Showing 18001 words to 21000 words out of 26141 words

Chapter 7 - ADALILIN 'YAR TSUNTUWA Complete Hausa Novel

06 Oct 2024

1616

dai ita ba fara ba.
Ankawo musu abinci da lemo kala-kala,Saidai basuci ko dayaba,Sbd a qoshe suke.
Jumaima cema da Aunty Fareeda suka sha Kunun Aya don yabasu sha'awa,shiko junior gwngwani lemo 7up ya dauka yasha.
Qarfe hudu za'a wuce da Amarya Abuja.
Wajejen 3:45 Aunty Fareeda takira Sabeetu direba a waya.
Saidai bazesamu zuwa ba,don yanzu Suke hanyar zuwa gyallesu shida Ummiey wajen mahaifiyarta.
Kamar a mafarki Aunty Fareeda ta hango abokin Ya Shuraaim,Wanda suke cema Ya saleem,Shima hangosu yayi Cikin sauri yaqariso.
Da gudu junior yaqariso tare da fadawa jikinsa"yace Ouncle!
Ya Saleem"yace my boi,kananan?
Eh Ouncle.
Ya Daddynka kana waya dashi?
Daga masa Kai yayi"Yace Eh Ouncle.
Aunty Fareeda da Jumaima ne suka gaisheshi,duban Aunty Fareeda yayi"yace kema gidan bikinnan kukazo?
Fareeda"Tace Eh.

Satan kallon Jumaima yayi,tare da yaba irin kyan da Allah yamata.
Ok muje na rage muku hanya Koh?
Aunty Fareeda"Tace yawwa Ya Saleem kamar kuwa kasan yanzu muka gama waya da driver yace sunfita da Ummiey.
Ayya!yafada tare da riqe hannun junior "yace mutafi.
Binsa a baya sukayi,bude musu murfin motan yayi suka shiga,shida junior a gaba.
Aunty Fareeda"Tace Ya saleem gidanfa Hajja zaka kaimu Saboda su Jumaima.
Juyowa yayi ya dubeta"yace wannan wacece maikama da Shuraaim Fareeda? Saidai don Shuraaim fari ne.
Aunty Fareeda tayi dariya"Tace qanwar muce,cousin sis namu.
Okk!yafada.

********
*_MARADI_*
A maradi kuwa su mommah sunsa an duqufa da addu'ah kan Allah yadawo mata da hankalin mijinta gareta,sannan Allah ya bayyana mata tilon 'yarta.
Suna zaune a gidan Goggoji ne,ita qanwar mahaifin Mommah ne,tana Aure da Sarkin Maradi.
Zaune Suke akan carpet anata Hira, Goggoji ta dubi Granny "Tace Ammi (kamar yanda suka San 'yarta nacemata,Suma Haka suke cemata ).
Yaya baitaba fada Miki kafin ke yataba Aure ba?
Granny"Tace Aure Kuma?
A'ah baitaba fadamunba.
Goggoji "Tace yataba Auren wata 'yar bauchi bafullatana,Suka zauna a Zaria,gashi mu bamusan gidan iyayenta A Bauchi ba,A Zaria ma bamusan inda Suka zauna ba.
Saidai tunda yadawo Maradi ya sanar Mana da tasamu ciki baisake tunawa dasu ba a rayuwarsa gabadaya akashafe masa tunanin su,Munyi qoqarin ya tuna Saidai abun yaci tura don da zaran yatuna to ranar yini zaiyi bai cikin hankalinsa.
Granny da Mommah hankalinsa yatashi qwarai.
Mommah"Tace Goggoji yanzu bakida wani masaniya akansu.
Goggoji ta goge qwallar da ya tarumata"Tace kayya banidashi kokadan don besanar Mana ba.
Kuka Momnah tafashe da shi"Tace gashi ya koma ga Allah batare da yasake saninsu ba,Suma Haka.
Granny "Tace duk inda suke Allah ya bayyana manasu.
Ameen! dukkansu suka fada.

