Showing 21001 words to 24000 words out of 26141 words
Chapter 8 - ADALILIN 'YAR TSUNTUWA Complete Hausa Novel
ya bayyana ta,idan Kuma ta rasu Allah yayi mata Rahama.
Adda Safiyya"Tace haba Aminiyata insha Allahu Jumaima nada rai,Kuma tana cikin qoshin lafiya da kwanciyar hankali.
Anan take sanar da ita labarin Abba da abinda yasameshi.
Mommah ta tausaya Mai sosai"Tace Allah yabani iko gobe naje na gaisheshi,but meye amfanin zuwa ma wajen Wanda ya manta da kai,?da tilon 'yarsa?
Adda Safiyya"Tace Ayya Aminiyata! Inace keda kanki anan kikemun fadan rashin yafiya?kikecemun ba'asaka mugunta da mugunta?
Momma"Tace hakane.
Adda Safiyya"tace Kiya haquri don Allah nasan abinda zafi sosai,Kuma kodan darajar su yakumbo ai Zaki.
Shikenan Allah ya kaimu,Mommah ta fada.
Ehemm Aminiyata kokefa.
Mommah tadubeta"ya su Zee Xee da Xaeyysherth ne?
Suna can gidajansu,sun ce sai ana jibi biki zasu.
Kinga banma fada Miki ansa Rana 6 month ba.
Mommah"Tace nawa ne Kuma?
Adda Safiyya"tace na Ameera.
Mommah"Tace Kai!Ameera dai Ameera? Inace Jumaima ta girmeta?
Adda Safiyya"Tace Eh Jumaima tabata 1year.
Koda bazanyi mmki ba,na manta Alhj Tukur da wuri yake aurar da yaran.
Adda Safiyya"Tace aikam,kinganta tanacan ta tare a gidan biki tare da su sumayya.
Mommah"Tace to Allah ya nuna Mana,yasa albarka.
Ameen! Adda Safiyya tafada.
Saida Suka raba dare suna fira sosai.
*******
_ZARIA_
Koda suka shiga dakin Sun ciddashi still Yana bacci hankalinsa kwance,Face dinshi Jumaima tatsaya tana ta kallo.
Kamar daga Sama taga Ya Shuraaim yabude ido,diri-ricewa Jumaima tayi.
Yatsine face nashi yayi tare da dalla mata harara"yace meye Kuma na kallon haka?
Duqar da kanta tayi cikin sauri tare da Jin haushin kanta.
"Hey gurl fitamun a daki,inaso na kimtsa.
Dagowa tayi ta dubeshi,tamkar bashi yayi maganar ba.
Juyawa tayi tafita,jikinta yayi sanyi sosai.
Bin bayanta yayi da kallo ya furta"Ya Salam! Wannan yarinyar tana gab da firgita ni.
Miqewa yayi tare da shiga toilet.
Koda taje falo tarar da junior tayi yafito kitchen hannunsa riqe da plate da saving spoon.
Dubanta yayi yace"Aunty Jumaima yunwa nakeji abinci.
Qarisowa tayi ta'amsa plate din"Tace junior ba dole kaji yunwa ba,tunda nayi nayi kaci abinci kaqi ci.
Qaran ta kalmi sukaji daga steps,alamun ana Saukowa...... Wow yayi kyau sosai wani yadi ne a jikinsa Sky blue,dinkin Muhammad,Mai iyaka gwiwwa,,hannun ma iya kacin Rabin damtsen hannu.
Sajensa da gashin kansa sukwanta lufff tare da baqi sidik.
Dagowa Jumaima tayi tadubeshi,kauda Kai tayi gefe daya.
Zubama junior chips din tayi Sai plantain a gefe ta dorashi akan kujerar dining din.
Bude firij tayi tadauko masa Bobo guda daya Sai faro.
Ya Shuraaim ne yaqariso tare da Jan kujera yazauna,juyawa Jumaima tayi zata tafi"yace Aunty Jumaima nifa?yayi maganar tare da langabar da wuya like junior.
Dariya yabata,taso tayi but saita dake.
Qyalqyalewa da dariya junior yayi"yace Daddy yakoma boi.
Dariya Ya Shuraaim yayi tare da kallon Jumaiman"yace Eh Mana Auntyn naka Bata da niyyar Saving Daddy naka ne.
Ita dai Jumaima Bata CE komaiba tayi Saving nashi tare da turamai gabansa da fork.
