Showing 30001 words to 33000 words out of 79238 words
,Anty Haleemah kin san zafin ruwan nan kuwa,haka fa take tsoma towel ta nada da ruwa ta juye mun a jiki Na ko tausayi babu,
Yar nema yo ba tausayin ya sanya nake miki haka ba wlhy Na bar ki jikin naki ya rube Ameenun ya karo wata ki shiga uku,
Fatan ki ya sauka a kan ki ,Zahra tace tana hararan Baba yalwa,
Kin ci gidan ku Zahra ban son iskanci fa,Anty Haleemah tace tana ma Zahra dakuwa,baki kawai ta turo sannan tace to ni me nace kina ji fa fatan kishiya take mun tun ban tsufa ba haka kawai,
Dariya Baba yalwa tayi sannan tace oh yaran yau saidai a bar ku wlhy,ni maza zauna in turara ki ga tuwo nan da kunnun Kanwa ki sha,
Haba Baba don Allah wlhh duk yanzu an daina irin wannan abun ,turawa nawa ke haihuwa ki gan su garau ba tare da sun sha wannan bakar azaban ba,magani kawai ake basu su sha shike nan sun hade fa,sai mu nan ayi ta dirka mana wahala,
Baki bude Baba ke kallon ta,don Allah kar ki kula ta Baba rabu da ita,bara ta san gata ake mata ba,je maza ki dauki babyn tun dazu mustsu mustsu yake kila yunwa yake ji bashi nono ya dan sha kafin ki ci abincin,ta kare tana barin dakin domin Zahra sam bara ta bashi ba in har suna dakin,wai ita kunya,
Ba musu Zahran ta nufi gadon da babyn ke kwance cikin shiga Na Alfarma,bashi kam ya sha don tun dazu da nake masa wanka Na ji jikin shi da dumi kamar wani me zazzabi,Allah dai ya sa ba me laulayi aka samo mana ba,Baba yalwa tace tana barin dakin,
Zama a bakin gadon Zahra tayi tare da dauko babyn a hankali,ji tayi yayi mata nauyi a hannu kamar duk jikin sa a sake,fuskan shi take kallo,sai ta ga yayi mata wani irin haske yayi fayau da shi,yarinta ya sanya ba ta gano komai ba ta ciro nonon a hankali tare da yin bismillah ta daura mishi a baki,ganin be kama bane ya sanya hankalin ta tashi domin har bude bakin shi tayi ta sanya masa a bakin Amman be ja ba ko alaman tsotsa,
A zabure ta mike tana kwala wa Anty Haleemah kira ganin kamar yaron ma be motsi,
A rude Anty Haleemah ta shigo tana fadin ke lafiyar ki Zahra kina jego kina irin wannan ihun ,miye?ta tambaya tana kallon zahran da kallo daya za ka mata ka gane a rude take,
Hannu take yarfe wa tare da Jan baya,idanun ta har sun kada zuciyar ta Na tsanan ta bugawa,tace Anty Haleemah Anty Haleemah junior ne Na bashi nono be kama ba,
Kamar ya be kama ba Anty haleemah tace tana nufan inda babyn ke kwance,Anty haleemah sai Na ga kamar be motsi fa,
Haba Zahra daga kin karban nono sai ki ce be motsi kila baya son sha ne baran duba shi,Baba daman tace kamar da zazzabi a jikin shi,
Salati ta sanya lokacin da ta dauko yaron domin kallo daya tayi masa ta gano Sam babu rai a jikin yaron,
Jin salatin ya sanya a tsorace Zahra tace Anty Haleemah me ya samu baby na bacci yake yi ko,don Allah ki sanar mun me ya samu yaro Na ta kare tana hawaye,
Da mugun tausayin ta Anty Haleemah ta bude baki da kyar tace Zahra ke musulma ce dole ki yarda da kaddara me kyau ko mara kyau,saidai muyi hakuri Baby kam ya koma Allahn da ya bamu shi ya karbi abun shi Allah ya sa me ceto ne,
