Showing 3001 words to 6000 words out of 29481 words

Chapter 2 - RINTSIN SO Book 1

Unknown   

11 Nov 2024

982

ruwa yasa yabar gidan ma baki ɗaya, tunane tunane sunyi masa cunkusss zuciyarsa cike take tafff da tsoro da fargaba wanda ya kasu gida biyu,na farko yana tsoron rasa Eeeshu na biyu kuwa shine abu mafi girma da ya ɗaga masa hankali, yanayin da ya gani a tareda ɗan uwansa haka kawai yaji yana matuƙar kishi Yana matuƙar tsoron gazgatuwar abunda zuciyarsa ke raya masa, wata rana a wayi gari ɗan uwansa ya kamu da son Eeeshu tabbas da yaga baƙar rana mafi muni, dan bayajin ze iya barwa Mohammad Khaalif ita.

Haka ya cigaba da tunaninta gaba ɗaya bashida sukuni da kallo ɗaya zaka gane yana cikin damuwa irin sosai ɗinnan yanzu abunda yafi tsaya masa arai shine INA MAFITA?????"

Yau Aisha tana zaune ta harɗe ƙafa tana danne danne, sallama yayi a ɗakin ta amsa ƙasa ƙasa.

Nemarwa kansa masauki yayi ya zauna dan bayajin yanada matsayin da za'a bashi masauki.

Cikin sanyi yace, "barka da yammaci ƙanwati"
A fizge tace, "barka dai"

Murmusawa yayi yace, "ƙanwata kowa yanada matsayi a gurinta kowa tana iya saurarar sa amma banda Mohh... ko wani laifi yayi me girma haka??"

ƙare masa kallo tayi sama da ƙasa sannan ta cigaba da abunda takeyi, cike da rashin kulawa tace, "ohh tambaya ma kake??"

Yace, " ƙanwata kinada matsaltsalu sai dai ke bakya jin magana ba kuma kya ɗaukar shawara, Ayeeshah meye rayuwar ne??, komai na maslaha fa yafi daɗi, komai idan kayi haƙuri sai kaga watan watarana komai ya wuce kamar ba'ayi ba, amma jure Iyayi da kwainanen yayan naki ya gagareki Ayeeshah"

cike da takaici tace, "Khaalif Mohammad baka da laifi, dan ance muni tudu ne ka take naka ka hangi na wani, Bana son jin irin wannan kalaman daga bakin ka Moh Khaalif, raina yana ɓaci zuciyata tana tafasa ina fusata fiye da tunaninka, hmm.. kai matsala ma idan kaji ana nemanta akazo kanka ai an tashi, bana son tsirfa ze fi kyau ka Rufe min bakinka ka tattara ka koma inda ka fito dan kafara takura min"

"KIYI HAƘURI"

jin kalmar da ta fito daga bakinsa kai tsaye yasa ta ɗago kai tana kallonsa, zatayi magana ya katseta da cewa, " me laifi Ayeeshah ina shi ina tsayawa sanya? neman afuwa shine abu mafi dacewa dashi, amma dan Allah idan babu damuwa ki amsa min wannan tambayar, Meyesa mukeyin faɗa a koda yaushe "

Tace, "laifin waye in ba kai ba? ko kanada abun cewa"
.
.
Yace, "banida abun cewa Ayeeshah wanda ya wuce neman mafita daga Allah, yasan da zamana kuma inaga a hakan yake son gani na, kinsan Ƙaddara kowa da irin tasa kuma babu me iya tsallake mata, ni da tatashi sai ta rabani da Mahaifiya ta haka Mahaifina a yanzu abunda yake sani fargaba shine tsoron ta rabani da wani sashi na rayuwata"

Da ido ta bi shi har yakai alama, ta buɗi baki zatayi magana yace, " na ƙara dasa wani surutun bari nayi waje"

Daga haka ya fice yabata guri, wani tattausan murmushi ne ya kufce mata wanda bata shiryawa zuwansa ba hasalima batasan na meye ba, Haka kawai Takejin bata gaji da ganinsa ba, tuno diramar da sukayi ne yasa taƙara sakin murmushi tana lumshe ido, take wasu tunani suka fara kelo mata, lallai anyi kutse cikin rayuwarta amma duk da hakan bata da abin cewa wanda ya wuce takai kukanta gurin Allah.


