Showing 12001 words to 15000 words out of 65883 words

Chapter 5 - AUREN USTAZ

22 Oct 2024

14151

abokanshi basu ankaraba sai zaman jira ake.

Haka yakaita har dakinta yafita ya rufe gidan gam ya kashe wayarshi yadawo ciki ya zauna yana murmushi yace dama wannan taron duk gulmace da bidi'a.


Aysha tace wai mikake nufi? kana nufin bazaka bu??e k'awayena da yan uwana su shigoba?

Ustaz yace eh gaskiya kiyi hakuri matata baza aman bidi'ar nan ba agida ke nikeso kadai ingani akusa dani.

Rai bace ta yaye lifayar jikinta sosai surar jikinta ya bayyana lace ne mai kyau ajikinta pink color dinki riga da siket sunkamata tsam, kasancewarta mai jikin kiba madai-daiciya ko ina nata acike Masha Allah tace to wallahi baka isaba wato dan kasameni yau shine zaka nunaan baka bukatar yan uwana ko?

Yau nefa kawai saikace bazaka bude ba.

Ustaz ya zubamata jajayen idanuwanshi yace eh gaskiya bazan bude ba saboda duk bidi'a ce wannan taron azo azigeki kiki yimin biyayya..

Aysha idonta ya kawo kwallah tace Dan Allah Honey.

Ustaz yayi dariya yatashi yasaki labule dakin yayi duhu sosao yace abunda yasanya kikaga nasaki labulan nan ina matukar jin kunyar fadamaki magana ido da ido.

Yakarasa wajenta tare da tallabota, akunne ya radamata miji na bukatar kasancewa da matarshi halaliyarshi....A??]
{
1/13/22, 09:55 - Buhainat: ??c??c??c??c??c??c??c??c
MATAR USTAZ
??c??c??c??c??c??c??c??c
NA UMMY AYSHA
??T???1??_/Q9??_/Q&2??_/Q0??_/Q

""" AYSHA ta zaro ido tare da tureshi ta'ce" karka soma, karma ka fara Wallahi,an'fad'ama ni Jakace da zaka Hayayyak'eman yanzu da rana, harda wani sakin labule, to Wallahi maza ka bu??e get ga yacen ana bugawa ayimin hidima kamar yanda akewa kowace mace.

Ido a limshe USTAZ ke binta da kallo, dan shi harga Allah baida bukatar wannan Bidi'a matarshi kawai ya keso, in'kuma taro a'keso a'mai a'bari sai ta Haihu kawai.

Aysha ta'ce"magana fa nike ma.

USTAZ ya'ce" ba matsala".

Aysha ta'ce" kamar ya ba matsala?

USTAZ ya'ce" ba cewa ki kai a'barsu su gaji su koma ba?

Bakin CIKI ya sa AYSHA fin'cike jikinta ta fad'a kan Gado ta fashe da kuka, wato tin yau dan ya sameta zai gwadamata baya da bukatar kowa nata kenan ko, ba komi Rayuwa ce.

Sosai a'ke buga gidan kamar za a'b'allashi Amma USTAZ yayi banza da su, saima shiga yayi toilet yayi wanka ya sanyo jallabiya ya fito, ya'ce" tashi kiyi Sallah zanje masallaci in dawo.

Aysha ta sha reshi! Amma a'ranta murna take ai dole in yaje fita su shigo, tana ganin ya fito farin ciki ya kamata harda lallabawa ta koma wajen window tana lekenshi, zuciyarta ce ta kusa bugawa ganin USTAZ da dogon tsani yayi wani D'an korid'o na gidan ya tattaka ya haye katangar, yayi zamanshi da ram cike da kuzari ya sake sab'ar Tsanin ya mayar dashi ta waje ya hau ya dire, tare da kwantar da Tsanin yayi Masallacin.

