Showing 15001 words to 18000 words out of 29481 words
ƙaddara tasa a lokacin da nake ƙoƙarin tinkararki a lokacin aka tsayarda maganar aurenki da abokina Saifu a lokacin ne nasan me ake nufi da tashin hankali a lokacin na tabbatar na faɗa cikin ƙuncin rayuwa a lokacin nasan nashiga RINTSIN SO me wuyar war-wa-ruwa ban gama shiga gararin rayuwa ba sai da naga kin dena saurarar duk lamura na abunda ya shafeni ma bakyason ganinsa ko jinsa na yankewa kaina hukuncin haƙura ko dan abotar tsakanina da Saifu nayi tunanin sonki ze iya raguwa gareni amma sai naga kullum ƙaruwa yake har ya kaini matsayin da a yanzu bazan ita ɓoye miki ba fuskata ma tana iya nunawa nasan daa, bakisan ina Sonki ba amma yanzu nasan kin fahimci hakan dan yagama mamayata, abunda baki taɓaji a bakin Mohammad ba Ayeeshah yau kiji INA SONKI kuma zan faɗa na mai-mai-ta ko a gaba waye, kiyi haƙuri babu yadda na iya ne idan ban faɗa ba ni kaina bansan irin ruɗun da zan ƙara shiga ba bayan wannan, gashi yanzu kinyimin nisa yanzu bakyasona Saif kike so na rasaki na saki damata ta guje min ni mutum ne mara sa'a da nakasa karɓar soyayyar mace mafi kyau da daraja komai ya kwarkance min Ayeesha na"
Ko motsin kirki Ayeeshah takasayi illa baza kunnawa da tayi tana sauraron sa, babu shakka kalamansa sun ratsa ta kuma sunyi bala'in tasiri akanta sosai kalmar INA SONKI ta ɗarsu a cikin zuciyarta kuma taji tayi na'am da ita sai dai akwai ƙalu bale me girma a rayuwrta wanda shi kansa Khaalif ɗin tasan ba lallai ya iya jura ba,
Babu shakka tasani yana shan baƙar azabarta yakamata lokacin wannan yaƙare, shin duk ina Soyayyar da tayi masa a baya?? ina tsananin tausayawar da take masa??? ko waye yace tana son Saif kuwa besan Asalin Barbela ba duk da tasan kowa tunanin da yake kenan sai dai abun ba haka bane"
Tunane tunane harda marasa hujja sukai mata rubdugu, muryarsa ce ta katseta cikin sanyi yace, "Ayeeshah baki ce komai ba indai har wulaƙantani da muzguna min yana saki farin ciki dan Allah ki cigaba karki dena zan iya jurewa wata rana sai labari"...
Wasu zafafan hawaye ne suka yararo kan fuskarta sai da ta ɗanyi gyaran murya saboda cunkushewar da zuciyarta tayi sannan tayi magana, "ka dena fa, dan Allah ka dena cewa ina wulaƙanta ka Ya Khaalif zuciyata tartsatsi take min kuma ka dena tunanin bana sonka har gobe har kullum ma INA SONKA sai dai nasan bazan aure ka ba shiyasa nake nesanta da duk wani farin cikin tsakanin mu bana saurararka ina janye jikina daga gareka domin ina tsoron muyi shaƙuwar da bamuyi a baya ba sai yanzu kuma azo a shiga tsakanin mu ina tsoron hakan shiyasa ko ganinka bana son yi ni tawa ƙaddarar kenan a lokacin da na soka ba ni kake so ba a lokacin da muke son juna kuma wani ya shiga tsakanin mu"
a sanyaye yace, " ba kina son Saif ba?? karki damu dani kiyi farin cikin ki nima abunda kikeso shi nakeso ina abu da dama dan naga Saif ya saki farin ciki ina son ganin farin cikin ki shiyasa nai ta haƙur-ƙurtar da kaina dan gudun ɓacin ranki, ni me iya jurewa ko wane ƙalu bale ne akanki ki manta dani kawai".
