Showing 9001 words to 12000 words out of 29481 words

Chapter 4 - RINTSIN SO Book 1

Unknown   

11 Nov 2024

981

karki damu wata rana sai labari bazaki ganni ba Ayeeshah, amma ki dena kukan nan dan Allah banaso kina kuka saboda ni, wasa kawai nake miki amma ina neman afuwarki"

Share ƙwallar ta shigayi tana ƙara turo baki gaba.

Mama tace, "Allah wahidun, kai jama'a ke ba'a isa ace bari ki bari ba ko?? zan ɓata miki rai fa Aisha meyesa bakida kunya ne??"

Murmushi me ciwo Khaalif Mohammad yayi kamar wanda akaiwa dole yayi magana yace, "Mama ki ƙyaleta dan Allah, hakan shine farin cikinta ki ƙyaleta ko menene zatai min tayi min indai hakan ze sa taji daɗi ni me iya jure mata ne tinda ita takasa jurar nawa kwainanen"

Rausayar da kai Mama tayi tareda cewa, "toh Allah ya sauwaƙe ya kuma shirya ni dai iya haka zance"

dariyar ƙarfin hali yayi yace, "amin Mamanmu"

Lokacin Aisha tini ta shige ɗakinta tana cigaba da sharar ƙwallah dama ƙiris take jira dan kuwa abubuwa da dama sun tare mata ta rasa mafita.

Jose haka shima ya shiga laluben inda ze samu lambarta sai da ya gama shan tashi wuyar sannan ya sameta a wajen ƙanwarsu ƴar ƙanin Umman sa, sai da ya samu sannan hankalinsa ya kwanta sai dai har ila yau ya kasa kiranta.

Tsakanin shida ABU kuwa babu wanda yaƙara tayarda zancen.

Azumi ashirin da tara akayi watan sallah ya kama washe gari aka tashi da sallah.

Farin ciki a wajen Aisha biyu ya haɗe ga murnar an kusa auren Anti Laila ga farin cikin sallah, ansha kwalliya kamar ba gobe.
tsakaminta da Khaalif kuwa sai kallon kallo dan kuwa babu me cewa ɗan uwansa cikal saboda faɗan da suka sha ta shata masa rashin mutunci, tin lokacin yakejin shakkar yimata magana ba dan baya so ba sai dan gudun abunda ze je yazo ta yuwu idan ya faɗi magana ɗaya ta faɗa masa biyu masu zafi dan haka ya janye bakinsa ya kulle, maganin kar ayi kar a fara.

Ranar biyu ga sallah ma bar mata gidan yayi gaba ɗaya ya koma gidan kakarsa wadda ta haifi mahaifinsa.

Rana ta biyar ne kamar daga sama taji sallamar ABU da Jose bata wani yi mamaki ba dan kuwa ya gaya mata zasu zo ko takansu bata bi ba ta cigaba da sabgoginta, tana zaune Mama ta shigo ɗakin da fara'ar ta tace, "Aisha ku shirya su Jose zasuje gidan kawun ku sai kuje kuma kunga kun huta dama su Khadija sunata tambayar yaushe zakuje musu"

Da sauri ta miƙe tana cewa, "bari ki gani yanzu kuwa zan shirya ɗazu kuwa nida Sayid muke lissafin zuwa"

Nuriya tace, "kai amma Allah ya tsindima su a Aljannah dama yawo nakeso amma wannan matar tace yau bazata ko ina ba"

Aisha tace, "da ƙafata kike yawon?? banson ruɗanin zuci kuji iskanci fa dole sai zan fita zaki fita??"

Dariya Nuriya tayi tana cewa, "zauna sababi su gudu su barmu kinaji Mama tana sauri suke"

Murguɗe baki tayi tace, "su fi ruwa gudu dallah"

Nuriya tace, "temaka dai kiyi saurin"

Bata saurare ta ba ta cigaba da shirya.

Ba ɓata lokaci ta shirya cikin wata atamfa riga da siket ta murza ture ka ga tsiya ba wata kwalliya tayi ba daga hoda ba ƙari ko kwalli bata sa ba sai man leɓe.

