Showing 24001 words to 27000 words out of 29481 words
wanda ze aureki kin kasa faɗa musu su uku kike so"
"Nuriya so fa ba ƙarya bane, kinsan waye Khaalif kuwa?? kinsan wace irin zuciya gareshi?? da bakina nace masa inason ɗan uwansa kina ganin baza'a samu matsala ba?? Jose yasan ina son Khaalif kamar yadda Khaslif yasan ina son Jose, sannan duka su biyun sun san inada Saif kuma sun san ze aure ni, Jose yace be ɗauki Saif a matsayin mutum ba dan haka ba komai bane a gurinsa, to ya kike so nayi dashi??, Khaalif ya fini sanin waye Saifu amma be fasa sona ba ya zanyi?? yasan ina son Jose amma be fasa ƙoƙarin samun soyayyata ba yace me nema baya gajiyawa shima kinaso na gaya masa abunda hankalinsa ze dugunzuma na jefashi cikin wani hali bazan iya hakan ba, Aminta ba abota ba itace tsakanin YUSUF da ABU na gayawa ABU ɗan uwansa yana sona abokinsa yana sona?? na gayawa Jose amininsa yana sona abun bazeyi kyau ba fa Nuriya, Komai yanada sila wata rana da sannu Allah ze kawo silar da zasu gane da kansu abun zefi zuwa da sauƙi, wani makauniyar zuciya gareshi wani baya iya jurar rashin nasara wani bashi da haƙuri kenan na tarwatsa duk wannan?? idan wani mummunan abu ya samu ɗayansu nima fa ya shafeni dan Allah kiyi nazari akan rayuwar mu"
Nuriya ta numfasa tana nazari kafin tace, "kinada gaskiya wallahi Allah ya kawo me sauƙi"
Sunsha hira sosai har yamma liƙis, duk yadda suka so ɓoyewa Umma abunda yake faruwa sun kasa dole sai da suka sanar da ita, sosai ta tausayawa Aysha kuma tayi Alƙawarin taya ta da addu'a"
Da yamma Khaalif yana zuwa shima Jose yazo ya tsikara fakin, motar tasa Khaalif ya bi da kallo yana mamakin ko waye wannan da yake goga layi dashi?.
yana cikin wannan tunanin Jose ya fito, yasha baƙin gilashin nashi na gado kai tsaye inda motar take ya nufa har sai da ya ƙwanƙwasa gilashin motar sannan Khaalif ya katse tunaninsa ya fito.
Hannu Jose ya miƙa masa tareda cewa, "barka da wannan lokaci ƙanina"
Da baze saurare shi ba amma sai ya danne ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan yace, "nayi mamakin ganinka fa daga ina zuwa ina haka??"
Gyara tsayuwa yayi tareda zare gilashin sannan yace, "gurin matata nazo zan maida ita gida"
Ƴar dariya Khaalif yayi yace, "bakaji kunyar faɗen haka ba?? matarka fa"
Jose ya murmusa sannan yace, "ehh ina mafarkin faruwar hakan kuma mafarkina yakan zama gaskiya idan Allah yaso"
Khaalif yace, "a wannan kam be zama lallai ba gara ma tin yanzu kasan me ake nufi da ɗaukar ƙaddara, amma kasan ai da wanda zata aura dan haka ka dena wannan jin kan kasa a ranka kawai ba taka bace"
Jose yayi murmushin yaro man kaza kafin yace, "na gode da tunatarwa ɗan uwa"
Suna cikin haka ta fito tareda Nuriya suna tafe suna dariya har suka ƙaraso wajen, ganin Jose yasa ta dena dariyar mamaki ya hanata cewa ƙala sai dai ta bishi da ido"
Kallonta yayi kafin yace, "ina fatan dai banyi laifi ba dan nazo maidake gida"
Murmushi tayi tana kallon gefe tace, "aa bakayi laifi ba kuma naji daɗin hakan amma dan Allah kayi haƙuri zan tafi ne tareda Ya Khaalif shi nace yazo ya tafi dani kuma dama shine ya kawo ni"
Duk da irin ɗacin da yakeji tinda yaga Khaalif ɗin amma sai ya danne yace, "shikenan zan wuce sai munyi waya ko??"
