Showing 18001 words to 21000 words out of 29481 words
mamaki da al,ajabi sai a lokacin ta samu damar cewa, "ke Aisha?? bakyason Saif dama nufinki?? kin haukace ne da kike cewa kina son mutum uku a lokaci ɗaya?? kodai kin zauce ne Aisha??"
Wasu zafafan hawaye ne suka samu nasarar Wanke mata fuska ta girgiza kai cike da tausayin kanta tace, "Wallahil azim kinji nayi miki babbar rantsuwa gaskiya na gaya miki bance ina son su ba amma jinake kowa yanada babban matsayi a zuciyata bansan so ba Nuriya saboda ni mahaukaciya ce ni ba mutumce kamar kowa ba tabbas na zauce indai yadda nakejinsu har cikin raina shi ke nufin ina son su to tabbas nagama haukacewa, bansan ina zan sa kaina naji daɗi ba dole ne ciwon tunane tunane ya kamani nan gaba ma nasan zuciyata ce zatayi tsawa ta tarwatse na mutu, be zama lallai ni me tsawon kwana bace dan ruhi na baze iya ɗaukar wannan masifar ba, Saif beyi min adalci ba beyi nazari akaina ba kawai da son zuciyarsa yayi amfani ni ban taɓa sonsa ba koda sunan wasa ban kawo a raina ba, kawai na wayi gari naji duniya ta ɗauka Saif yana sona nima ina sonsa, meyesa ze min haka?? kuma hakan be wadatar dashi ba babu zato ya kai maganar gurin mahaifina shi kuma ya amince musu ya basu ni, kawai sai naji labarin ya sauya daga batun soyayya zuwa ga aure, tin a lokacin raina ya ɓaci na gaya masa bana son sa amma yaƙi ya amince haka ya haɗani da su Antin mu sukai min faɗa nikuma wacece da zan bi ZAƁIN IYAYE NA ba?? na ajiyeshi a wannan matsayin kuma nake binsa sahu da ƙafa a matsayinsa na wanda zan aura duk hakan be burgeshi ba sai ya banzatar dani tukunna, banajin ze iya kulawa dani koda ya aureni ko a waya ba dai Saif yace bari na tuna da waccan ba sai nayi magana yace I love u na tsani kalmar nan kamar yadda na tsani Saif dalilinsa yasa naji banason jinta kuma banason auren Saif ki faɗawa wanda ranki yake so bana son sa kuma bazan so shi ba hasalima na tsaneshi na tsani auren nasa, rashin sani ne yasa
Babana ya yarda cewa ina son Saif kuma xan aureshi ne kawai saboda Babana bayan haka kuwa da ya gane ni ba tsarar sa bace"
Sallallami Nuriya ta shigayi tana tafa hannuwa, jinjina kai tayi gami da cewa, "tabb lallai ma Saifu sai yanzu na yarda bashida tausayi da imani, tabbas ya shiga haƙƙin ki ya jefa ki cikin Tara ba Uku ba, ya haneki da wanda kike so sannan ya sallama ki sai kace ance masa ke ba mutum bace??? amma ba komai akwai Allah kuma zeyi miki sakayya ko ba daɗe ko bajima, wallahi raina ya ɓaci Aisha gaskiya an zalumce ki amma sai dai kiyi haƙuri shine mafita dan bazaki tayarwa iyayenki hankali ba, amma yakamata maza su dinga tunani kuma su dinga yimana adalci dan akwai irinsa da yawa a duniya wannan ba kyautawa bace zalunci ne kuma duk wanda ya zalunci wani Allah ze sakawa mutum ƙarshe kuma abun yaƙi yimusu kyau, rayuwar aure fa ba zaman ayi a tashi bane taya yake tunanin da haka ze iya rayuwa da mace ta har abada ko ba ke ba?? dan dai kina da haƙuri ne amma in wata ce da tuni anyi an gama"
Share ƙwalla tayi kafin tace, "badan ina haƙurin ba ai da tuni anyi walle walle komai yaƙare, mutumin da yake sa ran rayuwa ta har abada dani kuma yake banzatar dani kamar abu mara amfani banajin son gaskiya ne wannan,, hmm... indai nice akwai lokacin da gaskiya zatayi halinta bazan damu kaina ba yayi kawai lokacinsa ne wata rana da kuɗi akace yayi bazeyi ba"
Nuriya tace, "Allah ya kawo muku mafita amma kuna cikin yanayi wallahi bama dai kamar Khaalif ni shi nafi tausayawa"
Murmushin takaici kawai tayi batareda tace uffan ba.
