Showing 66001 words to 69000 words out of 79238 words

Chapter 23 - UBANA NE KO KISHIYATA

dauki Nadeeya ya tafi da ita Kaduna daman tunda ya zo be je ba,

Nan take kuwa ran Habeeb ya Baci Akan meyasa zai ce haka,gani yake Yana takura su ko kuma su din sun gaza bara su iya Kula da ita ba,

AA wlhy ko daya Ka fahimce ni ba daidai ba,gani nayi yanda aka Fara binciken nan toh ban san iya yanda zai tsaya ba gwara in dauke ta tayi nisa da garin nan gudun Kar in Sanya Ku a wata matsalar,

Da kyar ya samu Habeeb in ya fahimce Shi be bar gidan ba sai dare bayan yace da Muhibba ta shirya ta da wuri don Allah don asubanci yake so suyi,

Da haka ya koma gida,Saida ya kuma wanka sabida Yana yi na zafi kafin ya gabatar da sallahn Isha sannan ya dauki waya ya Kira Mama,

Idar wan ta ke nan itama tana lazumi kiran nashi ya Shigo,ajiyar zuciya me karfi ta sauke domin yau Kusan kwana uku ba suyi magana ba duk hankalin ta ya tashi addua kawai take Allah ya Sanya Yana lafiya domin ko sun Kira basa samun Shi,

Da sauri ta dauka tare da sallama,amsawa yayi sannan yace ina wuni Mama,

Baba na ba zan amsa ba Ka ga yanda Ka daga mana hankali kuwa ina Ka shiga ne haba baba na,AI ko sako Ka turo in ma busy kake in dai san kana cikin koshi lafiya,ta kare kamar za ta sa kuka,

Numfashi ya sauke sannan yace kiyi hakuri hajiya mama wlhy ana ta dan rikici ne a gurin aikin na mu,

Subhanallahi ina fatan dai ba da Kai Ake rikicin ba dai ko,

Dan dariya yayi sanna yace haba mama ni kan AI bana rikici da kowa ba da ni bane,

Toh Alhamdulilah ina fatan kana lafiya sanan kuma kana cin abinci,ni wlhy duk hankali na ba a kwance yake da garin da Baka san kowa nan ba,ta kare tana jimami,

Dan murmushi yayi sanann yace hajiya mama ke nan toh ki kwantar da hankalin ki in sha Allah gobe a Kaduna Zan kwana asubanci ma Zan yi da yardar Allah kafin 10 ina gida, breakfast in ki ma Zan ci,

Cike da murna domin ita kanta tayi missing Dan nata tace da gaske kake Babana,Bani son zolaya fa,

Shima dariyar yayi sanann yace da gaske nake mama gobe Zan zo ba ma ni kadai zan zo ba,

Kai dawa ye ta tambaya,mama labarin da tsaho ki Bari sai na iso Zan Miki bayani za ki fi gane wa,

Toh shike nan ubangiji ya kawo Ku lafiya Allah ya tsare hanya,

Ameen thuma ameen Mama tah ina angel take,

Ka ganta can ta gama fitina ta na dake ta na hurga ta gado tayi bacci,

Haba mama nawa angel take da za a Mata dukan da har sai tai bacci ya kare kamar zai yi kuka,

Gidan Ku Baba na yarinya tayi mun bar na bazan buge ta ba,Ka fita a idona da wannan kwalafucin da kake Akan yarinyar nan fa,

Baki ya turo kamar karamin yaro sanan yace shike nan kiyi hakuri sai da safe,

Dariya ta Sanya sannan tace au don nayi fada shine zaka kashe wayar taka ko,

AA mama ba don haka bane fa,Allah ya shirye Ka Baba na da haka suka shiga hira irin ta " da uwa Wanda daga gani za Ka gane akwai tsantsan shakuwa da soyayya me karfi a tsakanin su,Saida suka yi Kusan 1 kafin suka yi sallama ya ya kwanta Yana Jin kamar ya janyo gobe tayi ya ganshi a gida,saidai wani gefen zuciyar Shi na tambayan Shi me zai ce da mama in ta ganshi da Nadeeya, inda ya samu kwanciyar hankali ya San Mahaifiyar tashi akwai saukin Hali da fahimta he is sure za ta fahimce Shi,da haka ya kwanta bacci me dadi ya dauke Shi,