ta gyaɗa masa kai tana murmushi.
sai da ya buɗe mata gidan gaba ta shiga sannan yayi gaba yana cewa, "ƙanina ka kulamin da ita fa"
Ko takansu be bi ba ya zauna a mazaunin direba ya ɗorawa motar wuta cikin gaggawa ya fige ta a sukwane.
Sai da sukayi ƴar tafiya sanan ya samu damar cewa, "har wani murmushi kike masa kina kallo yana cin mutunci na dama kinsan hakane shiyasa kika ce nazo ko?? ashe dan ki tozartani ne ko?? meyesa bakida tausayi Aisha kin dage sai kinga bayan raina sannan zakiji daɗi bakyason farin ciki na"
ƙasa tayi da kai cikin ranta tana kuka da halin Khaalif yanzu ko zata mutu baze taɓa yarda ba itace tace su zo su duka ba ita kuwa bata da dalilin ɓatawa ɗayansu rai dan haka bazatayi abunda ransu ze ɓaci ba.
Cikin sanyi tace, "Khaalif Moh... kasan dai bazanyi hakan ba akan me zan tozartaka"
Kafin taƙarasa abunda take son faɗa ya katseta da cewa, "babu abunda zaki gaya min na yarda kinaji kina gani har wani cewa yake na kula masa dake inda na sani to tin kafin ki girma na kashe ki sai ya huta nima na huta sai kace ba tare ya ganmu ba, duk kusancin ki dashi dai nasan bekai ya ni ba kodan kinga inayin shiru kawai banajin daɗin hakan kawai ƙyalewa nake dan babu yanda zanyi dake amma tabbas da inada yadda zanyi na sauya labarin nan da na canja shi ko ta wace fuska, a gabana kike yiwa wani murmushi kina nuna masa so Ayeeshah meyesa???"
Tinda yafara magana ta rintse idonta da ƙarfi tana mai-maita a,uzubillahi sai da ya gama sannan ta buɗe idonta hawaye suka fara zuba sharrrr, kasa yi masa magana tayi sai zancen zuciya inaga ta faɗa masa gaskiyar abunda yake ranta inaga da a ranar ze aiwatar da abunda bakinsa ya furta, subhanallah Allah ka rabamu da sharrin zuciya, tsoro da firgici ne yaƙara ɗarsuwa a cikin ranta baki shike yanka wuya tabbas tinda har ya furta wata rana ze kamanta zeyi abunda bazeyi kyau ba, meyesa Khaalif yake da son zuciya ne?????"
Tambayar da ta ƙara watsawa kanta kenan har zuwa lokaci batace masa ƙala ba.
*INDO CE..*
[7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 14*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
Yana shirin cigaba da magana ta dakatar dashi da cewa, " ni kuma ba abun a tausayawa bace ko?? meyesa kake da son zuciyarka Khaalif?? uzurin wani ba uzuri bane naka ne kawai uzuri hakan shine tausayawa??"
Cikin ƙuna da raɗaɗin da zuciyarsa takeyi yace, "haka ma zakice? meyesa tinda kinsan bakya sona tin asali baki sanar dani ba?? har wancan shashashan yana rainamin hankali yana gaya min maganar da yaga dama kuma duk kinaji"
Haɗiye ƙululun baƙin cikin da ya tsaya mata a maƙoshi tayi kafin tace, " banji wata maganar banza da Jose yayi maka ba kawai daui ka tsargu da kanka ne shiyasa, yanzu fa shikenan bazaka yarda bansan da zuwansa ba ko??"
Taƙarasa maganar tana shirin fashewa da kuka.
