Showing 12001 words to 15000 words out of 26141 words

Chapter 5 - ADALILIN 'YAR TSUNTUWA Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

1612

tayi.
15mint tadauka tareda gama hada breakfast din,domin har kunun gyada tahadamusu.

Bayan sungama karyawa tayi duk wani aikace aikacen da suka da ce,taje tayi wanka tare da sa wani material na buba mai zanen flowers gsky rigar tayi kyau Kuma ta zauna mata,tunda jumaima akwai diriiii.

******
*_BAUCHI_*

Abba duniya tamasa zafi komai yatsaya masa cak,ga tunanin rayuwa daya masa haka,yarasa wani lepi yama Allah yake fuskantar jarabawa haka.
_Hasbiyallahu wa ni'imal wakeel_. ...... _Allahumma ajirni fi musibati-wa'aklifni khairan minha_.
Rana ta farko kenan Dana ta6a jin Abba yayi addu'ah.
Hawaye ne masu zafi suka zubomasa,hakanan yakeji ajikinsa kamar yarasa wani tsoka na halittarsa but yakasa fahimtar komai.
Gashi Allah yahadashi da ballagazar mace,yau 2days kenan babu Hjy Rabi agida,to ina take?
Tambayar dayayima kansa kenan.
Miqewa yayi zai hau steps saiyaji ana knocking din door,da sauri ya qarisa wajen qofar.
Koda yabude wasu maza yagani,wadanda bazasu wuce sa'o'insaba,musabaha sukayi da juna.
Bismillah kalmar da Abba yace musu kenan tare da nuna musu alamun sushiga daga ciki.
Bayan sun zazzauna ne ,daya daga cikinsu "yace Alhj Habeeb maganar gidankane da muka siya yau zawon 2weeks kenan ance za'akawomana takardun gida but munji shiru,shine yanzu muka biyo sahu.
Cike da mamaki Abba yadubesu "yace maganar gida Kuma?wani gidan kenan mukayi nagana da ku?Kuma suwaye ku?
Kallon kallo sukebin junansu dashi,daya yadubi Abba (daya ke su biyune sukazo) "yace katuro matarka Hjy Rabi tasiyar da gida,Kuma mungama mgn da'ita munzo munga gida,domin har court mukaje tasa hannu,yau kwana biyu kenan da mukabata kudin 10millions,but munji shiru babu ita babu labarinta.
Take anan kan Abba yayi mugun sarawa,jiyayi qirjinsa yayi masa nauyi,tundaga lokacin besake sanin inda kansa yakeba.

******
*_KANO_*

Zaune take akan sallaya tanajan carbi,jitayi zuciyanta yanamata rawa,ga heart dinta da yake beating.
_INNALILLAHI WA INNA-ILAIHIRRAJI'UN_ kalmar da tafada kenan,wasu tears masu zafi suka shiga zubomata.
Daga hannuwa tayi tare da furta "Allah gani a hannunka duk inda diyata take Allah ka bayyana mun ita,Allah kakarkato da hankalin mahaifinta garemu Allah na roqeka Allah _Astagfirullah_ na tuba Allah taqarishe maganar tare da fashewa da kuka.
Granny ce tayi sallama ta shigo bedroom, "tace subhanallah maryama meke faruwa?
Mommah na kuka "tace hjy qirjina na bugamun jikina na bani daya daga cikin jinin jikina Yana cikin wani hali,kodai jumaima ko Abban ta,Taqarishe maganar tare da fashewa da kuka.
Kiyahaquri maryama insha Allah duk kansu suna cikin qoshin lafiya da kwanciyar hankali,kicigaba da addu'ah kinji maryama na? Allah natare dake,idan kina Cikin damuwar Nan nima nakan rasa natsuwa tane.
"Nace kishirya muje maradi wajen dangin mahaifinsu kinqi,haba maryama kemafa kinada haqqi a kamsu suma sunada haqqi akanki,Amma bakijin magana Sam,gashi mahaifinki ya rasu to idan basuyi mikiba waye zaiyimiki?
Cikin kuka momnah "tace hjy nayi shiru,shikenan Allah yadawomin da farin cikin ahlina.
Granny "tace Ameen diyar albarka,kicigaba da addu'ah Nan bada jimawaba komai zaidawo ya daidaita kinji?
Mommah "tace to Hjy Allah yasa.
Ameen,kokefa to kushiga bandaki kiwanke fuskanki ga talatu maqociyarmu can tazo wajenki akan maganar danta dakikace Zaki kai jami'ah.
Ok to Hjy kicemata ganinan,tayi maganar tare da nufar hanyar toilet din da ke cikin bedroom din,ita Kuma Granny tafita.