Ko da ya tashi sallan asuba be koma bacci ba,kayan Shi ya hada Wanda ya san zai bukata Saida ya Gama sannan ya fada wanka,bayan ya fito ne ya shiga Kitchen cikin sauri yayi frying egg da plantain sannan ya hada tea ya fito,a nutse yake cin abinci don in yace zai Bari sai ya Isa ya ci abinci zai jigata,domin daga Bauchi zuwa Kaduna ba karamin tafiya bane,

Around 6:30 ya gama hada koman Shi ya zuba a mota,Saida ya rufe ko ina na gidan sannan ya fito ya shiga motar nashi,

Saida ya biya inda yake Siyan masa ya siyo don yayi alkwarin Kai wa mama,sannan ya biya Jifatu siyayya yayi musu sosai wa mama Nadeeya da kuma angel inshi sannan ya dau hanyar gidan Habeeb,

Da isar Shi kuwa ya tarar da Muhibba ta gama shirya Nadeeya cikin dogon Riga,dauko ta yayi zai shimfida Leda tace da Shi AI ta Sanya Mata pampers Kar ya damu har su Isa bara ta yi komai ba don ba wani ruwa sosai ta bata ba,

Godia sosai yayi musu inda a karshe ya dauki kyautar 100k ya baiwa Muhibba sam taki karba Akan ita fa ya wuci haka don Allah ta kula da Nadeeya,da kyar ta karba bayan yace da ita AI ance gaida me gaida Ka ko bare amsa ba,godia tayi mishi sosai don har da kwallan ta,sabida ba karya ta Fara shakuwa da Nadeeyar duk da ba magana take ba,

Sallama suka yi da Habeeb bayan ya sanar da Shi in sha Allah bare wuce week in nan ba zai dawo gudun Kar a zarge Shi,shima ya kuma mishi godia sannan ya shige motar sa,adduar Allah ya kiyaye hanya suka yi mishi tare da daga mishi hannu har ya fice daga gidan,

Cikin kwanciyar hankali ya dauki hanya Saisa ya zabi tafiyar samako domin gujewa idon sani KO kuma road safety suke ne ko yan sanda 🤣,da haka ya dauki hanya Yana tafe Yana duba halin da yar mutane ke ciki,sai muce Doc Nameer Allah ya kiyaye hanya,


*********Sen Rilwanu

Bugun kofar dakin Shi ne ya farkar da Shi daga baccin safen da yake yi,da kyar ya samu ya tashi ya nufi kofar domin ya sha maganin bacci jiya kafin ya kwantan,

Bude kofar ya ga Falmata ce durgusawa tai tare da gaishe shi,da hannu ya amsa ta,a ladabce tace da Shi ranka ya Dade kayi bakuwa,

Bakuwa ya maimata da mamaki,eh Waye shine abunda ya tambaye ta,

Yallabai Hajiya ce,idanu ya zaro yace hajiya fa kika ce eh tace da Shi a nutse,be koma cewa komai ba ya fada daki cikin sauri ya wanke Baki tare da wanke fuska ya xura milk jallabiya tare da feshe turaruka ya dauko carbi yana dan ja a nutse ya fito da murmushi Kan fuskar Shi,

A zaune ya tarar da yar dattijiwar matar da ke tsananin kama da Shi,sanye da hijabin ta har kasa tana jan nata carbin,

A gaban ta ya zube tare da fadin sannu da zuwa Hajiya Ashe kina tafe,

Kallon Shi tayi tsaf daga Sama har kasa saidai sam yaki barin su hada idanu da ita,

Kai ta girgiza sannan tace Abul bait wai me ke damun Ka ne,

Cikin saukar da murya yace hajiya magauta sun sako ni gaba na rasa yanda zanyi,

Anya kuwa Abul bait Anya,sai kuma ta girgiza Kai,tare da gyara zama,

Mikewa yayi tare da fadin Bari na sanya a kawo Miki abinci na san Baki karya ba kika taho,

