Showing 12001 words to 15000 words out of 29481 words
hutu"
Yace, "to tinda hakane na ɓoyeki kiyi baccin ki hankali kwance ki ƙyalesu ranar da suka gama nasu sai su kwanta"
Dariya ya bata dan haka ta dara sannan tace, "lallai kam kai da kakejin bacci ina kai ina ɓoyeni nayi bacci?? ai kuma nima indai zanji motsinsu bazan iya baccin ba, ka samu kaje ka kwanta kawai"
Rausayar da kai yayi yana ƙarayin ƙasa ƙasa da murya yace, "anya kuwa?? zan iya bacci bayan ke baki rintsa ba anya kuwa son kan beyi yawa ba?"
Girgiza kai tayi tace, "a'ah babu komai wallahi ko ɗaya kar kayi laka'ari dani dan zaka iya kwana bakayi bacci ba kuwa "
Cikin wata narkakkiyar murya yace, "Ashsha bazan iya ba, tinda kika riga kika gayamin kinason yin bacci nima bazanyi ba har sai naga kin nutsu ba iya kwana ɗaya ba koma kwana nawa ne zan iya jura ko bazan kai ba dole na in jarraba"
numfashi taja ta sauke tana kallon gefe a take tunanin yadda sukayi da Nuriya ya dawo mata hakan yasa tayi sauri ɗagowa tana kallonsa ganin yayi mata rumfa aka yasa taƙara zaro ido sai a lokacin ta lura da wayo da wayo ya dawo da ita baya har ta dangana da jikin motarsa kuma yayi mata kaka gida ta yadda bazata iya sillewa ba"
Ɗan murmushi ya saki tareda shafar ƙeyarsa yana lumshe ido ya lura mamakin ta yadda akai yayi mata hakan take duba da yadda take kallonsa ta kalli gefe da gefe, yasan halinta sarai bata son tsayawa ta saurari mutum kanayi mata magana tanayin gaba musumman idan ta zumuɗanta da wani abun dan haka yayi mata wannan dabarar kuma ta rufta cikin sauƙi"
Buɗe idonsa yayi akanta gami da cewa, "zaki rakani??"
ƙasa tayi da kai tace, "ina kenan?"
Kai tsaye yace, "bakin titi zaki rakani amma fa idan ba damuwa"
Shiru ta ɗanyi kafin tace, "to zanje naga ma sun gudu sun barni nima kuwa bazan zauna ba"
Murmushi ya saki a ransa yace, "iyayen son yawo ba"
buɗe mata gidan gaba yayi ta shiga sannan ya zagaya mazaunin direba
(Team Khaalif Mohammad How Market😂😂😂😂😂😂😂🤣)
*INDO CE*
[7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 8*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
Ajiyar zuciya ta sauke saboda daddaɗan ƙamshin da ya risketa ta lumshe ido tareda jan numfashi ta sauke.
Ta gefen ido yake kallonta ya lura hakan yayi mata daɗi dan haka ya murmusa.
cikin nutsuwa yake jan motar har sukayi ƴar tafiya babu wanda yaƙara magana,
Har ga Allah ta manta ma a inda take dan kuwa neman inda zata faɗi ta mutu take tayi matuƙar gajiya dan haka takejin kamar ya tsindima ta a Aljanna, bata farga ba sai buɗe ido tayi ta ga har sun wuce bakin titin sun ɗau hanya.
Zaro ido tayi tareda cewa, "Kalamillah ya haka?? kace titi zamuje kuma naga kana tafiya harda gudu ko dai siyardani zakayi??"
Sassauta gudun yayi saboda wata muguwar dariya da ta antayo Masa ba zato ba tsammani, abun ya haɗe masa biyu ga sauran kalamanta ga kuma sunan da ta laƙa masa wai Khalamillah.
Yanayin yadda yake dariyar yasa murmushinta suɓucewa murys ƙasa ƙasa tace, "dariyarka abun dariya wallahi"
Ɗan tsahirtawa yayi kafin yace, "ai kece kika bawa dariyar tawa dariya, yaushe na zama Kalamillah kuma ban sani ba?"