Murmushi me ɗaci tayi kafin tace, "kake iya faɗe da bakinka?? waye yagaya maka ina son Saif? shi ba komai bane face ZAƁIN IYAYE NA har yau nakasa yarda ina son shi a iya wannan matsayin kawai na ajiyeshi"
Murmushin yaƙe yayi yace, "babu yadda muka iya sai haƙuri farin cikin iyayenmu shine namu iyayenki iyayena ne bazanso mu mayar dasu ƙananun yara ba, ki ɗauki Saif wani abu me daraja gareki hakan ze sa ki samu salama daga iyayenmu mu kasance masu haƙura da farin cikin mu domin wanzuwar farin cikin iyayenmu"
Jan numfashi tayi sannan tace, "hakan ne ma yasa nayi haƙuri na danne na karɓe shi a matsayin wanda zan aura badan haka ba da tini nayiwa kaina iyaka dashi, be bi takaina ba kawai sai jinayi ance shi zan aura"
Murmushin baƙin ciki tayi ta cigaba da cewa, "dole na haƙura dan mahaifina amma idan ni ba rabonsa bace??? uhmm... akwai lokacinda asalin masoyina na gaskiya ze bayyana har yanzu lalube muke a duhu bamusan waye ze ɗauke wasan ba, shima akwai lokacinda ze zo dole ya ƙyaleni indai ba shine Me Rabon ba kuma inajin hakan a jikina tabbas akwai wannan ranar, ranar da za'ayi tankaɗe da rairaya da yardar Allah"
Jinjina kai yayi yace, "hakane Allah yasa mu dace Ayeeahah, amma da kin faɗamin bakyason sa tin farko ai da na ɗauke ki mun gudu ko??"
Yaƙarasa Maganar yana dariya.
Itama dariya tayi sosai kafin tace, "sai kace ba namiji ba??"
Yana dariya yace, "gaskiya da kuwa son zuciya da ɓatan hanya me kyau yayi yawa"
Lumshe ido kawai tayi ba tareda tace koma ba.
Zeyi magana Rookha ta shigo da sallama tace, "Mama na nemanki Aisha"
Gyaɗa kai tayi cikin sanyin jiki.
Kallonta yayi cike da kulawa yace, "Ayeeshah tashi kije"
gyaɗa kai kawai ta sakeyi Tana son tashin amma jikinta yayi nauyi gashi bata gaji da ganinsa ba, sai da yaƙara magana tareda miƙewa tsaye sannan itama ta tashi.
Tafiya take tana haɗa hanya saboda ɗan jiri da takeji gashi idanunta kamar an watsa yaji sun wani ƙeƙashe.
Hannunta Rookha taja tana cewa, "wallahi ba ruwan Mama mu muke nemanki ina cewa ina kika shiga ashe kina can kina kashe Love"
Bata iya cewa, ƙala ba sai murmushin da baya wuce kan leɓe"
Kallo ɗaya Nuriya tai mata tagane tana cikin matsanancin yanayi dan haka tace, " yakamata muje mu kwanta wallahi"
Rookha tace, "wallahi nima nagaji dama ga wadda muke nema nan kuma mun samu dan haka mu kama mu tafi"
....
Ita lokacin ma har tayi gaba,
Sai da tasha ruwa kaɗan saboda bushewar da maƙoshinta yayi sannan ta kwanta.
Har suka gama surutunsu kowa yayi bacci ita baccin ya gagareta tunane tunane sin addabeta, har gari ya waye batayi wani bacci me daɗi ba sai juye juye da take da ƴan ƙananun mafarkai, abun ya tsaye mata a rai ainun, ta kasa babbance tsakanin Jose da Khaalif abun tambayarma menene dalilinda yasa kowa yake sonta? shin dama ana samun mace irinta a duniya wadda da namiji ya ƙyalla ido akanta shikenan? anya ma kuwa son gaskiya suke mata ba na wani abu ba??, so da yawa takanyi wannan tunanin amma idan ta tuna kalaman Jose sai taƙara jin takaraya batajin ko da wasa akwai kalmar da ya faɗa mata wadda ba gaskiya ba ta lura da gasken gaske yake har yafi Khaalif Mohammad zurmawa dan ahi a lokaci ɗaya ya bayyana mata abunda bata taɓa zata ba amma ga wanda taso tin asali Khaalif shi kuma yakasa wani motsi har saida lokacin ya wuce.
Tin safe ta tashi tayi wanka ta haɗe cikin wani lesi kalar marun me ratsin bulu kwalliyar ta-ta ba wata bace daga hoda sai man baki ko kwalli ba son sakawa take ba, Amma duk da hakan be hana asalin kyawunta bayyana ba.
Duk wannan kwalliyar da tasha taƙi sakin jiki da kowa sai ƙasa ƙasa take da ido har yanzu jikinta a sanyaye yake ko abincin kirki bataci ba a hakan ma sai da suka haɗa ta da Mama sannan ta nutsu.
Safiyya ce ta kalleta cike da kulawa tace, "amaryar Yaya Khaalif ku zo ku rakani can mana"
Nuriya ce tafara tashi tana cewa, "muje idan kika biyewa ta Yaya Khaalif ɗinnan bazakiyi wani abun kirki ba munyi wanka munyi kwalliya me muke jira??"