Dawo Ka zauan ba abinci ne gaba na ba,magana nake son muyi ta fahimtar juna,

Ba musu kuwa ya dawo tare da zaunawa Kusa da ita,duk iskancin Sen Yana mugun shakka da tsoron Mahaifiyar shi (Hajiya Rakiba),


Abul bait,naaam hajiya ya amsa ta,na tambaye Ka miye damuwar Ka Amman kace Dani magauta sun Saka Ka gaba,na Rasa gane wani irin abu ke bibiyar Ka Ka duba fa ace tun mutuwar Mahaifiyar Nadeeya ace har yau shekaru Kusan 25 baka kuma aure ba,

In anyi magana kace mun komai yar lokaci ne,sannan ace yarinyar nan jarabawa ta fada Mata ni Banda nasani ya and kace da ni babu abunda kake boye mun,

Ina yawan mugayen mafarkai da Kai Wanda na Rasa gane dalilin haka,Ka ji tsoron Allah Ka fada mun in har akwai abunda kake boye wa duk duniyar nan Baka da kamata ni ce uwar Ka ni ce uban Ka,don haka Ka sanar da ni miye kake boye mun,

Kan Shi ya kwantar a cinyar ta sai ya Sanya kuka,hajiya mutane sun Saka ni gaba kaina aka Fara siyasa an samu wasu mugayen da suka jefi yarinyar nan hauka tuburan tayi hajiya bata komai sai auna mun zagi,

Kallon Shi kawai Hajiya ke yi kafin tace Ka tabbatar babu abunda kayi wa yarinyar nan Baka zalunce ta ta ko ina ba,

Dagowa yayi sanann yace haba hajiya ke fa kin fi kowa sanin halina,

Yo wani sanin Hali Dan mutun da Ka Haifa ne Baka Haifi halin Shi ba,AI kana iya canzawa a KO wani lokaci amamn da mamamki ace Nadeeya ke maka irin wannan diban albarkan da na gani a video,

Wlhy hajiya sa hannun magauta ne,

Kayi mun shiru in sanya hannu ne Miya Sanya Baka kawo ta gurina ba sanin Kan Ka ne Ubana babban malami ne kafin ya mutu duk garin Azare har nan cikin garin Bauchi babu Wanda be san da Zaman Shi ba,

Kawunan Ka wani irin ayoyi da adduo'in karya sanmu ne Basu San Shi ba Amman Ka dauke ta Ka Mika ta asibiti,tunda ga rannan nasan tabbas akwai wani Abu a kasa KO ba haka bane,ta kare tana tsare Shi da idanu don son karantar Shi,

Idanu yayi saurin saukewa domin wani yarrr yake ji a duk lokacin da ta tsare Shi da idanu har rawa jikin Shi ke yi at times,

Cikin kwantar da Kai yace wlhy hajiya Bani son daga Miki hankali ne na ga ba isashen lafiya gare ki ba,and Kabiru ne ya bada shawaran a Kai ta asibitin domin likita yace kwakwalwan ta ya dan tabu dole akwai bukatan ayi na asibitin kafin a yi na gidan,Jira nake in an Gama daman sai na kawo ta gurin ki,sai kuma aka yi rashin dace an bita can asibitin an sace ta yanzu haka case in na gurin Yan sanda suna bincike akai,

A Ka sace ta salati hajiya ta Sanya tare da tafa hannuwa wanann masifa har ina,Anya Abul bait ba wani Sabon Allah kake yi ba shine ya tashi kama Ka ta wanann hanyan,

Cikin sauri yace wlhy hajiya Bana aika ta komai ina sallah ina azumi ina zakka ina sadaka ina kyauta,ina sauke farali sannan Ina kyautata muamala ta da mutane da makota na uwa uba kuma ina Miki biyayya ke dai kawai in jarabawa ta samu mutum,

Dan shiru hajiya tayi sannan tace ina fatan dai kana gujewa haramun domin cin haram kadai Kan iya wargaxa ma lamuran rayuwar Ka,


Da sauri yace Allah ya mana tsari da haram hajiya Bana cin ta Bana kusantar ta kuma Bana kaunar me taammali da haramun,

