda ake yi da ruwan gold ne wanda a kuɗin mu ta Nigeria zai kai 800k . mai haske ne , amma anyi shi da faɗi wanda ya tsaya ya kara mata kyau da cikar hajittaka ta manya .

Bushira zan iya bin stairs kuwa ? Babu lifta ne a gidan ? . Muryar ta mai kama da na shuwa ya katse Ni . afuwan Hajiya aƙwai tuba nake ko zamu bi tacan .

No..
No! Na ɗan miƙa ƙafa ai . Ta furta tana ƙare shigewa tare da hayewa matattakalan .

Mami!! Mami come out and see something surprise 🫶🏻💃🏻 “ Jidder ta furta da gudun ta tana saukowa daga stairs ɗin falon tana takowa inda Hajiya Hajara ke washe mata baki tana furta “ Come on my baby , give a warm hug 🤗 ”. Da gudu Jidder ta faɗa jikin ta tare da cewa “ I'm happy to see you mom , I'm so much happy ma'am . Murmushi Hajiya Hajara tayi tana Rungume Jidder kana tace “ Yeah my babe happy to see too . Kin ganki yanda kika ƙara ƙyau ? .

Murmushi Jidder tayi tana gyaɗa kai tare da cewa “ Yessss Mom I'm always prettie , Sannan Mami kinyi kyau sosai Kema , duka ɗakin Hajiya Kaka babu mai ƙyaunki me yasa? Ko Alhaji tsoho kika biyo sune yar larabawan mali ....... Murmushi Hajiya Hajara tayi tana buɗe baki zata yi Magana kenan idanun ta suka sauka akan babban hoton family na dake maƙale a bangon falon...dukan su cikin Farin ciki suke a wannan sa'ilin sai dai nata Farin cikin da harkar yafi na kowa . That's how she is ....Which girl is that? Wacece wannan na ganta a family photo naku ? Mamin ta ƙara haihuwa ne ban sani ba.....................?



Don girman Allah kar ki karanta indai baki biyani ba , haka kuma kema kar ki fitar mun da Littaffi🙏🏻ga masu buƙatar payment regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 only WhatsApp . Idan kuma Vtu transfer ne send it via 090614666409 only call thanks love 🫶🏻 .

Next chapter 35 is on the way✍🏻💃🏻 .#mrs usm...#Antymmnteddy.
[1/21, 3:01 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *(Book 3 three)*
*Love and Amazing story*
*Written....✍🏻 Aysha Mamanteddy Mrs Usm*




_________________________

*RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*



*Littafin na kuɗi ne please ban yarda wata ta karanta mun ba tare da Ta biyani ba , regular group ₦500... Vip group ₦1000... SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#🙌🏻😄 .*




35~36
_________________________

Ɗan Gimtse fuska Jidder tayi tana caɓe baki tare da ƙoƙarin magana dai dai Mami na saukowa cikin shigar ta na kamala complete house wife. Yanzu fa Mami abu yayi sauƙi wannan shigar turawan an daina shi ba kullum ba . Sai dai har yanzu yanda take takonta kasan macece mai kamar maza Wato police ”. Wani irin ƙayataccen murmushi ta saki tana ɗan karkacewa tare da kallon Hoton da suke kallo har da jidder wacce tayi tamkar yau ta fara ganin Ma'eesha a Duniya . That's my baby girl da nake baki labari Ma'eesha ta kenan! Mami ta furta tana faɗaɗa fara'ar ta . Caɓe baki Hajiya Hajara tayi tana kallon gyefen ta da shirin zama , don taji labarin Ma'eeshan tun kamin zuwan ta a bakin mutane da Dama . Sai dai kurum taji bata ra'ayin ta duba ga maganganun da jidder da faɗa mata akan yanda suke nuna soyayyar su ga yarinyar da basu san Asalin ta ba . Ganin tana shirin zama ne yasa Mami saurin dakatar da ita da cewa “ A'a Hajara anan kuma ? Mu shiga daga ciki ” . Hummmm ta numfasa tana kallon Bushira kana tace “ Ki jira mu ”. Tom Ranki ya daɗe ....Bushira ta furta tana yin ƙasss da kanta . Bin bayan Mami su duka suka yi Hajiya Hajara da jidder dake ta jin dadin Yanda Mom Hajara ta nuna akan Ma'eesha a Zuciyar ta tana cewa “ Ai ma Wani Abu sai Ya Haidar ya dawo dake zaki ci ubanki ne”.

