Showing 6001 words to 9000 words out of 29481 words
sauke sannan yace, "nagode sosai Umma Allah ya jiƙan mahaifanki"
Ta amsa da amin tareda ture shi daga jikin ta tana cewa, "do Allah ɗaga ni kana neman karya min kafaɗa, wai Jose duk ina wannan kunyar taka??"
Da sauri ya ƙara rungumeta yana cewa, "Umma dan Allah kiyi shiru"...
Ta murmusa gami da cewa, "fatan nasara YUSUFU Allah yai mana jagora"
Sosai Jose yaji daɗin ƙwarin guiwar da ya samu daga mahaifiyarsa dan haka yasha ɗamba ya gyara ɗamarar tinkarar guguwar dake gabansa.
ABU.
Yanzu bashida ishashshen lokacin da ze ware yaje gidansu Aisha gashi da ko wace Sa'a tunaninta da kewarta ƙara yawa suke gareshi dan haka ya yanke shawarar neman lambarta.
a yanzu tunaninsa ɗaya waye ze bashi lambar??
a gurin wa ze same ta???
ko dai ya nemi Rookha ta bashi??
anya kuwa idan yayi haka yayi adalci??
shin idan ya tambayi Khaalif Mohammad ta wace fuskar ze fahimce shi???.
(KU BASHI SHAWARA FANS ƊINSA😂)
*INDO CE..*
[7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 5*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
Ya daɗe yana neman lambar amma be samu ba duk wanda yake tunanin ze samu a gurinsa sai yaji babu har ƴar rama sai da yayi, sai daga baya ya sallama, wayarsa ya ɗauka ya turawa Khaalif Mohammad kira sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka, a tare sukayi sallama kafin Khaalif Mohammad ya amsa, ABU yace, "yagida?"
murya a cunkushe yace, "lafiya lau Bro"
Shiru ce ta biyo baya, ya shiga tunanin ta yadda ze shawo kansa cikin sauƙi haka kawai ya tsinci kansa da lafta masa ƙarya yace, "Hajja ce dama takeson yin magana da Mama kuma na nemeta ban samu ba ka turo min lambar Eeeshu"
Shiru Khaalif Mohammad ya ɗanyi sannan yace, "ok bari kawai idan na koma gida zan kira ka"
Cikin ƙarfin hali ABU yace, "idan kuma sauri ake kenan sai an jira ka??, ka turo min kawai ai nasan da hakan nace ka turo min ko??"
Badan ransa yaso ba yace, "to shikenan zan turo maka bata son a dinga rabawa mutane lambarta ne shiyasa, naji kamar ranka ya ɓaci kayi haƙuri"
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ABU ya sauke tareda rintse idonsa har ga Allah yana tausayin ɗan uwansa sai dai shima abun a tausaya masa ne, "ina jira" kawai ya iya cewa ya kashe wayar.
Khaalif mohammad ya raka wayar da ido yana mamakin abunda ya faru haka kawai yakejin kamar be gamsu da maganar ABU ba amma yasa a ransa koma menene Allah ya fishi sani dan haka ya fauwalawa Allah..
Ba wani ɓata lokaci lambar ta shigo murmushin farin ciki ne ya ziyarce shi, har ya tura kira ya fasa saboda idan ya kira ta a yanzu ma bashi da abun cewa.
koda Khaalif ya dawo gida suna Hira da Mama yace, "kunyi waya da Hajja ɗazu ko??"
Da ɗan mamaki tace, "Hajja kuma yaushe kenan?"
Cikin sauri yace, "Mama Hajja fa ɗazu ABU yace na bashi lambar Ayeeshah zakuyi magana da Hajja"
Mama tana shirin tayi magana Aisha ta fito ciki hanzari tace, "ya kira ni kuma lokacin bacci nake nace ni bazan tashi ba kuma kowa ma yasan ba son bada wayata nake ba ato"
Taƙarasa maganar cikin sigar ko in kula.
Ba Khaalif kaɗai ba Mama kanta sai da tayi mamakin hakan da Aisha tayi kuma tana gama maganar ta shige ɗaki duk suka rakata da ido.
