Showing 21001 words to 24000 words out of 29481 words

Chapter 8 - RINTSIN SO Book 1

Unknown   

11 Nov 2024

991

a gurinta baya wahala sai dai kowanne manufarsa daban matsayinsa daban amma neman zance yasa shi ya burkitowa kansa kaifaffar magana"

Jinsa shiru yasa tace, "Kishi kake ko???"

Da sauri yace, "ina ko ɗaya ni banida kishi ai ba kamar su Ayeesha da Ashsha ba"

Murguɗa baki tayi tace, "idan bamuyi ba waye zeyi? kaifa neman rigimar ka yayi maka yawa ana cikin kwanciyar hankali ka dinga kawo wani ƙauli da ba adi"
..

Yace, "Ayeeshah wasa fa nake miki amma kin ɗauka da gaske"

Tace, "ni kuma da gaske nake yau na haɗu da Jose"

ya Shafa kai, kawai yace, "wuce gida Ayeeshah bazan iya ji ba"

Dariya tayi tace, "ko me nace bazaka ji ba??"…

yace, "eh bana buƙata"

Tace, "idan nace ina sonka ma baka buƙata??"

Ido ya ware akanta tareda cewa, "kaii?? yaya zance bana buƙata kawai baki faɗa ɗin bane, ina sauraren ki"

Wucewa tayi tana dariya tace, "nafasa"

Shima dariyar yayi dan kuwa ko yanzu yaji daɗi amma ya sha wa kansa alwashin sai ta mai-maita.

Mama da taga ta shigo tana dariya bata tambayi dalili ba dan tasan baze wuce tace ɗanki ba.

Suna gaisawa ta shige ɗaki tafara cire kayan jikinta da nufin shiga wanka hankalinta ne yakai kan wayarta ta ɗauka tana dubawa taga kiran ABU har guda biyar wanda da alama tana hanya yayi mata su, da sauri ta bi kiran tana murmushi har ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka,
Sun kwashi lokaci suna wayar kafin sukayi sallama sannan ta nufi ɗakin wanka sai yauƙi take tana murmushi takunta ma kansa ya canja.

Mama dai ta ƙare mata kallo ta riƙe haɓa tareda cewa, "oo yau naga abunda na gani Aisha Indo kin koma macijiya ne?????"










*INDO CE..*
[7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 11*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*












Sai da tayi kuka sosai sannan ta tashi badan ya isheta ko ta gajiya da yinsa ba sanin bazeyi mata maganin komai bane yasa ta barshi ta tashi.

Cikin sanyin jiki ta ƙarasa gurin Mama ta lafe a bayanta jefi jefi takan sauke ajiyar ziciya, Mama tace, "ya rasulullah Aisha meke damuwarki ne haka kin ɗai-ɗaice a tsaye amma kina cewa ba abunda ke damunki idan baki faɗa min ba wa zaki gayawa damuwarki??, yanzu ma fa da alamun kuka kikai"

Lumshe ido tayi tana murmushin ƙarfin hali tace, "Mama cikina ne yake ciwo fa shiyasa duk na yamutse".

Da yake ba me jan zance bace sai kawai tace, "to Allah ya sauwaƙe kece bakyason shan magani sai kinfara ciwon cikin kuma ki ta mita"

Ƙara kwantar da kai tayi Kafin tace, "gobe idan Allah ya kaimu zam koma aiki insha Allah"

Mama tace, "Allah ya yarda".

da amin ta amsa sannan tayi shiru tafara tunane tunane ABU shine yake mata yawo a cikin tunaninta tabbas ze ga rashin kyautawarta da ta katse masa kira kuma bata ƙara bin takansa ba batasan halin da yake ciki ba anya kuwa ta kyauta masa??.

zumbur tayi ta tashi kamar wadda aka tsikara tayi ɗaki Mama ta rakata da ido cikin ranta tanayi mata add'ar samun sauƙi da rangwame daga duk wani abunda ya tsananta mata har ta koma kamar susutacciya haka"

