Showing 15001 words to 18000 words out of 26141 words
Chapter 6 - ADALILIN 'YAR TSUNTUWA Complete Hausa Novel
sannan tayi feeding Dina.
Na tambayeta ina mommy na "tace tana aljanna Kuma tana jirarmu,haka ne Daddy?
Daga Kai Ya Shuraaim yayi"yace hakane my boi Auntyn ka batayi qaryaba.
Ina Hajja ne?......Dai dai lokacin taqariso Falon hannunta riqe da goro tana ci.
"Tace ganinan fitinanne kazo kenan zaka takuramun diyata,ta dubi junior "tace jiniya ina Auntyn taka ce?
Inkirata ne?ya tambaya.
Hajja"tace A'ah rabu da ita.
Shuraaim"yace akirata inason magana da ita kam.
Koda junior yashiga dakin baeganta ba,but yaji motsin ruwa a toilet,dai dai bandakin yatsaya yayi knocking,"Aunty daddyna yace kizo yanzu.
Fitowa tayi jikinta daure da towel ta dubeshi"kaje kace ganinan zuwa.
Nufar gaban mirror tayi ta dauki manta CARETONE ta murza tasaka long hijjab tafita.
Yana ganinta yahade fuska tamkar baitaba dariya ba,kusa da junior ta zauna"tace Yaya gani.
Hajja kinsan abinda yarinyar Nan tayi?yayi maganar tare da duban Hajja.
Taya za'ace budurwa kamar wannan zata dunga Zama daga ita Sai Vest da fallen zani?gida cike da qatti.
Bude baki Hajja tayi cike da mamaki take duban Ya Shuraaim"tace inane Cike da Qattin Shuraaim?
Nan gidan Mana hajja to megadinki ba da me debo muku ruwa ba qatti bane?idan wani yazo yasameta a haka?
To mene?tunda ba tsirara suka ganta ba,inji Hajja.
Ya Shuraaim yadubi Jumaima"yace ke! Cikin daka tsawa,da sauri ta dago.
"Yace kada nasake ganin kinyi irin wannan shigar a falo kinzauna,kina jina?
Daga Kai tayi "tace Eah.
"Yace duk inda Zaki kidunga saka long hijjab ne,ko inane kinji?
Dogayen hijjab Dina biyu ne daga na islamiya Sai wannan,tanuna na jikinta.
Ok to idan Zaki fita mekikesawa?yayi tambayar babu alamun wasa a face nata,kallon yanda mouth dinnata ke motsi yayi,yarinyar kyanta da dirinta is too much yafada a ransa......
Wayarsa ce tayi ringing.
Dauka yayi tare da fadin hello,yakai 2mint Yana mgn daganan yakatse.
Yadubi Hajja "yace hajja ina wayarkine?Saboda yau Zanyi tafiya,zanje qasar Kuwait Saboda wani course namu,Kuma Zanyi a qalla 1year saidai duk bayan three months zandinga zuwa.
"Hajja tace to Allah ubangiji yatsare,Allah yabada sa'a.
Itakuwa Jumaima farin ciki take sosai bala'i zaiyi tafiya.
Ok Hajja ina wayar takine?
Kaganta can tunda jiniya(Haka take cewa don Bata iya junior ba) yafada da ita Miya yau kwana hudu kenan taqi Koda motsi.
Ok to Anjima zan dawo,Saboda gobe flight din 6 na safe zanbi.
Hajja"tace to shikenan saikazo.
Nan sukayi sallama ya fita tare da dannama Jumaima wata uwar harara,a fakaice ta rama itama......saidai kash gogan yakamata,baice mata komaiba yacema junior yabiyoshi ya'amsa tsaraban cweat.
******
Hjy Rabi ce zaune tayi ta gumi,wani gidan haya ta kama,Mai daki ciki da falo Sai bayi.
Abun duniya duk yataru yayi mata yawa.
Bata da kudi a hannunta Sai 5000,gashi tanaso taje gidansu Baba Alhj taga condition din mijinta kota fadama Boka but bazai yuwuba,tunda taje Adda Safiyya tacimata mutumci, (tunda andawo dashi Nigeria anrasa gane kan cutansa,lallaima aikin Boka Yana kyau),ta Kuma mata warning sosai"tace idan ta bari aka Kuma ganinta ko a jikin gate din gidanne saita kaita a canja mata kamanni.
