Showing 6001 words to 9000 words out of 26141 words
Chapter 3 - ADALILIN 'YAR TSUNTUWA Complete Hausa Novel
tace, aminiya kenan Allah yaqarawa abban jumaima lafiya,amma ni bazn sake komawa gidanshiba don ya cucemu nida jumaima.
Adda safiyya tace,haba kekoh aminiya wallahi duk abinda yaya yayimuku bayin kansa bane,bayan cikin hayyacinshi.
Dama kobaki fadaba aminiya abinda abban jumaima ya aikata duk Wanda yaji labari saiyamai kallon mahaukaci,domin in a mahaukaci ba babu Wanda zaima iyalinshi irin abinda abban jumaima yayi mana,yakoreni nida jumaima kuma kora ta daban daban bansan inda tilon 'yata takeba,mommah taqarishe maganar tana fashewa da kuma.
Adda safiyya tace kiyi haquri tabbas babu dadi,yace nagaisheki kuma nabaki haquri.
Mommah tace,INA amsawa kuma ni lafiyata qalau babu abinda yasamu qwaqwalwata,sannan kicemasa acigaba dasamun cigiyar tilon yata a bauchi.
Adda safiyya tace,ikon Allah aminiya yaushe kika koyi tsiwa da fada haka?
Mommah zatai magana saita kasa kurum tafada jikin adda safiyya suka fashe da kuka babu mai rarrashin wani.
******
Washegari 11:00 saiga abbiey yazo,su jumaima suka gaisheshi,cike da kulawa ya amsa,daganan sukace jumaima ta ciga.........
_Anan nadaka saboda banjin dadi yau pans,INA godiya da kulawarku allah yabar zumunci da qaunar juna_
```I love you so much masoya littafin A DALILIN 'YAR TSUNTUWA```โคโค๐๐
Ur lovely Xahran kuce๐๐๐ผ๐๐ผ๐๐ผ
[4/24, 8:09 PM] Zarah Bae: ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*INTELLECTU๐
ฐ๏ธL WRITERS ASSOCIATION*
*_(Home of experts and talented writers, kawo gyara da cigaba ga al'uma shine fatanmu)_*
*I.W.A*
_LABARI/RUBIUTAWA_
*PATEEMA XAHRA LAWAL*
*Bismillahir-rahmanir-raheem*
๐
ฟ:13-14
Abin mamaki Abba na yayi firrr yace,shi wallahi aurensa da aunty rabi babu fashi,domin shi yanaji ajikinsa idan bai aureta ba zai iya rasa rayuwarshi.
Yakumbo tace,wallahi Allah yajiqanka ai mutuwarka tafi dadai ganin wannan abin kunyar,alhj hakeem yace,a'ah yakumbo baza'ayi hakaba tunda yace haka Allah yasa hakan shiyafi alkhairi.
Hjy babba da yakumbo kuwa banda sababi babu abinda sukeyi.
Baba alhj yadubi Abba na yace,saika gaggauta don gudun wata rigimar,yamaida dubansa kan mommah na yace,maryama kezakice?
Mommah na Allah sarki baiwar Allah tace,babu komai baba alhj,Allah yasa hakan shiyafi alkhairi,Allah Kuma yabashi ikon adalci atsakaninmu.
Kowa na falon yaji dadin addu'ar mommah na suka amsa gabadaya.
Abba na kuwa banda farin ciki babu abinda yakeyi.
Anandai aka watse taro cike da addu'o'i.
Suko su yakumbo da hjy babba da Adda safiyya basu bari mommah na tabar gidannanva,har saida sukaga walwalarta tadawo .
Tun faruwar wannan al-amarin bamu sake ganin Abba na,har saida biki yarage saura 3days saigashe da akwatina set bakwai waina mommah ne,na fadar kishiya.
Mommah tace,ita Bata buqata yaje da kayanshi,aikoda daya aurota ba'a tsummma yaganta ba.
Budar bakin Abba na saicewa yayi aita kwana gidan sauqi,yaja akwatunansa yayi part dinshi dasu.
Niko jinake tamkar andasani sbd firgicin lamarin mahaifan nawa,musamman Abba na.