Falon Mami na sama suka shiga inda suka yi ma kan su masauki , Gaba Ɗaya Hajiya Hajara ta sauya fuskar ta babu Annuri don da magana fal a Zuciyar ta gami da Wannan baƙuwar fuskar da ta gani a cikin a halin General Saleh Yelwa . Tum-tum mat ta zauna inda Itama mami ta zauna gaban su shaƙe da kayan motsa baki . Ita kam jidder Resting chair ɗin dake daga gyefe kaɗan ta nema ta zauna , tana zaman jiran mene zai fito daga bakin Hajiya Hajara. Don kaf dangi anyi ittifaƙi da Rashin kirkinta musamman idan Abu bai mata ba .

Dan Tsawa Mami tayi tana Binta da kallo , don ganin yanda ta lula Duniyar tunani yasa ta tuno da maganan likita don ba'a daɗe da dawo da ita daga India ba akan lafiyar ƙwaƙwalwarta , don a shekarun baya Ta samu matsala na mantuwa, inda a yanzu ma Wasu Kaɗan ne daga cikin rayuwarta na baya ta iya tunawa dashi , shine Rayuwar ahalinta. Ta ɗebi shekaru a wani ƙauyen Fulani tana rayuwa da mutane masu amana , sai kuma rana ƙwatsaaam ta tuna da Ɓangare na Rayuwar ta da Iyalanta wannan ne sanadiyyar dawowan ta har aka yi nasaran ganin ta. Fatan su a yanzu shine kar ta tuna da Abubuwa da yawa da suka faru , wanda ya haddasa masu baƙin ciki a rayuwar ta mara iyaka . Har kuma iya yanzu suka tuno da Wannan mutumi babu Abin da suke bin sa dashi sai ALLAH ya isa!

Hummmm Jan numfashi Mami tayi kana tace “ Hajara tunanin me kike yi haka ? , Da Wani Abu ne ?” . Sauke lemun hannun ta tayi tana mai dashi saman plate ɗin dake gaban ta . Kana ta kalli Mami fuska babu walwala tace “ Ina Boy? Ya girma sosai ko? ”.


Yana tare da Ma'eesha ina zai tuna da ke Mom? Ai idan suna tare bai ganin kowa , har gwara shi da Khalil ma , don ko me zata yi ba'a mata faɗa ”. Muryar jidder ya katse su wacce take latsa wayar ta tana kwararo zance . Ya ishe Ni haka! Kuji mun mara kunya dake ake yi ne? . Mami ta katse Ta cike da Tsawa , Wannan yasa Jidder kallon ta tare da kama bakin ta .

Haba Mamin Haidar Meye na wannan faɗan haka ? Jidder ce kike ma wannan tsawan nawa duka take ? Ai wannan zaki firgita mata tunani ne , Aƙwai shekarun da idan yara basu kai ba wani Hayaniya duka bai kamata da ayi masu shi ba. Tsayawa Mami tayi tana kallon Mom Hajara don bata yi wani mamaki ba ,don tasan halin Hajara da son nata. Cike da San yi ta furta “ Ta dame Ni da Ma'eesha tun da nake ban taɓa ganin masifaffiya irin jidder ba. Wai ita wannan Ma'eesha wacece? Kai Anya??? .

Mom Hajara ta furta tana bin mami da Wani irin kallo . Yarinya ce mai kyau hankali da tarbiyya momy ga haƙuri ba irin Wancen mummunan mai ƙaton Goshi ba .

Saurin juyawa Duka suka yi suna kallon hanyar shigowa inda Khalil ke takowa cike da takon sa . Fuskar sa Sake yana kallon ɓangaren da Jidder take ya watsa mata Wani irin harara da sai da ta shiga taitayin ta. Kallon su duka tayi kawai sai ta miƙe tana saka kukan sarganci da Gata tare da cewa “ Mami nafi shekara goma a cikin wannan halin hantarar da suke yi mun , tun da Ma'eesha ta shigo Rayuwar mu nake fuskantar tsana.....Kawai sai ta rushe da kuka da gudu tana juyawa tare da barin falon . Kyaji dashi halin ki zaki gyara. Mami ta furta tana jan ɗan tsaki tare da tsuwa tana gyara zama .