Tana shiga ɗakin ta jingina da bango tana rintse idanunta da ƙarfin gaske, wayyo Allah na wai ni kaɗaice mace a duniya da kowane namiji yake ƙoƙarin fakewa dani??, shi yazo ya tirke ni da maganar aurensa, kai kuma ka damu dani a lokacin da na cire sa rai na da kai, ga ɗan uwanka yana neman jefa kansa cikin wani ƙangin duk a dalilina, ina tsoron Yaya ABU ya zama silar tarwatsewar ZUMUNCI DA AMINTAR dake tsakani na da Rookha, ina cikin firgici ina cikin wata rayuwa Allah ka kawo min mafita"
Zamewa tayi tai zaman daɓaro a wajen tareda fashewa da kuka.
Sayid tareda Khaalif har gware suke wajen shigowa ɗakin yayin da Mama take bayansu.
A matuƙar gigice Khaalif mohammad yake tambayarta abunda ya faru.
Ganin sun shiga ruɗani yasa ta dena kukan ta share ƙwallar tareda danne duk wani ƙuncin da takeji tafara ƴar dariya.
Sororo suka tsaya suna binta da ido, a marai-rai-ce Khaalif mohammad yace, "Ayeeshah meke faruwa??"
A shagwaɓe tace, "wallahi Mama tiles ɗin ɗakin nan mugu ne kawai daga shigowata ɗaki ya zameni na faɗi kuma sai da na buge kaina a bango"
Ɗan murmushi khaalif mohammad yayi tareda cewa, "Ayyaa Allah sarki ƙanwata sannu banji daɗi ba gaskiya be kyauta ba, dama ni ya kayar ba ke ba amma karki damu ki dena yi masa kuka kar ya raina ki"
Mama kuwa tsaki ta ja ta taɓe baki sannan tace, "to kuwa Allah ya shirya ku dukan ku kaima da taya ɓera ɓari, bata bugun bane da har ta samu bakin yiwa mutane ihu kamar wata yarinya ko mahaukaciya"
Da sauri tace, "Mama ina ganin fa kin faɗi gaskiya dan wani lokacin ji naje kamar na haukace ya kamata ku kaini asibiti naga likitan ƙwaƙwalwa tunani sun sa na fara zaucewa Mama"
Zuwa yanzu Mama riƙe haɓa tayi saboda abun yafara girman kanta.
Khaalif kuwa da yake akwai ƙarfin hali da juriya sai da ya dara sannan yace, "shikenan tashi muje dama na daɗe ina tunanin hakan ashe da gaske ne kina buƙatar likitan hankali"
Yayi maganar cikin sigar zolaya.
Harara ta buga masa taja tsaki kafin tace, "kaga wa kake da suna? Khaalif ko? idan kana neman mahaukaci kaje can ka duba amma ba'a gidan nan ba, bana son dattin ƙwaƙwalwa"
Harara Mama ta zuba mata hakan yasa tayi gim da bakinta ta miƙe tana karkaɗe karkaɗe ta koma gado ta kwanta.
Khaalif ya murmusa tareda cewa, "haka dai aci a ƙoshi a kwanta ba aikin fari ba na baƙi"
Ta murguɗe baki tace, "daɗin ta dai ba wani ne yake yin abincin da kuke ci ba, kuma lokacin da zanyi aikin ba gayyato ka zanyi ko nace dole sai ka sani ba dan haka karka samin ciwon kai ka fitarwa mutane daga ɗaki ko kuma ni na tashi na fita"
sim simm yayi ya fita dan baya son abun yayi tsauri yanzu sai ta ƙare masa rashin mutunci tinda tsakiyar kai har tafin ƙafa.
ABU yana zaune sai saƙi da warwara yake har wani ɗan lokaci sannan ya ciri waya ya tura mata kira.
Tana cikin jin waƙa ta saka iyafis kiran ya shigo bata tsaya dubawa ta ɗauka tareda yin fakare dan taji waye me nemanta.
sassanyar muryarsa ce tayi tafiyar mashi da ita lokacin da ya rangaɗa mata sallama, sai da numfashinta ya ɗan tsaya kafin ta sauke ajiyar zuciya ƙirjinta na bugawa, sai da ya kuma yin sallamar sannan ta amsa a sanyaye.
Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, "ina gaisuwa Queen Eeeshu barka da wannan lokaci"
A daburce tace, "barka dai yagida?"
Yace, "gida lafiya lau sai godiyar Allah ya Mama? ya jiki jikin nata??"
Tace, "taji sauƙi sosai bari na kai mata wayar"
Da sauri ya dakatar da ita da cewa, "Eeeshu ke nake nema dama kice ina gaisheta cewa nayi tinda bakya nema na ni bari na nemeki"
tattausan Murmushi me sauti ta saki sannan tace, "Ya ABU!! to amma dai bazance komai ba dan kuwa ka fini gaskiya nagode da tunawa dani"
jin tana ƙoƙarin kashewa yasa yayi saurin dakatar da ita,
yace, "idan na manta dake tamkar fa na manta kaina ne kinga kuwa daga lokacin na fita daga sahun masu hankali, Eeeshu har yanzu kin kasa sakin jiki dani kamar baki sanni ba? amma nasan ba haka kikewa Khaalif mohammad ba ai"
ƴar dariya tayi tace, "to ai nafi sanin Khaalif ɗin ne shiyasa kaifa sai yanzu nasanka amma daa labarin ka kawai nakeji"...
murmusawa yayi har sai da haƙoransa suka bayyana sannan yace, "tab gaskiya ba haka yakamata ayi ba, ni na riga khaalif Mohammad zuwa duniya dan haka ni yakamata kifara sani kafin shi"
Dariya tayi tareda cewa, "gaskiya kana da abun dariya, ga wanda nafara buɗar ido na gani ga kuma wanda zan fara sani, beyi maka kama da tatsuniya ba kuwa???"
yanayin yadda take maganar yafi komai ɗaukar hankalinsa ba shiri shima yafara dariya kamar yadda takeyi, jin tayi shiru yasa ya sauke numfashi sannan yace, "ko ɗaya yafi min kama da wasa amma, ni nasan Khaalif ya riga ya mamaye duk inda nake tunanin za'a tsakura ni nasan kinfi shaƙuwa dashi har cikin rai"
..
da sauri tace, "a'a a'a rufamin asiri Khaalif ɗin da baya son ganin farin ciki na??""
Ido huɗun da sukayi dashi ne yasa tayi saurin haɗiye sauran maganar tana ƙwalala masa ido.
kallon mage da ɓera suka shiga yiwa juna kafin ya matso tareda miƙo mata hannu yace, "mugani keda waye???"
Kallon wayar tayi taga har zuwa lokacin ABU be katse ba da sauri ta katse ta bankaɗa cinyarta ta jefa wayar sannan tasauke ɓoyayyar ajiyar zuciya a dake tace, "ai ba taka bace tawa ce"
Yace, "na sani kawai gani zanyi naji ana ambaton sunan marayan Allah bansan laifin da na aikata ba"
Murmushin gefen baki tayi tace, "cewa tayi Ayeeshan yaya Khaalif shine na faɗa mata gaskiya ko ƙarya nayi??? gaskiya ce ba son ganin farin cikina kake ba idan kuma kanada hujjar kare kanka to??"
Durƙusawa yayi kan guiwarsa yana fuskantar ta, kamar ze fashe da kuka yace, "Ayeeshah wallahi ban taɓa yin wani abu da gayya dan ɓata miki rai ba kuma bana fatan nayi wannan daga yanzu har zuwa lokacin da raina ze bar gangar jikina, ina son farin cikin ki sai dai bansan meyesa kika zaɓa mana irin wannan rayuwa ba, ina amfanin na ƙuntata miki kin ƙuntata min kenan rayuwata batada wani amfani Ayeeshah ko meye nayi banayi miki dai-dai abunda nake sa ran ya saki farin cikin sai naga ya saki ɓacin rai ƙanwata wai shin ni kaɗai ne mutum mara sa'a da ya kasance haka a duniya?? bana iya yiwa mutum abunda ze faranta masa kenan?? shiyasa wani lokacin nakanji inama ni ba rayayyen mutum me tsawon rai bane inama na mutu tin kafin na sanki Ayeesha, bana jin daɗin ɓata miki rai da nakeyi sai naji bazan iya yafewa kaina ba"
Ido ta zuba masa jikinta yayi matuƙar sanyi takasa furta masa ko uffan sai hawaye da suka cika idanunta.