Wayar ta ɗauka hannunta har kakkarwa yake ta lalubo lambarsa amma sai ta kasa kiransa sai da ta ɗebi lokaci a haka sannan ta canja shawara ta koma wajen tura saƙo tafara rubutu kamar haka, "Amincin Allah ya tabbata gareka ma'abocin murmushi ina fatan kana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, naji ba daɗi sosai kasancewar na katse maka kira ina neman afuwa gareka mutum me daraja da girma a gareni inaso ka sani ko ba yau ba kana da babban matsayi ga Eeeshu kuma ƙaunarka ta samu rinjaye akaina zuciyata ta alaƙantu da kai kuma ina barar sama maka farin ciki a koda yaushe, ina so ka kwantar da hankalinka banaso kayi damuwa hakan ze sa naji kamar bazan iya yafewa kaina ba"

Ta karanta ta mai-maita yakai sau huɗu share ƙwallar da take zirya a kumatunta tayi sannan ta tura shi, tana turawa ta ajiye wayar tareda jan dogon numfashi.

har ABU ya fitar da rai zata saurare shi a lokacin sai kuma yaji wayarsa ta motsa ya ɗauka ya duba, karo yaci da saƙon ya shiga karantawa jiki na tsuma a gefe guda kuwa yana cike da fargabar yaji tace be samu shiga ba, ƙafafunsa ne suka gagara ɗaukarsa har sai da ya durƙusa kan guiwoyin sa yana ƙara karantawa, rungume wayar yayi tareda lumshe idanunsa da suke masa zafi wasu sanyayan hawaye suka samu nasarar gangarowa, "Alhamdulillah" yafaɗa sannan ya cigaba da cewa, "ina godewa Allah a bisa ni'imomins gareni, banyi zaton haka daga gareki ba Eeeshu kuma insha Allahu zan cigaba da sonki fiye da kaina zan shimfiɗa rayuwata domin taki rayuwar"

Ya daɗe a gurin yana murmushi shi kaɗai kafin ya mayar mata da martani.

Bata kusa dan haka bata sani ba har sai dare ta ɗakko tana dubawa ta ganshi buɗe saƙon tayi tana binsa da ido "ina godiya gareki ƴar Aljannah kin sani farin ciki fiye da yadda nake tunani, na daɗe ban shiga cikin farin ciki irin na yau ba saboda jin tausasan kalamai akaina daga gareki Hayati ki huta lafiya"

idanunta ne suka ƙara girma yayinda take tambayar kanta wai me tace masa?? sai da taƙara karantawa ta gani sannan ta saki murmushi shaf ta ma manta me tace masa dan kuwa a lokacin idonta arufe yake ta shagala da son taga ta faranta masa, " kuma da gaskene har cikin rai abunda ta faɗa??" lallausan Murmushi ta saki tareda gyaɗa kai ta bawa kanta amsa, "tabbas hakane ba gaibu bane kin faɗa masa gaskiya a hakan ma baki baze iya furta iya matsayinsa gareki ba"

Kasancewar Nuriya ta koma gidansu yasa takejin duk ba daɗi dan haka kamar yadda ta faɗa tin da wuri ta shirya tsaff domin tafiya aikin, ta fito sai sauke rumfar ido take a hanyar fita tayi katari da Khaalif ido ya zuba mata kafin yace, "barka da warhaka ƙanwata"

A ɗan fizge tace, "ina kwana??"

Ya amsa da "lafiya lau ina zakije haka"


Amsa ta bashi sannan ya kuma cewa, "badan ina sauri zan fita ba da na kaiki da kaina amma ki kulamin da kanki dan Allah, da da yadda zanyi na hana kowane namiji ganinki da nayi dan ke macece me daraja ba kowane ido ne ya kamata ya sauka akanki ba"

Murmushi tayi tareda cewa, "insha Allah zan kula"

Har tayi gaba da nufin fita ya katse ta, murya ƙasa ƙasa yace, "dama ni kaɗai ne masoyinki duk faɗin duniya da nazama tamkar sarki"

Lumshe ido tareda cewa, sai munyi waya ko??"