Zama Khalil yayi a kujeran da jidder ta miƙe kana muryar Hajiya Hajara ya katse su tana cewa “ Gaskiya Nima naji na tsani wannan Yarinyar haba..........!


Don Allah kar ki karanta mun idan baki biyani ba . Ga masu buƙatar payment regular payment ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 mohammed Aisha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 tare da shaidar biya evidence of payment .idan Vtu transfer ne sai ki tura ta Wannan number 09061466409 .#Antymmnteddy.
[1/21, 8:12 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *(Book 3 three)*
*Love and Amazing story*
*Written....✍🏻 Aysha Mamanteddy Mrs Usm*




_________________________

*RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*



*Littafin na kuɗi ne please ban yarda wata ta karanta mun ba tare da Ta biyani ba , regular group ₦500... Vip group ₦1000... SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#🙌🏻😄 .*




37~38
_________________________


Gaba ɗaya kun fifita yarinya yar tsuntuwa ce fa? Meye kuke yi ne haka ? Gaskiya raina ya fara ɓaci yanzu zan tashi na bar cikin gidan nan , kuma dana san Wannan Zan taho na tadda da banzo ba . Hajiya Hajara ta furta tana miƙewa tare da Ɗaukar fankacecen Gilashin idon ta wanda ta Ajiye a gyefe . Sanin hali yafi sanin kama ,wannan yasa Mami saurin riƙo hannun ta , don ta san ta da zuciya irin na Haidar a yanda mami ke cewa ita ya ɗebo a saurin ƙufula da fushi . Habawa Hajara me yayi Zafi? Don Allah ki zauna . Yanzu ya gida ya kuma Hajiyar ta mu ?. Mami ta furta zancen cike da Sanyi da kuma rarrashi .

Ɗan jimmmm Hajiya Hajara tayi kana tace “ Kowa lafiya amma ba fa zaki gane kan gadona ba sai naji kin rarraso mun Jidder ta dawo mun cigaba da Hira ”.

Murmushi Mami tayi kana ta gyaɗa mata kai tana furta “ Shikenn Bara naje da kaina ma na rarraso Miki ita . Amma....Aaaaaammmm Khalil taho ka kira mun Boy yanzu tun da shi bai neme Ni ba . Hmmm. Wani guntun Numfashi Ya sauke , a hankali ya fara tuno da sihirtaccen ƙyawunta da Wannan murmushin nata . Gani suka yi ya saki Murmushi yana furta “ I miss You so much ”. 🤔To! Kai kuma da Wane? Matar da zaka Aura Maryam ko kuwa wacce kake magana? Mom Hajara ta katse shi tana bin sa da kallon rashin fahimta .

No mom , Ma'eesha nake nufi nayi kyawarta da Wannan murmushin nata.....mtswwwww! Mom Hajara ta ja dogon tsaki kana tace “ Anya Wannan yarinyar ba maƙiya ne ba suka jefo ta cikin gidan nan don wani mugun Abun?. Subhanallah! Mami ta furta tana ɓata rai ƙwarai wanda hakan yasa Hajiya Hajara miƙa masa waya tana cewa “ Kira mun shi yanzu ”.

Amsar Wayar yayi bai ce mata komai ba, don ransa sa ya fara sosuwa da maganan Mom Hajara ɗin . Gani tayi ya fara kiran Wayar Haidar ta Wayar sa , duk da yasan ba wani jituwa ke tsakanin su ba . Wata ƙil ya ɗaga ko kuma akasin haka ”.

**
Ɓangaren Aliyu kuwa yana Tsaye yana kange da Waya a kunnen sa suna Magana da Aminin nasa Areef wanda yake ta cewa “ Ina jinka, tun tuni kana ta Wani kame kame da fa magana a bakin ka amma kana mun shiru ya dai? . Ƙwanciya Areef yayi yana ɗan sosa ƙyayarsa don bai san ta ina zai fara masa bayanin lamarin ba . Mtswwwww! Dogon tsaki Ali yaja cike da fushi don bai san shiru Gashi dai ɓakin Miskili amma shi sam bai san ayi masa shiru wannan yasa shi cewa “ Zan kashe waya na fa”. I'm sorry Ali kana jina? . A'a ban jinka ”. Ya basa amsa dai dai yana kallon shigowar kiran Khalil amma ya watsar bai bi takai ba. Hummm Babban yayan mu kenan! Areeef ya furta yana wata yar dariya wanda Aliyu kai tsaye yace “ Kaje maganan ka Yallaɓai ”.