Tasan halin Adda zata aikata mafiyin hakan idan ranta yabaci.
Ita tsoronta kada mommah taji labarin ciwon tazo,a Koda yaushe maganar Sarkin bokaye kedawo mata(Muddin yahadu da tsohuwar matansa konai zai lalace, sannan komai zaidawo kanki ne),wannan kalmar na firgita ta.
Tashi tayi tahada kayanta"tace gwanda naje maidugri ko mota tace na siyar da nazauna da yunwa.
Ta Isa maidugri bayan sallar isha'i tatarar da mahaifiyarta zaune tanacin abinci babu abinda babu sakwara ce da miyar agushi Sai naman zabi.
Yarda jakan hannunta tayi"tace lallaima Lami ni inacan ina fama da yunwa ke kinanan kina fama da cin Dadi Koh?
Dariya Lami tayi"tace diyar albarka harkin dawo?
Harara Hjy Rabi ta dokawa mahaifiyar tata"tace yunwa nakeji ya maganar abinci ne?
Kije akwai ragowar Dan kadan a kitchen kidauka.
Dan kadan Kuma?tayi tambayar.
Eh Mana nasan da zuwan ki ne? Bata sake magana ba tanufi kitchen din.
Bayan sunci abinci sunyi qatttt ne,domin babu maganar sallah don basuyi.
Lami wai ya maganar jariri kinsamo?
Lami tayi dariya"tace tunima,Amma Saida nasha wahala asibitoci biyar naje da qyar nasamu naje daya a cikinsu wani likita Christa ya siyarmin,wanima asibitin 'yan sanda sukayi qoqarin hadani dashi.
Dariya Hjy Rabi ta qyalqyale dashi"tace to ya maganar canji na?
Harara uwar tata ta dokama mata"tace bangane canjin kiba?
Eah Mana nasan baza'arasa canjiba.
Lallaima Rabi baki da kunya,duk irin wahalar danasha sannan kizo kinamun mgnr canji?to bazan bayarba qarfi ya cinye.
Hjy Rabi Bata sake magana ba ,domin tasan uwannata tafita shedanci,don ita tasata a hanyar komai,Amma saita nuna mata nata karatun( _Wa iya zubillah_ , waifa uwa da 'ya kehaka).
Lami gobe da sassafe saimuje wajen Sarkin Bokaye kawai yagama da Alhj Habeeb don nagaji da wahala,bazan bari yayi rayuwar farin ciki ba,tunda ya nunamun qiyayya,kindaisan son da yakemun bana Allah bane, na aikin bokane Koh?
Lami "tace to shikenan Allah yakaimu goben.
*_I need ur comments dinku sosai,shizaisani nasake tsayin page nawa_*
Ur Lovely Xahran kuceβπΌβπΌβπΌ
β€οΈπ
β£οΈ
Lallai AlqalamiποΈYafi takobiπ‘οΈ
[4/24, 8:12 PM] Zarah Bae: π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*TAMBARI WRITERS ASSOCIATION*
π±(( *_Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah_*))
*T. W. A*
_LABARI/RUBUTAWA_
*PATEEMA XAHRA LAWAL*
*Bismillahir-rahmanir-raheem.*
π
ΏοΈ:27-28
Wajejen 8:30 Ya Shuraaim ya shigo gidan Hajja hannunsa riqe da Dan madaidaicin leda.
Sallama yayi tare da shiga Falon Hajja,wow ! Gsky yayi kyau sosai wani jessy yasaka a jikinta Riga da wando baqaqe,yayi kyau sosai kaman balarabe.
Hajja ce tafito daga daki"tace to fitinanne me yadawo dakai da daddarannan?
Dariya yayi"yace Kai kedai tsohuwannan fitinanne ce,yanzu Kuma menayi?
Hajja "tace kasake dawowa kafiti namun 'ya ce?
Murmushi yayi batare da yayi magana ba.