Shiru suka Dan yi Basu ce komai ba sannan can tace ko dai za Ka hakura da neman wannan takaran ne haka kawai Bani da good feelings Akan takaran nan naka Abul bait,Ka dube Ka duk Ka Rasa nutsuwa yarinyar nan ba ma mu san halin da take ciki ba duk Akan neman duniya wani irin arziki da dadi ne Allah be azurta Ka da Shi ba,

Kirjin Shi ne ya buga,a taya zai ma Fara Aje takaran nan bayan abubuwa da yawa da ya Rasa sabida Shi,AI ina bare ma taba yuwa ba,

Kayi shiru ina yi maka magana,

Zama ya gyara sanann yace hajiya Nima da zan so ajewar tunda hankalin ki be kwanta da Shi ba,Amman kuma mutane zaki duba gabada hopes in su na ga Allah na gare ni don alummah ta nake son yi,domin kawo cigaba Amman in Baki so zan hakura,

Dan tsaki tayi sanann tace ubangiji ya shige mana gaba Ka dai dage da azkar yanda kace an sako Ka gaban nan Nima Zan na taya Ka,sannan Ka ji tsoron Allah a duk yanda kake in kayi Abu kana tunanin bazan sani ba Allah zai sani kuma Yana gani domin Shi ya yayi mu duka,Allah ya gani na Baka tarbiya da ilimi daidai iyawa ta,

Haka ne hajiya ina Kan ji wlhy ayi ta taya mu da addua in sha Allah komai zai zo ya wuce,maganar Nadeeya kuma yau Zan Kara Sanya yan sanda suna checking duk wani shige da ficen motoci sannan Zan Sanya ayi sanarwa duk Wanda ya same ta Zan bashi kyautan makudan kudade,da yardar Odugwu nan take zaki ga an same ta,

Idanu ta watsa mishi tare da fadan Waye wani Odugwu,Abul bait da hankalin Ka kuwa,wani irin sakarci ne hka,

Da sauri yace hajiya Odugwu Yana nufin shugaba ne ina nufin Allah ke nan,

Bana son iskanci fa wani hauka ke nan Allah za Ka wani kira Shi Odugwu wlhy ka na kiyaye halcen Ka Kar Ka je fa kanka a wuta da kanka,ta kare cike da fada,hakuri ya bata sannan ta mike tace ni kam Zan koma ubangiji ya shige mana gaba,

Haba hajiya ko ruwa fa Baki sha ba,ina azumi Abul bait daman Jin Shirun ne ya sanya ni cewa Zan zo tunda Kai ka gagara zuwa,

Nan ma hakuri ya bata sannan yace da ita Yana zuwa,daki ya nufa kudi ya Ibo masu yawa sannan ya fito yayi daidai da fitowan Afzaal da gajeran wando,

Kai ko ba Afzaal ba,eh hajiya ni din ne Ina kwana ya kare Yana Sosa keya,

Abul bait uban me yaron nan ke yi cikin gidan nan na gani Yana da gida KO ba haka bane,

Eh hajiya daman sabida laluran da ta sami Nadeeya ne ya sanya Shi dawowa nan domin Zama Shi kadai in babu daadi,

Harara hajiya ta jefa mishi sannan tace yaron goye ne Shi,yanzu hka ya dace inda yake yawo daga Shi sai guntun wando,wannan AI iskanci ne,nan ko ta hau Sababi,

Shi dai Sen hakuri ya yi ta bata da kyar ya samu ya lalabata tayi shiru suka fito tana kuma mishi nisiha Kan ya ji tsoron Allah a duk abunda ya Sanya gaba,sannan in ya samu lokaci ya ci ya zo ya gaida kawunnan Shi tunda Shi komai sai an fada ma ka,

Hakuri ya kuma bata tare da Mika Mata kudadan hajiya gashi ayi tsaraba tunda kin ki kwana,

Mota ta shige sannan tace rike kudin ma Abul bait Wanda Ka aiko wancan satin ma ko ficika ban taba ba,ni dai ina kuma maka nasiha da Ka ji tsoron Allah a duk inda kake,murtala ja Mota mu tafi,a haka suka fice daga gidan aka bar Sen tsaye da kudi a hannu duk jiki a sanyaye,toh ko dai hajiya ta san abunda yake aikata wa ne,in ko haka ne da ya shiga uku,wani zuciyar ce tace da ta sani hajiya bara ta iya shiru ba sai ta tare Ka da maganar,sai dai in ta Fara zargi na,AI ko ya Zama dole ya canza taku domin ko giyar wake yake sha bare so hajiya ko wani ya San asirin Shi ba,ajiyar zuciya ya sauke tare da komawa cikin gidan.