Ɗan turo baki tayi tace, "to ai naga baka son magana ne Salihi da kai"
Kallonta yayi kafin ya maida hankalinsa kan titi cikin murya me matuƙar jan hankali da sanya nutsuwa yace, "Ashshah? kin tabbatar kuwa?? ina ganin nafiki surutu fa, dan baki taɓa bani damar da zaki gane hakan bane"
Kai tsaye tace, "haba Ya Jose anya kuwa akwai wanda ze fini surutu a diniyar nan??"
yana Dariya yace, "shikenan Ashshah tinda kin rama"
murmushi tayi tareda lumshe ido sannan tace, "to wai ina zamuje ne haka?"
A nutse yace, "kinsan meyesa na ɗakko ki?? nasan kina son yawo a mota da daddare, ko ban faɗa dai-dai ba??"
Da mamakin yadda akayi ya iya gane hakan ta zuba masa ido har wani lokaci sannan ta rausayar da kai tace, "shikenan amma kasan dai bana fita tareda kowa idan na ƴan gidanmu ba ko?? kuma idan Mama ta neme ni fa me zance mata?? ka rufa min asiri ka maidani gida kaji Kalamillah?"
Ta ƙarasa maganar cikin sigar rarrashi.
Murmusawa yayi yace, "Mama kikeji ko??"
Gyaɗa masa kai tayi tana ƙara binsa da ido.
wayarsa ya kara a kunne duk da batajin me ake cewa sai dai kawai taji yace, "Umma dan Allah idan Mama ta nemi Ashsha ki gaya mata muna tare"
Shiru yayi kafin yaƙara cewa, "Umma cewa tayi na rakata fa"
Yayi maganar yana dariya tareda kasheta da idanunsa masu matuƙar yimata kwarjini.
Da sauri tace, laa? hakama zakace??"
Girgiza kai yayi sannan yace, "Umma tinda baki yarda ba sai mun dawo kawai zamuje taga gari ne su Rookayya sunƙi barinta ta huta"
Daga haka ya ajiye wayar yana cewa, "to yanzu ai ba matsala ko??"
Tace, "eh da sauƙi tinda bata yarda nice zaka raka ba"
.
murmusawa yayi yace, "yace bakya buƙatar wani abun kuma??"
Gyaɗa kai tayi a hankali tace, "eh"
Shiru ce ta biyo baya shikuwa sai tafiya yake, iskar dake kaɗawa ba ƙaramin tafiya da hankalinta take ba shiyasa ma batasan tafiyar tasu tayi nisa ba bare tasan lokaci ya tafi.
Buɗe idon da zatayi taga ya zaro bindiga ƴar ƙarama piston daga jikinsa yana ƙoƙari saƙalata a wani guri na motar.
dakatar dashi tayi da cewa, "dama kai ɗan ta,adda ne??"
Idanunsa ne suka ƙara girma ya waresu tasss akanta yana kallonta har na ɗan wani lokaci, shi a tunaninsa tayi bacci ashe lumbu lumbu ce, dariya yayi yace, "Ashshah rigima tayaya me yaƙi da ta,addanci ze zama ɗan ta,adda??"
Zumɓuro baki gaba tayi tace, "to ko kasheni zakayi??"
Ƙasan titi yayi da motar ya tsayar da ita cakk sannan ya kunna fitilat cikin motar ya kalleta sosai kafin ya murmusa gami da lumshe idanunsa, murya ƙasa ƙasa yace, "Ashshahh!!! idan na kashe ki ni kuma sai na rayu?? idan bakya duniya kenan ni miye amfanin rayuwata??, sai naji kamar na fashe da kuka Ashshah muna zaman lafiya me yakawo zancen mutuwa?"
Ɗan murmushi tayi a ranta tana mamakin yadda yake kashe murya yanai mata magana har wani lallaɓawa yake, ga irin maganganun da yake mata masu kama da jirwaye sai dai har yanzu bata gazgata faɗar Nuriya ba bata yarda sonta yake ba sai dai haɗuwar jini.
