Showing 24001 words to 26141 words out of 26141 words
Chapter 9 - ADALILIN 'YAR TSUNTUWA Complete Hausa Novel
babu abinda takeyi a Saqe.
Fesss! Yagane hararar da take masa,A ransa "yace( yarinya zamu hadu a lungu,zakisha mamaki na) lungu Kuma Ya Shuraaimπ±
Koda Suka Isa wajen ya Isa tamqam,samari da 'yan mata Kowa ya wanku,Koda Ya Shuraaim yashigo da motansa gidan gaba daya kallo ne yadawo kan motansa.
Parking din motar yayi a parking space,yafito.
Aunty Aisha da Jumaima Suma suka fito.
'Yammata da dama hankalinsu yadawo kan Ya Shuraaim ne,kamar yanda hankalin samari da dama yadawo kan Jumaima,lura da hakan da Ya Shuraaim yayi ne,ya matso inda Jumaima take,tare da Kama hannunta.
Gaba daya wajen tafi akadauka,don sunyi matching sosai.
Aunty Fareeda CE tazo wajen cikin Murmushi"Tace Ya Shuraaim yaushe kadawo ne?
Mushiga daga ciki Sai kiji,gaba yayi tare da Kama hannun Jumaima yayi hanyar Falon gidansa .
Da yake gidansa da girma,da flowers sosai,Shiyasa za'ayi Event din acan.
Koda suka shiga sakin hannunta yayi yasamu daya daga cikin kujerun Falon yazauna.
Baeee jeki daukomin ruwa a firij pls.
Dubanshi Jumaima tayi ta turo mouth gaba"tace Ya Shuraaim basaika Kira budurwanka tamaka ba,tunda ai ranar nan kayi waya da ita.
Cike da mamaki Ya Shuraaim kedubanta"yace ok nagane DALILIN fushin don kawai bance kinyi kyau bane?
Oh Sorry baeee kinyi kyau sosai wallahi,Shiyasa ma bazan iya barinki a waje ba,wasu qatti su qaremiki kallo.
Qara turo Dan qaramin mouth nata tayi tare da miqewa,babu inda baya Shaking a jikinta,daukomasa ruwan tayi tabashi.
Amsa yayi Yana guntse dariyar da tazomasa.
Can hade rai kamar bashi ba "yace Eheem wato rannan Saida kikasa Veil Kika raka Fareeda biki ko?Duk idon Maza yadawo kanki Koh?
Mouth din Jumaima har rawa yake Tace"wallahi ba Veil nayi niyyar sawa ba,long hijjab din daka dinkamun na dauko zansa.
Shine tahanani sawa fah.
Ba nace Miki idannasake ganinki da veil ba zansameki?
Qara face din tausayi tayi"Tace duk Saida nafada mata fah.
Ok to yanzu zan hukunta ki,kinka wajen Arabian nights dincan? Baxakije ba,Sai Aunty Fareeda tazo ta daukeki.
Kuka Jumaima tasa masa Tace"to kasan bazaka bari najeba meye nabari nazo Nan?
Dariya yaso kubuce masa,but Sai yadake,baisake magana yamiqe yahu sama tare da Zama a balcony na wajen mutane da dama sun hangoshi.
Ita kuwa Jumaima tana falo tanacin uban kuka.
Aunty Aisha CE tashigo, Jumaima tabata labarin abinda kefaruwa.
Lallashinta ta shiga yi,tare da Bata baki.
Ummiey CE kewaya tana fadin hannu?yariqemata?lallai Shuraaim Yana neman zubar Mana da mutumci,zanyi maganinsa bari nakira mahaifinsa.
Wayar Ya Shuraaim ne yayi ringing,Koda yaduba sunan Abba yagani.
Picking yayi tare da sallama,bayan sungama gaisawa ne Abbiey"yace duk abinda yakeyi yadakata yazo shida Jumaima.
Abbiey lafiya kuwa? tambayar da yayi kenan.
Sakkowa yayi ya ciddatq tana ta kukan ne.
Dubanta yayi"yace inkin gama kukan kizo muje idan Kuma baki gama to.
Miqewa tayi tare da sake turomai mouth din..........Allah ne yabashi Sa'a yayi Wuffff yadamqe leben.
Kuka Jumaima tasake saki.
Wakike turoma Wannan qaramin bakin?takasa mgn tunda bakinta na hannunshi,saidai hawaye da taketayi.
Sakin mouth din nata yayi yaja hannunta suka fito harabar gidan,inda mutane suke damqam.
Waqar larabci akasaka.
Da yawan idon mutane yadawo kansu,bude mata mqzaunin Mai zaman banza yayi yasata,shikuma yazagayo ya shiga ya tada ya fita.
Koda sukaje Falon Abbiey suka wuce gaba dayansu,suka samu waje suka zazzauna tare da gaida Abbiey.