Asaalamu alaikum

Ina fatan anyi jumma lfy ubangiji ya kara mana lafiya da Zaman Lafiya Allah kuma ya amsa mana ibadun mu da adduo'in mu🙏🏻
[6/21, 8:37 PM] My Best Best ❤️: 😭😔 UBANA NE KO KISHIYA TA 💔💔

WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEYBEE)

........

My what's app group link

https://chat.whatsapp.com/FKZuWu1yj7VJ9L6izLqLhA

In har kin San ba karanta book ina da commenting bane zai kawo ki toh kiyi Zaman ki ba sai kin Shigo ba, haka zalika Maza should stay away from my group domin na Mata ne xallah 🙏🏻,

Ga masu son a tallata musu hajojin su should contact me via:

08100046388

.........
Page twenty-two

*********

Doc Nameer*******

Tsaye yake a bakin kofar dakin Mama, Yana me jiran umarnin shigowar Shi,

Shigo Babana mun Gama wankan tace da Shi,da dan karfi yanda zai ji abunda tace,

Cikin sallama ya Shigo cikin dakin,a kwance ya tarar da Nadeeya sanye cikin sky blue dogon Riga ban da kamshi babu abunda take yi,idanu ya lumshe yana me kara gode wa Allah da ya bashi Mama a matsayin Mahaifiyar shi,

A kujeran dakin ya ja ya zauan sannan ya ce sannan da kokari Mama ta ubangiji ya Saka miki da gidan Aljannah,

Murmushi tayi sanann tace Ameen Baba na Bana fatan yanda kake kyautata mun kake tattalin rayuwa ta da farinciki na,a ce ka nuna abunda kake so na Gaza yi maka,ko na Gaza Kula maka da shi,ta kare tana murmushi,

Shima murmushin yayi domin sam be gane inda zancen nata ya nufa ba,

Zama ta gyara sanann tace ni kam Babana jikin yarinyar nan Anya kuwa ma tsaya na asibiti kawai,

Shi din ma Zama ya gyara sanann yace wlhy mama Nima abun yana Bani mamaki,yanda kika ce tana yawan firgici cikin dare kamar me yin miyakun mafarkai,

Haka kawai fa Mama na gan ta ranar tsaka ta Zama haka,ko yatsa bata iya moving,ya kare cike da jimami,

Numfashi mama ta sauke sannan tace wannan lamari nata da daure Kai Babana babu komai Amman muyi ta fada wa Allah in sha Allah zai amsa ya bata lafiya,

Ameen ya rabil Alameen mama tah Bari na je 44 gurin Mujaheed tun shekaran jiya yake ta Kira nasan ya na can yana Mita na dawo ban neme Shi ba,kuna bukatar wani Abu ne,

Murmushi tayi tana me matsa kafan Nadeeya da ke bacci tace ubangiji ya kiyaye ya tsare Babana Bama bukatar komai,saidai in kana dawowa Ka biya ta Islamic chemist Ka karbo mana pure honey da man Habbatus Sauda,na gurina ya kare,

In sha Allah zan taho da su iya kan Shi kuke bukata??

Eh iya kan Shi ne Shi din ma ita nake baiwa tunda Manzon Allah da kanshi yace kuna shan Habbatus Sauda da Zuma domin yana magance ko wace irin cuta da ke jikin Ku banda mutuwa,

Haka ne kam Mama ubangiji ya Kara mana lafiya da nisan kwana me amfani Bari na je sai na dawo,

Toh ubangiji ya tsare,da haka ya samu ya fito daga dakin da kyar ya samu Zaliha ta Raba Shi da Hanan domin rikici ta Sanya Kan sai ta bishi,

Kai tsaye 44 ya nufa inda Saida ya tsaya aka gaggaisa da mutanan arziki sanann ya nufi office in Mujaheed,

A Bude ya samu kofar so shiga yayi Kai tsaye tare da sallama inda ya samu babu kowa a

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login