An zauna angyqra part din amarya,falone da 3 bedroom's,kowanne da toilet a cikinshi,daki daya ne akasama gado,sai dayan da akayar da katifa aka shinfida bedsheet kawai, dayan kuwa babu komai tamkar dakin larai๐
Ranar asabar aka daura after isha'i aka kawo amarya.
*******
Mommah da aunty rabi suna zaune,but zama suke na haquri sosai.
_AFTER FIVE DAYS_
Akwai watarana muna zaune da mommah muna fira saiga abbana yashigo falon tare da sallama,muka amsa,nan dai nagaisheshi ya amsa kadaran kadahan.
Ko zama bayyiba yadubi mommah yace,dama cemiki zanyi anjima zanyi baqi don haka inaso kimusu finkaso da miyar agushi.
Mommah tace,but Abban jumaima sainake gani kaman banice da girkiba,kaman Rabi ce.
Abbana yace,toh kenakeso kiyi don haka pls kuyi azama,yau jumaima saita haqura da islamiyya dama sungama Exam na boko Koh?
Cikin sauri nadubi Abba nace,Abba na yaufa zamuyi final exam a islamiyya,sannan hadisi ne,don Allah kamun afwa.
Abba na yadubeni yace,kina nufin ban Isa nasaki kiyi Abu kiyiba?to kije islamiyar mugani......zanyi magana kenan mommah tada katar Dani ta hanyar cewa,Abban jumaima basaita tayaniba,islamiyar ta yafimun ta tayani aiki mahimmanci.
Abbana yace,any way kukusani.
Yana fadin haka yayi hanyar qofar falon don fita,mommah tace,Abban jumaima na fadama yaubani ce da girkiba,don haka bansan hayaniya pls.
Abbana yace,Maryam bazan fasa zuwa da baqina ba yaso Inna kawosu susha lemo su tafi,Yana gama fadar haka yabar Falon.
Nadubi mommah nace,tunda yace kiyi kawai kiyi mommah ba laifinki bane.
Mommah tace,jumaima bazaki gane bane ni inada gudun zuciya,Kinga Rabi batada kunya,sannan tau ranar girkinta ne Kinga idan nayi haka kome yafaru ninaja.
Nadubi mommah nace,bafa laifinki bane mijinki ya tilasta Miki,Kuma bakece da lefiba.
Mommah tace,to shikenan Allah ya kyauta abunda zaifaru gaba,nace ameen da haka kikace tundazu da kin huta.
Mommah ta wuce kit hen nikuma natafi Shirin islamiyya.
*******
Washegari ana saura azumin Ramadan kwana biyar,nadawo daga islamiyya don munsamu hutu,naji aunty Rabi sa tsiya take.
Nidai bance da ita cikankiba na rabe ta gefenta zan wuce,Aiko kaman jira take takuwa fisgoni.
Ke!bari na aikeki wajen uwarki,kicemata Allah ya Isa datayi amfani da ranar gikina,wallahi ban yafeba,bari Kuma ogan yadawo.
Na dubeta nace,aini ba 'yar saqonki bane,domin tunkafin nashigo natararda ke kinayin 6a6atunki,sannan da wannan wasting time naki dakijayi aeyaci ace kinje kinsanarda saqonki tunkafin nadawo.
Ina gama fadar haka nakama hanya nayi tafiyata,nabarta da sakin baki. Koda na Isa part namu Banga mommah a babban faloba don haka saina haye step naje falonta,na ciddata tana karanta _hisnul-muslim_nayi mata sannu da gida.
Ajiye _hisnul Muslim_ din tayi tare da fara yimun fada,akan cekucen da taji munayi da Aunty Rabi nadubeta nace,mommah dama kina jimmu? Tace, Eh Mana.
Daga Nan nefa tafara yimun fada sosai, nudding kaina nayi tare da cewa mommah Kiya haquri bazan sakeba soon. Ok Allah yamiki albarka,nace ameen mommah na.
Tare da fadawa jikinta,tace yanzu mukagama magana da hjyr kano(mahaifiyarta)nace,Allah mommah?tace kigaisheni ?
Mommah tace,Eh Mana tace yaushe zakizo?nace saikin tambayi Abban ki Koh?
Dariya nayi tareda cewa,Eh Mana mommah na,bari naje na watsa ruwa pls. Mommah tace,Ok.