Rai ɓace yace, "banga alamu da zasu nuna min ba ke bace kuma ya cigaba da shiga gonata wata rana baze fita lafiya ba"
Zuwa yanzu dole hawayen da take ta hanasu zubowa suka zubo, kuka ta shigayi me cin rai da kyar ta iya cewa, "Khaalif kamar ba ɗan uwanka bane Jose meyesa ka zama wani daban ne?? banaso komai ya samu wani saboda ni nima ka tausaya min Khaalif da wanne zanji? har da bakin ka kace cewa dama kasheni kayi ka huta duk saboda sharrin zuciya kayi tunani fa, kodan ni bansan kaina ba da nafara sonka tin ina ƴar ƙarama amma ka banzatar dani sai da ka rasa wadda kake so sannan zaka dawo kaina hakan ba son zuciya bane ko bazaka iya tausayina ba??, bazan dena mai-maita maka ba bansan Jose ze zo ba duk da nasan ba yarda zakayi ba amma har yanzu ban zama matar wani ba kuma ina roƙon Allah zaɓin alkairi kuma zeyi min"
Huci ya furzar kafin yace, "Ayeesha ki fahimta fa wallahi sam abunda kike tunani ba haka bane na riga na kiɗime ne narasa makama ya ɓata min rai amma dan naso wata daa ba yana nufin bana sonki bane na riga na kamu kuma nayi zurfi shiyasa nakejin takaicin ganin wani ya raɓeki, ni kaɗai yakamata na soki ba tareda kowa ba"
Katseshi tayi da cewa, "daga yau ka dena sona Khaalif tinda bakasan tausayi ba, bazan taɓa ce maka ga yadda akai ka yarda ba saboda kafiya da taurin kai, bana son wannan halayen naka Khaalif Moh.. bana son jin komai daga gareka dan Allah ka rufe mun baki kawai"
Ransa in yakai dubu ya gama ɓaci dan haka ya tarkata yayi mata banza tana fita tayi cikin gida, akayi sa'a Mama tana ɗaki bata tsakar gida tayi saurin shigewa ɗakinta, zubewa tayi gefen gado tana ƙara fashewa da wani sabon kukan, ta kasa gane yadda akai Khaalif ya kasance wani irin mutum a bai-baice.
Ranar saboda baƙin ciki da ɓacin rai ƙin kwanan gidan yayi, da ƙyar ya samu idonsa ya rintsa da sunan bacci hakan ma sai juye juye yake ya rasa inda ke masa ciwo.
sai da suka kwashi tsawon kwanaki baya ce mata ko uffan ko gaidashi tayi ciki ciki yake amsawa, hakan yasa ta shiga damuwa sosai duk taƙara figewa ta zuƙe duk ba nutsuwa a tattare da ita tafaɗa mugun yanayi, dole ta sauke duk wani jin kanta tabashi haƙuri sannan suka dawo dai-dai.
yau tin safe Aunty Maimuna ta kirata ta sanar da ita tana nemanta Dan haka ta shirya ta nufi gidan ta, a can ta tarar da Anti Bilkisu itama taje sai shan hira suke, bayan sunyi sallar azhar ne Anti Maimuna take cewa, "Aisha Mama tace akwai abunda yake damunki amma kin ƙi faɗa mata to yana da kyau mu ki sanar damu saboda barin damuwa a cikin rai bashida wani amfani, mu ki faɗa mana idan ita nauyinta kikeji"
"ba komai"
itace amsar da ta basu, juyin duniya sunyi akan tafaɗa musu koda kaɗan amma taƙi gashi abun yana cinta a rai amma taƙi gaya musu sai aikin kuka wanda daka gani zaka ƙara tabbatar da akwai damuwa jingim a cikin ranta, babu yadda suka iya dole suka haƙura suka ƙyaleta.