Timmmm din da Anty haleemah ta ji ne ya sanya ta juyowa,ganin Zahra zube a kasa Towel in jikin ta har ya bude ya sanya ta aje gawan babyn da mugun sauri ta nufi inda take,tana kiran sunan ta,
Ganin babu alaman numfashi a tattare da ita ne ya sanya ta kwalawa Baba yalwa kira,tare da kiran Hajiya Hafsat(mahaifiyar Zahra),
Duk an rufu kan ta amman sam numfashin ta ya kasa dawowa,a rude hajiya Hafsa tana kuka ta Kira Alhaji Salis tace ya shigo a kai Zahran Asibiti,
Hour guda aka dauka sannan aka samu numfashin Zahra ya dawo daidai Wanda saida aka sanya mata drip sakamakon Jinin ta da ya hau lokaci guda,
Ko da ta farfado kuka kawai take yi kallo daya za ka mata ta baka tausayi domin lokaci daya ta koma wani iri,rungume ta gam Alhaji salis yayi yana tofa mata addu'oi domin aljanun ta tashi suka yi,fadi take a kawo mata Dan ta wlhy be mutu ba babu abunda ya samu Dan ta,kuka sosai Hajiya hafsa ke yi domin lokaci daya Zahran komawa tayi kamar Wanda tayi karamin hauka,saida aka mata aluran bacci sannan aka samu suka sauka mata baccin wahala yayi awun gaba da ita,
Jiki ba kwari Alhaji salis ya bar hospital in,shi da Alameen Wanda idanun shi sun kada sun yi ja daga ganin alama kukan zuci yake yi,domin miscarriage in Zahran 3 kafin suka samu wannan ya zauna ta haife Dan gashi kwanan shi 3 tal a duniya Allah ya karbi abun shi,
Nasiha me shiga jiki da kwantar da hankali Alhaji salis ke yi wa Alameen har suka iso gida,inda suka tarar an gama wanke jariri,an nado shi,ganin rashin kyautuwan a kai dan makwancin shi SEN be sani bane ya sanya shi ja gefe tare da dannawa SEN kira,
Yana zaune yana cin breakfast hankali kwance kiran Alhaji salis ya shigo,saisata kanshi yayi tare da danne farincikin da yake ciki,domin ko be dauka ba hakan ya tabbatar mishi an rasa jinjirin da aka haifa,
Daukan wayan yayi bayan ya kusa tsinkewa tare da yin sallama kamar kullum,
Murya a shake Alhaji salis ya amsa,cike da kulawa SEN yace Aboki na lafiya kuwa Na ji muryan ka haka me ke faruwa ne,
Hanci Alhaji Salis ya ja sannan yace wlhy SEN rasuwa aka yi,inalilahi waye ya rasu SEN ya tambaya sounding so very worried,
Takwaran ka ne ya koma yau da safen nan yanzu ma ana shirin yi masa sallah shine nace ya ci ace ka sani,
Allahu Akbar SEN yace kamar zai yi kuka Allah sarki Ashe yaro ba me zama bane,ikon Allah ba ruwan Allah yanzu kana nufin takwara Na ya koma,ubangiji ya sa me ceto ne gani nan zuwa yanzu,da haka ya kashe wayan bayan ya gama kwararo addu'oi,
Cikin sauri ya shirya tare da fitowa,saida suka biya ta gidan Alhaji Kabiru suka dauko shi sannan suka nufi makabar tan domin lokacin har an gama masa sallah, da su aka kai yaro makwancin shi Na gaskia,wanda saidai mu ce Allah ya jikan shi ya sanya me ceton iyayen shi ne,
Ganin irin damuwar da Sen ya shiga saida Alhaji salis da Kabiru suka shiga bashi hakuri suna cewa ya dau dangana in be karfafawa Zahra ba ai bare sanya ta kuka ba,da kyar ya nutsu domin ce musu yayi shi wlhy tausayin Zahran yake ji ba kadan ba,haka aka dunga xuwa gaisuwa domin Randa aka yi haihuwar labari ya bazu anyi wa SEN takwara so duk wani mutanan sa saida suka zo taaziya,
Kwanan Zahra uku a asbiti kafin jikin nata ya fara sauki aka sallame su suka dawo Gida,