Kuka Aysha tasa kamar zata shid'e cikin karaji ta'ce" shikenan na Auri bala'i, mai kulle Malam, ya aylah kabani juriya da huakuri, wayyo Allah Musty iyayen ka sun cucemu da yanzu muna nan a inuwa d'aya cike da farin ciki, tasha kuka sosai kana ta Hakura ta tashi ta warware kayan jikinta ta fad'a toilet tayi wanka, ta:sanya riga marar nawie tayi Sallah hade da Azkhar, tana gamawa ta fara tinanin Rayuwa, jin ana isha tayi abunta tare da fesa tirare ta lallaba ta haye gado dan kanta ke masifar ciwo, kwanciyar ta keda wuya bacci yayi gaba da ita.

Ustaz Sai da ya gama Sallah ya gan-gara bakin titi ya hau machine yayo masu sayayya kaji da sauran kayan makulashe, yana dawowa aka saukeshi nesa da gidan shi ya duba yaga ba kowa kana ya aza Tsanin shi ya hau, ya kuma d'auka tsanin ya jefa ta ciki kana yabi akai ya sauka, ya k'arasa wajen get din gidan ya dinga jin hayaniya ta yam mata kala-kala ,A'ranshi ya'ce" ga yanan mu munyi ibadar mu sukam suna nan suna jira, inama am'fani shiyasa kullum zamuyi Addu'a sai mun Bude da Allah ya tsaremu da Biddi'a kullu yaumu,Dan Bidi'a Wuta ce zallah,yayi tsaki ya shige d'akin tare da Rufewa .
Bayan ya gama komi ya k'arasa wajen Aisha da ganan naja kofar na fito.

Da Asuba USTAZ rungume da Aisha kanshi a'kasa yana bata Hakuri da lallashi, batace mai komi ba sai kasa datai da kanta itama tana jin nawin shi kwatan kwacin yanda yake jin nata, cikin kuka ta'c"e ko kabari sai an'gama taro.?

Ustaz ya'ce kiyi Hakuri zamuyi walimar Sunna ne, kuma am'fison ka Tara da iyalinka ina fatan kin fahimceni..?

Bayan watanni goma Aysha ta sumbulo Yaron ta mai suna Usman,(sunan Maifinta kenan)yaron tamkar balarabe saboda kyau, ya had'a da kyan USTAZ dana Aysha, bayan sungama wanka USTAZ yayi sabon Aboki mai Shari'a, ya share Mujaheed saboda yacika matsamai akan ga abunda ya dace.


WAYE MAI SHARI'A.


MAI SHARI'A mutum ne da bayason yaga wani ya fishi, a'cikin kasuwa ko kad'an, ada bayason USTAZ kwata-kwata ganin yanda yake da customers bakamar shiba, ga USTAZ attajirine na mutunci,dan kaf yan gidan su ba wanda ya kaishi Arziki, Mai Shari'a ya fara shishigemai saida yaga yasamu k'arbuwa kana ya fara jefomai ma'anonishin,ganin USTAZ duk abunda ya fadamai yake d'auka ya samu damar nunama USTAZ duk sadda Namiji ya kasance yana sakar ma iyalinshi ku??i tana facaka to Mace akwaita da wayo, zataita ta rasu taje tagi na wata babba masana'anta ta yanda zakaga in kace tayi ba zataji nawi tace batayi b,a saboda ba abun Hannunka take jiraba, tana da nata na kanta.

Sosai maganarshi ta samu muhalli a'zuciyar USTAZ dan bayan auransu ba laifi duk abunda Aysha ke so yana mata.

Mai shari'a ya'cema "USTAZ ka ganni nan ba abunda bandashi na kayan ABINCI a'gidana, shiyasa ko biyar bana bama Hajara, na yarda duk abunda ta keso taman waya zan kawomata ko biki zata na kashe mata biki, saboda haramun ne, duk abunda nai niyya zan'bata ada takai daga baya na fahimci in'kaba da D'ari biyar fatan wanda kaba yamaido maka Dubu, kaga akwai bidi'a anan ko ba haka ba?