Jin shirun tayi yawa yasa yace, "mamaki kike ko??, bazaki mutu yanzu ba insha Allah"
Girgiza kai tayi da sauri tace, "a'a banyi mamaki ba, tab ni wacece da bazan mutu ba idan lokacina yayi?, ai ko yanzu ma a shirye nake"
Yace, "da gaske??"
Tace, "eh mana"
Murmushi me sauti yayi kafin yace, "da kuwa abun yayi armashi kinga idan na mutu gani ga ke labarin ze fi daɗin faɗa ko?? na shirya mutuwa tareda ke dan haka yanzu abunda za'ayi zamu fara tafiya a motar nan muna cikin gudu sai mu tari gaban manyan motocin nan da suke tafiya a titin ko?? kinga gobe da labari kenan"
Ƙyalƙyalewa tayi da dariya harda ƙwallah shi kuwa aikinsa ido ne tinda tafara ya zuba mata su sai dai murmushi yake wanda yake ƙara tabbatar da irin farin ciki da shaukin da yake ciki.
Sai da tayi me isarta sannan tace, "wallahi Ya Jose a gaisheka nidai kar naje tsautsayi ne yake nemana ko ajali wallahi mu koma gida".
Sai a lokacin ya ɗauke ido daga kanta tareda sauke sassanyar ajiyar zuciya sannan yace, "nifa nakasa gajiya da tafiya amma zan koma saboda ke"
Murmushi kawai tayi batareda tayi magana ba.
lokacin surutun nata ya wuce har suka dawo batayi masa surutun ba maganar ma sai jefi jefi.
Ƙoƙarin buɗe motar ta shigayi amma taji a kulle, marai-raicewa tayi tace, "Ya Jose dan Allah buɗe min mana??"
Langaɓar da kai yayi shima da yake gwanin shagwaɓar ne kamar yadda tayi magana haka ya mayar mata da martani da cewa, " to Ya Ashshah jirani mu fita tare mana"
Sake langwaɓewa tayi ta kwantar da kai a jikin kujerar tana ɗage gira ɗaya tareda cewa, "ohhh dan Allah kai sauri mana!!"
Ya gyara zama kafin yace, "to ko da kaina zan kaiki ne??"
Da sauri tace, "aa rufan asiri mana bawan Allah"
Fitowa yayi yana dariya cikin ransa yana jinjina mata akwai iya rigima ya daɗe da shaidar hakan, zagayawa yayi ya buɗe inda take zauna, dama jira take tayi zumbur ta fito amma ya tare mata hanya dole tafasa tafiya ta jingina a jikin motar tana jiransa.
Haka kawai yakejin kamar kar su rabu bayason barinta ta ƙara sille masa dan bayajin zasu ƙara irin wannan kasancewar.
Yana shirin yayi magana muryar Mama Hasiya da tazo wucewa ta katseshi , "au ɗana kaine anan?? wacece wannan ko sirikar tawa ce??"
Da sauri Aisha tace, "aa Mama Hasiya nice wallahi"
dariya Mama Hasiya tayi tana cewa, "ohh ashe ta Khaalif Mohammad ce kaima yakamata ka fito mana da taka"
Lokacin da tagama maganar tini ta wuce dan kuwa sauri take.
Suman tsaye Jose yayi yayinda zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri sauri lokaci ɗaya zuffa tafara keto masa ya ɗebi lokaci ba tareda yayi wani motsi ba sannan ya shafa kansa ya yarfar da hannu, takawa yayi sau uku yaƙara riƙe ƙugu sannan ya juyo yana kallon Aisha wadda mamakin yadda taga ya burkice ya hanata motsawa.
Matsowa yayi dafff da ita cikin razani da ruɗani yace, "Ashshah da gaske ne?? nasan ko yanzu ko anjima ko an daɗe da yawa da ƙaunarki zan mutu amma ban taɓa zaton itace ajalina ba, Ashshah idan kina soyayya da ƙanina Khaalif ni kuma ya zanyi da sonki da ya gama mamaye jini da tsoka ta?? "
Tsananin firgicin da ta shiga yasa takasa furta komai illa jikinta da yake wata irin kakkarwa kamar me jin sanyi kanta ya shiga juyawa zuciyarta tafara tsalle kamar me shirin ɓalle ƙirjinta ta fito.