Tana zaune tana tufka da warwara kiran ABU ya shigo bin wayar tayi da ido har wani lokaci sannan ta ɗauka tareda yin sallama, amsawa yayi sannan ya cigaba da cewa, "barka da wannan lokaci kina lafiya?"
Ɗan murmusawa tayi tana cewa, "lafiya lau"
Yace, "masha Allah jiya muna magana naga kin gudu a online ina fatan dai lafiya"
Tace, "wallahi lafiya kawai dai na sauka ne"
Yace, "kenan bakyaso kiji abunda zan faɗa miki ne yasa kika gudu?"
Shiru ta ɗanyi tana tunani tabbas zata iya cewa hakan ne duba da yadda ya ɗakko zancen tasan baze wuce hakan ba shiyasa ta gudu dan batada amsar da zata bashi, a zahiri kuwa cewa tayi, "aa ai zaka ganni idan anjima kawai lokacine ban samu ba"
Da sauri yace, "ahh ba sai kin wahalar da kanki ba ba wani abun dama zance miki ba dan magana ɗaya ce zuwa biyu, nazo da ƙoƙon barata ne kuma ina fatan zan samu karɓuwa"
Shiru tayi tana sauraren sa jin tayi tsitt ne yasa ya cigaba da cewa, "Eeeshu haƙiƙa Allah ya dasa min tsananin sonki a zuciyata tin kina ƴar ƙarama har zuwa yanzu babu abunda ya canja sai ma wanda yayi gaba, na kasa ɓoye miki saboda inaso nayi rayuwa ta har abada tareda ke dan Allah kiyi tunani kafin ki yanke min hukunci zanyi farin ciki idan ya kasance na sameki a matsayin matata Eeeshu zanji kaina tamkar wanda yafi kowa sa'a aduniya nasha gwagwarmayar rayuwa tin daga lokacin da mahaifiyata ta rabu da mahaifina narasa asalin farin ciki na narasa gata da kulawa yanzu rayuwata tana buƙatar ki Eeeshu domin kece sirrin farin cikina"
Tinda tayi ƙasa da kai ko cikall takasa furtawa sai wani kurman kuka da take mara sauti sai cin zuciya da azabtarwa, babu shakka taji labarin irin mugun halin da yafaɗa a baya yayi rashi a yanzu kuwa yanada kyau ace ya samu farin ciki ita kanta zata so ta zama silar wannan farin cikin nasa tinda dai ita ya zaɓa kuma ya damƙawa kyautar zuciyarsa tareda ɗora sa rai gareta.
Katse kiran tayi ta saki wayar ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana cigaba da kuka.
ABU.
da kallo yabi wayar yana mamakin yadda akayi ta tsinke ta baya son takura mata dan haka be ƙara kiranta ba ya cigaba da tsammanin warabbuka tareda saran watarana zata amince idan Allah yaso.
*INDO CE*
[7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 12*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
"Ban damu da damuwa ta ba Ashsha damuwarki kawai itace damuwa ta koda ni nayi farin ciki nasan ke bazakiyi ba dan haka nima babu amfanin nawa farin cikin"
Rausayar da kai tayi kafin tace, "ni kam banda wata damuwa"
Ɗan murmushi yayi yace, "idan nace ki rantse zaki iya rantsewa??"