Bayan sallar isha'i,muna falo muna kallon wani series a Arewa24 mai suna Tarkon qauna.
Saiga Abba na shida Aunty Rabi ko sallama babu.
Nankuwa yafara zazzaga fada ta inda t
Yake shiga batanan yake fitaba,yadubi mommah na yace,shiyanzu ya lura da ita wani tashen rashin mutumci keda munta.
Wani magana yayi Wanda saida yasani sakin ihu,cewa mommah tayi tayashi ta tattara yanata yanata tabar masa gida yasaketa saki daya,shiyasani sakin wannan kukan.
Mommah tadafe qirji tare da duban Abba na tace,don Allah Abban jumaima kayahaquri kodan albarkacin jumaima.
Abba na yace,wata jumaima?itama gobe zata biyu bayanki,but kedai kitashi kibar gidannan maza maza,cikin sassarfa nariqe qafar mahaifin nawa nace,Abba don Allah kayahaquri ka qyale mu pls,idan muka fita a darennan Ina zamu?
Abba na yace oho matsa kibani waje,jumaima I hate ur mommah,tafita kaina gabadaya.
Mommah kuwa banda kuka babu abinda takeyi.
Aunty Rabi ta dubi Abba na tace,babe ai wallahi kayi qoqarin zama da ita,matarda kace,bakasan irin warinda takeyiba(kaji sharri irinna Rabi,to yaushema suke ganinshi)?
Abba yace,Maryam nabaki nanda awa uku kibarmun gidana kekuma da safe kibi bayanta,yayi maganar tare da nunani.
Cikin kuka nace,nidai Abba kabarni nabi mahaifiyata,Abba yace Ina bazai yuwuba.
Haka mommah ta kwashe duk wani abunata mai amfani,inaji inagani,mommah na kuka take nima haka,baba maigadi ma banda kuka babu abinda yake.
Haka mommah na tabar gidannan a tsakiyar dare,nikuma Abba na yakulleni a bedroom dina,haka na kwana da uniform din islamiyar ajikina(mommah tayi tayi naciresu nace,tabari na kwana dasu don Ina missing islamiyya,nasan za'a dinka mun wasu)
Da safe kuwa ko breakfast banyi ba,ana ruwan sama agarin bauchi wajen 7:14 nabar gidan mahaifina.
Banyi tunanin naje gidan wani nawaba,saboda rudewa haka nahayo motan Zaria memakon na kano,don na rude sosai.
Koda na sauka babu kudin mota haka me motannan yacimun zarafi ,shima na sauka garin da hadari ne sosai.
To wannan shine labarina Abbiey,tayi maganar tare da fashewa da kuka.
Duk na falon babu Wanda bayyi kukaba sai Abbiey shima dakaganshi kasan daurewa ne.
Shuraaim na hango a tsaye a qofar falon hajja ya Ciro hankicif Yana share tears dinda suka zobo masa,juyawa yayi zaifita,duk cikansu kallon inda sautin tafiyar yake suke babu Wanda ya iya magana.
Abinda ya basu mamaki shine,yaushe shuraaim yazo gidanne,?
Abbiey yadubi jumaima yace,Allah sarki 'yata Ashe haka rayuwarki takasance?Allah sarki kiyahaquri komai zaiwuce,Kuma zakuga sakayya.
Hajja tace,Allah sarki sannu kinji jummy.
Su fadeela susuka cigaba da rarrashin jumaima. Hartasamu natsuwa,Nan Abba yamusu sallama yatafi.
_Washegari_
*Ur lovely Xahran kuce*๐๐๐โค๐
~Tanx so much masu comment~
[4/24, 8:09 PM] Zarah Bae: ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*INTELLECTU๐
ฐ๏ธL WRITERS ASSOCIATION*
*_(Home of experts and talented writers, kawo gyara da cigaba ga al'uma shine fatanmu)_*
*I.W.A*
_LABARI/RUBUTAWA_
*PATEEMA XAHRA LAWAL*
*Wannan page din sadaukarwa ne ga mahaifiyata abun alfaharina Koda yaushe.Allah subhanahu wata Alah yajiqanta,yayimata rahama......Allah yasa tana kyakkyawan matsayi*๐ญ๐ญAmeen๐คฒ๐ผ๐คฒ๐ผ
*_Nasadaukar dashi ga duk wata uwa data rasu_*
R I P mommah
*Bismillahir-rahmanir-raheem*
๐
ฟ:15-16
Washegari bayan suntashi da wuri suka gyara gidan Tass tare da hada breakfast.