******
_ZARIA_

Dirrrrrrr!dirrrrrrr!!dirrrrrrr!!!! Qaran wayace alamun Kira ake,cikin sauri hajja tafito falon tare da daukar wayar nata( Tecno mai keypad).
Sallama tayi takara phone din a kunnenta,nidai banji me akaceba but naji hajja nacewa wani asibitin?
Cikin sauri jumaima tafito daga bedroom nata tazo kusa da hajja ta zauna.
Tom ganinan yanzunnan,hajja tafada.
Katse wayar tayi tadubi jumaima "jummy maza daukomin hijjabi na da takalmina zanje asibiti ne,ance yarinyar Nan matar shuraaim tana naquda.
Miqewa jumaima tayi cikin sauri takawo mata,tasaka.
Jumaima "tace to hajja wazekaiki asibitin?
Yaronnan "yace ga direban shi Nan yaturoshi yazo yadaukeni.......adaidai lokacin sukaji horn,cikin sauri suka fito farfajiyar gidan,hajja tashiga motar .
Jumaima"tace to hajja Allah yatsare,ita Kuma Allah yasauketa lafiya.
Ameen! Hajja tafada
Haka jumaima tadunga dagamata hannu har Saida tadena ganin motar sannan tadawo falo tazauna tare da fadawa duniyar tunani.



A. B. U teaching hospital tudun/wada Zaria aka rubuta.
Koda hajja sukafito haka tadungabin direban Alhj Basheer har suka Isa inda su Ummiey suke.
Kamar inajin ihu,kalmar da hajja tafada kenan,Cikin sauri suka karisa.
Ummiey ce ke kuka tare da su fareeda.
Abbiey natsaye idanunshi sunyi cazir kaman garwashin wuta.
Gefe guda iyayen Aunty Ni'ima ne,Sai wata mekama da ita,suma kuka suke babu saurarawa mutane sun cika a inda suke.
_innalilkahi wa Inna ilaihirraji'un,shikenan Ni'ima kintafi kinbarmu,munrasaki innalillahi wa Inna ilaihirraji'un_ kalmar da Ummiey kefada kenan.
Hajja"tace _La ha illa-ha illallahu muhammadar-rasulillahi_ kardai kucemun tarasu aituni waje yasake hargitsewa.
Wani babban likitane yazo "yace haba hajiya kiyahaquri Mana,kunga muna da patient masu labour kada wasu su rude kuyahaquri.
Abbiey ne da mahaifin Aunty Ni'ima suka musu magana,tare da yima drivers dinsu magana akan akwashesu Ummiey akaisu gida can gaskiya layout (wato gidansu fadeela) suma gasunan zuwa da gawar.


Readers wai ina Ya Shuraaim ne?
Wajen shabiyun dare Aunty Ni'ima tafara naquda,Ya Shuraaim dayaga haka Sai yadauketa,sbd rudewa ma yamanta da A. B. U See dake kusa dasu,shiyasa yawuto da ita nan.
Ko kafin su iso tajigata sosai,cikin gaggawa nuses din asibitin sukayi labour room da ita.
Manyan likitoci ne akan Aunty Ni'ima,saidai kaga Doctor's nagudu sun nufi room din da take.
Babu abinda Ya Shuraaim yake Sai kuka wiwi,wayarsa yadauko tare da Kiran Abbiey,ba'adauki time ba Abbiey yayi picking call din.
Jin muryam Shuraaim na kuka yasashi watstsakewa tare da tambayarshi lafiya?
Nan Ya Shuraaim yasanar mai abinda ke faruwa.
Ok gamunan zuwa,kalmar da Abbiey ya fada kenan.


Wajejen 2:300 Abbiey suka qariso shida Ummiey,sun cidda dan nasu cikin damuwa matuqa,kwantar mai da hankali suka fara.

