Showing 3001 words to 6000 words out of 26141 words
Chapter 2 - ADALILIN 'YAR TSUNTUWA Complete Hausa Novel
tare da qarisawa Inda take nace,mommah meyafaru ne?bata cemun komaiba tamiqe tare da shigewa part dinta.
Ranar haka na yini sukuku,duk Wanda na Tara a cikinsu babu sauqi,akwana atashi.
Bayan kwana biyu ina zaune kusa mommah na,ita kuma aunty rabi (mai aiki) tana gefenata suna hira,mommah na tadubeni tace,jumaimah danbamu waje inason magana da auntynki ne,qoqarin miqewa,aunty Rabi tace karkidamu uwar dakina ai babu matsala jumaimah base tatashi ba.
Mommah na tadubi aunty rabi tace,wani magana nakeso muyi,kuma inason kibani shawara,sannan sirri ne,ko kafin aunty rabi tace wani Abu wayar mommah na yadauki qara(alamun kira)bayan ta gama ne ta dubeni tace kitashi kike abban ki nanemanki.
Miqewa nayi tare da cewa toh, nanufi wajen Abba na,don haka bansan mesuka tattaunaba.
Abba na naraka gidan adda safiyya tayi murna sosai tarasa Inda xata ajemu,ta dubi Abba na tace,daga ina kuke ne haka yaya?
Kingammu daga gida Mike, fura mukaje siyowa sai Pringles na mamanki.
Ah! Lallai shuraimah kedai kinason Pringles koh ?
Dariya nayi nace eh Adda inaso sosai,tayi dariya tare da fadin gaskiya ne ga alamu nan.
Inah kabarmun aminiyata?wato mommah na take nufi.
Abba yace tana gida,bari muzo mutafi Sauri Mike,saboda ba dadewa zamuyiba shiyasa ma kikaga nashigo, Adda safiyya tace,toh aina gode wallahi,jumaimah bari Nazo.
Tashiga daki ta dakko min turaruka da yan kunnaye,godiya na mata muka tafi.
Yauma kamar kullum nadawo school a gajiye don haka direct kitchen nawuce,sai dai banga mommah ba,sai na wuce main falor babu kowa.
Danaga haka saina nufi bedroom dinta kaitsaye,tun kafin ta Shiga tafara jiyo magana qasa- qasa,kuma kamar muryan mommah Dana aunty rabi,
Suna magana.
Leqawa nayi tare da tura kunnena jikin qofar,sainaji aunty rabi na cema mommah kinga wannan kirinqa samishi a cikin miya,rubutu ne da yaji addu'o'i kalakala na kariya, kinsan kakana riqaqqen malamin allo ne,wannan kuma nakine kullum da daddare idan kinyi wanka kingama kimtsa wa zaki turakanshi sai kidunga shafawa duk jikinki.
Amma fah da sharadi kada kiyi gajin haquri,ko kinga bai canza ba kada kidamu a hankali zaidawo hayyacinshi,domin ance farraqu ake neman ayi muku.
Don haka ta Allah bata mutumba babu temakon da bazan mikiba uwar dakina.
Mommah na cike da farin ciki ta rungume aunty rabi tare da cewa dagaske rabi zaidaina wulaqantani muddin nayi haquri?aunty rabi tace sosaima ai kinada haquri uwar dakina saidai nace kiqara,kuma babu abinda bazanyi akankiba.
Mommah na tace nagode nagode rabi sosai.
Saboda farin ciki hartana bata kyautar galleliyar lace dinta Dan 30k.
Aunty rabi tayi murna matuqa tayi godiya harda kuka,
Momma na tace,babu komai rabi zanyimaki mafiyin wannanma.
Nidai ina tsaye inajinsu haka kawai jikina yabani wannan abun da aunty rabi takawoma mommah na ba alheri bane,qwallah ne yatarumin a ido. Sai kurum nashiga dakin tare da sallama.
Duk cikansu sun tsargu da ganina,mommah na tadubeni, A'ah jumaiman mommah meyafaru naga kina kuka?nace mommah kaina me ciwo run a school. Ayya sannu jeki shirya kiwatsa ruwa zakiji dadi,inji mommah.