******
_ZARIA_
A kwana a tashi dai babu wuya yau gashi Saura 1month bikin Auntyn Fadeela.
Ankawo kayan lefen Aunty Fadeela don su Fam din gidan Alhj Sule Mai Naira haka Sukeyi.
Gidan mahaifinta Gaskiya layout aka Kai kayan, Akwatuna ne dozin biyu,Sai key na mota da kujeran hajji.
Allahu Akhbar Ummiey abun nema yasamu ace dai yaranta na Auren masu Naira.
🤔Saidai abunda yabani mamaki kamar dai Family din Alh Mai Naira Aka ambata?Me hakan ke nufi ? Kodai Shine Yayan Alh Tukur Mai Naira?
Qani a wajen Alhj Sulieman Mai Naira?
Kenan da alaqa dasu da Adda Safiyya?

_Naqara tsayin page,inaso Naga yawan comments naku,da sharhi._
_Like._
_Share,_

Ur Lovely Xahran kuce pan's✍🏼✍🏼✍🏼
💖❤️💓
💞❣️
💕
Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi 🗡️
[4/24, 8:14 PM] Zarah Bae: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥

*TAMBARI WRITERS ASSOCIATION*

🔱(( *_Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah_*))

*T. W. A*

_LABARI/RUBUTAWA_
*_PATEEMA XAHRA LAWAL_*

*Bismillahir-rahmanir-raheem*

🅿️:31-32

________A Cikin masu kawo kayan lefe Harda Adda Safiyya,Saboda Dan wan mijinta Aunty Fadeela zata Aura.
Yanda suka kawo kayan Arziqi Haka Suma suka koma da kayan Arziqi.
Ko a lokacin Ummiey sunsaba da Adda Safiyya sosai.
Cike da mutumtawa Sukayi ma Juna sallama,'Yan bauchi Suka koma gida.

Ankon Aunty Fadeela kuwa Order dinshi akayi tundaga waje,wani lace ne me mugun kyau da tsada,guda Ashirin da hudu Akayi Order,duk da Wanda Amarya Zata saka nata daban 25.


Jumaima Cike da farin ciki take,saboda Hajja sunyi waya da Ya Shuraaim"yace daqyar inzaizo bikin.
Tasan babu Wanda zai takura mata zatayi abinda takeso,zatayi qara'i sosai.

Duk kayan da'akayi order na ankon dinner ne,Kuma mutane Ashirin akeso rakk!Su saka ishirin kowani kwali ka bude Dan dai-dai da material lace din Kuma kowanne da sunan wacce za'abawa,don kyauta za'ayima qawayen.
Kala Ashirin dinnan duk iri daya ne, Colour hudu Kuma daban ,Saina Amarya nata colour daban.
Koda Akakawo sun rabawa Kowa,ragowar na hannunsu sunkaima telan da zaimusu harda na Amarya.


*********
*_BAUCHI_*
A bauchi duk da shirye shiryen bikin da su Adda Safiyya suke baidameta ba,don yanzu saura 2weeks.
Kullum cikin gwada layin mommah take Bata samunta,yauma wayarce a hannunta tana sake try,kamar a mafarki taji wayar tashiga miqewa tsaye tayi ba'ajimaba akadauka tare da sallama.
Aminiyata! Kalmar da Adda Safiyya tafada kenan,tarasa wani irin farin ciki zatayi,kawai saita fashe da kuka.
Hankalin mommah yatashi tacan bangaren gefe guda Kuma gajin muryan aminiyarta da tayi.
Mommah "Tace Aminiyata kece?
Adda Safiyya"tace ni CE,wallahi banta6a zaton idan nakira ki zansameki ba,saboda gaba daya layikanki basu shiga.
Mommah"Tace Ayya!! Ai ansace wayar ne da mukaji MARADI biki.
Allah Sarki nazo ai bakyanan daqyar nasamo number naki na MARADIN a wajen wata maqociyarku.