Dai-dai lokacin da suka fito su ma su ABU sun fito ido ya zuba mata dan kuwa baze iya yiwa kansa shamaki da kallonta ba.

Jose kuwa sai dai satar kallonta da yake dan baya so su haɗa ido.

Kasa shiru ABU yayi yana murmushi yace, "Eeeshu irin wannan shan kyau haka?"

Yalwataccen murmushi ta saki tareda kauda kanta gefe tace, "kai Ya ABU harda zagi?"

Ido ya zaro yana dariya yace, "kaii Eeeshu ni waye da zan zageki?"

Murmusawa kawai tayi takasa magana dan kuwa ɗagowar da zatayi sukai ido huɗu da Jose kowannen su ya basar shi gaba ma yayi ita kuma sai da ta jira ABU yayi gaba sannan ta rufa masa baya ita da Nuriya da Sayid da Shaheed.

Sai da suka tsaya jayayya wajen tuƙa motar sai da ƙyar ABU ya karɓa dan kuwa Jose ya tirje baze ja ba a cewarsa shine ya kawo su dan haka dole yanzu ABU ne ze ja.

tinda suka fara tafiya batace ƙala ba sai su Nuriya da suke surutu tareda Sayid ABU da JOSE ma suna hira kaɗan kaɗan dan dukansu hankalinsu ba a jikinsu yake ba yafi karkata ga Aisha, ita kuwa tunanin yau da goben rayuwarta ya sakota gaba dan haka duk ta manta dasu sai aikin tunani take.

Daga baya ma ABU ya kunna sauti a motar dan haka kowa yayi shiru wanda be iya bin waƙar ba ma ya saurara.

har sukaje suka dawo babu wanda ta kula a ciknsu, dama Jose kasancewar ba wata magana suke ba yasa bata ce masa ƙala ba, shima be tinkari yimata magana ba dan be ga fuska ba.

har zata shige gida ABU ya katse ta da cewa, "yau ba surutu ko Eeeshu?"

Gyaɗa kai tayi alamar "eh"

Ya murmusa sannan yace, "shikenan sai wani lokacin ko?"

Yanzu ma gyaɗa kanta taƙarayi har abun yaso bashi dariya sai dai ya danne.

Ze ƙara magana Jose da takaicin yadda take saurarar ABU shi kuma ko kallo be isheta ba ya ishe shi yace, "sauri fa muke ka sani zaka tsaya surutu"

Dariya yayi kafin yace, "to naji"

bata tsaya sunyi sallama ba tayi cikin gida sosai taji daɗin dakatar dashi da surutun da Jose yayi.

bayan ta idar da sallar isha tana zaune wayarta ta ɗauka ta tsira mata ido, tunanin Saifu ne ya faɗo mata idan bata manta ba rabonsa da kiranta haka siddan wai dan suyi wata magana tin farkon Azumi, lumshe ido tayi tareda sakin murmushi me ɗauke da ma'anoni, aranta tana tunanin "anya kuwa ze iya kiran kansa masoyi? idan ma aka kirashi da sunan sai ya amsa?? kwata kwata beyi mata kama da masoyi ba, ya riga da ya gama cutar ta ya danne duk wata damar da take da ita gashi yanzu yasa ta shiga ruɗanin SO ta kasa banbance wa take so iya abunda ta sani kawai yanzu ko sunan Saifu bata cika son taji an ambata ba, idan kuwa ta tuna labarin aurensu sai zuciyarta tafara bugawa, tana matuƙar tsoro da fargaba gami da tunanin Anya kuwa ze iya riƙe ta ya bata kulawa?? batajin ze iya hakan gareta amma dan karambani ya nemi aurenta to me yake nufi da hakan?? ko dama yayi ne kawai dan cutar da ita?? zata iya zaman aure da mutum koda bata taɓa son shi ba amma banda wanda baze iya bata kulawa ba.


Langaɓar da kai tayi tareda sakin murmushin gefen baki tace, "bazan iya bujirewa iyaye na ba Saifu ta nan ne kawai ka samu tasiri a kaina, amma indai har ba da gaske kake ba watan watarana dole zaka karaya gaskiya tayi halinta a lokacin dolen ka kuma ka barni na auri wanda nake so.