Yau tana zaune gaban furji tana gyarawa abubuwan ciki zama Sayid ya shigo yana dariya cike da shikiyyanci yace, "a'ah kaga Amaryar Yaya Saif abar mana furji haka tinda ba'a can bane, wallahi sai naga kamar ziyara nazo"
Ko kallon iskarsa batayi ba bare ya cigaba da tara mata takaici, ganin bata rarumo madoki ba yasa ya cigaba da cewa, "to shikenan dai tinda ban samu shiga ba, dama Yaya Saifu ne yace dan Allah ki ara masa wayarki"
Sai a lokacin ta kalleshi tareda maka masa harara cikin gatse tace masa, "sai ka ɗauka ka kai masa ai shashashan banza"
Dariya yayi yace, "aikuwa kai masa zanyi"
Bata kulashi ba dan kuwa bata son duk wani zancen da ya shafi Saifu ɗin, ta dogara da cewar wayar ta akwai key sai dai abunda ta manta dashi sai tayi minti talatin sannan take shiga key ɗin kuma ta manta ta ajiye ta a haka ba tareda ta sata da kanta ba, shi kuwa jiki na tsuma ya ɗauka yayi waje ba tareda ta sani ba.
Sai da tagama tazo nemanta taga bata gani ba gabanta ya yanke yafaɗi har ƙasa zaman daɓaro kawai tayi takasa cewa komai, tana cikin wannan yanayin Sayid ya dawo mata da wayar yace wai ya gode"
Ta ɗora hannu aka tareda zazzaro ido tace, "meke faruwa dani Sayid wayata ka kaiwa Saifu?? meyesa?? da gaske kake ko tsokanata kakeyi"
Yace, "wallahi da gaske nake ba dai shi zaki aura ba ai babu komai dan yaga wayarki, kin ajiyeta babu key ni kuwa da kikai min gatse na ɗauka na kai masa".
dafe ƙirjinta da yafara tafarfasa tayi cikin muryarta da take sarƙewa saboda shiga ruɗu da tashin hankali tace, "na shiga uku ka jefani a tara Sayid meyesa zakai min haka?? shikenan ka jefani cikin matsala"
Da mamaki Sayid yace, "wai wani abu ne a ciki wanda bakyaso a gani??"
Da sauri tace, "a cikin wayata akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali na akwai sirrina a ciki amma yanzu duk ka bankaɗe min shi ka tayar min da masifa daga bacci ina zaune lafiya kasan adadin fitinar da ka jawo kuwa??"
Har yanzu ya kasa fahimtar komai amma duk da haka jikinsa yayi sanyi ganin yadda ta kiɗime dan haka yace, "Allah ya baki haƙuri ban zata haka ba"
Kasa cewa, "komai tayi sai tagumi da ta zabga tana jiran tsammani, abun mamakin shiru babu wani motsi,
Haka ta kwana tana zullumi da fargabar abunda ze je yazo"
ba wani mamaki abun ya bawa Saif ba sai dai be zata abun nata haka yake ba ansha kiransa ace masa tana kula samari tin yana ƙin yarda har yafara yarda dan kuwa a lokacin da za ace an ganta da wani to insha Allahu idan ya kirata lokacin bata gida hakan ne yasa yaji yafara yarda amma dan neman tabbaci ya buƙaci ganin wayarta kuma yayi sa'a sai dai be zata haka abun yake ba saƙonni da kira na ABU da su yafara karo abun ya bashi mamaki sosai dan be zata ma ta iya soyayya ba ashe yaudarar sa take tanayi ta bayan fage da wani ba shi ba, a lokaci ɗaya yaji tsanar ABU ta ɗarsu a zuciyarsa lambarsa ya cira ya saka a tasa wayar sannan ya aiko mata da ta ta.
Tin a ranar ya kira ABU akayi sa'a ya amsa tareda yin sallama, be amsa ba sai cewa da yayi, "ABU kake ko waye??"
ABU yace, "eh nine lafiya dai ko???"