Wasa Wasa Aunty Ni'ima har five,Abbiey da yaga haka saiya cema Ya Shuraaim suje su daura alwala suyi sallah raka'a biyu,babu musu Suraaim yabi Abbiey nashi suka wuce.Aunty Ni'ima Bata haihuba.
Wajejen 8:00 akafara qoqarin shirye shiryen yimata operation don har Shuraaim yasa hannu,Aiko saiga haihuwa gadan gadan ta iso......adaidai wanna time dinne mahaifanta da sister(wato yarta mace) dinta suka qariso.
Tahaihu ansamu baby boy saidai baizo da raiba,a wanna lokacinne tafara fitarda jini sosai a jikinta,tana wani irin jijjiga,ana qaramata jinine wani na zuba ajikinta.
Su fareeda suma sunzo asibitin.
Aunty Ni'ima batasan wake kantaba,kamanninta sun sauya,tayi wani irin kyau matuqa,Banda kuka babu abinda suke,hatta su Abbiey da mahaifinta d suke maza Saida suka zubda qwallah.

Ana cikin wannan halinne rai yayi halinsa, _Kullu nafsin za'ikatul maut_ .

Atake anan Ya Shuraaim ya yanke jiki yafadi,tuni asibitin ya hargitse, Nuses suka daukeshi tare da shiga dashi.

Wannan kenan.

******
Anyimata sutura, tare da kaita gidanta na gaskiya.
Har a likacin Ya Shuraaim bai far fadoba.


Sai wajejen qarfe biyar ne hajja ta tuna da tabar jumaima a gida,Isah drivern Shuraaim tasa yadauko jumaima.
Koda tazo taga abunda ke faruwa tayi kuka sosai itama,Allah sarki junior tun bayan rasuwar mahaifiyarsa yake kuka,dukda besan mutuwa ba,but cewa yake akaishi wajen mommynshi,yaqi yarda da Kowa hatta su fadeela,anyi lallashin har angaji.
Falon Ummiey cike yake da mutane,wasu 'yan uwan marigayiya,wasukuma 'yan uwan Ummiey da qawayenta.
Shiga Falon sukayi tare da su fadeela,tayima duk wadanda yakamata gaisuwa,ita kuwa Ummiey Banda harara babu abinda take dokawa jumaima(Oh ni Xahra, Ummiey a gidan gaisuwar ma)?

Can suka qarisa inda hajja take da 'yan uwan marigayiya, junior Yana hango jumaima yataso da gudu ya ringumeta Yana sake fashewa da kuka
Aunty ina mommyna ne?bangantaba.
Duk Falon tsayawa kallonshi akayi.
Hawaye ne ya wankema Jumaima face "tace ayya junior Mommynka tatafi tasiyo maka chocolate.
Shiruuuu yayi na dan wani lokaci "yace to ina Daddy na?
Jumaima tayi shiru saican dibara yafadomata "tace yaje kasuwa yasiyo maka jirgi.
Dariya junior yaqyal-qyale dashi tareda fadawa jikin Jumaima yayi hugging nata.
Duk wadanda ke falon Saida sukayi Murmushi koba komai yanzu za'asamu yayi shiru .
Ummiey kuwa aranta fadi take tabbb dijam! Inah ?aibazeyuwu inyi sake shima Dan Nan ta mallakeshiba(Uhm kaji Ummiey saikace wani Shuraaim?wai mallakewa)to a'ina junior yasan yarinyar nanne?
Kokafin tadawo tunani basu Jumaima da su fadeela da junior a Falon.