Sati guda SEN ya dauka yana zuwa gaisuwa tare da kai goma sha tara Na arziki don daukan nauyin abincin da za a ci Na mutuwar yayi,duk gurin kowa Albarka yake sanya masa ba kamar dangin Alameen da salis domin ba karamin nuna kula da damuwar shi yayi game da mutuwar nan ba,Wanda deep down kuma ba Wanda ya kai shi farinciki,
Randa suka hadu da Zahra jikin shi ba karamin sanyi yayi ba domin irin Rama da kukan da take tayi,lallashin ta yayi ta yi,tace da shi in sha Allah ko gobe ta Kara haihuwa sunan shi za ta maida,Allah kuma ya jikan wannan babyn nata da ya mutu,
Nasiha sosai yayi mata Wanda Alhamdulillah yayi tasiri akan ta domin har abinci ta ci me yawa wannan ranar, daman tun tana yarinya Allah ya hada Jinin ta da Sen haka kawai take kaunar shi zan iya cewa ma shine role model inta she look up to him,be bar gidan ba saida ya siya mata sabon mota ta mil 30 tare da biya musu ita da mijin ta Makkah da Manchester wai su Dan je hutun ko Na 3 months ne ko za ta manta da damuwar da ke damun ta,
Ba karamin dadi da godia Alhaji Salis yayi wa SEN ba yana ta sanya masa Albarka tare da yi mishi fatan gama wa lafiya,haba Aboki Na Zahra ai ya ta ce yau in ka fadi ka mutu ni ne uban ta so wannan ba wani abun godia bane,nayi mata hakan ne ko hankalin ta zai Dan kwanta, domin nasan dole ta ji ciwon abun Amman ya muka iya Allahn da ya bamu shi ya karbi abun shi Allah ya sa me ceto ne,baran wuce Hospital gurin yar ka,
Ameen ya Allah mun gode sosai SEN Allah ya bada lada,don Allah ka gaida Nadeeyan in sha Allah nima zan zo duba tan,to ba damuwa da haka suka rabu zuciyar shi cike da farin ciki,gefe daya kuma yana me Jin tausayin Zahra in,but da ya tuna nothing good ke zuwa cikin sauki ya sanya ya watsar da wani tausayin zahran at least ai yayi compensating in ta,ko gurin Allah he is sure be da wani laifi,he did it to protect his dignity,
(Ya Allah ka raba mu da son zuciya, Allah ka raba mu da son duniya,sannan ya mana tsari da cin amana ,tabbas mutanan mu sun dauki amana ba a bakin komai ba,kuma wannan a rubuce take duk Wanda ya amince da kai,ka ci amanan sa to tabbas Amana ma za ta ci ka,ina mamakin masu daukan hakki,hakkin ma Na ran Dan Adam ba tare da wata hujja ba suyi tsamanin za su ci bulus,rayuwar mu Na yanzu an maida ran mumuni Na a bakin komai ba,ya Allah,masu hali irin Na SEN Allah ka nisan ta mu da su ka kuma gyara mana halaye da kuma zukatan mu),
*************Nadeeya
A halin da ake ciki kam yanzu in akwai abun da ke gaba da hauka to Nadeeya tayi shi,sakamakon aluran da doc bashir ke dirka mata,Wanda sabida mugunta irin nashi har shock treatment ya sanya mata Wanda ya dada haukatar da ita,(Marin da SEN ya masa yake ramawa akan Nadeeya,sabida shi mugu ne shine harda sanya mata shocking),
Haaaaa Nurse Kareematu tace da Nadeeya da ke irga yatsayun hannayen ta tana dariya, ko kallon Kareematu bata yi ba,
Ki bude baki ki sha maganin ki mana, ta fadi cike da kosawa,
Harara Nadeeya ta Galla mata tare da cewa ooo,ran Kareematu ne ya soma baci tace zaki bude ko sai Na miki alura,