Ƙasa tayi da kai tafara wasa da ƴan yatsun ta dan kuwa bata rantsuwa akan gaibu.
Ganin tayi shiru yasa ya rausayar da kai sannan yace, "nasan kina cikin damuwa kuma ina ɗaya daga cikin wanda suka haddasa miki damuwar shiyasa gaba ɗaya banida walwala, mutane da yawa sunce na canja kuma kece kika kawo wannan canjin da ana ƙorafin bana magana yanzu kuma kowa cewa yake Jose ya canja kamar ba shi ba to wai ya ake son ganina ne?? faɗawa soyayya dama yana sa mutum ya zama wani daban ne? kodan ni mahaukacin so nake shiyasa kowa yake iya gane na susuce"
Rasa abun cewa tayi sai dai ta kalleshi ta sunkuyar da kai.
Hakan yasa ya cigaba da cewa, "Ashshah dan Allah ki amsa min tambayar nan kina so sona ko bakya sona??, Na ƙagauta da son jin wannan amsar ki faɗa min gaskiya dan Allah karki ɓoye min"
Dogon numfashi taja kafin tace, "lokaci yana tafiya fa"
lumshe idanunsa yayi gami da haɗiye mugun yawu sannan yace, "hakan yana nufin bakya sona kenan?? idan na kira ki bakya ɗauka bakya sauraron duk wani abunda ya shafeni, idan na tuna hakan zuciya takan gaya min bakya sona amma nakasa yarda bakya sona har sai na samu tabbaci daga gareki, inada damuwa sosai Ashsha ba iya Khaalif Mohammad ne yake buƙatar kulawarki ba nima ina buƙatar samun farin ciki daga gareki amma matsayina be kai nan ba, da gaske rayuwata zata ƙare a gantale da gaske mafarkin samun ki a matsayin matata da nake baze tabbata ba kenan nida farin ciki mun bawa juna baya?? da gaske bakya sona haukana kawai nake??
"hasbunallahu'wani'imal'wakil" itace kalmar da ta shiga mai-maitawa a cikin zuciyarta sabida turnuƙun zafin da take mata, da kyar ta iya dannewa tace, "kenan?? idan nace bana sonka kaima zaka yarda?? bana fatan ranar da zata zo na iya gazgata maka bana sonka"
Ɗan gyara zama yayi sannan yace, "banga alamun kina so na bane amma fa kiyi haƙuri nayi miki shigar sauri bana iya sarrafa kaina ne akanki ko abunda ya shafeki, komai yanada mahaɗin rayuwarsa shukoki da tsirrai mafi yawanci ruwa ne abokin rayuwarsu ko ga mu mutane rayuwa tana tsanani idan ba'a samun ruwa sosai kiyi tunani idan ya kasance babu shi duka fa?? rayuwar zata yuwu kuwa?? misalin hakane nakejin zata faru dani kinada muhimmanci gareni na riga nayi zurfi nayi nisa banajin kira akan sonki, so yana buƙatar tausayi da kulawa Ashshah amma ni bana samun ko ɗaya daga gareki, kin kasa yarda da irin tsananin ƙaunar da nake miki me kike so nayi wanda ze sa ki gazgata cewa na mutu akan sonki?? ki faɗa min ko mene zanyi indai be kaucewa hanya me kyau ba na shiryawa fuskantar duniya saboda ke amma narasa duk wannan damar kin kasa yarda dani kin kasa yarda ina sonki"
Tinda yafara magana kanta yana ƙasa tunanin kalamansa take wanda suke mata kamance-ce-niya da na Khaalif Moh.. ɗinta, shima yakance bata son sa bata tausayin sa ina suke son ta tsoma ranta ne taji daɗi?? ya zatayi da soyayyar mutum uku da take ƙara ruruwa a cikin zuciyarta da kowane lokaci?? shin bazasu iya tausaya mata ba suyi mata uzuri?? sai da ya gama sannan ta dago ta zuba masa idanunta da suka fara canja kamanni cikin rawar murya tace, "banajin daɗin hakan da kake faɗa Jo kenan yanzu babu wanda zan faɗawa magana ya yarda?? bazance ina sonka ka yarda ba kenan Ya Jose??, bazan ɓoye maka ba ina son Ya Khaalif kuma kaima ina sonka
Murmushi yayi yace, " amma baki taɓa faɗamin ba ko so kike zuciyata ta tarwatse?, duk da nasan Khaalif ya fini matsayi Amma ke allurar cikin ruwa ce me rabo ka ɗauka idan ba rabonka bace ko ka ɗauka sai ta sille, amma duk da haka inason ji daga gareki domin na tabbatar, yau ɗaya kuma ni kaɗai kice kina so na badan ni ba dan Allah"
tafukan hannunta tasa ta rufe fuskarta tana murmushi tareda sauke ajiyar zuciya, tace, "yanzu idan na faɗa zaka yarda??"