Amsawa yayi kamar yanda yasaba,saidai you face nasa babu wasa.
Daukar wayansa yayi ya Kira Ummiey.
Jumaima najin ankira hajja Saida cikina ya murda.
Mommah tashigo tadubi Jumaima Tace"kekam Wannan 'ya Allah ya shiryeki,kidunga Abu saikace wata tsohowar karuwa?.
Ya Shuraaim ne yadubi Ummiey yace"Subhanallah Ummiey yarinyar da zan aura kikekira da karuwa???
Abbiey, Ummiey da Jumaima a mamaki suka dago suna dubanshi, Ummiey kuwa tafi firgita.
_To Ummiey mekeshirin faruwa ne haka_???
NAGODE Muku sosai members din groups da dama:
*_XAHRA'S NOVELS_*.
*_EYMAN CASTLE_*.
*_ZEE XEE'S NOVELS_*.
*_TARTSATSI WUTA HAUSA NOVELS_*.
*_HJY MARYAM HAUSA NOVELS_*.
*_CHAM_*~*_NOVELS PANS_*
*_Inajin dadin comments naku agareni bazan ta6A mantawa dakuba_*.
Ur Lovely Xahran kuceβπΌβπΌβπΌ
ππβ€οΈ
ππ
β£οΈ
Lallai Alqalami ποΈ Yafi takobiπ‘οΈ
[4/24, 5:33 PM] Zarah Bae: π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*TAMBARI WRITERS ASSOCIATION*
π±(( *_Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah_*))
*T. W. A*
_LABARI/RUBUTAWA_
*_PATEEMA XAHRA LAWAL_*
*_This page is dedicated to my Aunty Ni'ima Salee's Mai Allura,sis zee Xee,sis hajy Maryam sakatare and sis Aunty Maryam tnx so much_*
*Bismillahir-rahmanir-raheem*
*_LAST PAGE_*
π
ΏοΈ:39-40
Ummiey tace"wallahi baka Isa ba,bakasa kadauko *_'YAR TSUNTUWA_* kakawo Mana cikin gida ba.
Gyaran murya Abbiey yayi tare da duban Ya Shuraaim yace"Alhamdulillah Shuraaim naji dadin maganarka,abinda yasa bance wani abuba sbd Naga kaman bekamata namuku shshshigi bane shysa.
Amma nayi farin ciki sosai,nikam Banda matsala saidai bamusan ita Jumaima dinba.
Abbie yadubi Jumaima"Yace diyata kinason yayanki?
Jumaima takasa magana,duqar da kanta qasa tayi batare da tayi mgn ba.
Ummiey Tace"wallahi ba'a isaba,Wannan ma ai maganar banza CE,tayi mgnr tare da fita fuuuu.
Ajiyan zuciya Abbiey yayi "yace kada kudamu insha Allah komai zaitafi yanda akeso.
Kutashi kutafi Allah yamuku albarka.
Ameen suka fada gabadaya su.
Ya Shuraaim ne yafara fita Jumaima tabi bayanshi.
Hawaye ne masu zafi suka tsiyayo mata,tarasa wani irin qiyayya Ummiey kemata,ita Gaskiya bazata iya auren Dan taba.
Kuka take sosai,sukashiga mota,Ya Shuraaim yadubeta tare da Kiran sunanta.
Amsawa tayi cikin muryan kuka.
Bakisona ne Jumaima?
Yayi tambayar.
Shiru tayi batace komaiba"yace pls feel free tell me the truth, wallahi babu Wanda ya Isa yayimiki dole kinji?
Fadawa jikinsa Jumaima tayi tare da fashewa da kuka Tace"Yaya Ummiey batasona menayimata?
Shafa kanta yayi "yace kada kidamu time nanan zuwa,Ummiey zata soki sosai.
Miqamata handkerchief yayi yace"share hawayenta toh .
Amsa tayi tashare hawayenta,daganan suka cigaba da hiransu,yanata Bata labarin da yasan zaisata nishadi.
Abbiey yayima Hajja magana tayi farin ciki sosai,da Kuma sa albarka.
_BAYAN KWANA BIYU_
A yau ne qarfe 11:00 aka daura Auren AHMAD SULIEMAN(MAI-DALA) & FADEELA B ABDULBASEED(MARADI).
Anagama daurin aure aka fara shirye-Shiryen tafiya da Amarya Bauchi.
Aunty Fadeela tayi kuka sosai,sun rungume juna ita da Fareeda sunsha kuka sosai, Jumaima ma haka.
Motoci biyar aka dauka duk da na Ya Shuraaim,motarshi Jumaima CE da Aunty Aisha Sai junior,Aka miqe hanyar Bauchi.
Qarfe hudu suka Isa bauchi,gidanta na jikin na mahaifan mijinta.