shigowar kiran Saifu ne ya katse mata tunanin tabi wayar da kallo har ta kusa katsewa sannan ta ɗauka, ba wani daɗewa sukai suna waya ba sukayi sallama tayi katantanwa da wayar zuwa gefe, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, a zahiri tace, "kowa da kalar tasa ƙaddarar amma ni nasan tawa ba me kyau bace"

Muryar Sayid ce ta katse mata maganar "Anti Aisha naji Mama tana cewa za'a saka ranar auren ku keda yaya Saifu, kai wallahi zamusha biki ai ranar kaya kala talatin zansa, kowa burin ganin wannan ranar yake Anti"

Katse shi tayi da cewa, "yayinda ni kuma nake fargabar zuwanta ba"

da mamaki yace, "fargaba kuma???"

Murmushi tayi tace, "kai yaro ne ba lallai ka fahimci me nake nufi ba, manyan mu ma bazasu fahimci irin ciwon da yake damun zuciyata ba bare kai, tashi kawai kaje Allah yayi min zaɓin alkairi kawai shine abunda zan iya cewa, amma yanzu ni kwata kwata auren Saifu baya gabana"

sosai maganganun ta suka ɗaure masa kai yakasa gane meke damunta sarai kuwa kamar yadda ta faɗa ɗin be fahimci komai ba dan haka yatashi yabata guri"


Haka rayuwa ta cigaba da garawa lokaci yana ƙara tafiya, kiran Mama ta ƙwala mata har sai da ta rintse ido da ƙarfi dan a rayuwa ta tsani kira me kamar tsawa sai taji tsikar jikinta har tashi take kanta yana sarawa, da sauri ta fita ta nufi inda Mama da Sayid harma da Shahid suke zaune kowa bakinsa har kunne, tsoro da fargabar abunda zataji ne ya kamata taƙarasa ta zauna tareda cewa "gani"

Mama tace, "Saura ƴan kwanaki bikin uwarku, bayan ƙaramar sallah"

Tace, "wa kenan?"

Mama tace, "Anti Laila mana"

Sai a lokacin ta washe haƙora cike da murna tace, "Mama zakije amma ko?"

Tace, "bikin autar guda ai dole naje banda abunki nida ƙanwata ?"

Dariya tayi tace, "to amma zaki kwana?"

Tace, "eh idan Allah ya yarda"

Ai murna a gurin Aisha ba kama hannun yaro a lokacin tafara lissafin abunda zatayi a bikin.

ana kwana ana tashi yau aka wayi gari da azumi.

rana ta goma da daddare kamar daga sama taga ABU tayi mamaki sosai Har sai da ta kasa ɓoyewa.

Khaalif ma ba ƙaramin mamaki yayi ba dan be sanar masa ze zo ba zuwan bazata yayi masa, koda ya tambayi dalili yace masa gaisuwar azumi yazowa Mama.

Mama kam tayi farin ciki sosai da sosai.
Sunyi hira sosai daga baya Maman ta fita Shahid yana shirin bin bayanta ABU ya dakatar dashi da cewa, "ƙanin ƙanwata kiramin Eeeshu kaji?"

Shahid yace, "to"

Da tsallen sa yaje ya gaya mata, ido a waje take kallonsa zuciyarta na tsalle, kardai mugun mafarkin da ta daɗe tanayi ya tabbata, taɓe baki tayi tace, "to me zanyi masa kuma?"

Shahid yace, "sai kinje zakiji"

Badan taso ba ta nufi ɗakin sai murguɗe murguɗe take, daga hanyar ƙofa ta zauna tace, " gani Ya ABU"

Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "Eeeshu badai har kin gaji dani ba daga zuwa biyu har anfara gajiya da gani na?"

Tana dariya tace, "aa"

Ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin yace, "naga daga gaisuwa ko takaina baki ƙara bi ba kodai nima na zama Jose ne??"