Yace, "da gudu ma kuwa"
Tace, " to shikenan ina sonka"
kukan da yaci ƙarfinta ne yaƙarasa kufce mata ta shiga rero shi ba ji ba gani.
Sosai hankalinsa ya tashi ya shiga tambayarta abunda ya faru amma tayi banza, da sauri ya riƙo hannunta cikin sigar rarrashi yace, " Ashsha kiyi shiru dan Allah ki dena kukan nan idan nine na ɓata miki rai ki gafarceni ba'a son raina hajan ta faru ba bazan iya yin abunda ze zamo ɓacin rai gareki ba, ki tausayawa masoyin nan naki ki dena kuka har kisa zuciyata ta buga kukan ki barazana yakewa rayuwata banaso na mutu batareda na mallakeki ba ki huce dan Allah"
ƙoƙarin dakatar da kukan ta shigayi amma takasa sai ma ƙoƙarin buɗe motar ta fita da tafarayi..
Shi kam kansa yafara kullewa yarasa meye musabbabin kukan nata, baze iya barinta ta tafi tana kukan ba dan hakan yaɗora motar kan titi ya sau tafiya.
Kai tsaye wani ɗan madai-dai-cin gida ya shiga sannan ya tsayar da motar ya zagaya ya buɗe mata, ba musu ta fito hannunta yakama yayi ciki da ita, gidan ba kowa da alamu shi kaɗaine yake karakaina a cikinsa a falon yayi mata mazauni wanda yaji ado dai dai gwargwado shima mazauni yayiwa kansa a gefenta cikin sanyi yace, "zan fi jin kwanciyar hankali kasancewarki anan bazan iya juya baya na tafi na barki kina kuka ba bansan halinda kike ciki ba zan iya rasa tunani na"
ƙasa tayi da kai cikin mamakin yadda akai ta janwowa kanta wata rundunar yanzu ba fata ba ace wani yaga lokacin da suka zo ai ta gama yawo kowa da kalar matsayin da ze ɗauki abun"
ruwa ya ɗakko ya kawo mata yace, "kisha ruwa ko zakiji daɗi"
karɓa tayi tareda yimasa godiya.
A waje kuwa yaron sa Haruna murmushin da yafi kama da na mugunta ya saki kafin ya ɗauki wayarsa ya tura kira, jimm kaɗan aka ɗauka yayi saurin cewa, "barka da wannan lokaci Oga ka gagari kowa"
A ɗayan ɓangaren wanda aka kira Oga ya saki wani murmushi tareda gyara zamansa sannan yace, "ina jinka meke faruwa??"