Saikizo kici abinci kiyi sallah kisha magani,OK mommah na nafada tare da miqewa(first time kenan na rayuwata Dana ta6ama mahaifiyata qarya).
Aunty rabi tace Allah sarki uwar dakina sannu Allah yaqara sauqi,bancemata cikankiba na fita.
Duk abinda akasa mommah na yi game da magani tayi,but kullum matsalarsu da Abba na qara gaba yake,gashi kwana biyunnan aunty rabi tarage shigowa gidanmu don haka mommah na tashiga damuwa.
Satin aunty rabi biyu rabonta da gidammu,saida tacika sati biyu sannan tazo,mommah na tayi farin cikin zuwanta don haka ne tasameta tayimata maganar abinda kefaruwa.
Budar bakin aunty rabi saicewa mommah tayi,uwar dakina kiyi haquri kowa nsnda kika ganshi haquri yake,ni wallahi na gaji da wahala. Da Sauri mommah tadubi aunty rabi don ta firgita da kalamanta tace,rabi!kinsan kuwa da wacce kike magana? Koko baki da lafiya ne?
Aunty rabi tace,a'ah uwar dakina lafiyata qalau ba cutar haukane daniba,kuma gaskiya nafada miki nima nan fama nakeda tawa damuwar,don mijina yamun saki ukku 3 cur,kekoh gwanda dake naki auren girgidi yake beriga daya guntuleba. Bata sake maganaba tawuce tabar mommah da sakin baki,cikin mamaki mommah kesake tuno abinda yafaru.
Daga qarshema aunty rabi tadena zuwa gidan kwata kwata.
Bayan faruwar hakan da sati uku lokacin Abba na yadawo daga Kenya wajen wani abokinsa Baeda lafiya.
Rayuwarsu takoma kadaran kadahan tsakanin mommah na da Abba, kullum tambayar kaina nake meyafaru ne lokaci guda familyn mu take nemar watsewa? Rayuwata tana Neman canzawa,sbd dama banda qawa ni.
Yaran Adda safiyya uku ne kuma duka mata biyu sunyi sure da aunty zainab(Zee zee) da aunty humairah(xayyesherth) sai qaramarsu sameera(meera) dake boarding school a Zaria basawa F G G C BASAWA ita kuma qanwata ce.
Watarana muna dinning gabadaya muna cin abinci,Abba na yadubi mommah yace,wai kwana biyu ina rabi ne? Cikin mamaki mommah tadago tadubi Abba na, tace abban jumaimah kaida bakason kabude ido kaga rabi a gidannan shine yau kake tambayarta? Kada kamanta katsani rabi ,bakason zamammu da ita,kaqare kace *_A DALILIN YAR TSUNTUWA_* ana fuskantar matsaloli a rayuwa,but shine yau kake tambayarta???
_lallai akwai lauje cikin Nadi mommah kibincika_
Ina godiya readers da bani qarfin gwiwa Allah yasaka muku da alkhaeriππΌππΌππΌππΌ
*sis Fatima Zahra Eyman da bazarki nake rawa*ππ½ππ½ππ½π
*Pateema Xahra Lawal*
πβ€π
[4/24, 8:08 PM] Zarah Bae: π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*INTELLECTUπ
°οΈL WRITERS ASSOCIATION*
*_(Home of experts and talented writers, kawo gyara da cigaba ga al'uma shine fatanmu)_*
*I.W.A*
_LABARI/RUBUTAWA_
*PATEEMA XAHRA LAWAL*
π
Ώ: 9-10
___Abba na yadubi mommah yace,yanzu inason kifadamin dalilin dayasa bata zuwa shikawai na tambayeki.
Mommah tace,nibansan dalilin dayasa tadena zuwa kwana biyu ba,Abba yayi shiru tamkar mainazari yace,wato kinkoreta da baqin halinki koh?
Cikin firgici nida mommah muke kallon abba, yace yes kingwada mata halin naki kenan,toh Allah yakyauta yakuma shiryeki.