Tace, "wallahi aa ai naga kuna hira ne da Mama kuma kaga bazanzo na saku gaba ba dan hirar yaushe gamo kukeyi"


jinjina kai yayi yace, "lallai ƙanwata akwai hankali, nima yanzu tafiya zanyi ai"

Tace, "wai tin yanzu ka bari sai anjima"

Yace, "ƙauyen mu da nisa Eeeshu kuma dare yayi"

Tace, "to Allah ya tsare"

yace, "amin"


Shiru ce ta biyo baya har wani lokaci sannan ya ɗan saci kallonta ya murmusa sannan yace, "Eeeshu?"

Kallonsa tayi alamun ta amsa.
Ya cigaba da cewa, "Eeeshu yaushe ne zaki cika min alƙawarin da kika ɗaukar min??"

Zaro ido tayi tareda cewa, "wane alƙawari kuma ni ƴarnan??"

Ƴar dariya yayi yace, "ba wani abun tashin hankali bane fa, alƙawarin da kikayi na zama dani idan zanyi aure"

Ido ta ƙara gwalala masa arazane bakinta har motsi yake saboda son tayi magana amma kallonda ya yake mata yasa takasa furta komai, girgiza kai ta shigayi dan kuwa kwata kwata bata fahimci inda jirginsa ya sauka ba.....



(🙄😏🙄 na rasa ma kalar hararar da zan muku😂😂 wallahi nasha wuya gurin rubuta fejin nan sau uku inayi yana gogewa😥 ga murar da nakeyi😿 kuma ƙarshe ma ko sannu bazaku iya yimin ba bare comment dan naji daɗi😒, wallahi in kunga typing error ma sai dai kuyi haƙuri🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️)





*INDO CE..*
[7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 4*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*




murmushi ya sakar mata kafin yace, "ina nufin lokacin da kina yarinya kinyi min alƙawarin zama a gidana idan nayi aure"

Ƙasa tayi da kai tace, "Laah ya ABU ai kuma yanzu na girma"

Yace, "hakan ne ma yasa nayi ƙoƙarin tuna miki, nasan baki manta ba ai ko?"

Tace, "ai kuwa na manta"

Murmushi yayi ya tashi yana cewa, "zan wuce Eeeshu sai wani lokaci ko??"

Kai kawai ta gyaɗa masa dan kuwa ya barta cikin ruɗani, a inda yatafi yabarta anan ta zauna tai ta tufka da warwara.

Koda ya koma gida shirin kwanciya yayi amma baccin ya gagara, tunani ne fall cikin zuciyarsa a duniyar nan wa yake dashi wanda ze fara sanin sirrin zuciyarsa?, bashida mahaifiya mahaifinsa be damu dashi ba, waye ze jiɓanci lamarinsa? tabbas yanason zayyana abunda yake zuciyarsa ga mutum mafi kusanci dashi sai dai ya rasa wa ze tinkara, a duniya ɗan uwa ɗaya gareshi Khaalif sai dai bayajin ze iya furta masa wannan babbar maganar yana matuƙar tsoron abunda da Khaalif ze faɗa a lokacin da ya sanar masa haka kawai yakeji kamar ɗan uwansa ma ya faɗa RINTSIN SO kamar yadda shima ya kasance, sai yanzu yake ƙara tabbatarwa kansa shi maraya ne wanda yayi rashin wani babban jigo na rayuwarsa, ya rasa mahaifiya wadda itace wadda ko be faɗa ba zata gane halin da ya faɗa, a yanzu waye zeyi Alƙalanci tsakaninsa da ɗan uwansa? mahaifiyarsu ta rasu gashi ba mahaifinsu ɗaya ba babu wani wanda ze iya tausasa ɗayansu idan hakane kuwa tabbas sun faɗa garari dashi da Khaalif ɗinsa, ya tabbata da mahaifiyarsu tana na wani abun ze zo musu da sauƙi.

kuka me tsanani ne ya ƙwace masa ya shiga mazgar abunsa kamar ƙaramin yaro lallai rayuwa duniya me yayi bayan irin wahalar da yasha ta rayuwa har ya girma ga wata baƙar ƙaddarar ta ƙara riskarsa.