Jinjina kai yayi sannan yace, "eh yanzu lafiya amma rashin lafiyar ze iya wanzuwa nan gaba, naga lambarka ne a cikin wayar matar da zan aura kuma naga kana soyayya da ita gaskiya kayi ƙoƙari, to amma inaso a tsahi wasan daga haka dan bana so nayi abunda ze zo ya ɓatawa kowa rai ka janye ka ajiye makamanka ita ɗin tawace aure kawai ya rage a ɗaura"
....
ABU ya ɗan murmusa kafin yace, "akaramakallah naji duk wannan bayanan naka sai dai basu da wata fa,ida aure ya rage a ɗaura tsakanin ku kace kuma ba,a riga an ɗaura ba ba dan haka ka dena cewa takace ta me rabo ce, kuma me nema yana tareda samu babu wata barazana da zaka yimin akan Eeeshu yadda na riga nayi zurfi a cikin sonta banajin zaka iya firgita ni koda da duniya kake tafe a bayanka, lallai ka saita harshenka ka gyara kalamanka ba matarka ba matar me rabo ka gane??"
Cikin ƙunar rai Saifu yace, "kaga malam mu bama haka bansan wannan zancen jahilci da rashin ilimin naka ba, kashedi kawai zanyi maka bana son harkar ƙaramta ka fita shirgin ta tin kafin lokacin da ganinta ma ze gagare ka nasan kai ɗan uwanta ne to amma kaci darajar masu daraja amma da sai ka raina kanka, bana so abun yayi tsawo nace maka ka janye karka ƙara kiramin mata karka ƙara magana da ita tin kafin nayi abunda be dace ba zan yanke ɗanyen hukunci akanka da duk wanda yaƙara gigin son Aisha"
ABU yace, "masha Allah wannan batu naka sunyi kuma sun zauna dai-dai, amma bazan fasa ba kurarin ka yayi kaɗan yasa na janye, son Aisha ban fara ba ma tukunna ina jiranka daga yau har yaumattanad zanga abunda zakayi"
Daga haka ya katse kiran tareda furzar da wata zazzafar iska yana girgiza kansa da yake masa wani rin sarawa, da yayi musu amma yanzu ya tabbatar Aisha takusa zama matar wani, kai kawo ya shigayi a ɗakin hannunsa goye a bayansa, yanzu tunaninsa ɗaya ta yaya ze karya lagon Saif da yake wasu banzayen zantuka akansa?? haka kawai yaji be kwanta masa ba a take yasa a ransa da Saifu ya aure ta gwara kowa ya rasa shi ya rasa ƙaninsa ya rasa shima Saif ɗin ya saɓa.
Saif kuwa kallon wayar yayi cikin takaici da baƙin ciki ya sake tura kiran amma sai yaji wayar a kashe taƙi tafiya juyin duniya taƙi tafiya hakan yasa jininsa yaƙara tafasa gashi akwai maganganun da yake son faɗa amma yarasa damar yin hakan zuciyar sa sai raɗaɗi take, miƙawa Khaalif wayar yayi yace, "kaga wannan lambar nake nema amma taƙi zuwa takaici yasa nakejin kamar na fasa wayar"
Da mamaki Khaalif yace, "wace lamba ce ka matsu da kiran har kake huci haka??"
Saifu yace, "wai yarinyar nan soyayya take da wani har binsa take yana ɗaukarta a mota"
Kai tsaye zuciyar Khaalif ta gaya masa ba kowa bane yake ɗaukarta a mota face Jose, dan haka yaja tsaki kafin yace, "bari na gani ko zata shiga a tawa"
Saif yace, "ka kwafa a cikin wayata to karka kira wani bana so a samu matsala dashi nake son yin magana, har ni ze faɗawa maganar banza ya kashe waya me akai akayi shi?? me yake dashi da ze takale ni akan wadda nake so??"
jikin Khaalif har rawa yake wajen duba lambar idanun sa ne suka ƙara girma saboda tozali da yayi da lambar yayansa ABU, ya