Ustaz yace kwarai ko A'bokina Wallahi inajin dadin zama dakai sosai saboda ina k'aruwa.

Mai Shari'a yayi Murmushin samun nasara ya'ce" to Wallahi Hajara ko waya ban barta da itaba mai kyau, saboda ba damar in'koma gidana in fiddo waya ina chart da customer d'ina da suke siye ko nike siye, sai gaka tana ??aukar ta-ta itama tana abunda ta keso tana huraman hanci, kaga kenan biyayyar da a'kace sumana a'matsayinmu na tsama dasu bazasuyi ba ko?..

Ustaz yace wannan gaskiyane Wallahi, kuma ni kaina haka Aysha keman, duk abunda nayi sai tayi maka mancin shi, in rasa wake tire ta.

Mai shari'a ya'ce" yawwa Aboki ka gane kenan, to ba kowa ke tire suba sai wannan K'awayen nasu da kuma makwabtansu dake shigar marece, daka fito a'fada ana baje sirrin ka sai kafito ai'tamaka daukar wawa .

USTAZ yace A'uzubillahi wai dama haka matan suke? ka son ni ba ruwa na da wannan binciken, kuma bana shiga shirgin su.

Mai shari'a ya'ce" ai sun mafi haka, in'kanason samun kan matarka kai ka??ai to ka rabata da kowa sai wanda ya dace, kar'ka bayar da k'ofar da za a'dinga shiga gidanka koda yaushe tinda dai ba a'bariki bane.

Sosai USTAZ yai na am da shawarar Mai Shari'a yamai godiya ya tashi.

Wanann Hudubobin su suka zauna daram a'zuciyar USTAZ, dama tin farko sai a'hankali dan Aysha nada Hakuri ne shiyasa baka ganewa, USTAZ yazo gida ya fara tsiro da abubuwa masu wuyar sha'ani ,tin Aysha na daurewa har ta fara mayar da martani tana nunamai gajiyawar ta, ga fita baya bari sai yaga dama, ya k'arbi wayarta ya bata wata lalata ta,tayi Hakuri ta shareshi ya rabata da kowa nata sai matan A'bokai, ba k'aramin damuwa Aysha ke ciki ba ko fara'a USTAZ bata gani sai bukatarshi ya tashi, a'haka har ta haifi Sadeeq ganin halin k'uncin da take ya sanya ta fara kula wata sst Maryam makwabciyar su, a'sace suke k'awance har Maryam ta son wani a'bun nata, daga nan Aysha ta bukaci ta naso tamata Allura planing dan ta dan huta, dan bata bukatar haihuwa a'yanzu, itama Maryam ta goyi da bayanta ta mata, a'haka rayuwar taita juyawa USTAZ yazama wawan karfi da yaji ko abu Aysha tamai sai ya fad'ama mai Shari'a, daga karshe Mai Shari'a ya fara jan USTAZ gidan Yayar shi da niyyar sunzo gaishe ta, tin USTAZ baya sakewa har ya fara daga baya yaizo ya kecema Mai Shari'a Aysha ta fara gudunshi A'shimfid'a, ba damar ya neme ta sai fushi da zuciya. MAI SHARI'A ya'ce" shawarar da zan baka ka k'ara aure kawai, kason mace in'tana ita kadai ba k'aramin iskanci take ma mutum ba, gani ma suke su Hakuri suke damu Wallahi, ni kaina na fad'ama nakusa AURAN nan nan da wata biyu in huta.

USTAZ yayi shuru yace Anya Aure mafitane kuwa.?

Mai shari'a yace yo ai dan cika Sunna, muna fama da geme kamar na Masara amma ace matan mu d'aya ai'kaga ba girma.