Chips sukayi da kunun gyada Wanda yaji kayan qamshi,bayan sungama karyawa ne suka gyara ko Ina jumaimah tadauraye kayayyakin.
Falo suka koma gabadayansu tare da gaishe da hajja. Zamansu kenan wayar fadeela tayi qara,dauka tayi tareda dubawa taga ansa Abbiey.
Cikin sauri tayi picking din wayar tare da kangasa a kunnenta tace Assalamua laikum,tadauki tsawon 6mint tana wayar bayan tagamane tadubi hajja tace,hajja Abbiey yace zaimun transfar din kudi ta wayana yanaso mujeda jumaimah super market ayimata siyayyar kaya.
Hajja tace,to shikenan Allah yakaimu anjiman gabadaya suka amsa da Ameen but banda fareeda don hankalinta nakan waya,fareeda ma'abociyar son wayane tanaba waya mahimmanci ssai a rayuwarta,da yawa dalilin waya kehadasu rigima da fadeela.
Wajejen 11:15 taji wayarta tayi qara alamun message yashigo,Koda taduba taga Abbiey ne yaturo mata da kudin 100k ne yace ayi manej kafin ayi salary.
Or ready dama sun shirya duguwar rigane a jikinsu na fadeela orrange da viel white,sai na jumaima maroon da viel black. Gaskiya sunyi ssai,fadeela tadubi fareeda tace madam phone pls kitashi muje.
Fareeda tace,Kai sis fitannan bazaiyuwuba kinganni wani novel nake karantawa *ABOUL UMMIEY* gsky novel din so sweat.
Fadeela tace,malama candaya warki Kinga tafiyarmu taja hannun jumaimah suka fita.
Sunsamu hajja a falo don haka suka mata sallama,ptn alkhairi tayi musu, fita sukayi suka tsaya dai dai junction din tukur/tukur wajen qofan kibo,Nan suka tari Mai adaidaita sahu tare da shiga.
Tambayarsu yayi Ina zaikaisu,fadeela tace mlm Nan daula store qofan doka zaka kaimu,me napep yace toh,jumaima ce take riqe da phone din fadeela a hannunta,tundazu taqurama pix din dake screen din wayar kallo.
But pix din yayimata kyau matuqa gayen yahadu yanada komai na rayuwa,komai na halittarsa Mai burgewa ne,(A zuciya jumaima keta wannan surutan tare da smile dauke a face dinta).
Kasa daurewa dai tayi tace,aunty fadeela wannan wanene a screen din phone dinki?tayi maganar tare da nuna mata pix din.
Murmushi fadeela tayi tace,brother namu ne,shine first born din Abbiey sunanshi ya shuraaim!
Jumaima tayi murmushi tace,but aunty yafiku kyau sosai,yanada kyau like imran Khan.
Dariya fadeela tayi tace no don kawai bakiga aunty aeysha bane itama tanada kyau ssai,jumaimah tace Koh ?fadeela tace yep.
Dai-dai Nan me napep yakawosu inda sukace,sauka sukayi tareda da sallamar Mai adaidaita,riqe hannun jumaima tayi suka shiga cikin store din.
Nandai sukayi siyayyar da zasuyi dogayen riguna zallah ta siyomata guda uku,kowane daya Yana nufin13k ne haka takwasomata five,tace tagwada,
Wow sunyi kyau sosai.
Daganan suka wuce sabon gari tasiyomata trolley da laces guda uku sukuma kowanne 8k,atamfofi tasiyomata English guda biyu red and blue,sai pink and copy,sai cote d voure guda daya,materials guda hudu, gyale guda biyar,sai takalma hell shoe uku plat shoe uku,sai fashion din dankunne.
Hijjab kuwa daya ta dinka mata chocolate colour, a cewarta suma sunfi saka veils.
Sai before 4:00 sannan suka koma gida don sunwuce wajen tala nasu ne tabashi dinki,tace jibi akeso tabashi kudinshi cash 15 thousand.