Jin shirun nata yayi yawa yasa yace, "Ayeesha hakan ma ya ɓata miki rai ko?? kice wani abu dan Allah"
Murmushi me ɗauke da wani Sirri ne ya wanzu akan fuskarta ta kauda kai tareda cije gefen leɓenta ta girgiza kai tareda cewa, "a'ah banida abun cewa ne indai kaji nayi shiru kasan dai baki na sai kace Reza haka yake idan kaji be furta ba to be samu abunda ze faɗa bane, karka wani damu kanka idan natashi magana wata ma ko ni kaina sai na faɗa nake ganewa" Murmushi ta sakeyi kafin tace, "ya akai yau ka dawo da wuri??"
ƙululun da ya tsaye masa a maƙoshi ya haɗiye da kyar sannan yace, "nima kaina ban zata haka ba kawai canjin yanayi ne, ni bari naje waje dama Mama ce tace na tambaye ki ina kika ajiye mana mukullin ɗakin mu"
Tace, "uhm bansani ba, sai dai ka tambayi Sayid "
Miƙewa yayi tareda cewa, "shikenan"
a daddafe ya fita sai faman cizon leɓensa yake yana rintse ido, duniya rawar ƴan mata wannan tayi gaba wannan tayi baya to shima misalin haka rayuwar ta gara masa, zuwa yanzu ya yarda babu yadda za'ai Ayeeshah ta yarda da duk wata hujjar da ze faɗa mata da sunan ba dan gayya yake mata wani abun ba, be ƙi ba ko ranar da ya furta mata asalin abunda ke ƙunshe a zuciyarsa sai dai bayajin ranar zata zo, bata bashi damar da ze iya bayyanar mata da hakan.
ABU.
Murmushi me haɗi da ƙwallane ya suɓuce masa cikin ransa yana cewa, "Khaalif Mohammad sai dai muyiwa juna uzuri SO yayi tafiyar ruwa da yayanka na riga na sabauta da Son Eeeshu ina kuma matuƙar kishinta".
Jose. da ABU suna zaune suna hirarsu irin ta abokai Jose yace, "ABU.......
(banson gulma😒 kun wani buɗe kunnuwa kuji zance to sai a shafin gaba🤭🤭🤭😂)
Share da Sharhi pls
Takun Nan Dai…
MARUBUCIYAR✍🏿✍🏿✍🏿...
SIRRIN ƘETA
A JINI ƊAYA
TAJMAHAAL paid book.
IB ƊAN WANKA😂
tareda...
RINTSIN SO.
*INDO CE*
[7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖*
(Wa nake SO???)
*Shafi na 6*
Aƙalamin
*INDO CE..*
ELEGANT ONLINE WRITER'S
*Bismillahirrahmanirrahim*
Yace, "ABU bani lambar Ayshan Mama mana"
Kafeshi yayi da ido yana masa kallon tuhuma ba tareda ya nuna masa komai ba yace, "kayi me da ita?"
Ƙasa ƙasa ya sakeyi da ido kafin yace, "kai me kake da ita?? banson iskanci fa ko ka fini kusanci da ita ne?? yadda kakejin kai ɗan uwanta ne haka nima nakejin kaina dan haka idan zaka bani bani idan bazaka bani ba ka faɗa da manyan baƙi".
ABU yace, "daɗi na da kai fa saurin hawa daga tambaya sai zarar zance? ta jina ban fika kusanci da itaba amma a zahirance nafika tinda kai ko lambarta bakada yanzun ma be zama lallai idan amfani kanka bane, to bazan bayar ba idan zaka nema da kanka ruwa ya rage naka, har ɗan wuya nayi saboda neman lambar nan dan haka bazan bayar ba"
Jose yace, "haka kace ko??"