Miqewa tayi cikin sauri tayi hanyar steps

Maganar su Jumaima kuwa kitchen fadeela taje tadeboma junior abinci, Jumaima tadunga bashi,don yaqi cin abinci tare da hada mai da Bobo.
Duk Wanda kakalla acikinsu tayi zuru zuru,Allah sarki mutuwa Allah yajiqanki Aunty Ni'ima,halinki nagari ya cimmiki, Jumaima ce tayi maganar tare da fashewa da kuka.
Su fadeela jikinsu duk yayi sanyi, fareeda kuwa babu danne dannen phone dinnan na fama,batamasan inda tayarda phone dinba.
Junior ne yamiqe ya isa gaban Jumaima "yace aunty meyasa kike kuka?
Jumaima takasa magana cuz kukan yaci qarfinta sharemata hawayen fuskanta yafarayi da hannunsa ......babu zato babu tsammani sukaji junior yafashe da kuka.
Aituni Jumaima tadakatarda nata tajawoshi jikinta "tace meyasameka Kuma kake kuka?
To bake bane kike kuka?yayi maganar guntun hawaye nasake zubomai.
To shikenan nayi shiru kayi haquri bazan sake kukaba kaji?........
Banko qofar bedroom dinsu fadeela akayi da qarfi a tsorace dukkansu suka juya.
Ummiey ce ! Tashigo fuskarta tamkar Bata taba dariya ba,nufo inda Jumaima take tayi a zafafe, Jumaima kuwa Banda rawa babu abinda jikinta keyi,zufa Sai aikin ketomata yakeyi,cikin sauri fareeda da fadeela suka miqe tare da shan gaban Ummieyn nasu.
Zaku matsa kubani waje ko sainaci ubanku anan? Fadeela taduqa gabanta "tace Ummiey kiwa Allah kada kitaba Jumaima Kinga rasuwa akai,Kuma gidan cike yake da mutane.
Harara Ummiey ta dokama Jumaima "tace kafin nanda awa uku kibar cikin family Dina inkuma ba hakaba,sainasa ancanza Miki halitta,sannan a dauke ki aje can bayan gari ayar( To Ummiey kodai kinkoma dabancine)?
Jikin Jumaima na rawa"tace to zantafi.
Ummiey Bata sake maganaba tafita.

Bayan fitarta ne Jumaima tamiqe jikinta haryanzu bedena rawa ba,fadeela"tace ina Kuma Zaki?
Fashewa da kuka Jumaima tayi"tace Aunty fadeela bansan inda zaniba,but dole nabar family naku, Ummiey ashirye take ta'iya yimun komai. Taqarishe maganar tare da fashewa da kuka.
Fareeda"tace Sam baza'ayi hakaba kujira ni bari nazo,miqewa tayi tare da fita.

_ko me fareeda zatayi oho readers,mudai Allah yasa muji alkhairi,wadanda sukarasu Allah yamusu rahama_

*_Gaskiya comments naku na jiya yasani nishadi,dukda bansamu yanda nakesoba Nagode sosai da comments naku_*:

_Ur Lovely Xahran kuce_✍🏼✍🏼✍🏼
β€οΈπŸ’ž
❣️
Lallai AlqalamiπŸ–‹οΈYafi takobiπŸ—‘οΈ
[4/24, 8:11 PM] Zarah Bae: πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯

*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*

*_πŸ”±((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*

*T.W.A*

_LABARI/RUBUTAWA_
*_PATEEMA XAHRA LAWAL_*

*Bismillahi-rahmanir-raheem*

πŸ…ΏοΈ:23-24

Koda fareeda tafita ta cidda andawo da Ya Suraaim gida,mutane suntaru akansa Kowa qoqarin yimasa gaiauwa yake.
Lokaci qanqani Ya Suraaim ya zuge tamkar bashine sadauki ba,idanahi sunyi jazir alamun yaci kuka.
Fareeda ce taqarisa wajen da sauri "tace Yaya sannu ya jikin?tsqyawa yayi kawai Yana kallonta tamkar wani mai tunanin wani Abu.
Yaya yaqarin haquri?hannu kawai ya iya dagamata,miqewa tayi tadubi Abbiey"tace Abbiey pls inada magana dakai !
Miqewa Abbiey yayi suka koma gefe bansan me fareeda tafadamasa ba saidai lokaci daya fuskarsa ta sake canzawa,da alamu wannan ta fushine,cewa yayi muje cikin gidan tare suka shiga ciki ya dubi fareeda yace takira masa Ummiey.
Ba'adauki lokaciba saiga Ummiey hannunta riqe da carbi taci hijjab dinta fari tass(Oh kaga Ummiey saikace mumuna).
Qarisowa inda Abbiey yake tayi cikin sauri,dubanshi tayi "tace Alhaji lafiya kuwa?naga kaman ranka a bace yae.
Look! Hjy kinsan nibanason damuwa Kinga gidannan rasuwa akayi matar danki ce tarasu Amma kamar bakidamu ba?Anya Anya wannan halin naki zaitafi dake?
Hade rai Ummiey tayi"menayi?mekuma akace ma na aikata yanzu?
Abbiey"yace mezesa kifitine yarinyar Nan ?waima look! Meyasa baki tsoron Allah ne ke?
Ummiey ta dubi Abbiey"tace lallaima Alhj ni ce bani tsoron Allah ?
To kinayi ne?bari kiji zankira hajja yanzu Sai asan abinyi......cikin sauri Ummiey"tace a'ah basaika Kira wata hajja ba shikenan bazan sake magana akanta ba. Fuuuu ta wuce.
Shima Abbiey komawa yayi wajen amsar gaisuwa,idan kaga Ya Shuraaim kasan Yana cikin damuwa.