Hummmm Aliyu Ni kuwa nace kunyi ma Ma'eesha miji ne?🤔🤣ƙitttttt! Yaji Aliyu ya katse kiran , wanda shi kan sa bai san dalilin da yasa shi yin hakan ba . Bai tsaya kuma jin ƙarikon mai zaice ba ,don tuni ya fahimci inda ya dosa a kalmar sa guda ”. Tsayawa yayi yana cizan laɓɓansa na ƙasa tare da dunkule hannun sa Zuciyar sa na masa zafi da Huci. Me yasa sai Ma'eesha? Ya furta cikin Tsawa yana saurin juyawa tare da nufar Bedroom ɗin sa inda ya barta tana shan Cofee don shi titir a shan Cofee yake . Hummmmm! Da ƙarfi taji saukar Ajiyar zuciyar sa kana cikin sauri ta juyo tana kallon sa .


Mamaki ne ya kamata ganin yanda gumi ke karyo masa Wannan yasa ta miƙewa daga tsaye , amma sai da hannu cike da Wannan isan nasa ya dakatar da ita yana mata Alama da ta zauna . Babu musu ta ja ta zauna , Amma Bata daina kallon sa ba , haka bakinta ya kasa shiru wurin furta “ Uncle motsa jini kayi naga Gumi ne a fuskar ka da jikin ka?”. Girgiza mata kai yayi kamin a ɗan daƙile yace “ No”. To wannan gumin fa? . Cike da Arrogant voice ɗin shi ya furta “ I hate Norse ”. Gummmm tayi da bakin ta tana komawa tare da shan Cofee ɗin tana kallon sa a sace a sace . Keeeee!!! Kin ma iya Cofee? . Ya furta cike da neman ta da laifi don ya fanshe Haushin shi ya bata Wahalar don yau ji yake tamkar ya bugi banza! A ganin sa itace take sakar masu fuska har su samu damar tunanin son ta .


Kin iya Cofee?? Ya kara Tambayar ta fuska Gimtse babu fara'a . Dan kallon sa tayi tana lumshe lumsassun idanun ta kamin ta girgiza masa kai tana cewa “ Aa ban iya ba , Mami ke yi sai kuma yanzu kai da kayi mun . You Are very stupid , kina nufin Common thing Cofee baki iya ba???..........Good night lavs🫶🏻🤣🤣😻 yau dai Ma'eesha taga banu a hannun Aliyu , Allah ya ƙwaceta don yau da wuya bata daku ba . Mu tara a next page 39~40 .

*Don girman Allah kar ki karanta indai baki biyani ba . Ga Masu buƙatar payment regular group ₦500 Vip group ₦1000 SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932 Vtu transfer Kuma ta wannan number 09061466409*
[1/22, 1:36 PM] Anty Aisha Mmn Teddy Marubuciya: *(Book 3 three)*
*Love and Amazing story*
*Written....✍🏻 Aysha Mamanteddy Mrs Usm*




_________________________

*RAINON SOJA*
*Through the gate of love a valiant fearless heroical and Sympathetic Story*



*Littafin na kuɗi ne please ban yarda wata ta karanta mun ba tare da Ta biyani ba , regular group ₦500... Vip group ₦1000... SPC payment ₦1500 via 6037312299 Mohammed A'isha keystone bank ko katin MTN ta Wannan number 08081202932#🙌🏻😄 .*



39~40
_________________________

Yayi zancen yana wani irin haɗe giran sama da ƙasa . Kallon ta ya kuma yi a karo na biyu ganin yanda jikin ta ke tsuma da kyarma yasa shi cike da Miskilalliyar Murya wanda ba don tana gab dashi ba sam ba zata ji mene yake furtawa ba. “Cofeee??? Ya nanata cike da Muryar damuwa, kana yace “ Maza zauna ki haɗa mun Wani yanzu ”. A hankali ta zauna tana fara jan flask ɗin ruwan zafi kamin ta fara ɗaukar Cofee cup tana kallon sa a ido ido . Gimtse fuska yayi yana hura hanci tare da tattare gida . Wayyo Mami Daddy Uncle yau duka ne yake son yi .

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login