ABU yana dariya yace, "eh idan kana shakka ma ka dena inason ganin wane lokaci zaka ɗauka kafin ka samu dan na lura lambarta ba gama gari bace, Hala ma su Salma ke neman ta??"
Shiru Jose yayi yana ɗan tunanin ko dai ya faɗawa Aminin nasa gaskiya?? wata zuciyar tace a'a kabari kafara samun kanta tukunna sai kaji daɗin faɗe, lumshe ido yayi sannan yace, "eh tinda su kaɗai ne mutane ba?"
ABU yace, "dama na sani ai, tashi mu fita mana nagaji da zama"
Jose yace, "to tafida ni kuma banajin zuwa ko ina doka ta hanani yawo dan haka sai ka dawo"
Komawa yayi ya zauna tareda cewa, "saboda nine gantali daɗi ko abi doka a zauna lafiya??"
Dariya Jose yayi yace, "bari kawai ABU Ni ke tausayin doka amma ita bata tausayi na, jiya ma nasha wahala a aiki wallahi sai ka tausaya min wani bincike suka bani me ɗaure kai ba shiri na sambaɗa musu ƙaryar rashin lafiya nayo nan sai litinin nake tunanin komawa aiki ka'in da na"in"
ABU yace, "Allah sarki abokina Allah ya bada nasara"
Jose ya amsa da "amin"
Haka suka cigaba da hira cikin nishaɗi batareda ɗayan su ya gane cewar ɗan uwansa yana son abunda yake so ba, kasancewar babu wanda ya taɓa zaton ko da wasa hakan zata faru yasa ko tunanin abun ma be zo musu ba dukansu, shi dama ABU idon hangensa yafi sauka akan Khaalif, shi kuwa Jose ji yake tamkar shi kaɗai ne mutum da yake sonta duk duniya dan yana jinta ne tamkar itace rayuwarsa hankalinsa da tunanin sa kuma yasa a ransa babu wani mutum da zeyi mata irin son da yake mata har abada, shiyasa baya ma tunanin komai idan ba nata ba.
Yau sosai Azumin yake wahalar da ita tayi shawal da ida ko tafiya ma da ƙyar takeyi sai bin katifa idan kuwa a tsaye take to tana jikin bango, Khaalif Mohammad yana shigowa yayi tozali da ita yafara yimata dariya, ko kallonsa batai ba dan kuwa ƙara mata ɓacin rai yake dama haushin kowa takeji, bayan sun gaisa da Mama ya ɗakko kujera musamman ya zauna harda tagumi ya zuba mata ido abun yayi masa matuƙar daɗi yadda take zumɓure zumɓure da murguɗe murguɗe shi yafi tafiya da imaninsa, shi sai yaga ma ta ƙara kyau hancin nan nata yayi wani zuwait dashi idon sunyi firi firi duk da ba ƙaunar buɗe su wanwar take ba.
Ita kuwa kallon nata ma da yake jitake ina wuta kusa ta jefashi ko zata huta da takaici, batada bakin yimasa magana dan haka ta fashe da kuka tana cewa, "wallahi Mama kiyi masa magana Allah idan nayi masa abunda ze zo yana kuka kar kiji haushina, wallahi badan ina tausayinsa ba da sai na hanashi shaƙar iska me daɗi a duniyar nan"
Taƙara ɓarje baki ta cigaba da kukanta ido rufe.
Mama tace, "tofa? a dalilin me?? har wane laifin yayi miki da zakice haka bana hanaki maganganun banzar nan ba wai???"
Tace, "kina gani fa dariya yake min kuma sai nayi masa abu yaje yai ta ƙunci ko?? badan ina tausayin ka ba Khaalif da ka ɗanɗaba kuɗar ka wallahi"
Cike da tausayin kansa yace, "Ayeeshah kiyi haƙuri iya hakama ya isheni badan ina da tsawon rai ba fa da tuni na haɗiyi zuciya na mutu Ayeeshah, dama bakyason gani na ai