Yafadi hakan tare da miqewa yabar dinning din,abincinda baiciba kenan.
Hawayene masu dumi suka zuboma mommah,tashi nayi naje duqa a gabanta tare da riqe hannunta nace,mommah waimeke faruwa ne tsakaninki da Abba na? Wallahi da Sam ba haka kukeba,rayuwar family namu abin sha'awane ga kowa,pls meyasa kukeson tarwatsa gidammu?
Mommah tashare tears nata masu zafi tace,jumaimah bansan meke faruwa ba,ban kuma San lepin da nayiwa abban kiba.
Pls inaso kije ki tambayeshi lefinda nayimasa,nace toh mommah zanmasa magana insha Allah, kidena kuka nayi maganar tare da hugging nata muryana yana cracking, nace mommah bari naje islamiyya nadawo kinga munada test idan nadawo saina shiga.
Mommah tace, to shikenan ki wuce bedroom dina kiduba bedside drawer kiciro 10k asa a asusun marayu.
Nace to mommah bye nayi weaving hannuna, itama tace adawo lpy Allah yatsare,Ameen na furta tare da wucewa bedroom nata.
After magrib naje falon Abba na tare da zama kusa da legs dinsa nace,Abba na sannu da gida.
Kadaran kadahan ya'amsamun abisa da dazai jawoni jikinsa muna magana.
Nadubi shi heart dina na beating don Abba na ya canza nace,Abba dama magana nakeso muyi inbabu damuwa.
Yace, OK go a head, nace dama ina shiga damuwa ne saboda yanzu abinda ke faruwa tsakaninka da mommah,shine Nazo naji ko tayima lepine.
Abba na yadago ya kalleni,to yanzu ita ta aikoki kizo ki tambaye ni ko ya?
Nace a ah Abba ko daya, ra'ayi nane kawai,yace to kingani banason qananun magana don haka tashi kije zamuyi magana.
Miqewa nayi don tafiya sainatsaya tare da juyowa nace,Abba......maganarce ta maqale dalilin dagamun hannu da yayi yace,jumaimah out! Cikin Saudi hade da sassarfa nafita saga part din.
Washegari Abba na befito dinning ba,mommah tace naje nadubashi don ta kira phone nashi switch off,koda naje part nashi a rufe don haka nafito tare da sanarmata,ta gumi tayi jikinta yayi sanyi nace,mommah kawai kimanta da Abba tunda abin hakane,kuma kikira granny ki fada mata,wato (mahaifiyarta)ko Adda safiyya.
Mommah ta dubi tare da yaqe tace,jumaimah kenan haryau bakida hankali, yhu re still young,bazaki gane dalilin da yasa bazanfadama hjy ba,riqe sirrin mini shine yafi cancanta ga rayuwar aure,sirri wata abace mai amfani kingane?
Nace,Eh mommah nagane sorry,mommah tace,no sorry for ur self.
Tashi nayi tare da daukar school bag dina nace momma kinga yanzu kinga muna S.S 3,kuma mun kusa fara waec kinga nayi jamb.
School din sae a hankali idan nashirye shiryen candy,mommah tace kuma ahaka za'a cigaba da zuwa harkuyi candy domin naqosa kigama sa wannan mini siket din.
Dariya nayi tareda cewa mommah bye,OK bye dear.
Koda driver yazo daukana gidansu Alh baba yawuce dani,wato gidansu Abba na.
Mutanen gidan sunyi murnan ganina sosai,kuma suka rasa Inda zasu ajeni,hjyn Abba na wacce Mike cema yakumbo tace,ga fura kisha nace,to nagode yakumbo.
Hajy babba kishiyar yakumbo tashigo falon yakumbo hannunta dauke da basket tace,lallai kishiyata sai yau kika tuna damu ko?
Dariya nayi nace,banmanta dakuba school ne yaboye ni shiyasa kuna lafiya tsaofaffi?dariya mukasa gabadaya dasu nace,ina dayan tsohon ne yaje?