Nan nefa Mai Shari'a yay ta tusama USTAZ son Aure daga baya yabashi shawarar nai man khadija yar Aunty Mai Shari'a, amma da sharad'in sai ta k'arasa shekarata ta karshe da baifi watan niba.

Dad'i sosai ya kama USTAZ zai auri Yarinya da tafi Aysha biyayya, daga nan ne duk abunda ya shafi mai Shari'a sai USTAZ ya rike wuta Aysha taje, ita duk batason mike faruwa ba, taje gidan Aunty mai shari'a bila adadin dan ko ciwon kai tai sai USTAZ yace taje ta gano Aunty Abokin shi batada lafiya, haka zata kwasa kafa taje ta dawo ko mafalkin da USTAZ yayi na Auran shi da khadija ne, shiyasa ya tashi cikin farin ciki wannan kenan.

Da safe USTAZ yayi wankan shi yayi kyau matuka, dan ko bakomi Aysha tayi K'ok'ari ta nan taraba shi da duk wata jallabiya inba sawar dare ba, yafito zai tafi kasuwa fuskarshi a'daure Aysha tace ya maganar fitar da zanyi jiya banje ba?..

Ya mikomata D'ari biyar ya ficce, har ya kai k'ofa yace gidan mai shari'a zaki kiyi kamar awa biyu, sannan kije cen inda zaki ko ina kiyi minti goma kidawo kinji na fadamaki, kuma zan'biya wajen Abdur-rahman din inji miyasa ya baki wayar ,yasa kai yakama gabanshi.
Yana fita Aunty Maryam ta fado tace nasamu Abdul din, kuma na fad'amai yanda mukai," yace ba matsala". Aysha ta mata godiya Aunty Maryam tace bari in tafi na fad'ama mai gida na zai mai magana an'jima har kasuwa zai iskeshi.
Da sauri Aysha tace ba matsala nagode da k'ok'ari.
Aunty Maryam tace bakomi ta fita.

USTAZ na fita yayi tsinke gidan su Aysha, ko Umma bai karasa ya gaida ba yatsaya A,
D'akin su Abdul ya tambayeshi "fuska a'daure Abdul yace eh ni na bata, saboda baka barinta zuwa kuma mahaifiyarmu na kewarta, shiyasan ya na kaimata tawa kamin in saimata sabuwa...

Kan USTAZ a'kasa yace to mafi Mishkila ya tada motarshi yayi gaba. .
Abdul ya'ce" na tsaneka wallahi amma nakusa kwatarma kanwata yanci Wallahi, bari dai ayi auran nan kagani da wani banzan gemanka kamar gashin ??iyar baby...

Bayan sati biyu Aysha kwance tana mura kanta yayi zafi matuka dan mura na bata wahala sosai, USTAZ ya fado gidan yayi tsaye kanta tare da cewa Dan Allah tashi kije gidan Aunty Mai shari'a ki gano ta, ulcer ta ta tashi, kuma kimata murna d'iyarta ta kammala makaranta.

AYSHA ta dago jajayen idanuwanta ta'ce" Wallahi USTAZ bazan iyaba kaina naman ciwo sosai, kason mura nike ka zoman ma da maganin kuwa?.

Rai a'bace ya da kamata tsawa tare da cewa wallahi sai kinje, ni zaki maida mutumin banza mutumin wofi, in masu magana zakije kana kiceman bazaki ba, tashi Dan Allah Malama, da daddare zan dawo miki dashi...

Aysha ta tashi tana kallonahi ta'ce" wai minaima ka kwana biyu duk ka canza, komi zanyi sai kwatsa da hantara..

Ustaz ya'ce halin banzarkine dakika koya shike had'ani dake, kin cika k'orafi ga rainuwa dan Allah kitashi nace...

Aysha batace komiba sai tashi da tayi ta d'auki dogon hijjob inta ta sanya, tare da safa tace bazan iya sanya nikaf ba saboda numfashina saita baki nike.

Ustaz yace naji ta shi ki tafi..