Eh wajen talatu kenan,domin ita kadai keda number na,wayyo Aminiyata Kiya haquri.
Adda Safiyya"Tace kada kidamu zandawo insha Allah.
Mommah"Tace A'ah ai wannan karan,wannan tafiyar da za'ayi nawa ne,ni CE yakamata da nazo.
Dagaske?tambayarda Adda Safiyya tayima mommah kenan.
Mommah"Tace Allah nizanzo da kaina.
Kinga kuwa yau bikin Dan wajen Hjy salamatu,Ahmad zaiyi Aure.
Mommah"Tace Allah Sarki mijin Jumaima kenan zaiyi Aure?
Dariya sukayi gabadaya,saboda Ahmad tun Jumaima na qarama yake cewa shizai aureta.
Mommah"Tace Gaskiya nikafin bikin zanzo don inaso na koma da wuri,Kinga next week kenan?
Insha Allahu ina kan hanya.Ya Kowa da Kowa?Yasu yakumbo da baba Alhj?
Adda Safiyya"Tace duk suna lafiya,tare da kewarki.
Mommah"tace kibasu haquri Kuma kice musu ina kan hanya.
Adda Safiyya"Tace to shikenan but naji baking tambayi mijinki ba.....
Bata qarishe maganar ba mommah da katse wayar.
Koda Adda Safiyya tasake gwada Kira Switch off taji,alamun ta kashe wayar gaba daya.
Adda Safiyya"Tace Oh ni Safiyya da Aminiyata Bata da fushi but yanzu ta koya,Koda yake hausawa na cewa kaguji fushin me haquri hakane.

Jikin Abba yayi sauqi sosai,yanzu Haka zaune yake da mahaifinsa da wanshi Alhj Hakeem.
Ya kumbo "Tace sannu habeebu ya jikin naka?
Alhamdulillah ya fada tare da dubansu "yace don Allah duk lepin da nayi muku kuyafemun,bansan lepin da na mukuba wallah Allah,yayi maganar cikin fuskar tausayi.
Baba Alhj yadubeshi yayi gyaran murya tare da Cewa"Habeeb aikasan matarka da 'Yarka Jumaima Koh?
Karkada Kai Abba yayi alamun A'ah.
Baba Alhj dama ni inada mata CE data wuce Hjy Rabi?
Baba Alhj yace"qwaraima kuwa.
Nikam Banda wata mata da 'ya Kuma banshirya daukansu a wannan matsayin ba.
Cikin muryan kuka Hjy babba ta dubeshi "Tace Habeeb yanzu kamance da Maryam Dinka?
Tsayawa yayi tamkar zaiyi tunani,tuni yaji kanshi yayi mugun sarawa! Cikin sauri"yace bansansuba.
Shiru duk sukayi Kowa da abinda yake saqawa a ransa,domin duk sunyarda Akwai asiri a cikin lamarin.
Alhj Hakeem "yace yanzu bakada komai duk matarka ta kwashe.
Yakumbo"Tace Haka zaka qyaleta? To bazaiyuwu ba dole ka sawwaqe mata.
Cikin sauri yadago tare da duban yakumbo.
Hjy babba Tace qwarai kuwa dole ne kasaketa.
Wallahi tallahi bazan iya rabuwa da Rabi ba,tariga tazama jinin jikina wallahi kuyafeni.
Baba Alhj ne yayiwa Alhj Hakeem mgn da ido alamun sutashi sufita.
Miqewa sukayi atare,Baba Alhj ya dogara sandarsa ta qarfe Mai mugun kyau da tsada.

Koda suka fita duban Baba Alhj Hakeem yayi "yace Alhj tabbas Habeeb Akwai Sammu a jikinsa.
Baba Alhj "yace Sammu ne sosai a jikin sa,insha Allahu komai zai daidaita.
Kiran sallah akafara a masallacin da Baba Alhj yasa aka Gina dake jikin gidanshi.
Abin mamaki Abba ne yafito daga daki,alamun yayi alwala,baice dasu komaiba yaraba ta gefensu yawuce.
Rabon da Abba yaje masallacin su, anasu tunanin tunkafin yafara Ciwon nan.
Godiya suka fara yiwa Allah subhanahu wata'ala,cike da farin ciki Baba Alhj ke furta kalmar Alhamdulillah.