Hjy babba tace,yaje gaisheda Alhj ummar abokinshi jiya sunyi accident,nace ayya Allah yabashi lafiya,suka amsa da ameen.
Tambaya na mommah sukadinga nace,tana lafiya da dai kamar infada musu abinda ke faruwa saina tuna nasihar mommah na yau da safe.
Nace tananan lafiya,kunga Ku qyaleni intafi gida time nawucewa kuma naqosa naje naga mommah na,don haka yakumbo kisakemun furar a jug pls,dariya sukayi hjy babba tace,to me uwa ,nandai nayi sallama da kakannin nawa cike da so da qauna.
*_BAYAN KWANA BIYAR_*
Mommah zaune a falo ita da jumaimah,jumaimah kanta na cinyar mommah, Pringle's ne a hannunta tana ci.
Sallaman Abba ne yasasu miqewa,jumaimah da sauri tatashi ta'amsa briefcase din hannunsa race,Abba sannu da zuwa,yace yawwa jumaimah nasameku lafiya?tace lfy lou wlh Abba, mommah itama isowa tayi Inda yake tace, ur welcome Abban jumaimah.
Babu yabo babu fallasa yace,tnx kuna lpy ? Ta'amsa da lpy lou, zama yayi a daya daga cikin kujerun falon,ita kuma mommah tawuce part dinshi don hadamasa ruwan wanka,ita kuma jumaimah tazauna aqasa kusa da qafansa tana bashi labarin taje gidan baba Alhj.
Yaji dadi sosai,yace to ya maganar islamiyya?tace Abba na gobe zamu gama Exam na islamiyya yauma zamuje,yace to acigaba da karatu sosai,nace to Abba na.
Shiru mukayi saican nace Abba na maganarmu ta rannan fa,duk da heat dina yana beating daurewa nayi kawai ina magana,Abba na dubana yayi jikinshi duk yayi sanyi yace,jumaimah bansan meke damuna ba,mahaifiyarki macace mai haquri,inasonta matuqa but idan nadubeta sainaji tafita cikin raina......cikin sauri nadago nadubeshi nace subhanallah Abba na kasan menene?yace a'ah nace kadunga dagewa da addu'o I.
Jumaimah insha Allah tashi kije kiyi shirin islamiyya,miqewa nayi tare da masa sallama nafita.
Nadawo islamiyya ban cidda mommah a falo ba don haka direct bedroom dinta na wuce.
Koda nashiga hangota nayi a kan gado tana lullube cikin blanket jikinta rawa yake,da sauri na cire hijjab din jikina tare da hawa kan gadon,yaye blanket din yayi jikinta rawa yake ga hawaye da yake tsiyayo mata,nima hawayen nafara tare da cewa,mommah na meyafaru?meyasa meki?cikin kuka nake mata wannan tambayoyin?
Bakinta rawa yake tanason magana but kuka yaci qarfinta,qarfin hali tayi tace jumaimah dauki phone dina kikiramun Auntyki safiyya(wato adda safiyya qanwar Abba na).
Cikin sauri nasauka daga kan gadon na dauko wayarta nayi dealing number,bayan tadauka ne tayi sallama tareda cewa,aminiyar arziqi kinganni wallahi yanzu nake tunanin kiranki.
Cikin muryar kuka nace,Adda ba mommah bane jumaimah CE,da sauri tace,subhanallah jumaimah meke faruwa ne.
Adda kiyi sauri kizo mommah ce babu lafiya,tace nakiramata ke.
Bata jira abinda zance ba taqatse kiran.
Minti ashirin tsakani saiga Adda safiyya tashigo cikin sauri tare da hawa kan gadon tace,aminiyata meyasameki?meke faruwa? Tayi tambayar tare da Dora kan mommah a cinyarta.
Daqyar mommah tabude baki tace,aminiya menayiwa Abban jumaimah ne yatsaneni haka?mena masa ne bayasona nida jumaimah?
Adda safiyya tace,dama kunsamu sabani ne kedashi?
Adda safiyya tace,kiyi magana ba shiruba.
Mommah taba Adda safiyya labarin abinda ke faruwa Tass,harda na aunty rabi.