Gyaɗa kai yayi sannan yace, "karkiyi nesa da ita har na kira ban samu ba"

Tace, "to"

Daga haka tai gaba ba tareda ta tsaya sauraron abunda ze ƙara faɗe ba.

tana fita titi ta samu adai-dai'ta sahu ta hau.
Aikin tunani kawai take tayi zugum, muryar direban ce ta katse ta, "dan Allah ranki ya daɗe zan ɗan shiga gidan mai idan ba damuwa"

Batareda ta kalleshi ba tace, "ba komai"

Kutsa kai yayi zuwa gidan man yana shiga wata baƙar mota me baƙin gilashi ta tare masa hanya dan haka ya tsaya yana shirin yayi magana Jose ya fito hakan yasa ya janye bakinsa yayi tsitt.

Bata ankara dashi ba har ya ƙaraso sai muryarsa taji yana cewa me adai-dai-tar "sannu fa" maza Rayyan a mayar min da ɗaya motar gida zan ƙarasar da ita da kaina"

Wanda aka kira da Rayyan yace, "angama yallaɓai"

Da mamaki ta kalleshi ta kalli me adai-daitar kenan ma shine ya turoshi?? ta jefawa kanta tambaya"

Hannu ya miƙi mata tareda binta da kallon da yasa taji jikinta ya mutu lokaci ɗaya, yau duk bashi da wata walwala ko da can da basa magana zata iya cewa bata taɓa ganinsa cikin irin wannan yanayin ba shi mutum ne me yawan fara'a maganar ce dai sai anga dama"

Kallon ido cikin ido suka shiga korawa juna ganin takasa motsi yasa yace, "a hanya muke mun tare mutane"

Hannun nasa ta bi da kallo kafin ta ɗora nata hannun, riƙeta yayi gam sannan ta sakko sai faman kallonsa take batada burin da ya wuce jin dumuwarsa dan ganinshi hakan beyi mata daɗi ba.

gidan gaba yace ta shiga sannnan ya zagaya yafara jan motar, shiru ce ta biyu baya har wani lokacin kafin yace, "narasa hankali da nutsuwa ta saboda rashin sanin laifin da na aikata kike hukuntani ta wannan hanyar"
....

Ɗago idanunta tayi ta zuba masa har ƙasan zuciyarta tana jin ba daɗi sai dai abunne yai mata yawa dan haka ta ajiyeshi gefe, tin da suka dawo daga biki sau ɗaya ya kirata ta amsa bayan haka kuma bata ƙara amsawa ba bata saurareshi ba"..

A hankali ta shiga motsa laɓɓanta tafara magana cikin muryar da bata fita sosai, "babu abunda kayi min, tayaya kasan cewa zan fita yau??"

Kai tsaye yace, "laifi ne dan nasan duk wani motsin matata?? tinda ke kin kasa gayamin kinga ai yanada kyau na gane da kaina??"

Ƙasa tayi da kai har suka isa takasa cewa uffan shima be ƙara magana ba.

Kallonta yayi a tausashe yace, "munzo "..

Taune gefen leɓenta tayi tareda rintse ido ta haɗiye ƙululun da ya tsaye mata a maƙoshi, cikin sanyi tace, "Jo meyesa ka dena murmushi?? rashin fara'a ba ɗabi'ar ka bace, dan Allah ka dinga farin ciki mana "

taƙarasa maganar cikin marai-rai-cewa.







*INDO CE.."*
[7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)



*Shafi na 13*



Aƙalamin
*INDO CE..*


ELEGANT ONLINE WRITER'S




*Bismillahirrahmanirrahim*







tintsirewa tayi da dariya tana cewa, "Mama nice na zama macijiya kuma??"

Mama ta rausayar da kai kafin tace, "tohh Aisha naga tafiya kike kina lanƙwashewa kamar almara me kika koma ne?? meke damunki duk kika susuce??"