A daki kuwa Jumaima suna kwance tana koyawa junior karatu kaman daga sama taji muryar gogannata.
Heart dinta ne yafare beating kamar ace takkk ! Tazura da gudu.
Da gudu junior ya miqe"yace oyoyo Daddy, Aunty Daddy na yazo inje?
Daga masa Kai tayi"tace Eh kaje but idan yace maka ina Nike kace nayi bacci kaji?
Dariya junior yayi"yace Aunty bakekika cemun haramun neba qarya?
Kallonshi Jumaima tayi"tace ai wannan ba qarya bane my boi,rufamun asiri zakayi.
Baibata amsa ba ya falfala a guje tare da shiga Falon.
Oyoyo Daddy,yayi maganar tare da rungume Daddyn nasa.
Oh my boi ainayi tunanin kana bacci kaida Auntyn ka.
Girgiza kai yayi.
Ya Shuraaim yadubeshi"yace ina Auntyn ka?
Daddy"tace idan ka tambayeta nace tayi bacci.
Bude baki Hajja tayi,tadubeshi"tace Amma wannan yaron da shegen magana kake,Kai baka iya sirri bane?
Murmushin gefen baki Ya Shuraaim yayi"Yace jeka ce na ce tazo.
Shiga dakin yayi saigashi yafito Yana qyalqyala dariya"yace Daddy Aunty zata zaneni.
Fitowa tayi jikinta sanye da long hijjab,ta duqar da kanta qasa,samun waje tayi ta zauna kusa da Hajja,"Tace Sannu da Zuwa Ya Shuraaim.
Dagowa yayi suka had a ido a lokaci daya,qurama Jumaima ido yayi babu ko kiftawa.
Kallonshi tayi tare da dallamasa harara........karaf ya lura da ita tsaff ! Hade rai yayi "yamiqo mata ledar hannunsa"yace ga wayanan kiduba da shi zamudinga communicating idan ina son jin muryan Yarona da Hajja ta.
Kaman Hajja tashiga zuciyar ta "Tace au Banda ita?
Baice komaiba ya shafa sajennsa tare da cizan lips nasa.
Akwai Sim Card da komai a cikinsu wayar,Number Tace kawai a ciki bana buqatan naga kinda number Kowa,Ok ?
Dagawa tayi tare da turo mouth"Tace harda nasu Aunty fadeela?
Hade rai yayi tamkar baita6a dariya ba"yace ko da kuwa nasu Uwar Aunty fareeda ce !
Daga Hajja har Jumaima diddilo idanuwa sukayi cike da mamaki.
Miqewa Hajja tayi"Tace to bari mubaku wuri.
Cikin sauri Jumaima ta dubi Hajja.
Dubanta Ya Shuraaim yayi"yace zoki amsa saqonki natafi gida.
Miqewa Jumaima tayi"Tace toh.
Futa sukayi har bakin wajen motansa suka Isa yabude bayan motar ya miqomata qaton leda.
Amsa tayi zata juya,cikin zafin nama ya fisgota a tsorace ta juyo ta dubeshi tare da zazzare ido tamkar mara Gaskiya.
Meyasa baki da kunya?yayi tambayar tare da hadata da jikin mota nasa.
Qara diddilo idanuwa Jumaima tayi.
"Yace wakekema rashin kunya fitsararriya?
Jumaima"tace nifa ba dakai nakeyiba.
To dawa kikeyi fitsararriya?
Wallahi da kaina nakeyi kayahaquri.
A hankali yafara matsowa kusa da ita...... Jumaima batayi auneva taji saukar numfashinsa cikin sauri ta runtse idanuwanta,wahayene suka fara silalomata.
Tashi mun a cikin mota mara kunya.
Cikin sauri ta bude idon ta.
Saura Kuma naji labarin bakisa long hijjab saina Saba Miki,duk wani abu da yashafe social media kada ki bude bare a batamunke,,,,,,,,,,,,,kina jina? Cikin daka tsawa yayi maganar,mouth dinta har rawa yake"Tace Eh naji.
Oya Maza ki shiga Ciki.
Jumaima har tutube take ta ciccibi ledar kayan ta shiga.