Haka ta tashi tana hada hanya ta fita, tayi tafiya mai dan tsayi kana ta iso dan gaban makaranta su Usman ne, da tazo ta dade tana buga kofar kana aka bud'e, wata budurwace doguwa fara ta bude suka zubama juna ido, hakanan Aysha taji gabanta ya fadi suka gaisa ta wuce ciki wajen Aunty, suka gaisa kamar kullum suna fira sama-sama budurwan nan tazo ta kwanta, tare da lumshe ido ,Aysha ta cema Aunty ina khadija yan makaranta.?
Aunty tai murmushi tare da nuna budurwar ta'ce gata anan ..

Ido Aysha ta zaro tace kai masha Allah She budurwace, nifa nasanya yarin yace lallai Aunty kunga jiya kunga yau.

Aunty tai murmushi ta'ce" aiko da dama mutane cewa suke waini na haifeta .

Aysha tace dan baki da jikin k'iba shiyasa.

Aunty ta'ce" hakane Aysha dama inaso in maki wata magana inba damuwa naga kamar bakisani ba .

Sosai gaban aysha ya Fadi tace miyafaru Aunty?.. Aunty tace to ba komi bane ba dama mijinki ne zai Auri khadija, tin tana gab dashiga ss3 yakawo kudin auran shi, da goro akasa rana yanzu dai bikin sati ukku ya rage dan Allah kiyi hakuri ku zauna lafiya..A??]
{

Naira dari ukku ne duk mai so na zafce dari duba da yanayin da ake ciki mai so yabada 200 ya kirayi wannan number.

07038423451

Last free page
1/13/22, 09:55 - Buhainat: ??c??c??c??c??c??c??c??c
AURAN USTAZ
??c??c??c??c??c??c??c??c
NA UMMY AYSHA
??T???2??_/Q1??_/Q&2??_/Q2??_/Q

"""Aysha tayi shuru zuwa wani d'an lokaci Hasbunallalu wani imal wakim take am'bata aranta zuwa cen ta d'ago fuskarta cike da fara'a kamar koda wane lokaci ta'ce" bakomi Aunty Allah ya had'a kawunan mu ya bamu zaman lafiya."

Fuskar Aunty fal da fara'a ta'ce" Ameen naji Dad'i kwarai da gaske.."

Aysha ta'ce" ba komi bari in'tashi zan biya in d'auki su Usman a makaranta.

Aunty ta'ce" ba komi ki gaida Gida". khadija tashi ki rakata. ta'ce da khadijar dake kwance ta lumshe ido.

Fuska ba Sukuni Khadija ta taso suka fito ba wanda ya'ce" da kowa komi, har suka isa get Khadija ta juya Aysha ma ta koma .

La'ilaha illah anta Subhanaka inni kuntu mina zalimin! shine kalmar da Aysha ta fara fad'a lokacin da ta fito jikinta ya fara d'auka Rawa ko ta ina, Ashe dama tsantsar so zai iya juyewa ya zama k'iyayya, ni USTAZ zaiwa haka duk Hakurin da nike da baud'ad'an halinshi, yanzu a'matakin iliminshi shine zaizo neman Aure ba tare da sani naba, hmmm A dai-dai wannan lokacin ya kanata in dawo Aysha ta- ta da Wallahi, ya kamata duk wani tsantsar iskanci da zayyi zanzubamai ido inga iya gudun ruwan shi,ta tashi taci gaba da tafiya harta isa makaranta su Usman, ganin akwai sauran lokaci dan karatu suke kawai ta wuce gidan ta, har zata bud'e gidan kuma ta fasa ta fada gidan Aunty Maryam .

Aunty Maryam na zaune taga Aysha murna ta kamata! ta'ce" yau kece agidana?