Ehemm Aunty Jumaima fura da yoghourt nanan a firij pls kidamamun.
Toh tafada,tare da dauka,shiga kitchen tayi ta dama masa tass takawo Mai,tare da juya.
Oyya madam zoki zauna kici abinci,yayi mgnr face nashi babu alamun wasa kwatakwata,kamar ba shine ya gama wasa ba.
Ganin haka ne yasa Jumaima dawowa taja kujeran kusa da junior ta zauna tayi saving kanta.
A hankali tafara cin abinci,ta wutsiyar ido yadunga kallonta Yana ganin Dan qaramin mouth nata da yanda take motsasa.
Cize lips dinsa na qasa yayi tare da fara tsotsa kamar yasamu lollipop๐ญ
Kiran Sallan Isha'i akafara, Jumaima a ranta "Tace subhanallah banyi magrib ba,gashi har isha'i yagabato.
Ture plate din tayi,tamiqe.
Ya Shuraaim"yace ina Zaki?
Ya Shuraaim banyi Sallar magrib ba,gashi har anfara Kiran Issha'i.
Ok Nima banyi ba.
Bari muje masallaci,duban junior yayi"yace oya boi atashi muje ayi Sallah ko?
Ok Daddy,kalmar da junior yafada kenan.
Bayan Sunyi Sallah sundawo ne"yace su shirya su tafi yamaida su gida.
Cike da farin ciki Jumaima tashirya tsaff! Suka fito,Shima ya lura da hakan a tattare da ita.
Suna cikin mota ya kunna musu karatun Qur'ani na Alaramma Ahmad Sulieman,Yana karanta Suratul-Yusuof.
A hankali Ya Shuraaim yafara bi,tamkar ma yanaso Yafi Alaramman.
Cike da mamaki Jumaima ta dago tana dubanshi.
Hada ido sukayi,ta madubin motar,ya hade rai gabadaya. Tamkar bashiba.
Wayarsa CE tafara ringing din waqar *Fateema* Wanda Ali jita yayi,ana _dawo dawo Fateema dawoooo,yayyafin ruwa shiyake wanke zuciya_
Dauka yayi tare da sallama"yace Maza kana inane?
Ok qofar gidan Hajja?
To Nima ganinan a hanya yanzu.
Minti goma yakaisu qofar gidan,Su Aunty Fareeda Jumaima ta hango tare da Wanda yayi masu lift da biki.
Koda yayi parking,bude motan Jumaima tayi qoqarin yi,taga yaqi,cikin sauri tadago tare da duban Ya Shuraaim.
Baimasan tanayiba don daddana wayarsa yashigayi can yakara a kunne"Yace hello baee yakike?
Oh nima I miss yhu too,am sorry dazu banjin Dadi ne yasa ban kirakiba,sorry baeeee kinji.
Ok Sai anjima I will call yhu back
Jumaima jitayi wani abu ya tokare mata maqoshi,kwallah CE yayi qoqari zubo mata Cikin Sauri ta maidasu.
Basu Ankara ba sukaji ana knocking glass din motar .
Budemata Ya Shuraaim yayi tafita.
Saleem yadubeta"yace A'ah qanwarmu CE?
Jumaima tayi murmushin yaqe tare da gaisheshi.
Amsawa Saleem yayi cike da fari'ah.
Shikuwa Ya Shuraaim yacika yayi dammm,saboda yanda yaga Saleem nama Jumaima wani irin kallo,kardai ace sonta yake? Lallai Akwai qura,Ya Shuraaim yafada.
Ouncle! Junior yafada tare da qoqarin bude motar.
Saleem yace"A'ah my boi yakk?
Lafiya Lou Ouncle.
Leqowa ta glass din motar Saleem yayi"yace Maza ya'akayi ne?naga Kanata wani ciccin magani ne meya faru?
Hade rai Ya Shuraaim yayi"yace a'ina kenan?
Ok ba Wannan ba Maza,nifa qanwarnan taka nagani Kuma Gaskiya Eh tayimun.
Wani kallo Ya Shuraaim yawatsa masa,irin na re yhu mad?
Saleem yace"Maza yada kallo haka?
Ya Shuraaim"yace Anywhere Sai kaje kasameta kafada mata.
Ina ganin Haka zefi Koh?
Ahh Maza baza'ayi hakaba,yanda nakeda Kai aibanda matsala.