Sun Isa gida ana Kiran sallah la'asar,Koda sukaje suncidda Aunty Ni'ima itada junior tare da tutsetsen cikinta haihuwa yauko gobe.
Tare da sallama sukashigo falon,are fadeela tana ganin Aunty Ni'ima ta saki ledar hannunta ta Isa wajenta da gudu tare da rungumeta.
Hajja sallah take but cikin sauri ta katse tare da cewa,ke!ke!ke! Bakida hankali ne?kina ganin yarinya da tutsetsen ciki saiki hau fadamata?
Fadeela tace,Kai hajja mekika maidani?tayi maganar tare da turo mouth nata.
Aunty Ni'ima itadai muushi tayi.
Jumaima ce taqariso tare da zama a 1 sitter,tadubi Aunty Ni'ima face nata dauke da smile ta gaisheta,itama Aunty Ni'ima cikin murmushi ta'amsa.
Tadubi hajja tace,hajja sannu da gida,hajja tace yawwa jummy kundawo lafiya?jumaima tace lafiya Lou hajja. Ina aunty fareeda ne?
Hajja tace tanacan sarkin waya,baiwuce tana latsata ba.
Miqewa tayi tare da wucewa dakin su fadeela .
Junior ne akusa da jumaimah sai surutu yakemata.
Jumaima tace,boi wat s ur name? Junior yace,my name is Basheer shuraaim Bashee.
Jumaimah tace wow ashe boi din yasan sunanshi.
Dariya junior yayi yace, aunty yhu re beautiful,kinfi mommah na kyau.
Dariya sukayi su duka,hajja tace,kajimun shakiyin yaro anan.
Dubanta yayi yace,Allah zancema daddyna yakawo ki gidammu saboda shima Mai kyau ne.
Nandai aka Kuma sa dariya,cuz kowa Yana daukan zancen nasa a shirme,cuz yanzu yakeda 7 years.
Zaiyyi magana kenan jumamah tace,junior ta Isa haka,bama sekafadama daddynka ba,nida kaina zandawo but saida yardar mommynka.
Aunty Ni'ima tayi dariya tace,A'ah nibani da matsala aini adadina zansamu qanwa Kuma abokiyar Hira.
Fadeela tace,lallaima auntyn Nan aibabu inda jumaima zataje,munanan tare.
Aunty Ni'ima tace,aidama Bata dalilinku zata zoba saidon hajja zatazo,Koh hajja?
Hajja tace,A'ah bazan iya nisa da jummy ba,Koh jummy?
Jumaima dariya tayi tace,Hajja Nima wasa nake bazan iya tafiya ko Ina nabarkiba.
Fareeda ce tafito hannunta riqe da phone tace,hmmm fadeela yanzu Ummie takirani sai fada take,wai wallahi anjima idan Abbiey yazo muddin bamu biyoshiba mundawo gida zata hadamu da ya shuraaim.
Diddilo idanuwa fadeela tayi tace,Kai meyasa ummiey zatayi haka?nifa duk a tunanina ta manta damu.
Hajja tace,ni wallahi nagama qoqarinta data barku kukadade haka.
Fareeda tace,Kai hajja memakon kisamo Mana mafita,sai Kuma kice haka?
Hajja tace,babu maishiga tsakanin 'da da mahaifi,bazan goyi bayan kubijirewa uwankuba.
Fareeda tace,wallahi da inata murna nasamu qanwa,zamu zauna tare.
Fadeela tace,to munafika!aike dake da babu duk daya ne,tunda kinzama madam phone.
Fareeda tace,Eh din naji.
Jumaima raurau tayi da ido tare da dubansu tace,yanzu tafiya zakuyi?idan kuka tafi yaushe zaku dawo?tayi tambayar hawaye na tsiyayomata.
Fadeela tace,karkidamu anatare vazamuyi nisa dakeba,bamuda nisa,duk after 2days zamudinga zuwa , Koh sis?
Fareeda tace,Ehmana.
Nandai suka hadu harda Aunty Ni'ima suka rarrasheta tare da kwantar mata da hankali.
Hajja tace baganiba,ai idan babu nine zakiyi kuka Koh?