~After three days~

Duk anwatse masu amsar gaisuwa,hajja itama shiri take na komawa gida itada Jumaima.
Sun fito driver zaikaisu.
Junior ne keta kuka shi wallahi saiyabi Aunty Jumaima,duk hankalinsu yatashi barimna Ya Shuraaim.
Kuka Hajja tafashe dashi"tace Allah sarki juniya kayahaquri ga mahaifinka nan,an lallasheshi Amma ina yaqi shiru.
Yaqi yarda da Daddyn shima.
Cike da bacin rai Ummiey tazo inda yake ta fusgoshi,cikin daka tsawa"tace Kai don ubanka kayimana shiru,sbd tsabar munafinci dakafin tazo suwa kasani?da yake anbaka a ruwa kasha shine yanzu zaka dagamana hankali taqarishe maganar tare da zaremai idanuwa.
Tsandara kuka ya Kuma,Wanda Shuraaim da Jumaima sukeji har ransu,kuka Jumaima ta fashe dashi.
Cikin bacin rai Hajja ta dubi hajy suwaiba"tace menene haka suwaiba?wannan Dan tatsitsin yaron kikema irin wanna fadar?saikace kinayi da sa'arki.
Zonan megidana,tayi maganar tare da yafito junior da hannu,da gudu ya fisge hannunsa daga na Ummiey yafada jikin Jumaima,rungumeshi tayi tsam a qirjinta tanajin son yaron.
Ya Shuraaim ne yagoge hawayen face nasa,baisan sanda murmushi ya bayyana a fuskarsa ba,dai-dai lokacin Jumaima ta dago, Aiko suka hade ido.
Cikin sauri Jumaima tayi noudding kanta qasa,wucewa yayi Tsohon part dinshi.

Nan su hajja sukamusu sallama tare da shiga mota,Isah direban Ya Shuraaim yajasu Suka tafi gida da junior.

*******
*_BAUCHI_*

*JUMAIMA TEACHING HOSPITAL* naga an rubuta.
Wani Ward kebantacce na hango mutane kamar 'yan family guda ne.
Baba Alhj,Alhj Hakeem,Alhj Tukur Mai naira(Shine mijin Adda Safiyya).
Gefe guda Kuma Adda Safiyya na hango tana ta kuka,Sai Hjy babba,babu yakumbo a ciki.
Haba Safiyya kiyahaquri kidena kukan zaitashi da yardar Allah kinji?
Alhj Hakeem ne yayi maganar,Cikin kuka"tace Yaya meyasa?meyasa farin cikin Yaya Habeeb lokaci daya suka tarwatse?taqarishe maganar tana fashewa da kuka .
Komai yasamu bawa rubutacce ne daga mahaliccinsa mudai addu'anmu Allah yabashi ikon cin jarabawanshi,Duk cikansu suka amsa da Ameen.


~After one week~

Jikin Abba babu Dadi saidai godiyan Allah kawai,domin baisanin wadanda ke kansa ba.
Yanzu haka ana shirye shiryen fita dashi India ne.
Yakumbo kuka take sosai tana fadin "Allahu Akhbar maryama ina kike ne kizo kiga halinda mijinki ke ciki?tayi maganar tare da sake fashewa da kuka .

Qarfe biyar jirginsu Abba ta daga Sai Indiya domin duba lafiyarsa,Alhj Hakeem da Alhj Tukur sune zasu zauna dashi,patan mu muce Allah yaba Abba lafiya,Allah yatada kafada,Ameen.

_Wai in Hjy Rabi ne_???

Tunda ta'amsa kudin gidannan Bata zarce ko inaba Sai maidugri garinsu,gida tasiya Dan dai-dai Sai mota qirar Honda.
Shanawa suke sosai itada mahaifiyarsa don batada uba Ehee.