Ya Shuraaim "yace ai indai tanine to bazatayi aure yanzu ba๐ค
Shiru Ya saleem yayi tare da Cewa Ok kasan menene?
Ya Shuraaim shidai baitanka ba......Ya saleem"yace wallahi nahango Son yarinyar Nan da kishinta a idonka.
Harara Ya Shuraaim ya dokamasa..... Ya saleem yace"Koda take Banga lepinka ba,yarinyar tana da kyau baka ganta bama da sukaje biki ita da Fareeda.
Maza yarinyar ta wankune duk inda suka wuce idon guys yana kanta.
Jumaima din??? Ya Shuraaim yayi tambayar Cikin 6acin rai.
Balle murfin motar yai qoqarin fitowa,Sudai su Fareeda suna tsaye basusan waye ya Sauke Jumaima ba,don bada motarsa Suka sansaba,wata sabowa dall ya siya jiya.
Saleem ya dakatar dashi"yace Calm down Maza ka manta ga qannenka Can a waje,Kuma babu Wanda yasan kazo.
Shikenan kalmar da yafada kenan yaja motar sa yayi gaba.
Dariya Ya saleem yayi yace"Zakasha mamaki na wallahi.
*******
_BAUCHI_
Waje-wajen 9:00 Alhj Tukur yashigo Falon Adda Safiyya.
Ya ciddasu sungama breakfast sunata Hira ne,Murmushi yayi"yace habawa Hjy Maryam lefin me mukayi mikine Haka?
Dariya mommah tayi"Tace au bakuma San lefin kuba?to ai shikenan.
Zama yayi suka gaisa,sannan yaqara Bata haquri da baki akan taje wajen Abba don Allah,kada taduba abinda yayi.
Momma"Tace to shikenan nagode Alhj.
Babu komai,idan kunshirya Sai kuyimun magana muje tare Koh?
Adda Safiyya ta'amsa da toh!!!!
Wajen shadaya Saura suka Isa gidan Baba Alhj.
Su yakumbo da Hjy babba sunyi farin cikin ganin mommah sosai,Falon Baba Alhj suka nufa gabadaya,kamar daga sama sukaga anshigo dakin.
Hjy Rabi CE tashigo wajen mommah tayo gadan gadan,ganin hakane yasa duk mutanen Falon tsayawa kallonta.
Kitashi kifita matsiyaciya tsinanna,kinyima mijina asiri don yamutu,baimutu ba shine yanzu Kika shigo da wani qullin Nan?
Abba ne yafito tsohon part dinsa,Gaskiya yayi kyau sosai yafara dawowa Abbansa,da gayunsa da komai,saidai Dan abunda ba'arasa ba.
Shigowa Falon Baba Alhj yayi tare da Sallama,cikin sauri Hjy Rabi Tasha gabansa tana kada kaqarisa don Allah kajuya mutafi.
Cikin mamaki Kowa yake kallonta.
Adda Safiyya ne tayi qoqarin fadin"Yaya ga momman Jumaima.
Ture Hjy Rabi yayi takoma gefe daya,shikuma yashigo Falon.
Kallon Mommah yayi,idonsu kuwa ya Sargafe ana juna.
Kan Abba ne yafara mugun bugawa,tare da Sarawa.
Dai-dai yafara ganin mutane......wani qara yasaki tare da sulalewa qasa.
Duk cikansu hankalinsu atashe sukayo kansa.
Wani irin baqin kumfan abune kefitowa daga bakinsa,gaba daya 'yan wajen sakin kuka sukayi,Banda Baba Alhj da Alhj Tukur,da suke tsaye akansa.
Ihu Hjy Rabi tafasa"Tace shikenan takashemun miji tayimasa asiri.
Mommah da Adda
Safiyya Suma kukan suketayi.
Baba Alhj yadubi Alhj Tukur"yace yakamata mukira Liman malam Garba da Dan uwansa Hakeem,kaman bana asibiti bane Wannan lamarin.
Addu'o'i Baba Alhj yadunga kwarorowa Yana tofa ma dannasa(Allahu Akhbar Tsoho mairan qarfe,shekaranshi a qallah kusan tamanin da takwas,but idan kaganshi baiwani ji jiki ba,saidai abunda ba'arasa ba na jikin tsufa)
Koda Mallam Garba ya iso lokacin Shima Alhj Hakeem ya iso,don Alhj Tukur yamasa waya.
Mallam Garba na ganinsa"yace Sammu ne a tattare dashi.