Saifu kuwa shi harkokinsa kawai yake baya tunanin ma kiranta kwata kwata yafi maida hankali akan harkar kasuwancin sa shine abunda yafi bawa muhimmanci be damu da kulata ba koda ta Whatsapp ne mafi yawanci ma itace take fara yi masa magana a hakan ma wani lokacin sai yaji kamar ta takura masa.







*INDO CE..*
[7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 7*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*






kwanci tashi ba wuya gashi har lokacin bikin Anti Laila yayi Aisha sai rawar kai take tin saura kwana biyu su tafi taje ƙunshi da kitso washe gari akai mata baƙi tayi rangaɗau yayi mata kyau sosai.

Washe gari kuwa tin safe ta riga kowa shiryawa ta zauna ta cancara kwalliya kamar ba ita ba.

Suna zuwa da ABU tafara yin tozali amma sai ta ɗauke kai tayi kamar bata ganshi ba tayi gaba, Rookha ce ta katse mata tunanin ta da cewa, "barka da zuwa ƴar halak yanzu nake maganar ki wallahi!, irin wannan shan kwalliya haka gashi Yaya Mohammad Khaalif baya kusa da ya gani ya biyamu kuɗinta "

Taƙarasa maganar tana dariya.

Itama dariya tayi tareda jan hannunta suka shiga ciki dan kuwa bata son abunda ze jawo ɓacin rai tsakaninsu kuma ta lura shirye shiryen da ABU yakeyi kenan"

Da yake gwanar surutu ce Rookha ga Nuriya a gefe sai abun yayi rabajau tinda suka zo basu huta ba faɗi wancan faɗi wancan gasu duka gwanayen rawar kai ne.

Miƙewa Aisha tayi tareda cewa, "Rookha kuzo mu zagaya mana wallahi nagaji da zaman surutun nan"

fitowa sukayi suka shiga zagaye a gidan suna gaisawa da wanda basu gaisa ba, Nuriya tace, "dan Allah kuzo muyi waje mana"

Kafin ma ta rufe baki tini Aisha tayi gaba tana cewa, "sai kun tawo"

Rookha tayi saurin zuwa kusa da ita tana cewa, "wallahi jirani, wai wacece wannan ban santa ba fa"

Aisha ta murmusa tace, "dama taya zaki santa bayan zuwan ki Kano ɗaya"

Harara ta zumbuɗa mata tana cewa, "banson iskanci fa wallahi ba zuwana ɗaya ba kema kin sani"

Dariya tayi tareda cewa, "Nuriya kenan ƴar ƙanwar Baba na ce gata nan itama sahun ku ɗaya tarkacen surutu"

Nuriya tace, "kice ke bakyayi mana, a'ahh yau naji"

Rookha tace, "barta kawai iya takunta tayi, shegiya zata gayawa mutane magana"

Dukansu kawai tafiyar suke amma hankalinsu ba'a jikinsu yake ba, bama kamar Aisha da gaba ɗaya hankalinta baya kusa tunanin ta inda zata ga Khaalif Mohammad ya ɓullo kawai take.

Ba zato sai ji tayi ta bangaji mutum tayi baya taga taga zata faɗi, a zabure yace, "Ashshah!!! tareda riƙo hannun ta idanunsa a warwaje zuciyarsa tsalle kawai take dan ya gama bayarwa Taje ƙasa"

Ganin yadda ya firgice yasa ta ƙame ƙyam sai taga nata tsoron me sauƙi ne akan nasa bilhaƙƙi a gigice yake, ido ta zuba masa har wani lokaci yayinda shima itan yake kallo.

zazzafar iska ya furzar tareda lumshe ido sannan ya saki hannunta da yake cikin tafin hannunsa, a sanyaye yace, "ki dinga bi a hankali dan Allah, idan kika faɗi a tiles ɗinnan zakiji zafi sosai"

Kallon hannunta da ya riƙe tayi haka kawai ta tsinci kanta da sakar masa murmushi idonta a ƙasa ƙasa a ɗan kunyace tace, "zan kula"

Jinjina kai yayi tareda maida kallonsa ga Nuriya da Rookha a marai-rai-ce yace, "ku dinga kula da ita dan Allah"

Rookha tace, "to" kallon Aisha tayi tace, "to ƴar yaye muje sai mu dinga kula dake ko ƴar gol? tinda mu ba mutane bane"

Murmusawa yayi yana shafa kai yace, "kai hajiyar gigi ba haka nake nufi ba naga kamar bata san mutane bane shiyasa kar taje ta ɓata ta barmu da sallallami"

Dariya suka sa ita kuwa tayi ƙasa da kai takasa ce masa uffan dan ba ƙaramin kwarjini yake mata ba.