Ƙara matsawa yayi daf da ita yayi mata rumfa, cikin rufewar da idanunsa sukayi yace, " kar kiyi mamaki da gaske nake karkiji kamar a mafarki tabbas rashin samun soyayyarki tartsatsin azabane ga rayuwata rasaki yafi komai haɗari gareni rayuwar zatayi min tsanani, na riga na haukace na ɗimauta da sonki tabbas idan narasaki zan haukace kiji tausayina ki tallafi rayuwata karki barni na shiga gararin duniya, ASHSHAH kece nutsuwa ta tabbas idan bana tare dake ni mahaukacine kuma mutum mara amfani, na faɗa wata rayuwa a yau saboda jin kina son Khaalif, bazan hanaki abunda kike so ba kuma bazanƙi haƙuri na rungumi ƙaddarata ba, abunda nake so kisa a ranki kawai shine zan mutu da tsananin so da ƙaunarki kuma zan rayuwa a cikin RINTSIN SONKI wanda ya zama babbar illa gareni, bazan iya dena sonki ba har sai bayan raina kuma idan bakya sona zan ɗauki haƙuri na barki da wanda kike so bazan shiga rayuwarki na tauye miki haƙƙi ba, amma INA SONKI Aishatul,Humaira"
shiru ya Ɗanyi sannan ya cigaba da cewa, "Gobe da wuri zan tafi saboda yanayin aikina ina fatan sake ganinki ko ganin ƙarshe ne zuciyata zata ɗanyi sanyi, zanje nayi jinyar zuciyata Ashshah"...
Daga haka yayi gaba yana haɗa hanya yabarta a wajen, idanunta da suke mata zafi kamar an watsa barkono ta zuba masa har ya ɓacewa ganinta, takawa tayi da nufin tafiya amma takasa jitayi ƙafafunta bazasu iya ɗaukarta idanunta suka dena gani sai duhu da ya mamaye su ga wani shu'umin jiri da ya ɗebeta tayi luuuuuu zata faɗi.
Da sauri Khaalif ya tareta tafaɗa kan ƙirjinsa, liff tayi kawai duk da batasan jikin me tafaɗa ba amma tasan tasamu madafa sai da tafara dawowa dai-dai sannan tagane a jikin mutum take, a hankali ta buɗe idonta ta zuba akansa.
cikin rawar baki yace, "Ayeesha meke faruwa haka?? wani abun akai miki??? menene gaya min"
Da ƙyar ta iya girgiza masa kai alamar ba komai ta ƙaƙalo murmushin gaibu ta ɗora akan fuskarta.
Ba tareda ya gamsu da abunda tafaɗa ba yace, "daga ina kike ke kaɗai haka? tin ɗazu nake nemanki ban ganki ba Ayeesha hankalina yaƙi kwanciya ina kika shiga, meye wannan da har yake miki irin wannan barazanar, hankalina baze iya jura ba Ayeeshah!"
Zamewa tayi daga jikinsa cikin rarrabewar kalma tace, "ba-cci na-ke-ji"
yace, "shikenan muje kisha ruwa amma naga kamar kinajin ƙishi, halama bakida lafiya kike ɓoye min"…
Kasa magana tayi sai lumshe ido kawai ga zuffar da tafara yimata wanka.
Jan hannunta yayi zuwa ciki can wani ɗaki da babu kowa ya nufa da ita sai da ya zaunar da ita a bakin ɗan madai-dai-cin gadon ɗakin sanna ya ɗakko mata ruwa ya miƙa mata, ta karɓa batareda ta jira komai ba ta shanye ta miƙa masa kofin, ta sauke wani gwauron numfashi sannan tace, "nagode"
tattausan Murmushi ya sakar mata tareda jinjina kai sannan yace, "inada damuwa fa Ayeesha kuma kece silar komai kuma kece maganin damuwar, Amma bazan gaya miki ba ki ki kwanta ki huta kawai"
*INDO CE..*
[7/5, 10:52 PM] INDO CE..: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IMbPeZwcVmK8hZ9UIJluKW
*💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 9*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
rintse ido tayi da ƙarfi tana girgiza kanta da ya kamu da wani azababben ciwo lokaci ɗaya, da ƙyar tace, "Khaalif nagaji da jura yau dai ka gaɗamin meye damuwarka da kake ikirarin nice silarta?? bazan iya bacci ba idan baka sanar dani ba dan hankalina yaƙi kwanciya"
Zama yayi a gefenta sannan yace, "kin shirya saurara??"