Wajejen la'asar suka shirya itada mahaifiyarta Sai gidan Boka.
Ahunku dai masu gida,kalmarda uwar Hjy Rabi kenan ta fada.
Wani irin ihu akayi tare da gurnani saiga hayaqi na tashi. Bulll ! Wani halitta ne wada maiban tsoro ya bayyana agabansu Hjy Rabi duk cikansu basu firgita ba.Alamun dama sunsaba da hakan.
Qyal Qyal Qyal akadunga sakin dariya,bokan yadubesu "yace ke Rabi aikinki na kyau,lallai kincika shegiya,lami batayi haihuwar banzaba.
Dariya mahaifiyar Hjy Rabi tayi tace,gaskiya ne sarkin bokaye babu qarya.
Turbune fuska yayi "yace saidai akwai babban matsala.
Cikin sauri Hjy Rabi ta dubeshi "tace matsala Kuma?wata iri ce?
Lallai tabbas asirinki na gab da tonuwa,idan baki wani abuba,domin 'Yarsa da matansa da 'yan uwansa sunanan sunduqufa da addu'ah.
Hjy Rabi tadubi Boka"tace wai Sarkin Bokaye sunhadu ne da uwar da 'yar?
Ina tukuna dai suda haduwa Sai andau lokaci,Sai dai yarinyar tafada hannu nagari domin da alamu akwai alkhairin da zesameta a gidan.
Cikin kaduwa Hjy Rabi"tace Boka to meye abinyi?kasan dai banason naganta cikin farin ciki tun tana qarama Koh?
Qyalqyalewa da dariya Boka yayi"yace babu abinda zamu iya yi akan yarinyar nan,don tafi qarfinmu, hatsabibiya ce ita a fannin addu'ah yanda kukaga uwarta.
Hjy Rabi"tace Boka to ya maganar Alhj?
Dariya yasakeyi yace"aimun jefashi wani hali yanzu haka ankaishi India don duba matsalarsa,hakanan zasu haqura sudawo gida don baze warkeba,indai Kinga ya warke to sunhadu da tsohuwar matarsa ce.

A ranar saikin canza kamanni domin kanki abubuwa zasu dawo.
Hjy Rabi"tace ai dole na dau mataki akan wannan komawa Zaria ya kamani kenan.
To ya maganar dukiyanshi yamun qaryan ankwashe.
Dubanta Boka yayi "yace tabbas baida komai yanzu,sannan mu kammu bamusan wadanda suka kwasheba Kuma duk inda Zaki haka za'a cigaba da fadamiki.
Cike da damuwa Hjy Rabi sukama Boka sallama tare da alqawarin zata kawo jariri sabon haihuwa.

_Toga dai Abba a hannun Allah A hannun Sarkin Bokaye,ko zasiyi nasarar kasheshi ohoπŸ€·πŸ½β€β™€οΈπŸ€·πŸ½β€β™€οΈ,masoyan Abba kusashi a addu'ah Allah yakubutar dashi daga hannun su Aunty Rabi_

Ur Lovely Xahran kuce✍🏼✍🏼✍🏼
β€οΈπŸ’ž
❣️
Lallai Alqalami πŸ–‹οΈYafi takobi πŸ—‘οΈ


[4/24, 8:11 PM] Zarah Bae: πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯πŸ₯

*TAMBARI WRITERS ASSOCIATION*

πŸ”±(( *_Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah_* ))

T. W. A

_LABARI/RUBUTAWA_
*PATEEMA XAHRA LAWAL*

*Bismillahir-rahmanir-raheem.*

πŸ…ΏοΈ:25-26

~AFTER 2 MONTH~

Jumaima ce zaune itada junior tana kooyamasa karatu.
Suratul Muhammad yake karantawa cikin gwanninta saikace yaron Abdurrahman Sudais.
Dai dai lokacin Ya Shuraaim yayi sallama tare da shigowa Falon.
Cikin hanzari Jumaima ta miqe tare da nufar bedroom dinsu itada junior.
Shikuwa Ya Shuraaim Banda harara babu abinda yake doka mata
Da gudu junior yaje yayi hugging Daddyn nasa"yace Daddy sannu da zuwa.
Yawwa my boi how per?
I'm pyn Daddy.
Wake koyama karatu haka?
Junior"yace Daddy Aunty Jumaima ce take koyamun,tamun wanka

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login