Turo Leɓen ta na ƙasa tayi a shagwaɓe tace, "Mama nifa babu komai fa"

"to Allah ya kyauta" kawai Mama tace ta cigaba da abunda takeyi.

Haka rayuwa take tafiya koda yaushe babu canji sai ma abunda yayi gaba, da tagama magana da wancan zatayi da wancan.
Indai har zata fita to tabbas zata ga Jose kwatsam tin tana mamakin ganin sa har ta dena ta kuma saba da hakan har tsammatar ganinsa take,
A ɓangaren ABU ma kullum shaƙuwar su ƙara gaba take, idan akace Khaalif kuwa ba'a magana, yanzu ba faɗa sai ɗagwarmashi iri da kala kasancewar ba tsirr yake wuni a waje ba in ya fita yasa suke samun damar zama su sha hira sai dai har yau basu bari Mama ta gane akwai wani abu a tsakanin su ba.

Yau kam tuburewa tayi akan sai taje gidan su Nuriya da MaMA ta hana Sai da Khaalif Mohammad yasa baki sannan ta amince, bayan ta gama ɗaskwara kwalliya ta fito tana yalƙi tace, "Mama sai na dawo"

Mama tace, "Allah ya tsare ki kula fa banason sakarci"

Ta amsa da "amin insha Allah"

Tana fitowa kai tsaye inda yake da mashin ta nufa da kyar ta hau baya saboda ba iyawa tayi ba shi dai aikinsa dariya ce yanda kasan zatayi wani babban yaƙi.

Sai da suka fara tafiya sannan tace, "gaskiya hawa mashin akwai wahala Ya Khaslif da yamma idan zaka zo ɗakko ni kawai ka ɗakko motar Mama dan Allah"

Yace, "shikenan???"

Tace, "akwai wani abu ne bayan hakan"

Yace, "ai nima tambayar da zanyi kenan to amma dai ba komai Allah ya kaimu"

Murmusawa tayi tace, "neman magana dai??"

Yace, "Ayeeshah kece kika sabar min da hakan idan ban tsokane ki ba banajin daɗi kin riga kin shagwaɓani da hakan"

Dariya tayi sosai kafin tace, "ka yarda in dai-daita ka??"

Da sauri yace, "aaa ban shirya mutuwa ba kiyi shiru kawai kar kunnuwa na su kurumce dan sun san jan gashi zan ɗauka kafin na dawo dai-dai"

Tace, "oh da kace eh kawai da sai na maidaka ajin farko na fara baka horo"

Yana dariya yace, "wallahi banaso iya horon da nasha a baya ma ya isheni baki san sauran mutuwa bane ni ko?? ƙiris nake jira, kuma ina so mu mutu tare mu rayu tare"

shiru ta ɗanyi kafin tace, "ta yuwu zamu mutu tare amma rayuwa tare ina jin kamar baze yuwu ba aure na da Saif lokaci kawai ya rage kuma banajin ze fasa, ko bama wannan ba inada wata matsala a rayuwa wadda ko kai ba lallai ka iya aure na ba, Khaalif Moh.. kawai ka ganni ka barni a yadda ka ganni amma ina da damuwa wadda takasance sirrin zuciyata ne babu wanda zan gayawa yayi min maganinta Na riga na cutu Khaalif"

Taƙarasa maganar tana sharar ƙwallah.

jikinsa yayi sanyi lokaci guda duk wani farin ciki da walwalarsa suka gushe, ya kasa gane inda kalamanta suka dosa shin me take nufi da hakan?? wannan wace irin damuwa ce?? wace matsala gareta wadda har take tunanin baze iya aurenta ba saboda wannan matsalar???.