Addu'o'i da ruquya akashiga kwararama Abba,a hankali yafara farfadowa bakinsa na furta _innalillahi wa Inna ilaihirraji'un,matata Maryam da yarinya na Jumaima don Allah kada kuyimusu komai na yarda wallahi na amince_
Ihu Hjy Rabi ta cigaba dayi,tana ta shiga uku shikenan tata taqare.
Addu'o'i akacigaba dayima Abba harya watstsake Sarai,bude idonsa yayi gaba daya tare da duban Kowa na dakin daya bayan daya,akan Rabi idonshi yasauka,cikin zafin nama yamiqe tare da Isa inda take.
Tasss!tasss!!tasss!!!tassss!!!! Saida ya saukemata maruka hudu kyawawa.
Ihu takuma tsandarawa"yace Ke nagani a cikin mafarkina ina Kika kaimun matata da 'yata?kiyi magana kokuma na illataki.
Kuka take sosai
Dauketa da wani Marin Abba yayi........
Habeeb ! Baba Alhj yakirasa cikin daga murya da bacin rai yace"Taya zakadunga dukan matarka haka?,koba matarka bama ai macece Koh?
Abba"yace matata Kuma Alhj ?Wannan abar CE matata?
Ina Maryama da Jumaima?
Cikin Kuka Adda Safiyya"Tace Yaya ga Aminiyata Nan.
Juyowa yayi garesu tare da nufar inda Mommah take,rungumeta yayi"yace Maryama ina Jumaima?ina mama na?
Kuka Mommah tasa but takasa magana.
Abin mamaki Wannan baqin kumfar da yafito bakin Abba yadunga hayaqi.
Ai duk cikansu firgita sukayi suka tsaya suna kallon ikon Allah .
Haka yadunga shiga jikin Hjy Rabi,itakuma Sai ihu ta ake,duk inda hayaqin Nan yata6a a jikinta,saikiga wajen yakwashe,ihu take fatan jikinta Yana Sa6ulewa.
Nandai ta sume garau.
Ranar gidan Alhj Baba sunga tashin hankali,Wanda basu tunani.
Daukar waya Abba yayi yakira tsohon driver din Jumaima Mai kaita School ada,Koda yazo haka aka kinkimi Hjy Rabi aka kaita asibiti,sukace yayi gaba kafin suzo.
Duk Wanda yaga Hjy Rabi bazaice ita ba CE,saboda yanda kamanninta Suka Sauya gaba daya.
Gyaran murya Baba Alhj yayi,yace"Lallai munga ishara da abun al'ajabi.
Mallam Garba ne yamusu Sallama,Alhj Tukur ya dauko kudi Wanda baisan yawansu ba a Aljihunsa yaiqa masa.
Ananne Alhj Hakeem ya umurce Adda Safiyya da tasanar da Abba abinda yafaru.
Bashi LABARI tayi tundaga A to Z babu abinda ta6oye har zuwa yanzu.
Kuka Abba yafashe dashi Yana"cewa kaicona ni Habeeb,yanzu ninayiwa iyalaina mafi soyuwa a gareni haka?
Dakaina na Kore 'yar cikina?ya tambayi kansa.
Adda Safiyya, Mommah, yakumbo,Hjy babba,Abba duk kuka Sukeyi sosai.
Matsowa Abba yayi kusa da Mommah yace"Maryama kiyafemun don Allah kinji mace tagari?
Mommah tashare hawayenta"Tace duk da ada na qullaceka but bashi yahanani kullum yimakq addu'ah ba,Akan Allah yakarkato da hankalinka garemu,ya Kuma bayyana mun 'yata.
Hjy babba"Tace Maryama keta dabance,Kuma zuciyarki tsarkakkiya CE,Sai dai muce Allah yayi Miki albarka.
Gabadaya Falon aka amsa da Ameen.
Wayar Alhj Hakeem ne yayi qara,Koda yaduba sunan driver din Abban Jumaima yagani,cikin sauri ya dauka.
Sallama yayi,daga can bangaren aka amasa,bayan an amsa ne,akace Alhj don Allah kuzo yanzu idan babu damuwa,Tace Akwai maganar da zata fada muku ne.
Alhj Hakeem yace"to gamunan zuwa. Tare da kashe wayar.
Sanarda su abunda ke faruwa.
Baba Alhj da Alhj Tukur,da Mommah sun amince,but sauran sunqi Saida aka danyimusu nasiha ne sannan suka amince.