Da kai ta bashi amsa.
Ya cigaba da cewa, "damuwata ba komai bace face yawan rashin jiton dake tsakaninmu bayan daa, ba haka muke ba, meyesa kika sauya min Ayeeshah?? kin zaɓi ƙuntatamin hakan shine ke saki farin ciki wane laifin nayi miki me girman haka?"
Daurewa kawai take tana sauraronsa a yanzu batada burin da ya wuce ta samu gurin da zata raɓe tayi kuka saboda abubuwa iri iri da suke mata turnuƙu, kamar me koyon magana tace, "nima ba'a son raina hakan take faruwa ba amma ko menene ma laifinka ne"
Yace, "bazan musanta ba, iyakar abunda zance shine ta wace hanya zamu samu dai-daito?? meyesa kike wulaƙantani Ayeesha?"
Kamar zata fashe da kuka tace, "banaso kake irin wannan maganar banajindaɗi nifa ba wulaƙanta ka nake ba"
Yace, "nasani amma ba lallai kina tunanin yadda kike jefani cikin tsanani da hakan ba, kuka ya zamo abokin rayuwata a dalilinki damuwa itace al'ada da duk wasu ɗabi'u na a yanzu tunani shine abincin da nafi amfani dashi kafin komai, da tini fa wata rana sai dai ki wayi gari kiga babu Khaalif a dalilinki, nasha yin tunanin tafiya wata duniyar na nesanta dake amma idan na tuna hakan rashin adalci ne ga iyayen mu sai na fasa, saboda ke har banason idan na fita na koma gida saboda ke nakan tsiri tafiyar da zatayi tazara tsakanin mu, amma duk da hakan zuciyata takasayin sanyi koda yaushe ƙuna take amma hakan baya sawa ki tausayamin Ayeeshah kuma daa, ba haka kike min ba"
Shiru tayi saboda duniyar tunanin da ta luƙaƙa tausayinsa yasa zuciyarta taƙara yin rauni kasa ɗago ido ta kalleshi tayi saboda bazata iya haɗa ido dashi ba.
murmushi me ƙuna yayi kafin ya cigaba da cewa, "meyesa hakan take faruwa?? nasan daa, kina sona Ayeeshah meyesa yanzu kika tsaneni?? bakyason ganina kullum wulaƙancin da kike min kalarsa daban kamar ba nine wanda idan banci abinci ba hankalinki baya kwanciya amma yau kece me cewa bakida asara dan na kwana da yunwa daa, zato nake ko wani ke tunzura ki amma yanzu na gane karatun, a baya kin soni nikuma lokacin nakasa nuna miki irin son da nake miki a tunani na wannan dalilin ne ya kawo haka"
....
katse shi tayi da cewa, "ka ma dena wannan tunanin ba shine dalili ba"
Gyara zama yayi yana fuskantar ta sannan yace, "zaki gaya min??"
Girgiza kai tai alamar "aa"
Ya ƙara da cewa, "Ayeesha wallahi ban taɓa ƙinki ba ƙaddarace tasa nakasa saurarar soyayyarki har lokacina yaƙare, lokacin akwai wadda nakeso ita ko sani ma batayi ba inason sanar mata amma nakasa har sai da lokaci yayi tsawo kuma abun kaico Ayeeshah tace bata sona, kai tsaye na ɗauki hakan a matsayin hukunci na na yin wasarere da soyayyarki Ayeeshah daga lokacin hankali da mutsuwata ya dawo kanki sai a lokacin na tabbatar da ke nakeso ba ita ba kuma lokacin kin fara sarewa daga gareni