Adda safiyya tace,basaida nafada mikiba nace wannan yar aikin taki bata arziqi nace,amma kina qeqashe qasa kikace wai ban fahimceta bane,to aigashinan wayasanima itace keshiga tsakaninku?
Mommah tace,a'ah aminiya zato dai zunubi kidena pls.
Adda safiyya tace,to kinji halinnaki ba,yanzu ace duk abinda tamiki bai isa yasa ki fahimci komaiba? Mommah tace,ba haka bane Allah.
To yanzu meyasa meki hard a yasamiki fever?
Atake anan tasake fashewa da kuka tace,aminiya waini abban jumaimah zaimun kishiya!ni?
Ba Adda safiyya ba hattani dabansan kushiya ba saida gabana yafadi babu abinda nake fadi sai _INNA LILLAHI WA INNA INNA ILAIHir-RAJI'UN_
Adda safiyya kuwa tsalle tayi gefe guda tare da qurama mommah na ido,tace lallai na miji, na miji hankaka gabansa baqi bayansa fari, na miji riqar qaya.
Lallai maza gsky yaya baiwa Kansas adalciba,nikam bansan mezance mikina da ya wuce don Allah kiya haquri don Allah,domin nasanki da haquri bani kadaiba duk Wanda zama yaha daku dashi,nasan da damuwa but don Allah kikwantar da hankalinki kada kisa damuwa a ranki don Allah.
Abinda nakeso dake,kada kinuna masa kinshiga damuwa,biyayya kuwa qiqara damtse wallahi Allah sai yayimiki sakayya,ki rabu da na miji, na miji tsinanne ne,kiyahaquri don Allah.
Adda safiyya bats bar gidan ba saida ta tabbatar da mommah na tasamu natsuwa,sannan tamata sallama tatafi.
Washegari Baba Alhj (Mahaifin Abba na)ya Aiko mommah tazo yana son ganinta.
*Readers godiya nake da comment dinku Allah yabar qauna*β€β€β€
_Ur lovely Xahran kuce pans_βπΌβπΌβπΌ
[4/24, 8:09 PM] Zarah Bae: π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯π₯
*INTELLECTUπ
°οΈL WRITERS ASSOCIATION*
*_(Home of experts and talented writers, kawo gyara da cigaba ga al'uma shine fatanmu)_*
*I.W.A*
_LABARI/RUBIUTAWA_
*PATEEMA XAHRA LAWAL*
*Bismillahir-rahmanir-raheem*
π
Ώ:11-12
Washegari bayan mungama breakfast da wuri muka shirya driver yadaukemu sai gidan baba Alhj.
Bayan munji gidan angama gagaisawa da kowa cike da farin ciki da kewar juna,muntarar da Adda safiyya da abbana.
A falon baba Alhj duk aka hallara but bndani aciki,bayan anbude taro da addu'ah ne baba Alhj yafara magana kaman haka.
Maryam 'yata,mommah tace na'am baba,yace magana nakeso muyi dake na fahimta,kina saurarona?mommah tace,Eh baba inajinka.
Da farko dai zance kiyahaquri kikuma yimana aikin gafara,habeeb yazomin da maganar aure cewa zai sakemiki abokiyar zama ina fatan ya sanar dake.
Jikin mommah yana rawa,muryanta na cracking tace, Eh baba yasanarmun.Su dai su yakumbo da hajy babba duk jikinsu yayi sanyi,baba Alhj yace,mezakice ne 'yata?
Mommah tace babu komai baba Allah yasa hakan shiyafi alkhairi,duk falon aka amsa da ameen kowa yace,Allah yasa hakan shiyafi alkhairi.
Hajy babba tace,ni kam banida abinda zance tunda na lura idonshi ya rufe, saidai yakumbo gatanan.
Yakumbo tace,ni banida tacewa saidai nace Allah yasanya alkhairi Yakuma bashi ikon yin adalci atsakaninsu,saidai bamusan inda zayyi aurenba ko zaka iya sanarmana? Yakumbo tayi maganar tareda duban Abba na.