_Bayan Sati Daya_

A bangaren gidan Alhj Sulieman Mai Naira anata shiryen shiryen biki.
Mommah ne ta kira Adda Safiyya take fada mata tana hanyar zuwa bauchi.
Cikin farin ciki Adda Safiyya ta sanar da maigidanta, Shima yayi murna sosai.

******
_ZARIA_

Suma shiryen shiryen biki suke,'Yan uwan Hajja na bauchi mutane shida suk sunzo,mata hudu Maza biyu.

Wajejen 4:30 na yamma,wayar Jumaima CE tafara ringing,Koda ta duba Ya Shuraaim ne da number nasa na 9ja,don duka yasamata a wayanta.
Dauka tayi tare da Sallama cikin Sexy voice nasa me tafiya da zuciyar duk wani maisauraro,ya amsa sallamar nata.
Gaisheshi Jumaima tayi,cikin cool voice.
Kikaima Hajja wayar idan tana kusa,tayi mamaki sosai.
Don tasan halinshi duk idan yakira dansa yake fara tambaya.
Yanzu Kuma yace taba Hajja,ga muryansa so silent yau sosai kamar ba Ya Shuraaim ba.
Kaima Hajja wayar tayi.

A Koda yaushe Jumaima na mugun tausayawa kanta idan ta tuna tana son maso wanine qoshin wahala,domin tun ranar da taga Pix din Ya Shuraaim a kan screen din wayar Aunty Fadeela yatafi da zuciyar ta.
Ta rantse son Ya Shuraaim takeyi ,don akanshi tasan menene so,tana qoqarin dannewa a matsayinta na 'ya mace.
Tana Kuma mugun tausaya ma kanta,idan ta tuna bazaita6a soyayya da ita ba.
Kuka ne ya kufce mata,shigewa toilet din dakinta tayi ta rufe tadunga kukanta babu Mai rarrashinta.

Kamar daga sama taji muryar Hajja na qwalamata Kira,cikin sauri ta wanke face nata ta fito .
Hajja ta dubeta"Tace shiryawa zakiyi yanzu isah Mai kaiki islamiya direban yayanki zaizo yadaukeki yakai ki Gidan yayannaki don baida lafiya,Kuma jiya yadawo da daddare,baiso asan yazo ne.
Saiyaga yananyin jikinnasa komai baici ,ba,kije ki gyara gidan kimasa girki kinji?
Qirjin Jumaima Banda lugude babu abinda yake"Tace to Hajja.

Hajja"Tace idan Zaki tafi ,to kitafi da jiniya ne inba Haka ba yazo baiganki ba saiya tadawa Kowa da hankali,sannan sip dinki kisama mukulli ki rufe don kinsan gidan yanzu zaifara cika da jama'a.
Jumaima"Tace to.

Wayarta ne yayi ringing Koda taduba sunan Isah driver tagani,long hijjab dinta ta dauka tare da wayarta ta fita.
A farfajiyar gidan taga junior Yana wasa da ball,komawa ciki tayi dashi ta canza masa kaya sannan suka fito suka shiga mota.

Sun Isa G.R.A biyar daidai na yamma,saukesu Isah yayi abakin gate yajuya.
Junior"yace Lah!! Aunty gidanmu muka dawo?da gudu ya shiga cikin gidan,duk inda yabi Jumaima Nan takebi,domin batasan kan gidan ba, gidan ya hadu saikace a turai.

Daidai bakin qofar shiga Falon suka tsaya,turawa sukayi Suka shiga,tare d sallama.
Babu Kowa a falon,wani steps junior yabi,Jumaima ma tabishi,wani corridor sukabi saigasu a wani Falon,still wani corridor din suka sake bai saiga dakunan bacci uku.
Kamar daga sama Jumaima tadungajin ana sheqa amai a daidai qofar dakin da take tsaye.
Cikin sauri ta murda handle din qofar ta shiga.
A firgice ta Kurma ihu da qarfi ta furta Ya Shuraaim!!!!!!