Haka yai ta kuka babu me rarrashinsa babu wanda yasan ma yanayi bare ya kawo masa ɗauki.

tana zaune tana karatun Alƙur'ani wayarta tafara ƙara ɗauka tayi ta zuba mata ido ganin ko wace yasa tafara murmushi ta kara a kunne gami da cewa, "Hello Rookha!"

A ɗaya ɓangaren Rookha tace, "yagarin ne Ayeeshan Yaya Khaalif"

Murmushi Aisha tayi tace, "lafiya wallahi"

Rookha tace, "ke shegiya saura kaɗan bikin Anti laila na kusa zuwa kano, wayyo Allah idan na tuna jinake kamar na mutu dan daɗi"

Aisha dai dariya ta shigayi sannan tace, "to ƙafar yawo asha biki dai"

Rookha ta ɗanyi sanyi da murnar da take sannan tace, "ba wasa fa Ayeeshah wallahi farin ciki nakeji kuma karki zata fa dan bikin nake murna, kawai dan zan haɗu da Ya ABU shine kawai farin ciki na, ina son nuna masa soyayyar da babu wata ɗiyar da zata iya yimasa ita a duniyar nan"

Laƙwas Aisha tayi jikinta yayi sanyi sosai, tausayin Rookha ya danne duk wani karsashin ta.

Jin shiru yasa Rookha tace, "lafiya kike kuwa??"

Cikin ƙarfin hali tayi murmushi me sauti tareda cewa, "lafiya mana Rookha kibari kawai ai nasan bikin zeyi daɗi Allah dai ya kaimu lokacin"

Tace, "amin ƴar uwa sai munyi waya"

Da haka sukayi sallama, Aisha tabi wayar da kallo cikin sanyin jiki.

itama Rookha mamakin sanyin da taji Aisha tayi take dan kuwa ta saba ƙwarara mata guiwa akan ABU amma yau duk ba wannan.


Khaalif Mohammad.
yana zaune ya haɗa kai da guiwa zuciyarsa tana masa wani irin tuƙuƙi da ɗaci, ya ɗan kwashi lokaci a haka kafin ya ɗago idanunsa da suka canja kala suka koma jaa ya zuba a guri ɗaya da alamu tunanin wani abu yake, ko motsawa bayayi sosai sai dai jefi jefi yakan haɗiyi wani mugun yawu, girgiza kai ya shigayi tareda cewa, "Ayeeshah ina cikin ƙuncin rayuwa ta dalilin ki meyesa kika dena SO na a lokacin da Sonki yayi min mugun harbi?, meyesa zaki nesanta dani a lokacin da nakejin kece bugun numfashi na?, Ayeeshah baki san ina sonki ba amma ni nasan ina sonki so na haƙiƙa son da ze iya tarwatsa rayuwata, zuciyata a ƙuntace take takasa bayyanar miki da abunda ke cikinta Ayeeshah nakasa faɗa miki ina sonki gashi har lokaci na yaƙare inama zan iya gaya miki ko zanji sanyi sanyi, watan wata rana zaki auri wani ba ni ba Ayeeshah ta bazan iya jura ba ya zamo wajibi gareni na nesanta gani na dake bazan iya jurar ganin ranar da zaki auri wani ba Ayeeshah.

Kasa ƙarasa maganar yayi saboda zazzafar ƙwallar da ta shiga zubo masa, Allah sarki Ummi na na rasaki narasa mahaifina yau gashi Ayeeshah zata gagareni na zama banida wani amfani dan babu wani jigo a gareni, nasan da kinanan rayuwar zatayi min sauƙi koda yaushe cikin tsanani nake Ummi nakasa sanin yaushe zan dena kukan rashi"

Wannan shine abunda zuciyarsa take gaya masa yayinda yake ƙoƙarin tsaida ƙwallarsa amma taƙi tsayawa.


Jose.
jin motsin Umma ne yasa yayi saurin soke wayar a Aljihunsa yafara zare ido da kallo ɗaya zaka gane bashi da wata cikakkiyar gaskiya.

Murmushi tayi irin na manyance sannan tace, "wayata dama na shigo ɗauka ko ka ganta??"

Shafa kai zuwa ƙeya ya shigayi yafara inda inda.

hannu ta miƙa Masa tareda cewa, "bani idan ka ganta"

Cikin in-ina yace, "ai tanaaa, gata ma a aljihu na ai"

ya faɗa tareda saurim zarowa ya miƙa mata.