Motoci biyu Sukayi, Mommah da Abba da Alhj Tukur da Adda Safiyya a mota guda,Sai Alhj Hakeem da baba Alhj dasu yakumbo a mota guda.
Suka nufi Asibitin.
_To Hjy Rabi ga qarshenki Nan,kinfara gani,kome Zaki fadamusu ohooo_
*Nagode masu comments da sharhi*๐
Kuma masu stickers ina godiya,Allah dai yabiya๐คฆ๐ฝโโ๏ธ๐คฆ๐ฝโโ๏ธ๐คฆ๐ฝโโ๏ธ
Ur Lovely Xahran kuceโ๐ผโ๐ผโ๐ผ
โค๏ธ๐๐
๐๐
โฃ๏ธ
Lallai Alqalami๐๏ธYafi takobi๐ก๏ธ
[4/24, 5:33 PM] Zarah Bae: ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*TAMBARI WRITERS ASSOCIATION*
๐ฑ(( *_Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah_*))
*T. W. A*
_LABARI/RUBUTAWA_
*PATEEMA XAHRA LAWAL*
*ุฅูููู ุงููููููู ููู
ููุงุฆูููุชููู ููุตููููููู ุนูููู ุงููููุจูููู ููุง ุฃููููููุง ุงูููุฐูููู ุขู
ูููููุง ุตูููููุงุนููููููู ููุณููููู
ููุง ุชูุณููููู
ูุง*
*Every day is a gift of new life, fresh hopes and blessings. May you continue to enjoy Allah's Mercy and Protection till Yaumul Qiyamah. May Almighty Allah accept all our ibada and our prayers may he let us witness the up coming Ramadan and much more ahead and may he let us to be among the beneficiaries of the upcoming holy month of Ramadan. May he forgive all our sins and protect us and our family from anything harmful dead or act amen ya Allah*....๐๐ป๐๐ป
*HPY Ramadan Kareem in advance my frnds*....๐๐ป
*_SECOND TO THE LAST PAGE_*
*Bismillahir-rahmanir-raheem*
๐
ฟ๏ธ:37-38
Koda sukaje Asibitin daqyar suka iya gane Hjy Rabi don kamanninta ya sauya sosai.
Qarisawa sukayi inda
Take,hawaye masu zafi suka tsiyayomata,jikinta na fitar da wani irin ruwa mara kyan gani.
Duban Mommah tayi"Tace Uwar dakina ki gafarceni,wallahi son zuciya ne da sharrin shedan.
Tun Sanda nazo gidanki amatsayin aiki,Allah yadoramun tsanar Jumaima,nayi qoqarin sonta Amma nakasa.
Abban Jumaima yanunamun qyama da tsana,don haka naje maidugri nasanar ma da mahaifiya ta abunda kefaruwa.
Ita takaini wajen Boka,yabani maganin da nadunga baki,don Abba yasakeki na aureshi.
Daganan tajigaba da zayyano musu duk abinda tadunga quqqulawa.
Gaba daya dakin salati akasaka
Adda Safiyya"Tace lallai kincika butulu,saidai ga sakamakon kinan kingani Koh?
Wani irin mimmiqewa Hjy Rabi tadinga tare da Ihu,warin ruwan dake zubane a jikinta ya tadama duk Wanda yajishi hankali.
Abba yadubeta"yace na sakeki saki uku,Kuma kije Allah ya Isa.
Wani ihun takwarma tana fadin"don Allah Alhj kayahaquri kayafemun.
Uwar dakina kisa baki yayafemun don Allah .
Kuka Mommah takeyi sosai"Tace don Allah Abban Jumaima kayafemata kaga halinda take ciki fah? Kuma ni nayafemata.
Abba yadaure fuska yace"kinji darajar umman Jumaima saboda zuciyarta tsarkakkiya CE.
Godiya Hjy Rabi tashiga yi sosae tare da neman gafarar sauran mutanen dakin.
Fita su baba Alhj sukayi gaba dayansu a dakin,don yanda yadunga wani irin wari Mai tada zuciya.
Gaba daya gidan Baba Alhj suka wuce,A falonsa suka yada zango.
Abba yanata kallon Mommah don yayi mhissing nata sosai.
Gyaran murya Alhj Tukur yayi"yace Alhj Habeeb maganar kudinka da aka kwashema tare da rufe duk wani company naka da gidan Mai Gaskiya a zahiri ba'a kulle ba,komai naka nanan yanda yakamata,hasalima juyama su akeyi.