Miƙewa Aysha tayi tana murmushi tace, "muje nima nagaji da zama gara naje nasha iska"
Sanye yake cikin ƙananun kaya riga fara tassss da wando baƙi sai gilashi baƙi wanda ya hana ganin ƙwayar idonsa, kansa a ƙasa yake tafiya, yayinda mahaifiyarsa take gaba yana take mata baya tafiya suke cikin nutsuwa Umma tanayi masa magana kaɗan kaɗan amma yayi banza ko ɗaya be ɗauka ba dan hankalinsa ba a kanta yake ba.
tin daga nesa ta hangosu taji gabanta ya faɗi har ƙasa rage saurin tafiyar tayi saboda fargabar isa inda suke sai dai ya zama dole dan kuwa tawowa suke suna nufo su, ganin ta zuba musu ido yasa Umma ta sakar mata tattausan murmushi tareda yimata alamar tayi kyau.
Ƙasa tayi da kai tana murmushi wata ƴar ƙaramar kunya ta kamata.
Kasa motsawa tayi har suka ƙaraso wajen Umma ta tsaya tana tambayarsu inda zasuje, sai da suka gama gaisawa da kowa sannan ta durƙusa har ƙasa ta gaisheta, ta amsa cikin fara'a da kulawa gami da sa musu albarka gaba ɗaya.
ganin sunyi gaba yasa tafara sauri dan ta cimmusu, caraf taji ya riƙo hannunta, tsayawa tayi cakk ba tareda ta juyo ba, cikin nutsuwa ya juyo inda take bayan ya zare tabarau ɗin nasa ya zuba mata ido, cikin wata kasalalliyar murya yace, "juyo na ganki mana Ashshahhh!!!"
juyowa tayi kamar yadda yace amma kanta a ƙasa takasa haɗa ido dashi.
Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke gami da ƙara yin ƙasa da murya sannan yace, "Murmushin ki yakan sani cikin farin ciki rashin sa kuwa shi yake nasarar tarwatsa farin cikina ya rabani da nutsuwa ta, Kintashi lafiya??"
bata san lokacin da ta ɗago idanunta ta zuba masa ba takasa magana sai dai kallo, hakan ya bashi damar jefa ƙwayar idonsa cikin nata, lallausan murmushin sa me ƙara kashe mata jiki da jefa ta cikin wani yanayi yasaki sannan yace, "nakasa yin bacci me daɗi saboda fargaba da rashin sanin a wane hali kika kwana na saki damuwa ko??"
Ɗan riƙe kunnen sa yayi tareda cewa, "Afuwan bazan ƙara ba, na kasa sarrafa kaina ne babu yadda na iya sai na faɗa miki banida mafitar da ta wuce wannan dan idan baki sani ba ma zuciyata zata hukuntani yana da kyau na gwada miki koda kwatan-kwacin irin ƙaunar da nake miki Ashshah ko zan samu wannan damar?"
Wani dogon numfashi taja tareda sauke kallonta zuwa ƙasa a hankali tace, "......................................."
(😜🙄baza kuji ba to🤭)
*INDO CE..*
[7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 10*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
Tace, "Umma tana jiranka kaje ka rakata gida"
Gyara tsayuwarsa yayi yana murmushi yace, "tayi tafiyarta saboda itama tanason kasancewa ta tareda ke"
Ƙara yin ƙasa tayi da kai tana wasa da zoben azurfar dake hannunta idanunta sun kawo ruwa kamar wadda take jiran ƙiris ta fashe da kuka"
Cikin nutsuwa yace, "bazaki cemin komai ba Ashsha? shikenan zan wuce sai mun sake haɗuwa ko??"
Gyaɗa masa kai tayi alamar "eh"
Yace, "kije ƙawayen ki suna jiranki"
Batace ƙala ba tayi gaba yana tsaye har ta isa inda su Nuriya suka tsaya jiranta sai da ya tabbatar ta isa gurin sannan ya furzar da huci ya juya ya cigaba da tafiya.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tareda goge ƙwallar da tafara zubo mata dan gudun kar su ankara.
Rookha tace, "ke kuma daga gaisawa sai zama?? ko ance miki lokacin jiranki garemu??"
Murmushim ƙarfiin hali tayi tace, "na sani ko kuna dashi? kodan idan baku dashi ma taya zaku tsaya kuma??"