Koda tashiga duba hijjabs din sukayi kala goma shabiyu ne,Kuma duka yadi hudu hudu.
Takaici yasa Jumaima fashewa da kuka"Tace Hajja yanzu irin hijjabs dinnan zandunga sawa?
Hajja ta dubeta"Tace ba dole bane kiss ga gyaluluwanki da fadeela ta dinko Miki.
Jumaima Cikin kuka"Tace Hajja idan nasaka veils wallahi Ya Shuraaim zaneni zaiyi saboda yace kada nasa.
Hajja Tace to shikenan.
*******
*Maidugri*
Koda su Hjy Rabi da Lami sukaje wajen Boka,sun koro Mai bayanan abinda sukeso.
Kyalkyalewa da dariya Sarkin Bokaye yayi,can Kuma Sai ya turbune fuska tamkar baitaba dariya ba"yace ina? Bazamu iya wannan aikin ba,domin Anfara kakkareshi da ayoyin Allah .
Cikin bacin rai Hjy Rabi"Tace wani irin magnr banza kake fada Boka?
Kana nufin bazaiyuwu akasheshiba?
Daka mata tsawa Sarkin Bokaye yayi"yace Ke! Aljanu zasuyi Miki qarya ne,Koko zakija da aljanu ne?
Cikin bacin rai Hjy Rabi tamiqe tare da tafiya. Qwalamara Kira Lami tashiga yi.
Dakatar da ita Sarkin Bokaye yayi"yace kibarta da kanta zata dawo,jeki na sallameku.
Miqewa Lami tayi tafita.
******
*BAUCHI*
Yanzu jikin Abba yafara sauki tunda Yana magana kadan kadan,sannan ba Kowa yake jinsaba,Sai mutum yakara kunnensa abakinshi yake ji,
Hawaye ne yake gangaromasa yadubi Adda Safiyya dake kusa dashi yafara motsa baki alamun yanason mgna.
Cikin sauri takara kunnenta a saitin bakinshi,ahankali "Safiyya ina Rabi take?
Hade rai Adda Safiyya tayi"Tace Yaya bansan inda takeba Gaskiya.
Kokaka yake"yace inaji a jikinta na rasa wani Abu Mai muhimmanci a rayuwa ta,Amma idan nafara qoqarin tunawa Sai kaina ya saramun.
Adda Safiyya ce tafashe da kuka tatuna cewa komai lalacewar naka nakane.
Sake gwada wayar mommah tayi but still cemata ake Swhitch off,lallashinta Abba tashiga yi,ta kwantar masa da hankali sosai.
Yasamu natsuwa daidai musali.
Sallama akayi tare da shigowa dakin,Alhj Hakeem ne Sai wacce ke bayanshi.
Cikin sauri Adda Safiyya ta miqe tare da nunata da yatsa.
_Wallahi naji dadin comment dinku,ina godiya,don Allah Adena turo sticker matsayin comments pls_ππ½
Ina godiya da comment dinku:
Ur Lovely Xahran kuceβπΌβπΌβπΌ
β€οΈππ
πππ΅ β£οΈ
Lallai AlqalamiποΈYafi takobiπ‘οΈ
[4/24, 8:12 PM] Zarah Bae: π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*TAMBARI WRITERS ASSOCIATION*
π±(( *_Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah_*))
*T. W. A*
_LABARI/RUBUTAWA_
*PATEEMA XAHRA LAWAL*
*DEDICATED TO MY FAMILY GIDAN ALH SALEE'S MAI ALLURA*
*Bismillahir-rahmanir-raheem*
π
ΏοΈ:29-30
Ba kowace Suka Shigo dakin da Alh Hakeem ba Sai Hjy Rabi.
Cikin bacin rai Adda Safiyya"Tace munafuka kinzo kiqarisa sane komai?
Kukan kissa Hjy Rabi tafara.
Alhj Hakeem"yace haba Safiyya kindaisan cewa mijinta ne Koh?Kuma tanada ikon kula dashi.
Adda Safiyya"Tace A'ah Yaya Nima zan kula dashi Allah.
Duban Hjy Rabi Alhj Hakeem yayi"yace matso kusa da mijinki Koh?