~Comments,likes,Sharhi and share.~
Banason tnx ko stickers ku riqe abinku NAGODE,

Ur Lovely Xahran kuce✍🏼✍🏼✍🏼
💞💖💓
❤️💕
❣️
Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi 🗡️


[4/24, 5:32 PM] Zarah Bae: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥

*TAMBARI WRITERS ASSOCIATION*

🔱(( *_Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah_*))

*T. W. A*

_LABARI/RUBUTAWA_
*_PATEEMA XAHRA LAWAL_*

_This page is dedicated to all_ *_XAHRA'S NOVEL'S_*, _I luv yhu my members,tnx so much for your comments_

*Bismillahir-rahmanir-raheem*

🅿️:33-34

____Cikin Sauri tashiga bedroom ciddashi tayi yanata amai gabadaya ya galabaita da qyar yake fidda numfashi.
Da sauri taqarisa gareshi ta tallabeshi cikin Kuka"tace Ya Shuraaim meyasa Meka?
Yakasa mata magana.
Ya Shuraaim katashi muje asibiti pls.
Karkadamata Kai yayi.
"Tace A'ah Ya Shuraaim don Allah kamiqe muje asibiti.
Junior"Daddy pls wake up,Murmushi Ya Shuraaim yayi tare da rungume dannashi yace
"Ayya my boi lafiyata Lou.
Dubanshi Jumaima tayi"Tace Ya Shuraaim meyasameka?
Murmushi yayi mata"yace Jumaima ya ambata.
Dagowa tayi tadubeshi"Tace na'am.
Beyi magana ba saidai yaqura mata Ido.
Gyaran murya Ya Shuraaim"yace Jumaima yunwa nakeji pls.
Dubanshi tasake yi"Tace mekakeson ci ne?
Anything for yhu dear.
Meqewa tayi "Tace ina ne kitchen din.
Oyya boi miqe karaka Aunty kitchen Koh?
Miqewa Jumaima tayi tare da bin bayan junior.
Har tafita idon Ya Shuraaim nakanta.

Koda suka shiga kitchen din dube dube tafara,can tahango wani qofa daga Dan nesa qarema kopan kallo tayi domin duk kyan gidan abbanta idan taga abubuwa anan saitaga na gidansu ba komai bane.
Hanyar qofar tayi tare da budewa tashiga haske ne kadan,daga idon da zatayi ta hango makunni,don Haka ta kunna glob din,wani irin haske medaukar hankali taga wajen yayi,kayan abinci ne sosai a wajen sakin baki tayi tana kallo.
A ranta Tace duk da beda matar ma saiya bar kayan abinci?
Junior Takirashi ! A tunanin a Yana kitchen dinne saitaji shiru.
Arish ta debo tare da kayn Miya daga tattasai Sai albasa sa galan din man gyada.
Shap shap ta fere arish din tasoya kayan miyan Dan kadan tattasai da albasa tayi greating nasu .
Koda tagama soya arish din zubawa tayi a wani wammer Dan dai dai.
Miyan qwai tayi Wanda bazakace miyar qwai bane don qwan da yaji,a taqaice dai chips tahada masa da miyar qwai.
Plantains Shima ta fere ta soya.
Junior ne ya shigo kitchen din da gudu"yace Aunty! Aunty!!kizo Abba na.
Allah yasa ta kashe gass din.
Atare suka hau steps din,Koda taje cikin blancket ta hangoshi yana rawar sanyi .
Hawa gadon tayi tare da yaye blancket din,jikinshi yayi zafi sosai,ga mouth nashi da yake ta rawa.
Matsowa tayi kusa dashi....
Muryansa na rawa"yace ki..kkki...ll...lube...n..nni,S....ssan...nnn....yiii.
Kuka Jumaima tafashe dashi tare da fadawa jikinsa,cikin muryan kuka"Tace Ya Shuraaim pls kabari na kirasu Hajja.
Kada mata Kai yayi alamun A'ah.
Rasa mezatayi masa tayi.....dibara ne yafado mata ta tuna lokacin da idan tana zazA6I abinda mommah keyimata.
Miqewa tayi taje kitchen ta Dora ruwa a gass shap shap ta juyo a wani bowl.
Shiga dakin tayi still Yana Jin jiki.
Shiga toilet dinsa tayi Bata ga towel ba,saidai ta hango want drower,budewa tayi taga towels a ciki,dauko daya tayi tadawo wajensa.
Hawa gadon tayi,shidai junior Sai kallonsu yake.
A hankali ta yaye blancket din,dama singilet ne a jikinsa da short necker.
Fara goge masa jikinsa tayi da towel din,a hankali yafara sauke a jiyar zuciya,jigabawa tayi da goge masa jikin,rawar
h nashi keyi yadena.