Nuriya ta gaisheshi bayan sun gama dariyar, ya amsa cikin sakin fuska tareda tambayarta yaushe suka zo ta gaya masa, jinjina kai yai sannan yayi gaba yana cewa, " ku kula fa"

Suna fita Rookha tace, "bari naje na dawo yanzu ba daɗewa zanyi ba ku jirani fa"

suka amsa da "to"

Zatayi magana muryar ABU ta katse ta, " sannun ta da zuwa Autar Mata jinjina ta ban girma, naga yau shareni ake ma an samu ƴan uwa da yawa ko??"

Dariya tayi gami da rausayar da kai tace, "ba haka bane Ya ABU kawai ina sauri ne kar Mama ta ɓace min narasa inda tayi"

Murmusawa yayi gami da cewa, "da wasa nake miki fa naga kinsha kyau sosai kamar yau itace ranar"

yayi maganar tareda kashe mata ido ɗaya.

juyawa tayi tana dariya tace, "tab ni dai ka dena ma cewa haka dan Allah"

Yace, "to na dena dan nasan ma idan ranarce kwalliyar sai tafi haka"

Nuriya tayi tsaram tace, "wallahi kuwa ai ranar dole ma na tsikari rayuwata da tsinke"

Yace, "kema dai kya faɗa"

Gaba tayi tana cewa, "Ya Allahu shikenan kuma kema biye masa zakiyi nifa ban isa irin wannan maganganun ba, sai kin tawo bazan jira ki gama zubar ba "

dariya ABU yayi yana cewa, "shikenan tinda kin tsorata nima bari nayi ciki sai kun dawo"

Nuriya ce kawai ta amsa masa da "Allah yasa"

huci Aisha ta furzar tareda jingina jikin bango tana rintse ido abubuwan da suka faru ne a yanzu suka shiga dawo mata, jikinta yayi sanyi ƙalau.

Nuriya ta kalleta ta murmusa kafin tace, "a dai bi a hankali kar a kasa mana Yaya Saifu dan na lura Ya ABU da ƙaninsa da abokinsa duk sonki suke"

Da sauri ta waro ido tana kallon Nuriya kallon tuhuma batasan lokacin da tace, "ƙarya kikeyi yarinya wallahi banason irin abunnan da kuke min Nuriya wannan ai rashin albarka ne ance miki kuma ni kaɗaice mace a duniya da dukansu zasu taru a kaina hala kin fara haukane???"

Nuriya tace, "kull!! wallahi karki sake ki ƙara gayamin kalmar hauka akan gaskiyata, ke yanzu tsakaninki ga Allah Aisha sai kice Ya Khaalif baya sonki idan kince sauran baki sani ba??, kiji tsoron Allah ki faɗi gaskiya"

Laƙwas tayi ko kallon Nuriyar taƙiyi dan kuwa ta fita gaskiya.

Nuriya kuwa ganin haka yasa ta murmusa tareda cewa, "ƙaryar banza ni zakiyiwa molanka idan baki sani ba in gaya miki ke kanki kina son Ya Khaalif kuma dukansu babu wanda zaki bugi ƙirji kice bakya son sa sai dai in ba gaskiyar zaki faɗa ba"

ajiyar zuciya ta sauke kafin tace, "dawo kan hanya mana ya kike da suna Nura kike ko Nuriya?? eh to kin faɗi gaskiya tabbas inason Ya Khalif Moh.. amma a yanzu yayi min tazara kuma shima nasan yana sona, abunda yake firgita ni kuma ina ganin yayansa ma yana so na Ya ABU ina jin tsoron hakan sosai, amma ko zaki haɗiyi zuciya ki mutu bazan taɓa yarda Ya Jose ma sona yake ba wannan ƙarya ne"