Matsowa tayi tare da Kama hannunsa tariqe qam tare da fashewa da kukan kissa"Tace Allah Sarki mijina meyasa Meka haka?
Hawaye suka shiga zuboma Abba yadubeta murya can qasa.........Atare suka Kara kunnensu ita da Adda Safiyya"yace Rabi kin cuceni kin siyarmun da gidana,kinrqbani da dukiyata.
A tare suka dago ita da Adda Safiyya, harara ta dokama Hjy Rabi.
Baisake Cewa komaiba Sai kuka da yakeyi.
******
Tun 4:00 Isah yadaukeshi yakaishi Airport din kaduna,6:30 jirginsu yatashi Sai qasar Kuwait.
Jumaima ce zaune itada junior suna zaune a falo Sai kallo suke, Hajja nakan 3sitter tasaki mouth Sai bacci take.
Qarar bude get sukaji,da alamun mota ce zata Shigo(Qila Abbiey ne).
Miqewa sukayi tare da fitowa farfajiyar gidan itada junior.
Tabbas Abbiey ne shida Aunty Fareeda,murnar ganin juna suke gaba dayansu,dogon Kai Jumaima ketayi kozata ga Aunty Fadeela,but babu ita.
Dariya Abbiey yayi"yace Aunty Fadeela kike leqe Koh?
Aunty Fareeda"Tace Abbiey bari najuya don Naga alamun Cweat sis Bata damu daniba Sai Twins sis.
Cikin sauri Jumaima"Tace Aunty ba Haka bane,kinfi Kowa sanin idan ina tare da ku gabadaya nafi Jin Dadi.
Aunty Fareeda "Tace ok sis sorry mushiga daga Ciki.
Shiga Falon sukayi suka tarar da Hajja da Abbiey suna gaisawa.
Jumaima ta Isa kusa da Abbiey tazauna a qasa kusa da qafafuwansa"Tace Abbiey sannu da Zuwa?
Shafa kanta yayi "yace yawwa diyar kirki Kuna lafiya?
Lfy Lou Abbiey,ya Aunty Fadeela da Ummiey?
Lfynsu Lou,Auntynki Fadeela batanan tana Kaduna wajen sister naku.
Jumaima"Tace Ok Allah yadawo da ita lfy.
Ameen suka amsa da shi gaba daya.
Miqewa tayi tare da shiga bedroom wajen Aunty Fareeda da junior.
Bayan tafiyar ta ne Abbiey yayi Murmushi tare da girgiza kai"yace Hajja inajin yarinyar Nan a jikina tamkar su Fareeda,ko wani hali iyayenta suke oho?
Hajja"Tace to yaza'ayi? Sai addu'ah.
Ananne yake sanar mata ansaka ranar auren Fadeela 4month.
Hajja "Tace Allah yanuna Mana yasa albarka, Allah yafitoma da 'yar uwanta itama nata.
Ameen! Abbiey ya fada.
Hajja"Tace yaron abokin dai naka zata aura,Na bauchi?
Abbiey"yace Eh shine,Nima jibi nakeso naje Bauchin don kaimusu goron saka ranar,dama na kwana biyu banjeba.
Hajja"Tace to , Allah ya kaimu.
~AFTER 2 days~
Abbie ya tafi bauchi,ya rabawa dangin mahaifiyarsa goron bikin 'Yarsa ya juya washegari,ko biyawa gidan amininsa kuma surikinsa baiyiva don bayanan.
Hankalin Adda Safiyya ya tashi saboda rashin samun aminiyarta da take a waya.
Don Haka tasanarma mijinta abinda kefaruwa,washe gari yabata izinin ta shirya driver yakaita kano.
Sha biyu da rabi 12:30 suka Isa kanon,saidai abin takaici Koda sukaje anan maqotansu suke cemata batanan tayi tafiya.
Cike da takaici Adda Safiyya kamar tayi kuka ta tambayesu ina taje?
Anan ake cemata sunje MARADI ne itada mahaifiyarta. Tambayar number nata nacan tayi daqyar tasamu wajen talatu maqociyarsu mommah din.