Ahankali yafara sakin zufa sosai,can Kuma Sai bacci t
Yasa CE shi.
Aunty Daddy na yayi bacci ne?
Dagamasa Kai tayi tare
Sa hannu abakinta"Tace shiiiiiiii!

Wayarta ne yafara ringing taduba taga Aunty Fadeela ne,sauka tayi akan gadon tare da riqe hannun Shuraaim suka fito Falon saman.
Picking call din tayi tare da sallama.
Jumaima ina kike ne?
Dirin dirin tafara don Hajja tacemata yace baiso asan yadawo....Am Aunty bananan ne Hajja ta aikeni ne.
Ok to shikenan in kindawo mazo gidan.
To Aunty.

Tashi tayi tashiga kitchen din tare da dauko
wammers din,tamiqawa junior qaramin,suka hau sama.

*********
*_BAUCHI_*

Qarfe takwas na dare mommah ta Isa bauchi.
Adda Safiyya jitake kamar ta goyata, lokaci daya akayi mata wani irin tarba Mai kyau anrasa ina za'a ajeta.

Nan Adda Safiyya takaita masaukinta,aka hada mata ruwan wanka,bayan tadawo wanka ne takimtsa tasaka jallabiyya baqi da farin hijjab,tayi kyau sosai tamkar 'yar 25.

Adda Safiyya tashigo fuskanta dauke da Murmushi"Tace harkin gama kimtsawa?
Mommah"Tace Ea Aminiyata.
To muje kici abinci ko akawo Miki Nan ne?
Mommah"Tace A'ah saikace nazama baquwa muje.


Bayan taci abinci ne tayi qattt! Suka zauna a kadasa firar yaushe rabo.
Shigowa dakin akayi tare da sallama...........

_I need your comments and Sharhi pan's_

Ur lovely Xahran kuce✍🏼✍🏼✍🏼
❤️💖💓
💞❣️
💕
Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi 🗡️
[4/24, 5:33 PM] Zarah Bae: 🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥🍥

*TAMBARI WRITERS ASSOCIATION*

🔱(( *_Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah_*))

*T. W. A*

_LABARI/RUBUTAWA_
*_PATEEMA XAHRA LAWAL_*

*Bismillahir-rahmanir-raheem*

🅿️:35-36

_____Ahmad ne yashigo Falon Adda Safiyya.
Zama yayi a daya daga cikin kujerun Falon,tare da gaishe da su mommah.
Murmushi mommah tayi bayan ta amsa"Tace Ahmad Ashe zakayi aure ne? Kafasa auren Jumaima din CE?
Murmushi yayi tare da Sosa qeya"yace mommah Kuna lpy ?
"Tace lafiya Lou wallahi,a'ina kasamu matan ne?
A Zaria ne mommah wallahi.
Momnah "Tace to shikenan Allah ya Sanya alkhairin.
Ameen duk suka amsa ya miqe zaifita yadubi Adda Safiyya"yace Adda babu wani saqo daza'ayimuku ne?
A'ah Ahmad babu wallahi,daga ina ka kene halan?
"Yace daga gida nake naji labarin zuwan mommah ne,shine nace bari nazo mugaisa.
Mommah tayi dariya"Tace nagode Ahmad,ka gaishemun da Hjy salamatu.
Ya amsa da insha Allah,ya musu Saida safe ya tafi.


Momma ta dubi Adda Safiyya"Tace Aminiyata ya maganar Jumaima ne?
Sun kuyar da fuska Adda Safiyya tayi"Tace bansan da wata irin kalmar zan dubeki ba Aminiyata,inajin nauyin na bude baki nace Miki har yanzu ba'aga Jumaima.
Murmushin yaqe mommah tayi"Tace shikenan,idan tanada rai Allah

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login