Jin haka ne ya sanya Nadeeya,bude baki da sauri domin ta tsani aluran da suke mata,cokalin maganin ta sanya mata a baki tana ai da baki sha ba da kin ga abunda zan miki, wai ke ga ki yar me kudi, har wani isolating in ki aka yi,banda ina samu a jikin ubanki da wlhy Rama dukan da kike mun zan nayi,
Bata kai ga rufe baki ba ta ji Nadeeya ta watso mata maganin bakin nata a fuskan ta,tana me tintairwa da dariya kamar wata karamar yarinya,
In ran nurse Kareematu sun kai dubu to duk sun baci yau,a zuciye tayi kan Nadeeya fadi take yar iska ni zaki watsa wa maganin baki,
Tashi Nadeeya tayi da gudu suka hau zagaye dakin tana wa Kareematu dariya Wanda sai binta take ita ala dole sai ta buge ta,garin bin ta da gudun ne ta harde kafafun ta sai ga ta a kasa ta fadi akan fuskanta, gwalo Nadeeya tayi mata tare da taka yatsun hannayen ta Wanda saifa ta saki Kara, ganin tana shirin tashi ne ya sanya Nadeeya nufan kofa da gudu tana dariya,
Lucky her kofar ba a kulle take ba,ganin tana ja ya bude ya sanya ta sanya ihun murna tare da ficewa da mugun gudu tana waiwayen Nurse Kareematu,
Fitowan shi ke nan daga office zai yana sauri zai nufi gidan Habeeb don ya gaiyace shi Lunch yace yayi sauri don harda masa matar shi tayi musu,(oh doc Nameer kai da Masa dai 5&6 ne Na ga alama,lol),
Waya ne a kunnan shi yana magana da Mama sai ji yayi kamar daga sama an bangade shi, Wanda saida wayan kunnan nashi ta fadi kasa,
Juyowan da zai yi don ganin waye haka ya sanya ta hardewa tayi taga taga za ta fadi da sauri ya riko waist in ta tare da manna ta a kirjin shi yana bin ta da kallon mamaki, domin daga ganin yanda gashin kanta ya rufe mata fuska ya tabbatar mishi da ita ce ya gani wannan ranar a zaune,
Jin bata kai kasa bane ya sanya ta sakin dariya cikin siririyar muryan ta tare da sanya hannu ta bude gashin kan nata in da nan take kyakkyawan fuskan ta ya bayyana,
Ya salam doc Nameer ya furta yana me zuba mata eyes ko blinking baya yi,ita din ma shi take kallo kafin can kamar Wanda aka tsikara ta fito da tongue in ta tare da lashe mishi kumatu sai kuma ta sanya dariya tare da daka tsalle,
Maganar Nurse Kareematu da ya ji a bayan su ne ya sanya shi dawowa daga Dan guntun sumar da yayi because he was totally shocked da abunda Nadeeya tayi mishi,
Go get her shine abunda Nurse Kareematu tace in da Sam Nadeeya ta ki sake Nameer daga ganin ta xaka San a tsorace take da Kareematun,domin zan iya ce wa she was so free with Nameer lokaci daya,duk da fitowa take ba,and daga ganin yanayin ta za ka san she is so depressed and scared saidai wannan childish behavior in nata da Nameer zan iya kiran shi watakil wai silan haduwar su,
Da kyar da sidin goshi aka ja Nadeeya zuwa dakin ta kuka take tana fadin ita bara ta je ba,ana yi mata injection me zafi bata so,shi dai doc Nameer Na tsaye cak har aka wuce da ita dakin ta tana mika mishi hannu idanun ta cike taf da hawaye....
[6/21, 8:37 PM] My Best Best ❤️: 😭😔UBANA NE KO KISHIYA TA💔💔
WRITTEN AND STORY
BY
NERNAH MARYAM
(MARTEY BEE)
.......
My group link
https://chat.whatsapp.com/JYJvskgTzZICC4ksRfiMlK
In har kin san ba comment bane zai shigo da ke to don Allah kiyi zaman ki,haka zalika maza kar su shigo mun cikin group domin Na mata ne zallah🙏🏻,
Ga masu son tallata musu hajar su contact me via:
08100046388
...........