Duk cikansu jama'an Falon duban Alhj Tukur Sukeyi.
"Yace ga dai Hjy Safiyya Nan zata Muku bayani.
Adda Safiyya tayi sallama"Tace ninaje nabawa mijina shawara akan duk wani kadaran(dukiya)Dan uwana,nace yatemakeni duk yanda yasan zaiyi yayi don ganin an adana ma Dan uwa na dukiyarsa.
Don na lura matansa Hjy Rabi tana gab da rabashi da komai,kamar yanda tarabashi da matarsa da 'yarsa.
To shinefa aka adanamasa dukiyarsa,yanzu haka komai nasa nanan yanda yadace.
Kabbara gabadaya 'Yan falon sukayi.
Godiya suka shiga yiwa Alhj Tukur da Adda Safiyya.
Mommah Tace"Aminiyata bansan wane irin godiya zanyimaki ba,da ke da mijinki.
Haba Aminiyata babu godiya tsakanina dake,fatana Allah yaqara dawwamar damu Cikin farin ciki.
Abba kuka yake sosai,yace ya gode ya gode sosai.
_Washegari_
Mommah still a gidan Adda Safiyya takwana,Shima daqyar Abba ya yarda Saida baba Alhj yasa baki tukuna ya'amince.
Kwanan Mommah biyu a garin bauchi tafara shirye shiryen komawa gida.
Saidai Antsayar da magana Abba zaije MARADI ayi magana da Cousin's din mahaifinta Sai ta koma gidan mijinta.
********
*_ZARIA_*
Yaudai biki Saura kwana uku 3days Kuma yaune za'ayi za'ayi Arabian nights.
Sun ci kwalliyarsu Sunyi kyau Sosai da shigar larabawan.
Amarya Aunty Fadeela tayi kyau sosai.
Aunty Aisha ita tayima Jumaima make up,Gaskiya tayi kyau sosai,Arabian gown nata yayi kyau sosai.
Aunty Aisha "Tace Gaskiya Ya Shuraaim ya iya za6en doguwar Riga,yayi kyau sosai.
Cikin Sauri Cike da mamaki Jumaima tadubi Aunty Aisha"Tace aunty kina nufin Ya Shuraaim shiya siyomun gown dinnan?
Murmushin Aunty Aisha tayi Tace"Eh Mana,yanason Jumaima dinsa tafi Kowa kyau ne.
Jumaima "ta e aunty a ina kikasan yadawo?
Eh nasan yadawo,domin shiyakira ni yafadamun.
Ok Jumaima tafada,akacigaba da shirya,saikace itace Amarya.
Mutane anata tafiya G. R. A gidan Ya Shuraaim don a can za'ayi, angama kwashe kowa.
Jumaima kuwa da Aunty Aisha suna gidan Hajja.
Kiranta akayi a waya tadauka tare da Cewa"Ya Sadauki barka.
Eh gatanan nagama Shiryata.
Ok yanzu zata fito.
Takatse wayar,turare tadauko kala-kala tadunga fesawa Jumaima a jiki,sannan takama hannunta sukafito.
Gidan Hajja babu Kowa daga ita Sai yarta Wanda suke 'yaya Maza,alamun jinjina Hajja tayima Aunty Aisha da hannu,lamarinsu Yana dauremun Kai.
Hajja Tace"Jummy na kinyi kyau.
Jumaima Tace"nagode Hajja na.
Baquwar Hajja wacce naji ana cemata Hjy habeey Tace"iyye lallai! Irin Wannan kyau haka?don Allah kada ayimun qwacen miji.
Tana nufin Ya Shuraaim kenan.
Koda Suka fita,wata mota CE Ash colour Mai kyan gaske, 'Yar dai-dai tayi kyau matuqa.
Glass din motar tinted ne.
Bude motar yayi suka qarisa.
Aunty Aisha tasaka Jumaima a sit din gaba,ita kuma tashiga nabaya ta zauna.
Kallon Aunty Aisha yayi yace"madam Adnan tnx.
Godiya nake Sadaukinmu,Aunty Aisha tafada .
Jumaima tadubeshi "Tace inayini,tayi maganar da qyar.
Dubanta Yayi "Yace lafiya Lou .
Sai kallonta yake ta wutsiyar Ido.
Ita Kuma Banda harara Jumaima