Haruna yace, "to Oga dai maganar gaskiya giwa tafaɗa tarko dan Ogana gaba ɗaya yanzu yafara rasa makamar aikinsa saboda yafaɗa soyayya da wata yarinya yanzu duk baya wani abun arziki a yanzun haka yana cikin gidan sa tareda ita waye ma yasan abunda sukeyi? amma babu dama mutum yayi farin ciki sai yace dan me ashe dama kowa ɗan iska ne sai dai ta wani tafi ta wani zafi"
Oga yayi dariyar sheƙeƙe ta yaro mankaza sannan yace, "zan turo maka kuɗi kaje kayi bincike ka gane ko ƴar waye sannan ina so ka sa ido akan abunda sukeyi ina buƙatar abunda idan na watsawa duniya uwarsa ma zataji kunyar fita daga gida shi kuwa idan ya fito mutane da kansu zasu gama min dashi"
Haruna yace, "Allah yaja zamanin Oga ka gagara Allah yayi maka jagora Oga"
Oga yayi dariya hehehehe yace, "Haruna kenan to ai ni akan YUSUF JOSE babu abunda bazan iya yi ba"
"Wannan haka yake Oga"
Faɗar Haruna kenan.
Da haka sukayi sallama Haruna ya cigaba da kiwon su yana lelewa a wajen dan sanin adadin lokacin da suka ɗiba atare.
Kallonsa tayi kafin tace, "JO ina son tafiya fa"
"kenan sai na bari ki tafi cikin damuwa bayan kuma nine na tsindima ki ciki??"
ya faɗa yana kafe ta da ido.
Murmushi tayi tace, "nifa na dena damuwar banaso ne Mama ta tambaya ace ban je ba"
yace, "shikenan muje na raka ki amma fa sai kin maimaita min abunda kika faɗa ɗazu"
Ido ta waro tareda cewa, "menene???"
Ɗan ƙasa ƙasa yayi saitin fuskarta yana kallonta, itama shi ta shiga kallo tin tana kallon cikin idonsa taga bazata iya jura ba hakan yasa ta sauke kallonta ƙasa laɓɓansa ta zubawa ido tareda lulawa duniyar tunani,
Babu tsammani taji yace, "INA SONKI"
Numshi ta ja tareda ƙara girman idanunta tsikar jikinta ta yarrfa yarrrr har cikin rai maganar tazo mata a bazata kuma ta firgita dan yanzu tsakani ga Allah tsoro irin wannan kalmar take.
ƴar Dariya ya shigayi ƙasa ƙasa tareda cewa, "matsoraciya ta zata haɗiye ta zanyi"
ta sauke Ajiyar zuciya murmushi ya suɓuce mata har sai da fararen haƙoranta suka bayyana.
Yace, "to ita nake so ki faɗamin amma ka zakice ba ki ba"
Miƙewa tayi tana dariya idonta a lumshe tace, "Ina sonka"
Murmushin farin ciki ne ya wanzu a tattare dashi ya miƙe tareda surar mukullin motar sa yayi gaba tana bin bayan sa.
Sai da ya tabbatar ya direta a inda zataje sannan yayi nasa guri.
Ba ita ta dawo ba sai yamma tana tafiya tana murmushi har ta isa gidan, a haraba ta tarar da Khaalid da Shahid suna hira irin ta yaro da babba, sallama tayi Khaalif ya amsa yana sakin murmushi harda ƴar ajiyar zuciya, gaishe shi tayi tana shirin wucewa yace, "jimana matar aboki na"
Dawowa tayi tana turo baki gaba.
Yace, "dama ba komai bane kawai naga kina murmushi ke kaɗai ne hala yau kinyi katari da wanda kike so Jose dan shi kaɗai naga ana yiwa irin wannan tsadadden murmushin"
Yanzu ma murmusawa tayi sannan tace, "kamar ka sani"
Sosai magana ta daki zuciyarsa a ransa yace, "shegen bakina ne ya jawomin dama ance kaza garin tone tonenta take tono wuƙar yanka ta to shima hakance tafaru, kawai shaci faɗi yayi dan murmushi