Dariya jumaima tayi tace, Eh hajja tayi maganar tare da rungumi hajja,tasaki kuka Mai sauti tace,Allah sarki momnah na!kotana Ina?oho,kotana wani hali bansaniba,tayi maganar tare da qara fashewa da kuka.
Duk cikansu saida suka tausayamata matuqa,hakadai suka lalla6a suka dinga lallashinta,har saida want baccin wahala yadauketa.
Wajejen qarfe takwas ya shuraaim yayi sallama falon hajja.
Kai gaskiyan jumaima ne guy din yhadu kota Ina ,tsayawa kwatance wasting time ne,tafiya yake a tsaye tamkar sadauki,idan Yana tafiya har wani shakking hannun shi nadama yake.
Sallama yayi falon da wata irin cool nd suger voice,duk cikansu amsa sallamar sukayi banda jumaima dake bacci.
Su fareeda ne suka gaisheshi fuskansu dauke da smile,babu yabo babu fallasa ya'amsa.
Yadubi hajja yace,Evining rigimammiyar tsohuwa,yayi maganar tare da murmushi alamun yayi tsokana yaji dadin.
Hajja ta dubeshi tare da kanne ido daya tace,yawwa fitinanne aedama inbaka roreni da maganava bakajin dadi.
Nandai sukayi wasansu na kaka da jika,duban Aunty Ni'ima yayi tare da cewa,madam saiki tashi muje Koh? Ina junior dinner?
Yayi maganar tare da dubansu fareeda,fadeela tace gasucan akan carpet shida jumaima sunyi bacci.
Sai a lokacinma idonshi yakai wajen,but tun shigo wanshi falon bai lura.
Tundaga kanta yake qaremata kallo har zuwa tafin qafarta. Y Salam!
Kalmar da yafada kenan a ranshi yadubi fadeela yace,ok daukoshi kikaishi mota muje,
Yayi maganar tare da qarisawa inda hajja take,yaduqa yace,rigimammiyar tsohuwa ga wannan asai goro,yayi maganar tare da miqa mata Envelop din.
Ansa tayi tare da sa masa albarka(Readers na manta banfada muku aikin shuraaim ba,shuraaim dai lowyer ne),Nan suka mata saida safe suka tafi,Aunty Ni'ima tace idan jumaimah tatashi agaisheta.
**********
Tanx masoyan littafin *_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
@โจMmn Aslamiyyaโฉ
@โจJuwairahโฉ
@โจMr's Aminullah๐โฉ
@โจZarah Ummi Ayshatโฉ
comment dinku naqaramun qarfin gwiwwan typing sosai tnx so much๐
*_Ur Lovely Xahran kuce_*โ๐ผโ๐ผโ๐ผ
Lallai Alqalami๐Yafi takobi๐ก
โค๐๐๐
[4/24, 8:10 PM] Zarah Bae: ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*_A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_*
๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ๐ฅ
*TAMBARI WRTER'S ASSOCIATION*
*_๐ฑ((Home of Expert and Talented writers, da tambarinmu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'umah))_*
*T.W.A*
_LABARI/RUBUTAWA_
*_PATEEMA XAHRA LAWAL_*
This page is dedicated to oll masoya *_ADALILIN 'YAR TSUNTUWA_* tnx so much love you ๐ฏ๐ฏ๐ฏ
*Bismillahi-rahmanir-raheem*
๐
ฟ๏ธ:17-18
Jumaima Bata tashiba saiwajen 11:30,Koda tafarka brush tayi tare da alwallah a gurguje tayi sallah,sallar take,tare da rashin jindadin lattin da tayi yau byn tayini tayi azkar dinta da addu'o'i tatashi tacire hijjab din,tadubi kanta tace,oh Ashe jiya haka na kwana da kayana?
To wayakawoni bedroom?rashin samun maibata amsarne yasata tajuya tareda fita bedroom din.
Falo tafita,hajja kadai tacidda a zaune Tana kallon Tashar AfricaTv3,sallama tayi tare da gaishe da hajjan,zama tayi kusa da hajjan.
Hajja tajuyo tare da murmushi ta'amsa gaisuwar nata tace,kintashi lafiya?
Cikin murmushi jumaima tace,lpy Lou hajja,Shuru taji