Ta kalli wayar ta kalleshi kafin tace, "me kake min da waya??"

Yace, "Umma hotuna nake kalla"

Ta murmusa tareda cewa, "hotuna kake kalla ko kuma hoto??, ba yau ne farko ba fa, hala babu hotuna a wayarka?"

Ƙasa yayi da kai yana mui mui da baki da alamu magana ce me ƙarfi a bakin nasa wadda besan tayaya ze furta ba.

Zama tayi a gefen gadonta sannan tace, "Aisha ƴar ƙanwata!! yanayin tsayuwar hoton ne ya burgeka??"

Zaram yayi ya kalleta dan kuwa ta sosa masa inda ke masa ƙaiƙayi, da sauri ya zauna gefenta sannan yace, "Umma ta maganar gaskiya bana iya ɓoye miki sirrin zuciyata wallahi na daɗe ina son ƴar nan taki sai dai banajin zata So ni dan naga kamar ta fiye girman kai, wallahi Umma Mahaukacin so nake mata tabbas zan susuce idan Ashsha bata sona"

Da ido Umma ta bishi har wani lokaci sannan ta sauke ajiyar zuciya tareda ambaton sunan Allah buwayi, sai da ta lumshe ido ta buɗe sannan tace, "Jose Aisha bata da girman kai miskilanci ne ya gamu da miskilanci shiyasa karon yaƙi yin kyau, amma bata da girman kai sai dai tana da nauyin baki, baka taɓa janta da magana ba baka bata fuskar da zakaga rashin girman kanta ba shine zaka yanke hukunci? abunda zuciyarka take gaya maka ba gaskiya bane banyarda ba"

Kafin taƙarasa abunda take son faɗa ya katse ta,
Da sauri ya riƙo hannunta gami da ɗorashi kan ƙirjinsa daidai ƙahon zuciyarsa cikin wata sabautacciyar murya yace, "Umma ke mahaifiyata ce bazan taɓa yafewa kaina ba idan na faɗi maganar da kece wadda zaki fara ƙaryatawa, Umma na rantse da Ubangijin da ya dasa zuciyar da take bugawa a ƙirjina ina son Ashsha fiye da kaina, Umma idan kin ƙaryata zance na ta yaya Aisha zata yarda cewa ina sonta?? ki yarda dani ki gazgata gaskiyata dama kawai nakeso wadda zan gwadawa duniya irin son da nakewa Aisha"

Rungumeshi tayi ta shiga bubbugar bayansa ganin yadda ya burkice lokaci ɗaya, sai da yayi sanyi sannan tace, "Jose bazan taɓa ƙaryata ƙaunar ka ga Aisha ba domin nima sheda ce, ba wannan ne naƙi yarda ba ban yarda tana da girman kai ba amma tabbas na gazgata Kana sonta kuma koda yaushe ina maka add'ar samun farin ciki a rayuwar ka tareda Alkairi akan komai, ka dawo nutsuwarka Jose, Aisha bata shiga sabgar wanda be shiga tata ba haka tana jan mutuncinta dan gudun wulaƙanci, amma tana da mutunci ga duk wanda yake mutunci da ita, kaima ka jaraba ka gani kuma zakace mahaifiyarka ta gaya maka wannan, kuma hakan sirri ne wanda ba kowane yake samu ba"


(Allah sarki me uwa ɗan gata.. Allah ka rabamu da iyayen mu lafiya ka sakanya musu da mafificin alkairi ka kare su daga dukkan wani sharri ka sanya su cikin entattun bayinka, ba dan mu ba badan wayon mu ko iyawarmu ba dan Albarkacin shugaban mu Annabi Muhammad (SAW) ya Allah kayi musu jagora ka wanzar da haske a tattare dasu a duk inda suke, wanda muka rasa Allah ka jiƙansu ka wadata su da rahmarka ya Allah, (Ameen) wannan addu'a ba ni kaɗai ba har ku masoyana dan Allah kuce AMIN. ALLAH YABAMU IKON KYAUTATA MUSU)


Nannauyar ajiyar zuciya ya

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login