Aysha ta'ce" ai'kuwa magana nikeso muyi dake ta fahimta, shape-shape ta fad'ama Aunty Maryam abunda ya faru yanzu." Dogon salati Maryam ta sanya sai ga hawaye shar a fuskar ta, dan harga Allah sosai take son Aysha so bana wasa ba, cikin kuka ta'ce Aysha abunda USTAZ ya zab'ama Rayuwar shi kenan?

Ina iliminshi ?
Ina bin Dokar Allah daya ke?
Mikikai mai da tsantsar so ya riked'e ya koma zalinci da k'untatawa?

Aysha ta'ce" oho" kila duk cikin ilimin nashi ne, Wallahi Aunty Maryam ni na son sai da tsantsar so ake kishi, azahirin gaskiya ban ma USTAZ wannan ham'shakin son balle inyi kishi na hauka a'kanshi, kuma Wallahi tallabi ni Aysha nayi Al'kawarin duk wuya duk rintsi bazan yiwa USTAZ wannan maganar ba ,kinga sati ukku ya rage ko? to ya dad'e ina kwance bai shigo yace in gyara zai wuce da wata ba. ta fada cikin hargagi.

Aunty maryam ta'ce" kiyi hakuri Aysha! fatana ki ??aukeni kamar yanda na d'aukeki, Wallahi tsakanina da Allah nike sonki, kana zanyi am'fani da dukiyar da Allah yaman zamuyi a'bunda ran mu ke so a'bikin nan, ta yanda babu shegen daya isa yakawo maki raini shikuma ki zubamai ido kiga iya gudun ruwan shi kinji?

AYSHA ta'ce" baki da matsala da wannan yanzuma wayata zan fiddo in fara am'fani da ita.

Aunty Maryam ta'ce" ai layin ki zaki sanya akai ko"?

Aysha ta'ce eh shine.

Maryam ta'ce to zanyi miki transfer credit yanzu in yaso saiki kira Umma kiji ta-ta shawara ko?

Aysha ta'ce" haba ki barshi Wallahi ba damuwa nagode hakama ".

Maryam ta b'ata fuska ta'ce" miyasa kikeman haka ne dan Allah? ko dai baki yarda da ni bane?

Aysha ta'ce aa wallahi ba haka bane! kawai kinson yau da gobe sai Allah, amma shikenan Nagode. sukai sallama ta fita! tana fita su Usman na dawowa ta kamasu suka shige gida shape-shape ta masu wanka ta zubamasu sakwara Doya da miyar a'gushi da tayi, sai kamshi take miyar ko nama babu dan USTAZ yace yawan cin nama cuwul wuta yake kawowa, bayan sungama sukai Sallahma tayi masu bitar k'aratu kana ta kaisu suka fitsari ta kwantar dasu, tare da tofesu da Addu'a ta fita har lokacin USTAZ bai shigoba abunda bayayi tayi wankanta fess ta fesa turarukanta da Aunty Maryam ta bata ta koma d'akinta tare da dakko wayar data cika da charger ta sanya layin ta ta kunna cikin lokacin wayar ta bude rass da ita tamakar sabuwa farin ciki marar musultuwa ya kama Aysha, ganin ta yau da babbar waya, shekara biyar kenan rabon ta da waya sai k'arama! k'arama ma saida hakkin a'shana malatsinta ke am'fani.

Tana kunna wa message ya fara shigo wa, ciki kuwa harda na transfer da Aunty Maryam ta Mata na D'ari biyar, da??i yakama Aysha ta lalubo Number Umma ta kira, bugu biyu Umma ta d'auka cike da farin ciki! ta'ce Auta kece A gari inji maki bak'o?

Aysha tai Dariya ta'ce Wallahi kuwa Umma! nan suka gaisa suka fara firar duniya anan Aysha ke sakoma umma zancen bikin Ustaz da bata saniba.

Umma tayi mamaki matuk'a amma bata nuna ba, sai cewa tai haba yo miye a'bunda yake maki shizai mata in ya kawota, kuma

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login