Safiyya tace, "wallahi kuwa ai Ya Jose ɗinne akwai mutunci akwai rashinsa amma ke naga taku tazo ɗaya ya fiye shan ƙamshi da yawa"
Gaba tayi tana cewa, "idan kun gama muhawarar nayi gaba, cikin ranta kuwa godewa Allah take da suka kasa gane asalin tsakaninta dashi.
Su Jose suna tafiya babu daɗewa Aisha ta dawo gurin Mama ta maƙale sai shagwaɓa a tashi a tafi gida daga baya ma fasa kuka tayi, Sosai Mama tayi mamakin faruwar hakan kuma tambayar duniya taƙi bata amsa, dan haka ta sauke alamar tambayarta akan Khaalif Mohammad dan tasan shine kaɗai wanda ze iya ɓata mata rai har tace a tafi gida.
Ba shiri Mama ta harhaɗa i nata i nata Sayid sai faɗa yake dan kuwa ba haka yaso ba kuma babu yadda ya Iya dolensa tafiya ta kamashi.
Aisha kuwa da ta tabbatar tafiyar za'ayi sai tayi murƙisisi ta dena kukan, tana shirin fita ne tayi karo da Khaalif da kallo ɗaya ta gane ba a wani nutsuwa yake ba dan haka ko kallon inda yake batayi ba, dan tasan ƙarshen zancen meyesa takeson tafiya"
Kamar yadda tayi tunani kuma hakanne tambayar da yafara jifanta da ita kenan, "meyesa zaki tafi yanzu??"
Ba tareda ta kalleshi ba tace, "inason komawa gida ne"
Yace, "na sani ai amma nan ma ai ba'a daji kike ba ko??? kodan saboda Jose ya tafi ne kema zaki tafi????"
Ido ta ware akansa tana masa kallon mamaki ya gyaɗa mata kai domin tabbatar mata da abunda ya faɗa"
Gaba tayi tana cewa, "duk daɗin gidan wasu kuwa be kai ya gidan ubana ba dan haka inason komawa can, sai ka tawo kawai"
Da ido ya rakata yana mamakin yadda ta juye lokaci ɗaya, kar dai Jose ya rushe duk wani tubalin ƙaunarsa a cikin zuciyarta"
Tunanin da yafara ɗarsuwa a zuciyarsa kenan lokaci ɗaya yaji ko sunan Jose baya so yaji an ambata wani masifaffen kishi yayi masa rumfa.
Har suka isa babu wanda ta saurara suna sauka ma ɗaki ta wuce ta kwanta.
sai bayan sati ɗaya da yin bikin sannan tafara dawowa hayyacinta shima ba warewa tayi fess ba duk ta rame tayi duhu saboda tunane tunanen da tasa wa ranta duk tambayar da Mama zatayi mata amsar ɗaya ce "ba komai"
Yau suna zaune daga ita sai Nuriya suna taɓa hira kaɗan kaɗan Nuriya tace, "nifa gaskiya yau sai kinyi min fashin baƙi, kuma kinsan akwai yarjejeniya a tsakanin mu to nabar wannan ma dan nasan yanzu kin gazgata ko kuma nace Yaya Jose ya gazgata miki yanzu abunda kawai nakeson ganewa tunanin da kike yake ƙarar dake a tsaye haka"
Tambayar tazo mata a bazata kuma tayi mata girma aka.
Shiru tayi tana wani tunanin lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi idanunta suka ciko da ƙwallah.
Kamar baza tai magana ba sai kuma tace, "tunamin makoma ta nake Nuriya ni abun tausayi ce tabbas ina tausayin kaina kuma ina tausayin wanda suke so na ina shiga tashin hankali a duk lokacin da na tuna ƙalu balen dake gabana inaga ƙarshen rayuwata ne yayi wa'adi na yaƙare shiyasa wannan wahalar ta kunno min kai, banason Saifu Nuriya kuma shi zan aura, Jose ya riga ya haukace da sona ina tsoron rayuwarsa ta ɓalɓalce saboda ni alhakinsa baze barni na rayu cikin salama ba, Khaalif ya daɗe yana azabtuwa duk saboda ni, wane hali zasu faɗa shida ɗan uwansa??, jinake inama zan mutu da na raba gardama, Meyesa wai sai ni Nuriya?? ba ni kaɗaice mace ba meyesa suke min so me tsanani ni kaɗai?? na shiga RINTSIN SO Nuriya cikinsu nakasa gane WA NAKE SO kuma wa yakamata naso?? zuciyata takasa samun nutsuwa da ɓangare ɗaya meyesa nakejin babu wanda zan iya juyawa baya a cikinsu?? "
Nuriya da ta saki baki ido da hanci tana binta da kallon