Hakanan Adda Safiyya Suka juyo don komawa Bauchi.
_Fatan muce Allah yamaida ku gida lafiya nida readers_π€ͺ
******
_ZARIA_
Yau Saturday, Aunty Fareeda tunda tazo Bata koma gida ba.
Shiryawa Sukeyi itada Jumaima da junior don zasu rakata bikin wata qawarta a qwarbai.
Sunyi kyau sosai.
Wata Shadda Lemon green Jumaima tasaka,Wanda yaji aikin Stone work,anyi A sharp style doguwar riga,.
Ita Kuma Aunty Fareeda Riga da sket na Lace tasaka blue itama tayi kyau tadauko veil yellow da takalmi tasaka, pos ce yar qarama blue a hannunta.
Jumaima Shadda gezner maroon colour tasaka ma junior da hula qube,Sai malum malum.
Gaskiya Shima yayi kyau sosai.
Farin hijjabs dinta tadauko Wanda yaketa shining na guga white zata saka....... Aunty Fareeda"Tace Kai A'ah kada muyi Haka dake yanda kikayi kyau dinnan kidau long hijjab kisa ai baiyi ba.
Jumaima ta marairaice face"tace a
Aunty Ya Shuraaim yahanani Saka Veil,Wallahi duka na zaiyi.
Ya Allah yanzu Ya Shuraaim din yanananne? "Tace yace zaisa Adunga dubamai.
Oh common duk rudaki da tsorataki yakesonyi,kinsan menene?
Jumaima ta kada Kai.
Aunty Fareeda"Tace kidaina yawan tsoronsa Haka kinji?
Itadai Jumaima batace komaiba.
A cikin kayan da Aunty Fadeela ta siyomata ta zaqulo mata wani farin Veil, Wanda yaji duwatsuna.
Takalmi hell shoe tajiro nata Shima white,Sai 'yan kunnenta fashion da pos duk green.
Gaskiya kwalliyan green white green yayi babu qarya.
Wowww! Kingankine ?Aunty Fareeda ta fada.
Junior"yace Allah Aunty kinyi kyau.
Jumaima wajen mirror taqarisa tare da qarema kanta kallo tass.
Tabbas itama tayi kyau,komai yazauna mata tamkar don ita akayi.
Aunty Fareeda"Tace keta dabance,ke din mekyau ce Cweat Sis Allah yahada kawunanku da maikyau irinki.
Itadai Jumaima bata fahimci kan maganar ba don Haka ta basar.
Sun Isa gidan bikin don direban Abbiey Aunty Fareeda ta kira,Qofar gidan Cike yake da Maza,don ba'adade da gama daura Auren ba.
Koda aka saukesu kallo dawowa wajensu yayi saboda Zuqeqiyar motan da ta fakasu.
A hankali suke Saukowa da ka cikin motar,qafar Jumaima na hango tana ziro dashi a hankali chocolate colour me kyau,yayi kyau a cikin takalmin nata.
Wowww! Maza da
dama suka furta a wajen.
Aunty Fareeda ta leqo dai-dai saitin direba "Tace oga sabeetu zaka dawo kadaukemune ko Yaya?
Zankai Hjy anguwa idan mundawo da wuri sainazo.
Ok babu damuwa duk yanda akeciki I will call yhu back.
Tom hajy!"ya fada.
Qawayen Aunty Fareeda cike da murna suka rungume juna tunda duk Course mate nasu ne a A. B. U Teaching Hospital Tudun/Wada Zaria(Barau Dikko).
Amaryar tayi kyau Tasha kwalliya sosai.
Wata qawar Aunty Fareeda ce,ta dubeta "Tace sis A ina kikasamu kyawawa haka?
Aunty Fareeda tayi dariya tare da nuna Jumaima"Tace wannan Coursin Sister tace yarinyar qanwan babana,Wannan Kuma tayi maganar tare da nuna junior"Tace yaron Ya Shuraaim ne.
Cike da farin ciki"Tace wowww! Gasu Kuma kyawawa.
Duk da su Fadeela da Fareeda farare ne,Saidai duk inda suka shiga da Jumaima saita dishe haskensu,gata