'yan uwan Ahmad sunyima dangin Amarya tarba Mai kyau.
Nan Jumaima suka Sha hiransu na soyayya itada Ya Shuraaim abokin fadanta,Kuma abokin rayuwarta anan gaba.
_Washegari_
Qarfe 11:30 su Adda Safiyya sukashiga bangaren Amarya, Jumaima tana zaune tsakiyarsu Aunty Fareeda da fadeela, Aunty Fadeela lullube take fuskarta da mayafi.
Ta juyama qofar bedroom din baya Jumaima.
Kamar daga sama tadunga Jin wani murya kaman Wanda tasani.......a firgice ta juyo Tace"Adda!
Saukowa tayi tana nunata.
Itama Adda Safiyya a rude Tace"Jumaima!
Jumaima sulalewa qasa tayi sumammiya.
Gabadaya dakin ya rude Sosai,kuka Adda Safiyya takeyi tana fadin "Jumaima Ashe dama zamu sake ganinki?
Maganar take ana yayyafamata ruwa.
Mota aka dauketa Sai JUMAIMA TEACHING HOSPITAL
Emergency aka kaita,Adda Safiyya takira Alhj Tukur tasanardashi.
Sai wajejen bayan isha'i Jumaimma tafarka.
Kuka take Sosai,tana fadin"Adda dama zansake ganinki?ina Mommah na da Abba na??
Share mata hawaye Adda Safiyya tayi Tace"Abban ki yananan zuwa yanzu.
Allah Sarki da da mahaifi Sai Allah, rungume juna sukayi sosai Jumaima da Abba.
Abbana ! Jumaima tafada tana kuka.
Jumaiman Abba Ashe zansake ganinki?
Abbana Ina Ummiey na?
Wani Dr ne tashigo yayi dariya yace"munbata sallama babu abinda kedamunta zaku iya tafiya.
Gaba daya a gidan Adda Safiyya aka tare a falon Alhj Tukur.
Abba, Alhj Tukur, Jumaima, Adda Safiyya,Ya Shuraaim,zee Xee da Xaeyysherth, Fareeda, Baba Alhj, yakumbo, Alhj Hakeem,Hjy babba,gabadaya suna Falon Cike da farin ciki, Jumaima na zaune kusa da Abban ta.
Ankira Mommah ansanar da ita Tace"gobe suna hanya don 'Yan uwan mahaifinta sunzo.
Suma Ya Shuraaim yakira Abbiey yasanar dashi anga mahaifin Jumaima,Suma sunce gone suna hanya.
Nan Jumaima tabasu labarin hannunda tazauna,da Kuma irin riqo na Amana da sukayi mata.
Godiya Sukayima Ya Shuraaim sosai, Aunty Aisha "Tace Kuma Abba shine mijin da zata aura.
Cikin farin ciki suka furta kalmar Alhamdulillah.
Jumaima da sauri tadubi Aunty Aisha "Tace Aunty bafa shi zan auraba,gsky banaso Ya Shuraaim nidai.
Zuciyar Ya Shuraaim ne ya girgiza da kalaman qanwar nasa.
Duk cikansu dubanta sukayi Cike da mamaki.
Dariya Adda Safiyya tayi"tace Uhm karkadamu Shuraaim Dana,ganin iyayenta ne yasa zatayi maka butulci.
Yaqe Ya Shuraaim yayi yace"karkidamu Addanmu.
Alhj Tukur yace"kasan Baba Alhj yafasha mata tsufa shysa batason rabuwa dashi,kasan tsohon Zuma.
Dariya Akasa gaba daya Falon.
Jumaima"Tace Adda Allah dagaske nakeyi bazan aureshi ba.
Harara Adda Safiyya tawurga ma Jumaima alamun kada tasake jin muryanta.
Qwallah ne yafara zuboma Jumaima.
Ya Shuraaim yadubi su Adda Safiyya yace"zamu tafi Adda.
Adda Safiyya Tace"a ina ne kuka sauka?
Ya Shuraaim"yace akwai gidan kakanninmu nauke sauka.
Sukace to shikenan,Nan sukayi sallama da juna akan Saida safe.
Fita sukayi ya Shuraaim da Aunty Aisha.
Jumaima kuwa duban Aunty Aisha tayi"Tace Aunty Saida safe.
Harara Adda Safiyya takuma dallama Jumaima.
Cikin sauri tamiqe tare da bin bayansu.
Koda suka fita harabar gidan Ya Shuraaim juyowa yayi tare da fusgo jumaima jikinsa.
Fuskansa babu alamun wasa yadubeta "yace maenayi Miki dazakice baki Sona?
I Tama daure fuska tayi,a zahirance tanajin dake,but a badinance tsoronsa ne Cike da zuciyarta.
Abinda yasa bazan aure ka ba,saboda zakadunga yimun mugunta ne.