Page fifteen
***********
Da kyar da sidin goshi suka samu suka sanya wa Nadeeya chain a hannun ta domin duka ta shiga kai musu ta ko ta ina, inda ta kai wa sis Kareematu wata hambara saida ta fasa mata baki sai ga jini, haka sauran workers in da suka kawo ta duk saida ta laka da musu duka saida aka mata aluran bacci kafin aka samu hankali ya kwanta,
Cike da bacin rai Kareematu ta fito daga dakin,domin kashedi Bashir ya mata kan ko me Nadeeya za ta mata be yarda ta buge ta ba in ba haka ba SEN uban su zai ci daga shi har ita,
Nameer Na nan tsaye har kareeamtu ta zo ta wuce shi,kafin ya dawo hayyacin shi,waye wannan yarinyar,me yasa ta rike shi haka,sannan wani irin injection ne suke mata Wanda take kira akwai zafi bata so,duk sune tambayoyin da ke ringing a cikin brain in shi,ganin wuce war Kareematu ne ya sanya ya bi bayan ta,domin babu me amsa mi shi wannan tambayoyin sai ita,
Da sallama ya tare ta,ganin shi ne ya sanya ta juyo a wulakance tare da kallon shi tana wani harare harare,
Sannu sister shine abunda ya fadi mata ko a jikin shi da irin kallon wulakancin da take bin shi da shi,
A yangance kamar wata yarinya karama tace hmmmm Na miji ke nan,in ce ni da kai Na,na biyo ka har office in ka amman kayi mun diban Albarka yanzu miye kake so daga guri na,ta kare tana hararan shi,
Dan karamin saki ya ja a ranshi yake fadi ji wannan kamar ce mata aka yi wani abun nake da bukata daga gurin ta,
Ka yi shiru ko baka da abun fadi nayi wuce wa ta,ta kare tana adduar Allah sa inviting in ta dakin shi ko in ce gidan sa zai yi,
Tambaya daman zan miki game da patient in dazu,wani irin tukukin bakin ciki ne ya tokare ta a kirji,wato shi ta Nadeeya ma yake ba ita ba,to wai ita me ta rasa ne da bare lura da ita ba,kyau ne ko diri bata da shi,in yayi zafi ne fa yace ta Dan fi shi a shekaru and miye a ciki ai age is just a number,ga yanda Bashir ke rawan kafa akan ta tana masa yar hali amman shi a karan banza za ta bashi jikin ta yana mata bura uba,
Tsaki ta ja sannan tace da shi ina ruwan ka da ita,ko ina ruwan ka da injection in da ake mata,patient in ka ce for your on information stay away from Nadeeya domin Doc Bashir ke handling case in ta,beside in kana da bukatar tayin da nayi maka har yanzu kofa a bude take za ka iya nema ta,Allah ya mun tsari shine abunda ya ce tare da barin gurin,
Kai tsaye motar shi ya nufa,gida direct ya wuce,takalman shi kawai ya iya cire wa tare da fadawa kan gado,
Goshin shi ya dafe tare da lumshe idanun shi,fuskan ta ke masa gizo yana kallon dariyar da take mishi,ya salam daman ita ce Nadeeya RILWANU Audu Waziri in,but ta ma fi kyau a fili Ashe akan kallon da ya mata a video in ta da ke treading ,
Shafo kumatun shi da ta lasa yayi kawai sai ya saki murmushi,lalle hauka bata yi ba,in ba hauka ba ai ko kudi za a bai wa Nadeeya ta yi mishi abunda ta yi masa he is very sure bara ta iya ba,zai iya ce wa this is the first time da wata mace ta taba shi bayan rasuwar Noor in shi,haka kawai ya tsinci kan shi cikin tunanin wani irin Alura ce haka suke mata da take cewa bata so,karan shigowar kira ne ya katse shi daga tunanin da yake yi,
Daukan wayan yayi tare da