Tambayoyin da suke masa yawo a tunaninsa kenan, muryarta ce ta katse shi cikin muryar da take ƙara tabbatar da irin tsananin damuwar da take ciki tace, "Ya Khaslif indai har kana sona da gaske Karka sa wannan tunanin a ranka damuwa ce wadda ta shafeni ni kaɗai ko iyayena ma na ɓoye musu ita dan gudun ransu ya ɓaci kabarni na cigaba da dakon abata ni kaɗai kamar yadda na taso da ita har na girma, A gaskiyance babu wanda ya dace da aure na kamar Saif bayanshi cikin ku duk wanda na aura na cuceshi ne dan ba kowane hankalinsa ze iya ɗauka ba"

Saboda tsabar ruɗanin da ya shiga kasa magana yayi sai mai-maita zancen nata yake a cikin ransa, har sukaje basu ƙara magana ba, bayan ya temaka mata ta sakko daga mashin ɗin kasa tafiya tayi saboda bata son rabuwa dashi sai faman kallonsa take cikin sanyi tace, "Khaalif Moh.. a rayuwa kowa da kalar tasa ƙaddarar kuma babu me iya tsallake ta kai nice ƙaddarar ka amma ni nawa ƙaddarorin da yawa ba iya soyayya ce damuwa ta ba, gaba ɗaya tubalin rayuwata ya gino ne akan damuwa ƙaddarata mummunar ƙaddara ce wata rana ma nasan dole zaku gujeni, ina sonka Khaalif har cikin ƙoƙon raina"

Daga haka ta shige cikin gidan su Nuriya tana sharɓar kuka ta barshi a tsaye da sakakken baki, har yanzu ko da wasa tunanin sa ya kasa bashi ma'anar maganganunta amma yasa a ransa tabbas akwai wani gagarumin abu a rayuwarta sai dai baze damu da hakan ba tinda har tace bata so ya damu amma koda yaushe ze kasance cikin tunani da jefawa kansa tambayoyin da yasan bashi da amsar su.

ya ɓata lokaci a wajen yana tunani sannan ya ɗau hanya.

A cikin gida kuwa Umman Nuriya tana zaune tana wanki Aisha tayi sallama cikin rawar murya, amsawa tayi tana binta da kallon tuhuma.

Nuriya ta bugo tsalle daga ɗaki tana murna, ganin tana kuka yasa tayi turusss tana tambayar lafiyarta.

Umman Nuriya ma tambayar da tafara yimata kenan, bata amsa ba sai share hawayen da tayi tana murmushin ƙarfin hali tace, "sannun ku da gida Umma"

Umma ta amsa da
"yauwa"

Sai da ta zauna sannan suka gaisa Nuriya ta ja ta zuwa ɗaki suka zauna, kallonta tayi da mamaki tace, "meye na kuka kuma??"

murmushi me ciwo tayi tace, "Nuriya bari kawai ni kuka ya kama a rayuwa ta akwai tangarɗa akwai ƙalu bale da tarin yawa a rayuwata"

Gyara zama Nuriya tayi sannan tace, "haka kawai ina tausayin ki Aisha nima nasan akwai damuwa sosai gareki amma kinada kafiya juyin duniya kin ƙi gayawa kowa abunda yake saki kuka tin daga ytintar ki har zuwa yanzu"

Tace, "ai daga lokacin ƙuruciyar ne labarin yafara ban kuma san yaushe ne ƙarshen sa ze zo ba"

Nuriya tace, "ki tuna fa koda yaushe lokaci tafiya yake tabbas ƙarshensa ze zo sai dai fatan yazo mana da kyau dan har yanzu bamu san mene labarin ba"

Tace, "nima a koda yaushe fatana kenan yazo min a ƙarshe me kyau"

Nuriya tace, "wallahi Aisha idan labarin ki naji a garari bazan taɓa yarda gaske ba sai gashi ina gani a kusa dani, son gaske ba na wasa ba kuma mutum har uku"

Aisha tace, "shiyasa nake tuhumar kaina ko nayi wani saɓon da Allah ya jarrabe ni da wannan mugayen iftila'in Nakanji kamar ni ba mace bace ko kuma ni ba mutum bace"

Numfashi Nuriya ta ja sannan tace, "kuma kin kasa faɗa musu gaskiyar akwai

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login