Ayya 'yar qanwata wallahi bazan Miki mugunta ba,Koda yaushe cikin riritaki zan kasance.
Dubanshi tayi ta kwaba face"Tace ya Shuraaim ka tabbata?
Allah mah baeee.
To shikenan.
Nan tarakasu sukayi sallama tadawo.
Adda Safiyya tafara yimata fada,meyasa zakice bakisonsa?,saboda butulci ko mene?
Shiru Jumaima tayi.
Adda Safiyya"Tace bari Mommah naki tazo saina sanarmata.
Cikin sauri Jumaima Tace"Adda don Allah kayahaquri zan auresa.
To shikenan kada kisake daga yau kinji?
Jumaima Tace"To.
Washegari Mommah suka iso itada aminin mahaifinta da Ammin ta(Granny),Sai Goggoji.
Jumaima tayi kukan farin cikin ganin mahaifiyarta sosai,itama haka.
Daga Nan aka tsaida maganar Mommah daga Nan tarewa zatayi.
Adda Safiyya ita tadauki nauyin komai na kayan daki.
Suma su Abbiey sun iso wajen goma na safe.
Ya Shuraaim da Aunty Aisha suka musu jagora,har zuwa gidan.
Hajja, Abbiey, Ummiey duk tare suka shigo Falon.
Suka zazzauna.
Aminin mahaifin Mommah ne yadinga qurama Hajja Ido.......Kai harseda haqurinshi yaqare ya tambayeta don Allah ba itace Asma'U ba?
Hajja Tace"Eh nice.
Kece matar marigayi Alhj ABDULBASEED MARADI Koh?
Cikin sauri Hajja Tace"Eh...Eh...ni...nice wanene Kai?
Cike da mamaki Yan Falon ke kallonsa.
Yace "Nine amininsa Alhj Abubakar da muke zuwa wajenki zance,ya tafi da niyyar sanarma da Yan uwanshi cewa kinsamu ciki.
Tunda yadawo aka juyamasa tunani yamanta daku.
Naje har Zaria don daukoki ko zaituna dake Amma bansameki ba.
Cikin muryan kuka Hajja Tace"Allah Sarki kaga abinda yabarni dashi Nan,ta nuna Abbiey.
Daganan tabashi labarin komai.
Gabadaya Falon yayi tsit Sai fitan numfashin jama'a dake tashi kawai,bayan ta gama ne yanuna mata Goggoji.
"Yace Kinga qanwarsanan sunanta Aisha saidai ana cemata Goggoji,wadannan Kuma! Ya nuna Granny da Mommah yace"matansa CE da yarsa,bayan tafiyanshi ya aureta.
Gabadaya Falon Akasa kabbara.
Ummiey take anan be Dan uwana,Allah nagode ma.
Daganan Kowa yadunga gabatar da kansa a wajen.
Abbiey anan yake maganar Shuraaim da Jumaima.
Baba Alhj yace"bacin kada namuku shishshigi da sainace a daura musu Aure kawai a wuce wajen Kowa ma yahuta.
Duk cikansu sun amince da shawarar Baba Alhj,anbarshi a za'a daura Auren idan an idar da sallar Azahar,shi saiyaje yasiyo goro da alawa da kansa yakawo.
Bayan Sallar Azahar aka daura Auren SHURAAIM B. ABDULBASEED (MARADI) & FATEEMA HABEEB SAN TURAKI.
Ya Shuraaim saboda farin ciki yarasa Ina zaisa kansa.
Ummiey ma taroqi gafarar Jumaima,sannan ta dauki nauyin yimata komai na kayan daki,Sai yanzu Ta tabbata *_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_* Abubuwa da dama nazama alkhairin,gashi ta dalilinta mijinta yahadu da ahlinsa.
Anbar tarewar Jumaima bayan 1week.
Itama aunty Fareeda ya Saleem yafito.
_Fatammu muce Allah yabasu zaman lafiya,yasanya alkhairi_
*Alhamdulillah nagode ma Allah da ya azurtani da lafiya,har yabani ikon gama littafin Nan Lami lafiya,kuskuren da nayi a cikinsa Allah yayafemun*. Qaqaggen LABARI NE bada wata ko wani akayi ba.
Nagode sosai Readersπ *SIS FATIMA ZARAH EYMAN* nagode matuqa Allah yabar zumunci.
Jinjina agareku shugaban qungiyar:
*TAMBARI WRITERS ASSOCIATION*
π±(( *_Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah_*))
Sai bayan sallah zakujini a sabon book Dina,Mai Cike da.......bari dai nayi shiru.
Ur Lovely Xahran kuceβπΌβπΌβπΌ
β€οΈππ
ππ
β£οΈ
Lallai Alqalami ποΈ Yafi takobiπ‘οΈ