Nuriya tace, "haka kikace ko?? haka kikace ko?? to wallahi daga yanzu har zuwa lokacin da zaki gane ki rubuta wannan ki aje wallahi yana sonki, kuma idan bakiyi da gaske ba zaki faɗa rijiyar masoya me wuyar fita, dan na lura cikinsu duk bakida gwani, gaskiya ina tausaya musu ma wallahi duk fa basu san akwai kuɗin auren Yaya Saifu akanki ba ko?? gaskiya suna ruwa kawai sai dai suji abu bagatatan sun kama ganye sun saki reshe shi Ya ABU dama Rookha ɗinsa ya ɗauka yabar dakon so abanza"

Lumshe ido tayi kafin tace, "Ya ABU kam banajin ya sani amma dai Khaalif Moh.. ai ya sani tinda Ya Saifun abokinsa ne, sai dai kinsan idan mutum ya riga ya zurmawa abu nasan ya riga yayi nitso sosai, babu yadda zamuyi sai dai haƙuri dan banajin ze iya cire sona daga rayuwarsa"

Nuriya tace, "wallahi kam shiyasa nake bala'in tausaya masa yana shan azaba a dalilinki Aisha kina son sa amma kike azabtar dashi meyesa haka??"

Ƴar dariya tayi wadda da ka gani kasan ta yaƙe ce kafin tace, " bazaki gane ba fa Nuriya kimin shiru kawai, kuma daga yau har ranar da zan auri Saifu indai baki tabbatar min da gaskiyar ki ba duk abunda nayi miki ke kika siya karki manta akwai wannan yarjejeniyar a tsakanin mu kinji ko??"

Nuriya tace, "na yarda ko menene kiyi, ke nifa tin ba yau ba nake ganin tsantsar sonki a idon bawan Allahn nan amma tinda baki yarda ba shikenan wata rana zaki gazgata"

Da harara kawai ta rakata a cewarta bata da lokacin da zata ɓata wajen jayayya akan abunda baze yuwu ba.


Da daddare.
sauri sauri take dan ta cimma su Rookha da suka haɗa tawaga suna tafiya suna hira suna raha.
duk ta gama gajiya dan batada wani lokacin zama sai kace itace uwar bikin itada su Nuriya Rookha Naseera da sauransu ba zama daga can sai can su zolayi wancan su fitini wancan aikinsu kenan.


Har ta gifta ta kusa da motar dake ajiye a gefe taji ya kira sunanta cikin ƙwarewa kamar a bakinsa aka samu Ashshah duk da dama mafi yawanci shi kaɗai ne yake kiranta da sunan.

Cakkk ta tsaya takasa juyowa har sai da yace, "ina zuwa haka naga anata sauri??"

Juyowa tayi sannan tace, "inason zuwa gurinsu Nuriya ne"

takowa yayi har zuwa gabanta sannan ya tsaya yana fuskantar ta kafin yace, "baki gaji ba??"

ɗan murmushi tayi tace, "eh mana sai lokacin bacci tukunna"

Yace, "bakya tsoron ki tashi da ciwon jiki??"

Dariya tayi gami da cewa, "kai to ko nice amaryar dai ai sai haka, ni kam da nayi bacci shikenan banida wata gajiya"

Murmush yayi gami da lumshe ido tareda cewa, "Gaskiya ke ƴar baiwa ce kin ganni nan gajiyar da nayi Allah ne kaɗai yasan iyakarta, bacci nakeji so nake naje na kwanta idan kinji ana nema na ma karki ce kin ganni"

Tace, "a'a?? bacci kuma yanzu?? ai kuwa nasan dole ma Ya Abu ze neme ka ni kuma zan faɗa masa gaskiya ta"

ya marai-raice a wani irin shagwaɓe yace, "Ashshah bakiji tausayina ba dan Allah?? tinda aka fara bikinnan ban huta ba bakyaso na huta ko??"

Da sauri tace, "o'o gaskiya bance haka ba kaje ka huta abunka, nima neman inda zan huta nake amma idan ina tareda su Nuriya ai ba

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login