Shidai Abba na kanshi a duqe yakasa magana,baba Alhj yace magana ake munajinka.
Abba na yasosa qeya tare da cewa,Eh to Alhj dama Rabi CE zan aura,baba Alhj yace itakuma yar inace?
Abba na yace,ba kowa bace, sai rabi mai aikin maryam!duk cikansu cikin furgici sukace Eyyeeeh!
Ita kuwa mommah a take anan tafashe da wani irin kuka mai cin rai.
Yakumbo tace,wallahi baka isa ba habeeb,karasa wacce zaka aura sai rabi don cin mutumcin maryam da tozarci?
Hjy babba tace lallai habeeb kabani kunya,wallahi tallahi kaji haushi.
Yakumbo tace,Alhj kanajinshi koh?kanajin duk maganganun banzan da yake fada koh?
Baba Alhj yace, dauki wayarka kakiramun Alhj Hakeem(Alhj Hakeem wan Abba na ne,uwansu daya but uba kowa danashi,dayake yakumbo a bazawara baba Alhj ya aureta,mijinta na far ko rasuwa yayi).
Bayan Alhj Hakeem yazo ne,baba Alhj yace Abba na yamaimaita abun daya fada,atake anan Abba na ya sake zayyano komai.
A firgice Adda Safiyya take,cikin kaduwa ta miqe tace,haba yaya wannan wane irin kwamacala CE kake qoqarin hadawa? Wanne irin gamin gambiza zaka hada a gidan ka?don Allah kada ka auri rabi don idan kayi haka ka cutar da maryam matuqa,bakayi mata adalciba.
Waima me aminiyata tarageka da shine yaya?matarka maisonka maison yan uwanka,tare da yimusu ladabi da biyayya?ta dauki iyayenmu tamkar NATA,kuma ka rasa wacce zaka aura sai 'yar aikinta?
Alhj Hakeem tayi gyaran murya tare da cewa safiyya ya isa haka nemi waje kizauna.
Ya dubi Abba na yace,wannan dai aure dazakayi bai haramtaba,kuma bai sabawa shari'ah ba,saidai me?
Alhj habeeb kaiba yaro bane,kuma kasan bakaima mataraka adalciba,kai shedane matarka matarka yace ta qwarai mai haquri,yar idan mutumci da dattaku pls kayi nazari.
Mommah na da Adda safiyya banda kuma babu abinda sukeyi anrasa mai lallashin wani.
Baba Alhj yayi gyaran murya yace to habeeb kadaiji abinda yan uwanka suka ce,me kake gani?
Jumaima tana kuka ta dubi hajja tace,hajja dangin Abba na sunason mommah na saboda kyawawan dabi'unta,tabbas Abba na baiwa mommah adalciba da zaimata kishiya da aunty rabi.
Abbiey yadubi jumaima yace,jumaima 'yata labarinki da dadin saurare,don haka inaso kimun wani alfarma daya,kibari gobe kya qarisa.
Hajja tace,saboda mene?kaida sai bayan isha kake dawowa daga wajen aikin,sannan labari yadauki dadi kace atsaya?A'ah aiba dole bane kaji.
Abbiey yace kiyahaquri hajja kinmanta gobe week end ne babu wajen aiki?da wuri zanzo soon.
Hajja tace,to aini namanta ne but giben da yaushe zakazo?
Abbiey yace,sha daya na safe insha Allah.
Hajja tace, to shikenan Allah yakaimu.
Nandai sukai sallama su fareeda suka masa saida safe,don sunce sundawo kwana gidan hajja don sunyi qanwa.
*******
*_KANO_*
Gabadaya mommah a rude take banda kuka babu abinda takeyi,ta zauna tadashe tayi fari Tass,tamkar babu jini a jikinta,damuwa yataru yamata yasa.
Adda safiyya CE tazo tana bata labarin yanda Abba Yakoma,yakuma rikice akansu.
Adda safiyya tace,dam a basaida nafada mikiba nace duk wannan abinda yake bayin kansa bane.
Mommah ta share hawayen fuskarta